Showing 33001 words to 36000 words out of 111128 words
bata isheshiba yad'akko kofin tee ya mik'a mata.
Kamar bazata amsaba saikuma ta amsa Dan ganin yayi tamau da fuska kamar bai ta6a dariyaba, yamik'o mata filet d'in soyayyar doya.
Saman kujerar dake d'akin Yakoma ya zauna yana danna waya, ganin haka yasa tadake taci abincinta Dan yunwa takeji sosai.
k'asa² yake kallonta, aransa ya ce, "k'aryar ciwo kikeyi yarinya, tumda har kika iya share filet guda na doya, Rahma ta kalleshi ta ce, " nagama.
Banza yay mata yacigaba da danna wayar, saida ya mula Dan Kansa sannan yataso yazauna saman durowar gefen gadon, maganin yacira yabata.
Tofa anan akeyinta, Rahma tayi kwalkwal da ido zatayi kuka, tsak'i yayi yana harararta, idan bazaki amsaba kibarsa kece zakisha wahalarki ke kad'ai wlhy, danni yanzuma zanbar miki gidan.
Yanda yake zabga ruwan masifa yasa ta k'ar6a, saidai tana hawaye tana sha, idan tasha d'aya saitayi kamar zatayi amai saikuma ta daure, shidai yana kallonta ta gefen idonsa Dan yacigaba da latsa waya, hakadai tadaure tasha maganin.
Tashi yayi ya d'auki kwanukan yafita dashi, babu dad'ewa yadawo da k'aramar roba da ruwan zafi aciki, sai k'aramin tawul.
Baiyimata maganaba yajawo d'ank'armin tebir na gilas dake kusada kujera ya zauna, Rahma ta ce, "kasada aranta.
K'afarta yad'auka yad'ora saman stool na madubi, itadai ikon ALLAH take kallo kawai.
Dukda yaga kallon datake masa bai kulaba yafara aikinsa batareda yabi takantaba, yasaka tawul d'in aruwan zafin yad'an yamatse, daganin yanda yake matsar tawul d'in kasan ruwan da zafi, amma Dan bak'ar mugunta ahaka ya nanama Rahma akan k'afar, wani wahalallen ihu tasaki, yay saurin rik'e k'afar yana harararta, kawai saitaji hawaye nabin kumatunta.
Raguwar banza yafad'a afili.
Itama ta ce, " ruwanfa da zafi wlhy, yanda tayi maganar ashagwa6e saiya tsaya yana kallon bakinta, ta kauda fuskarta tana tura Baki gaba.
Shima bakin yata6e yacigaba da aikinsa.
Da zame zame da mazurai aka gama wannan gashin k'afar, yad'auki maganin shafawar ya shafa mata sannan yakwashe kayan yafice itakuma ta kwanta tana sauke numfashi.
Bai sake shigowa d'akinba harsu Ammar suka iso shida matarsa da yaransu biyu duk maza.
Cikin farinciki yataresu, yanda yaketa murmushi saika d'auka bashibane yagamawa Rahma mazuraiba yanzu.
Cikin falon suka k'araso, Sumayya matar Ammar ta ce, "nibanga amaryarba ko ka sakata ta 6uyane?.
Murmushi yayi ya ce, " 6uyan lfy, tana d'aki kwance batada lfy.
Ammar yashek'e da dariya mutumina komun samu k'annen Nawal ne?.
Harararsa yayi kaifa bakada kirki wlhy, to Abu ta taka ak'afarta d'azu da safe.
Ammar ya ce, "ayya ALLAH yakiyaye gaba, amma yanda na sanka d'innan ai yanzu munsami baby duk wani zame ²n ka.
Kadaiji dashi d'an iska, bobo yafad'a yana nufar d'akin Rahma.
A zaune ya Tatar da ita tagama saka kaya, Dan k'afar tad'an saki shine taje tayi wanka.
Ki taso su Ammar sunzo.
To. tafad'a atak'aice, haryaje k'ofa takatseshi dafad'in bafa zan iya fitaba.
Cak yatsaya kuma bai juyoba, yakai minti uku ahaka saikuma ya waigo, yawani saki murmushin mugunta danyasan maganar dazaiyi, okey kinaso nad'aukeki Dan kinji Ammar ya ce, " namiki ciki ko?, kinaso su tabbar kenan?.
Ido Rahma ta gwalalo waje ta ce, "nid'in?.
Baki ya ta6e tareda takowa har inda take, taho na d'aukeki nikuma namiki alk'awarin tabbatar musu da hakan.
Matsawa tayi gefe, ta ce, " kabarsa kawai zan iya.
