Showing 105001 words to 108000 words out of 111128 words
ko ita kanta tasan taji gyara Dan fatarta tayi wani k'yau da laushi, kuma zammm takejin kanta.
Bobo nata fushi Dan yaso sukoma gidansu tuni, ammi ta ce, "saidai yakoma shikad'ai su Rahma dai ba yanzuba, wanan dalilinne yasashi fita harkar Rahma gaba d'aya, shi adole fushi yakeyi da'ita, daga gaisuwa babu abinda yake had'asu, saikuma yad'auki yaransa kokuma yazauna ad'akin yana musu wasa, ada Rahma tashiga damuwa da sauyin nasa, amma da Ammi ta zaunar da ita tana lallashinta da nuna mata itama tafita harkarsa da Kansa zai dawo gareta, daganan sai Rahma tasami nutsuwa, wani lokacinma har dariya yake bata idan yana shan k'amshi, musamman idan takamashi yana satar yimata kallonnan nasa k'asa-k'asa, dasun had'a ido saiya gimtse fuska, kokuma yakwashi yaran yabar mata d'akin.
Ita kanta ammi bobo yana bata dariya, data kasa daurewa har Appa tabama labari, shima yaci dariya ya ce, " babana na kaina.
Bayan kammala arba'in suka fara zaga dangi.
Gidansu tafara zuwa, bak'aramin farinciki Abba da ummi sukayiba daganin jikokinsu, anan tawuni sai dare oga yazo yad'aukesu abisa matsawar Appa, Dan ya ce, "dolene yakaita ko ina takeso.
Haka suke tafiya amotar babu mai tanka wani.
Washe gari kuma gidan ya ishaq sukaje suka yini saidare yaje yad'akkosu, daganan kullum akwai gidan dazasuje su yini, haka sukaita zaga dangi, sunje gidan ya sulaiman, gidan ya Hamza, gidan ya Shaheed, gidan ya muneer, gidan Ammar, gidan aunty yahanasu, gidansu marigayiya Ni'ima, gidan khairiya da khursiyya, gidan Ameera, gidan Basma, kai babu Inda basu zagaba, gidan Safna ne k'arshen zuwa, tabar gidan Safna k'arshene dantasamu suje weekend yakaita tunda safe tawuni sosai..
Aiko ayau Asabar suka Isa gidan, cikin farinciki Safna ta tarbesu, har mamaki Rahma tayi, sai nan-nan takeyi dasu, tamkar tagoyasu Rahma, cikin mutunci suka gaisa da bobo, Wanda shima canjawar safnar kebashi mamaki.
Itakam zuwa yanzun zuciyarta fes, kallon bobo takeyi amatsayin d'an uwa kuma mijin k'anwarta, bayan haihuwar Rahma tak'ara dukfa da addu'a, takuma k'ara Neman gafarar iyayenta, suka kuma k'ara jaddada mata sun yafe mata suna kuma k'ara tayata da addu'a ALLAH ya daidaita lamuranta.
Wad'annan abubuwanne suka taru suka k'ara taka rawar gani wajen inganta farincikita dakuma jin son bobo yafita fit azuciyarta, saidai tana ganin girmansa damasa soyayya irinta 'yan uwantaka tamkar su ya munner, soyayya mai tsafta kuma ingantacciya suke gudanarwa itada mijinta, wani bala'in sonsa takeji ayanzu haka, shima soyayya yake nuna mata irinta 'yangatan mata kamilallu, dankoba komai yana alfahari da safna, cif tazo MASA a cikakkiyar budurwa shiyya 6areta aleda, dama baita6a kallonta dawata illaba saita tsiwa.
Su Kansu Rahma da bobo yau sunsha kallo, danba kunya safna da ya Kamal suke narka soyayya agabansu.
Rahma taji dad'i sosai dataga 'Yar uwarta tak'ara kwantar da hankalinta, aiko yau sosai takejanta ajikinta, su shareefa kam ai tamkar ta lashesu Dan so da k'auna, wuni sukayi ahannunta, tad'auki wanan ta ajiye ta d'auki wannan, haka suka wuni cikin farinciki da k'ara k'aunar juna.
Su bobo na fita sallah Safna taja hannun Rahma suka shige k'uryar d'aki, magunguna tad'akko tabama Rahma, tanata mata bayanin yanda zatayi amfani dasu, Rahma tarufe fuska yana fad'in kai aunty Safna ALLAH kina bani kunya.
