Showing 39001 words to 42000 words out of 111128 words

Chapter 14 - Abdulmalik Bobo Part 1 Hausa Novel Complete

20 Dec 2024

751

Tatar da ummi tsaye da bak'ar leda ahannu.
Ummi tamik'a mata ledar ga wannan ki kaimata, Safna Dan ALLAH ki kama kanki, kingadai gidan mijin k'anwarkine.
Karki damu ummi, insha ALLAHU babu abinda zai faru wlhy, ainamiki alk'awari zan canja nakoma yanda kikeso.
To ngd ALLAH yayi miki albarka.
Amin ummi na safna tafad'a tana fita.
Hartakai k'ofa saikuma ta waigo, ummi wai miye wannan d'in?, tafad'a tana kallon ledar da ummin tabata.
Karki damu zankirata namata bayani.
Ummi ni baza'a fad'aminba.
A'a lokacinki bai zoba, ai yanzu autana takwace girman, tazama Yaya kinzama k'anwa.
Baki safna tatura tafice, aranta ta ce, "ummi nasan kayan matane aii."

Tana Shiga motarta ta kalli wayarta, hankalinta dukya tashi ganin bai bata amsaba, tunranda takirashi yakashe wayar saita k'yaleshi bata sake kiraba.
Yaudai abin ya dameta shine tatura masa message akan yabata address d'in office d'insa tazo, amma shine har yanzu babu kira babu sak'o.
Ranta duk adagule yake, takirashi sau wajen uku yak'i ya d'aga, hak'ura tayi tatada motar tanufi gidan Rahma.
Dama Dan tanason zuwa wajen bobone ta ce, "ma ummi tanaso yau taje wajen Rahma.
Ummi tayi murna, azatonta Safna tafara hankaline.

β€œAraina na ce, "koya zata kaya?.”

.*.*.*.*.*.*.*.*.*.*.*.*.
Yana zaune a office yaduk'ufa da duba wasu takardu, kallo d'aya zaka masa kagane yana matuk'ar busy, takardun dayake dubawa kuma sunada muhimmanci.
Yana kallon wayarsa tana wringing yay burus da ita, Dan baya k'aunar abinda zai dakatar dashi daga aikin gabansa.
Kwankwasa k'ofar office d'in akayi, sanin sakatariyarsa ce kawai keda wannan damar yasa ya amsa da yes.
Turo k'ofar tayi tashigo, haryanzu bai d'agoba ta had'iye wani yawu tareda tsura masa ido tamkar zata lashesa, sir kayi bak'o.
Waye?, bobo yatanbaya kansa har yanzu yana k'asa.
Cikeda salo ta ce, " bak'on jiyane Alh Sunusi Dala.
Sai yanzu yad'ago, aransa ya ce, "mi mutumin nan yakeso danine, afili kuma ya ce, " kigaya masa bana buk'atar ganinsa, kuma........saikuma yayi shiru ya ce, ''jeki wannan ba aikinki bane.
fita tayi cike da salo.
Batamasan shi tuni yamaida Kansa ga aikinsaba.
Zuwa tayi ta Isar da sak'on oganta ga Alh sunusi, maganar tak'ara Sosa masa rai, amma tunda bobo yak'i bashi had'inkai to lokaci yayi dazai d'auki matakin k'arshe akansa.
Fuuuu yabar wajen, masu gadinsa suka take masa baya.

