Showing 99001 words to 102000 words out of 111128 words

Chapter 34 - Abdulmalik Bobo Part 1 Hausa Novel Complete

20 Dec 2024

763

ya rufe laptop d'in yad'auki Rahma zuwa d'akinsa, saida ya ajiyeta sannan yakoma d'akinta yad'akko mata kayan barci yakwashi tarkacensa yakoma.
Kayan barcin ya canja mata shima yasaka nasa sannan ya haye gadon, mugunta irinta bobo bai k'yaletaba saida ya tada ita ya raya sunna sananan.......😎.

______________________
Biki yayi biki, yau aka gudanar da kamu daya k'ayatar aharabar gidansu Safna, anhad'eshi gaba d'aya itada Ameera, komai ya k'ayatar damutane, zuwa gab da magriba aka tashi.
Daga nan ancigaba da gudanar dabiki su Rahma amarori k'irjin biki danma ciki namata cikas bata iya komai yanda yakamata.

Ahaka aka wayi gari yau asabar safiyar d'aurin aure, Kujiba-kujiba su Rahma aketa sha Dan annan takwana, dak'yar bobo ya yarda ta kwana saida Ammi ma tasaka baki sannan, aiko gidan Ammi ya kwana wai bazai kwana gidansu shi kad'aiba kewa ta isheshi, dariya Rahma taitayi masa shikuma yana hararta.

*_2:30pm_* dai-dai aka d'aura auren Safna bilal Basheer mai Gold & Kamal Abubakar Basheer, sai kuma Ameera Abubakar Basheer & Hafeez Lukman sa'eed.
d'aurin aurene daya Tara d'unbin al'ummar Annabi, Appa dasu ya Hamza ya ishaq ya sulaiman bobo Ammar Musaddiq idris duksun halarci taron d'aurin auren.

To saimuce ALLAH yasanya alkairi safna da Ameera da ya Kamal da hafeez, duk ALLAH yabaku juriyar zaman ibada da hak'uri Wanda akasan ma'aurata dashi.πŸ€“

Bayan gama d'aurin aure su bobo abokan ango suka shigo tareda anguna domin d'aukar hotuna, bak'aramin tashin hankali Safna tashigaba da ganin bobo, jitake tamkar tad'ora hannu aka tarushe da ihu amma babu dama, sai satar kallonsa takeyi, shima yana kula dahakan shiyyasa yakoma can gefe nesa da inda take tsaye da k'awayenta.
Cikin ikon ALLAH ma saiga Rahma ta fito daga falon itadasu aunty ummy matansu ya Sulaiman, k'arsowa sukayi wajen suna gaisawa da angunan, Bobo yakamo hannun Rahma yana fad'in woow my Nusfulhayat kinyi k'yau, nakuma gode miki dakika saka gyale bakifito harabar gidanan hakaba.
Murmushi tamasa ta ce, "Murulk'albi na nasanka da kishi Dan haka zanyi k'ok'arin toshe duk wata hanyar da kishinka zai motsa.
Lumshe idanunsa yayi yana murmushi jin dad'in furucinta, zungurarsa ya Kamal yayi kai malam agabanfa jama'a kuke.
Dariya bobo yayi ya ce, "d'ansa ido miya kawo idonka kammu?, kabar amaryarka can kataho nan neman gulma, halan Ammar ne ya cinnoka Dan nasan yashahara sosai awannan 6angaren.
Ammar dake jinsu ya ce, " indai har na shahara tokuwa kai ka gawurta fitsararre.
Duka bobo yakai masa, Ammar yakauce yana fad'in abin kunya bobo agidan surukai saika nuna hali?.
Rahma dake dariya ta ce, "Nurulk'albi kabar Yaya Ammar zamu ramane.
Hakane my Nusfulhayat saiyazo gidanmu zamu tararmasa.
Dariya sosai ake musu, 'yammata dayawa sun k'yasa matasan samarin k'yawawa masu wadataccen ilimin addini Dana boko.
Dayawan 'yammatan wad'anda suka San labarin bobo abakin safna sukan tayata jimamin rasasa Dan babu k'arya guy d'in yahad'u tako ina, hotuna akayi kowa sotake taga tafito kusada bobo amma Rahma takasa ta tsare tana manne dashi ako ina ko 'Yar kunyar nan tata yau ta tureta gefe gudun kar wad'annan manyan 'yammatan dasuka FItA wayewar boko Suyi mata suruf bahana da Nurulk'albi d'inta.
Bak'aramin kishine ya turnuk'e safna ba, amma haka ta daure tadake akayi hotunan aka gama su bobo suka tafi.
Shagalin biki yacigaba da gudana acikin gida........... .











