Showing 102001 words to 105000 words out of 111128 words

Chapter 35 - Abdulmalik Bobo Part 1 Hausa Novel Complete

20 Dec 2024

767

Ammi dake fitowa daga kichin ta ce, "yauwa mukarram kadawo?.
Eh ammi nadawo.
A'a yanaganka da 'Yar leda?, sauran Kayanfa?.
Mik'a mata ledar yayi yana fad'in wlhy naje zan sayo saina tadda ya ishaq awajen yana siya, shiyyasa najuya nasiyo wad'annan kuma.
Ayyo aiban saniba, to ina yayan naku yanzu?.
Acan nabaroshi, amma nasan yana hanyar zuwa shima.
To shikenan ALLAH yakawoshi lfy.
Ameen, Ammi ina Rahma d'in?.
Tana d'aki kwance tana barci, kasan jiya bawani barcin kirki tasamuba, kaima aii yakamata kaje kad'an kwanta kona awa biyu kasamu kayi.
Shafa kansa yayi yana murmushi, wlhy Ammi ni namafa daina jin barcin.
Dariya ammi tayi, lallaikam murnar zuwan kishiya da miji yasa idonka bushewa kenan?.
Dariya sosai bobo yakeyi, ya ce, " ammi aii k'yautar ALLAH daban take, wlhy ko'a mafarki banta6a zaton Rahma zata iya haihuwar yara biyuba yanda nake mata kallon yarinya karama.
Itama ammi dariyar tayi, mukarram aii ikon ALLAH kenan, Ubangiji mai hikimane, amma gsky koni bankawo Rahma tana d'auke da cikin yara biyu bane, ALLAH dai yarayasu akan turbar addinin islama.
Amin ammi, bara nalek'a Rahman kota tashi?.
To, ammafa Indai barci take karka tada ita kaji nagaya maka.
Karki damu ammi, bobo yay maganar yana haurawa sama.

