Showing 15001 words to 18000 words out of 111128 words

Chapter 6 - Abdulmalik Bobo Part 1 Hausa Novel Complete

20 Dec 2024

746

Aiko dai, Rahma tafad'a.

Abubuwa ummi ta rink'a dannama Rahma a darennan, harsaida Rahma ta ce, " ALLAH ummi nak'oshi cikina zai fashe.
Dariya ummi tayi ta ce, "to barshi haka saida safe.
Daga nan wasu kayan gyaran jiki ummi ta murjema Rahma jiki dasu sannan suka kwanta.

*_BOBO._*
suna Isa gida yanufi d'akinsa, kayan jikinsa yafara ragewa, yana k'ok'arin zaro wayarsa a aljihu saiyaga ta Rahma, Kansa ya dafe O ALLAH, namanta ban bata wayartaba, zubesu yayi a durowar gefen gadon harda tasa, daganan yacire kayan jikinsa, bayi yashiga, bayan wasu 'yan mintuna yafito, badai wanka yayiba.
Shirin barci yayi ya kwanta, saidai barcin yak'i d'aukarsa, fuskar Rahmace take MASA gizo, k'yawawan idanunnan NATA yake hangowa, yasaki wani lallausan murmushi Wanda bansan na miyeba, saikuma yaja siririn tsaki yana gyara kwanciya.
Nima waje nayo nabarsa.

*_Washe gari_*
Tunda sassafe Rahma ta tashi tai wanka kasancewar tana fashin sallah, Basama tafara yarfa mata k'unshi, masha ALLAHU nafad'a Dan k'unshin yana bada ma'ana.
Jikin Rahma duk yayi sanyi, ta tabbata yau babu fashi saita bar gidansu, cikin dabara take share hawayenta dankar Basma tagani dansukad'aine a d'akin.
Zuwa 8:00am angama k'unshin, yayi k'yau sosai, 8:30am akasa Rahma yayi wanka agurguje dantafiya walimar makarantarsu.
Shiri tayi cikin zani da riga na atanfa pink, ta d'ora bak'ar alk'yabba mai shara shara wadda amaren zamani ke yayi, tayi k'yau sosai dukda yau babu kwalliya afuskarta, dak'yarma tayarda Basma tasaka mata pink d'in janbaki Wanda shiga da kwalliyar alk'yabbar.

Wajen walimar yayi k'yau sosai, acikin harabar islamiyyar za'ayi, malaman sunyi k'ok'ari gsky dukda abin yazo babu shiri.
Wajen da'aka tanada na musamman dan d'alibai su Rahma suka zauna, iyayen yara dayawa sun halarci wajen, su Abba ma duk sunje, su ya kamal ya muneer ya shaheed, da sauran matasan anguwar da iyayensu, dan Rahma mutuniyar kirkice, tsakaninta da kowa a anguwar sai girmamawa, batada hayaniya wannan yasa takasance mai jama'a kowa yana sonta.
Gurin yayi tsit ana addu'a, shigowar wasu motoci hud'u yaja hankalin mutane kowa soyake yaga suwaye?.
Appa yafara fitowa shida wasu dattijai uku, da alama abokansane, mota ta biyu kuwa matasan family nasune, ta ukuma haka harda ya ishaq da wasu zasukai sa'anninsa, motar k'arshe kuwa, ya Hamza da sulaiman, Lukman da tauheed ne, sai Bobo Wanda yakashe kala cikin manyan kaya, purple d'in shaddace mai haske ajikinsa, rigar iya guywa d'inkin zamani, yayi k'yau sosai harda d'ora bak'ar hula.
Wow! Wasu 'yammata dake gefen Rahma suka fad'a, d'aya tace kai Ruma guy d'incan ya had'u wlhy, dama ya ce, "yana sona?.
Rahma tad'ago dantaga wanene wai suketa kurantawa haka?, gabantane ya fad'i tayi saurin kauda kanta.
Abbane yataso shida abokansa da shuwagabannin makarantar suka tarbi su Appa.
Masauki maik'yau aka basu kamar ansan da zuwansu.
Bayan gaishe2 akaima bak'i barka da zuwa.
Itadai Rahma tunda tamusu kallo d'aya bata sakeba.

