Showing 87001 words to 90000 words out of 111128 words

Chapter 30 - Abdulmalik Bobo Part 1 Hausa Novel Complete

20 Dec 2024

758

Saida sukayi sallama sanan yadawo hayyacinsa, yay firgigita yana murmushi.
Nasiba ta ce, " to Yaya gata nan.
Yau Nasiba sannu da k'ok'ari.
Yauwa yaya Nasiba tafad'a tana juyawa cikeda jin dad'in yau ya bobo yamata doguwar magana.
Tana tafiya bobo yamatso daf da Rahma tamkar zai shige jikinta, baya tad'anja tana fad'in mutanefa na kallonka.
Baki yata6e yana fad'in ina ruwana dasu, nifa kema kad'ai nake gani awajen.
Fararen idanunta tajuya tana gyara tsayuwa, itafa haushinsa takeji idanma bai saniba.... K'yass k'yass taji ana d'aukar hoto, d'agowar nan dazatayi aka k'ara mata, Ammar tagani abayan bobo d'aukeda camera, bobo yay masa alamun jinjina sanan yamatsa Kusada ita aka d'aukesu tare, bata ankaraba taji hannayensa biyu bisa k'ugunta, da sauri tad'ago suka kalli juna aka d'auka, gira yad'aga mata.
Bak'aramar kunya abun yabataba Dan haka tajanye jikinta tamatsa gefe Dan kunya, ga mutane sai kallonsu sukeyi, wasu naganin sun dace, wasu kam kishi yahanasu ganin dacewar.
K'awayen Nasiba sikace kar dai itace matarsa?.
Dariya Nasiba tayi ta ce, "eh mana, aii itace yace na nemo MASA.
Kai ammafa itama ta had'u, amma yarinyace sosai yamata yawa, saidai kuma tamore sosai dasamun wananan miji na garari, wata acikin k'awayen Nasiba tafad'a tana kuma k'arema Rahma da bobo kallo da Ammar keta kestasu hotuna.
Ana cikin haka amarema suka fito dasu ya Hamza aka cigaba da hituna harda sauran jama'ar wajen, bobodai duk inda zaka gansa yana manne da Rahma, ita dai duk kunya ta isheta, haka aka gama hituna hardasu Ammi da umminta Dan itama tunda safe tana gidan.
Haka aka cigaba da gudanar da biki awanan yini Alhmdlh kowa kagansa yana tareda walwalarsa.

*_6:30pm_* d'unbin jama'a suka raka amare d'akunansu, sundai sha kuka tamkar zasu shid'e, Ammi ma tasha kuka sosai na rabuwa da 'yan autocinta wad'anda suka kasance su kad'ai mata.
Appa da yayyensu duk sun musu fad'a yanda yadace, hakama dangin uwa Dana uba kowa yamusu daganan aka kwashesu sai gidajensu, Anfara kai khairiyya tunda itace hassana, sanan akai husaina khursiyya.
Bayan kamar awa d'aya 'yankai amare suka dawo kowa yafara shirin tafiya dinner da anguna suka shirya.
*_8:30pm_* aka fara tururuwar tafiya wajen dinner faty d'in data tara d'unbin jama'a na 6angare uku Dan had'ewa akayi domin sauk'ak'ama mutane wahala.
Masha ALLAH amare sunsha k'yau kamar babu gobe, sunyi kwalliya cikin kaya iri d'aya, farin material doguwar Riga, annad'e musu kawuna da golden d'in gwaggwaro, idan kagansuma saika Gaza ganesu abin sai Wanda yagani.
Can nahango su Xoxo su Deejerh kakus, su Sa'adatu sa'ad, zulaihat, mamn haneep, mamn sultan, Maryam zuntu, miss Ayush, deexerh, hawwa, kai idanfa naita lissafosu saina cika muku page d'in taf dasunayen masu karatu, ammafa har wad'anda ban ambataba na k'yallosu awajen.
Har Anfara gudanar da shagali hankalin amare atashe Dan basuga walk'iyar kod'aya daga cikin yayensuba bare matansu, amma yaran duk dangi sunzo dasu, su Nawal ma suna tare dasu daga kai amarya ba'a koma dasuba.
Tsayuwa wasu motoci yasakani gwalo idanu dansan ganin suwaye acikine?.
😳tofa masu karatu manyan yayyene.
Hummm tuwon girma miyarsa nama muka fad'a nida Maman ussy, sai baza ido muke muga wankansu.
Chaiiii!, namuku na IBO, wankafa aka d'auka iya wanka awajennan dankuwa kowa yahad'e cikin shiga ta alfarma shida matarsa, ya ishaq ya sulaiman ya Hamza, oga bobo duk sanye suke cikin wasu dakakkun shaddoji milk colour, sunsha d'inki 'yan ubansu, komai najikinsu iri d'ayane, takalmi hula agogo kai komaidai.
Suma su aunty Rasheeda Anty sameera Anty ummy, Rahma sanye suke cikin less milk da d'igon Silva, sun nad'a d'aurin d'ankwali kalar Silva, suma komai nasu iri d'ayane, cikin hall d'in taron suka dosa kowa rik'eda hannun matarsa, shigowarsu kallo Yakoma sama, kowa yabawa yake azuciyarsa, guri na musamman da aka ware musu suka zauna.
Kai yanzu ran khairiyya da khursiyya yay fes.
Dagananfa al'amura aka fara gudanarwa cikin farinciki.
Awajen lik'i kam manyan yayye sun ajiye tarihi suda matansu, abindai saimuce sambarka.
Dahakadai taro yatashi lfy, anguna sukad'auki amarensu suka maida gida, suma su bobo kowa gidan Appa yamaida matarsa Dan yauma anan zasu kwana.
Washe gari aka gudanar da walima dawuri Dan 'yan nesa su sami damar tafiya.
To dagadai yau biki yatashi, zuwa dare kuma gidan yarage hayaniya Dan mutane duksun ragu.
Sai bayan isha'i su Rahma suka bar gidan amare, kowa mijinta yaje yad'auketa sai gida.



