Showing 30001 words to 33000 words out of 111128 words

Chapter 11 - Abdulmalik Bobo Part 1 Hausa Novel Complete

20 Dec 2024

748

maganarsu Appa nadawo.
Dariya aunty Rahma tayi, takira Taufiq babban d'an ya ishaq ta aikesa ya d'akko.
A can kuma ya Hamza ya kalli Bobo ya ce, " mutumina kafa fetsare soyayya har a gabammu.
d'an tsaki yaja Mara sauti, Yaya nifa bawata soyayya nakeba, bigenifa tayi.
Ya Sulaiman dake jinsu yay dariya, danta bigeka saika damk'e mata hannu kaki saki, kumafa kallon soyayya kake mata.
Shiru yayi bai tankaba, ya Hamza da ya Sulaiman suka shek'e da dariya.
Ya ishaq ya ce, "kukuma lfyarku?.
Bobo daya fara k'uluwa yamik'e daga tsakkiyarsu yana fad'in inafa sukaga lfy Yaya, Kusada ya ishaq yakoma yazauna, saiyayi fesin d'in Rahma sosai.
Ya Hamza ya ce, " habawa auta munfa gane wayonka na komawa nan saboda..... Basu k'arasaba suka kuma saka dariya.
Suma sauran duksai Kansu yakawo musu wuta, suka kalli Bobo suka kalli Rahma, sai kawai suma suka shek'e da dariyar, shimadai awannan karon ya murmusa, Dan wlhy baima kawo kamai aransaba yadai zaunane kawai saboda bayaso su ya Hamza sucigaba da takura masa.
Fitowar Ammi da Appa yasa suka tsagaita, Ammi ta ce, ''tomikuma yafaru?.
Ya Sulaiman ya ce, "ba komai Ammi, autanki ne zai mana gulma, yanaso yana kaiwa kasuwa.
Ammi da Appa sukayi murmushi dansun gane inda zancen yadosa.
Kubarmin babana yasha iskar marece, cewar Appa.
Yauwa Appa na fad'amusu, wlhy sun takuramin, Bobo yay maganar cikeda shagwa6a.
Shagwa6ar tasa tabama kowa dariya, harda yaran, shikam yasaki baki da hanci yana kallon Rahma dake tuntsura dariya sosai, baiyi tunanin tana dariyaba.
Tana d'agowa suka had'a ido saikawai ta gumtse dariyar tadaina.
Anty Rasheeda da Anty Sameera sukace kai ALLAH yayi magulmatan masoya awajennan.
Kowa yaga abinda yafaru tsakanin Bobo da Rahma Dan haka dariya hardasu Appa da Ammi, bayan an tsagaita Appa ya ce, " to ya isa haka, asauka aci abinci.
K'asa suka sakko sukaima falon zobe, ga abinci atsakkiya, Ammi tana kusada mijinta, sai yaran sun sakasu tsakkiya, dandanan kuma gidan yay tsit bakajin komai sai k'arar filet da cokali, kowa abinda yakeso yakeci, family's d'in Alh Aliyu hamshak'i yahad'u masha ALLAH.
Shida Ammi, 'Ya'ya shidda, surukai hud'u, jikoki goma cif.
Yaran ya ishaq, Taufiq, Sageer, Zainab, muhseen.
Yaran ya Sulaiman, Sumayya, mustapha, Jiddah.
Yaran ya Hamza, Ahmad, Kamal.
Sai Bobo, Nawal.

Bayan sun kammala cin abincin, 'yan aiki sukazo suka gyara ko'ina yakoma tsaf, yaran suka fice tsakar gida suna wasa.
Sukuma sunata hirarsu.
Duk juma'a haka suke zama, Appa yashige tsakkiyar iyalinsa asha fira, da karantar halayen dasuke ciki, babu ruwansa har matan 'ya'yansa 'ya'ya yad'aukesu.
Afirarne yake sanar dasu maganar kawo kud'in auren su khairiyya dukda su mazan duk sun sani, kowa yayi murna, dafatan ALLAH yasa akai da rai.
Kiran sallah la'asar ne yatadasu, mazan suka tafi masallaci sukuma sukayi agida.

