Showing 27001 words to 30000 words out of 111128 words
yaushe hakan tafaru?, yanzufa Haneef d'in yashigo gidannan ya sauya kaya yafita.
Bai sauraresuba yafice yabarsu cike da tashin hankali.
Abin kamar wasa Alh sunusi har dare yana Neman Station d'in da akakai Haneef amma babu ko Alamarsa, ransa yak'ara 6aci da harzuk'a, aiiko wlhy saiya d'auki mataki akan 'yan iskan police d'in dasukai k'arfin halin shigar masa gida harda kama masa tilon d'ansa namiji.
Gida Yakoma danufin zaije ga Qumissioner of police gobe idan ALLAH ya kaimu, saidai zuciyarsa namasa rad'ad'i idan yatuna Haneef zai kwana a Station yau.
.*.*.*.*.*.*.*.*.*.*.*.
*_9:30pm_* ya isa gidansa duk agajiye, jinsa yake yau fes tunda ankama masa d'an iskan nan, bayan sun gaisa da mai gadi yashige cikin gidan.
Babu kowa afalon, har TV akashe yake ga gidan tsit kamar babu kowa, da alama masu gidan har sunyi barci.
K'ofar yamaida yarufe sannan yanufi d'akinsa, yazube kayan hannunsa cike da gajiya, babu 6ata lokaci yacire kayansa ya fad'a bayi domin yin wanka.
Bayan yafito yagabatar da shafa'i da wutiri, 'yan dube dube yafayi da alama akwai abinda yakeson gani, amma babu, d'an k'aramin tsaki yayi tareda mik'ewa yafice.
Cikin barci Rahma taji ana bubbugata, afirgice ta tashi, Dan dama tsorace takwanta, saboda rashin dawowar mai gidan.
Ganin shine atsaye yasa ta sauke ajiyar zuciya, ahankali ta ce, "sannu da zuwa.
Bai amsaba ya ce, " ina shayina?.
Tad'an dafe kanta, wlhy na manta ne.
Aii yanzu na tuna miki, yafad'a yana ficewa.
Asanyaye Rahma tasakko daga gadon, Dan barcin data fara yasa jikinta yin lakwas, haka ta k'arasa kicin tana jan k'aramin tsaki, idonta cike da barci tadafa masa shayin, tajuye akofi tareda yanka lemon tsami ta matsa aciki, tad'ora akan k'aramin tire tafice.
Ganin baya falo gabanta yafad'i, kenanfa d'akinsa zata kai masa?, tai shiru kamar mai nazari, zuciyarta ta ce, "kije kikai karya huce Rahma ki k'ara jama kanji wani laifin", tunda tazo gidan yauce rana tafarko dazata Shiga d'akinsa, Dan haka k'irjinta keta dukan uku uku, haka tadaure ta kwankwasa, saida tayi kusan Monti biyu sannan ya ce, " tashigo.
Ahankali ta tura k'ofar tashiga, wani k'amshi yadaki hancinta tashak'a talumshe idanunta, saikuma ta bud'e ta sauke akan Bobo dake zaune abakin gado yana latsa laptop, k'afarsa d'aya ak'asa d'ayar kuma ya tank'washeta a gadon, sanye yake da kayan barci ruwan ganye mai turuwa, tana mamakin yanda yakeson latsa laptop da karatun jarida.
Jin shiru bata ajiyeba, bakuma tayi maganaba yasashi d'agowa ya kalleta, shima baiyi maganaba saidai tura mata k'aramin tebir na gilas dayayi.
Ganin haka yasa itama tad'ora batareda ta ce, "k'alaba.
Bayan ta ajiye saikuma tayi tsaye takasa tafiya.
Yana danna laptop d'insa yana shan shayi, tsawon minti 7 ita batayi maganaba shikuma ya shareta yanata aikinsa, yakula bazatace komaiba, kuma akwai magana abakinta, Dan haka shi ya daure ya ajiye NASA shan k'amshin ya ce, " kinada matsalane?.
Kad'an ta kalleshi taga har yanzu idonsa nakan laptop d'in.
gyara tsayuwarta tayi, muryartan nan mai kasheshi ta daki kunnensa, dama sonake naji yau ko lfy Baka dawo da wuriba?.
Cak ya tsaya da abinda yakeyi, yad'ago fararen idanunsa ya sauke akanta, sanye take cikin dogon hijjabinta har k'asa, sa6anin d'azu daya Tatar da ita da kayan barci.
Ahankali yasauke ajiyar zuciya, koba komai yaji dad'in kulawarta agareshi, cikin miryarnan tasa ya ce, "babu wata Marsala aikine yamin yawa a office.
