Showing 54001 words to 57000 words out of 111128 words

Chapter 19 - Abdulmalik Bobo Part 1 Hausa Novel Complete

20 Dec 2024

755

Daganan aka shirya Nawal cikin kaya masu k'yau, shima ogan kwalliya yakuma ci, aka fara gudanar da biking birthday d'in Nawal.
Masha ALLAH komai ya k'ayatar abin burgewa.
Wajen bada cake Nawal tacuro tasakama babanta tasakama Rahma, tabi sauran iyayen matansu ya hamza dukta basu, su khairiyyama haka, daganan aka fara cashiya.
Biki dai bai tashiba sai gab da sallar magriba.
Masu tafiya suka tattafi, akabar yaransu ya hamza kawai da matansu, bayan isha'i suma mazansu suka iso, saida sukaci sukasha akasha hirara zuminci sannan kowa ya kwashi family nasa sai gida.
Bobo ya tsarama kansa wani Abu yau, amma saiyaji wai agidan su khursiyya zasu kwana, ba k'aramin haushi abin yabashiba amma saiya dake tunda bashida yanda zaiyi.

_bayan kwana hud'u_
Duk burin da bobo yaci akan Rahma ya rushe Dan har sannan su kursiyya suna gidan, doledai yad'aga k'afa.
Ranar Litinin da safe su khursiyya suka koma gida abinsu, shima bobo yafita aiki, Nawal kuma tana makaranta sai Rahma kawai agidan.
Tayi aikinta tagama komai tsaf, 1:30pm tana zaune afalo tana kallo wayarta tayi wringing da sauri ta kalli wayar bak'uwar no. ce, shiru tayi Dan yau tunda tatashi gabanta ke fad'uwa, har wayar ta yanke bata d'agaba aka sake kira, ganin babu dacewa arashin d'aukar yasa ta d'auka tunda batasan ko wayeba.
Sassanyar muryarsa tadaki kunnenta, ta sauke ajiyar zuciya wadda yajita har yatsan kafarsa, yad'an lumshe idanunsa yabud'e tareda jingina da kujerarsa, ahankali yake d'an lulita, ya ce, ''matsoraciya da kinzata waye to?.
Murmushi tayi ta ce, "nifa ba tsoro najiba, baki yata6e tamkar yana gabanta ya ce, " dama zancemikine kid'aukko babynki a school yau aiki yamin yawa a office bazan samu damar d'akkotaba.
Okey babu damuwa.
So zaki iya deriving d'in ko?.
Eh zan iya.
Okey tom ALLAH ya tsare, saina sake kira.......
d'if ya kashe kafin tayi magana, murmushi tayi kawai tamik'e tacanja kayanta.
d'akinsa tashiga Dan key d'in motarta yana hannunsa, tagama dube dubenta bata ganiba, sai wani na jar motarsa a durowar gefen gadon, shita d'auka tafito.
Tashiga motar daketa tashin k'amshi, tana mamakin turaren da Bobo yake amfani dashi haka, komai nashi Yakama k'amshin turarensa, mai gadi yabud'e mata gate tafice.
Tafiya take ahankali saidai wani Abu mai kama da tsoro yana ta6a zuciyarta Dan tunda tafito daga gida take gani kamar wata bak'ar mota nabinta abaya, ajiyar zuciya tayi dataga motar kamar ta6ace, dahakadai tak'arasa makarantar su Nawal ta d'akkota.
Labarin makaranta Nawal keta bata, amma itafa hankalinta yafara tashi Dan yanzuma k'ara ganin motar d'azu takeyi.
Sunzo daidai danja ta rik'esu saikawai taga anbud'e motarsu anshigo, atsorace takalli bayanta saitaga wasu zaratan samari majiya k'arfi zaune tamkar motar gidansu, d'aya yanunata da bindiga, d'ayan kuma yatoshe bakin Nawal.
ga Motar bak'in Gilas ce, nawaje baya ganin naciki...............




*_“😳masu karatu nikamdai atsorace nake, kosuwaye wad'annan mutane?, mikuma zasuyima Rahma da Nawal?.”_*
Hummmm koya zata kaya?????????.







_kutayamu murna my sister d'ina ta haihu mace._




*_luv u oll my fan's_*
*_(((S))).....2017_*
[11/12, 2:56 PM] mrs bilkisu: 👩🏻‍💻typing........