Dukda da daddare yaganta hakan bai hanashi ganetaba, babu laifi yarinyar tanada k'yau da nutsuwa, bobo yafad'a azuciyarsa.
Mayun idanunsa yadasa mata batareda ya saniba.
Rahma datakejinta atakure, jikinta yana bata kallonta akeyi, tana d'agowa sukaima juna kallon ido cikin ido, Dan suna fuskantar junane.
Da sauri ta janye nata gabanta na fad'uwa, hular alk'yabbar taja takuma rufe fuskarta.
Samun kansa yayi da sakin lallausan murmushi, ya sauke ajiyar zuciya yana kauda kai daga kallonta.

Addu'a aka fara gabatarwa sannan aka buk'aci Rahma tafito tayi karatu.
Gabantane yafad'i, tatuna d'unbin mutanen dake wajen amma acikinsu akeso tafito tayi karatu?....muryar malaminsu taji yana k'ara nanata sunanta.
Ihsan ta ta6ata Rahma kitashi mana.
Ihsan inajin kunya wlhy.
Kinga saka wannan gilasπŸ‘“ zaki rage jin kunyar.
Siririn farin gilas d'in takar6a tasaka, o ALLAH nafad'a danganin k'yawun da gilas d'in ya k'ara mata.
Ahankali tamik'e tak'araso har inda ake buk'atar ganinta, malam jamilu yabata abin magana.
Tunda tatsaya gaban tebir d'in da aka ajiye alkur'ani mutane ke kallonta, wasukam halittar ALLAH suke yabawa da nutsuwa Rahma.
Appa sai dad'i yakeji Dan yarinyar tashiga ransa.
Gurin yayi tsit danjin zazzAk'ar muryar Rahma tafara fidda sautin karatun alkur'ani mai girma cikin suratul Maryam.
Bobo yalumshe idanunsa danjin muryar Rahma na ratsa ko ina na sassan jikinsa, ALLAH ya albarkaci rayuwarki yafad'a azuciyarsa, ahankali yabud'e idonsa yasauke akan Rahma dake karatu tana hawaye Wanda gilas d'in bai hana agansuba.
Masu hotuna sai k'allata suke, wasu kuma da waya suke mata, harda masu vedio d'inta.
Saida takai har k'arshen surarar sannan taje ta zauna tana cigaba da share hawayenta Wanda narasa namiye?.

Angabatar da nasiha ga amarya da Ango mai ratsa jiki da 6argo, har malam yana tsokanar Rahma da ALLAH yasa wata shekarar su taru haka a sunan baby, dayawan mutanen wajen sunyi dariya dafad'in ameen, (bobo kam murmusawa yayi kawai).
Angabatar da k'yaututtuka ga amarya Rahma, Wanda makaranta suka karramata da yaba k'ok'arinta na hazik'ar d'aliba mai ilimi da girmama manya da rashin karya dokar makaranta.
Abba sai dad'i yakeji.
Cikin abokan Appa dasukazo tare yamik'e shima ya ce, "yayma Rahma k'yautar mota sabuwa dal saboda namijin k'ok'arinta.
(Kabbara akayi da tafi).
Rahma tamik'e tayi godiya, takuma godema iyayenta da malamanta dasuka taka rawar gani arayuwarta, ta ce, ''iyayena sune gatana dasuka tsaya tsayin saka Dan ganin ingantuwar ilimin mu na addini dana zamani, tana kuka tana godiya ga iyayenta abbanta da umminta da yayyaensu da malamanta,....... Kuka mai k'arfi yaci k'arfinta takasa magana sai shashsheka."
Ahankali bobo yamik'e yataka har Inda take, hanky yamik'a mata fari tas daketa tashin kamshin daddad'an turarensa.
Jiki a sanyaye takar6a idonta ak'asa ta ce, " ngd tafad'a cikin shashshekar kuka.
Abin maganar yakar6a daga hannunta, yafara mik'a godiya ga iyayensu da kuma malamai da 'yan uwa da abokan arzik'i dake wajen taron, yahad'a da sakama Rahma albarka da yaba mata.
Kabbara akayi da tafa MASA, abin ya burge mutane gsky, Rahma taji dad'i sosai, dukda tasan ba Sonta yakeba tunda had'asu akayi, amma yay mata wannan karamcin.
Abba da yayuntama sunji dad'i abinda bobo yayi.
Hakama su Ya Hamza bobo yaburgesu, fatansu ALLAH yasa yad'ore haka har gidan aurensu.
'Yammata kam dayawa sun k'yasa saidai sun 6oye kodan Rahma.
Bayan jawabin manyan bak'i da nasihohi taro yatashi lfy, daga nan akayi hotuna kowa yakama gabansa.

