Showing 60001 words to 63000 words out of 111128 words
matuk'ar rud'ani danadamar bijirema iyayena, lallai ranar zuciyata yayi tamkar zata fashe......
Bobo yakatseta da fad'in no wonder shiyyasa kikamana pretending wai kina jin juwa koma mine?, yafad'a yana yatsine fuska tamkar yaga wani tutu.
Safna tasakko tatsugunna agabansa tana hawaye, Dan ALLAH my boboo kataimakeni ka aureni?.
Wata uwar harara bobo yajefeta dashi, cikin kaushin murya ya ce, "bakida hankaline?, kokin manta nid'in *_MIJIN K'ANWARKI NE!!?._*
Itama cikin d'aga murya ta ce, " inacikin hankalina kuma INA kan sani, Maleek nasan bakason Rahma, itama batasonka, Niko ina Sonka.......
Da Sauri yakatseta dafadin ubanwaye yagaya miki?.
Tazaro manyan idanunta, ta ce, "zamankune yafad'amin, Dan wlhy ko rantsuwa nayi bazanyi kaffaraba baku ta6a had'a shimfid'a da Rahma ba, wannan yana cikin dalilin zamanka anan gurin, idan kuma nayi k'arya karantse mini da ALLAH kata6a had'a shinfid'a da ita, nikuma indai kayi zan hak'ura dakai nabar mata.
Harara bobo yasakar mata, to ina ruwanki?.
Tayi wani murmushin mugunta, daruwana maleek harda d'an tsaki, domin kuwa Sonka nakeyi, sokuma mai tsanani, Dan ALLAH kasaki Rahma kamaye gurbinta dani, wlhy namaka alk'awarin maka biyaya, zankuma cire maka duk wani kunci da damuwar dake tare da kai....
Cikin tsawa bobo ya ce, " Dallah malama yimin shiru, yay murmushin nan nasa na munguta sannan yasauke k'afarsa k'asa, Yakuma gyara rungumar fillonsa yana kallonta, ya ce, "yarinya bakida abinda zaki iya mayemin gurbin my cute dashi, dantafiki komai wlhy, k'yawun sura ilimin addini iya zama da mutane hankali nutsuwa k'yak'yk'yawan tunani uwa uba hankali, yoni nayi canjinki da Rahma aina fad'o wlhy nakuma ci baya arayuwata, kisa azuciyarki dama can ALLAH yarubuta Rahma CE matata bakeba, ubangiji yagwada kine kawai danyaga k'arfin imaninki, amma saikika Nuna masa kinfisa wayo, to wallhy kisani kullum godema ALLAH nake dakikace bazaki aureniba, mahalliccina maisona da nasara yabani Rahma amadadinki, zuciyarki tadaina shirya miki k'aryar zan iya rabuwa da Rahma, wlhy yaudararki kawai takeyi, nida Rahma mutu karaba takalmin kaza.
_Yay k'asa da murya tamkar mai rad'a, ya ce, "Rahma sai Abdulmaleek, Abdulmaleek kuma sai Rahma k'yak'yk'yawa mafi k'yawu acikin mata._
Yafigi filonsa da littafi yay cikin gida yana 'Yar dariyar mugunta.
Durkushewa Safna tayi awajen tana kuka, wlhy baka isaba saika saketa ka aureni kokak'i kokaso, danni kad'ai ALLAH ya halicceka shiyyasama yakashe matarka tafarko yabarminkai, k'arya kake kace Rahma CE k'yak'yk'yawa acikin mata, ko makaho yashafa yasan nafita k'yau, kuma kaima kasani, boboo wlhy saika rabu da rahma, kuma muzuba nidaku d'an halak kafasa, daga yau zamu saka k'afar wando d'aya daku, saina addabi rayuwarku wlhy, duk cikin kuka take sambatunnan, saida tayi mai isarta sannan tamik'e, wlhy *_Abdulmaleek_* saina mallakeka koda ta hanyar kashe Rahma ne.
π³munga banu, safna!!.
Tabd'ijan masu karatu akwaifa Marsala, safna kuwa tanada hankali?.
Muje zuwa danjin yazata kaya.
.*.*.*.*.*.*.*.*.*.*.*.*.
Haka bobo yakwana tunanin maganganun Safna da yadda zai 6ullo musu, tabbas yayi kuskure dayake barin Rahma tana kwana d'akinta tun zuwan Safna, d'akinsa yadace tana kwana aii, haka yayta juye juye da tunani har asubahi baiyi wani barcin kirkiba.
