Showing 21001 words to 24000 words out of 111128 words

Chapter 8 - Abdulmalik Bobo Part 1 Hausa Novel Complete

20 Dec 2024

745

ko k'annensa mata biyu wata tashiga irin wannan halin yasan zasushiga cikin tashin hankali fiyema da haka, ALLAH kad'ai yasan itama halin da iyayenta suke aciki yanzu.........jiyowa yayi dasauri danjin an ta6asa, ya Sulaiman ne.
Kaikuwa miya fiddoka da sassafennan?.
Haba Yaya yanzune safiyar?.
Harararsa ya sulaiman yayi, ya ce, "amatsayinka na sabon ango wanda aka kaimar sabuwar amarya jiya baikamatama duk yau aganka awajeba, kai daganan harma sati d'aya.
Hummm Yaya kenan, amma yanada k'yau nazo naga jikin yarinyarnan, kagafa tunda aka fara bikinnan bana samun damar zuwa.
To aii yanzu kaganta saika koma.
Yay...... Hannu ya sulaiman yad'aga masa alamar baya buk'atar jin komai.
Bayanda zaiyi haka yaymasa sallama yatafi.

Indai tak'aicemuku bayani yau tsawon kwanan amarya takwas bata saka angonta a idoba, sadai taji motsin shigowarsa da fitarsa, ko motsin cin abinci, kulum tana d'aki, inkaga tafito wani Abu zata d'auaka shima saita daidaici baya falon.
Aganinta shine yakamata yajata ajiki ya sake mata, tunda shine mai gidan, ita yanzu tamkar bak'uwa take agidan.
Shikam yana ganin ita yakamata taringa masa abinda zai sake mata d'in Dan da wannan halin Ni'ima tai saurin cafe zuciyarsa har yake ganin tafi sauran mata............


To masu karatu kuyi hak'uri da wannan yau naje anguwane, Marak'isiyya ta mannamin aiki tagudu.




*_luv u oll my fan's_*
*_(((S)))......2017._*
[11/12, 2:21 PM] mrs bilkisu: 👩🏻‍💻typing........

❣ *_ABDUL-MALEEK_*❣
_•{BoBo}•_


*_NA_*
_*Bilyn Abdul*_

_sadaukarwa_
*_Abba Gana_*
*_Batul mamman_*
*_Billy giro_*

*_wannan page d'in nakine miss xoxona, inafata kinyi sallah lfy?, ALLAH ya maimaita mana._*
_Luv u wujiga wujiga_😂❣.

2⃣9⃣=3⃣0⃣

Kwance take akan had'ad'd'en gadonta Wanda yaji shimfid'u na alfarma, tajuya kwanciyarta zuwa rigingine, idanunta suka sauna kan agogon dake manne a bangon d'akin 3:42am.
Ta waro manyan idanunta Dan mamakin yanda lokaci yatafi, afili tafurta kai kenen na kwana banyi barciba?.
Taja dogon tsaki da k'arfi, dama da gsk ne idan mutum ya ce, "yakwana baiyi barciba?, gsky itakam tana k'aunar iyayenta, tanaso kuma tayimusu biyayya, saidai tunkan ayi nisa tafara hangen tarin matsaloli a rayuwar auren nata. Domin kuwa alissafinta yau kwana takwas da kawota gidannan, saidai tundaga randa aka kawota gidan bata sake saka angon nataba a idonta, saidai taji motsin shigiwarsa dakuma fitarsa, kocin abincinsa, idan tatuna kulawar dayayta bata awajen taron bikin saitaita mamaki wlhy, mutum tamkar mai aljanu, kodayake saitaga kamar itama akwai laifinta, tunda ad'aki take wuni, saidai idan taji yunwa tadameta tafita tad'ebo abincin da Ammi ta aiko musu, gidan kansa takasa nutsuwa taimasa kallon tsaf........
Kwala kiran sallar asubane yadawo da ita hayyacinta, tamik'e domin gabatar da sallar, jitayi jikinta duk yayi nauyi saida tayi wanka sannan ta d'auro alwala.
Tana idar da sallah taji wani irin barci na d'ibarta, tashitai ta haye gado ta kwanta, cikin 'yan mintuna barci yay gaba da ita.