Kowa yana zuwa gida yafara shiri a gaggauce Dan ana sakkowa daga masallaci za'a d'aura auren.
Kowa yafito anata shiga mota Dan tafiya sallar juma'a da d'aurin aure.
Masha ALLAH nafad'a yayinda na hango muku ango Bobo yaci kwalliya cikin Sky blue d'in shadda harda babbar riga, wayyo masu karatu bayyana muku k'yan dayayi 6ata lokacine, ammafa ya had'u.
Masallaci suka nufa.
Bayan sakkowa suka wuce anguwar su Rahma.

_Alhmdllh anguwar tacika mak'il da jama'a, wasuma akan mota suke zaune, gurin yacika har babu gurin faking, dukda nisan da su Rahma suke dashi da titi, wasu sai abakin titi sukayi faking motarsu._
K'arfe 3:30pm d'umbin al'ummar Annabi suka shaida d'aurin auren *_"Abdulmalik Aliyu Abdulmalik hamshak'i, da amaryarsa Rahma Bilal Basheer mai Gold. "_*
(To ango da amarya saimuce ALLAH yabada zaman lfy da fahimtar juna ameen).

Dak'ar na iya samo muku Rahma amarya ad'akinsu itada gayyar k'awayenta Wanda yawanci duk yaran family nasune, wasu kuma 'yan islamiyyarsu da boko.
Tahad'u cikin less ja mai adon farin siton masha ALLAHU, amarya tafito ras saidai mak'iyi.
anacewa and'aura auren tafara kuka, su Ihsan suna lallashinta.
(To Rahma sai hak'uri aii).

*_Safna_*
Safna ana gidan su ya kamal, ita adole tayi gudun hijira, ko wanka batayiba bare kwalliya, tana kwance ad'akin Ameera tana chart abinta hankali kwance, fira suke da k'awayenta a group suna tsokanarta wai tamusu bak'inciki, dayanzu sunata shan shagalin biki.
Dariya tayi ta ce, " karku damu aii kwanannan zakusha bikin nida bobona.
Toma ALLAH ya kaimu...
Kafin tabada amsa Zainab autarsu Ameera tashigo tana fad'in an d'aura aunren.
Wata gagarumar fad'uwar gaba tariski safna dake kwance, tadafe k'irji tana fad'in ya salam, saikuma ta sauke ajiyar zuciya takoma takwanta, haka kawai taji jikinta yayi sanyi, zuciyarta tayi k'unci.
Zuwa wani lokaci kuma saitaja tsaki, tomima zai dameni tunda ALLAH ya tsallakar dani daga wannan auren k'addarar.
Rahma ALLAH ya yanka miki kazar wala sai aje aita figa.
Sainazo gayyatarki aurena da Bobo na.....


Na ce, "hummmmm.