❣ *_ABDUL-MALEEK_*❣
_•{🅱🅾🅱🅾}•_


*_NA_*
_*Bilyn Abdul*_

_sadaukarwa_
*_Abba Gana_*
*_Batul mamman_*
*_Billy giro_*


5⃣1⃣

Babu dad'ewa aka basu hannu, tuni jikin Rahma yajik'e da gumi dukda AC dake aiki amotar, jikinta sairawa yakeyi, duk addu'ar datazo bakinta karantawa takeyi.
Dakansu suke nuna mata hanyar dazatabi, sunyi nisa sosai datafiya awata hanyar k'auyen da Rahma batasan ko inaneba, wayartace tayi wringing harzata d'auka Wanda yake rik'e da bindiga yadaka mata tsawa, kina d'agawa zan tarwatsa kanki.
Janye hannunta tayi da sauri akan wayar, Wanda yake rik'eda Nawal ne yad'auki wayar, saidai kafin yad'aga ta katse, wata uwar dariya yashek'e da ita Dan ganin sunan daya kira Rahman, *_dadyn Nawal_*.
Wani gida suka kaisu, zuwa sannan Nawal tayi barci, Dan sun shak'a mata wani abune, Rahma tarungume Nawal tana kuka maiban tausayi, aranta tana tunanin misukayima wad'an nan mutane dazasu kawosu nan??.

Bobo kam hankalinsa yafara tashi Dan ganin yayima Rahma kira wajen 10+ amma bata d'agaba, dukda d'umbin aikin dake gabansa haka ya tureshi yabaro office d'in.
Makarantar su Nawal yafara zuwa, auntyn su ta ce, "aii tund'azu bayan yakira kamar yanda ya ce, " momynta ce tazo ta d'auketa, to babu dad'ewa tazo ta d'auketa.....
Bai tsaya yagama saurarentaba yayo waje, daga nan gidansa yanufa, tun a gate yatambayi mai gadi, amma ya ce, "basu dawoba.
Innalillahi wa'inna'ilaihirraji'un kawai yake ammabata azuciyarsa, amma dukya birkice, da sauri yaciro wayarsa a aljihu yakira khursiyya, itama ta ce, " basu zoba, Abu kamar wasa dukya rewad'e dangi dakira amma kowa amsa d'aya yake bashi *_basu zoba_*.
Cikin rawar jiki yakira Appa yaturo masa number Abbansu Rahma.
Cikin girmamawa ya gaidashi, tareda masa bayanin shine, Abba ya ce, "ALLAH sarki Abdulmaleek ngd ALLAH yayimaka albarka, ya su Rahma d'in?. Tun anan jikin bobo yayi sanyi, murya asark'e ya ce, " dama ita zantanbaya ko sunzo nan gidan?.
Kai A'a gsky Rahma batazoba, kunyi da'ita zatazone?.
A'a Abba dama...... Nan yafad'a masa yanda akayi.
Abba yaja numfashi, to mud'an k'ara hak'iri zuwa d'an anjima mugani kota biya wani wajen, dukda dai nasan wannan baya d'aya daga cikin halayen Rahma, tabbas da Safna cema bazan damuba Dan nasan tanada rawarkai, amma Rahma kam batada wannan halin.
To abba. Kawai bobo yafad'a ya yanke wayar, kuma kiran Number Rahma yayi amma ank'i d'auka, yadafe Kansas tamkar zai FASA ihu, yana nan tsaye ak'ofar gate saiga ya ishaq da ya Hamza, suka tambayi yanda akayi yasanar dasu.
Ya hamza ya ce, "kasanarda Ammar ne?.”
Girgiza kai kawai bobo yayi danya kasa magana, ya Hamza yakira Ammar yayamasa bayanin kimai, salati ammar yashiga yi, bai tsaya 6ata lokaciba yabaza yaransa ki ina.

Al'amarifa kamar wasa hardare babu wani bayani, zuwa yanzun labari yakarad'e dangi, bobo kam dukya fita hayyacinsa, sai kuka yake tamkar mace, shidama haka yake akwai jarumta amma Abu kad'anne ke karya azuciyarsa.
Duksun dawo daga sallar isha'i, suna zaune afalo gidan Appa zugum², harda Abban Rahma da Umminsu, momyn ya Kamal da dad d'insu Ameera ihsan ya Muneer ya shaheed duk suna gidan Appa, Safna CE kawai babu, dantana makaranta abin yafaru, bayan tadawo mai gadi yashaida mata komai, yad'ora da fad'in 'yangidanma duk suna gidan surukan Rahma d'in.
Safna ta ta6e Baki ta ce, " kaga baba bud'emin gate nashiga nahuta tukunna, Dan bazan iya zaman jigum jigum ba wlhy tunda ba mutuwa akace sunyiba.
Maganar tata tarazana baba mai gadi, bayan yabud'e mata gate yabi mortar da kallo yana jin kina kai, aransa ya ce, "lallai yau nakuma shaidawa yarinyarnan batada mutumci ko kad'an, inbanda rashin mutumci d'an uwanka uwa d'aya uba d'aya ya6ata kanuna rashin damuwarka, kai ALLAH dai ya k'yauta to.
Safna dai bamatasan yanayiba Dan tuni tashige cikin gida abinta, sai wata fara'a takeyi wadda nadad'e ban ganiba daga gareta.