Dariya yayi ya ce, "Yar rainin hankali, yana gama fad'a yafice yana cigaba da dariyarsa.
Rahma tarike baki o ni Rahma dama haka mutumin nan ya ke?, barikiga natashi kafin yaje ya nafkamin wani sharrin.
Haka ta d'ingisa har zuwa falon, ta zauna suka gaisa sunata tsokanarta, itadai bata iya cewa komai sai murmushi, mik'ewa tayi danufi basu ruwa da abin motsa baki, ya ce, " ina zaki?.
Ruwa zan basu tafad'a tana tafiya da d'ingishi.
Sumayya ta ce, "kinga dawo kizauna amarya, bari na d'akko mana aimu ba bak'i bane, Rahma ta ce, " haba daga zuwanku sai asaka ki aiki?.
Karki damu kinji, idanma kika kusa haihuwa nan gidan zan dawo, hannu tasa tarufe fuskarta Dan kunya, Ammar Kuma yayi dariya, Bobo ya ce, "Ashe na huta nikam?.
"Aiko ka huta."
Sumayya ce tamusu komai daya dace Rahma tayi, abincima atsakar falon sukaci, mutuminku sai wani kaffa² yakeyi da Rahma, ita abunma kunya da dariya yaringa bata, idan kukaga kulawar dayake bata saika d'auka haka suke kullum.
Har dare su Ammar suna gida, sai bayan isha'i suka tafi, bobo kuma yatafi d'akko Nawal Dan gobe zasu koma makaranta.
Rahma tad'an daddogara kamar gurguwa tad'an gyara abinda yadace sannan tayi wanka, shirin barci tayi tazauna jiransu.
Bayan wasu 'yan mintuna da zamanta saigashi ya iso da Nawal akafad'a tayi barci.
Saman gadon ya kwantar da ita, Rahma ta ce, " sannu.
Yauwa, tafad'a atak'aice.
Batabi ta kansaba harya sauyama Nawal kayan barci, shima baice mata komaiba yafita, babu dad'ewa saigashi da ruwa da Kofi, abakin gadon ya zauna yaciri magungunanta ya mik'a mata, tuni ta 6ata rai amma babu yanda zatayi haka ta amsa tana matse ido ta shanye, hawaye harsun cika mata ido.
Baki yata6e yayi kamar baiga hawayenba, yad'auki maganin shafawar yad'ago k'afarta yad'ora saman cinyarsa, maganin yashafa mata, ta lumshe idanu danji take kamar yana mata tafiyar tsutsa.
Shikanshi cikin nishad'i yake shafa k'afar, Dan yakai minti 7 yana shafa maganin, saida tad'an janye k'afarta sannan yadakata.
Mik'ewa yayi yamusu sallama yafita.
Rahma ta sauke ajiyar zuciya aranta ta ce, *_"Zaki na Ammi da Appa kafi karfin wargi"._*
_(Nikam Bilyn Abdul kirarin nata yabani dariya, nima zan kiya naringa yima my Abdul d'ina lol.)_
.*.*.*.*.*.*.*.*.*.*.*.*.
Yau bobo dakansa yayma Nawal wanka, yaymata shirin makaranta, Rahma kuma tadaure tahad'a musu break da abincin Nawal na makaranta.
Sauri² sukayi break d'in suka fita.
Har harabar gidan Rahma tarakasu, tana musu addu'a, bobo daya tada motar yalek'o kansa yana kallon Rahma, 'Yar gurguwar gidanmu akuladai karkuma akarya d'ayar.
Yana gama fad'a yafigi motar suka fice.
Ita maganar tasama dariya tabata wlhy, afili ta ce, "dama yanama mutane wasa?.
Tayi murmushi tareda shigewa ciki.
---------------------------+
Yana ajiye Nawal a school yanufi office, amma duk saurin dayakeyi saida yatadda mutane na jiransa, ciki harda Alh Sunusi Dala.
Kasancewar kowa yasan waye Alh sunusi dala suka barsa yafara shiga domin ganin Bobo.
Hannu yabashi suka gaisa, sannan ya ce, " Alhaji mike tafe dakai?.
Alh sunusi yasauke ajiyar zuciya, Brr... abunda ke tafe dani babbane kuwa, d'ana 'yan sanda suka kama tun ranar juma'a, kuma sunk'i bamu belinsa wai saisun kaimu kotu, gashi lauyana baya k'asarnan naturashi wajen wasu kayana a k'asar Chaina.
Alh to yanzu ni mikakeso namaka?, bobo yayi tambayar kamar baisan komaiba.