β€œna ce, "humm kowane mataki kuma Alh sunusi ke shirin d'auka akan bobo?.πŸ€”β€

+++
Da sauri yad'ago danjin anta6ashi, danufin yin bala'i yad'ago azatonsa Alh sunusi ne yanunama sakatariyarsa fin k'arfi yashigo, ganin Ammar ne saiya sauke ajiyar zuciya tareda yin murmushi.
Ammar ya ce, " mutumina irin wannan fusata haka?, tamkar zaka bigeni.
Ajiyar zuciya Bobo ya sauke kayi hak'uri wlhy nazata wannan shashashanne Alh Sunusi.
Murmushi Ammar yayi ya ce, "munzo shigowa naga fitarsa Ashe na shaida motocin nasa kuwa.
Baki bobo yata6e batareda yayi maganaba.
Saican yace halan yauma kazo kacikamin bakin office da yaranka?.
Hhhhhhh kaima Kasan dolene Dan babu yanda za'ayi subarni nafito ni kad'ai.
Bobo Yakuma ta6e baki, Sakai awahala kenan, haka kawai ace duk Inda mutum zayi ana binsa tamkar wata jela?.
Girman kenan my guy Ammar yafad'a yana dariya.
Ammar ya ce, "mutumina kafa rame wlhy mike damunka?.
Bobo yafitar da huci mai zafi, babu komai Ammar.
To shikenan tunda babu komai yafad'a yana mik'ewa.
Da sauri Bobo yaruk'oshi Dan yasan haushi yaji, yi hak'uri abokina zauna muyi magana.
Ammar yadawo yazauna, wlhy Abdulmaleek kana bani mamaki yanda kake iya 6oyrmin wasu al'amura naka awasu lokutan.
Bobo ya ce, " kayi hak'uri Ammar bawai ina 6oye maka wani Abu baneba, saidai ina ganin wannan sirrin gidanane, dukda nasan babu abunda zan iya 6oye maka arayuwata, kai kad'aine abokina Dana yarda dashi, nasan kaima hakane.
Hakane Bobo amma Dan ALLAH miyasa kake 6oyemin abinda ke damunka?, ina kula dakai tunda nadawo kana cikin damuwar datafi tada akan Rasuwar marigayiya Ni'ima.
Sabodafa damuwar dakake ciki su Appa suka yanke shawarar yimaka Aure, to amma maimakon asamu sauk'i sai kuma damuwarka ta k'aru.
Minene damuwarka Abdulmaleek?, kasanar dani mu nemo mafita.
Bobo yataso daga kwanciyar dayayi ajikin kujera, yadafe tebir d'in gabansa da hannu bibbiyu.
Wato Ammar da ina cikin kewar matatane Dana rasa, dakuma tausayin Nawal na rashin uwa, wannan yasa nak'iyin aure dukda dama Kasan matan bawai suna agabana bane, su Appa sun takura nayi aure harda kai aciki, amma na ce, "muku har yanzu ban shiryaba, an auramin Rahmane saboda bijirewar yayarta akan aurena.
Tundaga randa aka kawo yarinyar gidana ban k'ara yarda ta ganniba saida na d'akko Nawal..
" amma kasan wani abin mamaki?."
Ammar ya girgiza kai.
Koda muka shigo gidan saitamana tarba ta mutunci, ko kad'an bata nuna fushinta akan rashin zuwana garetaba.
Wannan itace jarabawa ta farko data cinye, saikuma yanda take kula da Nawal, wlhy idan baka saniba bazakace ba ita ta haifetaba, abu na uku tsafta, iya girki, saidai akwai shegen muskilanci atareda yarinyar wlhy.

Ammar ya tuntsure da dariya, to aii indai miskilancine babu matsala tunda kaima halinkane.
Harara Bobo ya galla masa malam aii wannan ta fini.
Bobo acigaba da bandamuba kafin ayi auren, amma yanzu ganinta agidan saina shiga wani hali, Dan gsky ina buk'atar mace.
Ammar yagyara zama, to aii ni banga abin damuwa ananba, ba matarka bace?, kawai kanemeta mana.
Ammar baka fahimceni bane, haryanzufa yarinyar k'aramar yarinyace, bata wuce 17 ba, banafa ta kammala secondary, kosu khursiyya sun girmeta da shekara d'aya.
Murmushi Ammar yayi, karka damu abokina aii yaranma sunfi bada Nutsuwa ka gwada kagani kuma.
Amma Dan ALLAH karagema kanka damuwa.
To aiini bakasan wani abuba, tayayama zan tunkareta na nuna mata ga abinda nakeso?, kasanfa banason raini wlhy.
Dariya Ammar yayi ya ce, "Abdulmaleek Aliyu Abdulmaleek hamshak'i, wlhy AAA kana bani dariya, lokuta da dama nakan rasa kai wane irin mutumne?, wlhy da aikin Soja ka dace ba lauyaba, kaifa wani irin murd'ad'd'en mutumne, towai sanda kake gwadama Margayiya Ni'ima soyayaya kirana kayi na koya makane?.
Ajiyar zuciya Bobo ya sauke, bazaka ganebane kawai kadai.
To ganar dani cewar Ammar yana kallon Bobo.
Komawa yayi yalafe jikin kujerar yanad'a lilata ahankali, Ammar ya ce, " my guy kafito kawai anamijinka kaji, kakula da matarka na tabbata Rahma Alherice arayuwarka, kaga kuwa yanda ka canja kak'ara fari, so ka kwantar da hankalinka kayi k'ibama, Rahma k'yak'yk'yawar yarinyace nitsatstsiya ga ilimin addini, wlhy randa na kalli vedio d'in bikinku jinayi inama ina wajen, bak'aramin birgeni tayiba awajen walimarnan.
d'an iska awajen biki kanata tattalin yarinya amma yanzu kazo kana mata muzurai.
Murmushi bobo yayi ya ce, ''kankadai akeji.
Kaima za'aji nakane, amma saikaje hanun Rahma, mik'ewa yayi yana dariya kaga bara nawuce sumayya nacan na jirana harkaja na wuce lokaci.
Bobo daketa murmushi tun d'azun ya harareshi iskanci zakamin kenan?..
A'a babu wani iskanci gsky dai.
Bobo ma ya mik'ewa yayi, nima tafiyar zanyi zanje na d'auki Nawal a school, yau direbanta babu lafiya.
Ayya ALLAH yabashi lfy.
Amin.