" okey saida safe."
Harta kai k'ofa yana binta da kallo, yadaure ya ce, "incedai babu wata damuwa daga babyn taki?.
Bata juyoba amma ta tsaya, Dan furucinsa na k'arshe yaymata dad'i, muryarta araunane ta ce, " a'a babu Marsala, saidai tata jiran dawowarka, harta gaji tayi barci..... Bata jira amsarsaba tafice.
Ajiyar zuciya ya sauke tareda lumshe idanunsa, zuwa wani lokaci ya bud'e idon, d'an murmushi naga yayi Wanda bansan da liliba, saikuma yacigaba da aikinsa yana shan shayi.
Itakam Rahma tana komawa d'aki tahaye gado ta kwanta abinta sai barci.
::::::::::••••••••••••:::::::::
Washe gari Rahma ta tashi kamar yanda tasaba ta had'a break fast da gyaran gida, taima Nawal wanka itama tayi, kwalliya sosai taima yarinyar tai tsaf da ita, Dama ga ruwan k'yau d'an Asali, kan baby Nawal yasha gyara Dan jiya da yamma Rahma tayi mata kalba, kasancewar yau juma'a.
Tana cikin saka mata janbaki yaturo k'ofar yashigo da sallama ciki ciki kamar Wanda akaima dole
Da sauri Nawal ta hantsilo daga kujerar madubi danta hango daddynta ta madubi, oyoyo papa na tafad'a cike da farinciki tana rungumesa, shima d'aukarta yayi yad'aga sama yana dad'in "I luv u my child," yasumbaci kumatunta.
Ta shagwa6e fuska, papa shine jiya kak'i ka dawo ko?, lah nadawo mana, saidai kinyi barci sannan kitanbayi momy kiji?.
Nawal takalli Rahma dake kallonsu cike da sha'awa, wai haka momy papa yadawo jiya?, kai Rahma tad'aga mata tana murmushin daya kusan narkar da Bobo atsaye, hakane babyna yadawo kina barci.
Nawal tasunbaci kumatun babanta da k'asunba ta kwanta luf tanata shek'in gara.
Shikam hankalinsa nakan Rahma yana mata wannan munafikin kallon NASA k'asa k'asa.
Talura dashi tsaf dan haka tatsargu, rissinawa tayi ta ce, "INA kwana?."
Lfy, yafad'a cike da basarwa shi adole ba ita yake kalloba.
Rahma ta d'an ta 6e baki, dukda ta fahimci salon amsa gaisuwarsa kenan...... Muryarsa ta katse mata tunani, kushirya idan mungama break gida zamu wuce, Dan duk juma'a a can kowa yake yini.
Ahankali ta jinjina kai kamar wata k'adan garuwa.
Shikam yajuya yafice da Nawal ahannu.
Itama fitowa tayi tahad'ama kowa abinci agabansa, hankalinsa kwance yakecin abinci shida d'iyarsa, amma Rahma duk atakure take, haka kullum take cin abin ci atakure, bakuma danwai bata saba da ahakan bane, saidai kawai nauyinsa datakeji, tunda agidansu gaba d'aya suke had'uwa suci abinci tuntana yarinya.
Tananan tana juya cokali haryagama shida Nawal, yad'auketa suka koma falo suna jiranta.
Ganin yatashi yasata sakin jiki taci abincinta sannan takwashe kayan taje ta d'auraye.
d'aki takoma tacanja shigarta cikin wani had'ad'd'en doguwar rigar shadda pink colour, kayan sunmata k'yau sosai, tasaka k'aton farin hijjabinta sannan tafito, babu kowa afalon, danhaka takashe komai na kayan wuta, gamawata keda wahala yafito shida Nawal daga d'akinsa, hannunsa rik'eda jakar aikinsa.
Kallo d'aya yaymata yad'aukekai, saidai har azuciyarsa yaji dad'in hijjabin data saka, yanason kamilar mace arayuwarsa, gaba yay suka bishi abaya.
Tashaya kulle k'ofar falon shikuma sukai gaba cikin mota shida Nawal.
Ganin Nawal abaya itama tabud'e bayan zata shiga, ahankali yay maganar tamkar mai ciwon baki.
"Halan ni direban kine?."
Cak tatsaya tafasa bud'ewa, kuma tak'i dawowa gaban.
Yakuma cewa kina 6atamin lokacifa, kuma wajen aiki zanje, jiki a sanyaye tabud'e gaban tashiga, shima baisake cewa komaiba yatada motar suka fice bayan sun gaisa da baba mai gadi.