Itamadai Safna haka tafaru gareta, batayi barcinba kwana tayi tunani.
Sai bayan sunyi sallar asubane barci yakwashesu suduka biyun dayake weekend ne.
Rahma da Nawal ne kawai keta kaikawo agidan, suka gama had'a break fast suka gyara gidan tsaf.
*_10:6am_*
Bobo yatashi, yagama komai na al'adar rayuwarsa sannan yafito falo cikin dogon wandon jins blue da farar t-shirt mai gajeren hannu, sai zabga uban k'amshi yakeyi.
Rahma da Nawal suna zaune afalo tana ma Nawal kalba, da gudu Nawal taje ta rungumeshi tana fad'in my papa ina kwana.
Lfy lau baby yafad'a yana rik'e hannunta sukazo suka zauna.
Rahma ta gaisheshi ya amsa amma fuskarsa babu walwala.
Azuciyarta ta ce, "boss yaukuma muskilancin ne yamotsa?, afili kuma ta ce, "ga break.
Yad'an kalleta, atausashe ya ce, ''kawomin tea kawai.
Mik'ewa tayi tahad'o masa tea mai k'auri takawo masa, ya amsa yana binta da kallo, ahankali ya ce, "ngd, itama d'an kallonsa tayi takauda ido.
Yana shan shayi yana kallon film d'in dasuke kallo wani India film yakula Rahma tanason film d'in India komiyasa?.
Safna tafito itama, Rahma ta kalleta aunty harkin tashi?.
Saida tad'an ta6e baki sannan ta ce, " eh natashi.
Takalli Bobo dayayi tamkar baima san da shigowartaba kuma yanajinsu.
Ta ce, "ina kwana?.
K'ara d'aure fuska yayi sannan ya ce, " lfy."
Rahma bataji dad'in yanda ya amsama auntyn ta gaisuwaba amma yaza yayi.
Takalli Safna dake zaune tana kallon bobo ta gefen ido, aunty gafa break.
Uhum kawai safna tace mata.
Haka akaita zaman kurame afalon, saidai Nawal daketa surutunta, shi bobo yanayine saboda Safna, itakuma Rahma tanajin haushin yanda yake share 'Yar uwarta, itakuma safna suduka haushi suke bata.
Shima yalura da Rahman amma sai itama ya shareta.
Bayan takammala abincin Rana tajere a dinning tak'ara gyara gidan tsaf, dama Safna bata tayata, saidai idansu khursiyya sunzo, to sukuma yanzu sunk'ara zama busy Dan bikinsu baifi saura 12days ba.
Rahma tanufi d'aki zatayi wanka, Dan Nawal nawajen dadynta.
Yaukam ALLAH yabama safna sa'ar zuba magungunanta acikin abincin bobo, bayan tagama takoma falo ta Fiske abinta.
Mintuna kad'an Rahma tafito cikin doguwar rigar material ja, kayan yayi mata k'yau sai zabga k'amshi takeyi.
Ta kalli safna dake zaune afalo, aunty bara nakirasu muci abinci ko?, tawuce batareda jiran amsar Safna ba.
Baki safna ta ta6e tareda raka bayan Rahma da harara.
Yana kwance rigingine Nawal tana gefensa tana barci, idanunsa na kallon p,o,p d'in d'akin da alama yana duniyar tunanine.
Rahma tashiga d'akin da sallama, shi baima jitaba sai k'arar rufe k'ofar yaji, yad'ago kai yana kallonta, tamasa k'yau kwarai da gsk, idanunta suna k'ara narkar dashi akanta......
Takatse masa tunani dafad'in dadyn Nawal gafa abinci yana jiranka.
Bai tankaba amma yatsura mata ido tamkar zai cinyeta.
Tasake maimaita masa sannan yay ajiyar zuciya, dama inason ganinki yafad'a yana yunk'urin tashi, saida yazauna sosai sannan yanuna mata bakin gadon alamar ta zauna.
Tad'an zauna nesa dashi kamar mai tsoron wani Abu.
*_RAHAMA!!._*
taji sunanta har cikin kwakwalwarta, Dan ya iya fad'ar sunan.
Yakuma fad'in _Rahama!._
Itama akasalance ta ce, "na'am.
Yagyara zamansa sosai yana fuskantarta, tsareta yayi da mayun idanun nan nasa ya ce, "inaso daga yau kidawo kwana d'akin nan.