*_luv you oll_*
*_(((S)))........2017_*
[11/12, 2:59 PM] mrs bilkisu: πŸ‘©πŸ»β€πŸ’»typing........

❣ *_ABDUL-MALEEK_*❣
_β€’πŸ…±πŸ…ΎπŸ…±πŸ…Ύβ€’_


*_NA_*
_*Bilyn Abdul*_

_sadaukarwa_
*_Abba Gana_*
*_Batul mamman_*
*_Billy giro_*


7⃣0⃣

Zuwa dare aka halarci dinner faty daya tara d'unbin al'umma, ita Ameera ankaita gidan mijinta tund'azu, dagacanma suka taho dinner d'in, safna kam sai zuwa gobe idan ALLAH ya kaimu tunda angon d'an gidane.
Amare da angwaye kam sunsha k'yau matsa ALLAH, fuskokinsu duk cike suke da annuri da akasan amare da anguna nayi aranar bikinsu, balaifi awannan karonma safna tad'an saki jikinta.
Sai hange-hange da lek'e-lek'e nakeyi amma ban hangomuku Rahma da bobo ba saboda cikar da wajen yayi.
Sai awajen lik'i ALLAH yabani nasarar sauke idanuna kan Rahma da bobo dasuketa zubama su Safna lik'i, Rahma taci ado cikin less yellow riga da zani buba kamar d'inkin yarabawa, ta nad'e kanta da blue d'in d'ankwali sark'arta 'yan kunnenta dakomai blue ne, bobon tama sanye yake da shadda blue sai maik'o da d'aukar ido takeyi, shikam komai ajikinsa blue ne, sai kamshi suke zabgawa tamkar sune amarya da angon.
Tunda suka fara musu lik'in idanun safna da Kamal akansu kowa da abinda yake tunani, sukam sai zabga murmushi sukeyi hankalinsu kwance, ganin kud'in dasuke zazzagarwa mawak'i yafara wasasu tamkar sukad'aine a hall d'in taron.
Safna dai data kasa daurewa saida tayi kuka, kular da bobo yayi yasashi kama hannun Rahma sukabar wajen.
Inda sukeda suka koma suka zauna, awajen bada cake ma safna saida suka had'a ido da bobo, murmushi yamata kawai yana masu tafi, murmushi nasa ya sanyaya zuciyarta Dan haka itama tayi.

