Showing 63001 words to 66000 words out of 111128 words
Amma afili saita turo baki, cikin shagwa6a ta ce, " nafa yimaka tun d'azun.....
Murmushi yayi tareda jawota jikinsa yamatseta sosai, suduka suka sauke ajiyar zuciya, jikin Rahma harya fara rawa, hakama k'irjinta sai dukan uku uku yakeyi har bobo yanajin bugawarsa, murmushi yayi Azuciyarsa ya ce, "yazanyi da matsoraciyar nan nikam?.
Jin tana mutsu mutsun kwacewa yasakashi k'are matseta tareda tallafo kanta, kissing d'in wuyanta yafarayi, daddyn Nawal pls kayi hak'ur.......
Bai bari tak'arasaba yahad'e bakinsa danata, sosai yake wasa da harshenta da jikinta, ganin yana Neman wuce gona da iri tafara haure haure da k'afarta tana mintsilinsa.
Saida yayi mai isarsa sannan yasaketa yana maida numfashi.
Da sauri itama tamatsa gefe tana maida numfa, saida yanutsu sannan cikin murya mai taushi amma asark'e ya ce, " kizo kimi Addu'ar inba hakaba namiki abinda yafi haka.
Babu shiri tajuyo tamasa addu'ar tashafa masa kamar yanda yabuk'ata,, shikam sai dariya yake k'asa k'asa wai matsoraciya.
Shiru tamasa tana tunanin hali irin na maza, Dan itakam wannan *_SABON AL'AMAREE_* yazarce wayonta.
Safna kam hankalinta a kwance yake yanzun, tunda malam da'u yace mata aii babu abinda zai shiga tsakanin Rahma da bobo tunda basusan junansu, acewarsa yaturo wani aljani dazai dinga gadinsu karsuji sha'awar junansu ma bare har wani Abu yashiga tsakaninsu.
Hummm kaji masu jayayya da hukuncin ALLAH.
######
DA SAFE haka Rahma tatashi tanamai tsananin jin kumyar Bobo, Sam tak'i yarda su had'a ido.
Safna tana lura dasu, Dan haka ko awajen break tayi kicin kicin da fuska tanata harare harare, babu Wanda yakula da ita, bobo idonsa nakan matarsa, itakam Rahma tamaida hankalinta wajen bawa Nawal abinci abaki dankarta makara, dahakadai aka gama break, bobo yad'auki Nawal suka fice, Rahma tarakasu har wajen mota, tafiyarsu babu dad'ewa itama Safna tatafi makaranta.
Har gabda magriba safna bata dawo daga makarantaba, hankalin Rahma dukya tashi, gashi takirata amma yak'i wucewa, duk halin datake ciki bobo nakula da ita ammadai baice komaiba.
Bayan yayi shirin masallaci yafito, afalo ya iske Rahma tanata safa da marwa, yay mata kallon tsaf, kamar zai wuce saikuma yajuyo, wai lfy kuwa?.
Yatsine fuska tad'anyi, wlhy aunty Safna ce har yanzu bata dawoba, gashi nakira wayarta tak'i hucewa, dan ALLAH kozakad'an gwada kiranta? muji.....
Yanda tayi maganar saita bashi tausayi, baice komaiba yazaro wayarsa a aljihu, harzaiyi amfani da family layinsa saikuma yafasa daya tuna wazai kira, layinsa dakowa yasani na office yay amfani dashi, ido yad'ago yana kallonta alamun tafad'a masa number.
Tafad'a shikuma yana sakawa, cikin mamaki sosai yake kallon number dan ana kiransa da turo masa message da ita, basarwa yayi yakirata Dan bayaso Rahma tafahimci komai, cikin sa'a kuwa yana kira tashiga, bugu biyu tad'auka jikinta har rawa yakeyi Dan ganin Wanda yakirata.
Cikeda salo tace assalamu alaika, sanin muhimmancin sallama kawai yasakashi amsawa, murya adak'ile ya ce, "kina inane?."
Wani sanyin dad'i Safna taji, takuma kashe murya can k'asan mak'oshi, wlhy moto nane yad'an samu matsala kozakazo ka taimakeni.......
Baibata amsaba yakashe wayar gaba d'aya, ya kalli Rahma ya ce, "tace tana zuwa motantane yasamu matsala amma angyara.
Hummm kunfaji bobo da k'arya🤣.
ita kam safna yana yankewa tayi saurin kallon wayar, ranta yad'an 6aci amma saita danne takirashi, jin wayar akeashe yasa tayi zaton ko bashida caji.
