Showing 18001 words to 21000 words out of 111128 words
ya Kaleel can yana kiranki Ku zauna wajensu momy.
To baby bye, tafad'a tana sauka daga wajen.
Shima hannu yad'aga mata yana murmushi.
Taro aka cigaba da gudanarwa yanda yakamata, yauma amarya da ango basuyi rawaba, saidai lik'i dasukaita zubama juna, yayinda dangima suka rufesu suna lik'a musu suma, mai wak'a yaga ruwan kud'i yakuma haukacewa yana wak'e ango da amarya.
Bayan sun koma mazauninsu akace su yanka cake.
Mik'ewa sukayi suka k'arasa inda aka ajiye cake d'in mai hawa uku, Wanda tasha ado mai k'yau, Rahma aka umarta tafara d'ora hannunta akan wuk'ar, sannan Bobo yad'ora nasa hannun akan na Rahma, bayan k'irga uku suka yanka, tafi akayi Raf raf raf.
Akace Rahma taciyar da Bobo, kunya dukta isheta amma yazatayine, haka taciro daidai bakinsa ta rissina tasaka masa abaki idonta ak'asa, aka kuma sakin tafi, tasaka masa kofin lemo abaki, kur6a biyu yayi tajanye tasaka hanky tagoge masa bakin, ihu aka saka ana bata tafi.
Itadai kanta nak'asa tayi d'an murmushi, bobo madai murmushi yakeyi.
Shima akace yabata.
K'aramin shima yaciro, yamatsa daf da ita sosai tamkar zai shige jikinta, batayi auneba taji yasak'alo hannunsa ak'ugunta, ajiyar zuciya ta sauke ahankali.
Cake d'in yasaka mata abaki, tafi mai k'arfi aka bashi, fuskarsa d'auke da murmushi yasaka mata cup d'in lemo, ku6arta d'aya ta kauda kai, yasaka hanky shima yad'an goge mata baki kad'an saboda janbakinta, sai kawai taji yabata Sumba akumatu (kiss) wani ihu aka saki gaba d'aya wajen ana tafi.
Rahma jitake kamar zata nitse awajen Dan kunya, gashi yak'i sakinta.
Dahakadai taro yatashi lfy, bayan hotuna da aka yi.
Amarya da ango suka shiga mota aka maidasu gida.
Luv u oll⛹🏻♀.
[11/12, 2:11 PM] mrs bilkisu: 👩🏻💻
❣ *_ABDUL-MALEEK_*❣
_{Bobo}_
_Story & editin_
*_Aunty Bilyn Abdul_*
✍🏿 _Written_
*_Marak'isiyya_*
_hak'in mallaka_
*_Aunty Bilyn Abdul_*
_sadaukarwa_
*_Abba Gana_*
*_Batul mamman_*
*_Bily giro_*
2⃣5⃣&2⃣6⃣
Kowa yagaji, ana shiga gidan gurin kwanciya kawai mutane suke nema.
Rahma kam harma tafara barci a mota, saida bobo yatada ita, aiko ko kallonsa batayiba tafice saboda kunya.
.*.*.*.*.*.*.*.*.*.*.*.*.
Wanka yafarayi sanan yay shirin barci, kad'an kad'an saiyayi tsak'i dad'an cije le6e, candai yakasa jurewa yakira khursiyya.
Duk suna d'akin Ammi inda Rahma take harda matamsu ya Sulaiman Dan suma yau anan zasu kwana.
Sunata shirin Barci aunty Rasheeda na tsokanar Rahma tanata murmushi da 6oye fuska.
Aunty ummy tamik'oma Khursiyya wayarta.
Kai aunty waye Dan ALLAH a darennan?, ke Bobo nefa.
Ya bobo kuma?, lfy bayanzu muka rabuba?.
Cikin tsokana aunty Sameera ta ce, "kika sani ko muryar matarsa yakesonji........ Dariya sukayi yayinda Khursiyya tad'aga wayar tasaka akunne hello yaya.
Muryarsa can k'asa ya ce, " kidafamin Lipton kimatsa lemon tsami biyu manya aciki, baijira amsartaba ya yanke wayar.