🤔araina Na ce, " safna Kodai kidai??.



*_3days_*
Tsawon kwana uku kenan da 6atansu Rahma, Abu tamkar wasa, zuwa yanzu kam aii kowa yajigata, Appa yabaza rok'on ALLAH amasallatai, hakama gidan redio Dana TV, social media ma haka, amma shiru kakeji wai malam yaci shirwa, kuma tun ranar ba'a sake samun number Rahma ba.
ALLAH sarki bobo acikin kwana ukunnan Yayi wata uwar Rama, ko abinci bayasonci sai ammi ta tsareshi tamkar yaro tabashi abaki, shima lauma hud'u zuwa Biyar zaice yak'oshi, saitata lalashinsa sannan zaiyarda yak'ara kad'an.

Nikaina yabani tausayi k'warai da gsk😥.

Yanzuma suna zaune afalo Ammi tana lalla6ashin sa akan yasha shayi amma sai yatsine baki yakeyi, ya mararairaice murya tamkar zaiyi kuka, ALLAH Ammi nak'oshi.
A'a mukarram kadaure kasha koda kad'anne, kaga rabonka da abinci tun jiya da yammafa, komai na rayuwa hak'uri yakeso, Addu'a suke buk'ata daga garemu kaji, ALLAH ya ku6tar mana dasu idan suna Raye.
Hawaye suka ziraro bisa kumatunsa, Ammi ta share masa..
Yana shirin yin magana sukaji sallmar ammar, suka amsa, yashigo ya zauna.
Ammi yarissina yagaida sannan yabama bobo hannu suka gaisa🤝, cikeda tausayi Ammar yake kallon bobo.
Ka kwantar da hankalinka Abdulmaleek insha ALLAHU za'a gansu, yanzu inaso naji time d'in Daka kira Rahma kafin tatafi d'aukar Nawal?.
Wayoyinsa yakwaso dukya yamik'ama Ammar Dan yanzun bayason yawanyin magana sosai.
Bincike sosai Ammar yakeyi a wayoyin Bobo yanayi yana waya da office d'insu, bayan sun kammala yabama bobo wayoyinsa, ya ce, "kabar wayiyinka akunne daga yanzun Duk Wanda yakiraka zamu gani, zakuma mu iyabi ta wannan hanyar dangano ko waye.
Jinjina kai kawai bobo yayi batareda yayi maganaba.
Ammi ta ce, " Ammar karinga yima abokinka fad'a yaringa cin abinci jibifa yanda yaketa ramewa.
Ammar ya ce, "kik'ara hak'uri Ammi insha ALLAHU zai ringaci yanzu yana cikin rud'anine.
To ALLAH yasa Ammi tafad'a tana mik'ewa tabasu waje.
Haka Ammar yatsare bobo yad'ansha shayin da soyayyen dankalin sannan yaymasa sallama yatafi.

