Showing 90001 words to 93000 words out of 104561 words

Chapter 31 - Exiled Prince Book 3 Hausa Novel Complete

Meerah   

13 Dec 2024

399

"

" na sani momy , amma shi za a nada , dan na san Bayan shi babu wanda zai iya rike min ahalina , na san zai kula da masarautar nan kamar yadda ni zan kula da ita , na yarda da Diya fiye da rayuwata , ba dan shi ba da yanzu ban san inda zan tsinci kai na ba , ba dan shi ba da ba zan taba haduwa uncle bare har ya ba ni auren Cutie , duk wani abun al'heri da ya same ni cikin rayuwata shi ne sila , shi ya sa na yarda da shi fiye da rayuwata , he is my best and ONLYfriend's , He is my Brother not my Cousin , dan haka ya na da ikon hawa kujerar Malik "

wani dan karamin murmushi MALIKAT AL'UMU ta saki kafin ta ce " ka tabbatar shi ne abun da ka ke so ? "

" na tabbatar momy " ya fada kai tsaye

" shikenan , amma kar ka fadawa kowa maganar nan , har ranar nadin "

" okay momy " ya fada ya na mikewa tsaye

da sauri MALIKAT AL'UMU ta ce mishi " ina kuma za ka tafi ? "

" ina son na ga babyna kafin mu tafi mosque lokacin sallat ya yi "
da to kawai ta amsa , da ga haka ya sa kafa ya fice part din

har ya nufi hanyar word room a ka fara kiran sallat , kawai sai ya juya ya nufi mosque dan ya yi sallat

bayan sun yi sallat , Diya ya ja hannunshi ya nufi part din shi da shi , sai tambayar shi Malik ya ke me ya faru , ya sake shi
amma ko sauraron shi Diya ba ya yi , su ka shiga part din shi

sai da su ka shiga cikin dayar bedroom sannan ya saki hannunshi , ya meda kofar ya rufe , ya saka mata security

Malik na ganin haka ya ce mishi " wai lafiya ka kawo ni nan , ina son na je na ga babys di na , ka wani kawo ni nan har da rufe kofa "

cikin sanyin murya Diya ya ce mishi " please , ka tsaya akwai wata magana da na ke son mu yi "

wani dan karamin tsaki Malik ya yi ya na fadin " magana ba za ka iya yi min ita ba a mosque sai ka kawo ni har nan ? , wlh ba ka da hankali , ban hanya na wuce " ya fada ya na nufar kofar dakin

da sauri Diya ya riko hannunshi ya janyo shi bayan da karfi ya na fadin " please Nawfel , ka tsaya wlh maganar mai mahimanci ce , don girman Allah ka tsaya " ya fada ya na marairaice fuska

wani dan karamin tsaki Malik ya yi ya na fadin " okay , ina jin ka , amma yi sauri "
wani dan karamin murmushi Diya ya yi kafin ya gyada mishi kai

a hankali ya lumshe idanunshi a fara motsa lips din shi kamar ya na karanto wani abu
a hankali skin din shi ta fara sauya launi , ta koma wani launi shi ba green ba shi ba yellow ba , scales su ka fara fito mishi , nan take skin din shi ta koma irin ta maciji , a dubu dari Diya ya bude idanun shi dai'dai lokacin da ya koma wani babban maciji , amma yanayin jikin shi da tsawon shi duk dai'dai yanayin jikin shi Diya ne da tsayin shi , sai wutsiyarshi a baya ta na motsi