6ata rai Khursiyya tayi tamkar zatayi kuka ta ce, ''kai wlhy nidai nabani, daga dawo ga barci inaji amma zaiwani sakani aiki, ALLAH yasa abaka matarka gobe kuwuce muhuta da saka aikin tsiyarka.......
Lafiya kekuma aunty Rasheeda ta tambayi Khursiyya?.
ALLAH ya Abdulmalik d'innan ne, wai atsohon darennan zaisha Lipton Dan iyayi harda lemon tsami, nibansan tsiyar dayakeji ashan Lipton da lemon tsamiba.
Dariya su aunty Rasheeda suka kwashe da ita harda tafawa, aunty Sameera ta ce, "aii dolene yay control kansa da lemon tsamin irin wannan Sumba d'azu dayabama amarya awajen Dinner, o ni Abdulmalik anaso ana kaiwa kasuwa, suka k'ara shek'ewa da dariya.
Itadai Khursiyya fita tayi tana k'unk'uni da kumbura Baki, Dan batasan Inda zancen matan yayen Nasu yadoba.
Itama Rahma ba fahimtarsu tayiba, Dan haka ta tashi tashige bayi dan k'imtsa jikinta.
Akicin ta iske Ammi tana d'ibar abinci.
Ke kuma lfy baki kwantaba?, wakikema k'unk'uni ma haka?.
ALLAH Ammi ya Abdulmalik d'innan ne mana, wai adarennan zaisha Lipton hardasu lemon tsami, kawai salon saka aiki.
To idan kinyi hak'urima aii yaune kawai, gobe iyanzu yana gidansa.
Hakane ammi, ammafa kullum kamar ibadar ALLAH saiyasha shayinnan. Azuciyar Ammi saitake mamakin halin Abdulmalik, yana cikin damuwa amma bazaiyi aureba sai ammasa ta k'arfin tsiya, shidai halinsa daban acikin 'yayanta, ALLAH ma kad'ai yasan tun yaushe yake acikin wannan halin.
Afili kuma saita girgiza kai tana fad'in kidafa masa to dare nak'arayi.
Bayan fitar Ammi Khursiyya tadafa Lipton tanata mita, ta matsa masa lemon tsamin sanan tasaka a k'aramin tire tafice zuwa d'akinsa.
Akwance tasameshi rufda ciki, sanye yake cikin kayan barci.
Yaya gashi tafad'a tana ajiyewo.
Baice mata k'alaba bare ya d'ago.
tajiye tafito cike da haushi, babu yanda za'ayi yasaka ka aiki kaimasa yaymaka godiya bayan kagama, duk cikin yayinyunsu shine halinsa da ban, duk masifar ya ishaq yafi yaya bobo sauk'i.
Shikam kobayan fitarta yakai Monti Biyar sanan yatashi zaune yana matse fuska.
Dukda turirin da shayin yakeyi saboda zafi, haka yayta shansa yana cije le6e, yana gamawa wata zufa tafara karyo MASA adukkan sassan jikinsa.
Kwanciya yayi ahankali yana sauke numfashi, bayan wani lokaci yasamu nutsuwar sarayar ciwon nasa.
Kwanciyarsa yagyara barci yay a won gaba dashi.
*_washe gari_*.
K'arfe 10:30am aka fara gudanar da sisters day aharabar gidan, masha ALLAH komai tayi k'yau, yaudai basuga idon bobo ba, yana d'aki kwance barcinsa yaketa kwasa na gajiya.
Sisters day kam yabada ma'ana, amaryama yau tasha k'yau, su khairiyya sun raba k'yaututtuka taro yatashi lfy.
2:00pm aka gabatar da walima, mutane suka fara kama gabansu, wasuma bak'in sun wuce tun safe, wassu kuma sai gobe idan ALLAH yakaimu.
Rahma dum jikinta yayi sanyi tunda aunty ummy tashigo tace ta shiraya da angama sallar isha'i za'a mik'ata gidanta.