Babu dad'ewa kanikawan data kira suka iso, mukullun mortar tabasu tatari adaidaita tayo gida............
*_luv you oll_*
*_(((S))).....2017_*
[11/12, 2:57 PM] mrs bilkisu: 👩🏻💻typing........
❣ *_ABDUL-MALEEK_*❣
_•{🅱🅾🅱🅾}•_
*_NA_*
_*Bilyn Abdul*_
_sadaukarwa_
*_Abba Gana_*
*_Batul mamman_*
*_Billy giro_*
_assalamu alaikum, kwana biyu kunjini shiru masoya bobo, wlhy wutarmuce tasamu Matsala, amma yanzu komai normal._
5⃣5⃣
Ana cikin sallar isha'i safna ta shigo gidan, babu kowa afalon sai k'arar TV tawuce d'akin Rahma suna sallah itada Nawal.
Da sauri tadawo baya dan tanada tabbacin Rahma bata gantaba, kai tsaye wajen abincin kan dinning tanufa, ta bud'e abinci tayi barnad'e barbad'enta tamaida tarufe sannan tanufi d'akin.
Zuwa sannan sun idar da sallah, Rahma ta ce, "kai aunty har hankalina yatashi wlhy, naga dare yafarayi kuma nakira wayarki tak'i tafiya.
Safna ta ce, " ayya my lil motatace tasamu matsala gashi wajen babu network.
To ALLAH ya kiyaye gaba.
Ummi takiraki kuwa?.
A'a safna tafad'a cikin kallon Rahma, miya farune?.
Babu komaifa d'azu bayan tafiyarkine takirani wai Abba yanata fad'a yakamata ki koma gida tunda nasamu sauk'i, shine nace suyi hak'uri ayi bikinsu khairiyya saiki koma ko?.
Numfashi safna ta sauke, azuciyarta ta ce, "su ummi fa kuna k'ok'arin 6atamin aiki, amma zanyi k'ok'ari acikin 'yankwanakin dasuka ragemin nayi duk abinda yadace, afili kuma saitayi murmushi haka yayi Rahma, abinda tafad'a kenan kawai tamik'e zata shige bayi.
Bobo yak'arasa shigowa d'akin Dan tund'azun yana bakin k'ofa tsaye yana sauraren firar tasu.
Safna dake k'ok'arin shiga bayi tajuyo tana kallonsa, suna had'a ido tasakar masa wani lallausan murmushi, ya Bob ngd fa da d'akkoni ALLAH yabar zuminci tak'arashe maganar da d'aga masa gira.....
Bobo kam ya daskare atsaye miyarinyar nan take nufi?, agidan uwarwa nad'akkota d'in?.....
Rahma madai kallon tuhuma take masa, Dan duk abinda Safna tamasa akan idonta, tuni idonta yaciko da kwalla saboda kishi, ita kanta batasan tanada kishi mai zafiba kamar haka, ta had'iye wani Abu mai d'aci daga mak'ogoronta, mik'ewa tayi tafice daga d'akin kawai.
Da sauri yajuyo yabi Rahma da kallo harta fice, Nawal ma dabatasan bikin da akeba tatashi tabi bayan Rahma, daidainan Safna tafito daga bayi, murmushin mugunta tasaki sannan ta tako ahankali har zuwa gabansa, my jaan rago baya zama gwani, nasan kaima kana sona, amma bansan mike hanaka nunawaba?, so karka damu ni bana tsoron Rahma zan fahimtar da ita ta kurman bak'i, idan bata ganeba zan mata fassara.
Tunda tafara maganar kallonta kawai yakeyi, yama rasa wane mataki zai d'auka akanta, kafin yafarga tafice abinta, haka shima yabi bayanta tamkar soko.
A dinning suka tarar da Rahma da Nawal sunacin abincinsu, bobo yaja kujerar dake kusada Rahma ya zauna, itama safna tazauna akusa dashi suka sakashi tsakkiya, tunda suka fito ko Inda suke Rahma batama kallaba, abincinta kawai takeci.
Safna taja filet tafara zubama bobo abinci, tunda yafahimci shiitake zubamawa saiya d'auki cokali kawai yafaraci acikin filet d'in Rahma.
Abin yak'onama Safna rai, amma saita dake tafaracin abincin data zuba masan, Rahma kam koda bobo yasaka hannu a abincinta bata kulashiba, shikam mamaki take bashi Dan baita6a ganin fushintaba saiyau.
Bayan sun k'are cin abinci bobo yamik'e zaitafi d'aki, Safna tai saurin cewa ya Bob maganarmufa ta d'azu?, kosai ka kaini makaranta gobe?.