Cikin barci Rahma taji ana shafa kanta, ahankali tamotsa, jin k'amshin turarensa yasakata bud'e idanunta ta sauke akansa.
Murmushi yamata murya a sanyaye ya ce, "my Nusfulhayat kin tashi?.
Kanta tad'an jin jina tana murmushi, yunk'urawa tayi zata tashi yataimaka mata, ta zauna sosai amma tana jingine ajikinsa, Nurulk'albi yaushe kashigo?.
Sumbatar kumatunta yayi idanunsa cikin nata ya ce, " tun d'azun ina zaune ina gadinki aii.
Tofa saikace wata sarauniya?.
Aikinfi sarauniya awajena Rahma, Ubangiji ALLAH yayimiki albarka, tabbas ke Alherice arayuwata, shigowarki Rayuwata kin yalwata alkairi mafi daraja agareni, inason yara sosai Rahma, inaso yara fiye dazaton mai tunani, saigashi tashi d'aya ALLAH ya albarkacemu da samun biyu, Rahma yanzu nine da yara har uku?, kai ALLAH na gode maka godiya Mara adadin kididdiga, lale dake yasanyin idaniyata.
Dad'i da farinciki duksun yalwatu afuskar Rahma, takuma narkewa ajikinsa, ngd my Nurulk'albi, ina rok'on ALLAH ya tsawaita rayuwarmu domin miyita bauta masa da kuma kasancewa tare har abada.
Ameen my cuty na.
Amma Dan ALLAH ina neman wata alfarma agareka.
Gyara zamasa yayi Yakuma jawota sosai ajikinsa ya rungumeta, kitambayi Duk abida kikeso agareni insha ALLAH zanmiki shi inhar bai sa6ama ALLAH ba.
Murmushi tamasa ta ce, "inason asakama macen sunan marigayiya aunty Ni'ima Dan ALLAH kamin wanan alfarmar, idan kamin haka zanyi farinciki sosai.
Tsura mata idanu yayi nawani d'an lokaci, har jikinta yafara sanyi ko bazai aminceba, amma saitaji ya rungumeta tsam yana bata Sumba takowane 6angare ajikinta.
Ammi dake tsaye tun d'azun tana kallonsu ta kauda kai tana murmushi, dama tabiyo bayansane danta tada Rahma tabama yaran nono, Dan sunfara kukan yunwa.
Jin maganar dasukeyi yasa tatsaya bata shigoba Dan batason katsesu saga farincikin dasuka tsinci kayinsu.
Saida bobo yagama bata hot kisses sanan yad'agota yana kallonta, ALLAH yamiki albarka shine abinda yaketa maimaitawa, cikin raunin murya ta ce, " my Zuma kayarda kenan?.
Jinjina mata kai kawai ya iyayi yana murmushi, ahankali ya ce, "Rahma nazama naki, kinrigada kin dabaibaiye komai daya shafi rayuwata, aduk duniya daga iyayena saike acikin jerin Abu mafi Girman muhimmanci a tafiyar rayuwata, sai kuma 'yan uwana wad'anda suka zama jigogi kuma matakan tsaro agareni, 'ya'yana sanyin idaniyata, ALLAH ngd maka daka yalwatani da wad'annan ni'imomi naka badan Nafi sauran bayiba kabank, badan nakasance mafificiba acikinsu, badan wayonaba, badan iyawataba, badan k'arfinaba ka yalwatani ka azurtani ka ni'imtani, ka suturtani, ka ingantani, ka d'aga darajata acikin bayinka, ya ALLAH yanda kamin wanan k'yauta aduniya ka Albarkaceni dasamun mafiyinta alahira....... Hawaye suka zuraro akumatunsa, Rahma tasa hannunta tana share masa.