Har dare suna nan, akasha shafta sosai, tuni Rahma tasaki jikinta acikinsu, hakan yayma kowa dad'i sosai.
Bayan isha'i sukaci abincin dare, kowa yakwashi matarsa da 'ya'yansa sai gida.
Rahma kam jitake kamar ayita zama ahaka, Dan taron yaymata dad'i sosai.

Kafin su Isa gida har Nawal tayi barci, Rahma tasa6eta sukayi ciki, shiya bud'e gidan suka shiga, kowa yanufi d'akinsa, babu maimagana saikace wasu kurame.
Dama anyima su Nawal wanka a can, sai kawai ta canja mata kayan barci, itama tashiga wanka, bayan tafito tayi abinda yadace, harzata kwanta tatuna da shayin oga.
Babu shiri tafito zuwa kichin, shayin tadafa takai masa, sallah ta tarar yanayi, Dan haka ta ajiye tafito abinta........



*_Happy juma'at Mubarak_*



*_luv u oll my fan's_*
*_(((S))).......2017_*
[11/12, 2:51 PM] mrs bilkisu: 👩🏻‍💻typing........

❣ *_ABDUL-MALEEK_*❣
_•{BoBo}•_


*_NA_*
_*Bilyn Abdul*_

_sadaukarwa_
*_Abba Gana_*
*_Batul mamman_*
*_Billy giro_*


3⃣9⃣=4⃣0⃣

_washe gari_
Rahma tatashi tayi duk abinda tasabayi dukda tasan yau weekend Bobo bazai fitaba, tana cikin saka turare a falo bobo yafito sanye da jallabiya ruwan toka mai gajeren hannu, rissinawa tayi ta gaidashi, kamar yanda yasaba ya amsa da lfy.
Amsa gaisuwar nan nabama Rahma haushi, amma babu yanda zatayi.
Yad'anbi falon da kallo komai tsaf, gawani k'amshi na musamman, yana jin dad'in kasancewarta mace mai tsafta.
Itadai cigaba tayi da abundan takeyi. Ya ce, "bari nad'anje wani waje nadawo.
Aranta tace kofa wanka bakayiba, amma afili ta ce, " to ga Break.
No barinaje nadawo, aiba dad'ewa zanyiba, yafad'a yana ficewa.
Itama ta ce, "ALLAH ya tsare.
Dukda yafita amma yajiyo addu'arta.

Bayan takammala saka turaren zuciyarta tabata shawara dataje ta gyara masa d'akinsa, kamar bazatajeba saikuma tatuna nasihar mahaifiyarta da ummansu Basma.
d'akin tanufa da tunanin ALLAH yasa bai rufeba, tana tura k'ofar tabud'e, k'amshinnan yana nan kamar kullum, yau tanutsu takalli ko ina na d'akin, komai farine tas, aranta tace farin Abu name tsaftane.
Sai manya manyan hotunanan Ni'ima Maman Nawal, bani gurin ita kad'a, wani gurin kuma shida ita.
Ko kad'an bataji haushiba bare kishinta, Bata 6ata lokaciba tafara gyara ko ina, Dan danan tagama d'akin yak'ara d'aukar haske komai yana d'aukar ido.
Bathroom tashiga zata wanke saitaga kaya ajik'e abokiti.
Shiru tayi tana tunanin ta wanke kota barmasa abinsa, wata zuciya ta ce, " ki wanke, kobabu komai zaki samu lada aii.
Haka tazauna tahau wankin gajerun wandunansa da vest, akunyace take wankin tamkar tana gabansa, gudu gudu sauri sauri tagama bataso yazo yataddata tanayi.
Dandanan tagama tawanke bayin, tad'auki kayan tafito waje, acan baya taje tashanyasu sannan tadawo d'akinta tashiga wanka, Dan Nawal bata tashiba.