Kallo ihsan dake zaune Kusada ita tayi, ihasan wai ina wayatane?, kwana biyu wlhy bangantaba nazata tana wajenki.
A'a wlhy wayarki bata a wajena, amma bari akira muji.
Kiran wayar suka farayi....
Bobo nazaune ad'akinsa yana danna laptop yaji wayar Rahma dake caji tana wringing, kamar bazai dubaba saikuma yamik'e yad'auka.
Ana d'agawa ihsan tamik'ama Rahma wayar tana fad'in and'aga.
Cikin sanyinta ta ce, "Assalamu alaikum.
Lumshe idanunsa yayi danjin sassanyar muryarta.
Wa'alaikissalam ya amsa cikin nutsuwa.
Gabantane yafad'i danjin murayarsa, taganeshi sarai amma saita dake ta ce, " Dan ALLAH wanene?.
Jin haka shima saiya basar ya ce, "kema wacece?.
Mai wayarce, Dan ALLAH ya akayi tazo hannunka?.
Murmushi yayi tareda shafa gemunsa na gayu, ya ce, " mijinkine, nasamu wayar ahanunkine kuma.
Ajiyar zuciya ta sauke, muryarta nad'an rawa ta ce, "to shikenan.
Yanke wayar yayi kawai yana murmushi shima.
Ihsan dataji komai bata Neman k'arin bayani dantaji komai.
Screen d'in wayar yadasama ido, photon Rahma ne ajiki da Safna, sunyi masifar k'yau ahoton.
Tunda wayar tazo hannunsa baita6a tunanin dubataba, Dan tunda ya ajiye baibi takantaba, yau yaji tanata kukan k'arewar caji shine yasaka mata cajin.
Yad'an lumshe idon yabud'e akan wayar, kowacece wannan kuma?, yafad'a aransa.
K'ila yayartace, (wadda tace bata sona kenan?) Afili yay maganar, bakinsa yata6e yana k'arema safna kallo, tabbas tafi rahma k'yau, amma Rahma tafita kwarjini da fuskar kamala.
Bakinsa yak'ara ta6ewa yamaida wayar a caji.
Hawowa gadon yayi yacigaba da aikinsa.
.*.*.*.*.*.*.*.*.*.*.*.
Bayan Sallar isha'i Rahma tagama shiri cikin kyakykyawar Shiga ta material siket dariya, tayi k'yau sosai kuwa, sai tashin k'amshi turare takeyi.
Haka wasu k'alilan daga cikin danginsu, dakuma su aunty Rasheeda sukai mata rakkiya had'ad'd'en gidan Bobo dayasha gyara tamkar sabo.
Idonta na rufe tanata sharar kuka, da tunanin gamonta da ango yau, koyaya zai k'ar6eta kuma?, dukda yanuna mata kulawa awajen taron bikin hakan baya tabbatar mata dazata samu kulawarsa ayayin zamansu.
Dan zai iya yuwuwa yayima iyayensa biyayyane kamar yanda itama tayima nata biyya......
Da wannan tunani su aunty Rasheeda sukaimata sallama harda su ihsan suka tafi.
Kuka sosai tashiga rabzawa harda shashsheka, tana tausayama kanta da rayuwarta. Amma tana rok'on ALLAH tazama mai hak'uri da juriyar biyayya ga ALLAH da MANZONSA, dakuma iyayenta.
Zamewa tayi ta kwanta tana cigaba da kuka maiban tausayi da tsuma zuciya.
.*......*.......*........*.....*.
A6angaren Bobo kam yana d'akinsa harya kwanta hankalinsa kwance.
Ammi takalli agogon falon karfe 9:53pm amma har yanzu Bobo bai fito yatafi gidansaba.
Mik'ewatayi ta haura saman Dan gidan mutane sun ragu sosai.
Kallon mamaki tabisa dashi.
Shima yad'ago yana kallonta, Ammi na lfy kuwa?.
Lfy lau, mikakeyi har yanzu baka tafiba?.
Cikin mamaki ya ce, "Ammi ina kuma zani?.
Gidanka mana.
Gidana kuma?, Ammi canakefa sai gobe?.
