Showing 51001 words to 54000 words out of 111128 words
k'ayatarwa.
Kamar ance Rahma takalleshi tad'ago, baya tayi da Sauri tareda zaro ido, cikin Rawar murya ta ce, "sannu da dawowa.
Khairiyya da khursiyya suka d'ago alokaci d'aya suma suna kallonsa.
Amamakinsu saisukaga yayi murmushi tareda fad'in lallai yarannan gaba d'a film yatafi da imaninku ko sallama bakwaji ko?.
Wlhy Yaya bamusan kashigoba sannu dazu.
Murmushi yayi tareda nufar d'akinsa.
Khairiyya ta kalli Rahma, auntynmu yaufa mijinki yana cikin nishad'i wlhy.
Rahma tad'anyi murmushi, nimadai nakula da haka khursiyya, komiye yasakashi nishad'i?.
Dariya sukayi gaba d'aya, Rahma ta tashi dukda zuciyarta na dukan Tara Tara Dan kwana uku kenan baya cikin wata walwalar kirki, amma yau gashi yashigo musu cikin nishad'i, ruwa ta d'auka da cup tanufi d'akin.
Ahankali tayi Knocking kamar bataso. Yana kwance akan gado fuskarsa cikeda nishad'i, yau jinsa yake sakayau dashi, jin Knocking d'in k'ofa yasashi juyawa tareda amsawa, ya ce, " shigo mana.
Rahma tashiga a sanyaye tareda yin sallama a can k'asan mak'oshinta.
Fararen idanunsa yad'ago yana kallonta, yad'an lumshesu sannan yabud'e akanta, hakan yayi daidai da rank'wafowarta zata ajiye masa tiren agabansa, wani nannauyan numfashi ya sauke yayinda idanunsa sukayi tojali da k'irjinta daya bayyana saboda wuyan rigar babbane.
Itakam dabatasan miyakeyiba ta tsiyaya ruwa akofi tad'ago zata bashi, kallo d'aya tayi. Masa ta kauda kai Dan ganin yakafeta da mayun idanunnan nasa masu hasken tsiya.
Ya lashi le6ensa nak'asa tareda kar6ar kofin tamkar wani soko, tana bashi takama hanya zata fice yay saurin damk'e hannunta.
Gabantane yafad'i amma bata juyoba, shima baiyi maganaba hasalima ruwansa yake sha idonsa kuma akan TV dake manne abagon d'akin, sunkai minti uku ahaka sannan ya ajiye kofin hannunsa yadawo da kallonsa kanta, bayanta yakebi dakallo aransa ya ce, "yarinyar tanada sura mai k'yau saidai tacika yarinta..... Mutsu mutsun kwacewa da takeyine yadawo dashi hayyacinsa, yakuma rik'e hannun nata sosai, cikin muryarnan tasa mai sanyin dad'i ya ce, " jimana.
Maganar tabama Rahma dariya wai jimana saikace Wanda yaga budurwa a hanya, shiru bata juyoba danhaka shikuma yamik'e, haryanzu hannunta yana cikin nasa, yamatso daf da ita hartanajin saukar numfashinsa akan bayanta, tad'an runtse idanunta Dan idanhar bobo yakusanto ta takanji tsigar jikinta tana tashi....
Bata k'are tunanin nataba taji yarungumota ta baya, yazagayo da hannayensa duk biyu saman cikinta, jikintane yakama rawa cikin rawar murya ta ce, "pls kayi hak'uri su khursiyya suna jirana a falo.
Murmushi yayi tareda kawo bakinsa Kusada kunnenta muryarsa tayi low sosai can k'asan mak'oshi ya ce, " wato su khairiyya sunfi mijinki muhimmanci ko?, yanda yay maganar akunnenta sai duk ta dabarbarce, tajuyo akid'ime, kallo d'aya tamasa gabanta yafad'i, Dan ganin fuskarsa ta canja hartayi d'anja, hakama idanunsa sunyi ja, girgiza kai tayi tana fad'in bafa haka nake nufiba, munayin girkine Dan Nawal takusa dawowa daga school.
Baki yad'an ta6e yana jinjina kai, idonsa akanta ya ce, "aikinga anraba kenan, su khairiyya sukula da Nawal, kekuma ki kula da baban Nawal ko?.
Rahma tak'ara kasa da kanta, shikuma yayi murmushi tareda saka yatsunsa biyu yad'ago ha6arta, lumshe idanunta tayi, shikuma yashiga Raba idanu bisa k'yak'yk'yawar fuskarta, muryarsa ta canja Dan akasalance yake magana, ya ce, " Abu d'aya zakimin nabarki ki tafi.