*_" kuyi mana afuwa jiya bamuyi posting ba, mai copy d'ince take mura, nikuma nayi busy, amma gashinan yau nadage nayi muku kafin ta warke tacigaba."_*
Luv u oll.
_bilyn Abdul ceβ›ΉπŸ»β€β™€._





*luv u oll my fan's_*
*_(((S))).......2017._*
[11/12, 2:20 PM] mrs bilkisu: πŸ‘©πŸ»β€πŸ’»

❣ *_ABDUL-MALEEK_*❣
_{Bobo}_


_Story & editin_
*_Aunty Bilyn Abdul_*

✍🏿 _Written_
*_Marak'isiyya_*

_hak'in mallaka_
*_Aunty Bilyn Abdul_*

_sadaukarwa_
*_Abba Gana_*
*_Batul mamman_*
*_Bily giro_*



2⃣3⃣&2⃣4⃣

Biki yacigaba da gudana cikin farin ciki da Annashuwa, gidajen biyu anata hada hada.

Bayan kammala d'aurin aure anguna suka shigo cikin gida akayi gaishe gaishe da hotuna, itadai Rahma koda wasa bata yarda sun had'a ido da Bobo ba har aka gama hotuna suka tafi.
Shikam jinsa yake wani iri kuma cikin nishad'i, komai na Rahma yana burgeshi, musamman yanda take komanta cikin sanyi.
Haka suka k'arasa gidasu, nanma cike yake da mata, tunda suka shigo akai caa kan bobo, sai tsokanarsa su aunty Rasheeda sukeyi, baya cewa komai saidai murmushi.

+.+.+.+.+.+.+.+.+.+.+
*_5:30mp_* aka gama shirya amarya domin mik'ata gidan angonta, tana falon Abba inda dangi suka zagayeta anata nasiha gareta, sai rabzar kuka take tamkar zata shid'e, ummi ma kuka takeyi Dan takasa cewa komai yayinda aka kaimata Rahma gabanta dan taimata nasiha, babu abinda take fad'i sai ALLAH yay miki albarka Rahma, yanda kikai mana biyayya kema ALLAH yabaki 'ya'ya masu yimiki, kuka yaci karfin ummi takasa cigaba.
Haka aka hak'ura aka fito da Rahma, Abba dakansa yasakata mota tanata kuka, ya Hamza dazai tuk'a amarya jiyayi tabashi tausayi, shima kamar yay kuka yakeji.
Kuka sosai Rahma takeyi abin tausayi, momyn su Ihsan da Maman Basma suka shiga motar suma, tsakkiya suka saka Rahma daketa kuka har numfashinta na d'aukewa.
Yayinda Abba yaga motocin amarya sun Lula, yatabbatar da gsk yau Rahma ta barsu, sai kawai yaji hawaye sun cika masa ido, yasa gefen rigarsa ya share tareda juyawa gida.
Canma tararwa yayi ummi NATA kuka, yashiga lallashinta damata nasiha.

