Showing 6001 words to 9000 words out of 111128 words
suna kalakala.
Dariya Bobo yayi ya ce, ''yaya aii duk kune kuka mak'ala mini.
Sukayi dariya harda tafawa kamar wasu abokai.
Sai k'arfe 5:00pm dai dai sukabar asibitin, kuma har sannan yarinyar bata farkaba, kai tsaye gida suka nufa har ya sulaiman shima zai gaidasu Ammi.
Kowaya yafito cikin motarsa suka nufi cikin gidan suna 'yar hira.
Gaba d'aya mutanen gidan suna falon sama, Dan haka suma can suka nufa............
*_luv u oll fan's d'in aunty bilyn Abdul❣💓❣😁👌🏼._*
_Ngd da had'in kanku_
[11/12, 2:15 PM] mrs bilkisu: 👩🏻💻
❣ *_ABDUL-MALEEK_*❣
_{Bobo}_
_Story & editin_
*_Aunty Bilyn Abdul_*
✍🏿 _Written_
*_Marak'isiyya_*
_hak'in mallaka_
*_Aunty Bilyn Abdul_*
_sadaukarwa_
*_Abba Gana_*
*_Batul mamman_*
*_Bily giro_*
1⃣1⃣&1⃣2⃣
Da gudu Nawal ta taso ta rungume ya Sulaiman, yad'agata sama yana dariya, Nawal kin k'ara nauyifa yafad'a yana lakatar hancinta.
Ta kalli daddynta ta ce, "baby waikaji uncle yace nak'ara nauyi.
d'an hararta yayi cikin wasa, ya ce, "sai yanzu kika ganni baby.
A'a baby naganka tun d'azufa, nafara gaida uncle ne ko uncle?.
Ya Sulaiman yad'aga mata kai yana dariya, cikin falon suka k'arasa.
Bobo ya ce, "o kace yau family ya had'u?.
Ya Is'haq da ya Hamza, sukayi dariya suna mik'a musu hannu.
Khairiyya da Khursiyya ma dariyar sukeyi.
Guri suka samu suka zauna, ya Hamza ya ce, " ashe kuna tare?.
Eh wlhy muna tare, naje Asibitinne.
Tofa miya sameka?, cewar ya Is'haq.
No bani bane wata yarinyace......
Fitowar Ammi ta k'atse masa zance, tazauna cike da farin cikin ganin manyan 'yayan nasu.
Gaidata ya Sulaiman da bobo sukayi, fuskarta cike da fara'a ta take amsawa, tareda tambayar aikinsu dakuma iyalin ya Sulaiman.
Suna lfy wlhy Ammi.
Ammi ta kalli bobo, Mukarram yadai naganka wani iri?.
Fuska ya shagwa6e yana kallon Ammi, ALLAH Ammi nagaji over yau, kaina hard'an ciwo yakeyi.
Yanda yay maganar a shagwa6e saiya basu dariya.
Ya Is'haq ya ce, "Bobo shagwa6ar dakayi ko Nawal bata yinta.
Murmushi yayi kawai baice komaiba.
Ammi ta ce, " kubarmin Mukarram d'ina yayi shagwa6arsa lokacinsane ko bobon Ammi?.
Nanma dariya sukayi gaba d'aya, ya harari su khairiyya dake tuntsura dariya harda rik'e ciki.
Ku yarannan nakulafa kun fara rainani?.
Ya Hamza ya ce, "to aii abin dariya kayi, saika hanasu su dara?, kawai kayi maganin abun.
Bobo ya ce, " ta yaya kenan?."
Kayi aure kabar musu gidan cewar ya Sulaiman.
Mik'ewa Bobo yayi danjin and'akko maganar dabayaso, kunga bari nad'an watsa ruwa nadawo.
Baridai kagudu idan angama maganar kadawo, ya Is'haq yafad'a yana dariya.
Nanma dariya kowa yasaka harda Ammi.
Shikam yay shigewarsa d'aki yana fad'in kwa gaji kubarni.
Ammi ta ce, "nidai inaga Mukarram tare yake da aljana shiyyasa baya son maganar aure.
Ya Sulaiman ya ce, "Lah Ammi wane irin aljana kuma?, wlhy ras yake, shidai haka ALLAH yayosa bashida matsala da mace.
Hakadai kuke gani, nifa abinda na lura dashi ga Abdulmalik kawai bazai iya tunkarar mace ya ce, yana sonata bane, gani yake ajinsa zai zube kawai.
Hhhhhh wlhy hakane Hamza, Bobo dakake ji dagani akwai d'aukar kai agaban mata kai harma mazan, kamar wani jinin sarauta.