Da sauri tabud'e idanunta ta ce, "minene?.
Gira yad'aga mata yana wani kasa k'asa da idanu, kibiya bashin danake binki na kiss, dankinsanfa ni bana mantuwa.
Zaro idanu Rahma tayi, ta marairaice fuska kamar zatayi kuka, Dan ALLAH kayi hak'uri wlhy bazan iyaba.
Yakuma narke murya to saboda mi?.
Inajin kunya.
Kunya kuma?.
" eh".
Lallai kinada aiki, dole ki shirya zama mara kunya kuwa indai kina taredani, danni mutumne dabayason kauce², sak nake kuma komai nawa sak yake, inaso da sauri shiyyasa nakasance mai sauri, inaso da k'arfin zuciya shiyyasa nakasance mai dakakkiyar zuciya, inayi da yak'ini shiyyasa nakasance mai nasara, inayi da ikilasi shiyyasa ubangijin al'arshi yake taimakona adukkan al'amurana, kizama jaruma sai duniya tasanki, kizama mai gaskiya sai azzalumai suji tsoronki, kizama mai zuciya saiki kasance mai k'arfi, kizama mai hak'uri saiki ganki dayawan riba, kizama mai tunani saikomai naki yazama namasu hikima da k'yak'yk'yawan tunani, Abdulmaleek nakowane amma bakowa bane na Abdulmaleek, 'yammata karki tsaya kallon ruwa kwad'o yamiki k'afa, kizama mai jarumta dankiyi nasarar maida jiyana da yau da gobena duk suzama naki kekad'ai da 'yayanmu.
Yana gama fad'ar haka yasumbaci kumatunta tareda sakinta yashige bathroom.
Kamar sokuwa haka Rahma tabishi da kallo harya shige, sai juya maganganunsa takeyi aranta da k'arfin tunani da kwanji, amma kaf tarasa fassara ko guda d'aya aciki, tama rasa inda maganganun suka dosa, takai tsawon minti 6 awajen tsaye amma takasa fasa koda magana d'aya aciki, takuma kasa barin wajen, shikuma har yanzu bai fitoba.
Ahankali tafice tamkar munafuka, tunda tafito su khairiyya kebinta da kallo suna k'unshe dariya, tazauna tana binsu da kallon mamaki, khursiyya tamatso Kusada Rahma tana shinshina jikinta, dariya sosai khursiyya takeyi, Rahma ta ce, "wai miye abin dariya?.
Cikin dariya khursiyya ta ce, " a'a babu komai nadaiji kinata zuba k'amshin turaren ya Abdulmaleek ne.
Da sauri Rahma ta shinshina kayanta, ilai kuwa kamshin turaren bobo takeyi, da sauri tamik'e tashige cikin kichin, khursiyya da khairiyya suka shek'e da dariya harda tafawa.
Itadai Rahma tana kichin itama dariyar takeyi k'asa², lamarin bobo yana bata mamaki wlhy.............
*_luv u oll my fan's_*
*_(((S)))..........2017_*
[11/12, 2:56 PM] mrs bilkisu: 👩🏻💻typing........
❣ *_ABDUL-MALEEK_*❣
_•{🅱🅾🅱🅾}•_
*_NA_*
_*Bilyn Abdul*_
_sadaukarwa_
*_Abba Gana_*
*_Batul mamman_*
*_Billy giro_*
5⃣0⃣
Tana cikin kichin zaune danta kasa fitowa, jitake kamar su khairiyya sunsan miya faru, ihun Nawal ne yasakata fitowa dole, tasaki su khursiyya tanufo Rahma da gudu tarungumeta tana murnar ganinta, tana cikin cire mata uniform bobo yafito sanye cikin farar jallabiya, Shima Nawal taje ta rungumesa, yad'agata sama yana fad'in babyna yaushe kika dawo?.
Papa yanzun nan.
Toya school?.
Lafiya lau my papa.
To masha ALLAH sauka naje masallaci yafad'a yana direta k'asa, ya kalli Rahma datun fitowarsa tayi k'asa da kai, ya ce, "bara naje sallah.
Saika dawo tayi maganar kanta ak'asa.
Baice komaiba yafice.
Yaudai haka Rahma tawuni atakure Dan duk inda tayi idon bobo yana kanta, ko kunyarsu khursiyya bayaji.
Bayan sallar isha'i yashirya zai maidasu khairiyya Nawal tamak'ale wai saitaje, harsun fita yaturo Nawal takira Rahma itama tazo su tafi.
Murna tayi sosai Dan dama tsoro takeji wlhy.