.*.*.*.*.*.*.*.*.*.*.*.
Washe garima dai su Rahma saida suka koma gidan Ammi, suka gyara duk Inda aka 6ata suda 'yan aiki, duk kuma abinda aka aro aka maida.
Sudai su bobo kowa Yakoma kan aikinsa, hakama yara duksun koma makaranta, sai dare kowa yazo yakwashi iyalinsa, daganan kuma sai juma'a kowa ya huta.
Ammi da Appa sai sakamusu albarka sukeyi da jinjinama k'ok'arinsu, sun taimaka an rufama juna asiri anyi angama lfy cikeda farinciki.
Babu abinda kake ganin afuskar 'ya'yan na Appa da matansu sai murmushin jin dad'i.
Dahakadai kowa yay gida.




*_Safna.............._*

πŸ€”πŸ€”πŸ€”πŸ€”πŸ€”βœπŸΏβœπŸΏ










*_luv you oll_*
*_(((S)))........2017_*
[11/12, 2:59 PM] mrs bilkisu: πŸ‘©πŸ»β€πŸ’»typing........

❣ *_ABDUL-MALEEK_*❣
_β€’πŸ…±πŸ…ΎπŸ…±πŸ…Ύβ€’_


*_NA_*
_*Bilyn Abdul*_

_sadaukarwa_
*_Abba Gana_*
*_Batul mamman_*
*_Billy giro_*


6⃣5⃣


_wai masu karatu ina Safna?._

ALLAH sarki rayuwa, duk wanan shagali da ruguntsumi da'ake fama Safna nacan tana fama da ciwo batareda kowa yasaniba.
Babu yanda Ummi batayi da itaba akan tashirya suje wajen bikin amma tak'i ta ce, "kanta namata ciwo.
Ummi bata d'auki zancen ciwon nata serious ba dantasan halin Safna sarai da d'orama kai ciwon k'arya idan batason yin Abu.
K'yaleta tayi ta cigaba da jerangiyar zuwa bikin, yayinda Safna ke jiyyar zuciya Dana ruhi, zuwa yanzu tayi ALLAH wadai damai hali irin nata yafi sau dubu, tabbas tagane illar bijirema iyaye dazama akan ra'ayin rik'au, idan tatuna ranar data tuburema iyayenta batason auren dasukayi shirin yimata takan tsani kanta dadukkan rayuwarta, lallai zuwa yanzu tagane sharri zuciya dana k'awa, Dan baseera ta taka rawar ganin wajen zurma rayuwarta ga halaka.
ALLAH sarki zeenat dama kin fad'amin zanyi nadama, amma na k'aryataki, nak'i yarda da zancenki lokacin Sharrin shaid'an Dana zuciya suna d'awauniya dani, sai yanzu nagane ke mai k'aunatace da gsy, kece k'awa abar alfahari agaren......tarushe dawani kuka maiban tausayi.
Da sauri ummi tak'araso gareta tana fad'in Safna lfy kuwa?.
Tashi tayi zaune da sauri tak'ank'ame ummi tana kuka, ummi wlhy nayi nadama, yanzu zan canja, dan ALLAH ki gafarceni keda abba dasu ya munner, wlhy nayi nadama bazan sakeba........
Takuma rushewa da kuka yayinda numfashinta ke sama yana k'asa, k'irjinta tadafe tana fad'in wash ummi zan mutu, ummi k'irjina zai fashe..
Arazane ummi take girgizata tana kwala kiran Safna! Safna!!, ke Safna!!!.
Ina Safna tayi nisa batajin kira, numfashinta yatsaya cak da aiki, afirgice ummi ta ce, " nashiga uku ni sa'adatu mizan gani haka?, wayar safna ta raruma jikinta sai rawa yake takira abba, yana d'agawa tafashe dakuka mai tsuma rai, abban shaheed ka taimakeni kada safna tamutu dan ALLAH.
SHIMA cikin mamaki ya ce, "safna kuma?, miyafaru da safnar?.
Abba Shaheed nidai kataho gida wlhy safna bata numfashi gabad'aya wayyo ALLAH na safna karki mutu, munyafemiki dan ALLAH karki tafi kibarni wayyo safna....
Surutai da sambatu kawai ummi ke zubawa.
Cikin lokaci k'alilan saiga abba da likita harda ya munnir, ai ganin Safna sharaf kamar gawa doctor ya ce, " sud'auketa kawai atafi asibiti, jikinta yawuce adubata agida.
Ya munnir yasa6eta batareda yabarima likita ya k'arasa fad'aba.
Agaggauce suka isa asibiti.
Taimakon gaggawa aka shiga bama safna wadda saidai abinda ALLAH yayi kawai, dan kwance take sharaf babu alamar numfashi.