Juyowa yayi yana kallonta kamar zaiyi magana saikuma yafasa yajuya yatafi.
Rahma tayi saurin share hawayen dasuka cika mata ido, ita tama kasa fahimtar inda maganganun Safna suka dosa, kuma takasa fassara yanayin fuskar bobonta bare tagane mike faruwa?.
Hakadai takama hannun Nawal suka koma falo, kallo takunna musu sukeyi dukda ita hankalinta baya a wajen, hotunan mutane kawai take kallo, amma bata fahimtar komai.
Safna kam tana d'aki tanata zuba tsallen murna Dan dad'i aikobabu komai tasaka rud'ani atsakaninsu, gashi kuma yau bobo yaci abinci da maganin data zuba, tadaka wani tsalle tareda fad'in saini Safna ikon ALLAH, k'adangaruwar baking tulu nake, akasheni akar tulu, abarni na 6ata ruwan, takuma tuntsurewa da dariya.
Na ce, "hummm safna kenan ba girin girin badai tayi mai."
Bobo madai yana d'akinsa, sai safa da marwa yakeyi, yamarasa tunanin dazaiyi akan Safna da kaidinta, ganin Kansa ya tushe yad'auki waya yakira Ammar.
Cikin zolaya Ammar yad'aga wayar, kaga barrister dodon 'yan iska, mijin Rahma baban Nawal ya yadai my guy?.
Numfashi Bobo ya sauke tareda fad'in Ammar ajiye wasa gefe inaso muyi maganane.
To inajinka Ammar yafad'a cikin gyara nutsuwarsa.
Ammar wata matsalace agidana nakeson kanemamin hanyar maganinta danni kaina gaba d'aya ya kulle.
Ammar ya ce, "kaida Rahma ne.
A'a no Rahma batayimin komaiba yayartace Safna.
Haba bobo tokai miya had'aka da safna kuma?, bayan kai yanzu mijin k'anwartane.
Hakane Ammar ni mijin k'anwartane, amma yarinyar tana Neman shigowa rayuwata, yakwashe kaf abinda Safna tamasa yafad'ama Ammar, yanzun zancennan danake maka nadawo daga masallaci na Tatar tana barbad'a magani a abincinmufa, amma bata ganniba, Rahma kuma suna d'aki itada Nawal suna sallah.
Ammar yaja wani gwauron numgashi, lallai yarinyarnan hatsabibiyace, to amma kunci abinci?, a tomizai hana, sammu yakanyi tasirine da izinin ALLAH, Dan haka zuba maganinta bazai hanani cin abinciba nikam.
Hakane Abdulmaleek, ammafa natayaka murna da aurenka bai kasance da yarinyarnan ba wlhy.
Aikodai nima haka naketa godema ALLAH akullum Ammar, Dan nasan da itace matar tawa nasan saita rabani da Nawal.
Wlhy kuwa zata iya. ni yanzu hanya d'aya nake ganin mafita kuma maganin yarinyarnan.
Da sauri bobo ya ce, " minene?.
Maganinta d'ayane Wanda zata gane lallai kamata nisa fintin kawau shine kayi k'ok'arin kusantar matarka, ka ajiye batun Barin Rahma sainan gaba, Dan wlhy Idan kayi sake sai shaid'aniyar yayarta d'in nan taci galabar rabaku nan gaba, Dan kuwa 6arakar ta hango har take iya tunkararka kasaki 'Yar uwarta ka aureta, inhar tabud'e ido taga Rahma daciki, tom dolene tasakama zuciyarta salama ko itace shigabar jaheelai ta duniya, kuma yakamatama ta tattara takoma gida tunda su Rahman sun sami sauk'i.
Duk abinda kafad'a gsky ne Ammar, saidaifa gsky Rahma yarinyace.
Ammar yay dariya to abokina yaza'ayi, yaran k'auye da'akemusu aure shekara 12/13 fa?.
Hummm kai asuma mazan yarane shiyyasa.
Wata dariyar shak'iyanci Ammar yasaki cikin dariya ya ce, "kaikuwa gaka k'ato ko?, so kabimusu yarinyarnan ahankali wlhy Dan nasanka sai a slow.
Kai d'an iska saida safe, dankasamu nafad'a maka sirrina shine zakamin wulak'anci.
Hhhhhhh haba angon Daren yau maida wuk'ar mana.
Murmushi bobo yayi tareda yanke wayar yana fad'in kai Ammar mafa d'an iskane wlhy.
