Showing 63001 words to 66000 words out of 104561 words

Chapter 22 - Exiled Prince Book 3 Hausa Novel Complete

Meerah   

13 Dec 2024

394

, ga tray din fruits a gaban ta sai sha ta ke ta na kallon Tv
ta na a haka Diya ya fito da ga cikin corridor , ya na sanye da wando three cuter sai t-shirt

ta na ganin shi ta saki wani kyawatencen murmushi ta ce " yau ba za ka je fada ba ? "
sai da ya karaso geffen ta ya zauna sannan ya ce " to me zai kai ni fada , bayan wanda na ke tafiya domin shi ba ya nan "

" yaya Zayd ba ya nan ? " ta fada ta na kai orange a baki

" Eh , ya tafi Honey moon da baby , ke ma ki shirya za mu koma Qatar da zama "

cikin rudu ta ce mishi " Qatar ? ina ne kuma Qatar ? "
wani cool murmushi ya saki kafin ya ce " daya da ga cikin gariruwan da na ke burin zuwa , za mu koma cen da zama "

" kamar ya ? ka na nufin zan bar mama da baby ? "

" amma ai za ki kasance tare da ni , ita da kan ta baby ba ta cikin Saudiya , Malik ya dauke ta sun tafi US , kuma a cen za su zama ba za su sake dawowa ba "

cak Nesrine ta tsaya ta na zaro idanu , shikenan ta rabu da Inaya har abada kenan ? ba za ta sake ganin ta ba ? ba za ta sake ganin Abdoul da mama ba ? ta kassa yarda

ta yi nisa duniyar tunaninta kawai ta ji ya na yi mata tafiyar tsutsa a wuya da tongue din shi
wata yar karamar dariya ta yi ta na fadin " ka kyale ni na gama shan fruits di na "

" ke ba ki da aiki sai shan fruits da cin abincin , kar ki zama katuwa "

hararrar wassa ta yi mishi ta na fadin " ai duk laifin babynka ne , shi ya ce min ya na son shan fruits , kuma ya ce min kihi ya ke so , dan haka tashi ka je ka kawo mishi "

" Fish kuma ? an ya ba so kawai ki ke ka gajiyar da ni ba , ina ya kai cin Fish ? "

nan take ta sakin mishi kukan shagwaba ta na fadin " ni wlh kihi na ke so , ka je ka kawo min ko kuma ba zan ci abinci ba yau " ta kai karshen ta na daukar Apple guda ta kai a baki

wata yar karamar dariya Diya ya yi ya na kallonta , ta na kuka ta shan fruits ba karamin burge shi ta yi ba

ya yi nisa duniyar tunanin shi kawai ya ga ta tashi da gudu har sai da tray din fruits din ta ya fadi , ta toshe bakin ta da hannu guda
a hankali ya mike ya bi bayan ta




❀⚘E X I L E D P R I N C E⚘❀

( LOVE MEETS POWER ) πŸ‘‘πŸ”₯




( A heart touching love story , Romance , injustice & destiny )




