Showing 45001 words to 48000 words out of 104589 words
wuce nan, wani irin masifaffen sanyi ne, dake ratsa cikin k’ashi da bargo, musamman ga ita da take da asma, gaba d’aya bata son sanyi, saboda had’ari ne ga rayuwarta.
Koda suka k’arasa cikin wajen kuwa, duk suna tsaye lambobin trolleys dinsu ke fitowa.
Saida kowa ya gama d’aukan nasa ne kuma, Rayyern din ya juyo ya kalli Jannart wanda Idanunta suka sanja launi, ga kuma wani irin sautin numfashi da yaji tana fitarwa.
Hannunsa ya mik’a Ahankali ya k’arbi trolley nata, juyowa yayi ya kalli d’aya daga cikin Doctors din.
“Sadiq kira mana taxi.”
“To.”
Sadiq din yace, kana cikin girmamawa ya fita zuwa babban compound din, Airport din.
Sud’inma kuma fita sukayi, dai-dai lokacin kuma Sadiq din ya nuna musu wasu taxi guda biyu.
Wanda ya taro musu, kasancewar acikin airport dinma, masu taxi ne kaca-kaca.
K’arasawa jikin taxi din sukayi.
Rayyern ne ya bud’e k’ofar d’aya daga cikin taxi din ya shiga, Ganin hakane kuma yasa Jannart ma bud’ewa ta shiga da sauri, Dan acewarta ayanzu bata buk’atar wani jira har sai anbata izinin shiga, saboda uban sanyin da takeji, tana k’ara wasu y’an mintuna awaje zai illatata.
Ganin su Rayyern din sun shiga cikin mota ne kuma, yasa sauran Doctors dinma duk suka shiga ragowar taxi din.
Kaitsaye hanyar wani babban hotel din dake cikin garin suka nufa, bisa umarnin Rayyern.
Mik’awa kan titi da sukayi ne kuma yasa Jannart, kwantar da kanta ajikin kujerar motar, tare kuma da Ware dan siririn mayafin Kanta ta rufa ajikinta.
Atunaninta zama a cikin motar zai rage mata sanyi, saidai kuma taji sab’anin haka, saboda acikin motar harda AC.
Idanunta ta d’an rumtse tare kuma da sake matse jikinta, cikin zuciyarta tace.
“Kai amma way’annan mutane akwai mayu, duk wannan uban sanyin bai ishesu ba, har sai sun had’a da AC.”
Rayyern dake zaune agefenta kuwa, gaba d’aya duk yana lura da yanayinta, saidai yi yayi kamar ma baisan cewa tana jin sanyin ba.
Tafiyar mintuna kad’an sukayi kuwa, sai gasu agaban wani had’add’en hotel mai tsananin kyau da tsari *Brosko hotel Arbat Mascow.*
Idanu Jannart ta d’an zaro ta cikin glass din window’n motar, tare da Kallon dogon ginin beneyan hotel din, da bazata tab’a iya misalta kyawunsa ba.
“Kijira ni anan.”
Rayyern din ya fad’a adai-dai lokacin daya bud’e murfin motar ya fice.
Haka ma sauran Doctors din duk sun fito, kaitsaye cikin babban hotel din suka nufa, bayan Rayyern ya sallami sauran masu taxi din.
Kaitsaye cikin katafaren hotel
Din da kaitsaye za’a iya kiransa da Aljnnar duniya suka nufa.
Komai dake cikin hotel din mai kyau ne, kuma abun burgewa, duk da cewar dare ne amma kuma saboda yawan jama’ar dake ta zirga zirga awajen, da kuma wadataccen hasken da ke wajen, yasa wajen ya zamo tamkar rana.
Kaitsaye reception suka nufa, wanda kuma Rayyern dinne keyi musu jagora, kasancewar garin shi ba bak’onsa bane, sab’anin sauran Doctors din nasa, da babu wanda ya tab’a zuwa acikinsu.
Ayau kuma suka sake tabbatar da cewa, kyawun Mascow din ya wuce tunaninsu.
Koda suka k’arasa reception din Rayyern ne yayi musu duk wani abu daya dace, d’akuna 5 ya kama musu, kowannensu da d’akinsa, kud’i ya kashe sosai, domin duk wani abu daya san zasu buk’ata, saida ya umarta da a basu.
Bayan ya sallamesu ne kuma ya juyo, tare da nufo inda Taxi din nasu take.
Dai-dai lokacin kuwa Jannart take k’ara maida hankalinta, akan had’add’en ginin hotel din Brosko Arbat Mascow din, wanda aka k’awata ko ina d’insa da farin haske, ga kuma wasu irin followers wanda ita arayuwarta, bata tab’a ma ganin irinsu ba, domin furannine masu kyau da walwali.