Tare suka fito, kowa yashiga motarsa, Ammar da tawagan 'yan sandansa suka tafi, shima Bobo yanufi school d'in su Nawal ya d'auketa sai gida.


.*.*.*.*.*.*.*.*.*.*.*.*.
Sun shigo gidan falo babu kowa, sai k'amshi da k'arar AC ke tashi, saikuma TV dake kunne amma babu k'ara sosai.
Nawal ta ce, "papa momy na d'aki zomuje, tarik'e masa hannu.
Rahma tana tsaye jikin wardrobe tana d'aukar kaya suka shigo, batayi zaton taredashi sukeba, Cikin farin ciki tad'auki Nawal tana juyi da ita suna dariya, babyn papa da momy ya School.
Momyn lfy.
Masha ALLAH my lovely daughter, muje namiki wanka to kiji dad'i.
"K indai kina tareda Nawal baki ganin kowa sai ita?.
Da sauri ta kalli gurin da maganar take fita, Dan batayi tunanin suna tareba.
Kayi hak'uri basan tare kukeba aii sannu dazuwa, sai matse jikinta takeyi Dan daga ita sai tawul.
Baice komaiba yajuya yafita, amma ya rikice daganin surar Rahma, dukda k'aramar yarinyace amma tanada sura mai k'yawun gani, yanaso yak'ara ganin ainahin Rahma d'in.
Da wannan tunanin yak'arasa d'akinsa, kaya yacire yashiga wanka.


β˜…β˜…β˜…
Bayan wasu 'yan lokuta kowa ya kammala abinda yakeyi, suka had'u afalo sukaci abinci, itadai Rahma kanta ak'asa.
Yakula tunranda yay mata abinnan bata sakewa dashi, kuma bataso su had'a ido, tak'ara birgeshi da samun matsayi a zuciyarsa Dan yana k'aunar mace mai kunya

_(kunya tana d'aya daga cikin tarbiyya ga mace, amma 'yammatanmu na yanzu sun 6arar, aganinsu rashin kunya itace wayewa, gsky anama wayewa bahaguwar fahimta, yakamata mugyara, kunya tana d'aya daga cikin alamomin imanima wlhy, ALLAH yasa mugane.)_

Duk suna falo zaune, Rahma da Nawal suna game da aka had'a da TV, shikam boss yana karanta jarida.

Safna tayi hon maigadi yalek'a danyaga wanene, ganin bak'uwar motace yasa yaytsaye batarda ya bud'eba, cikin haushi Safna talek'o tana masa magana cikeda masifa, aii babu shiri yabud'e mata gate d'in tashiga, guri tasamu tai farking sannan tafito, sai harar mai gadin takeyi, sanye take cikin jan less Riga da siiket sun kamata sosai amma sunyi mata k'yau, ta d'ora siririn farin gyalenta a kafad'a, takalmi da handbag d'inta duk farare, tad'auki sak'on Rahma tanufi k'ofar datake zaton itace zata sadaka da gidan.
Sallama tayi tareda kwankwasa kofar.
Rahma tamik'e da sauri lah kamar muryar aunty Safna nakeji.
Da sauri Bobo yad'ago kai yana kallonta danjin ta ambaci Safna.
K'ofa Rahma tanufa, shikuma ya ta6e baki yaudai zaiga yarinyar datace bata sonsa...........



πŸ’ƒπŸ» _ayye mata kuk'ame k'am sabuwar rawa, nidai bansan maganarba, bansan zafin ata6anba, nidai nace Ku k'ame k'am kusami natsuwa_πŸ€£πŸ€”???????…


πŸ€ΈπŸΌβ€β™‚πŸ€ΈπŸΌβ€β™‚πŸ€ΈπŸΌβ€β™‚πŸ€ΈπŸΌβ€β™‚πŸ€ΈπŸΌβ€β™‚πŸ€ΈπŸΌβ€β™‚πŸ€ΎπŸΏβ€β™€goooooooooπŸ˜‚πŸ˜œ






*_luv u oll my fan's_*
*_(((S))).........2017_*
[11/12, 2:55 PM] mrs bilkisu: πŸ‘©πŸ»β€πŸ’»typing........