STORY & WRITTEN BY : MEERAH βš˜πŸ•Š


【THE ROYALTY LOVE β€πŸŒΉγ€‘



【 BOOK ________3 πŸ“šβœπŸ’Œ 】





______________________πŸ•ŠπŸŒΈπŸ•ŠπŸŒΈπŸ•ŠπŸŒΈπŸ•ŠπŸŒΈπŸ•ŠπŸŒΈπŸ•ŠπŸŒΈπŸ•ŠπŸŒΈ___________________




ο½› P A G E ………20 πŸŒΉπŸ•Šο½





β–ͺAFTER SOME DAYS


sannu sannu lokaci na tafiya yanzu wajen sati biyu da tafiyar su Malik US , a cikin satin a ka nada Aymane Malik din Saudiya , RIANNA kuma MALIKAT , a cikin satin kuma Diya ya dauki Nesrine su ka koma Qatar da zama dan a ganin shi ba zai iya zama cikin Saudiya da Aymane a matsayin Malik , dama Saboda Malik ne ya ke zaune a Daular Saudiya tun da ba ya nan ya kama hanyar gaba ne
Aymane kuwa farin ciki kamar ya kashe kan shi , burin shi na zama Malik ya cika , yanzu kuma su shirya sabon mulkin shi dan ina ji a jikina ba zai mulki bisa gaskiya ba
idan mu ka leko mutanan US kuma , kullum ciwon cikin Inaya kara tsananta ya ke amma sai ta danne dan kar Malik ya lura , har ya kai yanzu ta na faman da matsanincin ciwon kai har wani dishiΒ² ta ke gani idan ya fara yi mata ciwo , ga kuma tashin zuciya , har ya kai qamshin turaren Malik kadai ya isa ta yi amai , duk abun da ta ci sai ta amanyo shi , bayan fruits ba ta iya shan komai , har wata yar rama ta yi , duk abun da ta ke Malik ya na sane kawai ya na kokarin dannewa ne dan ya faranta mata , amma har cikin zuciyar shi ba ya jin dadin ganin ta cikin wannan halin , shi ya sa kawai ya yanke shawarar zubar da cikin tun kafin ya rasa ta



β–ͺUS ( WASHINGTON D.C )


β–ͺINAYA


zaune ta ke tsakiyar gadon su sai dafe ciki ta ke ta na lumshe idanunta , da allamun ciwo ya ke mata
ta na a haka ta jiyo Muryar shi ya na sallama kassa kassa
da sauri ta janye hannunta , ta bude idanunta sannan ta amsa mishi sallamar shi a ra'rabe

a hankali ya karaso bakin gadon ya mika mata wasu drug guda biyu , da glass din ruwa kai tsaye ya ce mata " karbi ki sha "

kallon drug din ta yi kafin ta dago kai ta ce mishi " yaya Zayd maganin minene ? "

" maganin abun da ke damun ki ne , karbi ni sha "

da sauri ta girgiza mishi kai ta na cewa " ni ba abun da ke damuna yaya Zayd "

" No Cutie , wannan abun da ke cikin cikinki shi ya ke damunki , ki karba ki sha ya tafi kawai , Allah zai ba mu wani babyn amma ban shirya rayuwa babu ke ba , duk abun da ki ke cikin gidan nan ina sane da shi kawai na sa miki ido ne na gani "

marairaice mishi fuska ta yi kamar za ta yi kuka ta ce " yaya Zayd da gaske ba abun da ke damuna please ka bar maganar nan wlh ba zan iya zubar da cikin nan ba "

cikin bacin rai ya ce mata " ba tambayar ki na ke ba umarni na ke ba ki , ki karba ki sha , a sani na , ni ne uban yaron na kuma ce ba na so dan haka ki karba ki sha ko so ki ke ki bata min rai ? "

da sauri ta girgiza mishi kai ta na hawaye ta na fadin " yaya Zayd ka bari don Allah "

" No , na bari sai ya kashe min ke sannan ? ban shirya yin rayuwa babu ke ba , saboda ke na hakura na bar kassar Saudiya , na bar kujerar Malik kawai dan mu yi rayuwar mu cikin konciyar hankali , amma ki na neman ki ruguza komai , ki karbi maganin nan ki sha please "

kuka ta sakin mishi ta na fadin " yaya Zayd "

da sauri ya katse ta da cewa " please Inaya ki sha maganin nan ? "

dan zaro idanu ta yi ta na kallon shi jin ya kira sunanta kai tsaye , a iya sannin ta duk zaman da su ka yi ko so guda bai taba bude baki ya kira sunanta kai tsaye ba , ba shi ba har Diya bai taba kiran sunan ta kai tsaye , yanzu kuma ga shi ya kira sunanta hakan na nufin yau ranshi ya baci

a hankali ta bude baki ta na shirin magana kawai ta ga ya saki drug din hannun shi da glass din ya fadi kassa ya watse , ya juya ya fice dakin

da sauri ta sauko da ga saman gadon ta ma manta da glass din da ke bakin gadon kawai ta taka su kafar ta ta fashe amma ba ta ji komai ba
da gudu ta bi bayan shi ta na kiran sunan shi , ya na jin ta amma ya kyale ta

sai da su ka karaso cikin parlourn ya nufi hanyar fita sannan ta riko hannun shi
da karfi ya juyo ya kwace hannunshi ya na fadin " kar ki sake ki min magana ! " ya fada da karfi ya na nuna ta da yatsa
ba karamar razana ta yi ba , ko so guda bai taba daga mata murya ba , yau ga shi ya na mata tsawa