Araina na ce, "safna kinada aiki wlhy, yakamata kihak'ura hakanan.πŸ€“

Rahma tanarke ajikin bobo tana yatsine fuska, tallafota yayi sosai zuwa jikinsa ya ce, " my Nusfulhayat ya dai?.
Shagwa6e fuska tayi, Nurulk'albi barci nakeji.
Idanunsa yad'anzaro waje, barci kuma?, bafa agama ba.
Takuma yatsine fuska nidai wlhy nagaji hayaniyarnan tama isheni.
Kingani ko, saidafa nace kiyi zamanki karkizo kikak'i, to gashinan tun ba'aje ko'inaba harkin gaji.
Tab, nazauna agida wata ta manne maka, inacan nikuma sagaga da baki.
Dariya tabashi amma saiya gimtse, yay nufin zolayarta, my cute nifa mijin mata hud'une, kumafa inada sha'awar k'ara aure.
Zame jikinta tayi daga nasa, amamakinsa saiyaga tamik'e zata bar wajen, da sauri yaruk'o hannunta yana fad'in sorry my hayatee wasa nakeyifa, dagake aii babu k'ari, dukda haka bata saurareshiba, su ya hamza dake kusadasu kowane da matarsa suka shiga musu dariya, Ammar ya ce, "karki yarda Rahma dad'in bakine kawai yanada budurwa.
Hararsa bobo yayi ya ce, ''tod'an had'i kuma tunzurata.......
Baijira cewar ammar ba yabi bayan Rahma da sauri Dan har takama hanyar barin hall d'in.
Su ya ishaq da mamansu sai dariya suke musu.
Da Anty yahanasu sukaci karo itama zata fita, a'a Rahma lfy ina zakije haka da sauri?.
Saurin saisaita kanta tayi, Anty wlhy nagaji barci nakeji.
Aidama rigimar kice tasa kikazo, mujeto nima gidan zani nagaji......
Dai-dainan bobo yak'araso yarissina yagaida aunty yaha, Anty yaha ta ce, "ko tare zaku tafine?.
d'an Sosa kansa yayi yana murmushi.
Dariya aunty yaha tayi tareda fad'in kaga koma kayi zamanka saimuwuce tare tunda nima gidan zani.
To shikenan Anty saida safe.
Har waje yarakasu, har suka tafi Rahma bata yarda sun had'a ido da bobo ba.
Dariya yayi bayan tafiyarsu ya ce, " humm my Nusfulhayat kishinki na burgeni da k'ara tsundumani a lodin k'aunarki.
Juyowa yayi zai koma, daidai zai Shiga sukayi karo dawata k'yak'yk'yawar budurwa, suduka kowa jadabaya yayi, sorry my guy, yarinyar tafad'a cikeda yanga.
d'aure fuskarsa yayi baice komaiba yara6a ta gefenta zai wuce.
Da sauri tasha gabansa tana fad'in pls jimana.
Tsayawa yayi yana kallonta saidai fuskarsa babu alamar yasan miye dariya, tamkar bashine yagama dariyaba yanzu.
Tagyara tsayuwarta tana wani far da idanu, ni sunana Anisa Ahmad Sa'eed, so atak'aice ana cemin neesa, k'anwace ga angon y Hafeez.
Wlhy tunjiya awajen launch kaketa birgeni bansamu damar maka magana bane sai yanzu, pls ina fata zaka kar6i tayina?, tayi maganar tana tsura masa ido da langa6ar da kanta gefe.
Yamutse fuska yayi yana mata wani kallon rainin wayo, baice da ita k'alaba yara6a tagefenta yawuce.
Binsa tayi da kallo tamkar zata FASA kuka dan bak'inciki, Dama saida Anty laura ta ce, "kartazo Dan daga ganinsa zaiyi Girman kai, kuma taga kamar yanada mata, amma tak'i azatonta kodan k'yawun da ALLAH yay mata dolene bobo ya saurareta saigashi ya bud'a mata k'asa a ido.
Jiki asanyaye takoma cikin hall d'in, amamakinta saita hangoshi yana dariya shidasu ammar, shagala tayi sosai tana kallonsa da addu'ar ALLAH ya mallaka mata bobo amatsayin miji.

" Araina na ce, "humm."

Dahakadai taro yatashi, ango Hafeez yad'auki amaryarsa Ameera suka tafi, shima ya kamal yad'akko safna sukayo gida, su bobo da sauran jama'a kowa yay gida.
Sanda suka iso tuni Rahma tayi barci a falon Abba dama a can takwana jiya.

Washe gari aka kai safna d'akinta itama bayan anyi walima.
Masha ALLAH gidan yayi k'yau, su ummi sunmata gata irina iyayen kwarai, kowa ya yaba kam saidai mak'iyi.
Tom daganan taro yatashi kowa Yakama gabansa, Raham ma bobo yazo ya d'auketa sukai gida abinsu.