Harararsa tayi, cikin d'an fad'a ta ce, " tunda d'azu su Rasheeda suka dawo daga rakkiyar matarka, amma kananan zaune, katashi katafi gidanka anbarta ita kad'ai, nasan tanacan atsorace.
Bata jira amsarsaba tafice afisace.
Ajiyar zuciya yasauke yana turo baki gaba kamar wani k'aramin yaro.
Haka yatashi ya canja kaya kamar zaiyi kuka Dan haushi.
Farar shadda yasaka sai maik'o takeyi, yad'ora jar hula da silifas ja mai k'yau, turare yafeshe jikinsa dashi, sannan yajawo jakar lop-top d'insa yasaka duk abinda zai iya buk'ata na 6angaren aikinsa, yakashe kayan wutar d'akin yafito sai zabga k'amshi yakeyi.
Ammi yatarar afalonsa tana jiransa, ganin ranta ad'an 6ace yasa yasaki fuska, cikin murmushi da zolaya ya ce, "Ammi na nayi k'yau.
Itama fuska tasaki tana kallonsa, ta ce, " masha ALLAHU Mukarram d'ina kayi k'yau sosai, ALLAH yaymaka albarka kaji, yabada zuri'a tagari, ya albarkaci wannan aure.
Biyayyar dakake mana ALLAH yasa kaima 'ya'yanka suyi maka.
Ammin Ammi na ngd sosai da addu'arki gareni, bari naje wajen appa namasa sallama ina baby mutafi?.
A'a ita ba yauba, sai bayan sati d'aya tukkuna.
Ammi saboda mi?, cikin shagwa6a yay maganar.
Dariya ammi tayi ta ce, "shagwa6a66ena sai angama amarci tukkuna, idan d'iyata tagama hutawa da gajiyar biki saikazo kad'auki Nawal d'in.
Shike nan ammi, amma.......
Katsesa tayi da fad'in kaga jekayima Appanku sallama dare nak'ayi.
Haka yahak'ura yanufi d'akin Appa, bayan sun gaisa yaymasa nasiha sosai da saka masa albarka sannan yafito yatafi.
Mota yashiga yabar gidan cike dakewar iyayen NASA.
Awajen wani gasa naman kaza ya tsaya, yasayi guda biyar sai k'amshi sukeyi, yasayi kayan fruit dayawa yanufi gidansa zuciya acinkushe da tunani kala kala...........
*_" Alhmdllh. inaga 'yan uwa yakamata mudakata anan sai bayan sallah, gobe idan ALLAH yakaimu kowa zai nemi k'unshi da k'itso babu time d'in karatu, jibima haka ga aiki tunda daren sallah ne, Dan haka muyi hak'uri zuwa bayan sallah idan ALLAH yakaimu lfy."_*
_ina muku barka da sallah, inakuma baku hak'uri da godiyar had'inkai da kuka bani, ngd sosai, inaga ni anan zan barku Dan bayan sallah zan koma gida, gashi wayata ta lalace bana charting yanzu, dasai nacigaba damuku, dama da wayar aunty Billy nake typing d'in, amma ina rok'on ALLAH yasa tacigaba damuku, dukda naga tanada aiyuka agabanta._
_Na rok'ar muku ita sosai akan taringa muku typing d'in ko babu yawa sosai, Dan wlhy buk d'in yahad'u sosai masu karatu, shiyyasa Nima narikice nahau yimuku copy, lagwadar labarin nagaba, Dan akwai cakwakiya sosai acikin Novel d'in, kardai nacikaku da magana ALLAH yasa tayi muku._
_Wanda na 6atamawa Dan ALLAH ya gafarceni nabarku lfy._
*_taku Marak'isiyya ibraheem musa._*
Luv u oll.
By ✋🏻✋🏻✋🏻✋🏻masoya, ALLAH yahad'amu da alkairinsa.
Ngd.
Aunty bilyna gareki, Dan ALLAH kicigaba da gashi🙏🏻🙏🏻🙏🏻🙏🏻plzzz.