Cikin sauri tad'ago takalleshi, hanjin cikinta ma saida suka yamutsa danjin furucinsa.
Fuskarsa babu alamar wasa Dan haka tamaida kanta k'asa, muryarta na rawa ta ce, "saboda mi zandawo kwana d'akin nan?.
Ya ce, " saboda ni *mijinki* ne, umarni nake baki ba shawara ba, kuma daga yau nakeson ki fara.
Bata iya cewa komaiba Dan yau yakoma mata ainahin *_Abdulmaleek_* data fara gani ranar aurensu.
Shima baisake cewa komai yamik'e yashiga bathroom.
Tana nan zaune tamkar gunki harya fito daga bayin yacanja kayansa zuwa shadda milk colour d'inkin boda yayi k'yau masha ALLAH.
yad'auki Braun d'in takalmi yasaka agogoma haka, yafesa turarurrukansa tareda kwasar wayoyinsa da key d'in mota, saina dawo yay maganar yana k'ok'arin fita, itakuma tabisa da kallo tamkar sokuwa, ganin zai fice daga d'akin ta ce, "abincinfa?.
Tsayawa yayi amma bai juyoba ya ce, nak'oshi yay gaba abinsa.
Safna tana zaune afalo yafito, tamik'e da sauri tasha gabansa..............
Kuyi hak'uri dajina shiru, munyi sunan babyne, sunanta *_ummu habeeba_* (Iman).
*_luv you oll_*
*_(((S))).....2017_*
[11/12, 2:57 PM] mrs bilkisu: π©π»βπ»typing........
β£ *_ABDUL-MALEEK_*β£
_β’{π
±π
Ύπ
±π
Ύ}β’_
*_NA_*
_*Bilyn Abdul*_
_sadaukarwa_
*_Abba Gana_*
*_Batul mamman_*
*_Billy giro_*
*_Happy independence day, God bless you and God bless Nigeria. π³π¬π³π¬π³π¬π³π¬π³π¬π³π¬π³π¬π³π¬π³π¬π³π¬π³π¬π³π¬π³π¬π³π¬π³π¬π³π¬π³π¬π³π¬ We love Nigeria._*
5β£4β£
Wani kallon sama da k'asa yamata ya ce, "bani hanya.
Ta ta6e bakinta tareda fad'in aidama zan baka, amma inaso na tunatar dakai maganar jiya.
Ya watsa mata harara amma baice komaiba.
Murmushin ko a jikina safna tayi, ta ce, "Nasan bakason Rahma, Dan dakana sonta bazaka fice batareda kaci abincin taba.
Tsaki yayi cikin nuna razanarwa da kaushi ya ce, "dallah bani hanya kokuma wlhy yanzunnan namiki abinda har jikokin jikokinki saisun samu labari, banza jahila kawai.
Ganin gaba d'aya kamaninsa Sun canja tamkar zai daketa yasa tabashi hanya tana murgud'a baki da yin k'unk'uni.
Ficewa yayi yana Jan tsak'i, adaidai lokacin Rahma tafito, amma bataga abinda yafaruba.
Itakam Safna bak'incikine yarufeta da fargaba, kardai ace mutumin nan yak'icin abincin nan, lalai daya cuceta.
Rahma takatse mata tunani, auty Safna lfy kuwa?.
Safna taja numfashi tana wani kicin kicin da fuska, lfy lau mikika gani?.
Rahma ta ce, "a'a nagadai kamar bak'ya cikin nutsuwarkine?.
Cikin masifa safna ta ce, " to k'alau nake, tatashi tabar wajen.
Rahma tagirgiza kai, Dan indai dasabo tasaba da halin yayar tata.
%%%%%%%%%%%%
Sai dare bobo yadawo gidan, Nawal taje dagudunta ta tarosa.
Rahma da Safna suka masa sannu suma, ya amsa fuska ad'aure, d'akinsa yawuce itama Nawal tabisa.
Itama Rahma tamik'e tad'auki ruwa tabi bayansu, Safna taja tsaki tareda mik'ewa tashige d'akin Rahma.
Rahma ta shiga d'akin da sallama, saidai bayanan yashiga wanka, Nawal ce kawai take zaune tana wasa da wayarsa, ta ajiye ruwan ta ce, "Nawal zomuje ki kwanta.
Nawal ta nok'e k'afad'a tareda kwa6e fuska, ta ce, " um um momy ni ad'akin papa zan kwanta,
Rahma tayi tayi amma Nawal tak'i Dan haka ta k'yaleta takoma d'akinta.