Saboda sunce munemi lauya, nasa abincikamin kwararren lauya shine aka kawoni wajenka, kuma nima idona ya tabbatar mini da hakan.
Shiru Bobo yayi yana karantar Alhaji sunusi, saida yaja minti biyu sannan ya ce, "Alhaji kozan iya ganin takardar sammacin da aka baku?.
A wannan mai sauk'ine aii Brr, Alh sunusi tafad'a yana mik'ama bobo takardar.
Saida yagama karantawa sannan ya ce, " Alhaji gsky akwai Matsala?.
Matsalarmi kuma Brr......?.
Wato wad'anda suke k'arar d'anka sunzo sun sameni tun ranar juma'a, kuma nine lauyansu.
Wani huci Alhaji yasauke, saikuma yay k'ok'arin 6oye 6acin ransa, ya ce, "Brr kataimakeni kamaida musu, ni namaka alk'awarin zan biyaka nikin baninkin d'in abinda suka baka wlhy.
Murmushi bobo yayi, sorry Alhaji hakan bazai yuwuba, duk Wanda yad'aukeni aiki a farko shinake yimawa gsky, inabaka hak'uri akan hakan, saidai nace maka mutari gaba kuma........
Kai k'aramin shashasha!!!! Alhaji sunusi yakatse Bobo a tsawace.
Shima Bobo ya katseshi ta hanyar d'aga masa hannu, Alhaji sauraramin nan office d'inane ba gidan kallon boll ba, ra'ayinane kuma nayi duk abinda nakeso alokacin danakeso gakuma Wanda nakeso, Dan zaman kaina nakeyi bana waniba.....
Kwafa Alhaji sunusi yayi tareda mik'ewa, yanuna Bobo dad'an yatsa yaro yarone, nakula bakasan koni wayeba, amma ina gab da sanar dakai, ni nafika zafin kai Brr...... Dan haka muzuba nidakai.
Mtsowwww muzuba mana Alhaji, nidakai za'a tantance damisar takarda.
Fuuuuuuu alhaji Sunusi yafice, masu tsaronsa suka take masa bayan.
Bobo kuma yaja wani wawan tsaki tareda zama saman kujerarsa.
*_" hummm masu karatu, bobofa yad'ebo ruwan dafa Kansa, kokuwa Alhaji sunusi ne yay gamo da gamonsa?, to kudai biyo d'iyar malam Ibraheema mata agidan Abdus'salam kusha labari."_*
_labarin bobo bagajeren lbr bane, idan na gajarceshi kuma bazakuji dad'iba, Dan haka karku damu da basarwar bobo zai dawo hanyane😂🤸🏼♂._
💃🏻💃🏻💃🏻yeeeeee ruwa akemana yanzun nan🌧🌧🌧.
*_luv u oll my fan's_*
*_(((S))...........2017_*
[11/12, 2:52 PM] mrs bilkisu: 👩🏻💻typing........
❣ *_ABDUL-MALEEK_*❣
_•{BoBo}•_
*_NA_*
_*Bilyn Abdul*_
_sadaukarwa_
*_Abba Gana_*
*_Batul mamman_*
*_Billy giro_*
*_Shafin nakune masoyan Bobo, bilyn Abdul d'in ma takuce gaba d'aya, gaisuwa da fatan alkairi su tabbata agareku masoyana, ngd da k'yauna sosai, duk masoyin Bobo ya d'auka wannan shafin nasane, Alkairin ALLAH ya tabbata agareku aduk Inda kuke._*
Luv u mazga mazga🤸🏼♂😂❤🤝.
4⃣2⃣
_waye Alh Sunusi dala?._
Alh sunusi dala rik'ak'k'en d'an siyasane, kuma d'an kasuwa Wanda yay zarra akan canjin Dala, matarsa d'aya haj Falmata da yaransu hud'u, Surayya itace babba yanzun haka tayi aure yaranta biyu, sai Haneef shikam babuma auren a tsarinsa, sai Hafeeza da Shareefa suduk 'yammatane.
Alh Sunusi bashida kirki ko kad'an, mutumne mai matuk'ar had'ari, idan yanason Abu zaibi takowace hanya ya sameshi, yana matuk'ar Son Haneef kasancewarsa shikaid'aine d'ansa namiji, sosai Haneef yad'akko halayen mahaifinsa harma yaso zartashi, Dan Haneef tamkar d'an bunsuru yake wajen Neman mata, idan yakwafama mace tota shiga uku, kasancewarsa k'yak'yk'yawa gakuma kud'i saiya zama 'yammatan dakansu suke kawo Kansu gareshi, Ak'alla Haneef yakai shekara 36 amma yak'iyin aure sai iskanci da ta6ara.