Tsirarun mutanen dake wucewa akan titin ta kalla, kowannensu sanye yake da manya manyan kayan sanyi, daga sama kuwa dusan k’ank’ara ne ke d’an sauk’owa.
Duk da hakan kuwa mutanen wajen rayuwarsu suke normal, da dukkan alama sun saba da yanayin nasu.
Ahankali ya bud’e murfin motar ya shigo.
“Go.”
Ya fad’a yana me gyara zamansa akan kujeran, hakanne kuma yasa Jannart din d’ago Kanta ta kalleshi.
Karab kuwa suka had’a idanu dashi, janye Idanunta tayi daga kallonsa, tare da sunkuyar da kanta k’asa.
Shikuwa Rayyern y’atsun hannunta ya kalla, dai-dai lokacin kuwa driver’n taxi din yaja suka tafi.
Tafiya sosai sukayi kafun suka iso gaban wani dan madaidacin gida, adai-dai wani babban k’ofa wanda gabansa ke cike da shuke shuken furanni mai taxi din ya tsaya.
Wanda hakanne kuma yasa Jannart d’ago kanta, Ahankali ta soma k’arewa wajen da ta gansu din kallo.
Wajene maitsananin kyaun gaske, wanda yake dauke da had’add’un gidajen, da kusan tsarinsu da yanayinsu ya kasance iri d’aya.
Bud’e murfin motar da taga Rayyern yayi ne kuma yasa ta fitowa itama.
Idanunta ta lumshe ahankali, saboda sanyin da taji ya sake shiga jikinta, saurin d’an takure jikinta waje d’aya tayi, saboda zama ta iya cewa, sanyin wajen ya banbanta dana wasu wajaje dake cikin garin, kasancewar arean kowani gida kewaye yake da wasu irin shuke shuke masu Bala’in kyau.
Rayyern kuwa sallaman mai taxi din yayi, bayan ya d’auki trolley d’insa ne kuma, kaitsaye ya nufi jikin wannan gidan, da Jannart ta kasa d’auke idanunta akansa, domin hakanan take ganin ginin tamkar zane.
Ganin kuma Rayyern din na kokarin wucewa, ya barta ne yasa cikin sauri, ta d’auki nata jakar itama, tare da nufan inda taga yabi.
Ahankali take bin bayansa, Yayinda shi kuwa yake k’ara kutsa kansa cikin gidan.
Dai-dai sun iso tsakiyar gidanne kuma, idanunta suka sauk’a akan wani, makeken swimming pool, wanda aka k’awatasa da wani irin ruwa, gefe da gefensa kuwa wani wuta ne me fidda kala kalan haske, sosai swimming pool din yayi mata kyau.
Daga can gefen swimming pool din kuwa, wasu jajayen furannine masu kyaun gaske.
Itakam batasan dame zata tsara had’uwa da kuma kyaun gidan ba.
Atakaice ma ganinta take acikin wata duniya sabuwa.
Isarsu jikin wata k’ofa ne kuma yasa, Rayyern d’an tsayawa, tare da d’aura Hannunsa na dama akan k’ofar.
Wasu na’urori dake jikin k’ofar ne suka d’auki hoton y’an yatsun hannunsa, bayan da kamar second 5 kuwa sai ga k’ofar glass din ta kawo haske.
“Wellcome back Dr. Rayyern Bashir Muhammad Mai-nasara.”
Wata y’ar siririyar murya ta fad’a, Wacce ta fito daga cikin d’an wani na’ura mai kaman camera dake jikin k’ofar.
Na’urar na gama fad’in haka kuwa, lokaci d’aya k’ofar ta bud’e.
Idanu Jannart dake tsaye abayansa, ta d’an zazzaro saboda itakam bata tab’a ganin, security door irin haka ba.
Rayyern kuwa tura kansa ciki yayi, batare kuma da ya juyo ya cewa, Jannart din k’ala ba..
Jannart dake tsaye kuwa Ganin kofar na kokarin rufewa ne, yasa ta jan trolleynta cikin sauri ta shige.
Ahankali ta jefa k’afarta na dama akan wani masifaffen carpet me shegen laushi.
Da sauri ta kalli k’asanta, saboda yanda taji k’afafunta na kokarin nutsewa acikin carpet din.
Ajiyar zuciya ta sauk’e tare kuma da d’agowa, ta sauk’e idanunta, acikin babban falon da ta samu kanta.
Falone daya amsa sunansa falo, haka kuma falo ne da aka zubawa dukiya mai tarin yawa acikinsa.