Bata dawo d'akinsaba sai 10:34pm, yana zaune yana danne dannen laptop tashigo, Nawal kam tayi barci.
Takai minti 3 da shigowa sannan yad'aga kai yakalleta sau d'aya yamaida kansa ga laptop, ki d'auki Nawal kikaita d'akin ki mana, yay maganar cikin nutsatstsiyar murya.
Rahma ta shagwa6e murya ta ce, "Dan ALLAH kabarta anan mana.
Yanda tayi maganar yasa dole yad'ago yana kallonta, tawani narke fuska, saiyaji wani Abu ya mintsini zuviyarsa, yad'an lumshe idanunsa harda yin wanid'an murmushin gefen kumatu, Wanda itakanta Rahma bataga yayibama, ya ce, "yaza'ayi ta kwana anan? aitayi girma da kwana tare da mu, in dama babu kowa a d'akin saikice anbarta ita kad'ai, amma tunda dakowa acan zata kwanta, yamaida kansa yacigaba da aikinsa abinsa.
Haka tad'auketa badan tasoba tanufi d'akinta da ita, Safna tana zaune tana danna waya Rahma tashigo tacanjama Nawal kaya sannan tagyara mata kwanciya.
Ta kalli safna, aunty Safna saida safe.
Safna takalleta cikeda mamaki, cikin yatsine fuska ta ce, " ina zakije? Kike fad'in saida safe?.
Cikin d'anjin nauyinta Rahma ta ce, "d'akin dadyn Nawal".
d'akin dadyn Nawal kuma?, tofa sabon salo kenan wai gemu akafad'a, yaukuma?.
Rahma dai batace komaiba tafice abinta.
Har yanzu yana gaban laptop, tashigo tazauna akujerar d'akin.
Yad'an kalleta bayan yakalli agogo, sannan yamaida kansa kan aikinsa.
Bayan kamar minti biyu ya ce, bakijin barcine? Kobakiga agogoba?.
Murmushi kawai tayi batareda tace komaiba, ya ce, " kije ki kwanta abinki wannan aikin Nawal k'areshi ba yanzuba.
Dukda zuciyarta cike take da fargaba hakan bai hanata tashiba, gadon tahau amma dagacan gefe ta kwanta, tayi addu'oin ta, shiru tayi tamkar tana barci, amma duk motsin da bobo yayi sai gabanta ya fad'i, ganitake tamkar kanta yayo.
Dukda Rahma ba yarinya bace mai yawan kwaramniya kuma batada yawan surutu dan haka bata cika shiga cikin k'awayeba, bare ayi firar aure da ita, k'awayenta basa wuce basma ihsan, to amma ana koya musu wasu abubuwan a islamiyya, kuma takan d'an ta6a karatun hausa Novels idan tagani awajen Basma ko ihsan, wad'an nan dalilan yasa tasan wasu abubuwa da yawa akan zaman takewar aure, saidai yanda taga bobo yayi burus da lamarinta yasakata sakin jikinta sosai da manta sirad'in daren farko, saikuma gashi zuwan safna nashirin jamata.....
Hakadai taita tunane tunane har barcin gsky yay awon gaba da'ita.
Shikam bobo dabaima san tanayiba hankalinsa nakan aikinsa dan zuwa gobe idan ALLAH yakaimu yanada wata shari'a.
Ad'akin Rahma kam Safna takasa zaune takasa tsaye, wato saboda tayi magana jiya shine yau yagayyaci Rahma kwana d'akinsa? Yanaso yanuna mata maganarta ba gsky baceba kenan.
Tacije le6enta tana hawaye, aiko ya kusanceta saiya saketa ya aureni narantse, Dan INA sonsa sanda banta6ama wani mahalukiba aduniyarnan, tafashe da kuka.
Waya tad'auka takira Baseera, can aka d'auka ko gaisuwa bata tsaya sunyiba ta CE, "baseera inacikin matsala.
Wace irin Marsala kuma k'awata?.
Baseera duk shawarar dakika bani na aiwatar jiya, nasameshi namasa magana, shine ya CE, " yau Rahma taje d'akinsa ta kwana, yanzun haka zancen nan danake miki tanacan.
Baseera ta sauke ajiyar zuciya safna ki kwantar da hankalinki babu abinda zai mata, nasan yayi hakane Dan kawai ya 6ata miki rai, Rahma d'in nawa take dahar zai kusanceta Indai yanada tausayi......