_____________________
Haka rayuwa tacigaba da tafiya, Rahma anata rainon ciki, suma su khairiyya da khursiyya an gamu, Dan jiya agidansu Rahma da Nawal suka wuni, sunjajje musu yawo, aiko bak'aramin farinciki sukayi da hakanba, suntarbi su Rahma tamkar su goyasu, ansha hira zuwa dare bobo yaje yad'akkosu.

Su safna amare anata shan amarci, sosai ya Kamal yake k'ok'ari wajen mantar da Ita bobo, rayuwa sukeyi mai dad'i, itama kuma tanata k'ok'arin faranta MASA dukda har yanzu idan son bobon yamotsa takansha kukanta a6oye, amma tana iya bakin k'ok'arinta danganin tacireshi azuciyarta.
Ameerama dai ba'a barsu abayaba sunata shan soyaya itada hafeez d'inta.

Sai masu gayya da aiki bobo da Rahmarsa soyayace tsantsa ake zubawa agidan cikeda kulawa da tarairayar juna, yanzukam sai abinda yay gaba wajen kulawar da bobo yake bata musammam da cikinta yashiga wata Tara na haihuwa, datace wash, zaice miya faru?, wani lokacin har tsokanarshi takeyi saita langa6e tana zuba shagwa6a, dataga yarud'e saita saka MASA dariya, yakace haba yarinya zan ramane baridai ki haihu.

Awannan tsakaninne yasamu nasarar shari'arsu da Alhaji abdurrazak, yanzu haka an Yanke musu hukuncin d'aurin rai da rai agidan yari, Dan ba wannane karo nafarko dasuka saka yaransu yin kisaba.
Mutane sai yabama k'ok'arin bobo sukeyi, yak'ara girma a idon al'uma, kowa k'ara k'aunarsa yakeyi Dason tarayya dashi, hakama iyayensa da 'yan uwansa kowa alfahari yakeyi dashi.
Gama sharia'ar babu dad'ewa yak'arasa ginin gidansu idiris harsunma koma amma ambarma ammi hibba kamar yanda ta buk'ata, babansu idris yayi murna yasakama bobo albarka harbabu adadi.