Dukan wasa Safna tayima Rahma, kai auta gulmarki tayi yawa wlhy, idan kina tareda ya Abdulmaleek aii idonki rufewa yakeyi amma saikina gabanmu kice wata kunyar gulma, dama sabodake na had'asu, jiyannan nakecema my heart yakaini gidan Ammi nakuma gano yarana, ya ce, "nabari sai ranar Sunday, to ashema kuma hanya, 'Yar uwa k'ara gyara kanki ya Abdulmaleek yaji zammm danya k'ara rik'e manake d'amm, safna tak'are maganar da d'agama Rahma gira, dariya suka saka harda tafawa tamkar wasu k'awaye, Rahma ta ce, " ALLAH yabarminke auntyna, suka kuma kashewa da dariya.
😂wayyo masu karatu dad'i tamkar yakasheni, nasan kumafa yau hakan take agareku musamman masoyan Safna, luv you so much safnarmu😘👍🏻.
Sosai tahad'a 'Yar k'anwar tata Dan acewarta batada kamarta aduk fad'in duniya, sukad'aine mata agidansu sukashe su rufe abinsu, hira sukayi sosai ad'akin harsu bobo suka dawo basu saniba.
Abubuwa sosai safna tahad'ama Rahma harda sabulai na gyaran fata, Rahma sai dad'i takeji da k'ara k'aunar 'Yar uwarta, yanzukam sunzama tamkar yanda take buri tun farko, saidai fatan ALLAH yak'ara had'a Kansu waje d'aya.
Sai bayan isha'i suka fito zasu tafi, shareef da shareefa suna hannun Safna da ya Kamal, Rahma tashiga Kusada bobo ta zauna sanan Safna taziro mata shareef da ledar kayanta, my sweet lil gasu karfa ki tsaya Sanya Dan da zafi-zafi ake dukan k'arfe, abinda Baki ganeba to naji kira.
To my aunty godiya nake sosai ALLAH yabar zuminci saikinzo d'in.
Bobo dake kallonsu sun burgeshi sosai, cikin zolaya ya ce, "auntynmu mi muka samune haka?.
Dariya Safna tayi ta ce, " k'anina abin sirrine aii.
Lalala yanzunan auntyna dake za'a had'eminkai?, Kamal zoka ganemin nan.
Dariya ya Kamal yayi idonsa akan safna, tad'aga MASA gira, shikuma yasakar mata lallausan murmushi, bobo ya ce, "Kamal sai magana akeyi agabana adunk'ule bana gane komaifa.
Cikin dariya ya Kamal ya ce, " kaikuma ga rashin hak'uri, aisaika kwantar da kai kaji Inda bakin zaren yake, kokuwa my Angel?.
A to my heart gaya MASA dai.
Rahma dai dariya take musu, bobo ya ce, "shikenan idan tayi wari aii maji, cikin dariya Rahma ta ce, " aibama zatayiba.
Dariya suka kwashe da ita su duka, safna takuma gwargwad'ama Rahma magana akunne suka kuma tafawa suna dariya.
Bobo ya ce, "Kamal bara kaga nagudu da my Nusfulhayat d'ina kafin matarka tak'ara zugemin ita.
Nanma dariya suka kumayi sosai, daganan sukayi sallama bobo yana mota suka tafi, zuciyar bobo k'al da farincikin Safna tasaki jikinta yanzun komai ya wuce, gashi sun had'e Kansu itada 'Yar uwarta, dama fatansa kenan akullum.
A can kuwa su bobo na tafiya safna ta narke ajikin ya Kamal wai saidai ya d'auketa bazata iya tafiyaba, dariya yayi ya ce, " my Angel kemafa shagwa6a66iyace tafad'a a ji, d'aukar kayansa yayi tamkar jaririya suka shige gidan suna dariya, asaman doguwar kujera ya sauketa suna cigaba da dariyarsu, cikinta yashafa yana fad'in Nima yaushe zaki bani nawa babyn my Noor?.
Ido d'aya safna takshe masa ta ce, "ayanzu hakama ina zaton kasamu, Dan kwanakin preod d'ina sun wuce kobaka lissafi?.
Cikin farinci ya k'ank'ameta yana fad'in kumafa hakane my Angel, soyayya mai tsafta kuma nagartacciya yashiga Nuna mata, safna ma tana bashi gudummawa saida suka soyu sanan suka tashi adarennan sukaje pharmacy, tsinken gwajin ciki suka siyo, aiko suna gwadawa sukaga tanada ciki, wayyo zokaga murna da farinciki awannan gidan, tun adaren suka fara bazama dangi.
Safna Rahma tafara kira wadda harsunje gidan tuni, tagama shirin barci kenan kiran safna yashigo, ta guntsa mata abin farincikin daya samesu bayan tafiyarsu, tsalle Rahma takeyi harta bama safna dariya, safna ta CE, " kai lil ya bobo nashan fama, har yanzu ana nan ana gwada halin k'uruciya.