Gayyar amarya ta isa gidansu Bobo, Dan nan za'a ajiye amarya sai gobe idan ALLAH yakaimu amaida ita gidanta.
Har cikin harabar gidan aka shiga da motar amarya.
Suna fitowa saiga Ammi da gayyar k'awayenta, wasu sosuke kawai suga mace mai sa'a data samu bobo amatsayin miji, Dan sunsha bashi 'yayansu amma ya ce, a'a, (basu San itama had'asu akayiba ba soyayya bace).
Sanye Rahma take cikin shadda ruwan madara zani da Riga, ta lullu6a da k'aton mayafi ruwan k'asa mai turuwa, hakama takalmin k'afarta, kanta arufe yake shiyyasa masu tsogumi basu ganiba, Ammi tarungume Rahma tana lallashi, kama hannunta tayi takai har cikin d'akinta na sama, lallashinta tad'anyi na minti biyu saida taga tad'an tsagaita da kukan sannan tafito aka tura k'awayenta.
Gida ya harmutse Dan cike yake dank'am da jama'a, gashi yau Ammi takeyin yinin biki dama.
Sai bayan magriba dangin amarya suka juya domin zuwa suyi shirin tafiya wajen dinner daza ayi k'arfe 8:30pm to 12:00.
Gidan yad'an rage hayaniya kad'an tunda mutanen sund'an ragu babu laifi.
Duk wannan hidimar da akeyi bobo yana can cikin lambun gidansu da aka k'awata da haske, shikad'aine zaune akan kujera mai lilo idonsa alumshe yana duniyar tunanin rayuwarsa shida marigayiyya Ni'ima.
Yatuna itama haka akaiyi aurensu baya sonta, Dan ko taro d'aya bai halartaba alokacin na shagalin bikinsu, shiyyasa yake mamakin wannan karon komai Appa yace yayi baya musu saiyaje yayi.
(Wata zuciyarsa ta CE sannan ai kana kan hayak'in samartaka ne).
Hakane kuma yafad'a afili.
Bud'ar data cika gidance da k'aruwar hayaniya ta tabbatar MASA da amaryarsa ta iso, yamatse idonsa dake arufe tareda fad'in ALLAH yajik'anki Ni'ima ta, kifahimceni ba laifina baneba, nima sakani akayi dole badan inason aurenba."
Jiyay tamkar maganar Ni'ima acikin kunnanensa tana fad'i masa, _"karka damu mijina Nima zanyi farincikin kasancewar Rahma amatsayin matarka, kodan tarin alkairai dake tartare da ita, na tabbata Nawal tasamu uwa tagari wadda kullum take maka nacin samu, INA tayaku farincikin mallakar Rahma kaida Nawal, ka kwantar da hankalinka kakuma rik'eta amana"._
Shirun dayajine yasakashi mik'ewa zumbur yafara dube dube da mutsike idanu, Kodai mafarki yakeyi?, da gsk fa muryar Ni'ima yaji wlhy.
Jikinsane yafara Rawa, cikin Sauri yabar cikin lambun Dan aganinsa wata aljanace takeson bud'e MASA ido.
Cikin hanzari ya iso harabar gidan inda su ya ishaq suke, Dan bandasu wajen maida 'yan kawo amarya.
Najeeb abokin ya Ishaq ya ce, "ango lfy kuwa naganka a hargitse?, ko duk murnar zuwan amaryarne?.
Saurin saisaita nutsuwarsa yayi ya sauke ajiyar zuciya yanajan farar kukera d'aya ya zauna, babu komai ya Najeeb yafad'a ad'an d'arare.
Wai tun d'azu kana ina?, ya Ishaq ya tambayeshi.
Ina lambu." Yabada amsa atak'aice.
Hira su ya Ishaq sukeyi amma bobo kokad'an baya sakamusu baki, addu'oi kawai yake zabgawa azuciyarsa, fatansa ALLAH yasa abinda yaji ya tsaya iya haka.
Suna nan zaune har aka kira sallar isha'i suka tafi sukayi.