Safna tayi saurin katseta, Baseera bazaki ganeba, sufa mazan yanzu babu ruwansu dawani k'ank'antar mace, kema kuma kinsani, balleshi d'an hutu yana ganin komai yana tafiya daidai arayuwarsa,, kinsan dolene yabuk'aci mace aii.
Hakane Safna, amma kilura da wani Abu had'asu akayi kowa bayaso, kinga kuwa bazaije mata gaba gad'iba kasancewarsa mutum mai d'aukar kan tsiya, towaima na tambayeki?, kin aiwatar da aikin malam kuwa?.
Na aiwatar jiya, amma d'an zafinkan baiciba, canta had'osu shida ita yafito d'aki rai a 6ace daga nan yafice, Dan jiya abincin safe kawai yaci agidan, inda ALLAH yasoni baduka nazuba bama.
To aii da sauk'i, yanzun ga shawara d'aya dazata kawo miki nutsuwa harki samu barci, kisamu kota window ne kilek'a su, kiga halin dasuke ciki.
Kai baseera wannan ba shawara baceba, idan naje Nagano abinda zaisaka zuciyata bugawafa?.
Karki damu, insha ALLAHU bazaki ganoba.
Bayan sunyi sallama safna tayi tamaula tanufi bayan d'akunan, cikin ikon ALLAH window d'akinsa abud'e take, da sand'a taje wajen, bobo tahango abakin gadon zaune yana danna laptop, Rahma na kwance nesa dashi tarufa da bargo tana barci.
Wata sassanyar ajiyar zuciya tasaki sannan tajuya, cikin kwanciyar hankali tayi barcinta.
βHummm kunjifa saka kai awahala masu karatu, ALLAH yarabamu da aikin Dana Dani.β
Marak'isiyya ta ce, "aunty Billy muma muje mukwanta, bobo ne kawai yajuri Rana dare yana danna laptop.β
Na ce, βaikinsan mutumin na Madeena kamar k'arfe yake, baya gajiya da aiki.β
.*.*.*.*.*.*.*.*.*.*.*.*.
Yau tsawon kwanan Rahma uku da fara kwana d'akin bobo, amma ko alama baita6a kawomata wani Abu sa6anin hankalintaba, Dan haka tafara sakin jikinta sa6anin da datake barci a d'arare.
Tana zaune tanayin addu'ar barci yafito daga wanka, dagashi sai tawul saikuma k'arami dayake goge sumarsa, da sauri Rahma tashafa addu'a ta kwanta.
Yay murmushi tareda fad'in gsky Rahama kinada sonkai kulum saidai kima kanki addu'a amma banda ni.
Murmushi tayi sannan ta ce, "kaima ina maka aii.
Anya kuwa my cute?.
ALLAH kuwa da gsk nakeyi.
Toshikenan na yarda yay maganar yana saka kayan barci, tsaf yagama shiryawa yasaka turare sannan yazauna abakin gadon, yad'auki wayarsa yana dubawa Dan d'anzu ankirasa yana wanka, khairiyya ce Dan haka ya kalli agogo sannan yakirata, bugu biyu ta d'auka, ta ce, " ya bobo ina yini?, lfy kawai ya ce, "yad'ora da fad'in k miye nakirana adarennan?.
Kayi hak'uri Yaya nakira number Anty Rahma ne akashe dama da'ita zanyi magana.
Miya faru?.
Babu komaifa, somuke muju kozatazo gobe idan ALLAH yakaimu d'in.
yaran nan nakula kunefa kuke son koyama matata bakin yawo, yanzu inbanda son gantali mizata muku giben?.
Ayya Yaya wlhy shirye shiryefa mukeyi, kuma kaga yanzu Ammi tahanamu fita ko ina.
d'an k'aramin tsaki yaja ya ce, " ALLAH yakaimu, baijira cewartaba ya yanke wayar yama kasheta gaba d'aya.
Juyowa yayi yana kallon Rahma wadda tai muk'us adole ita barci takeyi, yay murmushi komaidai wayon amarya sai ansha manta, nasan idonki biyu, idan baki juyo kimin addu'aba zakisha mamaki yau.
Da sauri tajuyo.
Yako tuntsure da dariya kekam anyi matsoraciya anan, to amin Dan barci nakeji.
Azuciyarta ta ce, "yaukuma babu latsa laptop.