Showing 69001 words to 72000 words out of 111128 words

Chapter 24 - Abdulmalik Bobo Part 1 Hausa Novel Complete

20 Dec 2024

759

baza suyita kallon mutum.
Hhhhh toka had'une shiyyasa suke kallonka, Inda basu sankabama bazasu barka ganinaba ehe, ato bara nayi zamana Idan kamatsu kazo office kasameni.
Hhhhhh to yi hak'uri na Ammi kodayake yanzu kazama na Rahma.
Dariya bobo yayi ya yanke wayar, baikai ga ajiyewaba kiran Ya Sulaiman yashigo, yad'aga suka gaisa.
Bobo ya ce, "yaya dama wlhy INA niyyar kiranka, magani nake buk'ata.
Maganinmi bobo?.
Ummm saidai Nazo, inafata kana asibiti.
Eh, amma kai kana ina?.
Gani zanje gaidasu ammi, OK nima yanzu nabar gidan babu dad'ewa nida ya ishaq da Hamza.
Ayya tosaina shigo.
Okey, ina jiranka.

Bayan ya ajiye wayar yakalli Rahma kad'ain ya kauda kai, murya k'asa k'asa ya ce, " gara naje na k'ar6o miki magani wannan tafiyar taki tadawo daidai, damma kinki hak'ura ne amma yanzu haka zakije gidan Ammi kina tafiyar 'yan kaciy......
Bai k'arasaba yay saurin rufe bakinsa da hannunsa yana dariya.
Rahma taturo baki gaba, yakuma kallonta yashek'e da dariya.
Ba Rahmaba har Safna da Nawal saida suka kallesa, suna had'a ido da Safna ta madubi ya gimtse fuska.
Aranta ta ce, ''zakazo hannune malam.
Itakam Rahma ta ce, "mugu d'an masa sai ALLAH yasakamin aii.
Da hakadai suka k'arasa gidan AMMI.

Safna da Nawal suka fice, Rahma na niyyar fita bobo ya kulle motar, juyowa tayi tana kallonsa shima ita yake kallon, ya ce, "yadai 'yammata namiki k'yaune?.
Kauda idonta tayi daga kansa, ta ce, " Dan ALLAH kabud'emin.
Aidama zan bud'e miki, sonake nacemiki kiyi k'ok'ari koyaya kid'an gyara tafiyarki inba sokike kowa yasan miya faruba.
Kallonsa tasakeyi, saikuma tayi k'asa da kai tana turo baki gaba, nifa wlhy zafi nakeji awajen.
Shiyyasa nace ai kiyi zamanki sai gobe amma kikak'i, amma babu damuwa bara na kar6o miki magani wajen ya sulaiman, yanzudai muje ciki, amma idan kinje kiyi kwanciyarki ki huta kinji.
Batace komaiba takama k'ofa zata bud'e yarik'o hannunta haba tawan ko sallama babu?.
Tokai bazaka shigaba?.
Jawota jikinsa yayi yana fad'in zan shiga mana, amma ai bazan dad'e ba, k'ok'arin saka k'wayar idonsa yake anata itakuma tak'i basa dama, saima talumshe idanunta gaba d'aya, wani murmushi yayi Wanda har tanajin sautinsa, jin bakinsa kan nata yaskata saurin zabura, amma ina tamakaro yarigada yayi nasarar cafkar harshenta.

Na ce, "humm bara nakoma daga waje najiraku."

Ak'alla sunkai minti biyar sannan naga Rahma tayi saurin fitowa tana murmushi, shima bobo yafito yana dariya, gaba tayi abinta hartana had'awa dad'an gudu, bin bayanta yayi yana fad'in matsoraciya kawai.
Ak'ofar falo tatsaya ta daidaita nutsuwarta sannan tashiga.
Gaba d'aya yaran suka taso suka tareta, itama tahad'asu tarungume tana dariya, Rahma akwai San yara shiyyasa duk inda taje saikaga yara suna sonta.
Bobo yana shigowa suka saketa suka nufeshi, zama Rahma tayi suka gaisa da su aunty Rasheeda, aunty ummy, aunty sameera, khairiyya da khursiyyama suka gaisa.
Bobo yak'araso shima suka gaisa su aunty Rasheeda suna tsokanarshi, Rahma dai mik'ewa tayi tanufi d'akin Ammi itada khairiyya.
Bobo ya ce, "ALLAH idan baku daina matsaminba saina saka mazanku sun k'ara aure.
Da sauri aunty Sameera ta ce, " a'a Abdulmaleek wlhy nikam nabari yi hak'uri, tashi yayi yana murmushi ya ce, "waiku mata miyasa kuke tsoron kishiyane?.
Aunty Rasheeda ta ce, " jeka katambayi Rahma, d'akin Ammi yanufa yana fad'in ai ita bata tsoron kishiya.
Dariya suka saka gabad'aya shikuma yashige d'akin Ammi da sallama.

