Showing 3001 words to 6000 words out of 111128 words

Chapter 2 - Abdulmalik Bobo Part 1 Hausa Novel Complete

20 Dec 2024

739

Mukarram karshen shekarafa kace?, kai kana ganin zamu iya barinka harnan da watanni Tara babu aure, nifa nagaji da ganinka hakanan gsky.
Ammi tashigo hannunta d'auke da tire, yaa is'haq yana biye da ita.

Appa ya ce, "yauwa aii gara dakukazo.
To miya faru Alhaji?.

A'a wai Murarram nakeyima zancen sure, shine yake rik'ona abarsa sai k'arshen shekara.
K'arshen shekara kuma ya ishaq yafad'a yana kallon Bobo dayake wani 6ata rai. Kai idan anbarka zuwa k'arshen shekarar saika yarda?.
" emana yaya aii nake ganin zaifi ko?.
shin wai Abdulmalik kodai bakada lfy ne?.
Yaya banida lfy kuma kamar ya?.
Harararsa ya ishaq yayi ya ce, " bansaniba.
Appa ya k'atsemusu zancen dafad'in Ishaq babu wani abinda ke damunsa iya shegene kawai irin nasa. Amma nima abin yana bani mamaki wlhy, hakamafa lokacin aurensa na farko mukaita fama, kokuwa maganar ishaq gsky ce?.
Ran Bobo yakuma 6aci, aii dama yasan tunda wannan masifaffen yazo saidai ALLAH, gashinan yak'arama wutar fetir.......
Appa yakatsema Bobo tunani da fad'in Mukarram baka jinane?.
Kansa ya girgiza, murya a sark'e ya ce, "wlhy Appa lfy ta k'alau.
Appa ya kalli ammi, kai ammi ta girgizama Appa kawai.
Appa yayi murmushi, ya ce, " shikenan Mukarram tashi kaje, ALLAH yakaimu k'arshen shekarar.
Yakwa mik'e yana washe baki yafice, azuciyarsa ya ce, "su yaa Ishaq ansamu game over.
(Nikam dariya yabani, Dan k'ila shine mai game over d'in).

Ammi ta ce, " Alhaji nifa ban fahimcekaba?.
Appa yay murmushi, yanzu zan fahimtar daku, shekaran jiya naje mun gaisa da abokina Alh bilal, anan nakemasa maganar ranshin auren Mukarram abin yana damuna.
To yanzudai azancen nan danake muku munyanke hukuncin had'a auren mukarram da 'Yar wajensa.
Ammi tayi murmushi tana fad'in Alhmdllh, kai nayi farinciki wlhy, ALLAH ya tabbatar da alkairi.
Amin ya ishaq yafad'a shima fuskarsa cike da annuri.
Ya gaida Appa Dan ko gaisawa basuyiba ma, daganan suka tattauna akan bikin, ya Ishaq yatafi...........





*_rubutu hikimace da baiwa ta musamman gsky, shiyyasa bazan gajiyaba da yabonki aunty bilynaπŸ€™πŸ»β£πŸ‘ŒπŸΌ._*

[11/12, 2:14 PM] mrs bilkisu: πŸ‘©πŸ»β€πŸ’»