A6angaren bobo kam yamaida dukkan hankalinsa wajen binciko Wanda yayma yarinyarnan fad'e, sukansu 'yansandan dukya addabesu da masifar basusan aikinsuba, sanin shi d'an babban mutumne yasasu dagewa sosai kuma ana hangen nasara zuwa yanzu.
Rahma kam yana buk'atar ganinta amma aganinsa ita yakamata tafara nemansa tunda shine babban, ganin kamar tana shamasa k'amshi shiyyasa yafita harkarta ya maida hankalinsa akan aiki.

.*.*.*.*.*.*.*.*.*.*.*.
Sai k'arfe d'aya Rahma ta tashi, takai dubanta kan agogo, kai harnakai haka ina barci?, lallai nasha barci sosai.
Wanka tashiga, bayan tafito tashirya cikin Riga da siket na atanfa kayan sun bala'in mata k'yau, tayi sallar azhur sannan tanufo kicin Dan cikinta yafara kiran ciroma, gashi jiya tacema Ammi adaina kawo musu abinci zata cigaba da girkawa, Dan aganinta yakamata tamik'e wajen juya akalar mijinta zuwa gareta.

Alokacin Bobo yana gidansu, Nawal tamak'ale masa saita biyoshi yakawota wajen momynta.
Ammi ta ce, "Mukarram inaga katafi da ita kawai nasan insha ALLAHU Rahma zata rik'eta da Amana, kasan yarinyarnan kullum burinta ta kasance da mamanta akullum.
Bobo yahad'iye yawu Ammi ba tafiya da Nawal bane matsalar ina ganin kamar idan nad'auketa ban k'yauta mukuba.
Ammi tayi murmushi Wlhy ko d'aya mukarram aii munsan ba k'waceta kayiba, dama tunjiya Appanku yay maganar yau idan kazo kawuce da ita.
To shikenan Ammi ngd, ahad'a mata kayanta to muwuce.
Ammi tahad'o mata kayanta, wasu kam sai ahankali aringa kaimata.
Nawal kam sai murna take yau zata wajen momynta.
Ammi bari mutafi naga Appa haryau bai dawoba, gobe idan ALLAH yakaimu ma had'u, Dan zan koma aiki.
Ammi ta ce, tom ALLAH yatsare, yakaimu lfy, tazo gefen Nawal tana d'aga mata hannu.
Bobo yatada mota, yauwa Ammi idansu khairy sun dawo suhad'amin kayana duka Nima.
To zan Sanar musu agaidamin da d'iyar tawa.
" zataji."
Haka suka fice ammi da Nawal suna d'agama juna hannu.