nan take ta sakin mishi sabon kuka ta na fadin " yaya Zayd tsawa ka min ? "

cikin bacin rai ya ce " me ki ke so na yi Cutie ? kin fi kowa sanin irin son da na ke miki , yanzu in ki ka tafi ki ka bar ni ya zan yi da rayuwa ta , kashe kaina kawai zan yi "

da sauri ta ce mishi " in ka kashe kanka wa zai kula da babyn mu , ka sani zai bukace ka a kusa da shi "

da sauri ya katse ta da cewa " wai ki na tunanin zan iya kallon shi ma idan ya yi sanadiyar rabuwa ta da ke ? , bari na fada miki wannan cikin shi ne ma fi munin abu da ya samu rayuwata Cutie "

" yaya Zayd ka na jin abun da ka ke fada ? " fada cikin raunin murya

" Eh , ina ga ke ce ba ki ji abun da na ce ba , wannan abun da ke cikinki kashe ki zai yi , ni kuma ba abun da zan iya yi a kai , kin gwammace rabuwa da ni har abada a kan rabuwa da wannan abun , bayan kin san za mu iya samun wani bayan shi "

ya na gama fadar haka kawai ya ga ta dan lumshe idanun ta kamar mai jin barci ta yi baya kadan kamar za ta fadi allamun jiri ta ke ji

ya na ganin ta amma bai ce mata komai ba ya juya ya fice gidan baki daya
ta na ganin shi har sai da ya fita sannan ta juya a hankali ta nufi stair ta haye
kai tsaye bedroom din su ta koma ta haye saman gado , ta dunkule waje guda ta saki kuka mai cin rai
ko one minute ba ta yi ba da fara kukanta kawai ta fara rage sautin kukanta kawai jikin ta ya dauki sanyi da allamun ta sume dan ko motsi ba ta yi

bangaran Malik kuwa tuki ya ke cikin fitar hayaci ba ya maganin gaban shi duk idanun shi sun rufe
sai da ya share wajen good ten minutes ya na irin wannan tukin kafin ya ja wani mugun burki geffen titi

a hankali ya kai hannu ya fido wayar shi da ke faman ringing , dalilin ta ne ma ya ja burki
kallon screen din ya yi kafin ya dauki kiran ya kai kunne ba tare da ya ce komai ba

a daya bangaran kuma wata yar karamar dariya Diya ya yi kafin ya ce " haba abokina ka yi sallama dai ko ? "

wani dan karamin tsaki Malik ya yi kafin ya ce " lafiya ka kira ni ? "
" Haba , yanzu tsakani da Allah wajen kwana nawa rabonka da ni , ni na kira ka shi ne za ka ce lafiya na kira ka ? Ah dan na ji in ka mutu ne , dan rainin sens "

tsaki kawai Malik ya yi ya kontar da kan shi saman steering motar

wata yar karamar dariya Diya ya yi kafin ya ce " shikenan , yanzu fada min ya ka ke , ya kuma baby ? "

" Fine " ya fada a takaice ya na lumshe idanun shi

shiru Diya ya yi yanayin da Malik ya yi mishi magana sam bai konta mishi ba , ya San yanayin maganar abokinshi idan ya magana cikin damuwa cikin bacin rai ko cikin farin ciki

cikin sanyin murya Diya ya ce mishi " Malik , tell what's wrong with you ? "

a hankali Ya dago kan shi ya na tsaki ya ce " nothing " a takaice

da sauri Diya ya ce " wani abu ya samu baby ? " ya fada a razane

" ba abun da ya same ta yanzu , amma nan gaba zai same ta " ya fada kamar ya na cikin bacin rai