❣ *_ABDUL-MALEEK_*❣
_{Bobo}_



_Story & editin_
*_Aunty Bilyn Abdul_*


✍🏿 _Written_
*_Marak'isiyya_*


_hak'in mallaka_
*_Aunty Bilyn Abdul_*


_sadaukarwa_
*_Abba Gana_*
*_Batul mamman_*
*_Bily giro_*



7⃣&8⃣
_washe gari_
Da wuri Bobo yatashi yay shirin zuwa wani bincike akan shira dazaiyi.
Fes yakejinsa akan maganar dasukayi jiya da su Appa.
Yafito sanye cikin shadda ruwan k'asa d'inkin boda, kayan sunmasa k'yau sosai, sai tashin k'amshi yakeyi, wayoyinsa yad'iba da jakar aikinsa.
Babu kowa afalon ya kalli bak'in agogon fata dake d'aure a tsintsiyar hannunsa 7:23am, yasan yanzu babu Wanda yatashi, Dan al'adar gidance indai sukayi sallar asuba sukoma barci, ficewarsa yayi saboda yanada uzuri.
Yabude d'ayan gefen motarsa yazuba kayan hannunsa sanan yazagaya yashiga ya zauna.
Saida yatsaya suka gaisa da maigadi sannan yafice, anguwar shiru babu hayaniya saidai iskar Safiya dake kad'awa, gakuma rana tad'an hasko maibada d'umi mai dad'i, cikin nutsuwa yake juya sitiyarin tamkar bayaso, yafito daga layin gidansu yahau babban titi, tafiya kad'an yayi saiya hangi taron jama'a a tsaitsaye agefen titi, wasuma daka gansu suna cikin rud'ani, harya wuce saiya dawo baya yanemi guri yay fakin.
Fitowa yayi daga motar yanufi wajen taron jama'a.
Malam lfy kuwa?, yatambayi wani matashin saurayi daketa zage2.
Saurayin ya balla masa harara, kacemin lfy kuwa, aii dama duk irinkune, kud'i sunsaku bakwa tsoron ALLAH, gani kuke komai kukayi kunada kud'i zasu kareku........ Hannu Bobo yad'aga masa, kaga bawannan nake tambayarkaba nikam, mike faruwa anan?.
Saurayin ya share hawayensa sannan ya ce, "wani mara imanine yayma yarinya fad'e yazo nan ya yardata.
Fad'e!!, Bobo yafad'a arazane, da sauri yafara kutsa kai cikin taron jama'ar batareda ya saurari maganar da saurayin yake masaba.
Innalillahi wa'inna ilaihirraji'u yafad'a yayinda yay tozali da k'aramar yarinya kwace tamkar gawa.
Da sauri ya rarumi yarinyar batareda yakula da jinin dake zuba ajikintaba, wasu daga cikin mutanen suka fara tambayarsa koya Santa?.
Bai sauraresuba yabud'e mota yasakata abaya, harya shiga mota yakira saurayin d'azu ya ce, " shiga muje.
Babu musu saurayin yashiga, Bobo yaja motar a 360 suka nufi asibiti.
Azuciyarsa yana Addu'a ALLAH yasa ya Sulaiman yana asibitin.
Suna Isa aka amshesu cikin gaggawa Dan ansanshi k'anine gamai asibitin.
Ma'aikatan masu gaisheshi ya tambaya ya sulaiman yazo?.
A'a baikai ga k'arasowaba wata matashiyar budurwa tafad'a cikeda sanabe.
Baibi takantaba yafara kiran ya sulaiman.
Bugu d'aya ya d'auka.
Cikin zolaya ya ce, "Bobon Ammi ya akayi?..
Muryar bobo na rawa ya ce, Yaya kana ina?.
Ina hanyar zuwa asibiti miya faru?.
Alhmddlh Bobo yafad'a, saika k'araso kawai, nima ina asibitin, baijira amsar ya sulaimanba ya yanke wayar.
Gudu ya sulaiman yak'ara danjin Bobo ya ce, " yana asibiti.
Cikin k'an k'anin lokaci ya iso, atsorace yake kallon jikin bobo da jini ya 6ata.
Bobo daketa safa da marwa ak'ofar d'akin da aka shigar da yarinyar ya hango yaa sulaiman yashigo cikin asibitin arazane.
Cikin hanzari yatareshi, yayana Dan ALLAH ka taimaki yarinyar nan karta mutu plzzz.......
Cikin rashin fahimta ya sulaiman ya ce, "nutsu Abdulmalik miya samu Nawal d'in?.
Yaya ba Nawal bace wata yarinyace, kaje wajenta zanmaka bayani daga baya plzzz.
Ya sulaiman yasan halin bobo da rikici Dan haka da Sauri ya afka d'akin Dan ganema idonsa.
Kansa yadafe cikin tashin hankali yafara yima Nos masifa akan sunzubama yarinyar ido babu abinda sukai mata.
Kayi hak'uri sir aikin banamu bane dole saikazo, inazaton Fad'e akamata.
Ajiyar zuciya ya sauke, taimakon gaggawa yafara bama yarinyar.