Dariya aka kumayi, Ammi ta ce, " aii yashafi sarautar, kunfa takurama yarona gsky.
Ya Is'haq ya ce, "ALLAH ammi yaron nan yawuce yanda kike zato, amma kwanannan zamuyi maganinsa, aure zamu MASA kawai.
Dakun k'yautamin wlhy, nidai nagaji da ganin Mukarram babu mata, nasan har yanzu rashin Ni'ima na damunsa, amma idan yayi auren ALLAH yasa aka dace da matar k'warai komai zai zama tarihi.
Insha ALLAHU ammi komai yazo k'arshe karki damu...
Daga nan suka cigaba da tattaunawa, annan ma ya Sulaiman take basu labarin yarinyar da bobo yakai asibiti da safe.
Zancen ya girgizasu daganan suka Shiga tattauna matsalolin fad'e da yara k'anan suke fuskanta ak'asar nan.
+
Bobo kam yana Shiga d'aki yacire kayansa, wanka yashiga yayo, yashafa mai yazura doguwar Riga blue da dogon wando bak'i.
Falo yadawo Inda 'yan uwansa suke akacigaba da hira da tattauna al'amuran rayuwa, ahaka har Appa yadawo.
Gaba d'aya suka mik'e cikin girmamawa sukayi MASA sannu.
Fuskar Appa cike da annuri yabi matasan samarin 'ya'yan NASA da kallo, masha ALLAHU yaukuma gidan cike yake da basawa.
Dariya sukayi danjin furicin mahaifin nasu.
Ya ce, " bari naje nawatsa ruwa sainazo ayi hirar dani ko?.
To Appa asakko lfy sukafad'a atare.
d'akinsa yanufa rik'e da hannun Nawal data k'ar6ar MASA jakka, dama kullum itace mai kar6a inhar tadawo school.
Hirarsu suka cigaba dayi, kiran sallah yasa suka mik'e sukayi alwala, Appa yafito ya samesu suka tafi masallaci abin gwanin sha'awa, shima Appa sai dad'i yakeji ganinsa cikin samarin 'yayansa ababen alfaharinsa.
Ko'a masallaci sun burge mutane, Dan a sahu d'aya suka jera reras.
Agidama khairiyya da khursiyya da Nawal sallar sukayi, ammi ma haka.
Bayan an idar ammi tasakasu suka shirya abinci a tsakkiyar falon Dan yau duk su ya Is'haq anan zasuci abinci, suka gama shirya komai da taimakon 'yan aiiki sannan suka koma d'aki domin gabatar da sallar isha'i da aka kira.
Basu dawoba saida akayi sallar isha'i, suka rankayo zuwa gida suna 'Yar hirarsu da tsokanar juna.
Afalon suka zube Appa ya ce, ''aini zuwannan naku yamin daidai, kamar kunsan dama ina nemanku.
Ya Hamza ya ce, "to Appanmu ALLAH yajishemu alkairi.
Amin suka fad'a gaba d'aya.
Ammi dasu khairiyya suka fito suma, rissinawa sukayi suka gaida Appa da yayyensu, Nawal taje jikin Appa tazauna.
Yashafa kanta yana fad'in amaryata kinyi sallah?.
Kai ta jinjina tana dariya.
Tomi kika rok'amana?.
Hannunta tasa abaki idonta na kallon p,o,p d'in falon alamar tunani, can takalli Appa tana washe wawulinta da hak'ori biyu yafad'i, ta ce, " Appa kasan mina rok'a?.
Saikin fad'amin amaryata.
Narok'i ALLAH ya kaimu Aljanna nida kai, da Ammi, da baby, da uncle Sulaiman, da uncle Hamza, da Uncle Is'haq, da aunty khursiyya da aunty khairiyya, da mom din gida uncle Is'haq, da momyn ya Ahmad da aunty Sameera, kuma nace ALLAH yasa muje makakka muduka sau dubu dubu babu iyaka muga kabarin Manzon ALLAH a madina.
Tafi sukai mata gaba d'aya suna fad'in ameen mai sunan manya.
Ya Is'haq dake kusada ita har sumbatar hannunta yayi.
Appa ya ce, ''lallai na more da amarya Ashe.
Ta ce, "Appa kasan mikuma na rok'a daga k'arshe?, ya girgiza kai yana murmushi, canayi ALLAH yasa nima naga momyna.
Gaba d'ayansu kallonta sukayi, tabasu tausayi sosai, Appa ya rungumeta cikeda tausayi, Bobo kam k'asa yayi da kansa zuciyarsa tayi rauni sosai, jiyake tamkar yafasa kuka saboda tausayin 'yarsa, tausayinta yana d'aya daga cikin abinda yasa yak'i k'ara aure, bayason ya auro wadda zata takurama d'iyarsa sanyin idaniyarsa.