Jiyayi zuciyarsa yayi wasai kamar anyaye masa damuwarsa, mik'ewa yayi yashiga bayi ya salla wanka tareda d'auro alwala, bayan fitowarsa yad'an shafa mai da turarur rukansa yazira doguwar Riga ya zauna yana jiran shigowar Rahma.
Jareda yad'auka yana karantawa, saidai lokaci lokaci yakan kalli agogo, tun yana saran shigowarta harya fara mamakin miya hanata zuwa Dan 11:47pm, yad'anyi tsaki tareda gyara kwanciya yamaida Kansa ga jaredar, sai yakasa cigaba da karantawa, wayarsa yajawo yakirata amma bata shigaba yakumayin tsaki, afili yace mi yarinyarnan take nufi danine?.
Ganin wankin hula zai kaishi dare yasakashi mik'ewa yafito, fitilir falo yakunna Dan har ankashe alamar sunma kwanta kenan, le6ensa yacije yanufi d'akin Rahman.
Nanma fitilar akashe take saida ya kunna, yakai dubansa ga gadon Safna da Nawal ne kawai kwance suke barci, ad'an kid'ime yafara baza idanu, can yahango Rahma zaune akan sallaya tana karatun alkur'ani mai girma, ajiyar zuciya yasauke ahankali.
Itakam Rahma tun shigowarsa tana jinsa amma ko d'agowa ta kalleshi batayiba.
Ahankali yataka har inda take, wani d'an tsugunnon gayu yayi agabanta, ido tad'ago ta kalleshi, kallo d'aya tayi masa ta kauda kai, wani d'an murmushi yayi mai had'eda ta6e Baki, yay wani k'asa da murya yana mata kallon nan nasa na k'asan ido, Sayyada yau baza'a bani shayibane?, konayi laifine?.
Idanunta dake cike tabda hawaye tad'ago suka had'a ido, tai saurin juya k'wayar idonta Wanda yabama Hawayen damar zubowa, alkur'anin ta ajiye tamik'e batareda ta tanka masaba tafice.
Shima mik'ewa yayi yana murmushi azuciyarsa ya ce, "yammata kwantar da hankalinkima yanzun bada dad'ewaba zakiyi kukan mai dalili.
Ficewa yayi yakoma d'akinsa.
Itakam tana kichin, bayan tadafa masa shayi tad'ora atire tareda yanka lemon tsami kamar yanda tasaba, d'auka tayi tanufi d'akinsa.
Yana zaune abakin gado yajingina da fuskar gadon yana latsa waya tashigo, idanunsa yad'ago yana kallonta, itakam ko Inda yake bata kallaba taje saman dirowar gefen gado ta ajiye tiren shayin, batareda ta tanka masaba takama hanyar juyowa, da sauri bobo yarik'e hannunta, cak tatsaya amma bata juyoba, yawani narke murya can k'asan mak'oshi, miyake damunki?.
Hawayene suka k'ara zubo mata akumatu, dama Rahma akwai arhar kuka, ganin bazata amsashiba yajawota tafad'o jikinsa, mutsu mutsun kwacewa tafara amma yay mata nagartaccen rik'o, hannunsa yasaka yakama ha6arta yarike yanamai fuskanto da fuskarta gareshi my cute kishi ko?.
Da sauri tad'ago idonta dayay ja tana kallonsa, ya akayi yagane asirin zuciyarta, ita kanta tana mamakin yanda ta nuna kishinsa ayau, wani 6angare na zuciyarta ya ce, "kin kamu da sonsane, da sauri ta ta6e baki.
Bobo yamatso da fuskarsa gabda tata tamkar zaimata kiss murya k'asa k'asa ya ce, " miyasa kike ta6e Baki?, kobaki yardaba kina kishina?.
K'ok'arin mik'ewa tafarayi tana fad'in shayinkafa zai huce.
K'ara k'ank'ameta yayi, cikin salon maganarsa ya ce, "aii shayi yagama aikinsa daga yau, saidai idan nasha da marmari amma badan damuwaba, daga yau kece zaki zama shayina.
Da sauri ta kalleshi saikuma ta kauda kai yayinda suka had'a ido, bata fahimci Inda zancen nasa yadosaba amma taji aranta akwai shak'iyanci aciki.
Yunk'urawa tasakeyi zata tashi, ta ce, " tonaji kabarni naje nacigaba da karatuna.
Ayya aynanma karatu zamuyi kuma jira kigani, tashi kiyi alwala kizo.
Dukda gabanta yafad'i amma saita dake Dan batason rud'a kanta da zargin abinda ba hakaba.