" calm down , yanzu ka fada min abun da ke faruwa cikin konciyar hankali " Diya ya fada

ba musu ya shiga bashi labarin abun da ya faru bayan zuwan su US amma bai fada mishi abun da ya faru yanzu tsakanin shi da ita ba

wata yar karamar ajiyar zuciya Diya ya sauke kafin ya ce " bai kamata ka damu kan ka a kan wannan ba , kar ka manta cikin kassar US ku ke , shawo kan matsalar ta abu me sauki ne , Kai ta manyan Hospital , akwai kwararun likitoci a US , za su iya ceton rayuwar ta tare da ta babyn ku "

cikin nitsuwa Malik ya ce mishi " Diya , Doctor hudu na gani da wannan maganar , yau kuma na cika na biyar , amma duk amsa guda su ke ba ni azubar da cikin , wasu kuma su ce min a bari sai cikin ya kai wata 7 ko 8 sannan a cire mata shi but it isn't sure yaron zai rayu saboda bai cika wata tara ba , ko ya rayu zai samu matsala wajen girma gwara kawai a cire cikin "

shiru Diya ya yi ya na sauraron abun da ya ke fada mishi , lalle ya na cikin tsaka mai wuya
sai da ya dauki wajen two minutes kafin ya ce mishi " yanzu kai wata shawara ka yanke a kai ? "

" a cire cikin kawai "

" a ka je kuma bayan shi ku kasa samun wani ? "

da sauri ya ce mishi " Diya i don't care , ba dai za ta kasance tare da ni ba ? ban damu ba da mu samu baby , ko kar mu samu , ni dama ban da niyar haihuwa yanzu , kawai dai Allah ya kaddara sai mun bi ta wannan Step "

" ka rungumi kaddarar ka mana , na san halin ka , ba ka san ka na kara mata damuwa ba , hakan ko ya na kara yi mata illa , please ka tsaya ka kula da matarka kamar ba ka san yadda ikon Allah ya ke ba "

" hakan na nufin saka rayuwar ta cikin hatsari , a ka je ba ta rayu ba kuma fa , na yi ya kenan ? "

" ka kula da babynku mana , ko ba komai zai dinga tuno maka ita "

" zai dinga tuno min raba ni da ita da ya yi dai "

wani dogon nunfashi Diya ya ja ya san halin abokinshi in ya ce ba ya son abu ko sama da kassa za su hade ba zai taba son shi ba , tun da har ya ce zubar da cikin zai yi , to ba makawa sai ya zubar da shi sai in Inaya ba ta ba shi dama ba

a hankali Malik ya sauke ajiyar zuciya kafin ya ce " shikenan mu bar zancen please , ya ka ke ? da su Ammie da Tesnim ina fatan duk su na lafiya ? "

wata yar karamar dariya Diya ya yi kafin ya ce " yo ai ni na jima da na baro Saudiya "

cikin rudu ya ce mishi " ban gane ba ? ka ina yanzu ? Daular Ottoman ? "

" No , Qatar , Ni da Nesi "

" ba ka da labarin Daular Saudiya ? "

" ina da , kar ka damu duk su na cikin koshin lafiya , but Γ  nada Aymane a matsayin sabon Malik "

wani dan karamin tsaki Malik ya yi kafin ya ce " and so what ? su su ka sani , su nada duk wanda su ke so ni ba zan dawo ba "

murmushi mai dan sauti Diya ya yi kafin ya ce " za ka koma , ni na fada maka kai da kanka za ka dauki kafa ka koma kuma ka nemi kwatar kujerar Malik , na tabbatar maka da haka "

wani dan karamin tsaki Malik ya yi kafin ya ce " sai an jima " ya na gama fadar haka ya sauko wayar ko amsar Diya bai jira ba
da ga nan ya kontar da kujerar shi ya konta a nan geffen titi


❀⚘ EXILED PRINCE ⚘❀

( LOVE MEETS POWER ) πŸ‘‘πŸ”₯




( A heart touching love story , Romance , injustice & destiny )




STORY & WRITTEN BY : MEERAH βš˜πŸ•Š


【THE ROYALTY LOVE β€πŸŒΉγ€‘



【 BOOK ________3 πŸ“šβœπŸ’Œ 】





______________________🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸___________________




ο½› P A G E β™‘β™‘β™‘ 21 πŸŒΉπŸ•Šο½






β–ͺMISALIN KARFE 1 NA DARE


a hankali ya ke tako stair kamar wanda a ka cirewa lakar jiki , a haka ya ida haura stair din
maimakon ya shiga bedroom din su , sai na ga ya shiga bedroom din da ke fuskantar tasu
har ya riko handle din kofar ya murda ya jiyo Muryar ta ta bayan shi ta na fadin " yaya Zayd sai yanzu ka dawo ? tun dazu na ke jiran ka mu yi

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login