A waje kam Bobo yakasa zaune yakasa tsaye, sai kaida kawo yakeyi, hankalinsa atashe, yanzunan haka al'umma suka lalace akan zalinci?, insha ALLAHU saiya k'ar6oma yarinyar nan 'yancinta, zaiyi bincike kod'an gidan ubanwaye saiya gurfanar dashi a gaban shari'a.
Wayarsa dake wringing ya Ciro a aljihu, Br..... Kamal yagani, yarintse idonsa Dan yamanta abinda ya fiddoshi daga gida, bai d'agaba har wayar ta yanke aka k'ara kira.
Daurewa yayi ya d'auka suka gaisa, AA Hamshak'i wai ya akayine?, kacemin kafito gida amma najika shiru.
Sorry Kamal ina nan zuwa, wlhy wani abune ya rik'rni ahanya, amma plz kabani minti talatin zuwa arba'in zan iso.
Okey saina ganka.

A can kuwa bobo nabarin wajen police suka zo, mutane suka sanar dasu wani ya d'auki yarinyar zuwa asibiti.
Wane asibin ne?, wani d'ansanda ya tambaya fuska atamke.
Muma bamu saniba wlhy, amma antafi damai shagonnan, suka nuna shagon dake kusadasu.
d'ansandan baice komaiba yashiga mota suka juya.
Gulma mutanen gurin suka fara da zagin 'yan sandan, wai sai yanzu suka gadamar zuwa, bayan tun d'azu aka kirasu.
Wani ya ce, "bar munafukai malam aii k'asarnan munga takanmu, buharine kawai ke k'aunar talaka, (ALLAH dai ya k'ara masa lfy).
Amin ya rabbi Garzali.

+++++++++++++
Safna tafito sanye cikin atamfa Riga da siket, sunmata d'am kamar zata fashe.
Rahma ta kalleta ta girgiza kai, wannan lamari na 6ata mata rai, ita bataga wayewaba ga mace mai saka suturar dake fidda jiki, shiyyasa fad'e yaketa k'ara yawa aduniya, to matan basusan darajar jikinsuba, (suyita fiddo jiki tamkar akuyoyi da sunan wayewa).........
Me wait lfy kike kallona?, karfa ki cinyeni wlhy.
Rahma takauda kai saga kallonta, ta ce, " aikinsan Nina mayya bace.
Da sauri safna takai mata duka, to ubanwaye mayen?.
Rahma ta kauce tana dariya, maida wuk'ar ta hannun damar Abba, Dan ALLAH zanbiki makarantar wlhy zaman gidannan ya isheni.
Safna ta harareta tozoki hau kaina uwata.
A'a ALLAH yabaki hak'uri, yi tafiyarki zanje gidan yaa Munir nama taya aunty Naja'atu aiki.
Yafimiki sauk'i, dama da 'yan aiki kike kama aii, safna tafad'a tana ficewa.
Baki Rahma ta ta6e tareda Jan tsaki.
Ummi tafito tana fad'in kekuma lfy?.
Lfy lay ummi nida aunty Safna ne.
Ina Safna d'in?.
Tafita makaranta.
Shine yau ko sallama babu?, dariya Rahma tayi ta ce, "haryanzu aljanun masifar nasu saukaba.
Ummi batace komaiba tashige kicin.