Karatun Alkur'ani yasaka musu, cikin k'ira'ar shiek Abdurraham sudes, ahankali Rahma kebin karatun, yana kallonta ta gefen idonsa, jiyay tak'ara girma a idonsa.
Har sukaje gidan Appa babu Wanda yay magana, garama Nawal takanyi jefi2.
Saida yatsaya suka gaisa da baba mai gadi, yaymasa alkairi kamar yanda ya saba sannan yashige ciki.
Yana faka motar Nawal tafice da gudu zuwa cikin gidan, sukuma suka fito cikin nutsuwa, da gudu khairiyya da khursiyya suka fito, rungume Rahma sukayi suna farin cikin ganinta.
Ta ce, "aini nayi fushi, daga zuwa d'aya baku sakeba.
Kiyi hak'uri auntyn mu, Ammi ce ta ce, " mubari sai nan gaba.
Bobo yak'araso yana harararsu to maganannu ai kwabari kushiga gida dai ko?, yay gaba abinsa.
Khursiyya ta ta6e Baki, aifa yau munga banu jarabatu yazo, ALLAH yasa aiki zai wuce cewar Khairiyya.
Rahma najinsu dai tayi murmushi kawai.
Cikin gidan suka shiga, hakan tayi daidai da sakkowar Ammi daga saman Appa, Dan Nawal nazuwa canta haura.
Ta rungume Rahma tanamai jin dad'in ganinta, cike da kunya Rahma ta rissina ta gaida Ammi, ta amsa cikeda fara'a, da tambayarta ya zaman babudai wata Marsala ko?.
Kan Rahma ak'asa ta ce, "Ammi babu matsalar komai, to Alhmdllh d'iyata haka nakeson ji.
A'a mukarram d'ina lfy dai ko?, Ammi tafad'a tana kallon bobo dayay tsaye yana kallonsu tun d'azun.
yaturo baki gaba kamar wani yaro, yo Ammi sai yanzu kika san dani?.
Ammi taje takama hannunsa, o ni na isa namanta da babana, kawai ina murnar ganin d'iyatane.
Yakuma turo Baki, Toni bari nakoma tunda bak'ya murnar ganina, yanda yay maganar ashagwa6e yasa su khairiyya kwashewa da dariya.
Harara ya watsa musu suka bar wajen, itadai Rahma murmushi takeyi da mamakin Bobo, irin wannan shagwa6a haka kamar wani d'an shekara 5, anace mata tanada shagwa6a toga Wanda yatakata iyawa.
Ammi ta lallashesa suka haye sama domin gaida Appa.
Appa yaji dad'in ganinsu sosai, Dan haka yaymusu nasiha sosai sannan bobo yamik'e yaymusu sallama Dan wucewa aiki, saikuma antaso.
Yakalli Rahma k'asa k'asa ya ce, "saina dawo.
Kanta ak'asa ta ce, " ALLAH yatsare yabada sa'a.
Yaji dad'in addu'arta Dan dama ita yake son ji.
Ammi taji dad'in addu'ar da Rahma taima bobo, hakama Appa, suma sukai masa yatafi.
Zuwa 10:30 gidan yagama cika, aunty Rasheeda da 'yayanta, aunty Sameera ma da NATA, aunty ummy ma haka, mazan kuma suna ajiyesu suka wuce wajen aikinsu.
Dan danan gidan ya haukace da hayaniya, yaran duk suna falon sama wajen Appa, sukuma iyayen suna falon k'asa sunashan hira kamar wasu k'awaye, babu wannan shegiyar ak'idar ta kishin Sauri, hirarsu suke sosai, Dan danan Rahma tasaki jikinta dansu, su aunty Rasheeda akwai saurin shiga rai, gasu khursiyya iyayen shafta............
*_luv u oll my fan's_*
*_(((S))).........2017_*
[11/12, 2:25 PM] mrs bilkisu: 👩🏻💻typing........
❣ *_ABDUL-MALEEK_*❣
_•{BoBo}•_
*_NA_*
_*Bilyn Abdul*_
_sadaukarwa_
*_Abba Gana_*
*_Batul mamman_*
*_Billy giro_*
*_wannan shafin nakune sister's, Raheenat Mamoudou, billy ladan, Asmy b Aliyu, Aysha Umar Abubakar, Alkairin ALLAH yakai muku aduk inda kuke, ALLAH yabarmana zuminci._*
Luv u dayawa dayawa❤⛹🏻♀😂.
3⃣7⃣=3⃣8⃣
Safna da k'awayenta ne tafe, daka gansu kasan agajiye suke, fitowarsu kenan daga lectures.