Amarya tanacan ana zabga mata kwalliya, da k'yar aunty Sameera da aunty ummy suka lallasheta tayi shiru aka fara kwalliyar.
Hummm amaryafa tagama had'ewa abin kamar babu gobe.
Shiryata akayi cikin farar doguwar riga ta aure, amma mai dogon hannu, aka nad'a mata d'aurin d'ankwali da bak'in d'an kwali, tasha sark'ar gold wadda k'yautace daga Abba, kai jama'a yaufa take sallah, amma awajen amarya da ango, amaryakam tayi d'am kamar kasaceta ka gudu, na tabbata ko bobo yagani yau saiya narke.
Shimadai ba'a barsa abayaba wajen d'aukar wanka cikin farar shadda harda babbar riga, ya murza bak'ar hula sai kyalli takeyi, sajensa da sumarsa sun kwanta luf luf sai tashin k'amshi yakeyi, cikin hanzari yake d'aura agogon azurfa ahannunsa saboda masifar da ya sulaiman yake masa.
Haba Abdulmalik kai kullum sai anjiraka?, aurenka nefa, kai yakamata ace komai kana gaba amma kaine abaya haba Dan ALLAH."
yi hak'uri nidai ya sulaiman muje nagama aii.
Haka suka fito sai zabga k'amshi yakeyi, yaukam amarya tarigasa, Dan tuni tana mota, bud'e masa Ridwan yayi yashiga inda Rahma take.
K'amshinsu yahad'e Dana mortar ga sanyin AC saiya bada wani yanayi mai dad'in gsk.
Rahma kam lumshe idanunta tayi dataji shigowar Bobo motar, kanta na k'asa Dan bataso su had'a ido ko kad'an.
Shikam saida ya zauna sosai harma sun fita daga gidan sannan yakai kallonsa kan Rahma da k'amshin turarenta ya addabesa.
Tsigar jikinsace ta tashi yarrrrrrr O ALLAH, yafad'a ahankali wandda har Rahma taji furicinsa, wani Abu yaji yana mintsinin zuciyarsa, da k'yar yay control d'in kansa, murya k'asa2 ya ce, yauma aramin fos d'inki.
Bata kalleshiba tamik'a masa bak'ar fos d'in wadda tasha adon fararen duwatsu sai kyalli suke.
Jiki a sanyaye yak'ar6a, yauma kud'i yazuba mata, rafar 'yan d'ari biyar Biyar, sababbi k'al.
Bai bata fos d'inba har suka isa wajen taron, itakuma bata tambayeshiba.
Bayan tsayawarsu Ridwan yabud'e musu suka fito, Rahma tana tsaye har bobo yak'arso wajen, hasken wutar lantarkin daya yalwatu awajen yabashi damar k'are mata kallo sama da k'asa, itadai kanta na k'asa Dan dukta Raina kanta kallon dayake mata.
Murmusawa yayi Dan ganin yanda take sinne kai k'asa, fos d'inta yamik'a mata, tasaka hannu biyu takar6a tareda fad'in ngd.
Baice komaiba yagyara tsayuwarsa suka jera.
A Bokansa da 'yan uwa samari da 'yammata duk suna bayamsu kowanne shida budurwa d'aya, gabansu kuma Nawal ce da Kaleel d'in ya Ishaq, suma anmusu kwalliya cikin kaya kamar su Rahma doguwar Riga Nawal, Kaleel ma kwalliyarsa kamar ta bobo harda malum malum.
Abin ya k'ayatar da jama'a masha ALLHU.
Ahankali taji Bobo yasak'a hannunsa mai azabar laushi da sanyi cikin nata, da sairi ta kalleshi, shima kallonta yayi da sauri danji wani laushi na musamman da hannun nata yakeyi, k'asa ta maida kanta danjin wani yarrrrr ajikinta saboda lallausan murmushi da Bobo yasakar mata.
Tafiya sukeyi ahankali Rahma tana zancen zuci, tunda aka fara bikinnan koda wasa bobo bai ta6a jikintaba sai yau, saikuma jiya data kusa fad'uwa awajen mothars night, wannan kuma takalleshine amatsayin taimako daya bata dankarta fad'i. Dan haka k'irjinta ya hau luguden daka, (zuciyarta ta ce, "yanzu kinzama matarsa sa6aninda daba halalinsa bace ke.)
Kobabu komai ya burgeta, tunda yakasance mumum mai sanin muhimmancim addininsa da bin dokokin ALLAH.
Har suka k'arasa inda aka tanadi kujeru biyu ajere dansu, saida tafara zama haryanzu hannunta na cikin nasa, sakin hannunta yayi ya tattare babbar rigarsa ya zauna shima fuskarsa ad'an sake babu laifi.
Nawal dasuka rakosu tazo kusada shi tatsaya, baby tafad'a ahankali.
Kallonta yayi yamata murmushi tareda kamo hannunta, babyna kinyi k'yau yau, miya faru?, tayi 'Yar dariya bakomai baby amma wacece wannan?.
Juyawa yayi yakalli Rahma da kanta ke ak'asa tana wasa da duwatsun jikin fos d'in ta, yay murmushi.
Zan fad'a miki amma ba yanzuba, kije ga

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login