Shigarta wanka babu dad'ewa yashigo gidan, d'akinsa yanufa kai tsaye, baki da hanci da ido yasaki yana kallon d'akin NASA, yalek'a bayi nanma fes, bokitin daya jik'a kaya wayam, wani lallausan murmushi yasaki, labulen window d'insa yad'aga, can yahango kayan ashanye.
Jiyay wani Abu nata6a zuciyarsa, afili ya ce, ''ALLAH yaymiki albarka.
Fitowa yayi yanufi d'akin Rahma, hakan yayi daidai da fitowarta daga wanka, daga ita sai guntun tawul iya cinya.
Wata tsayuwar sojan badakkare bobo yayi, sai Raba idanu yake akan Rahma, da wannan munafikin kallon nasa k'asa k'asa.
Itakam dukta rikice, waige waigen abinda zata rufe jikinta kawai takeyi, can ta hango hijjabin sallarta, amma dole saitabi tagabansa zata d'auka, ganin haka saikawai takoma cikin bayin da sauri.
Murmushi yayi tareda sauke ajiyar zuciya, yak'arasa inda hijjabin sallarta yake yad'auka, ahankali yak'arasa har k'ofar bayin ya kwankwasa, Rahma dake jingine da k'ofa tagwalo ido waje, k'irjinta sai dukan Tara Tara yakeyi.
Yak'ara kwankwasawa.
Muryarta narawa tamkar zatayi kuka tace yes, yanda tayi maganar tabashi dariya amma saiya gimtse ya ce, "bud'emin k'ofar.
Innnalillahi tace azuciyarta, wai mi mutumin nan yake nufi.........maganarsa ta katse mata tunani, " wai kobaki jinane?.
Bayan k'ofar takoma tala6e sannan tabud'e, gaba yay tamkar zai Shiga, saikuma yamik'a mata hijjabin, dasauri takar6a tamaida k'ofar burum tadatse.
Girgiza kai yayi yanad'an ta6e bakinsa, yazauna bakin gadon yana shafa kan Nawal daketa barcinta hankali kwance, shi mamakin kansama yakeyi, wai miyake jirane?, zuciyarsa ta ce, "kanason sake kallon Rahma ne.
d'an tsaki yaja yamik'e yafice, shi adole zuciyarsa tayi k'arya.

Saida taga yafita sannan tafito, taje tasakama k'ofar key, sannan tazauna tagyara jikinta, tasaka Riga da wando na Pakistan, nakula tana son irin kayannan sosai.
Nawal ta tashi itama tayimata wanka tashiryata cikin wandon Jin's da pink d'in T shert mai k'yau.
Falo suka fito, fitowarsu babu dad'ewa shima ogan yafito, haryayi wanka yashirya cikin jins blue da farar Riga sai zabga k'amshi yakeyi.
dinning suka nufa, Rahma sai sinne kai takeyi Dan kunya, shikam ko'a kwalar rigarsa, yanacin abinci Nawal namasa surutu, iyakarsa Yamata murmushi koya d'aga kai.
Rahma ta ce, " azuciyarta, muskili kafi mahaukaci ban haushi.
Suna kammalawa Nawal taja hannun Rahma wai suje tamata lilo, fitowa sukai sukabarsa kwance saman doguwar kujera yana kallon film.