Masu karatu nimafa atsorace nake😟, safna saidai wani abu ga ALLAH.

Su Abba sai safa da marwa sukeyi ak'ofar d'akin da'aka sakata, ummi kam banda hawaye babu abinda take shar6ewa, Abba da ya muneer sai hak'uri suke bata.


*................................*
Awanan lokacin kam Rahma nagida itada Nawal da direba yad'akko yanzu Daga school.
Bayan Tamata wanka sukadawo falo, Nawal nagefenta zaune tanacin abinci itakuma tana duba buks d'inta taga ko anbasu homework
Nawal ta ce, "momy!.
Na'am babyna, miya farune?.
Nawal tayi 'Yar dariya, momy auntynmu ce ta ce, " wai bankai mata kayan bikiba, shine nace gobe zan kaimata, aizaki bani nakai mata ko?.
Murmushi Rahma tayi tareda d'agamata kai, zan baki my sweety na insha ALLAH.
murna Nawal tafara, itakuma Rahma tana kallonta tana dariya.
Bayan takammala cin abincin ta koya mata homework, suna kammalawa suka fito harabar gidan suna shan iska, Nawal tanata wasanta cikin 'Yar motarta, ita kuma tana zaune tana karatun book awaya dansu Basma sun sakata groups na Novels.
Jin k'arar bud'e gate yasa tad'ago tana kallon hanyar gate d'in dukda basosai take hangowaba amma taga kamar motar bobo.
Agogon dake manne ahannunta ta kalla _4:15pm_ afili ta ce, "lfy kuwa Nurulk'albi?.
Bobo yay farking a inda yadace sanan yafito, sanye yake cikin k'ananun kaya, blue d'in wandon jins da farar Riga mai dogon hannu, yayi k'yau tamkar yanzu yay kwalliyar, jakar aikinsa yad'auka ya rataya sanan yakwashi wayoyinsa, harya nufi hanyar falon saiya jiyo dariyar Nawal da Rahma abaya.
Dawowa yayi yanufi inda yakejin dariyar.
Nawal naganinsa ta tashi da gudu ta taroshi, rungumeta yayi yanamai farincikin ganinta, ya ce, " baby ya school?.
Lfy lau papana.
Masha ALLAH, amma yau ba'aje islamiyyaba?.
Kanta ta d'aga.
Ya ce, "miyasa?.
Shiru tayi Dan tama manta abinda yasa yau bazasu islamiyarba.
Ganin haka yasaka bobo d'agowa yana kallon Rahma, sauke idonta tayi daga satar kallonsa, idonsa yalumshe yana murmushi, afili ya ce, " gulma.
Kallonsa tayi tana turo baki Dan tasan da ita yake, fuska akumbure ta ce, "sannu da zuwa".
Bakinsa yata6e ya ce, " bazan amsaba, aiba haka ake tarar mijiba.
Idanu tad'an zaro tana kuma satar kallon Nawal.
Shima Nasal d'in ya kalla saikuma yamaida kallonsa ga Rahma, gira yad'aga mata yana wani murmushin gefen baki.
Tashi tayi tak'araso gareshi, tamik'a hannu nufinta yabata jakarsa, maimakon yayi haka saiya mik'a mata kafad'arsa duka.
Nawal takuma kalla taga takoma wajen motarta, d'an kad'a idanunta tayi sanan tasaka hannu tazare jakar.