Zeenat tasauke numfashi tana fad'in wayyoni ALLAH na yaukam munji jiki wlhy, hummm kema kike fad'a wani naji, cewar Baseera.
Safna dai batace komaiba, saima tsirama wani guri ido datayi, baseera ta zungureta Safna yadai?, mikike kallo hakane?.
Ajiyar zuciya ta sauke tareda kallon Zeenat, Zee Dan ALLAH kalli Sir Hamza sosai, baya miki kama da Bobo?.
Zeenat takalli ya Hamza dake k'ok'arin bud'e motarsa da takardu ahannunsa, Zeenat ta ce, "wlhy safna saifa yau nakula sosai, towaima miyasa bakita6a tambayarsaba?, tunda naga awajensa muka fara ganin Bobo.
Baseera ta ce, " kumafa hakane, ALLAH baita6a kawo mana wannan tunaninba.
Kunga dawannan surutun kumuje gunsa karya tafi to, cewar Safna.
Assalamu alaikum.
Wa'alaikummussalam, ya Hamza dake k'ok'arin shiga mota ya amsa tareda juyowa.
Gaidashi sukayi, ya amsa yana nazarinsu suduka.
Baseera mai ido atsakar ka ta ce, "sir Dan ALLAH munzo tambayar wanine agurinka?.
Tofa ALLAH yasa nasani.
Insha ALLAHU kasani, Dan ALLAH sir waye Bobo?.
Wani d'an murmushi ya Hamza yayi, ya ce, " miyasa kuke son sanin waye shi?.
Zeenat ta ce, "wlhy sir babu komai sai alkairi.
Motarsa yabud'e yashige, azatonsuma bazasu sami amsaba, amma bayan yazauna saiya kallesu, ya ce, " Bobo kanina ne uwa d'aya uba d'aya.
Wata sassanyar ajiyar zuciya Safna tasauke, jitake tamkar ansakata a aljanna, muryarta na Rawa ta ce, "sir Dan ALLAH kataimakamin da number sa mana.
Yay d'an Jimm sannan ya ce, " tom kid'anban zuwa Monday zan nemi izininsa tukunna, idan ya amince saina baki.
Dukda ba haka tasoba amma taji dad'i sosai, ta ce, "ngd sir ALLAH yakaimu lafiya.
Amin yafad'a yana rufe motarsa, sallama yamusu yabar wajen.
Safna ta ce, " guys insha ALLAH matsalata takusa k'arewa.
ALLAH yasa cewar Baseera da Zeenat.
.*.*.*.*.*.*.*.*.*.*.
Fitowarsa kenan daga wata shari'a, hannunsa d'auke da takardu da hularsa, sai kuma d'ayan hannun ya sak'alo k'atuwar rigarsu ta lauyoyi, ya k'arasa Inda Br Nazeefi yake sukayi musabaha, dashi suka kara yau, shi yana kare mai k'ara, Bobo kuma mai laifi, yanda suka gaisa cikin girmama juna da sakin fuska bazakace sune yanzu suka d'auki zafiba akotu ba.
Wayar bobo tafara ruri, hannu yasa cikin aljihun wandon jins d'insa ya d'aukko, Br Nazeefi yaymasa sallama, shikuma yafar'a k'ok'arin kiran Ammar Dan wayar ta katse.
Bayan sun gaisa dad'an tsokanar junansu, Ammar ya ce, "nakirakane na gumtsa maka labari, tund'azun nake Neman wayarka akashe.
Eh wlhy muna shari'ane, wane labari kasamo mana my Guy?, nasanka baka labarin banza.
Ammar yay dariya, mutuminkane yazo wajena d'azu a haukace.
Mutumina kuma wakenan?.
Alh Sunusi dala mana, ahargitse yazomin yanason Sanin Inda d'ansa yake, nikam namasa kwatance, bayan kamar awa d'aya saigashi yadawomin da kud'i wainasa asakar NASA d'ansa, Dan yasan kud'i nake buk'ata.
Na ce, " masa karya damu zuwa Monday zamukaisa kotu.
Hankali tashe ya ce, "wai akan mima aka kama masa d'a?.
Shine nace masa ana zarginsa dayima yarinya fad'e.
Indai tak'aice maka bayani yashiga zage zage wai sharri akaima d'ansa, wlhy saimunyi Dana Sanin kama masa yaro, harda cewa zaije yasamu dady yaji idan shine yasani naringama mutane rashin mutunci, kajimin mutumfa.
Dariya sosai bobo yakeyi, ya ce, " shashasha kawai, baimaga komaiba saiya wayi gari d'ansa a prison.