+++++++++++++
Asibiti kam lamura saidai addu'a bak'aramar mugunta akaima yarinyarba, amma cikin ikon ALLAH yaa sulaiman yayi nasarar ceto ranta.
Bak'aramin lokaci ya6ataba kafin yafito, zuwa yanzu bobo na tsaye jingine da bango ya hard'e hannuwansa biyu ak'irji, k'afarsa d'aya dogare a bango fuskarnan d'aure tamau.
Ya sulaima yafito yana shere zufa, da sauri Bobo ya taresa, Yaya ya jikin nata??.
Alhmdllh. ya sulaiman yafad'a, yaja hannun Bobo suka shiga office d'insa.
Koda ya zaunar dashi saiya bude firij yad'akko fresh milk ya tsiyaya a kofi yamik'ama Bobo.
Bobo ya ce, "ya.... Hannu ya d'aga masa, kaga k'ar6a kasha kasamu nutsuwa, nasan ko karyawa bakayiba kafito.
Ajiyar zuciya Bobo yayi, yakar6i kofin yasa abaki, ahankali yakesha harya shanye tas.
Cikin zolaya ya sulaiman ya ce, " Bobon Ammi damadai yunwa kakeji, ko a k'ara?.
Murmushi yayi batareda yace komaiba, ya girgiza kai.
Ya Sulaiman ya zauna yana dariya, saida yayi rubuce2 sannan yad'ago ya kalli k'aninnasa, Abdulmalik ina kasamo yarinyarnan?.
Ajiyar zuciya Bobo ya sauke shima yayan nasa yake kallo, ya ce, ''Yaya wlhy abakin titi..... Nandai yakwashe komai yasanar dashi.

Girgiza kai ya sulaiman yayi, ya ce, ''ALLAH ya saka mata, amma yanzu yakamata musan iyayenta kafin ad'au mataki, sannan ina yaron dakace kunzo tare?.
Yana nan awaje.
Wani Abu ya sulaiman ya danna, saiga Nos tazo, ya ce, "akwai wani saurayi anan waje shigomin dashi.
OK sir.............






*_kuyi hak'uri ina muku typing bakamar aunty billy ba, wlhy akwai wahala, writers suna k'ok'ari gsky, ALLAH dai ya biyasu._*πŸ™πŸ»


*_" luv u aunty bilyn Abdul"_*
[11/12, 2:15 PM] mrs bilkisu: πŸ‘©πŸ»β€πŸ’»



❣ *_ABDUL-MALEEK_*❣
_{Bobo}_



_Story & editin_
*_Aunty Bilyn Abdul_*


✍🏿 _Written_
*_Marak'isiyya_*


_hak'in mallaka_
*_Aunty Bilyn Abdul_*


_sadaukarwa_
*_Abba Gana_*
*_Batul mamman_*
*_Bily giro_*




9⃣&πŸ”Ÿ

Assalamu alaikum.

Wa'alaikassalam yaa sulaima da bobo suka amsama saurayin.
Gurin zama yaa sulaiman ya nuna masa, bayan ya zauna yabasa hannu sukayi musabaha.
Ya sulaiman ya ce, "d'an uwa ance awajenku aka samu yarinyarnan ko?..
Eh anan akazo aka yardata wajen misalin k'arfe 6:44am, fitowa ta kenan zan bud'e shagona naga wata jar mota ta tsaya agurin, nasan su basu ganniba nida abokina Nura, Dan saida suka wawwaiga sukaga babu mai kallonsu sannan aka turota waje.
Bobo ya cije le6ensa zuciyarsa na k'ara zafi.
Ya sulaiman ya jinjina kai, Yakuma fad'in to kunsanar da police?.
Eh suna barin wajen muka kira 'yan sanda, amma har bawan ALLAH nan yazo ya d'auketa basu zoba.
Ya sulaiman ya sauke numfashi, babu damuwa ayanzu nasanar da wani d'an sanda dan kes d'in dolene police sushiga, namata abinda duk yadace, kuma narubuta bayanai akan komai.......
Kwankwasa k'ofarne yahana yaa sulaiman cigaba da magana, wata nos tashigo tana sanar dashi wani police nason ganinsa.
Shigo dashi mana ya sulaiman yafad'a.
Bayan d'an sandan yashigo shida wani suka gaisa dasu bobo sannan sukayi musu bayani akan komai.
Har d'akin da yarinyar take aka kaisu, bobo tamkar yay kuka danganin yarinyar, shidama haka yake da tausayi dukda kasancewarsa masifaffe.
Bayan sun kammala komai 'yan sandan suka tafi, shima saurayinnan yatafi akan zasu sake nemansa.
Ya ce, "insha ALLAHU duk sanda sukazo zai basu had'in kai.
Godiya sukai masa yatafi, bobo yay masa alkairi.