.*.*.*.*.*.*.*.*.*.*.
Rahma na zaune a falo tazurama filet d'in indome idanu, dukda 'Yar Karen yunwar datakeji amma abincin yagagara ciyuwa agurinta.
Tabi falon da kallo, caraf idanunta suka sauka akan wani hoton Bobo yana zaune akan wata kujera, fuskarsa d'auke da tsadadden murmushi mai kashe zuciya, saina kusadashi shida Nawal, wanikuma a can gefe shida yayyensa maza dasu Ammi da khursiyya da khairiyya, sunyi k'yau sosai, daka gansu Kasan ciki d'aya suka fito masha ALLAH....
DA gudu Nawal tashigo tana kiran Momy! momy!!, da Sauri Rahma tamik'e Nawal tafad'a jikinta, itama saita rungumeta.
Ahankali Nawal ta ce, momy I miss u.
Miss u too my baby Rahma tafad'a tana mamakin 'Yar waye kuma wannan?.
Nawal takatse mata tunani da fad'in , momy inakikaje kika barni?, kullum saina tambayi baby da Ammi sai sucemin kina zuwa amma baki zoba.
Cikin mamaki Rahma tad'agota daga jikinta tana kallonta, gata 'Yar mitsila sai zance irin na manya.
Bobo na a tsaye yana kallonsu, Wanda azahiri kallonsa akan Rahmane, Ashe k'yan dayake kallonta dashi awajen taron biki tafi k'yau a Natural batareda kwalliyaba..... Maganar Rahmace takatse masa tunani, ta kuma rungume Nawal tana fad'in tom gani nadawo babyna kiyi hak'uri kinji.
Ita sai yanzu tatuna ance mata Bobo yanada d'iyama, jitayi tausayin yarinyar ya mamayeta, ALLAH sarki Rayuwa, ALLAH baya Barin wani Dan wani yaji dad'i, tafad'a acikin ranta.
Nawal tazare jikinta tanufi Inda Bobo yake, hannunsa takamo cike da murna tana fad'in baby naga momyna yau.
d'an murmushi yayi ya ce, "natayaki murna babyna, karasowa cikin falon sukai yazauna.
Rahma ta daure ta ce, ina yini?.
Lfy ya amsa batareda ya kalletaba.
Rahma ta ta6e baki aranta ta CE, " dama baka amsaba aii, dama na gaidakaine saboda kana gaba dani.
Maganar Nawal ce tasakata dawo da hankalinta Kansu, Nawal ce takai bakinta Kusada kunnen Bobo wai zata masa Rad'a, amma kuma kanajin maganar tata.
"Baby mikayima momy tak'icin abinci?, koka duketane?.
Da sauri Bobo ya kalli Nawal a'a baby ban daketaba, k'ila batada lfyane.
Tamaido dubanta kan Rahma, momy waibakida lfy inji baby.
Rahma tayi d'an murmushi A'a lfy ta k'alau, to momy idan lafiyarki k'alau miyasa bakici abinciba?, ko kinaso baby yabaki dakansane?......
Kafin Rahma tayi magana Nawal tamaida dubanta ga Bobo, baby kabama momyna abinci abaki kamar yanda kake bani idan nak'ici.
Bobo ya ce, "to baby idan banda abinki....... Da Sauri ta ce, "baby indai baka bama momyna abinci abakiba mun 6ata daga yau, ta tashi daga kusadashi takoma kan cinyar Rahma data daskare azaune danjin furicin Nawal.
Rahma tadaure ta ce, ''kinga babyna zanci dakaina, Dan lfy ta k'alau, kibar Dady yahuta kinga ya gaji ko, tashima muci tare.
Nawal ta tashi zaune, Rahma taringa bata abincin itama tana dannawa badan yaymata dad'iba, saboda damuwar dataima zuciyarta yawa.
Bobo yanad'an satar kallonsu, tabbas yaji dad'in yanda Rahma takar6i d'iyar tasa wadda akullum yake zullumin sama mata madadin mamanta data rasa......
Yanata tunaninsa harsuka mammala, Nawal ma tafara barci, mik'ewa Rahma tayi da ita zuwa d'aki, dama zaman dukya gundireta.
Yabita da kallo k'asa k'asa babu laifi tanada k'yau daga na fuska harna jiki, saidai bazai sotaba Dan Ni'imarsace kawai keda gurbin zama azuciyarsa.

"na ce, "hummmm ALLAH yasa."

Itakam Rahma koda takwantar da Nawal saitayi zamanta bata sake fitiwaba, sai bayan sallar la'asar.
Sannan baya falon, tanufi kicin tana fad'in baridai yau nayi girki kodan Nawal, had'ad'd'en abinci na gargajiya tahad'a mairai da lfy, tagyara kicind'in tsaf kamar ba'ayi komaiba, hakama falon takuma bad'e ko ina da nau'in turarurrukan wuta.