Bak'aramar kasala tasakarma boboba data kad'a idanunta, yalashe la66ansa sanan yamatso daf da ita ya manna mata kiss akumata.
Ja baya tayi da Sauri, harma taso bama bobo dariya saboda yanda ta razana kamar wani maciji ya ta6ata amma yadake.
Ra6awa tayi ta gefensa tawuce, binta yayi da kallo harta shige.
Yakalli Nawal daketa wasanta da mota, ya ce, "baby kijirani yanzu zanyi wanka nadawo.
To my papa, Nawal tayi maganar hankalinta awasa.
Ciki shima yanufa.
Yana shiga d'akinsa Rahma na niyyar fitowa, Ra6awa tayi tagefensa zata fice yay saurin shan gabanta, k'ara kaucewa tayi nanma ya tareta, tad'ago ido tana kallonsa saitaga fuskarsa ta canja yakomamata ainahin bobo nada data sani ada.
Jada baya yayi yajingina da k'ofar, ya hard'e hannayensa ak'irji yazuba mata mayun idanunsa, k'asa tayi dakanta gawani tsoro yana shigarta, jitai miyasama take masa haka?, kodan taga yanzu ya sake mata yana wasa da ita?.
Kallonta yake daga sama har k'asa, shifa ganin yakema tak'ara MASA k'yau da haske, yad'an lumshe idanunsa yabud'e, murya a tausashe ya ce, " Rahma!."
Kanta tad'ago ahankali tana kallonsa, ganin ya zuba mata idanunsa da awanan munafikin kallon NASA k'asa k'asa yasa tamaida idanunta tana wasa da zoben hannunta.
Yakuma fad'in Rahma!.
Na'am ta amsa kanta asunkuye kuma muryarta tana rawa.
Ya ce, "miyeni awajenki?.
Tambayarsa tabata mamaki Dan haka tad'ago tad'an kallesa ta maida kanta k'asa sanan ta ce, " mijinane.
Ajiyar zuciya ya sauke sanan ya warware hannayensa yatako ahankali zuwa gareta, jin k'amshin turarensa yak'ara kusantota yasakata rumtse idanu, nanma tsayawa yayi yana k'are mata kallo, saikuma yasaka hannunsa yad'ago ha6arta, kalleni yay maganar akasalance.
K'ara rumtse idonta tayi Dan bazata iya kallon nasaba.
Yakuma cewa My Nusfulhayat kalleni.
Girgiza MASA kai tayi alamar a'a.
Ya ce, "miyasa?.
Batace komaiba amma tagyara tsayuwarta.
Bobo Yakuma narke murya can kasa tamkar mai rad'a ya ce, ''kina fushi da mijinki ko?, saboda kina zarginsa dacin amanarki yakeyi?.
Hawaye suka ziraro daga idanunta, ahankali suke silalwo visa kumatunta, yad'an cije le6ensa yanamai k'ara tsura mata idanu.
Matsota yakumayi, yasak'alo d'ayan hannunsa kan k'ugunta, ahankali yad'ora bakinsa visa nata, cikin Sauri da rawar jiki tabud'e idanunta saidai tamakaro Dan haryayi nasarar zira harshensa aciki, kissing nata yake cikin kwarewa danuna zalama.
Itakam tun tana yunk'urin kwacewa harta hak'ura tamik'a wuya Dan tuni ga6o6in jikinta sun saki, da wanan damar yayi amfani wajan cud'anyata San ransa, ganin tsayuwa tana Neman gagararsu yad'auketa can sukayi gado.

πŸšΆπŸ»β€β™€sum sum nafito wajen Nawal.