Abaya ta tararda su khursiyya, dole tabud'e gaba tashiga, har Nawal zata shigo gaban ya ce, " takoma baya, Rahma tadaure ta ce, "pls kabarta muzauna aii zai ishemu.
Baice komaiba yatada motar, saida yafita daga gidan sannan ya ce, " kina 'Yar lukutarnan ne kujera d'aya zata isheku?.
Da sauri tajuyo tana kallonsa, amma shiba ita yake kalloba, idonsa nakan titi, d'an harara tamasa tareda murgud'a bakinta.....
Babu zato ya ce, "nikikema murgud'e da harara?.
Kanta tadafe Dan batasan yana kallontaba, aranta ta ce, " kai mutumin nan ya iya munafikin kallo wlhy, afili kuma ta ce, "nifa ban hararekaba, tak'are maganar da turo baki gaba.
Murmushin gefen baki yayi batareda yace komaiba.
Tunda suka shiga harabar gidan sukai karo da motoci reras, wannan alamace ta basawan gidan duksun zo kenan, shima guri yasamu yay fakin suka fiffito.
Yana gaba suna biye dashi, da sallama suka shiga falon daya k'awatu da haske.
Ya sulaiman ya ishaq ya Hamza duk suna gidan, hannu bobo yashiga basu suna gaisawa, su Rahma ma suka gaishesu tareda hayewa sama Dan gaida Ammi.
Ya Hamza ya ce, " kace tare kuke gaba d'aya, bobo dake k'ok'arin zama ya ce, "yana iya baby tamak'ale saitazo, nikuma bazan iya barin Rahma ita kad'aiba shine na ce, kawai tataho mu tafi.
Ya ishaq ya ce, " kai bobo banwani yardaba, kaid'innan baban soyayya.
Murmushi bobo yayi ALLAH Yaya kunyi bala'in sakamin ido agidannan amma babu komai dukzan ramane.
Dariya sukayi gaba d'aya ya sulaiman yad'an daki kafad'ar bobo yana dariya, autan Ammi barsu kaji, sumafa suna soyayyarnan.......
Sakkowar Ammi daga sama ta tsaida dariyar tasu, bobo yarissina ya gaidata, bayan sun gama gaisawa ta ce, "tom kutaso Appan naku yakammala.
Gaba d'aya suka mik'e abin sha'awa da burgewa, cikeda fara'a Appa yatari matasan samarin 'yayan nasa, suma duk suka zauna suka zagayesa, Ammi ta ce, "to akawo abinci ko?.
Kowa ya CE, " a'a.
Appa ya hararesu bangane a'a ba, tuni nak'icin abinci saboda nasan zakuzo shine yanzu zakuce wani A'a.
Dariya sukayi sukace to akawo ko kad'an suci.
Tare sukaci abinci da Appan su, bayan sun kammala sukashiga tattauna abinda yakawosu, dama akan bikinsu Khursiyyane, antsaida sati hud'u kacal, dama shi Appa haka yake saka bikin yaransa bayaso danisa d'innan, anan take suka tsara komai data dace, kowa yad'auki abinda zai iyayi, Appa sai sakamusu albarka yakeyi shida Ammi, daganan hira sukad'an k'ara ta6awa sannan suka mik'e zasu wuce, bobo ya ce, "Ammi ina yarannan muwuce.
Suwaye yara? Ya ishaq yatambayi bobo.
Rahma da Nawal.
Lah matarka kakecema yarinyar? cewar Appa.
Dariya sukayi gaba d'aya, bobo kam murmushi kawai yayi, ya ce, " Appa yarinyace mana shekarartafa 17.
O Dan shekararta 17 saika ringa cemata yarinya?, to aii yanzu tagirmi wannan sunan, cewar ya Sulaiman.
Bobo yaturo Baki gaba nidai kunga tafiyata saida safe, suduka dariya suka saka harda Appa da Ammi shidai yayi tafiyarsa d'akin Ammi, a can kuwa yasamesu sunata rubuce² itadasu kahiriyya yana shigowa suka 6oye, kallonsu yayi ya ce, "mikuke 6oyewane?.
Babu komai Rahma tayi maganar dasauri tana mik'ewa, yasan basuda gsky amma yayi fitowarsa yak'yalesu, azatonsa ko tsare tsaren biki sukeyi.
Rahma tad'auki Nawal datayi barci, saida taje tagaida Appa tamusi sallama sunata sakamata albarka sannan ta iske bobo aharabar gidan shida sauran 'yan uwansa.
Mota tashiga tajirashi, bayan sun kammala kowa yashiga mota sai gida.