Ammi ta ce, "a'a mukarram d'ina kaine?.
Wlhy nine Ammi wad'ancan 'ya'yan naki duksunbi sun rainani, nakusa daina musu dariya.
Dariya Ammi tayi ta ce, " kunfi k'asa aii.
Shima dariyar yayi sannan yagaida Ammi cikin girmamawa, yanayi yana satar kallon Rahma dake zaune kusada Ammi suna ware wasu kaya itada khairiyya.
Ya ce, "Ammi yunwa nakejifa.
Kallonsa Ammi tayi tana dariya, haba mukarram aii gwauro aka sani da zama da yunwa, murmushi yayi shima, ya CE, " Ammi nima tawa matarce babu lfy."
Ayya, Ammi tafad'a tana kallon Rahma, nima tunda tashigo nake kallonta duk naganta sukuku babu walwala sosai, ga idonta sund'an kumbura, mike damunta?.
Sosa kansa yayi yana fad'in em...em.. Ammi zazza6ine.
Dariya Ammi tayi ta ce, " mukarram magana da in ina kamar mara gsky.
No Ammi inada gsky kawai inaso natuna sunan zazza6inne.
To ALLAH yabata lfy kunje asibitine?, a'a ammi jiya da daddare zazza6in yasameta, dama yanzu zanbiya tawajen ya sulaiman na kar6o mata magani.
Okey to Aida tayi zamanta agida tahuta ko.
babu yanda banyi da ita tazaunaba amma fir tak'i wai itadai saitazo, yayi maganar yana kallon Rahma.
Tana jinsu amma tashare kamar batasan zancen da akeba, Ammi ta ce, "khairiyya jeki had'omusu break fast ko, suma su Safna haka.
To Ammi khairiyya tafad'a tana mik'ewa.

Ammi da bobo suna 'Yar hirarsu khairiyya takawo break fast, bobo yalangyare wai saidai Ammi tayi feeding d'insa.
Rahma tad'ago ta kalleshi saiya yimata gwalo, Ammi na kallonsa, danhaka tayi murmushi had'eda girgiza kai, koba komai tasan d'anta yasamu farinciki daga matar tasa,.
Rahma d'auke idonta tayi daga kansa tana d'an murmushi, aranta ta ce, " Indai ta6arace kaganta salo salo ga daddyn Nawal, wani abunma idan yayi saiya baka dariya wlhy.
Ammi kam dakanta tabama bobo abincin yaci, saida yak'oshi sannan yamik'e, AMMI bara nad'anje office naga mike tafiya.
To ALLAH yabada sa'a yatsareka babana.
Amin ammina.
Ya kalli Rahma, ya ce, "my cute nawuce.
ALLAH yabata kunya amma saita dake ta ce, " ALLAH yabada sa'a, ameen yafad'a yana fita, idon ammi kawai yahanashi mata kiss.
Afaloma yamusu sallama yafice.
Da sauri Safna ta tashi tabi bayansa..................














*_luv you oll_*
*_(((S))).......2017_*
[11/12, 2:57 PM] mrs bilkisu: 👩🏻‍💻typing........

❣ *_ABDUL-MALEEK_*❣
_•{🅱🅾🅱🅾}•_


*_NA_*
_*Bilyn Abdul*_

_sadaukarwa_
*_Abba Gana_*
*_Batul mamman_*
*_Billy giro_*


5⃣8⃣

Bobo dabaisan Safna nabinsa abayaba yabud'e mota yashiga, harya tada motar yaji ana kwankwasa masa gilas.
Sauke gilas d'in yayi ahankali Dan atunaninsa Rahma ce kosu khursiyya, had'e fuska yayi Dan ganin safnace, baice komaiba ya kauda kai daga kallonta.
Rik'e k'ugu tayi tanamai jifansa da shu'umin kallo, cikin narkewar murya ta ce, "haba my jaan wai miyasa kakeson wulak'antanine?, aiko bakomai ance kaso mai sonka, yanzu Dan ALLAH abinda kamin agaban Rahma d'azun yadace?.
Tsaki yaja tareda yatsine fuska tamkar Wanda yaga kashi, ya ce, "ke awa? dabazan miki abu agaban Rahma ba?.
Ya nunata da d'anyatsa wlhy kifita hanyata, karki yarda kibari na nunamiki asalin colour d'ina, ina d'aga miki k'afane saboda 'Yar uwarki, amma zakisha mamaki idan kikacigaba da bibiyata.......
Kafin ta ce, " wani Abu yaja motarsa yafice, dama tuni mai gadi yabud'e masa gate.
Hawaye suka kwararo afuskar safna, wani d'an lungu tasamu dagacan baya ta zauna, saida tad'anyi kuka sannan tad'auki waya takira baseera, bata d'agaba takuma kira nanma haka, ajiye wayar tayi tazabga tagumi cikeda damuwa.