[11/12, 2:21 PM] mrs bilkisu: 👩🏻💻typing........
❣ *_ABDUL-MALEEK_*❣
_•{BoBo}•_
*_NA_*
_*Bilyn Abdul*_
_sadaukarwa_
*_Abba Gana_*
*_Batul mamman_*
*_Billy giro_*
🤝 *_Assalamu alaikum, ina mik'o muku sak'on barka da babbar sallah, ALLAH ya maimaita mana, muga ta bad'in bad'in bad'ad'a, saidai akwai matsala babu Wanda ya aikomin da kai da k'afafu, bare suya.☹😋😂_*
2⃣7⃣=2⃣8⃣
Hon yayi mai gadi yabud'e masa gate, saida yatsaya suka gaisa sannan yay cikin gidan, guri yasamu yay fakin zuciyarsa cike da tunani kala2.
Yafito tareda kwasan kayansa yanufi ciki, tafiya yake tamkar bayaso, zuciyarsa cike da waswasi, yaushe rabonsa da gidan nan a rin wannan lokacin?...... K'ofar falon yabud'e yashiga, wani k'amshin dad'i yadaki hancinsa, yashak'a ya lumshe idannunsa sannan yabud'e, bin ko INA na falon yakeyi da kallo, komai masha ALLAH, Iyayen amaryar tasa sunyi k'ok'ari gsky, komai na falon farine da ratsin golden.
Hasken fitilun yak'ara yalwata k'yawun falon sosai, ajiye ledojin yayi yad'au jakar lap-top d'insa kawai yanufi d'akinsa.
Yazube kayan tareda fad'awa saman gado yana fad'in wash ALLAH na.
Yay lamo yana tunani Wanda bansan namiyeba, yakai minti goma ahaka sannan yatashi, harya fara cire ma6allin wuyan rigarsa saikuma yatsaya yana tunani, koba komai yakamata ya lek'a d'iyar mutane, k'ilama bataci komaiba, mik'ewa yayi yafito falon, kicin yafara shiga yad'auki filet da Kofi yadawo falo yasaka kaza d'aya afilet d'in, hakama kayan fruits d'in yazuba awani filet d'in daban, yad'orasu saman babban tire harda ruwa da fresh milk sannan yanufi d'akin.
Tiren ya ajiye ak'asa saman kafet d'in dake gefen lafiyayyayen gadon nata, yabita da kallo tana kwance ta takure waje d'aya kamar tanajin sanyi, yad'anyi tsaki yana kauda kansa daga kallonta, "k! Yafad'a ad'an kausashe.
Komotsi batayiba Dan bama tasan yanayiba, fuska yak'ara had'ewa yana kuma fad'in " k!! Wai bak'ya jinane?, ganin bata motsaba har yanzu yasashi matsawa Kusada ita daf, ashema barci takeyi yak'arshe maganar da tsak'i. Hannunsa yasa ya bubbuga filon data saka kanta, firgigit ta tashi tana kad'a manyan danunnan NATA masu suffar kwai.
Kauda idonsa yay daga kallonta Dan idanunta suna masifar tafiya dashi babu k'arya, ga abincinan kitsashi kici yay maganar yana k'ok'arin ficewa daga d'akin.
Ngd, amma nak'oshi, nitsatstsiyar muryarta ta daki kunnuwansa, bai juyoba amma yatsaya, hannayensa cikin aljihu wandonsa ya ce, "wannan yarage kuma naki, yay waje abinsa.
(Ni bilyn Abdul nace sabon salo, bobo Yakuma zaka canja mana?, bamuyi zaton hakabafa☹).
Itakam Rahma hawaye tamatso takuma komawa takwanta, saida tayi kuka mai isarta sannan ta tashi zaune, afili ta ce, " dama nasan bazan samu farincikiba, duk wata kulawa Daka nunamin awajen taron bikin naganin idon danginane danaka, ya ALLAH ka kawoma rayuwata d'auki, kodan darajar biyayya danaima iyayena, nashare musu hawayensu alokacin dasuke zuba, Nima ALLAH kaji k'aina ka daidaita zamana da mijina yafuskanceni tamkar kowacce mace, takuma rushewa da kuka.