Tunda suka tafi babu mai magana, daga Rahma har Nawal barci sukeyi, dahakadai suka k'arasa gida, harya kashe motar yafito babu Wanda yamotsa, yaduk'o yana kallonsu Yoshi yanzu yama zaiyi dasu?, d'an tsaki yayi yad'auki Nawal yanufi cikingida, har d'akinsu yakaita ya kwantar bisa gado sannan yadawo, azatonsa zai Tatar Rahma ta tashi amma INA barcinta taketa shek'awa da Alama kuma yanamata dad'i.
Aransa ya ce, " kegaki orobo amma sai son d'auka.
(Nikam bilynku nayi dariya araina, koyaushe tagaya masa tanason d'auka?.)
Itama d'aukarta yayi, yarufe murfin da k'afa sannan yanufi cikingida, sunkusa zuwa k'ofar falin tasak'alo hannayenta awuyansa, kallon fuskarta yayi yaga har yanzu barcinta takeyi, dak'afa yatura k'ofar yashiga, itama yadireta akan gadon, saidai yazo mik'ewa amma tak'i sakar Masa wuya Dan haryanzu hannayenta suna nan asak'ale, tsayawa yayi yana kallon fuskarta dad'an bakinta, sosai yake k'are mata kallo, yana kallonta amma bakamar yau dayake mata kallon k'urullaba, aransa ya ce, "babu laifi yarinyar k'yak'yk'yawace.
Sunkai minti hud'u ahaka, yakai bakinsa kamar zaimata kiss, komi yatuna? saikuma yafasa yad'an kalli gefen da Nawal take kwance, cikin dabara yazare hannanu NATA wai duk ak'ok'arinsa nakar ta tashi, him baisan Rahma dashegen nauyin barciba kenan.
Yacanjama Nawal kayan barci, yatsaya yana tunanin yanda zai canja na Rahma, zama yayi gefen gadon, yasa hannu ahankali yazuge zip d'in rigar atamfar dake jikinta, cikin dabara yasa6ule hannun Riga d'aya, Yakama k'arfen bra d'inta yacire.... Aiikamar ance tafarka tamik'e zumbur, ganinsa zaune kusada ita gakuma rigarta har Anfara cirewa yasakata d'an zaro ido, cikin muryar barci ta ce, " malam lfy?.
Lafiya k'alau malama yafad'a yana mik'ewa, baijira cewartaba yafice abinsa, itakuma tabishi da kallo tana muci muci da idanu.
Na CE, "humm kwadaiji dashi.
.*.*.*.*.*.*.*.*.*.*.*.*.
*_Bayan kwana Biyar_*
🅱🅾🅱🅾 yana kwance yana barcinsa kasancewar weekend ne, sama sama yaji kamar ana wak'ar.
_“happy birthday to you, happy birthday, happy birthday, happy birthday to you...”._
Tashi yayi zaune aransa ya ce, "birthday kuma?, tonawa kenan?, ihun Nawal dayaji yasakashi mik'ewa da sauri yanufo falo.
Tofa, yafad'a yana rik'e k'ugu tareda tsayawa kallon Rahma da Nawal, Rahma tanata zubama Nawal wani Abu mai k'yalk'yali itakuma tana tsale, yabi falon da kallo shima yasha decoration d'in balam balam.
Saikuma wani kati mai k'yau anrubuta...
*_“happy birthday my luvly Nawal, rice 100 may ALLAH bless you abundantly...... I luv yau so much”_*.💝
Murmushi yayi yataka ahankali har zuwa inda suke tsaye, yatura hannayensa duka a aljihu yatsaya yana cigaba da kallonsu.
Nawal ce tagansa, cikin farinciki ta ce, " my papa today is my birthday.
Murmushi yayi yadurk'usa k'asa tareda bud'e mata hannayensa, tazo tashige ya rungumeta, sorry my habibaty gaba d'aya namanta yau birthday d'inki, amma kigodema ALLAH daya baki momy tagari d'iyata, wannan yak'ara nunamin baki tareda maraicin rashin uwa, wasu 'yan hawaye suka mak'ale masa agefen ido.
Jiyayi ana goge masa, yad'ago ido yana kallonta, dasauri tamatsa baya saboda kunya, yayi murmushi tareda mik'ewa tsaye shida Nawal, k'arasawa yayi inda Rahma take daf da ita tamkar zai shige jikinta, cikin wata sassanyar murya yace my Cute ngd sosai ALLAH yabaki lada mai tarin yawa, ALLAH yakaimu ranarda zaki haifamin k'annen Nawal agidannan......
Da sauri tad'ago takalleshi, yad'aga mata gira... Aii saita shek'a da gudu tabar waje, tabashi dariya sosai Dan haka ya murmusa.