Kwata kwata haj Falmata bata k'aunar halin d'an nata, kullum cikin yimasa nasiha take da nuna masa kuskurensa, amma yayi burus da zancen nata acewarsa har yanzu bata wayeba.
Halin Haneef da haj Falmata take k'yamata shine yasa Alh Sunusi yake ganin bata son Haneef d'in kwata², aganinsa tafison yaranta matane.
Itadai kullum cikin nuna fasa ba haka bane take, amma baya ta6a saurarenta, Dan haka tazuba musu ido shida Haneef d'in.
Yaranta mata duk halinta suka biyo, suma basa k'aunar halin babansu da d'an uwan Nasu, amma babu yanda zasuyi saidai addu'a kawai.
Toyanzu mugun halin Haneef yaja masa Shiga tarkon bobo, shikam bobo karanbani yaja masa shiga tarkon mahaifin haneef, Alh Sunusi dala, toko waye keda nasara?.
Saimun cigaba dabin labarin zamu tabbatar.
.*.*.*.*.*.*.*.*.*.*.*.*.
K'afar Rahma ta warke, amma tasha bak'i 'yan dubiya, ammi kanta saida tazo dubata, Matansu ya Ishaq ma haka duk sunzo, harsu ya ishaq d'in kansu.
Itakam daga Rahama saitace gara dataji ciwon, Dan kobabu komai acinkin kwana ukun kullum gidan yana cike da dangi asha hira, su khursiyya kuwa kullum suna gidan.
Kwata² tadaina gyarama Bobo d'akinsa, tun ranarma bata sake kallon ko hanyar d'akinba, su khairiyyane suke gyara masa idan sunzo.
Dama bawani shiga harkarsa takeba, to akwana ukunnan ma talura yana matuk'ar busy, Dan kullum yana danna laptop, wani sa'inma saiyakai 10 baidawo gidanba.
Dukda abin na damunta tanason kuma tambayarsa abinda ke faruwa?, amma tana tsoron wulak'ancinsa, Dan haka ta shareshi itama, tanadai tayasa da addu'a samun nasara akan abinda ya burkitashi haka.
+++
A6angaren bobo kam ya ajiye komai gefe, gaba d'ayan hankalinsa yabada akan shari'arsu da Haneef, bak'aramin shiri yayma shari'arba, Dan yayi bincike na musamman akan halayyar haneef, wannan yasa yakeson ceto sauran yara daga gudun fad'awa tarkon Haneef d'in na gaba, Dan ance mai halin bata barin halinsa.
Tun washe garin daya kai Rahma asibiti taga muheebat kuma yaji tasanta, da safe yakar6i address d'in gidansu Idris, tare sukaje shida ya Hamza da ya sulaiman har gidan suka maida muheebat.
Dangin hebba sunyi murna da dawowarta garesu, sunkuma sakama su bobo albarka gameda taimakon dasuka bama yarinyar, saidai sunyi kuka sosai akanjin k'addarar data afka mata.
Nansu ya Hamza sukaita lallashinsu, sukace sukwantar da hankalinsu zasu kwatoma Hibba hak'inta dukda dai budurcinta yatafi bazai dawoba.
Sunji dad'i sosai tareda yimusu k'yak'yk'yawar addu'a.
Bobo ya ce, " zamu tafi, amma ga no. d'ina Indai dawata Matsala sai'a kirani, sannan akan rashin maganar heeba d'in kodama tanada wannan matsalar?.
Eh damacan bata iya magana tun bayan ciwon k'yanda datayi lalurar ta sameta, amma tanajin abinda ake fad'a cewar baba Hamisu mahaifinsu hibba da idris.
ALLAH sarki, amma baba kunta6a d'aukar mataki akan hakan?. Dr sulaiman ya tambaya?.
A'a yaro, gsky bamuta6a yiba kasancewarsa kada muyima ALLAH shishshigi.
Hakane baba amma yana da k'yau anema mata magani, Dan naga zata iya samun lfy, ban yimata aikin bane dama saboda inaso saida izininku, amma insha ALLAH zamu yimata wani aiki komai zai dawo daidai, Dan matsalarta bata cika tsananiba.
To shikenan mungode ALLAH yasaka muku da alkairi, yayma Rayuwarku albarka, ALLAH yajik'an mahaifa.
Ameen suka fad'a suna mik'ewa, sukai musu sallama suka tafi akan sai suhad'u a kotu ranar talata.
*.......................*
Washe gari talata su bobo suka shiga shari'a.