Ya Hamza ya ta6ashi d'agowa yayi yana kallonsa, ya Hamza ya jinjina masa kai fuskarsa d'auke da tausayi.
Murmushi bobo yayi.
Saikuma ya kalli sauran 'yan uwannasa da iyayensa yaga dukshi suke kallo.
Kansa yamaida k'asa yana cigaba da murmushi mai ciwo.
Ganin haka Ammi ta katsesu da fad'in bismillah kusauka ga abinci.
Kowa ya sakko tskkiyar falon in da abincin yake.
Bayan Ammi tasakama Appa kowa yafa k'ok'arin zubama Kansa abinda yakeso.
Falon yayi tsit bakajin motsin komai sai k'arar filat da cokali, saikam surutun Nawal lokaci2.
Bayan sun kammala cin abincin 'yan aiki suka gyara wajen tsaf, Appa yakalli khairiyya ya ce, "auta zoki kaita d'aki ta kwanta.
To Appa khairiyya tafad'a tana mik'ewa, d'aukar Nawal tayi daga jikin Appa tanufi d'aki.
Falon yay tsit kowa ya maida habkalinsa kan Appa.
Appa yamusu sallama suka amsa.
Ya gyara zama cikin hikimar zance yafara musu nasiha da k'ara jaddada musu muhimmancin zuminci da hak'uri da juna, ahankali ya gangaro kan auren Bobo, Wanda tunda Appa ya ambaci sunansa gabansa yafad'i.
Appa yabasu labari kamar yanda yagayama su Ammi da ya Is'haq jiya.
Ya d'ora da fad'in yanzu dai mun yanke hukunci ranar juma'a idan ALLAH ya kaimu za'a tura dakomai har sadaki Dan badogon lokaci za'a d'aukaba, k'arshen watannan za'ayi bikin kowa ya huta.
Zuface tafara fita addukan sassan jikin Bobo, yakasa koda motsi dukda tsokanarsa da 'yan uwansa sukeyi suna fad'in ango kasha k'amshi.
Ammi ma sai dariya takeyi danjin dad'i, sai Alhmdllh take dad'i, su khursiyya kam harda 'yar bud'a.
Bobo ya galla masu harara.
Gaba d'aya akayi dariya harda Appa.
Daganan suka cigaba da tattauna yanda biki zai gudana da shagalin daza'ayi.
Appa ya ce, " suyi duk abinda sukeso bazai hanasuba, Dan Andad'e ba ayi wani shagaliba agidan.
Har k'arfe tara suna gidan, saida Appa yace yakamata sutafi gida hakanan wajen iyalinsu sanan suka mik'e kowa yanufi gidansa.
Bobo bayan yarakasu harabar gidan yanufi d'akinsa jikin a sanyaye, yama rasa wane irin tunani zaiyi shikam.............
_Tofa masu karatu, Yaya kenan?, shin ina Safna?, gafa gwaninta zai angwance, kowacece amaryar Bobo?, ya wannan zama zai kasance?, kudai biyoni kawai, basirar aunty bilyn Abdul ce, nikam copy nakemuku masoya._
*_hummm wasa farin girki, masoya yanzufa aka fara, kumuje zuwa wai mahaukaci yasai kura, yanzu muka dasa alk'alamin labarin Bobo!._*
*_masoya muna godiya ALLAH yanar zuminci._*
[11/12, 2:15 PM] mrs bilkisu: 👩🏻💻
❣ *_ABDUL-MALEEK_*❣
_{Bobo}_
_Story & editin_
*_Aunty Bilyn Abdul_*
✍🏿 _Written_
*_Marak'isiyya_*
_hak'in mallaka_
*_Aunty Bilyn Abdul_*
_sadaukarwa_
*_Abba Gana_*
*_Batul mamman_*
*_Bily giro_*
1⃣3⃣&1⃣4⃣
*_Gidansu Safna_*
Safna na kwance akan gado tana chart, sai faman murmushi takeyi, da alama tana jin dad'in charting d'in.
Rahma dake zaune akan sallaya tana karatun alkur'ani ta waigo ta kalli safna dataketa 6a66aga dariya harda rik'e ciki, kai Rahma ta girgiza tareda fad'in ALLAH ya shirya azuciyarta.
Kanta tamaida tacigaba da karatunta.