" inallillahi wa'ina illaihi raji'un " Malik ya fada da karfi har ya na yin baya ya fadi , ya na zaro idanu ya na kallon macijin da Diya ya koma zuciyar shi na duka uku uku , ganin abun ya ke kamar a mafarki

a hankali ya bude baki lips din shi har kerma su ke ya na fadin " Diya ! " ya furta lokaci guda

ya na gama fadar haka ya ga A hankali skin din macijin nan ta sauyawa , sannu sannu har ya bace Diya ya dawo tsaye

a hankali ya zauna a kassa ya yi irin zaman cin tuwo ya sunkuyar da kai murya a sanyaye ya ce " na je na kira ka mu tafi mosque dan lokacin sallat ya yi , amma ban gan ka ba a part din MALIKAT HOUDA , shi ne da na tambaya , a ka ce min ka na part din MALIKAT AL'UMU , na je part din zan shiga na jiyo Muryarka ku na magana da MALIKAT AL'UMU , na ji abun da ka fada mata , ka yi hakuri na boye maka wannan sirrin tsawan shekaru , just na rasa yadda zan iya fada maka ne , na san duk lokacin da ka san ya na ke ba za ka taba ci gaba da yarda da ni ba , that's why ya bunne abu na , amma bayan na ji abun da ka fadawa MALIKAT AL'UMU shi ne na yanke shawarar fada maka "

" ya Salam " Malik ya fada cikin zuciyar shi , ka fin ya bude baki ya ce " kai , kai ma tsafi ka ke yi ? kamar Aymane ? "

da sauri Diya ya dago kai , nan Malik ya ga hawayen da ya ke zubar wa
da sauri ya ce mishi " No , ba na tsafi , duk zaman da mu ka yi da kai ka taba gani na na yi wani abu mai kama da tsafi ? "

a hankali Malik ya girgiza mishi kai allamun a'a kafin ya ce " ta ya a ka yi ka ke zama wannan abun kai ma , kenan ka na sane da Aymane shi ma ya na zama hakan ? "

dan jinkirtawa Diya ya yi kafin ya ce " tsinuwar macijiya ce a kan ahalin Abdoul Mujeeb , lokacin da mahaifin mu ya hau mulkin masarautar Ottoman ya yi kokarin kara fadada girman masarautar , akwai wani fili da ga bayan masarautar , kawai sai ya ce a sanyo shi cikin Daular , a yi sabin gine² a cen , ashe wajen snake's nest ne , lokacin da ya samu labarin wajen gidan macizai ne kawai sai ya tura a kashe duk macizan , haka ko a ka yi , amma abun da ba su sani ba , sarauniyar macizan mayya ce , kafin ta mutu sai da ta tsinewa Ahalin Abdoul Mujeeb , duk yaran da zai haifa za su zo rabi maciji , rabi mutum , kuma haka a ka yi , ba Aymane kadai ba , duk yaran Abdoul Mujeeb mu na iya komawa wannan macijin da ka gani na koma yanzu , amma na Rouksar daban ne , dan duk lokacin da idanunta su ka koma na maciji a ka yi katari wani ya kalli cikin su , to sai ya koma status har sai ta yi mishi kiss sannan ya dawo dai'dai , shi ya sa ma mu ke kiran ta da Medusa , ina da shekara 17 na fara komawa wannan macijin , abun ya yi matukar ban tsoro , da na fadawa Daddy shi ne ya ke ban labarin yadda a ka yi na zama macijin , da na ji hakan kawai na ji na tsani masarautar , shi ya sa ma na daina zama cikin Saudiya baki daya , na koma UK da zama , idan na gaji na tafi Dubaï ko Jordan ko Asia , tsakanin wadanan gariruwan hudu na kammala karatu na , shi kuma Aymane nashi macijin daban ya ke shi ma , saboda shan jinin mutum ya ke , mutanan ma sai mata , ba yin da Daddy bai yi ba dan ganin Aymane ya daina shan jini amma ya kassa , har ya kai ya gogawa Rouksar shan jini , ba tare da sanin shi ba , ga shi kuma ya koyo yin tsafi , da ya ga abun ya fara gagara shi ne ya tura shi kassar Rouma wajen wani babban masanin tsafi dan ya cire wannan macijin da ke jikin Aymane , amma ya kassa asali ma tsafin shi sai karuwa ya yi , babu yadda ya iya ya sa mishi ido har ya girma a haka , ba zan maka karya ba , lokacin da Aymane ya yi kokarin kashe ka shekara bakwai baya , ina sane , saboda na zo wucewa na ji ya na maganar , dalilin da ya sa ma na shigo masarautar Saudiya a ranar dan na cece ka , amma ina shigar ta kai ne mutum na farko da na ci karo da shi , ba karamin sanyi na ji ba ganin ka a raye , shi ya sa ma na hakura na bi ka Nigeria , saboda ina tsoron Aymane ya cutar da kai idan ya samu labarin ka na raye , na san ka manta amma ni na sani , duk lokacin da ka je kai wa papi Ziyara a Daular Ottoman kai da Tesnim , sai Aymane ya yi kokarin kashe ka , amma bai taba yin nassara ba , akasin da a ka samu , duk lokacin da ka ke zuwa Daular ni ba na nan , shi ya sa ba ka san ko ni wanene ba ranar da mu ka hadu , tun lokacin da na sauke idanu saman Baby na san ta na da aljanu , na san kuma Malik ya shiga jikinta ya ce maka dole sai ka fara karaya tsafin Aymane sannan za ka iya kashe shi , ko kuma ka cire mishi kai , ni na san inda Aymane ya boye sihirin shi , amma ba zan iya fada maka ba , saboda a jikin RIANNA ya boye shi a ranar da a ka yi auren su , hakan na nufin sai ka kashe RIANNA , shi ya sa na ja bakina na yi shiru , bare kuma ba ni da tabbacin za ka yarda da ni , mistake daya a ka samu Aymane ya koma maciji a gaban ka , da ni ma ba zan fada maka ba saboda ya na daya da ga cikin abun da ba na son tunawa a cikin rayuwa , dalilin da ya sa ma na yi bincike a kan yadda zan cire macijin da ke jikina , kuma Alhamdoulilah ya na fita a hankali ta hanyar karatun kur'ani da sallar dare dan macijin ba ya son adini , da farko girman shi ya kai irin na Aymane , ka yi hakuri na boye maka wannan abun tsawon shekaru but i don't know how to explain you , i'm just afraid idan na fada maka ka ji ka tsane ni ba zan iya jure hakan ba , I'm so sorry " ya fadi na karshen kamar zai yi kuka