Tun azaman farko hankalin lauyan Haneef yatashi, dan tabbas yasan Bobo kwarone tunda bayau suka fara karawaba, yasan kuma bobo baya tsayama Mara gsky koyaya suke kuwa, komin k'arfin alak'arsu.
Zaman nan nafarko kawai bobo yakawo hujjoji da dama wad'anda suka saka mutane dayawa yadda Haneef ya aikata abinda ake zarginsa dashi, amma dayake alk'ali yaci kud'i saiya d'aga shari'ar sai nan da sati biyu masu zuwa.
Anan lauyan Haneef yanemi Belin haneef amma bobo yace Sam bai yardaba, Alk'ali yasan halin bobo dabin kwakwaf dama kuma bawani shiri sukeba, Dan haka yace k'orafi bai kar6uba, zasucigaba da rik'e Haneef.
Ran Alh Sunusi ya6aci, sai kallon miye haka?, yakema Alk'ali.
Alk'ali kuma yanamasa magana da ido akan subi ahankali.
Duk abinda ke faruwa bobo yana kallonsu, Dan haka yasaki murmushin sa na mugunta, Wanda Ammar kankira da yafi saukar Boom ban tsoro, amma ga Wanda yasan ma'anar murmushin ga bobo kenan.
Suna fitowa daga shari'ar gida bobo yay shirin tafiya, daka gansa Kasan yana cikin farinciki, bud'e motarsa yayi zai shiga Alh Sunusi da masu tsaronsa suka k'araso wajen, bobo yaja sirin farin gilas d'insa k'asan ido Wanda yadawo k'arshen hancinsa ya tsaya.
_( na ce, "anyi shirin rashin arzik'i kenan😂)?._
Alh Sunusi ya watsama bobo harara, yaro har yanzu kanka yana rawa ko?.
Murmushi bobo yayi, tareda bud'e motar yawatsa kayan hannunsa a sit d'in baya, yarufe murfin sannan yajingina da motar yana kallon Alh Sunusi cikeda basarwa.
Alh wai minayi maka hakane dazafi? kasaka rayuwata agaba.
Yakamata ka lura dawani Abu, ni lauyane mai zaman kansa, banida banbanci dad'an kasuwa, so saina gadamar saida maka hajata, idan banida ra'ayi saikaje gaba kasiya, Alhaji karik'e girmanka, banaso mufara game tare dakai, Dan akwai matsala.
da d'anka nake shari'a bada kaiba, so ka kalli gabanka kada katsaya kallon ruwa kwad'o yayi maka k'afa wlhy.
Yana gama fad'a yashige mota, Alh Sunusi kuma yana zabga ruwan masifa da bala'i, jiyake yak'ara tsanar yaronnan.
Fuuuuu bobo yaja mota tareda bud'ama Alh Sunusi k'ura, by Alhaji sai zama na biyu, bobo yafad'a yana figar motar yabar harabar get d'in.
Kwafa Alhaji Sunusi yayi, tareda fad'in zakasan koni waye yaro.
.×.×.×.×.×.×.×.×.×.×.
Da sallamarsa yashigo falon, saidai shiru babu kowa, yakalli agogon hannunsa 12:15pm Nawal bata dawo school ba, aransa yace to ina momynta?.
K'arar Rahma yajiyo daga d'akinta, da sauri yanufi d'akin, hakan yayi daidai dafitowar Rahma dagudu daga bayi, daga ita sai tawul, jikin bobo tafad'a tana rawar jiki, bashida za6i saina rungumeta, yanda jikinta kerawa kawai ya isa kasan wani abune yabata tsoro.
"K!, miya farune?."
Dadyn Nawal Dan ALLAH kataimaka ka kashemin shi wlhy inajin tsoronsa, kataimakeni plzzz, tafad'a tana kuma ruk'unk'umesa, tamkar zata fasa jikinsa tashige.
Bobo ya girgizata "k kinutsu kifad'amin minene mana?.
d'agowa tayi tana d'an hakki, tuni idanun nan NATA masu kasheshi sun wani sake fitowa, yakula duk yanda yarinyar tashiga rud'ani ko tsoro idonta baya canja kala..... Tunani takatse masa da nuna hanyar bayi.
Hannunta yakama suka nufi bathroom d'in, kinga Nutsu ki nunamin banason shirme, abayansa ta mak'ale, tashiga waige² Neman abinda yatsotata saidai wayam yabar wajen.
Yaja tsaki yarinyarnan ALLAH kinyi mugun rainani, yanzu inbanda raini minene a Bathroom d'innan?.
Wlhy naganshi da idona, saidai idan ya 6oyene, harara ya watsa mata yayo baya zai fita yad'an matseta da bango.
Sukur² taji abayanta, Dan haka tayi