Sunacan a lambu Rahma NATA biyema Nawal suna lilo, jiyay falon babu dad'i Dan haka yafito, jiyo dariyarsu alambu yasashi nufarcan, Rahma na zaune akan lilo, Nawal na shillata suna dariya, k'arasowarsa yasa Nawal cewa lah papa kaima zona lilaku.
Kai ya girgiza mata alamar A'a.
Takwa6e fuska zatayi kuka, cikin takun k'asaitarsa yak'arasa wajen lilo d'in, Rahma tayi yunk'urin sauka Nawal ta ce, "momy kubiyufa zanyimawa, sandarewa Rahma tayi azaune, kafin ta farga Bobo ya haye lilo d'in amma d'an nesa da ita.
Da k'arfi Nawal ta hankad'a lilo d'in, aiko sukayi gaba kamar zasu fad'i, da Sauri Rahma ta ruk'unk'ume Bobo, shima yarik'eta.
Nawal Yar kwal uba tacigaba da lila lilo da k'arfi, basuda za6i bayan rik'e junansu dak'yau, Nawal dai sai dariya takema iyayen nata, saida tagaji Dan kanta sannan tadaina lilasu.
Bobo yabud'e idanunsa ahankali danjin lilo ya tsaya, ga Rahma na mutsu2n kwace kanta, yana sakinta tasauka, da Sauri tabar wajen, binta da kallo yayi yana murmushi, Nawal takatse masa tunani, baby d'orani muyi tare tunda momy tagudu.
daukarta yayi yad'ora sukacigaba da lilonsu zuciyarsa cikeda tunani kala kala.

.*.*.*.*.*.*.*.*.*.*.*.
Safna zaune gaban Abba da ummi da alama fad'a ake mata, Dan fukarnan adagule take.
Abba ya ce, " wlhy nabakinan da wata uku zuwa hud'u kifito da miji a had'a aurenku keda amira, inbandama auren ameerar da sati biyu zan baki, amma Abubakarne yaceceki ya ce, "abari ahad'a bikin dan a samu sauk'i."
To saikiyi gaggawar sanar da Wanda kikace kinason harkikaso wulak'antamu akansa.
Insha ALLAHU Abba zan kawoshi, nidai kuyi hak'uri kubar ganin laifina, ALLAH yariga yarubuta Dama shid'in Mijin k'anwatane baniba...
Dallah yimana shiru!!, ummi takatseta atsawace, Mara mutunci kawai, Indai duniyace aigaki gata nan, kuma koyaya Wanda kikace kinason yake wlhy haka ZAMU aura miki shi, kijecan kiji da bak'in halinki, tashi kibamu waje mu.
Mik'ewa Safna tayi tabar falon tana k'unk'uni.

Na ce, " ALLAH ya shirya to.


.*.*.*.*.*.*.*.*.*.*.
Ad'an hanzarce takeyin aikin gidan, Sauri take tagama dawuri taje tayi girki Dan maigidan ya ce, "mata yau abokinsa zaizo da iyalinsa, tagama komai tsaf har girkin ta kammala d'akin bobone kawai yarage mata shima Dan yana kwance ad'akinne.
Saiwajen 12 yafito daga d'akin yafita danufin siyo ruwa datace masa babu.
Yana fita tashiga d'akin Dan gyarawa, tagama aikinta lfy lau, tsautsayi yasa takai hannunta kan wani hoton Ni'ima datayi bala'in k'yau, Ashe bai zauna da k'yauba aiko yafad'o jikake taratsatsa!!! ya tarwatse ak'asa abinka da gilas.
Hakan yayi daidai dashigowar Bobo falon, da hanzari yanufi cikin d'akinsa, aiko abinda yake zarginne yagani, dandanan fuskarsa ta canja kama idonnan sukayi ja danshi aganinsa da gangan Rahma tayi saboda batason ganin hotunnan tunda dai yasan mata da kishi.
Tunda yashigo jikinta ke rawa, tabud'e baki arazane zatayi masa magana yadaka mata tsawa.
Dallah yimin shiru, dama kina shigowa gyaramin d'akine danki kashemin hotuna?, to wlhy idanma kishi kikeyi da ita kidaina Dan babu yanda kika iya da ita, wannan dakike gani itakad'aice nabawa zuciyata, daga itakuwa babu wata mace dazata samu haka daga gareni, wlhy akan wad'an nan hotunan sainayi mugun sa6a miki, banason cikin da iskanci.
Rahma tamatso danufin tsugunnawa tabashi hak'uri amma abisa tsautsayi ta taka gilas ak'afa, runtse idonta tayi saboda azaba, dama ga hawaye tuni sun wanke mata fuska.
Tsawa yasake dama mata, dallah malama fitarmin ad'aki, kuma karna sake ganin k'afarki ad'akina.
Ran Rahma ya6aci sosai ganin yanda yake cimata mutunci akan hoto, Wanda inyanzu yaso zaikai amaida gilas d'in daya fashe, haka tataka k'afa tabar d'akin tana kuka, tanazuwa tazube akan gado, ga azabar da k'afarta take mata amma bata kulaba, sai kuka maicin rai data saki.
Duk abinnan yake faruwa Nawal tana can baya tana wasa, Rahma taturata wajene dantabarta tayi aiki, batason surutu.