Kai aunty nid'in?, Rahma tafad'a cikefa shagwa6a.
Eh mana.
Bubbuga k'afafu Rahma tafarayi ak'asa ita adole ba haka bane, bobo daya shigo yanzu yakwantar dasu Shareef yatsaya yana kallonta, suna had'a ido yakauda kai yana ta6e baki, shi adole ba kallonta yakeyiba, Ra6awa yayi tagefenta ya fice, Rahma tabishi da kallo yana turo baki gaba.
Bayan fitarsa Rahma ta ce, "wlhy Anty d'azun namanta muyi wata magana, tamkar zatayi kuka take maganar.
To inajinki auta miya farune?.
Zayyane mata abinda ke faruwa tsakaninta da bobo tayi.
Dariya safna tayi ta ce, " kema ki shareshi, kedai kita amfani da magungunan nan, na tabbata duk randa kuka koma gidanku yakashe amarci insha ALLAHU saiya dawo dakansa yana Neman shiri da lalla6arki, kuma zakice Nina fad'a miki.
To shikenan aunty na ngd ALLAH yabar zuminci ya saukeki lfy kema, ki Haifa mana yaranmu 'yan uku.
Kai auta rufamin asiri 'yan ukun lfy.
Dariya sukayi gaba d'aya, Rahma ta ce, "I luv you so much my sweet auntyna.
Luv you more my lil sisina, ALLAH yak'ara kauda shed'an atsakaninmu, Yakuma k'ara had'akanmu waje d'aya muzama taintsiya mad'aurinki d'aya, asuba tagari my heart yana jirana nabashi d'umin jikina, gwauruwa arungumi fillo lfy... d'if ta Yanke wayar, tabar Rahma da dariya.
Kai Anty safna ALLAH ya shiryaki, Nima aii nakusa tashi daga Layin gwagwaren, ALLAH INA k'ara godiya Daka daidaita mana komai cikin sauk'i, ALLAH ka k'ara ninka salatinka ga annabi Muhammad tsira da aminka su k'ara tabbata agareshi.
Sumbatar yaranta tayi ta tamusu addu'a dukda papansu yamusu, gado tahaye tamusu addu'a itada Nawal tareda rungume Nawal dake barci, itama ta sumbaci kumatunta, har yanzu zuciyarta yana k'ara k'aunarta tanajinta tamkar su Shareefa, bak'aramin tausayi yarinyar Take bataba saboda rashin uwa, amma tayi alkawarin zamema Nawal uwa har abada, bata fatan ranar dazatazo ta banbanta soyayyarta dasu shareeff.
*_BAYAN KWANA UKU_*
bayan kwana uku da zuwa gidan aunty Safna Ammi tashirya Rahma tsaf da shirin maidata d'akin mijinta, nasiha sosai Ammi da Appa sukai musu tareda fatan alkairi agaresu, sosai Rahma tasha kuka Dan ko babu komai tayi sabo da zama gidan sosai ayanzu, amma babu yanda ta iya.
Zuwa dare bobo yakwashesu sai gidan, ko a mota kuka Rahma taitayi, bobo yana kallonta amma baice da ita k'alaba.
Koda suka Isa gidan saitaga komai tsaf, angyara gidan sosai, wanka kawai tayima yaran tamusu shirin barci, Nawal na kwance bisa gado tanatama su shareef wasa, sosai yarinyar take k'aunar yaran, komai tasamu ta ce, "na Shareef da Shareefa ne.
Rahma dake tsaye agaban madubi tana shirin barci ta ce, " babyna bazakiyi barciba?, gobefa idan ALLAH ya kaimu akwai school.
Momy nidai bazanjeba zan zauna gidan taredasu Shareff.
A'a babyna to idan bakison zuwa makaranta suma idan sunyi girma aii bazasuje ba ko, ki kwanta kiyi barci abinki da antasoku bakina tareda suba.
To momy bara suyi barci sannan nayi.
Dariya kawai Rahma tayi batace komaiba.
Bobo dake tsaye abakin k'ofa yanajin hirarsu ya ida shigowa cikin d'akin, ta madubi Suka had'a ido da Rahma, batace komaiba haka shima bai tankaba yahaye gadon wajen yaransa.
Lalla6a kayansa yaytayi harsukai barci suduka ukun sanan yagyarama Nawal kwanciya, yamata addu'oin barci ya shafa mata, suma su Shareefa ya kwashesu zuwa d'akinsa, itadai Rahma da kallo kawai tabishi, ad'an gadonsu yasakasu yamusu addu'oi suma, Rahma na zaune abakin gado tana addu'oin barci danta k'udiri aniyar bazata bishi d'akinsaba.