Saida tayi Sallar magriba sannan tayi wanka tayima Nawal, shiri tayi cikin wando dariga na Pakistan sky blue, rigan iya cinya sai wandon yakamata sosai, amma tayi k'yau kamar kasaceta kagudu, itama Nawal tasaka mata 'Yar Riga Mara nauyi.
Harzasu fito Nawal ta ce, "saita goyata, Rahma taduk'a Nawal tad'ane.
Falon suka fito inda ta tarar da Bobo zaune akan kujera mai d'aya ya d'ora k'afafunsa saman k'aramin tebir na gilas yana karanta jarida, gefensa lemo na kwali da Kofi anzuba rabi, yana sanye da wando 3/½ fari da riga ja Mara hannu.
Masha ALLAHU Rahma tafad'a azuciyarta.
Baby kalleni Nawal tafad'a tana d'agama Bobo hannu.
d'an d'agowa yayi ya ce, " naganki baby yamaida Kansa.
Rahma tasauketa tana fad'in tonima gobe saikimin goyon.
Nawal tawaro idanu waje kamar wata babba, lah momy bazan iyaba saidai baby yay miki, taje tadafa bobo, baby.
Ya ce, "na'am.
Zaka ramama momy goyon data minko?, kagani ban girmaba, bazan iyaba..
Bobo yakalli Rahma dake zaune tana mamakin wayau da surutu irinna Nawal, Dan yau d'aya tafahimci Nawal d'in tanada shegen wayau irinna sai antona d'innan ake samun irinsu.
Ahankali ya janye idonsa yamaida kan Nawal eh zan rama miki.
Tanufo Rahma tana murna, momy taso baby yagoyaki kinji.
Rahma tayi murmushi k'arfin hali a'a babyna nayafe basai yagoyaniba, kinga muje kici abinci, tafad'i hakane Dan mantar da Nawal wancen zancen.
Ta kalli Bobo daya maida hankalinsa kan karatun jarida ta ce, "ga abinci dady.
d'agowa yay yana kallonta danjin takirasa da daddy, itakam tai k'asa da kanta, takirasa da dadyne Dan batasan yazatace masaba, kuma baikamata takira sunansa kai tsayeba.
d'an lumshe idanunsa yayi yana wani guntun murmushi, tabashi dariya wlhy, amma saiya dake, wai dady yakuma maimaita sunan azuciyarsa.
Haka yamik'e yanufi dinning d'in.
Tuwon shinkafane miyar Agusi wadda yaji busashshen Kofi da nama sai tashin k'amshi takeyi, saikuma lemon ayaba Wanda yaji had'i na musamman.
Aransa ya ce, " ya akai tasan abincin danafi so ko Ammice tasanar da ita?.
Itadai Rahma tazuba masa komai tatura gabansa.
Tayi mamakin yanda yaci abincin sosai, Dan ita tayi tunanin zaice bayacin tuwo, tunda taga d'an hutune.
Bobokam abincinnan yaymasa dad'i jiyayi Rahma tak'ara girmaba a idonsa, taburgeshi sosai gata yarinya k'arama amma ta iya girki mai dad'i.
Bayan sun kammala suka dawo falo..........




*_saidafa nace kuyi hak'uri dani, Dan wlhy akwai buk d'in danayi niyyar fara posting ba wannanba, amma babu yanda zanyi Marak'isiyya tafara wannan, naga kuma bai dace nabarshi ban k'arasa mukuba, randa nake da ishashshen lokaci zakuringa ganin 2page Dan inaso nakammala nafara wancan, randa kuma nake busy zakuga 1 kawai._*
_Bak'in Haure shine buk d'in dazan fitar muku Wanda zai fita akark'ashin wata k'ungiya dana sanar daku abaya, ina buk'atar addu'arku, ngd sosai da k'auna, ina k'aunar masoyana aduk inda kuke._





*_Luv u oll my fan's_*
*_(((S))).........2017_*
[11/12, 2:22 PM] mrs bilkisu: 👩🏻‍💻typing........