sai da ya dan jinkirta kafin ya ci gaba da fadin " lokacin da a ce ka sha poison , lokaci guda na san da Rouksar ce , dan ita kadai ke da poison , ba rokon da ban yi mata ba a kan ta ba ni antidote , ka yi hakuri har alkawari na yi mata idan ka tashi za ka aure ta , amma fir ta ki , ta na cewa idan ta ba ni kashe ta zai yi , na tambaye ta wa amma ta kassa fada min saboda ya rufe bakin ta da tsafin shi , sa'ar mu guda aljanun Baby sun tashi , ba dan haka sai dai ka mutu dan antidote din poison din ta , yawunta ne , ka yi hakuri ahalina ya cutar da kai dayawa , please ka samu wani gurbin a zuciyar ka ka yahe min , na san ko na mutu ruhi na ba zai samu salama ba idan ban fada maka gaskiya ba "


❤⚘ EXILED PRINCE ⚘❤

( LOVE MEETS POWER ) 👑🔥




( A heart touching love story , Romance , injustice & destiny )




STORY & WRITTEN BY : MEERAH ⚘🕊


【THE ROYALTY LOVE ❤🌹】



【 BOOK ________3 📚✍💌 】





_______________________♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡______________________




{ P A G E ________ 29 ✍💕🔥}






wata nanauyar ajiyar zuciya Malik ya sauke kafin ya mike tsaye , ya na kallon Diya da ya tsare shi da ido ya na hawaye

a hankali ya tako gaban shi ya tsaya , sannan ya mika mishi hannu
wani cool murmushi Diya ya saki kafin ya dago hannun shi a hankali ya daura saman na Malik kafin ya mike tsaye

ya na mikewa tsaye Malik ya kai hannu ya goge mishi hawayen shi ya na fadin " ni wlh na zata wata babbar magana ce za ka min , kawai dan ka yi zaune ka min kuka ne , ko dadi ya yi maka yawa ne ? "