Yacigaba da fad'in ya ALLAH karka jarabceni da kasancewa acikin masu butulci agareka, ya ALLAH karka jarabceni dagacikin masu sa6onka, ya ALLAH karka jarabceni daga cikin marasa godiya agareka, ya Ubangijin Al'arshi ma'abocin Rahma da gafara, ka gafartamin dukkan kurakuraina nida zuri'ata data musulmai baki d'aya, ya ubangijina kak'ara imani da tsoronka azuciyata, ya ubangijina katsare harshena daga sa6amaka komai ribar hakan agareni, ya Ubangijina ka tsare idanuna daga kallon haramun komai farincikin da hakan zai sakani, ya Ubangijina katsare k'afafuna daga zuwa inda haramun yake komai d'aukakar da hakan zata jamin, ya Ubangijina katsare gangarjikina, zancena, numfashina, furucina, daga afkawa tarkon shaid'an la'ananne nida dukkan zuri'ata data musulmai baki d'aya, ALLAH ka k'arama annabi daraja da fadila da Wasila, ALLAH yasa munacikin al'ummar da zaiyi alfahari damu muda zuri'armu baki d'aya, ALLAH yasa munacikin wad'anda zasu amsa kiran cetonsa awata rana mai cikeda rud'ani da hargitsi, ya ALLAH idan katashi d'aukarranmu kad'auka munacikin imani da tsoronka bacikin shagaltuwa da duniya da abinda ke cikintaba.
Ameeen Rahma tafad'a tana k'ank'amesa hawaye sharkaf da fuskarta saboda addu'ar mijin NATA ta ratsa dukkan sassan jikinta da 6argon jikinta.
Ammi ta share guntun hawayenta itama sannan tamusu sallama.
Da Sauri Rahma ta tashi daga ajikinsa tamatsa gefe kanta asunkuye saboda kunya.
Shima k'asa yayi da kai yana Susa k'eya.
Sunbama ammi dariya amma saita gimtse.
Fuskarta d'auke da murmushi ta ce, "Rahma kintashi?.
Kan Rahma akasa ta ce, " eh ammi natashi tund'azu.
Kodai mukarramne yatadaki?, dannasan halinsa sarai.
Girgiza kai tayi cikeda kunya tana murmushi.
Ammi tayi dariya, to tunda kintashi bara nakawosu ki basu abincinsu tun asuba yara basuci komaiba sai ruwan zam zam da Zuma aketa basu......
fita ammi tayi, bobo ya kalli Rahma baki bud'e, my cute wai kinanufin basuci komaiba yarannan harfa 12 tawuce?.
Shagwa6e fuska tayi Nurulk'albi wlhy ina gama wanka na kwanta saboda barci danakeji sosai.........
Kafin ya ce, "wani Abu Ammi tashigo d'auke da yaran ahannunta.
Bobo ya kar6i macen, saida yasumbaci goshinta sanan yamik'ama Rahma ita.
Cikeda kunyar Ammi ta kar6a Dan ita saima yanzu zata gansu tunda sukazo duniya, jitayi k'aunar yaranta tana ratsa dukkan sassan jikinta, Aranta Ta CE, " ALLAH sarki haka iyayenmu sukeji akanmu, ALLAH ka k'aramana k'aunar iyayenmu dakuma taimaka musu iya iyawa Dan bazamu iya biyansuba.....
Ganin tayi shiru ammi ta ce, "Rahma bata tasha mana.
Ajiyar zuciya Rahma tasauke, idanunta Akan k'yak'yk'yawar jaririyar daketa bud'e baki alamar tana Neman abinci, ga idanu kyar masha ALLAH, (Yaran yanzu haka ake haihuwarsu da wayensu, saidai fatan ALLAH yatsare manasu damu kanmmu).
Tana saka mata abaki yarinyar tafara sha, da sauri tacire tana fad'in wash da zafi.
Daga bobo har Ammi dariya suka saka mata, Ammi ta ce, "haka zaki daure kibasu, daga baya zaki daina jin zafin.
Tasowa bobo yayi yadawo Kusada Rahma, ita kunyama yabata ga Ammi a zaune kan kujerar madubi, bobo ya ce, " kinga kidaure mana, kokin manta wahalar jiya tafi wannan.
K'asa-k'asa yay maganar yanda ammi bazatajiba, ita tunima tad'auke kanta daga Kansu tana kallon baby boy d'inne Wanda take kallo amatsayin tarihi ya maimaita kansa, Dan tamkar bobo yana jariri haka take kallon yaron.
Rahma takuma sakama yarinyar, tana kamawa tacire tana yarfe hannu dafad'in shiiiii wlhy da zafifa.