Bobo kam tana fita yadurkushe agaban hoton, d'agosa yayi yana gogewa tamkar zai fasa kuka, muryarsa na Rawa ya ce, "kiyi hak'uri Ni'imana bada sanina tayiba, ALLAH ya gafarta miki ya yafe miki kinji.

Nawal tashiga d'akin Rahma tana kwala mata kira momy! Momy!!, tak'arasa cikin d'akin da murnarta, amma ganin jini ahanyar sai jikinta kuma yay sanyi, tak'arasa har bakin gadon tana kallon k'afar Rahma da gilas ke jiki ga jini yanata zuba ak'asan wajen.
Fitowa tayi da gudu tanufi d'akin Papan ta, har yanzu yana gaban Hoton adurk'ushe, papa papa zokaga k'afar momy jini yanata zuba dayawan tsiya.
d'agowa yayi yana kallonta, yanda tabirkice shima sai jikinsa yay sanyi, mik'ewa yayi suka nufi d'akin Rahma d'in, gsky shima abin yabashi tsoro ganin jinin dad'an yawa, ga gilas babba kafe ak'afarta, tana kwance rubda ciki tana darzar kuka.
Tsugunnawa yayi Kusada k'afar yakama gilas d'in zai cire tasaki wata k'ara wadda tasaka Nawal fashewa da kuka itama, ga gilas d'in yakafe dayawa, ganin karya k'ara jimata ciwo yasa yamik'e dasauri yaje d'akinsa yad'akko key d'in mota.
Dawowa yayi ya ce, " tashi muje asibiti acire miki wannan kwalban.
Banza tayi masa tacigaba da kukanta, wani haushi yak'ara turnik'eshi, baisan lokacin daya sungumetaba yay waje da itaba, Nawal nabinsa abaya, Nawal tabud'e masa k'ofar motar yasakata aciki, suma suka shiga sai asibiti.........





_kuyi hak'uri da wannan yau kaina namin ciwo._



*_luv u oll my fan's_*
*_(((S)))..........2017_*
[11/12, 2:51 PM] mrs bilkisu: 👩🏻‍💻typing........