Ya sulaiman ya kalli bobo, Abdulmalik kaima yakamata katafi gida ka canja kayannan duk sun 6aci da jini.
Sai asannan yakula, yad'anyi tsaki wlhy yaya bamma kulaba, bari naje wajen Br kamal Dan yana jirana, idan muka gama saina koma gidan.
Dadai kafara zuwa ka canja kayan tukunna.
To yaya bari naje, saina dawo.
Okey saika dawo.
Saida sukad'an rungume juna sannan sukai musabaha yatafi.

+++++++++++++++++
Rahma tafito sanye cikin dogon hijjab har k'asa yake ja, hijjabin mai hannune Dan haka hannunta rik'e da fos, sallama tayima ummi sannan tafito.
Ta wawwaiga bataga idiris diraiba ba, d'an tsaki taja ta k'arasa wajen mai gadinsu, rissinawa tayi ta gaisheahi.
Ya amsa cike da fara'a, yana k'aunar yarinyarnan saboda hankalinta da girmama nagaba da ita, halinta ya banbanta da yayarta sosai.....
Rahma tak'atse masa tunani da fad'in baba ina Idris!.
aiko d'iyata Idris yaje gida yanzu babu dad'ewa, kinsan suna cikin tashin hankalin 6atan k'anwarsu tun jiya da yamma.
K'anwarsu kuma?, 6ata tayi?.
Wlhy kuwa haka yake gayamin d'azu, wai tunjiya bata dawoba daga aikenta.
Tofa ALLAH yabayyanata, Toni bari naje na hau adaidaita.
diyata dakanki?, toki tuk'a kanki mana.
Murmushi tayi ta ce, "A'a baba, Abba ya hanani tuk'i."
ALLAH sarki 'Yar albarka, aii haka akeson mutum yaringa bin maganar iyayensa, ALLAH yay miki albarka, yabaki miji nagari.
Murmushi Rahma tayi, ahankali tace ngd baba saina dawo.
To adawo lfy.