Su Rahma suna ciki basusan bikin da akeba, bayan sungama ware kayan da ammi tasakasu suka dawo falo wajen sauran 'yan uwansu suna hira, saidai hankalin Rahma yana kan tunanin ina aunty Safna?, gashi batason tashi Dan gudun karsu fahimci halin datake ciki, tasan ko kowa bai tanka tafiyartaba sai aunty Rasheeda tayi magana, Dan tun d'azu take binta da kallo, itakam idan antambayeta batasan amsar dazata bayarba.

Da sauri Safna ta kalli wayarta ganin Baseera CE yasa tad'auka da hanzari, ko gaisuwa bata tsaya sunyiba ta ce, ''kekam baseera ina kika Shiga haka inata kiranki tun d'azun?.
Safna muna lectures ne, kinsan ba'a d'agama sir hamza waya idan yana lecture, waimi yahanaki zuwa school yaune?.
Wlhy babu komai hakanan naji banason zuwa.
Lallai kinyi wauta Dan wlhy sir hamza yayi test yanzu.
Ke babu damuwa aii ina gidansu, kinsan ankusa bikin k'annenesu nextweek, to muna gidan ana shirye².
Hummm ALLAH yasa yad'aga miki k'afa to, Dan wlhy ya CE........
Da sauri Safna ta katse baseera kenifa bawannan bane damuwata, nakirakine muyi magana.
To inajinki baseera tayi maganar tana zama kusada zeenat data fita harkarsu tuntuni dantaga sunyi nisa basa jin kira, idanma zasuyi k'ulle k'ullensu basaya akusada ita.
Safna ta ce, "baseera wlhy inacikin matsala."
Matsala kuma kamar ya?.
Safana tafara zayyanama baseera abinda yafaru tundaga Daren jiya da motarta ta lalace harzuwa abinda bobo yamata yanzunnan.
Jinjina kai baseera tayi sannan tad'an kalli zeenat dake karatu amma hankalinta na Kansu kuma tanajin duk abinda safna ke fad'ama baseera awaya, baseera ta ce, "lallai safna bakida wayo wlhy, keyanzun harya sakaki dafa ruwan zafin Gaza Rahma amma ki Gaza ganewa?, kumafa k'uru k'uru yafito yace miki Rahma tagirma amma duk Baki ganeba.
Safna tad'an ta6e baki baseera ban... bangane kema mikike nufiba aii.
Tsaki baseera taja tana fad'in aikin banza, asheke zaman banzama kikeyi agidan, ayanzukam kid'auka bobo yamiki nisa wlhy dankuwa adaren jiya ya angwance kenan.....
Agaban safna yafad'i cikin masifa ta ce, " baseera karki k'ara 6atamin rai kema banason fatan tsiya, taredakefa malam da'u yacemana yaturomusu aljani dazai hana ya kusanceta.
Baki baseera ta ta6e ta ce, "wannan zancekam yazama labari tunda bobo ya aikata hakan ajiya, saidai kuma kujira result d'in ciki.
Kuka wuy wuy safna tasaka tana kuran tashiga uku bobo yaci amanarta itakam rayuwarta tazo k'arshe garama tamutu ta huta.
Tsaki baseera tayi tareda yanke wayar tana fad'in 'Yar wahala keni nagaji da matsalolinki, wlhy da bobon zaice yana sona nimafa sonshi nakeyi harma nafiki Dana kula yamin nisa saina hakura, amma nakula ke kinkasa ganewa *_" ANNABI"_* yafaku, haba Dan ALLAH ayi mutum da tosashshiyar basira, idanma bakisaniba kisani dagani har malam da'un cin k'ud'inki kawai Mukeyi babu wani aiki dayake miki Dan tun farko yafad'amin komai wlhy, ya ce, "kwata kwata babu aure tsakaninki da bobo Dan bazaima sokiba.
Zeenat tayi galala tana kallon baseera wadda da alama tamanta tana wajen shiyyasa taketa sakin zance babu (,) babu (.).
Ganinfa da gsk tamanta tana wajen yasaka zeenat zungurar ta baseera kinsan mikike fad'a kuwa?.
Figigit baseera ta kalleta saikuma tafara Kame kame au.. au.. Ummm zeenat dama kina nan?, Dan ALLAH kinji minake fad'a?, pls kirufamin asiri maganarnan tatsaya dagani saike Dan ALLAH, kitaimakeni Zeenat wlhy su6utar bakice.
Girgiza kai kawai zeenat tayi tamik'e tabar mata wajen Dan wlhy yau bak'aramin tsoro baseerar tabataba, lallai maganar Sajna gsky CE datace *_wata k'awar tafi guba_*, itakam yau ta shaida akan baseera, idan bata mantaba baseera CE tasaka safna ahanyar bin malami da bokaye, amma Ashe tanacan tahad'a baki da bokayen sunacin dunduniyar safnar, ALLAH ma ya k'ara, aiduk Wanda baiji bariba yaji hoho, babu irin nasihar da bataima safna ba amma tak'i saurarenta daga Bayama daina mata magana tayi wai bata k'aunarta, toga baseerar datake d'auka tana k'aunarta d'in nan tajefata arami mai zurfi kuma mai duhu, aii duk Wanda yagagara yima iyayensa biyayya to yanatareda gamon wahala, to ita baseera CE gamon wahalarta kuwa.
Ganin baseera tanufota yasakata saurin yin gaba.
Da gudu baseera tacimmata kuwa.