❣ *_ABDUL-MALEEK_*❣
_•{BoBo}•_


*_NA_*
_*Bilyn Abdul*_

_sadaukarwa_
*_Abba Gana_*
*_Batul mamman_*
*_Billy giro_*


3⃣1⃣=3⃣2⃣

*_SAFNA_*
Tun bayan biki 'yan gidan suka fita harkarta gabad'aya, gaisuwarta kawai suke amsawa, itama aciki cikin.
Itako hakan bai dametaba Dan ta ce, "sagaji su sakkone tunda itaidai ALLAH ya tsallakar da ita daga auren dolen da akayi nufin k'ak'aba mata, to duk abinda zasu suyi tayi daga baya kenan.

Yau tana school, zaune suke itada k'awayenta zeenat da Baseera, hirarsu suke hankali kwance sunata shek'a dariyar shak'iyanci ga wani d'alibi bai suna Rabi'u, yayi wani dressing ne waishi adole babban yaro, yazo gurunsu yana fafa sukuma sai famfashi suke suna masa dariyar shak'iyanci.
*boy ne yak'araso wajen, tunda Safna ta hangoshi tafara washe Baki, ta ce, R.. Boy kaga k'ara gaba sai anjima mun had'u.
Sanin halin rashin mutuncin safna yasa Rabi'u barin wajen.
A'a *boy yayane?, incedai akwai labari mai dad'i?.
Aiko akwai labari mai dad'i saidai........
Saidai me?, kai dad'ina dakai komai dad'in zance saika nemo abinda zai 6atashi, baseera tafad'a tana hura hanci, Dan halinsu d'aya da Safna, shiyyasa sukafi shiri.
Muzauna kabamu misha zeenat tafad'a cikeda shak'iyanci.
*boy yakalli zeenat, zee baby yanajiki tsit ne.
Zeenat tayamutse fuska, babu Marsala kawai ina mamakin k'awatane yanda tarud'e akan wanj, saikace wata sakarai.
Harara safna ta watsa mata, indai bazaki dad'i alkairiba to kiyi shiru, Dan indai bansamu guy d'innanba to bak'in bakinkine yajamin.
Ido zeenat tazaro to ALLAH ya k'yauta yasa kisamu guy d'inki k'awata.
Baseera ta ce, "yanzu kikayi magana *boy jamuje.

*boy yagyara zama ya ce, " guy d'inki sunansa Abdulmalik Aliyu Abdulmalik, amma ana kiransa da (BOBO), lauyane maizaman kansa, mai tausayin talaka da kwatar musu 'yancinsu, danshi kud'i ba matsalarsa bace.
*boy yafara bama su Safna cikakken tarihin bobo daga farko har k'arshe, har aurensa nafarko da mutuwar matarsa, da kuma d'iyarsa Nawal.
Safna tazaro ido waje, *boy yanada d'iyafa kace?.
*boy ya ce, "shiyyasa nace, " miki akwai Abu Mara dad'i alabarin, ayanzu danake gaya miki kwana goma kacal da aurensa......
Aure kuma!!!?. suka fad'a suduka arazane.
Jikin safna Yakama rawa, tamik'e arazane batareda sha'awar jin k'arshen labarinba.
Zeenat tarik'eta da sauri, safna ina kuma zaki?, hannunta tafusge cikin rawar murya ta ce, "gidan zanje.
Gida kuma?, munfa kusa shiga lecture.
Tsaki taja batareda tabata amsaba tayi gaba.
Zeenat ta ta6e Baki tana fad'in 'Yar wahala.
Cikin masifa Baseera ta ce, "dammi zakice mata 'Yar wahala?, soyayyafa ba k'arya baceba.
Nima aii bance k'arya bace, amma ta safna batada tsari, kuma kad'anmma tagani indai tak'amarta bijirema iyaye, ta tashi fuuuu tabar wajen.

*boy ya ce, "nifa kuji dani Basee, cikon kud'inafa".
kaga dan ALLAH kaje idan mun had'u agida zanbaka, itama ta tashi tabar wajen.