Tafiyar Amma babu dad'ewa saigasu ya Hamza sudukansu.
Guri suka samu suka zauna suna k'ara kwantarma da bobo hankali, yana kwance saman doguwar kujera yana jinsu, badai ya iya cemusu komai amma sunsan yana saurarensu, wayar bobo tafara wringing yayi burus da ita tamkar baijiba harta tsinke aka sake kira, ya ishaq ya ce, "kad'auka mana, 6ata fuska yayi tamkar zaiyi kuka amma baice komaiba, ganin wayar tana niyyar tsinkewa ya sulaiman yay saurin d'auka ya ce, " hello.
Muryar data daki kunnensa CE tasakashi mik'ewa zumbur yana fad'in Rahma Rahma....... Kuna ina ne?.....miya faru daku?........
Aiikafin yafarga bobo ya warce wayar, muryarsa har rawa take ya ce, "Rahma Ku........
Bai k'arasaba wata muryar takatseshi da fad'in ba ita bace ta cancanta tabaku amsar tambayoyinku mine nan.
Ku suwaye!!!?, Bobo yay maganar Afusace.
Daga canma aka Daka masa tsawa, kai malam karka d'aga mana murya.
Bobo ya ce, " kaga bawannan bane damuwata, miyasa kuka kamamin matana da d'iyata?, misuka muku?, waye yasakaku?, mukuke buk'ata?, idan kud'ine kufad'i konawane za'a Baku, pls karku cutar dasu.
A'a a'a muba kud'i muke buk'ataba domin anrigaya an biyamu, kai kanka muke buk'ata, inkuwa bakazoba tom ran 'yarka da matarka zaizama fansar ranka amaimakonka.
Bobo yarintse idonsa tareda cije le6ensa, saboda 6acin rai yagaza cewa komai.
Daga can akace haba zaki kardai ace ka tsorata?, hhhhhhhh, bai kamata kaji tsoroba, munbaka daganan zuwa jibi idan bakazoba tom zaka tsinci gawar matarka da 'yarka, idan kuma kana buk'atarsu darai tom fine sai ka fanshi ransu.
Saidai zuwan naka yanada sharad'i, wlhy koda wasa kada kayi gangancin zuwa da police zamu gane, na biyu saika taho zamu ringa fad'a maka hanya,, na uku idan ka 6ata mana lokaci zamu kacaccala matarka da 'yarka mu watsar, gashi kasakejin muryarta.
Kafin bobo ya ce, "wani Abu saiyaji muryar Rahma cikin kuka tana fad'in dadyn Nawal karkazo pls, Dan ALLAH karka bada ranka akanmu, insha ALLAHU zanfanshi rayuwarku dagakai har Nawal, Nawal tana buk'atar mahaifi tunda tarasa uwa pls karka salwantar mata da ranka, Dan girman ALLAH karkazo, I luv you so much my Abdulmaleek.
I luv you too my cute Rahma na, bobo yafad'a da saurin Baki,....kafin yakuma cewa wani Abu suka kwace wayar, cikin k'araji sukace kai wawa harka samu damar yimana soyayyane??.
Wlhy kacika mana baki sai munmata fad'e hhhhhhhhhh dama gata daga gani zata bada feeling.
Kaiiiiii!!!!!!!!!! Wawa, Bobo yadaka masa tsawa, wlhy kabari zuciyarka takuma kissima maka wani Abu akan matata saina tarwatsa kanka da bullet, na rantse maka da ALLAHn daya halicceni saina shayar dakai gidauniyar azaba, tabbas ni *_Zakine_* kujira zuwan zaki gareku, saina lak'umeku!!!!!!!!!, yanda yayi maganar cikin tsawa harsu ya ishaq da Ammi Appa su khursiyya duksun tsorata da yanayinsa, gabad'aya jikinsa yayi jajur abinka da fari, gashi jikinsa dukya mimmk'e, hakama jijiyoyinsa duksunyi rud'u², yay jifa da wayar, da sauri ya Hamza ya cafeta.
Kowa yasan kuma ransa ya6aci kenan, k'arasawa yayi gaban Appa da Ammi yana yawaye ya ce, "iyayena kusamin Albarka zanje nataho dasu yanzun nan da kaina.
Yanda yake magana dukya basu tsoro da tausayi, Ammi ta ce, " mukarram kayi hak'uri Ammar yazo kutafi tare, kai yagirgiza mata ya ce, "Ammi kedai sakamin Albarka kawai, basu musaba suka dafa kansa tareda saka masa Albarka da k'yak'yk'awar addu'a.
Ya mik'e afusace zai fice, ya sulaiman yay saurin shan gabansa, wata irin hankad'awa bobo yayma ya sulaiman yay taga taga zai fad'i ALLAH yasoshi ya ishaq nakusa yarik'eshi yafad'o jikinsa.
Bobo kam kota kansu baibiba yayo waje, yana fitowa ammar yashigo gidan, da sauri yatsayar da bobo, badan yasoba yatsaya yana kallon ammar dayaci wanka cikin shadda harda babbar Riga, wani d'an guntun tsaki bobo yayi danshi Ammar d'in yabashi haushin kwalliyar dayayi.
Ammar baice masa komaiba yamik'o masa babbar Riga ta shadda.
Galala bobo yatsaya kallon Ammar, wannanfa? yafad'a yana huro hanci.
Kaga kasaka mutafi, Dan mungano Inda suke tasanadin wayar dakukayi yanzu, kasandai babu yanda za'ayi muje kai tsaye dole saimun canja kama gudun karsu San da zuwanmu su cutar dasu.
Bobo yanajin haka yakar6i babbar rigar shaddar yasaka shima harda hula, duk abinda ke faruwa su Appa Ammi ya sulaiman ya ishaq ya Hamza khursiyya khairiyya duksun futo sunajinsu.
Appa ya ce, " ALLAH yayi muku Albarka yayi taimako.
Amin suka amsa.
Bobo da Ammar dawasu police uku suka shiga mota d'aya, su ya ishaq ma mota d'aya, saikuma mota biyu itama duk police ne aciki amma da kayangida Dan kowa shadda yaci tamkar zasu d'aurin aure, ganin haka shima Appa saiya shiga motar su ya Hamza, su khursiyya sukace zasuje suma, AMMAR ya ce, "suyi hak'uri su zauna suyi ta musu addu'a.
Ammi ma kuka takeyi, hakadai suka fice.
Amota Ammar yake sanarma bobo yatura mutane biyu amashin dansuyi gaba.
Jinjina kai bobo yayi Dan har yanzun ransa a6ace yake Musamman idan yatuno da maganar wawan nan wai Rahmar sa zata bada feeling, wlhy saiya cirema d'an iskannan hak'ora....