Rahma tafito daga gida, tad'an wawwaiga anguwar babu mutane sosai, sai jefi jefi, dakuma motoci dake fitowa daga gidaje inaga masu Fita aikine da kasuwa.
Ajiyar zuciya ta sauke sannan tafara tafiya da addu'ar ALLAH yasa tasamu adaidaita da wuri, Dan tsakaninsu da titi da nisa.
Tad'anyi tafiya kanta ak'asa, jitai ance a'a Rahma sai Ina?.
Ad'an tsorace tad'ago takalli inda aka ambaci sunan nata, tayi murmushi lah ya kamal kaine.?.
Nine Rahma ykk?.
Lfy lau yaya, lfy naganka anan?.
Wlhy lfy k'alau wani abokina nake jira, amma shiru bai zoba shine naked'an shan hantsi anan.
Ayya, yasu momy da aunty Ameera.
Lfy lay suke, bazaki Shigabane?.
A'a yaya gidan ya Muneer zanje wlhy ka gaidaminsu.
Zasuji, to amma ina direbanku kika fito ak'afa.
Hummm wlhy wani d'an uzuri yarik'eshi.
Okey, to amma ba girmanki bane.
Dariya tayi kai yaa kamal to miye girmana?.
Kafin yabata amsa wata mota ta tsaya adaidai saitinsu.
Kamal ya ce, "ga abokina nan ya iso.
Waigawa tayi takalli motar, saikuma tadawo da kallonta kan kamal, tom nikam nawuce.
Bazaki tsaya Ku gaisaba.
A'a yaya aii bai sanniba.
Bobo yafito daga motar fuskarsa babu yabo babu fallasa, yad'an kalli Rahma datazo zata gitta ta gefensa, kanta ak'asa ta gaisheshi.
Ya amsa da lfy, yana kauda Kansa daga kallonta.
Gaba tayi tana Jan tsaki, dukda bata kalleshiba abin yabata haushi, tana bak'in cikin ta gaida mutum ya ce, " mata lfy."
Bobo yak'arasa wajen kamal suka gaisa, sannan suka Shiga cikin gidan.

Rahma kam tana k'ara 'Yar tafiya tasamu adaidaita tashiga.

.+.+.+.+.+.+.+.+.+.
Safna Ana makaranta, yau itace harda zuwa office d'in yaa Hamza amma ta tarar baizoba.
Basira ta kalli safna daketa jan tsaki tana kallon agogon hannunta, wai safna lfy kuwa?, naga kinsamu zuwa office d'in malam Hamza miye dalili?.
Zeenat dake zaune gefensu ta ta6e baki, kazar wahala ALLAH ya yanka mata shiyyasa tafara figa.
Kazar wahala kuma kamar ya?.
Zeenat tabama Baseera labarin abinda yafaru jiya, Dan ita batazo school ba.
Wata dariyar mugunta Baseera tasaki, o, ni Baseera wai yau Safna kece saurayi ya sacema zuciya?, lallai zanso ganin wannan guy mai suna Bobo, nasan tabbas ya amsa sunansa bobo.
Hummm kibari kawai Baseera wlhy jiya banyi barciba, mafarkinsa nayitayi, harda mafarkin munyi aure harda yara.
Dariya zeenat da Baseera suka saka harda cafkewa.
Safna ta 6ata rai tana hararsu, kuga nifa banason ciki da iskanci kunsani, zeenat damafa haushinki nakeji, Dan maganar jiya ta 6atamin rai wlhy.
Cikin dariya zeenat ta ce, "afwan Tawan, ALLAH yabaki bobo.
Amin, namasan yabani tunda har yasamun sansa azuciyata.
Zeenat tad'an ta6e baki tana fad'in garadai adogara ga ALLAH.
Baseera tai saurin kar6ewa toda dake tace ta dogara?, Safna karki damu ina bayanki d'ari bisa d'ari, kota halin k'ak'a saikin mallaki Bobo.
Safna tayi murmushi shiyyasa nakesonki k'awata ALLAH yabarmu tare ngd.
Zeenat tana jinsu bata kuma tankawaba.

+.+.+.+.+.+.+
_3:30pm_ Bobo yashiga cikin asibitin, kai tsaye office d'in ya sulaiman yanufa, suka gaisa ya tambayi yamai jiki?.
Da sauk'i Bobo, aiina zata bazaka dawoba?.
Tab yaya wlhy hankalina yana asibitin nan, yanzu haka bamu gama aikinba nabarma Br kamal nataho, yaya ta farka kuwa?.
A'a har yanzu tana barci, ana buk'atar tahuta sosai yanda zata tashi k'wak'wal warta Normal, ta wannan hanyarne kawai zamuyi saurin samun bayanai daga gareta.
Okey tom ALLAH yabata lfy.
Amin Mukarram d'in Appa, mai

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login