A6angaren Safna kuwa baseera tana Yanke wayar tAk'ara sautin kukanta, tama rasa wane irin sambatu zatayi?, amma jitake Duk duniya babu Wanda ta tsana kamar Rahma arayuwarta, jitake zata iya kashe Rahma wlhy, afili ta ce, "wlhy natsaneki Rahma, natsaneki tsana irin wadda banta6ama wani mahalukiba, Rahma kin cuceni kedasu Ya Shaheed munafukai kawai, duk bakwa sona nimakuwa natsaneku bana sonku harma ya munnir d'in dasu ummi dukna tsaneku, kuka take Rurus da sambatu.

Zeenat Dan ALLAH ki saurareni pls.
Mizaisa na saurareki baseera?, aini yanzu kinfi k'arfina wlhy, keba k'awar rayuwa bace, tunda har kika iya cin amanar safna data d'auki sirrinta Dana gidansu tabaki duka, tonikam sai yaya kenan?, ALLAH abin tsoro kema baseera dole aji tsoron kaidinki, kecefa kika jefa rayuwar Safna a halinnan amma Ashe kina gefe kina cin dunduniyarta, haba baseera miye ribarki Dan ALLAH?, tundaga sanda iyayen safna sukace sun mata miji kika Shiga kika fita kika kanainaye rayuwarta, kin hana afad'a mata gsky bare ta fahimta, saboda son zuciya irin naku yanzu kun koma danku 6ata rayuwar auren k'anwarta, haba baseera kashe aurefa ba abin wasa bane, *_"ALLAH ne ya halatta aure da saki, amma shikanshi bayason sakin aure, duk sanda igiyar aure ta katse sai al'arshin ubangiji ta girgiza saboda kad'uwa, shaitan yakanyi farinciki awannan rana saboda yaraba aure, shin kuma kunaso kuzama daga jerin shaid'anu?."_*
Wlhy kuji tsoron ALLAH kutuba tun kuna da dama, idan kuka bari damarku ta su6uce kunci amanar kanku, kutuba tuba na gsky ALLAH zai iya yafe muku *_"domin shi gafurun rahimunne, kuma maji6incin al'amuran bayine."_*, kuma godema ALLAH daya fargar daku da wuri Dan yana sonku da rahmarsane.
Tunda zeenat tafara maganar baseera kuka takeyi, tabbas ta tafka babban kuskure kuma sharrin shaid'anne, wlhy tayi nadamar halayenta, tarik'o hannun zeenat tana hawaye ngd sosai zeenat kin tunatar dani abinda ban saniba kuma ngd wlhy kinsamu ladana Dan nayi nadamar abinda na aikata, kuma daga yanzu insha ALLAHU zan tuba, zan samu Safna na warware mata dukkan k'ulli, amma inaso ki taimakamin da nuna mata hanya itama, Dan inaso yanda natuba na dawo hanya itama ta tuba ta gyara kodan mugudu tare mu tsira tare.
Jinjina kai zeenat tayi tana murmushi had'eda sharema baseera hawayenta, karki damu 'Yar uwa ngd Nima dakika fahimceni kika kuma gane abinda nake nufi, ALLAH ya yafe mana gabad'aya ya kar6i tubanmu, ALLAH yasa mufi k'arfin zuciyarmu, ina fata yanda kika fahimta da wuri ALLAH yasa Safnama ta fahimta d'in.
Ameen zeenat ngd.
Karki damu muje Dan sir koba hakabane,😜 yakusa Shiga mana, muje muk'arasa lecture d'in muwuce gida.
Jinjina kai baseera tayi tana murmushi suka kama hannun juna suka nufi holl.