Da sauri yashige cikin wata gona ya6oye bayan bishiya, boss gafa wasu motocinan har guda hud'u suna zuwa.
Akwai motar 'yan sandane?.
A'a gskiya wad'annanma duk wankan shadda sukayi.
Mtsoooww kaiwane irin wawane, bana gayamaka akwai wani d'aurin aure daza'ayi acikin k'yauyen damuke ba, na tabbata wannan d'aurin auren sukazo, angayamaka su wawayene dazasu taho tun yanzu?, ko ka manta yanzu muka gama waya dashi?, nasan saisunyi shiri sosai kafin su ce zasuyi gigin zuwa, tabbas nasan zuwa gobe saisunzo nan Dan haka karka damu da wad'annan motocin.
Okey boss nafahimta, yafad'a yana gyad'a kai tamkar k'adan gare.
Yana yanke wayar yaji anshak'eshi tabaya, ido ya zazzaro waje Dan mamaki, shikuma wannan daga ina haka? Yaya maganar azuciyarsa.
Wani wawan naushi musaddiq yabama guy d'in tareda k'ar6e wayar, a ina suke?, musaddiq yatambaya yana k'ara shak'eshi.
Zan zan zan fad'amaka kaga sakeni Dan ALLAH karka kasheni.
Wani wawan mari yasake bashi, fad'amin ahaka, cikin Rawar baki yasanarma musaddiq, shikuma yakira su Ammar yafad'a musu.
Musaddiq yakuma fad'in kunawane aka baza Dan kawo rahoton zuwanmu?.
Mu mu mu mu goma shabiyar ne.
Murmushi musaddiq yayi, yad'auki waya yakira sauran 'yan uwansa yace su bazu akwai sauran mutum goma sha hud'u.

_(ALLAH sarki musaddiq bayan Ammar yaturosu amashin su biyu, sunyi shiga k'auye kamar 'yan k'auyen gsk, shikuma yazagaye yakuma samun 'yansanda goma suka taho batareda sanin Ammarba, shine yanzu yakira su dansu bazu adajin)._
Su bobo kam sunatabin hanyar kamar yanda waya take nuna musu, suna zuwa daidai wani wajen mararraba wayar tatsaya wannan alamune na sun iso wajen.
Mutum biyune suka fito suka k'arasa ga wani matashin saurayi dake tsaye yana kallonsu, da alama shima yana cikin mutum 15 da'aka baza Dan kawo rahoto, Dan kallo d'aya Ammar yay masa yagane bashida gsky.
d'an saurayi Dan ALLAH tambaya Muke?.
ALLAH yasa nasani yay maganar yanata zazzare idanu.
Wani hanyar k'auye muke nema da ake d'aurin aure.
Ajiyar zuciya saurayin yayi tareda wale baki, ya ce, "to to zan nuna muku, yana motsawa danufin nuna musu hanya d'ansanda d'aya yanuna masa bindiga, kana motasa zan tarwatsa kanka, ina kuke 6oye dasu?.
Yawu saurayi ya had'iye ya ce, " zan nuna muku yanzun nan....
K'asa yay da bindigar yanda baza'a ganeba yatasashi gaba, suma su bobo suka fiffito, amma sun rarrabu.

Su Rahma suna zaune tana rungume da Nawal suka farajin k'arar harbin bindiga, da sauri takali Wanda yake tsaronsu,

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login