Safna kam bamatasan tanayiba, dariyarta taketayi cikin farinciki, hira takeyi da Baseera akan nemomata Bobo, Baseera tana gayamata akwai wani guy a unguwarsu sunansa *boy shiyakama subama aikin, Dan tasan cikin sauk'i zai samomusu bobo da labarinsa.
Tak'ara wani d'an ihun farinciki, tareda fad'in saini mata agidan Bobo.
Rahma takuma kallonta cike da mamaki, ganin bazata barta tayi karatunta cikin Nutsuwaba yasa tarufe alkur'anin tayi addu'oin ta tamik'e ta ajiye alkur'ani ama'ajiyarsa.
Hijjabinta tacire tana fad'in aunty Safna kofa sallar magriba bakiyiba har anyi isha'i amma kina kwance kina charting akan abinda k'ilama bazai amfaneki da komaiba.
ALLAHU Akbar maikaratu nagaba, Safna tafa idonta akan waya, tacigaba da fad'in malama Rahma jawo wata ayar na haddace wannan.
Ajiyar zuciya Rahma ta sauke, ta ce, "Niba malamarki bace, kuma ba wa'azi nake mikiba, ina tunatar dakene dannaga kin shagala.
Wani wawan dundu safna tasaukema Rahma abaya, Dan ubanki idan aljanna takice ki hanani, shegiya 'Yar iska uwar tsari, kenikam daba agabana ummi ta haifekiba wlhy danace anmata canji a asibiti, anya kuwa acikin 'yan barka wata bata sace ainahin d'iyar da ummi ta haifaba ta ajiye mata ke?.
Rahma tashare hawayenta ta ce, " kije kitanbayeta k'iladai kece aka canja mata, Dan halinki daban dana mutanen gidanna.
Afusace Safna taduro daga gado tana d'urama Rahma zagi.
Tuni Rahma tafice tabar mata d'akin.
Afalo taci karo da abbansu yadawo masallaci, sannu da dawowa Abba. Yauwa d'iyar albarka ina zuwa haka?.
Ba inda zani Abba, nadai fito falone nasha iska.
Masha ALLAHU, ina 'Yar uwar taki to?.
Tana d'aki Abba.
Yauwa jeki kiramin ita zamuyi magana, ina umminku?.
Ganinan Abba Shaheed ummi dake fitowa daga d'aki tafad'a.
Tamai sannu dazuwa sannan tafara shirya musu abinci.
Rahma tatsaya abakin k'ofa ta ce, "aunty Safna kizo Abba yana kiranki.
Shegiya munafuka gulmata kina kaimasane?.
Niba munafuka bace, yace dai kizo..., tana gama fad'a tafice.
Safna tasakko daga gadon tana mita, zan koya miki hankaline 'Yar banza maikan dankali.
(Araina nace kekuma maikan doya ko?.)
Kusada Abba taje tazauna, Abba gani.
Kanta yashafa yana murmushi haba safnan Abba miya faru kika k'unshe kanki a d'aki?.
Zamanta ta gyara tana ballama Rahma harara, babu komai Abba nayi sallane INA zaune ina Azkar.
Da k'yau 'Yar albarka.
Rahma kam ido tazaro waje danjin k'aryar da safna ta gilla, saikuma ta k'unshe baki tana dariya.
Safna na kallonta, Dan haka haushi yak'ara kamata.
_(Hattara iyaye kuringa kula da addinin 'ya'yanku, akwai yara dayawa masu wasa da salla irinsu Safna, wata zakiga tana zaune tana chart za'a kira salla, amma ko'a kwalar rigarta, har Matan aurema akwai masu halinnan, musamman yanzu da karatun Novels sukayi tasiri arayuwarmu, yakamata duk lokacin da aka Shiga sallah kiringa lek'a d'akin yaranki kitabbatar suma suyi, ALLAH yasa Mugane)._
Ummi ta ce, "kutaso ga abinci, atare suka tashi har zuwa dani, anacin abinci Safna na chart saida ummi Tamata magana sannan ta ajiyewayar tana zum6ura baki.
Bayan sun kammala Rahma takwashe kayan, takaima masu aiki su wanke.
Falon tadawo Inda iyayenta suke zaune harda safna.
K'asa ta zauna kusada Abbansu.
Zamansu babu dad'ewa ya Shaheed da ya Muneer sukayi sallam.
Cikin girmamawa suka gaida iyayensu, suma suka tambayesu ya iyalinsu?.
Kowa ya amsa da lfy k'alau.
Suma su Safna suka gaishesu.
Bayan gama gaishe2 Abba ya ce, "dama bawani abune yasa na tarakuba zancen auren safna ne yatashi.
Wata irin d'agowa Safna tayi arazane, aurena kuma Abba tafad'a da k'arfi!!!.