😁 _wlhy abinda yaburgeni kuma yamin dad'i masu karatu, ALLAH yasa safna itama ta fahimta kamar yanda baseera tagane kuma ta tuba.🙏🏻ameen._

Su Rahma duk suna kichin suna aikin soya cincin d'in gara, amma jitake zazza6i yana neman rufeta, ga k'asanta yana mata zafi har yanzu ko motsi bata sonyi ma, Ammi dake kallonta tun d'azun ta ce, "Rahma yaya dai?.
Murmushi yak'e Rahma tayi ta ce, " babu komai Ammi."
Aunty Sameera ta ce, "kai Rahma bakida lfy gsky, tun d'azun nima ina lura dake, aunty Rasheeda ta ce, " wlhy nima nakula tundama tashigo batada walwala kamarma tana d'ingishi, kokinji ciwo ak'afarne?.
Shiru Rahma tayi kanta ak'asa, jitake duk kunya ta isheta, itakam bobo yaja mata, yanzu hakama kowa yagane abinda yafaru........
Ammi CE ta katse mata tunani dafad'in tashi muje kisha magani.
Ahankali Rahma tamik'e tana duk'ar da kai, duk sukai mata sannu amma banda safna, azuciyarta ma sai tsinema Rahma takeyi.
Kama hannun ta Ammi tayi suka nufi d'akinta, ta zaunar da ita abakin gado sannan itama ta zauna tana fuskantarta, kallonta take cikeda nazari, ita kam Rahma kanta na k'asa tana wasa da zobenta.
Rahma kodai fad'a kukayi keda mukarram d'in?.
Girgiza kai Rahma tayi ta ce, "a'a Ammi bamuyi fad'aba."
To mike damunki?.
Ammi babu komaifa k'afatace kemin ciwo, shuru Ammi takumayi tana kallonta, zuwa can ta ce, "fad'uwa kikayine?, a'a, to ciwo kikaji kenan?.
Eh, Rahma tafad'a cikeda kunya, ga hawaye suncika idonta taf, bata fata ammi tasake tambayarta wani Abu kuma bayan wannan Dan batasan mizataceba kuma.
Ammi ma batasake cewa komaiba Dan sai yanzu tafahimci komai, amma tayi mamakin hak'urin mukarram dahar ya iya barin Rahma har zuwa yanzun, dawani yagaya mata bazata yardaba, amma gashi tagani da idonta, koda yake tasan duk cikin 'yayanta babu Wanda yakai mukarram kawaici saidai zuciya da masifar tsiya.
Bayi tashiga tahad'a ruwa mai zafi tareda magunguna masu k'au cikin wad'anda takema su khairiyya gyara, fitowa tayi tana fad'in Rahma taso kigani.
Rahma tamik'e tamkar wata muna fuka tanufi Inda ammi take tsaye, bayi ammi tanuna mata da hannu, kishiga ruwa na nan aroba kicire kayanki saiki shiga ruwan, amma saikin daure Dan yanada d'an zafi, idan yahuce kikuma Tarar wani ga maganin nan ajiye aroba saiki kuma shiga kinji, shima saiya huce insha ALLAHU k'afar zata daina ciwo sannu, nima idan k'afata na ciwo dashi nake amfani.
Sanyi Rahma taji aranta Dan duk tunaninta Ammi taganene, amma dataji tace itama dashi take amfani idan tana ciwon k'afa saitaji dad'i, risinawa tayi Tanama Ammi godiya.
Ammi tayi murmushi tana fad'in aii babu godiya tsakaninmu Rahma, kud'inma 'ya'yanane, matsayinku d'aya dasu mukarram araina.
Murmushi Rahma tayi tashige bayi tanamai jin k'aunar tsohuwar aranta, itama jinta take tamkar umminsu.

Ammi tana niyyar fita saiga ya hamza da bobo sunshigo d'akin da sallama.
Baya ammi takoma tana musu sannu, suka gaisheta sannan suka zauna

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login