.*.*.*.*.*.*.*.*.*.*.*.*.
Rahma tare sukai kwanciyarsu itada Nawal, koba komai tasamu 'Yar tayon kwana da hira, barema harga ALLAH tanason Nawal, jiya kad'ai dasuka rayu tare taji son yarinyar sosai a zuciyarta, dawuri ta tashi ta had'a musu break, kasancewar su Nawal suna Hutu yanzu bata tada ita daga barciba saidai tagama komai na gyaran gidan.
Tana d'aki zatayi wanka Bobo yafito cikin shigar suit bak'ak'e hannunsa d'aukeda k'atuwar rigar lauyiyi, d'ayan hannun yarik'e da jakar aikinsa da hular lauyoyi, yau yanada shari'a k'arfe 9:30am.
Ganin babu kowa Afalon saidai yasha gyara sosai sai k'amshi ke tashi, yad'an lek'a d'akin Rahma batanan sai Nawal kad'ai kwance tana barci akan gado, ahankali yak'araso yaymata kiss akumatu sannan yafito, dinning yanufa Dan yanajin kwad'ayin k'aracin abinci Rahma ayauma.
Itakam tana bathroom tana shirin yin wanka taji k'amshinsa, takafar mukulli tad'an lek'o ta hangesa yanama Nawal kiss akumatu, a ranta ta ce ,"yau albarkacin d'iyarsa anshigo d'akina kenan?, dukda dai bai nemi inda nakeba tad'an ta6e baki.
Shikam yana gama lodama cikinsa abinnan mai dad'i dasaka kunnen maici mik'ewa yatashi tareda yin hamdala dasakama Rahma albarka, agurguje yafice Dan time yawuce sosai.

.*.*.*.*.*.*.*.*.*.
Ikon ALLAH ne kawai yakai Safna gida, tana shiga d'akinta tanufa Dan falo babu kowa tasan ummi tana barci k'ila.
Tafad'a kan gado jagwaf kamar wadda akacema Abba yamutu haka tashiga kuka rurus, saidai tayi mai isarta sannan tayi shiru danba mai lallashi, yauce rana tafarko dataji kewar Rahma, Dan dukda tsangwamarta datakeyi indai yarinyar taganta cikin damuwa ita take lallashinta da kwantar mata da hankali, amma yau tamata nisa.
Tacije le6enta tana k'ara zubda kwalla masu zafi, ta ce, ''nad'au alk'awarin kota halin k'ak'a saina auri guy d'inanan, kuma saina rabashi da matar tasa Dan bazanyi shearing d'insa dakowacce maceba, banta6a Neman Abu narasaba a duniyar nan, nasan kaima bazan rasakaba bobona.
Ban ta6a bin malamaiba ko bokaye, bammasan inda sukeba, amma awannan karon duk inda suke saina nemosu, kuma zan kashe konawane Dan in mallakeka mijina, wasu zafafan hawaye suka zubo mata, kuka takeyi sosai da zuba sambatu harma da sa6o.


( Na ce, "hummmmm safna kenan, duk d'an daya hana uwarsa barci tofa shima bazai yiba).

------------------------:::::::::::
Agidan Bobo kam Rahma da Nawal ne suke wasan 'Yar 6oye, Rahma tarufe ido da k'yalle Nawal kuma ta6uya Rahma na nemanta, Nawal ta ta6ata tana fad'in momy kin ganni, da Sauri Rahma tajuyo inda taji maganar Nawal.
Bobo yashigo da sallama wadda babu Wanda yajita, tsayawa yayi yana kallonsu cike da burgewa, Rahma dake laluben Nawal tak'aro inda yake tana laluben Nema, jitayi ta damk'i wani hannu mai laushi da santsi.
Da sauri tacire k'yallen data rufe fuska danjin Nawal tana tafa hannu tana dariya dafad'in shikenan baby zai goya momy.
Kallon ido cikin ido sukaima juna shida ita saikuma suka dawo da kallonsu kan Nawal.
Baby ka ajiye jaka ka goya momy kawai.
Da sauri Rahma ta ce, " nikam Nawal na yafe.
Nawal ta k'ya6e fuska tana fad'in um um

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login