Su Rahma sunsha bikin Basma Wanda dak'yar bobo yabarta take zuwa saboda cikinta yatsufa sosai ga cikin yayi girma masha ALLAH.
Bayan kammala bikin da kwana biyu Ammi tazo hargida zata tafi da Rahma takoma gidansu Dan ta CE, "bata amince tabarsu sukad'ai agidaba ga haibuwa yau ko gobe.
Rahma dai tayi murna da haka amma bobo tamkar zaiyi kuka, daga k'arshema shima shirya kayansa yayi Yakoma gidan Appan, Ammi dai ta CE, " shiyya sani Rahma cedai bazata bayarba sainanda wata hud'u.
Idanu bobo yazaro yace ammi wata hud'ufa kikace?.
Eh Ashe kajini?, sainan da wata hud'u lokacin baby yayi kwari, d'iyata ta huta sosai.
Shiru yayi kamar zaiyi kuka.
ammi sai kunshe dariya take, Rahma dake zaune Nawal na matsa mata k'afafunta dasukeyin fishi, itakam kasa daurewa tayi ta tuntsure da dariya.
Hararta bobo yayi tareda yin kwafa yatashi yafita.
Saida yafita sannan ammi tayi dariya itama.
Da Appa yadawo tabashi labari shima dariya yayta k'yalk'yawltawa, ya ce, "wai da gsk shima yahad'o kaya yadawo nan gidan?.
Wlhy kuwa Appan ishaq karkaji wasa, yana nan tsohon d'akinsa kwance yanzu haka yana barci.
Appa ya ce, " kai mukarram kayan shirirta, shi koyaushe zai gane yagirma ne?. To ALLAH yak'ara had'a kawunansu shida ita dakuma sauran 'yan uwansa da matansu gabad'aya.
Amindai Ammi tafad'a cikeda farin ciki.
______________________
Rahma tana kwance itada Nawal akan gado, Ammi na zaune bisa sallaya tana addu'oi bayan ta idar da nafila datakanyi akowane tsakar dare, yanzu itama ad'akin take kwana saboda gudun kar Rahma tafarka da ciwo cikin dare.
Agogo Ammi takalla 2:54am, filo tajawo daga saman gadon ta ajiye akan sallayar tazame ta kwanta, barcine yakwasheta, akuma daidai lokacin Rahma tafarka dawani matsanancin ciwo, amma saboda jarumta irin tata takasa magana saidai cije le6e da hawaye daketa sharara.
Zuwa wani lokaci takasa daurewa, ahankali ta daddafa tasakko daga gadon tadawo k'asa ta duk'usa tareda d'ora kanta bisa gadon tana murk'ususu.
Abin tamkar wasa sai gaba gaba yakeyi, can taji bayanta da k'ugunta cikinta ko ina yarik'e, wani wahalallen kuka tasaki tana fad'in nashiga uku ummi zan mutu, wayyo bayana cikina k'irjina zasu cire........
Afirgice Ammi tafarka, ganin Rahma durkushe tana kuka Takuma rud'ewa, Rahma yadai?.
Ammi cikina, bayana, ko ina ciwo zan mutu Ammi kuyafemin.
Bazaki mutuba Rahma, runk'a addu'a, akid'ime ammi take maganar, ga waya a hannunta tana kiran bobo.....
Shima azaune yake, tun d'azun yafarka saboda mafarkin Rahma dayayi tana kuka dakiran sunansa, tund'azu yakeson ya lek'a d'akin yaganta amma yanajin kunyar had'uwa da ammi, ganin damuwa zata masa yawa yatashi yad'auro alwala yazo yay nafilfili yanzu haka yana zaunene yana karatun alkur'ani, ganin kiran ammi yasashi d'aga wayar da hanzari.......
Zumbur yamik'e danjin ammi tana fad'in yafita da mota gasu nan fitowa, Alkur'anin ya ajiye yafigi key yay waje da sauri, mota yaje yagyara fakin sannan yadawo ciki, afalo yagamu da Appa d'auke da Nawal zai kaima 'yan aiki ita, wuceshi yayi yatarbo Ammi dake rik'eda Rahma tanata kuka.
Aii baijira cewar Ammiba yad'auki Rahma gaba d'aya yay waje da ita, ammi kuma d'akinta takoma ta d'akko kayan daza'a buk'ata, cikin mintuna k'alilan Ammi da Appa suka fito, bayan Ammi tashiga Kusada Rahma, shikuma Appa yazauna Kusada bobo, a 360 bobo yaja motar sai asibitin ya sulaiman.
Koda suka isa cikin gaggawa aka kar6esu, dandanan doctor Fa'iza takar6i haihuwar Dan ya sulaiman akwai kunyar surukuta tsakaninsu.
Har zuwa 4:46 Rahma bata haihuba, anatadai shan tata6urza, aii bobo dayaga abin bana k'are bane sai kawai yadanna kai cikin d'akin, duk maganar da ya sulaiman yake masa bai saurareshiba.
Inda take kwance yak'arasa, tana ganinsa tafara mik'a masa hannu tana kuka dakiran sunansa, Nurulk'albi ka gafartamin zan mutu, wayyo ALLAH dadyn Nawal nima mutuwa zanyi kamar Anty Ni'ima.
Dukda arikice yake shima haka yake shafa kanta yana fad'in a'a My cute bazaki mutuba, insha ALLAHU lafiya zaki haihu........kafin tabashi amsa wani sabon ciwon yazo.
K'ank'ameshi tayi sosai tana wani wahalallalen nishi.
Aiko bobo yaji rik'onnan na Rahma, sai jije le6e yake shima kamar mai Nak'udar.
Cikin ikon ALLAH saiga jariri yafad'o yana tsayyara kuka, cikeda murna doctor Fa'iza ta ida ciroshi tana fad'in Alhmdllh, saikuma sabuwar nak'uda, mik'ama Nurse tayi jaririn takuma kar6ar sabon baby daya kunno kai.
Ai Rahma na sauke wannan kaya saitayi lakaf ajikin bobo.
Ahargitse yake kiran my Nusfulhayat!, my cute!, momyn Nawal!!.
Katseshi doctor Fa'iza tayi da fad'in sir babu abinda yasameta tana hutun wucin gadine.
Doctor Fa'iza bafata numfashi.
A'a yalla6ai tanayi kalli k'irjinta kagani, kallonkuwa yayi saiyaga tana sauke numfashi ahankali.
Dukda bai samu nutsuwa dukaba yaji dad'i, ko sauraren 'ya'yan baiyiba dukda yana cikin matsanancin farincikin zuwansu duniya, amma ta mamansu yakeyi yanzu, bayan shigewar mintuna Rahma tad'aga idanunta dasuka k'ank'ance tana kallon bobo, murmushi tamasa.
Cikin farinciki yarungumeta yana fad'in Alhmdllhi Alah kulli'halin, sai yanzu d'unbin farincikinsa yafito fili.
Tuni labari yakaigasu Ammi, anhaifi twins namiji da mace.
Dan dad'i Appa har rungume ammi yayi, ya sulaiman sai kauda kai yayi yana dariya.