Inada alwatafa. Tayi maganar kamar zata fasa kuka.
OK tom tashi muyi sallah, bata musa masaba tamik'e suka hau sallaya, shine yajasu jam'i, raka'a hud'u sukayi kafin daga bisani yafara kwararo addu'oi Wanda ita bama tata6a zaton ya iyaba, daganan yadafa kanta yay addu'a da *Annabi tsira da amincin ALLAH su tabbata agareshi* ya koyar damu, yayi musu addu'oi sosai sannan suka shafa tareda mik'ewa.
Da sauri Rahma takama hanyar ficewa, bobo yay azamar shan gabanta, idanu tad'ago tana kallonsa, yad'aure fuska tamau tamkar bashine yagama lalla6ataba yanzun, k miye haka wai?, yaushe raini yashiga tsakaninmune?.
Yanda yacanja mata lokaci d'aya saitaji tsoransa yak'ara kamata, murya na rawa ta ce, "kayi hak'uri zanje nacanja kayane.
Hannunta yakama zuwa gado, karki damu bama saikin canjaba yay maganar yana k'ok'arin zame dogon hijjabin dake jikinta.
Idanu kawai Rahma ta runtse, zuciyarta sai faman bugawa takeyi da k'arfi............
Hummm.....😎Rahma yau kinga takanki👻.
*_luv you oll_*
*_(((S))).....2017_*
[11/12, 2:57 PM] mrs bilkisu: 👩🏻💻typing........
❣ *_ABDUL-MALEEK_*❣
_•{🅱🅾🅱🅾}•_
*_NA_*
_*Bilyn Abdul*_
_sadaukarwa_
*_Abba Gana_*
*_Batul mamman_*
*_Billy giro_*
5⃣6⃣
Daga ita sai zani d'aurin k'irji, ya ajiye hijjabin gefe shima yazauna yana kallonta, yayinda itakuma taduk'ar dakai k'asa idanunta cike da kwalla.
Tashi yayi daga bakin gadon, yajawo d'an k'aramin tebir na gilas dake gaban kujera ya zauna a agabanta suna fuskantar juna, saida yay mata kallon tsaf sannan yasaka hannu yad'ago ha6arta.
Idanunta talumshe, kwallan datake mak'alewa suka zubo, yad'an lumshe ido yabud'e akanta, murya k'asa k'asa ya ce, "wai miye damuwarkine?, shin kukan nan bazai k'arebane?, kokuwa ban cancanci sanin matsalarkiba?.
Girgiza kai tayi alamar a'a.
Ya ce, " nafison kimin maganar da bakinki.
K'ara matso hawayen tayi muryarta na rawa ta ce, "babu komaifa.
Ya ce, " amma kike yin kuka?, kinga fad'amin kinji my cute.
Yanda yaymata maganar cikin muryar lallashi saitaji sanyi aranta, wannan yabata kwarin gyuywar kallonsa, ta d'an kauda idonta sannan ta ce, "Dan ALLAH ya Abdulmaleek miye had'inka da aunty Safna?.
Tabashi dariya kwarai da gsk, amma saiya dake, yad'an tsura mata ido nawani lokaci kamar mai nazarinta, batareda yabata amsartaba yamik'e tsaye, doguwar rigarsa yacire yarage dagashi sai gajeren wando.
Itadai satar kallonsa takeyi da mamaki, tamasa tambaya amma yashareta yacigaba da harkar gabansa.
Fita taga yayi, bayan kamar minti 3 saigashi d'aukeda fresh milk da cup, sake zama yayi akan tebir d'in, yatsiyaya fresh milk a cup, itadai tana kallonsane kawai, saida yacika kofin taf sannan yamik'a mata, girgiza kanta tayi ahankali ta ce, " nak'oshifa.
Yanzu d'inma baitanka taba, saidai yakai kofin saitin bakinta, yanda yatsareta da mayun idanunsa wad'anda ayanzu suka sake canja kala yasata dole tabud'e baki tasha, haka yayta bata tanasha badan tanasoba, data janye bakinta saiya had'e fuska dole nacigaba da kar6a, ahaka dai harta shanye tas, shima zubawa yayi yana sha yana kallonta, itadai kanta na k'asa tana wasa da zoben hannunta.
Bayan yagama yamik'e ya ajiye cup da kwalin fresh milk adurowar gefen gadon, bayi yashiga yayi brush, ya umarceta itama dataje tayi, sanin datayi akwai sababbin brush a bayinsa dayakan ajiye yasa batayi musuba yashiga, aiko tararwa tayi ya ajiye mata sabo a Leda,