Tabama bobo dariya amma awannan karon saiya dake, dakansa yasakama yarinyar akaro na uku, Rahma tarik'e hannunsa ga zafi ga kunyar Ammi data lilli6eta, kallon Ammi tayi sannan takalli bobo tamkar zatayi kuka, ammifa na kallonka Dan ALLAH kasaki zan bata da kaina.
Ammi shima ya kalla yana murmushi, to aii bamu Ammin takema kalloba, hankalinta nakan angonta sabo fil.
Dole Rahma tahak'ura har babyn tad'ansha amma sai matse baki takeyi da yarfe hannu harta sha da yawa.
Ammi takatsesu da fad'in to abarta haka shima maigida yasamu yasha.
Sosai kunya ta lilli6e Rahma, Ashe Ammi na kallonsu amma ta sharesu.
Ammi tamik'ama bobo Namijin, itakuma takar6i macen, akafad'a tasakata tana shafa bayanta danson tayi gyatsa.
Shikuma bobo yad'ora ma Rahma beby boy acinyarta, yanzuma haka yasaka masa shima abaki da kansa, Rahma nakukan zafi-zafi, ana cikin haka saisukaji sallama, ammi dake tsaye ta amsa, Safna tashigo cikin 'Yar fara'a, rissinawa tayi yagaida ammi, ammi ta amsa mata cikeda fara'a da tambayarta mai gidan?.
Yana nan lfy Ammi, Ashe ansamu k'aruwa?, ALLAH ya raya.
Ameen Safna, yaukam kunyi 'ya'ya gasunan masha ALLAH, ammi tafad'a tana mik'a mata baby gal dake hannunta.
K'ar6a Safna tayi cikeda sha'awar babyn.
Rahma ta ce, "Anty Safna sannu da zuwa, tana maganar tanad'an yarfa hannunta.
Dariya Safna tayi, ke lfyarki kuwa?..
Zafi wlhy, Dan ALLAH kabarshi haka Nurulk'albi wlhy yak'oshi.
Bobo yad'ago yanama Safna sannu dazuwa, ya ce, " wannan k'anwar taki akwai ragwantaka.
Zama Safna tayi abakin gadon tana dariya, Ammi tafice abinta dama.
Bobo yacirema babyn nono abaki yana dungure kan Rahma, raguwa kawai.
Eh naji babu komai koma miye kufad'a, anjima kuma saiku nemi abinci awajen jaruma.
Dariya bobo yayi ya ce, "koda k'arfin tuwo aii sai anbamu 'yammata.
Rahma ta ce, " shikenan k'arfinku yabaku to.
Kizuba ido mana zaki gani aii.
Safna dai dariya take musu, Dan yanzu Alhmdllh son bobo yaragu sosai azuciyarta saboda k'ok'arin da ya Kamal yakeyi wajen mantar da ita hakan.
Tal'ek'a fuskar baby boy dake hannun bobo, masha ALLAH yaran duk kai suka biyo kaida Nawal.
Cikeda farinciki ya ce, " ko auntynmu?.
Wlhy kuwa, Safna tafad'a tana dariya, ta kalli Rahma dake gefe tana jiyyar kanta, auta next time saiki haifa mana mai kama dake.
Idanu Rahma tazaro Anty safna ban fito daga magagin wannanba amma kike zancen wata, yanzu kam saidai ku.
Kallonta bobo yayi yana dariya, my Nusfulhayat aikema nanda next year nakeason ki k'ara haifo wasu biyun.
Narke fuska tayi tamkar zatayi kuka, Dan ALLAH my Zuma kudainamin fatannan wlhy akwai wahala.
Dariya safna da bobo suka saka mata..........adaidai nan kuma khursiyya da khairiyya suka shigo dagudunsu, rungume Rahma sukayi suna murna, suduka suka haye gadon khairiyya tazauna Kusada bobo tana amsar baby, itama khursiyya na hannun Safna ta amsa, sai dad'i sukeji sunata k'ank'ame yaran.
Khairiyya ta ce, "yaya, su ya Hamza suna kirankafa.
Mik'ewa yayi yana fad'in lah sunzo gidanne?.
Eh yanzu suka shigo suma.
Fita yayi yabarsu sunata hirarsu da dariya.
Safna sai kallon yaran takeyi cikeda sha'awa, dayanzu itace ta haifesu, dayanzu ita bobo yakema wanan tattalin, ya ALLAH kaciremin son bawan ALLAHnnan gaba d'aya, nima namaida hankalina ga mijina kodan tattalina dayakeyi.
Duk a zuciyarta takeyin maganar.