Batayi auneba taji anyi sama da ita, ciccila k'afafunta takeyi tana fad'in wayyo dadyn Nawal Dan ALLAH kabarni ALLAH barci nakeji.
Bai sauraretaba yadireta agadonsa, ganin zata addabi kunnensa da surutu ya had'e bakinsu waje guda, zallar soyayya mai tsafta yashiga aika mata, hummm lallai bobo uayi missing d'in Nusfulhayat d'insa, itamafa mutuniyar taku muk'us kakeji, tuni tafara maida murtani........🤰🏻😜.
Hummmm yaukam ansha fama Dan sabon ango da amarya suka koma, ranar kam Rahma ta murzu ta shaida bobo yayi kewarta sosai Dan bai d'aga mata k'afaba har gabannin asuba ana Abu d'aya.
Washe garima dak'yar ta lala6ashi tatashi tahad'a musu breakfast.
Wankama tare sukayi, nanma saida suka kashe juna da soyaya sanan akayi wankan suka firo, ta shiryashi tsaf cikin shirin office, sanan ta tata Nawal itama tamata wankan shikuma yataimaka mata da shiryata, tayima su Shareefa suma duk shine yashiryasu.
Gaba d'aya suka d'unguma zuwa dinning shi yana d'aukeda shareef nawal tana d'aukeda shareefa, Rahma kuma tashiryama kowa breakfast agabansa sanan ta kar6i sharifa ahannun Nawal danta samu nutsuwar cin abinci.
Bayan gamawarsu yad'auki Nawal suka tafi, aka bar Rahma itadasu Shareefa kawai.....
Haka rayuwa taciga da tafiya musu wataran Zuma wataran mad'aci, yaransu sunata k'ara samun girma da kulawar iyayensu.
Soyayya kam Rahma da bobo ba'a cewa komai sai sambarka.
To ALLAH yacida 'yan bayan haka irinsu o e😂.......bandai fad'i sunaba bare ace nace😜🤸🏻♀.
*_"BAYAN WASU SHEKARU........_*
*_Luv you oll_*.
*_(((S)))........2017_*
[11/12, 3:00 PM] mrs bilkisu: 👩🏻💻typing........
❣ *_ABDUL-MALEEK_*❣
_•🅱🅾🅱🅾•_
*_NA_*
_*Bilyn Abdul*_
_sadaukarwa_
*_Abba Gana_*
*_Batul mamman_*
*_Billy giro_*
7⃣3⃣
*_BAYAN WASU SHEKARU...._*
Abubuwa sun faru da dama, ciki harda haihuwar Safna, tasamu d'iyarta mace wadda taci suna khadeeja, bayan ita takuma haihuwar Abubakar sadiq, yanzu haka tana goyon mace Asma'u.
Soyayaya itada ya Kamal d'inta ko sai abinda yay gaba, komai yawuce tamkarma bai faruba saidai tashin zance.
Su khairiyya da khursiyyama duk sun haihu, yanzu suma yaransu uku uku.
Anty Ameera ma yaranta biyu.
Hakama Basma tanada biyu.
Anyi Auren zeenat da baseera suma harda tsarabar ciki.
Itama ihsan k'anwar ya kamar ansha bikinta da musaddiq k'anin marigayiyya aunty Ni'ima, Wanda sun had'une ranar bikinsu Safna suka shirya Kansu.
*_bara nalek'a muku gidan bobo naga wace waina ake toyawa kuma._*🤓.
Tundaga harabar gidan naked'anjin hayaniyar yara, nak'arasa falon saina tadda Rahma kwance saman doguwar kujera idonta akan TV, gefe kuma Nawal ce zaune itada Shareeff da Shareefa tana koya musu homework, saikuma yara biyu dake fad'a duk maza wad'anda ak'alla zasukai shekara hud'u da kuma 5½, d'an shekara hud'unne Kebin d'an shekara Biyar suna zagaye falo yana fad'in nisaika bani abuna, nisaika bani abuna.
Nawal datazama 'yammata Dan ayanzu tana ss2 a Secondary ta ce, "Farhan wai bazaka bashiba, ALLAH natashi saikayi kuka, kabashi kazo kayi homewook d'inka.
Wanda aka kira Farhan ya ce, " yo Anty Nawal nawanefa shi kulum kulum saiyayta yima mutane rigimar banza sai anbashi Abu, yaje d'akin papa yad'akko NASA mana.....