❣ *_ABDUL-MALEEK_*❣
_β€’{BoBo}β€’_


*_NA_*
_*Bilyn Abdul*_

_sadaukarwa_
*_Abba Gana_*
*_Batul mamman_*
*_Billy giro_*


4⃣5⃣

Rahma tarungume Safna cikeda farinciki, itama rungumeta tayi Dan tayi kewar 'Yar k'anwarta abokiyar fad'anta, I miss you my lovely aunty.
Miss u too my lili na.
Safna tad'agota daga jikinta tana fad'in 'Yar lukutar ummi kinfa k'ara lukucewa, mi angon naki yake baki haka?.
Rahma tarufe fuskarta saboda jin kunya, kai aunty Dan ALLAH ki bari.
To na bari Safna tafad'a tana kama hannunta sukai cikin falon.
Rahma ta kalli mazaunin Bobo wayam, Nawal ta kalla data maida hankalin akan game, baby ina papa?.
Nawal tad'ago tana dariya, yashiga d'akinsa momy..... Tsayawa tayi tana kallon Safna, saikuma ta kalli Rahma, momy wacece wannan?.
Aunty ce babyna.
Nawal ta taso ta rungume Safna, oyoyo aunty na.
Itama safna rungumeta tayi tana fad'in oyoyo babyn mom.
Bayan sun zauna Safna sai bin Nawal da kallo takeyi, gani take kamar tasan yarinyar.
Rahma tadire tiren kayan motsa baki agaban safna, tana fad'in wlhy aunty banyi zaton ganinkibafa.
'Yar dariya safna tayi ta ce, ''saikuma gani kin ganni.
Zama tayi sukafara hira, kamar basu bane sukeshan fad'a ada.
Sun shagala sosai akan firar idon Safna ya sauka akan hoton Bobo, wani k'ululu cikinta yabada, batagama dawowa daidaiba Bobo yafito daga d'akinsa.
Ah bak'uwa mukayi agidan??.

Afirgice safna tad'ago tana kallonsa, fad'uwar gaba, bugun zuciya, murd'awar ciki, duk suka k'ara samunta alokaci guda, yanda take raba ido akan Bobo sai kawai ya d'aure fuska.
Itama Rahma kallonta takeyi ita atunaninta Safna taji kunyane akan abinda ta aikata abaya.
Safna taduk'e k'anta bisa cinyarta danjin falon yana juya mata, jikinta sai rawa yakeyi, lallai ta tabbata kuka rahamane tunda gashi ita yau takasayinsa.
Bobo yana zaune saman kujera yad'ora k'afa d'aya kan d'aya, dagashi har Rahma idanunsu nakan Safna, Nawal ma tana mak'ale abayan Rahma tana lek'en Safna, bobo yakalli Rahma, dama tanada wani ciwone?.
Kai Rahma ta girgiza masa ta CE, ''amma dai ban saniba ko bayan nabar gidan.
Lumshe idanunsa yayi ya ce, "bata ruwa tasha, Rahma ta tsiyayama Safna ruwa a Kofi tabata, jikin Safna na Rawa takar6a ta shanye duka tamik'ama Rahma kofin, k'ara mata bobo yasake fad'a.
K'ara mata takumayi, aii ko ta shanyeshi tas.
Rahma takalli Safna kamar zatayi kuka, aunty ki kwanta kihuta, kiringa fad'in _innalillahi wa'inna ilaihirraji'un_ zaki samu nutsuwa insha ALLAHU.
BABU musu Safna tabi shawarar Rahma ta kwanta, dukda ayanzu jitake babu Wanda tatsana aduniya sama da Rahma d'in, jitake tamkar tatashi ta shak'eta ta mutu, talumshe idanu tana ambatar innalillahi..... Danjin zuciyarta tana shirin fashewa.

Bobo dai tuni yad'auke kai daga kallon Safna, ya maida hankalinsa ga TV.
Bayan kamar minti15 Safna tad'anji Nutsuwa tazo mata, tabud'e ido tareda tashi.
Rahma tai saurin fad'in aunty Yaya jikin?.
Murmushi Safna tayi Wanda yafi kuka ciwo, da sauk'i kuyi hak'uri na rud'aku, juwace nakeji dama tun ina hanya.
Sannu Rahma tashiga jero mata, Dan ita tayarda da zancen na Safna 100%.
Bobo kam azuciyarsa ya ce, " juwar kuma bata tashiba saida kika ganni?, shifa Sam bai yarda da maganartaba, Dan haka yacigaba da kallonsa batareda yak'ara kallon ko inda sukeba.
Safna kam tafad'i hakane saboda tunowa da maganar malaminta, dayace kota had'uda bobo karta nuna masa komai harsaitaje wajensa yabata wani sirri, da wannan tunanin tad'anji sanyi aranta, shiyyasa ta tashi ta zabga wannan k'aryar.
Takai kallonta ga bobo daya maida hankali kan latsa wayarsa, muryarta na rawa ta ce, "ina yini.
Lfy, kawai ya ce, " yamaida Kansa ga waya.