(Ayya Rahma tabani tausayi gsky).
Sauka tayi daga gadon tad'auki tiren tafito, kicin tanufa Dan saida su aunty Sameera suka Nuna mata ko INA na gidan kafin su tafi, firij tabud'e ta saka komai Inda taga yasaka sauran, tad'auki fresh milk d'in da kofin tafito.
ko tsayawa kallon falon batayiba takoma d'aki, saida ta kulle k'ofarta sannan tacire kaya tayi canji Dana barci.
Zama tayi bakin gadon tasha fresh milk d'in sosai sannan tashiga bayi tai burosh tadawo tai kwanciyarta bakinta d'auke da addu'ar barci.
Shima yana komawa d'aki kayan jikinsa yarage yasaka na barci yahau gadon yazauna, jakar dayazo da ita yabud'e ya fiddo lap-top d'insa yafara aiki.
Ganin ba kwanciya zaiba nayo waje nikam Dan barci nakeji sosai.
_washe gari._
Da asuba kafin yawuce madallaci saida ya kwankwasa mata k'ofa, saida yaji alamar ta tashi sannan yafice.
Jin yafita takoma tayi kwanciyarta Dan har yanzu tana Hutu.
Saida gari yay haske sannan bobo yadawo gida, barci Yakoma abinsa Dan yana buk'atar Hutu sosai.
*_7:48am_*
Rahma ta tashi, wanka tafarayi sannan tagyara gidan tsaf dukda ko ina fes yake amma tak'ak'k'ara gyarawa, tabud'e ko ina da k'amshi, tana k'ok'arin komawa d'aki taji ana kwankwasa k'ofa, saida tad'anyi shiru nawani lokaci sannan. Tanufi k'ofar tabud'e, ganin khairiyya da khursiyya yasata sakin murmushi, hanya tabasu suka shigo sannan tamaida k'ofar tarufe.
Itama zama tayi suka gaisa (Dan zasu iya zama sa'anni itada tagwayen Ammin), ta ce, "yasu Ammi?.
Lfy lau tanama gaisheki, ga break fast tace akawo muku.
ALLAH sarki Ammi mungo sosai.
Khursiyya ta ce, " Yaya fa?.
Saida tayi k'asa da kai sannan ta ce, "yana barci bai tashiba.
Khairiyya da khursiyya suka kalli juna suna dariya, saikuma suka mik'e tomu bari muwuce sai anjima.
Kai haba dawuri haka?, ALLAH nazata anan zaku wuni.
Rufana asiri wannan mijin naki bayason warigi, khairiyya tafad'a ahankali.
Saida tarakasu har bakin k'ofar sannan tajuyo ciki, kwandon abincin ta d'auka takai dinning, ta ajiye komai inda yadace, taje kicin tad'akko duk abinda za'a buk'ata ta ajiye, abincinta tad'iba takoma bedroom taci.
Bobo kam ana gado ana kwasar barci, sai 10+ yatashi yay wanka yashirya cikin k'ananun kaya yayi k'yau sosai masha ALLAH, yaci sunan nasa Bobo.
Yaji dad'in ganin falon fes dagani kasan yak'ara shan gyara, baibi takan Rahma ba yanufi firij d'in dani danufi d'aukar fresh milk yasha saiyaga abinci, ganin kamar kulolin gidan Ammi yasa yazauna yaci abincinsa yay nak sannan yafice.
(Araina nace yadace ace yalek'a yaga yata kwana aii).
Rahma tanajin fitarsa, danhaka tarabga tagumi tana tunanin sabuwar rayuwarta ta yanzu.
.*.*.*.*.*.*.*.*.*.*.*.
Asibiti yanufa Dan duba yarinyarnan da akaima fad'e, jikinta yayi kyau sosai Alhmdllh, saidai har yanzu bata magana, tsakaninta da Bobo saidai kallo, tana bashi tausayi sosai Dan yanajinta tamkar Nawal, yasan idan Nawal ce ko cikin 'yayan yayensa