To nimadai na amsata da Ameen, Dan yanzu tausayi take bani.

_bayan kwana uku_
Aka kawo kayan barka, bobo yataka rawar gani, kayan sai sambarka a keyi, Appa da Ammi ma ba'a barsu abayaba suma da nasu, Rahma sai fad'in kayannan sunyi yawa takeyi, jitake k'aunar mijinta da 'yan uwansa nak'ara ratsata.

Haka akaci gaba da kar6ar bak'i yan barka har zuwa ranar suna.
Yara sunci sunansu, Namijin sunan Appa yaci, wato Aliyu haidar, macen kuma Ni'imatullah.
Za'a ringa cemusu Shareeff da Shareefa, to saimuce ALLAH yaraya Aliyu & Ni'imatullah.
'Yan uwan Aunty Ni'ima sunji dad'in wanan karamci daga Rahma, Appa ma sai albarka yake saka mata, hakama sauran dangi.
Suna yak'ayatar alhmdllh abin sai Wanda yagani, naga tarin masu karatu awanan suna masha ALLAH.
kwalliya kam Ranar Rahma tashata, kamar kasaceta ka gudu, awajen yin hotunama bobo sai yabawa yakeyi, shima yaci wankan shadda sai k'yalli da k'yawun haiba kefita agareshi.
K'yaututtuka kam sun samu bila adadin, gadon Ammi damk'am yake da kaya iri-iri.
Zuwa dare taro yatashi mutane kowa yakama gabansa, sai su Ammi kawai, da Rahma bobo Nawal hibba, Appa da 'yan aiki, saikuma shareeff da shareefa.
Bayan Rahma tafito wanka tashirya kanta cikin kayan barci.
Tana zaune ak'asa shayi takesha, yayinda Ammi takeyima Shareeff da shareefa shirin barci, Nawal da heeba suna zaune kan gado sai k'irga kayan jariran da aka samu sukeyi da turame.
Da sallama bobo yashigo d'akin shima sanye yake da kayan barci, zama yayi Kusada ammi yana fad'in Ammi shirin barci kukeyine?.
Shirin barci mukeyi mukarram, suma sun gaji yakamata su kwanta su huta ko.
Gsky ne ammi.
Mik'a masa Shareeff tayi tana cigaba da shirya shareefa, umm my sweet dady, yau kunsha hayaniya ko?........ Nawal ta ce, "papa!.
Na'am Mamana miya faru?.
Kaga kayasu baby's d'inmu dayawa.
Nagani kuwa, kunyi goshi, nawa kuka k'irga?.
Papa bamu gamaba'ai cewar hibba.
To kudage mugani nawa muka samu.
To papa.
Dubansa yamaida ga Rahma, ohni 'yammata dankina shan shayi saikiyita shama mutane k'amshi?.
Murmushi Rahma tayi ta ce, " aibanaso kace zakashane.
Ummyim aina ganoki, Ammi ALLAH nima yunwace takoroni nakasa kwanciyafa.
Dariya Ammi da Rahma sukayi, ammi ta ce, "Ashe da gskyar Rahma datak'i yimaka tayi.
Humm ammi kibarta aii zan rama.
Mik'a masa shareefa tayi, to rik'eta nasamo maka abinci.
Kar6arta yayi yana sumbatar kumatunta, my beauty na.
Rahma takallesu cikeda sha'awa, yanda yaketa wasa da yaransa abin birgewa.
Babu dad'ewa Ammi takawo masa abinci, ta d'auki yaran shikuma yasakko yanacin abincin, heeba da Nawal suka sakko suna murna dafad'a musu adadin kayan.
Sudai su Rahma sai dariya suke musu.
Ammi ta kwantar da yaran ad'an gadonsu sanan tafice wajen Appa.
Rahma takalli bobo daya ture filet d'in abinci, wai harka k'oshine?.
Alhmdllh my Nusfulhayat nak'oshi.
A dama bayunwar dakake fad'a kakejiba.
Haka kikacedai, amma kinsan ALLAH, tun safe damukayi break nidasu ya sulaiman bankuma samun nutsuwar zaman cin abinciba har awajen waleema, Ammar nata fama dani nazauna naci amma nakasa, lokacinma banajin yunwar saboda d'awainiyar mutane, kai my cute mutane sunmana halacci wlhy, yanda kikasan mun Tara taron bikifa, sandasu Ya ishaq sukace za'ayi walema kamar yanda akeyi duk sanda aka haihu canayi kawai abarsa tunda lokacin haihuwar Nawal anyi, Dan gani nake mutane bazasuzoba.
Amma suka dage sai sunyi, wai yanzuma yadace suyi tunda wanan ne karo nafarko da'aka haifa mana twins a family.
Saiga mutane tamkar anbusa k'aho.
Dariya Rahma tayi ta ce, "Zumana aikai mutumin muranene kowa zaiso halartar taronka, gakuma gayyar su ya Hamza.
Hakane my Nusfulhayat, kumafa Appa shima yayi tasa Walemar da safe.
Kai haba?.
Wlhy kuwa my cute.
Tab lallai mungodema ALLAH sosai, ALLAH yasakama mutane da alkairi dansuyi rawar gani, jibifa kayan da'aka Tara mana.
Nagani wlhy, ALLAH yabar zuminci dai.
Amin.
My Nusfulhayat yaushe kuma zamu koma gidanmu?, tunda angama suna.
Wata 'Yar dariya Rahma tayi tana hayewa gado, ta ce, " sai bayan arba'in.
Shima dariyar yayi danbai d'auki maganar tata serious ba, tashiyayi yana fad'in haba yarinya kima canja shawara dai, gaban gadonsu shareeff yaje yamusu kiss sanan yayma Nawal dasuke kwance agado idata hibba, Rahma dai duk tana kallonsa.
Gabanta ya iso ya durk'usa ak'asa yana kallonta, itama kallonsa takeyi, batayi auneba taji bakinsa cikin nata.
Kissing nata yake sosai danba k'adamar kewarta yayiba.
To itama daga gareta hakane, sosai ta taimakeshi suke faranta ran juna, jin tahowar Ammi d'akin yasaka Rahma saurin k'wace kanta, suduka duk maida numfashi sukeyi a wahale.
Ammi tashigo da sallama, kasa bobo yay da kansa Dan bayaso suhad'a ido da ammi, ya tabbata saita gane halin dayake ciki.
Ra6awa yayi tagefenta yafice kansa asunkuye, itadai Ammi ta kalleshi ta kalli Rahma dake kwance akan gado tayi luf ita adole barci takeyi.
Saida yakai gab dazai fita sanan ya ce, "Ammi saida safe.
ALLAH yakaimu Ammi tafad'a tana binsa da kallo harya ida ficewa.
Kallonta ta maida ga Rahma, ta ce, " kidai dage kibiye masa keda kikeda la6u6un jarirai, wannan dalilin yana d'aya daga cikin abinda yasa na maidoki gabana, dannasan halin mukarram ko kad'an bashida hak'uri akan abinda yakeso.
Rahma dai tayi luff kamar ruwa yacinyeta, sai fad'in take a zuciyarta My Zuma kabani kunya yau wayyo ALLAH na.
Ammi ta shige bayi tana cigaba dayima Rahma fad'a................πŸ˜‚








*_Luv you oll._*
*_(((S))).........2017_*
[11/12, 3:00 PM] mrs bilkisu: πŸ‘©πŸ»β€πŸ’»typing........

❣ *_ABDUL-MALEEK_*❣
_β€’πŸ…±πŸ…ΎπŸ…±πŸ…Ύβ€’_


*_NA_*
_*Bilyn Abdul*_

_sadaukarwa_
*_Abba Gana_*
*_Batul mamman_*
*_Billy giro_*


7⃣2⃣

Alhmdllh abubuwa nata tafiya yanda yakamata, su Rahma harsunyi arba'in, yara sunyi 6ul-6ul dasu abin sha'awa da birgewa kamar subani, bak'aramin gyara Ammi takrma Rahma ba awanan zaman wanka, aiko

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login