Ammar ma dariyar yakeyi, ya ce, "mutumina bakada dama wlhy.
Dariya sukayi gaba d'aya, sukai sallama bobo yashiga mota sai gida.
Gidansa Yakoma yay wanka, cikin wata d'anyar shadda blue yashiya, abinka da fari sai d'aukar ido yakeyi, yad'ora farar hula da farin takalmi, (araina nace kai guy d'innan fa yaci sunansa bobo gsky, ya iya d'aukar wanka babu k'arya), haka yafito yanata zabga k'amshi kamar Wanda yay 6arin turare, mota yashiga sai gidan Appa.
.*.*.*.*.*.*.*..*.*.*.*.*.
Sukam su Rahma bayam sungama shaftarsu kicin suka Shiga kamar yanda su aunty Sameera suka saba duk randa sukazo, sukeyin girki.
Yauma haka suka dafa abinci kala kala, Ammi sirikar arzik'i, mai d'aukar matan 'yayanta tamkar yayan ta, sai saka musu albarka takeyi.
'Yan aikin gidan suka gyara ko ina, akaima yaran wanka kafin iyayensu su k'araso, Dan tare zasuje masallaci, kowa aka shiryashi tsaf.
Sumadai iayayen wanka suka sakeyi.
Rahma takar6i kayan su khairiyya tasaka Dan bata d'akko wasu kaya dabanba, kayan summata k'yau sosai kamar Dan ita akayi, dama jiya suka kar6osu faga wajen tela.
Suna d'aki suna surutu harsu Bobo suka k'araso suka kwashi yaran sai masallaci, harda Appa amota d'aya suka fice, dama duk juma'a haka suke tafiya gwanin sha'awa.
Sun gama suka mik'e da niyyar fitowa falo Rahma tad'auki hijjab zata saka, aunty ummy tarik'e, haba amaryarmu abari ango yazo yaga kwalliyar mana, Rahma data duk'ar dakai ta ce, "Anty ummy plzzz kibarni.
Aunty Rasheeda takwace hijjabin ALLAH bazaki sakaba, sokike kima auta bak'in cikin kallon kwalliyar?, kunga kumuje, babu yanda zatayi haka tabiyosu.
Abinci suka shirya a tsakkiyar falon, bayan an shifid'a k'atuwar ledar cin abinci, sungama shirya komai aka manta da wani Abu, Rahma ta ce, " bara nad'akko.
Gaf taji tayi karo da mutum, da sauri tad'anja baya, tad'ago ta kallesa Bobo ne tsaye cikin gayunsa.
Maida kanta tayi k'asa Dan yaymata k'yau da kwarjini, kayi hak'uri ban ganiba.
Baice mata komaiba, saidai binta da kallo dayakeyi kamar yau yafara ganinta, kayan sunyi mugun mata k'yau da kama jikinta Dan siket da rigane, kuma tad'anfi su khursiyya jiki, ganin bai tankaba kuma yak'i bata hanya tawuce, ta ce, "sannunku da dawowa, zan wuce.
Nanma bai motsaba, wani haushi ya turnuk'e Rahma, saikawai tajuya zata koma, caraf ya damk'e hannunta, abirkice tajuyo tana kallonsa, ga maganarsu Appa tanaji dasuke tahowa.
Baki na rawa ta ce, " plzz gasu Appa nanfa...... Bata gama rufe bakiba suka k'araso wajen, ya Sulaiman ne agaba, sai ya Hamza abayansa, sai yara da Appa da ya ishaq abaya.
Ya sulaiman da ya Hamza suka kalli juna suna murmushi, tuni Rahma tayi k'asa da kai, jikinta harya fara d'an rawa, amma d'an bala'in naku yak'i sakinta.
Ya Hamza ya ce, "romeo d'anbamu hanya mudai.
Saiyanzu yadawo hayyacinsa, Dan ba k'aramin narkar dashi Rahma tayiba yau, yasaki hannun Rahma, aiko takwasa da gudu tai ciki.
Abin yabama Bobo dariya, Dan haka yay murmushin gefen Baki, karasowar su Appa yasa ya sulaiman yaja hannunsa sukayi ciki.
Sannu da zuwa da gaisuwa Matan nasu suka Shiga mik'owa, bayan sun Risina sun gaida Appa, Rahma tanacan bayan khursiyya tamak'ale kamar wata muna fuka.
Appa ya haura sama Dan rage kayan jikinsa.
Waimiya faru naga kin dawo baki d'akkoba?, cewar Aunty Sameera dake kusadasu Rahma.
Tad'an Sosa wuyanta, aunty harfa natafi naji