" ta ya za ka min irin wannan maganar bayan abun da na fada maka "

a hankali Malik ya janye hannayan shi , kamar wanda bai san komai ba ya ce " me ka fada min , ni ban ni abun da ka fada ba " ya kai karshen ya na nufar kofar fita dakin

da sauri Diya ya riko hannunshi ya na fadin " kar ka tafi ba ka ce min komai ba don Allah "

a hankali Malik ya juyo ya ce mishi " don Allah malam tun dazu ka kawo ni nan ka tsaya ka na min kuka kamar wani karamin yaro , ni fa ina son na je na ga babys di na "

" ka na nufin ba ka ji abun da na fada maka ba ? " Diya ya fada cikin rudu

" yeah ban ji ba , ban kuma gani ba , zan iya tafiya yanzu ? "

wani cool murmushi Diya ya saki dan ya gano abun da Malik ke kokarin yi
a hankali ya saki hannunshi ya na fadin " shikenan tafiyar ka , ni barci ma na ke ji "

" na gode " Malik ya fada a takaice kafin ya juya ya cire security din kofar ya fice ya bar Diya nan tsaye ya na sakin murmushi
dama ya jima ya na son ya fadawa Malik wannan maganar amma ya rasa ta ina zai fara , amma yau ya samu kwarin guyiwar fada mishi , kuma ya ji dadi da Malik bai dauki abun wani iri ba , ya san da wani ne zai yi mishi wani kallon daban har ya yi kokarin kashe shi , amma Malik ko ajikinshi , shi ya sa ya ke Alfahari kasancewar shi dan uwa kuma amini ga Malik



▪MALIK


bakinshi da Sallama ya shigo room din da Inaya ke konce , nan ya tardo ta zaune saman gadon , ta na rike babynsu wata nurse na gwada mata yadda za ta ba shi nono
har ya karaso wajen ba su lura ba , a hankali ya yi musu gyaran murya ya na fadin " za ki iya tafiya "
ba musu nurse din nan ta fice ta ba su waje
ta na fita ya janyo chair ya zauna bakin gadon ya na kallon Inaya
ta na ganin ya zauna ta turo mishi dan bakin nan nata ta na shirin magana ya riga ta cewa " no please kar ki min wannan shagwabar taki a gaban babyn mu "

ai ko sai da ta yi mishi shagwabar ta na fadin " ka ce mishi ya sake ni , zafi na ke ji "
" ki bari idan ya ishe shi zai saki " ya na gama fadar haka ko babyn ya sake mata nipple
wani dan karamin murmushi ta saki ta na kallon shi
a hankali Malik ya kai hannu ya dauki babynshi , wani dan karamin murmushin geffen fuska ya saki lokacin da idanunshi su ka sauka cikin na babyn shi

ya na a haka ya jiyo Muryar Inaya ta na fadin " la baby , da gaske murmushi ne ka ke ? " ta fada ta na dan leko face din shi
a hankali ya dago ya dago babyn ya kai bakinshi wajen kunnen babyn ni dai ban ji abun da ya ke fada ba

sai da ya gama sannan ya sauko babyn ya kalle ta ya ce " ba za ki gane ba , i'm just Happy to day , specially da ba abun da ya same ki "

marairaice mishi fuska ta yi ta na fadin " amma yaya Zayd ba za mu sake samun wani babyn ba ko ? wlh sai da na ji kamar zan mutu sai da na dinga ganin wutar lahira "

maganar ta ba karamar dariya ta so ta bashi ba amma ya danne kayanshi ya saki wani dan karamin murmushin geffen fuska ya na fadin " don't worry , Nayel kadai ya ishe mu , bayan shi ba kari "

wani cool murmushi ta sakin mishi kafin ta ce " ta gaske Nayel ka saka mishi ? "

a hankali ya gyada mata kai allamun Eh
wani kyawatencen murmushi ta saki har da dariya , ta na kallon shi rike babynsu

" dubi har ya yi

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login