Suduka kallonta sukeyi, Abba ya ce, " eh aurenki safna ta, kiyi hak'uri abin yazo miki wani iri kuma 1time, wlhy nima haka lamarin yazomin babu shiri.
Kuka safna tafasa tana fad'in itafa wlhy akwai Wanda takeso Dan haka bazata yardaba.
Ya Shaheed ya daka mata tsawa, wlhy idan bakimana shiruba jikinki zaiyi tsami, iskancim banza kawai, Abban kike fad'ama haka?.
Toni Dan ALLAH baza'a bari aji uzurinaba haka kawai amin auren dole, narantse bana sonsa karma afara wlhy.
Idan bahakaba kuma wlhy zanbar gidannan.
Duka ya Muneer yakai mata tatashi dagudu tashige d'aku tana kuka da fad'in wlhy itafa bata sonshi.
Ajiyar zuciya Abba ya sauke ya ce, "akwai matsala kenan?......
Babu wata matsala Abba Shaheed ashema ita ta haifemu bamu muka haifetaba, wlhy acigaba da hidima kawai, idan ankaita ta mutu aranar, ni wlhy dama halin Safna ya isheni agidannan.
Shikenan ummin Muneer yanzu dai munyi dasu ranar juma'a zasu kawo komai, nasanar da Alhaji Rabi'u, (yayan ummi), sannan kuma suma su yaya na sanar dasu shida Abubakar.
Tom ubangiji ALLAH ya tabbatar da alkairi yasa ayi damu.
Amin Abba yafad'a, ya kalli su Muneer ya ce, " to manyan yayye yakukace?.
Dariya sukayi, yayi daidai Abba ALLAH ya Sanya alkairi, insha ALLAHU zamu fara shirya biki.
Tattauna maganar bikin suka cigaba dayi har zuwa wani lokaci, daganan su ya Shaheed suka tafi gidajensu.
+.+.+.+.+.+.+.+.+.+.+.
A 6angaren bobo kam abubuwa biyune suka cinkushe masa tunani, ga tunanin yarinyar da akaima fad'e, gakuma tunanin zancen Appa na yau, yasan appa sarai mutumne mai sauk'i da sanyi, komai zaiyi zaiyishine cikin hikima da lallashi, to amma mutumne kaifi d'aya idan ya ve e babu maisakashi fad'in A'a, Dan duk abinda zaiyi baya yinsa da ka saiyayi bincike.
Yasan ko giyar wake yasha bai isa ya gujema Auren nan ba, to amma shikam harga ALLAH baiji zaiso wata mace bayan Ni'ima ba, duk macen datayi kuskuren shigowa rayuwarsa bazata samu wani farincikin saba, ya rintse idonsa, ahankali yak'asa gaban wani k'aton hotonsa shida Ni'ima, sunyi k'yau sosai ahoto, suna tsayene gaban wasu filawoyi sun fukanci juna, yad'an rissina yadafa cikinta sannan tanada cikin Nawal, itakuma tana kallonsa shida cikin tana murmushi.
Hoton sunyi bala'in k'yau, wasu hawaye suka zuraro akumatunsa, baidamu daya gogeba sai shafa hoton daya cigaba dayi, yad'au tsawon lokaci yana kallon hoton daga baya yafad'a kan gado yana hawaye kamar wani mace.
.*.*.*.*.*.*.*.*.*.*.*.
Babu 6ata lokaci aka su Appa suka kai k'ud'i da komai ranar juma'a, antarbesu tarba ta mutunci da girmamawa, cikin girmama juna komai ya gudana aka tsaida biki sati uku kacal, saidai daga amarya har ango suna cikin tashin hankali, garama angon yadaure sosai yamaida komai ba komaiba, harma yanad'an saka baki idan 'yan uwansa suna maganar shagalin bikin.
Haka yasa ammi taji dad'i sosai itada Appa, sai albarka suke saka masa.
Nawal ma sai murana take ankusa kawo mata momynta.
Shirye shiryen biki ya kankama sosai Dan hidima akeyi babu kama hannun yaro, abubuwa sosai su ya Hamza suke shiryawa.
+.+
Yarinyar da akaima fad'e tana samum sauk'i saidai har yanzu bata iya magana, kullum sai Bobo yaje asibitin safe da yamma, har yanzudai ba'a samu iyayentaba ana kan nema, gashi bata magana bare asamu wasu bayanai daga gareta.
'Yan sandama suna aikinsu na binciko Wanda ya aikata laifin ta hanyar Number motarsa da matashin nan ya d'auka.
To ALLAH yasa adace amin.
A6angaren