Nawal ta ce, "papa miyasa momy tagudu?.
Murmushi yayimata ya ce, " babu komai, jeki tashiryaki yau yawo zamuje tunda ba'a shiya miki wani bikiba.
Sosai Nawal take tsalle za'a yawo.
Bayan kamar minti30 Rahma tagama shirya Nawal cikin kaya masu k'yau, falo suka fito suna jiran boss, babu dad'ewa shima yafito cikin k'ananun kaya, sunbala'in MASA k'yau sai zabga k'amshi yakeyi.
Rahma ta ce, "masha ALLAH, ALLAH yayi halitta awajennan, duk azuciya take maganar shiyyasa harya k'araso kusada ita bata saniba.
Namiki k'yaune?, yay maganar acikin kunnenta.
Da sauri tad'ago tad'an murmusa tana jinjina masa kai tareda rufe fuskarta da tafin hannu.
Shima murmushin yayi, yakuma fad'in aiini nakine 'yammata, kiyyiata kallona harki gaji.
K'ara rufe fuskarta tayi Dan maganganunsa kunya suke bata, kutashi mutafi time nadad'a k'urewa.
A'a kuje kaida Nawal ni akwai abinda zanyine.
d'an harararta yayi ya ce, " ban ganeba?.
Rahma ta marairaice tamkar zatayi kuka, ALLAH akwai abida zanyi, gobe idan ALLAH ya kaimu masake fita tare.
Baice komaiba danyaji haushi, azatonsa batason zuwane kawai, Dan haka yakama hannun Nawal afusace suka fice daga falon.
Binsu da kallo Rahma tayi tana murmushi, ta ce, "ayya dadyn Nawal kayi fushine?, saikuma ta jinjina kai ta ce, " zaka huce idan kadawo kaga miya tsaidani.
Bobo sai zagayawa da Nawal yake wajajen shak'atawa na musamman, duk inda suka giftta sai an kallesu kuma sai an k'yasa bobo Wanda in ba kasaniba bazakace d'iyarsa bace Nawal, zaka d'auka irin d'iyar yayansace kokuma k'aramar k'anwarsa, bakowa yake yarda bobo yata6ama aureba bare akai ga haihuwa.
'Yammata marasa hak'uri kam har magana suke masa, wasukuma suyima Nawal kodan yatanka, amma ko kallo basu isheshibama.
A6angaren Rahma kam suna fita babu dad'ewa saiga Khursiyya da khairiyya sun iso damasu decoration, nandanan aka share harabar gidan suka fara aikinsu, tsaf suka gyara ko ina yad'auki k'yau, suka jere kayan kid'ansu..
Haba zuwa k'arfe biyu ai gida yafara cika da yara, matansu ya sulaiman da yaransu duksun iso, tare suketa hidimar had'a abinci, ga kayan rabonan ank'ukkula, zuwa k'arfe hud'u duk Wanda suka gayyata ya iso gidan.
Awannan lokacin kuma bobo da nawal suna can sun lodo kaya daya sayama Nawal sun kamo hanyar dawowa gidan, dukda abinda Rahma ta masa da safe saiyaji baiji haushintaba sosai, tun awaje yakebin motocin da akayi fakin awaje da kallo, aransa ya ce, "k'ila wani gidanne a anguwar sukayi bak'i, yay hon maigadi yalek'o, ganin shine yasa yak'araso wajen mortar batareda yabud'e masa gate ba.
A'a yabaka bud'emin gate ba kuma?.
Aii oga wlhy babu wajen fakinne aciki.
Kamar ya babu wajen parking?, mike faruwa acikin Gidan?.
Mai gadi yad'an Sosa kai Dan Rahma ta ce, " karya fad'a masa, ya ce, "saidai kashigo kagani oga.
Bobo yagirgiza kai kawai batareda ya tankaba yanemi waje awaje yay fakin suka fito shida Nawal, wayoyinsa kawai yad'auka amotar Yakama hannun Nawal suka nufi cikin gidan, bin ko ina yake da kallon mamaki yajinjina kai tareda nufar cikin gidan, suka shiga falon nanma shiru babu alamar akwai mutane awajen, baigama tunanin mike faruwaba yaji yara suna tafi dafad'in.
*_“happy happy birthday to you, happy happy birthday to you...... Saikuma gasu Rahma suma sun fito”._*
Aibaisan sanda yasaki lallausan murmushiba, dama abinda Rahma tashirya kenan shiyasa tak'i binsu?, jiyayai tak'ara girma da daraja azuciyarta. lol
Na ce, " hummm gaba gabadan bobon Appa.
------------------------