❣ *_ABDUL-MALEEK_*❣
_•{BoBo}•_


*_NA_*
_*Bilyn Abdul*_

_sadaukarwa_
*_Abba Gana_*
*_Batul mamman_*
*_Billy giro_*


4⃣1⃣

Asibitin ya sulaiman sukaje, ALLAH yasosu sun tarar dashi.
Aiko ansha fama wajen cire gilas d'in nanan, Rahma tasha kuka dukta fita hayyacinta, ga k'afar harta d'an kunbura.
Shikansa Bobo ya tausaya mata, saiyanzu yake ganin abinda yay mata bai k'yautaba, to amma idan yatuna miyakai hannunta wajen hoton saiyaji ransa ya 6aci.
Da hakadai aka kammala, ya Sulaiman yamata allurai tad'an samu nutsuwa.
Bayan an kammala bobo ya ce, "ya yarinyar nan kuwa?.
Jikinta kam saidai muce alhmdllh, ammafa yakamata asan iyayen yarinyar nan Abdulmaleek, gashi kace zaku fara shiri'a ranar talata, kasanfa Alh sunusi dala mutumne mai had'arin gsk, sarai zai iya bincike akan yarinyar, kuma zai iya aikata kimai Dan ganin d'ansa ya ku6ta.
Hakane Yaya, amma inata iya k'ok'arina wajen Neman iyayenta, saidai kutayamu da addu'a kawai.
To ALLAH ya taimaka.
Amin dai, bari mubiya muganta saimu wuce gida.
Okey, kardai kamanta kusiyi maganin.
Babu damuwa, k'arasawa yay inda Rahma take fuskarsa babu walwa, yakama hannunta ta sakko.
Ya Sulaiman dake kallonsu ya ce, " saidaifa kad'auketa kamar d'azu, Dan babu yanda za'ayi ta iya taka wannan k'afar.
K'ara 6ata rai yayi, kamar bazaiyi maganaba, saikuma ya ce, "Yaya ba ancire ba?, eh ancire, amma karfa manta yanda gurin yake a yanzu, idanmma kunje gida ad'an gasa k'afar da ruwan zafi.
Baice komaiba ya d'auketa, saiwani kauda kai yake daga saitin fuskarta, itama saita runtse ido Dan bata son ganinsa.
d'akin da yarinyar nan take yakaita, yadireta saman kujerar gaban gadon, lahh Muheebat! kece?, Rahma tafad'a tana kallon yarinyar.
Itama tashi tayi zaune tana dariya Dan ganin Rahma.
Bobo ya ce, " kinsanta ne?.
Eh nasanta, K'anwar direban muce idris, dama sunata nemanta tun tuni wlhy.
Ajiyar zuciya bobo ya sauke ya ce, "Alhmdllh, yaciro wayarsa yakira Ya Sulaiman, babu dad'ewa kuwa ya iso, shima yaji dad'i sosai dajin labarin.
Sun ajiye magana akan anjima zasuje gidansu Muheebat, dukda bata iya magana to tanajin abinda suke fad'a, Dan haka taita murmushi.

Bobo Yakuma d'aukar Rahma zuwa Mota, daganan sukayi gida, motar tsit babu mai magana kamar wasu kurame, Bobo sai shan k'amshi yakeyi, itama ganin haka saita d'auke kanta, dama can suka baro Nawal zatabi ya Sulaiman gidansa.
Koda suka shiga harabar gidan saiya bud'e motar yay tafiyarsa ciki yabarta.
Rahma tayi wata dariya azuciyarta ta ce, " kama dawo wlhy, dan babu inda zan motsa.
Aiko tayi zamanta amotar, shikam haryaje k'ofar falon saiyaji babu motsinta abayansa Dan haka ya waiga, can ya hangota cikin mota ko motsawa batayiba, afili ya ce, "wai mi waccan abar take nufi da nine?, koni bawantane dazanta d'aukarta ina ajiyewa mtsooow, yak'arashr maganar dajan tsaki.
Komawa yayi wajenta sai wani d'aurewa yakeyi, Rahma ta hangoshi yana tahowa, tayi murmushin mugunta tana fad'in kadaiji dashi.
Bemata maganaba yabud'e motar ya d'auketa, itako ta lumshe idonta kamar mai barci, haushine yak'ara turnuk'e zuciyar bobo, gani yake tana k'ara langya6ewa ne kawai.
Koda yadireta a gadon bai kalletaba yajuya ya fita.
Ita kuma taimasa gwalo😜, wai dole dai ad'auketa. lol.

Tana nan zaune har kusan minti talatin, harta fara tunanin yanda zata fita taci abinci Dan yunwa takeji sosai, tayunk'ura zata tashi taji wani azababben zafi, danhaka takoma ta zauna, wai miyasama tabar Nawal tabi ya Sulaiman ne?, yanzu da tananan ai data rage mata wani abun.........bata rufe bakiba taji anturo k'ofar.
Kamshinsane ya tababbatar mata dashine, Dan haka tak'i d'agowa danko sallama bataji yayiba.
Tire yadire ak'asa na kayan break, Rahma tayi kamar bata ganshiba, shima ko kallo

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login