Falon yay shiru nawasu 'yan mintuna, safna dai satar kallon Bobo takeyi, sai yanzu yak'ara tabbatarwa da k'yak'yk'yawane ajin farko, Ashe ranar kallon tsoro sukayi masa, lallai ALLAH yayi halitta awajennan masha ALLAH, sai sambatun k'yawun bobo takeyi ita kad'ai zuciyarta.
Rahma kam tayi shiru tana tunanin halin da safna tashiga yanzun nan, kome ke damun 'Yar uwar tata?.
Bobo yamik'e Dan ganin kallon k'urillar da safna take masa, yakalli Rahma bara nad'an kwanta kafin sallar la'asar, kitadani idan lokaci yayi.
To. Rahman tafad'a kanta ak'asa.
Shikuma yanufi d'akinsa, harya shige safna tanabinsa da kallo.

Nawal ma tamik'e momy zanje wajen papa.
A'a Nawal kibar papa ya huta kinga ya ce, "barci zaiyi, Nawal ta kwa6e fuska tana shirin yin kuka, momy nimafa barcin zanyi.
Tokije d'akinmu ki kwanta, kamar gsk tanufi d'akin Rahma, dataga basa kallonta saita gudu d'akira, papan ta.
Safna ta ce, " wannan yarinyarfa ina kuma samota?.
d'an murmushi Rahma tayi, aunty yarinyarsa ce wadda matarsa tarasu tabari.
Baki safna ta ta6e shine kekuma aka jajibo aka kawomiki?, kedai sakaraice wlhy, kina 'Yar yarinyarki har anfara kiranki da suna momy mtsoooow, nibansan randa kanji zai wayeba wlhy, danice agidannan wlhy saidai yasan Inda zaikai 'yarsa.
Itadai Rahma batace komaiba, saima wasa da zoben hannunta datakeyi, amma har zuciyarta bataji dad'in maganar 'Yar uwartaba, aganinta aii d'a na kowane, kuma shida gidansa tahanashi ajiye Wanda yakeso?, itafa har zuciyarta tana k'aunar Nawal, kuma yanda zata rik'e 'ya'yan cikinta haka zata rik'e Nawal.

Yana zaune abakin gado yana danna laptop Nawal tashigo.
Lah papa bakayi barciba?.
Bobo yad'ago yana kallon d'iyar tasa, banyi barciba babyna ya akayi?.
Na cema momy zanzo wajenka, shine ta ce, " a'a wai nabarka kagaji zakayi barci naje d'akinmmu na kwanta.
To miyasa bakije kin kwantaba?.
Ai bata ganniba nikuma na gudo nan, ammafa karka gaya mata.
Murmushi yayi Dan ganin yanda Nawal tazaro idanu saikace wata babba, to shikenan bazan fad'aba yanzu ya za'ayi?.
Ta ce, "papa barci zanyi.
To zoki kwanta, kan gadon tahawo ta kwanta, kwantar da kanta tayi kan k'afarsa daya tankwanshe, tana kallon rubutun dayakeyi a laptop suna labari, dahaka barci ya d'auketa, yagyara mata kwanciya dankar wuyanta yay sanyi.

Afalo kam safna da Rahma suna hira, dukda safna dauriya kawai takeyi, Dan zuciyarta na cikeda tsanar Rahma, dakuma haushin tashin bobo Afalon, Dan bata gaji da ganinsaba.
Tamik'a mata sak'on ummi gashi inji ummi.
Rahma takar6a ta na dubawa, miye kuma ummina tabani?, safna ta ta6e Baki ta ce, " zata kiraki tamiki bayani, kinga bari nawuce, safna tafad'a tana mik'ewa.
Kai auntuna tun yanzu?, Rahma tai maganar tamkar zatayi kuka.
Kenifa banason iyayi, dama kika samu Nazo shine zakimin Ta6ara.
Sanin halinta yasa Rahma tai saurin fad'in yi hak'uri aunty Safna wlhy nayi kewarkune sosai.

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login