Kafin Nawal tace wani Abu bobo yafito daga d'akinsa sanye cikin jallabiya fara da alama ma alwala yayo......ya ce, "a'a Farhan mike faruwane haka?, momy kina zaune kina kallonsu sunata faman fad'a idan wani yazame yafad'i yaji ciwo fa?.
Yatsina fuska Rahma tayi ta tashi zaune tana fad'in wlhy bazan iyaba Nurulk'albi, ni takaina nakeyi, idan nabiyema Farhan da Shureim gidanan wlhy sainamusu mugun duka, Dan ALLAH gobe idan ALLAH yakaimu ka kwashesu ka kaima Ammi weekend kokuma anty Safna nikam nahuta koda na kwana biyune.
Dariya tabashi da tausayi, tunda tasamu cikinnan yake bata wahala, hargashi yashiga wata na hud'u amma bata hutaba, yay saurin rik'o Shureim dake bin Farhan suna zagayashi, d'aukarsa yayi yana fad'in haba Abbana miyasa kakeda rigima?, yanzu kai ina naka jirgin yake?.
Papa nawafa baya tashi sama yanzun....... Papa wlhy k'arya yakeyi, d'akinkafa yakai ya 6oye jiya dadaddare ko Anty Nawal?.
Shareefa ce mai maganar tana Harar Shureim daketa turo baki gaba.
Kallonsa bobo yayi ya ce, " Abbana wai da gsk aunty Shareefa takeyi?.
Girgiza kai Shureim yayi alamar a'a ba gsky bane.
Farhan ya ce, "ALLAH papa da gsk Anty Shareefa takeyi d'akinka yakai ya ajiye.
Dire Shureim bobo yayi, Yakama hannun Shureim da Farhan kunga kuje kuyi alwala mutafi masallaci lokacin sallar la'asar yayi, Ya Shareeff atashi idan mundawo acigaba da homework d'in tunda babu islamiyya yau.
Mik'ewa Shareeff yayi, araina na ce, " like father like son, gaba d'aya yaron kamarsa d'aya da bobo sosai har d'an Karen muskilancin na bobone, idan baigadamaba sai agama wanan shaftar bazai sakama kowa bakiba, haka yake bashida hayaniya ko kad'an.
Rahma tabishi dakallo tana girgiza kai, miskili kafi mahaukaci ban haushi, wai yaronnan duk abinnan da akeyi bamu isheshi kalloba?.
Dariya bobo yayi ya ce, "k'yawun d'a.....
Rahma ta ce, " yagaji ubansa.
A to kingani, bashida lokacin yahaniyarku ne, baby kuma kutashi kuyi sallah.
To papa Nawal da Shareefa suka fad'a suna mik'ewa.
Nawal ta ce, "momy haryanzu bakijin yunwar?.
Wlhy babyna inajin yunwar amma bana sha'awar cin komai.
Langa6e kai Nawal tayi kamar zatayi kuka momy kidaina zama da yunwa dukfa kin rame.
Daga bobo har Rahma dariya sukayi, bobo ya ce, " to momy ba'aso ki ramefa kullum anfison ganinki Orobo.
Nanma dariya sukayi, Nawal ta ce, "momy bara nayi Sallah Nazo nadafa miki wani abun, to baby jekiyi.
Nawal nabarin wajen bobo yadasama Rahma mayun idanun nan nasa cikeda so da k'auna, my cute Kodai wajen ya Sulaiman zamu komane?, yakuma duba minke?.
Murmushin k'arfin hali Rahma tamasa, a'a Zumana bama saimun komaba, yanzu babu Inda kemin ciwo saidai kasala da d'acin baki.
To shikenan my Nusfulhayat, amma inaga wannan karon uku zaki Haifa mana shiyyasa cikinnan ke baki wahala da yawa, dama gashi kin huta dayawa ga Shureim da shekara hud'u aduniya.
Wayyo zumana dainamin fatannan, idanma ALLAH yasa na haifi mace ai hakama sun ishemu maza uku mata uku Alhmdllh.
Ido yad'an zaro tab my cute saura shidda kenan 12 nakesofa, kuma duk daga gareki.........
Kafin tabashi amsa su Shareeff suka fito kowa yayi alwala, bobo ya kalli Shareeff babana koma ka canja wanana wandon, koma ka saka dogon wando dai kokuma kasaka jallabiya.
Papa jallabiyoyina duk sunyi dattine.
Rahma ta ce, " ba saida nace jiya kad'akko Ashiru ya wankeba tunda zayyi wankin papanku.
Momy ALLAH nibanjiba.
Yaza'ayi kajini tunda kamaida kanka dud'um dunkum, mutum sai muskilanci.......
Bobo yakatsesu