Soyayya sosai Bobo yasha, saida nutsuwa tazo musu sanan Yakuma jawota jikinsa yarungume, muryarsa can k'asan mak'oshi ya ce, "Rahma da gsk kina zargin mijinki da cin amanarki?.
K'ara kwanciya tayi luf visa faffad'an k'irjinsa tana shak'ar daddad'an k'amshinsa, muryarta nad'an rawa ta ce, " nifa ba zarginka nakeyiba.
Ya ce, "to miyasa kike 6ata rai idan kinganni?, miyasa kuma Safna tatafi gida batareda nasaniba?.
Idonta ta rumtse tareda sauke sassanyar ajiyar zuciya, wlhy bani nakori aunty Safna ba, kuma bansan abinda akai mataba tatafi, nidai naganta da kaya kawai.
To miyasa baki hanata tafiyaba?, Ko kuma ki sanarmin?.
Inatsoron kartamin masifane, kuma gashi acikin mutane Muke.
Huci yafitar daga bakinsa, yasaka hannu ahankali yana shafa kanta, suduka sukayi shiru nad'an lokaci, jin shirunta yayi yawa yad'ago yalek'a fuskarta saiyaga barci yakwasheta.
Maida kansa yayi ya kwanta shima ya lumshe ido amma ba barci yakeyiba yafad'a duniyar tunanine kawai, tundaga randa Appa yay masa maganar auren Safna harzuwa canjamasa da akayi da Rahma, bikinsu, rayuwarsu tanesa nesa, har zuwa yau dasuka zama Abu guda, yad'anyi murmushi dantuna darun Rahma, yasan kishine kawai kecin zuciyarta, jiyayi yak'ara k'aunarta nikin baninkin, yad'ago ahankali yana kallon fuskarta, ahankali take sauke numgashi ak'irjin nasa, fusakarta tayi fayau gawani annuri namusamman datake fitarwa, shiru yayi yana sauraren yanda Nawal take buga k'ofa tana kiran momy! papa!.
Tashi yayi ahankali da Rahma ajikinsa, cikin hikima yazameta daga jikinsa ya kwantar da ita tareda kara mata filo, kafin yagyara mata kwanciyarma harta gyra kanta tareda jawo filo tarungume.
Murmushi yayi yana mai kallon k'yak'yk'yawar fuskarta, azuciyarsa ya ce, "ragguwa da anta6aki sai barci.
Jin Nawal takuma bugawa yamik'e yad'auki tawul yad'aurama k'ugunsa sanan yanufi k'ofar yabud'e.
Tana tsaye abakin k'ofar, ya ce, " baby miya faru?.
Papa ina momyna?.
Saida yajuya yakalli Rahma sanan yadawo da kallonsa kan Nawal, momynki tana aikine jeki kijirata afalo kinji d'iyar albarka.
Kanta ta jinjina, ta ce, ''papa nakalli cartoon?.
Eh babyna jeki saka MBC 3 kigani, muma yanzu zamu fito.
Tafiya tayi abinta tana murna, shima yamaida k'ofar yarufe harda saka key.
Bathroom yashiga yay wanka, dama Rahma tahad'a masa ruwan wanka, bayan yagama k'alk'ale k'alk'alensa yafito.
Kujerar madubi yaja yazauna, yana cikin shafa mai yaga Rahma yatashi afirgice tana sambatar aunty Safna! Aunty Safna!!, Dan ALLAH karki mutu, A'uzubillahi minashshaid'anirrajim!, sai jikinta ke rawa, da Sauri. Bobo yamik'e yaje yajata jikinsa yarungume, yana kiran my Nusfulhayat nutsu kinji, mafarki kikeyi ba gske bane, nutsu.
Hawaye tafara zirarwa, a'a my Nurulk'albi Dan ALLAH ka kaini na ganta, kacemin bata mutuba, wayyo aunty Safna karki tafi ki barni.........
Kafin tarufe baki wayar bobo tafara wringing, dak'yar tayarda ya janyeta daga jikinsa yatashi yad'auki wayar, gabansane yafad'i shima Dan ganin sunan ya Shaheed 6aro 6aro akan screen d'in wayarsa.
Haka kawai yasamu zuciyarsa dayin rawa, dakuma k'ok'arin gaskata mafarkin Rahma, shiyyasa ba'ason barcin la'asar yafad'a azuciyarsa yana kallonta.
Ganin kallon dayake mata saita sake fashewa da kuka, cikin muryar kuka ta ce, "yan gidammune ko?, namasan zasu fad'amin aunty Safna na tarasune kawai...... Tasaki kuka maiban tausayi da tsuma zuciyar mai saurare.
Kiran ya Shaheed ne yakuma shigowa, jiki a sanyaye yad'aga yakara akunne, muryar ya Shaheed kawai dayaji yasaka zuciyarsa karaya, bayan sungaisa ya Shaheed yasanarma bobo abinda nikaina banjiba.
Cikeda tashin hankali ya ce, "ya Shaheed gamunan zuwa, koda suka yanke wayar.. Innalillahi wa'inna'ilaihirraji'un kawai bobo ke iya ambata, Rahma tataso ta warce wayar, ganin sunan Wanda yakirashi yasakata fashewa da kuka, matsowayayi Kusada ita ya ce, " addu'a Safna take buk'ata yanzu agaremu Rahma, kinga tashi kiyi wanka muje.

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login