Cikin 'yan mintuna aka gyara baby's da mamansu, bobo yad'akkosu yafito dasu wajensu ammi, bakinsa yak'i rufuwa yaukam.
Had rige-rigen d'aukarsu ake tsakanin ya sulaiman dasu Ammi.
'Yan gata sun iso duniya, yara masha ALLAHU basuda maraba da yayarsu Nawal, dakuma mahaifinsu Abdulmaleek bobo.
To saimuce ALLAH yaraya 'yan dugwuy-dugwuy iyalan baba.

Sai karfe 8pm sukabar asibitin, aka rankaya zuwa gidan Appa, zuwa sannan labari yabaje dangi, sanda suka Isa gidan Appa cike yake dasu anty rasheeda, har and'ora ruwan wanka.
Innar su hibba tayima Rahma cikakken wanka, tanata zille-zille da zame-zame har aka kammala, yarama anmusu, annad'esu cikin fararen kayan sanyi masu laushi sai barcinsu sukeyi.
Rahma tafito daga bayi Dan tuni inna tafito tabarta tana k'imtsa kanta.
Zama tayi tashafa mai tashirya tsaf cikin atanfa sabuwa dal, itakad'aice ad'akin mutane duk suna falon k'asa har jariran.
Abincin da Anty ummy ta ajiye mata tazauna taci, shayine mai kauri da farfesun 'yan ciki, saikuma soyayen dankali, citai kad'an sanan tahaye gadon ta kwanta sai barci, dama barcin bai ishetaba..............








*_luv you oll._*.
*_(((S)))........2017_*
[11/12, 3:00 PM] mrs bilkisu: πŸ‘©πŸ»β€πŸ’»typing........

❣ *_ABDUL-MALEEK_*❣
_β€’πŸ…±πŸ…ΎπŸ…±πŸ…Ύβ€’_


*_NA_*
_*Bilyn Abdul*_

_sadaukarwa_
*_Abba Gana_*
*_Batul mamman_*
*_Billy giro_*


7⃣1⃣

Falon cike yake da dangi, bobo yashigo da sallama hannunsa d'auke da leda babba, gaisawa suka shigayi da mutanan falon anata masa barka, cikeda farinciki yake amsawa, mutane dayawa dabasa ganin dariyarsa yau har mamaki sukeyi yanda yaketa yak'e hakwara.

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login