For the first time da ta somayin k’auyanci arayuwarta, domin zata iya cewa bata tab’a Ganin falo mai kyaun wannan ba.
Komai dake cikin falon na yellow and milk colour ne, more especially cushions din falon, way’anda suke da matuk’ar kyau.
Kasancewar kuma ginin falon nada tsawo ne, yasa aka k’awata jikinsa da wallpaper, brown, milk and golding colour, sai kuma wasu had’add’un cottons masu masifar kyau, kasancewar cottons din farare, shiyasa aka d’an tsara baki bakinsu da brown style.
Atsakiyar falon kuwa, wani d’an madaidaicin carpet ne brown and milk colour, sai kuma brown table da aka d’aura akansa.
Daga can sama kuwa wani abune mai kaman glass babba, wanda ya d’an sako kansa cikin tsakiyar falon.
Sai kuma babban tv plasma dake aje akan wani glass mai kyaun gaske.
Daga can gefe kuwa wani d’an abune mai sheki wanda aka killacesa acikin rose, sai kuma na’urar sanyaya d’aki, da kuma wanda yake saka d’aki d’umi.
Daga can gefe kuwa two bedrooms ne, sai kuma kitchine and dining table.
Jannart dake tsaye kuwa Idanunta ta zubawa cikin falon bata ko k’yaftawa, Yayinda acikin ranta take mamakin irin tarin dukiyan, da aka kashe wajen k’awata falon.
Rayyern kuwa kaitsaye d’aya daga cikin bedrooms din ya nufa.
Ganin hakanne kuma yasa Jannart, ajiye trolleyn ta cikin d’an yanayin matse jikinta, ta zauna akan d’aya daga cikin kujerun falon, tayi hakanne kuma saboda batasan inane zata sauk’a amatsayin masauki ba.
Shiko Rayyern koda ya shiga kayan dake jikinsa ya rage, cikin gajiyawa kuma kaitsaye ya nufi wani waje, wanda nake da yakinin cewa toilet ne, duk da kuwa yanda aka k’awata wajen da gilasai kala-kala.
Ahankali ya murd’a kofar ya shiga, kamar yanda nayi hasashen kuwa hakanne ya kasance, domin nanne toilet din dake cikin d’akin, saidai kuma ganin yanda aka k’awata toilet din, yasa ni tafiya duniyar mamaki, saboda yanda akayi wajen tamkar wajen shak’atawa.
Tabbas wajen ya had’u sosai, ga wanda bai tab’a zuwa ba kuwa dole ne yayi kauyanci.
Anutse ya sakarwa kansa shower, bayan yayi wankanne kuma ya d’aura da alwala, domin zuwa yanzu kusan k’arfe shabiyun dare ake nema, anan wajen nasu.
Ahankali ya bud’e murfin bathroom din ya fito, rike da towel ahannunsa yana me tsare ruwan jikinsa.
Bayan ya kammala goge duk jikin nasa ne kuma, ya k’arasa tare da bud’e trolleynsa, lotion mai dadin k’amshi ya ciro, tare da shafawa ajikinsa.
Bayan ya gama shafa mai dinne kuma, ya saka wani riga da wandon payjamas ajikinsa, mik’a ya d’anyi kana Ahankali ya k’arasa, gaban fridge ya d’auki goran ruwa yasha.
Saida yaji ya koshi da ruwan kafun ya rage hasken wutan dake cikin dakin.
Kaitsaye kan had’add’en gadon dake cikin dakin ya nufa.
Da addu’a abakinsa ya kwanta, tare kuma da lumshe idanunsa, saboda wani irin gajiya da yakeji, Sam kwata kwata shiya ma manta da wata Jannart.
Acan falon kuwa Jannart ne ta sake matse jikinta waje d’aya, akaro na barkatai kuma kenan yanzun, da ta d’aga Idanunta ta kalli agogon dake kafe ajikin bango.
Idanunta ne suka d’anyi narai narai, saboda wani irin fitinannen sanyin dake ratsa ta takota Ina, har wani huci numfashinta ke fitarwa, duk da cewar ta duk’unk’une jikinta waje d’aya, amma hakan baisa ta daina jin sanyin ba.
Ganin Idan ta tsaya ahakan zata cutune yasa ta bud’e Jakanta, wani babban abayanta mai kauri ta zaro, tare da zurawa ajikinta, sake komawa saman kujeran tayi ta mak’ale.
Idanunta ta d’an lumshe Ahankali, saboda Jin sanyin ya d’an ragu mata.
Akan trow pillows din dake manne ajikin cushion din ta d’aura kanta.
Ahankali ta soma sauk’e Ajiyar zuciya, tare da had’e Idanunta ta lumshe.
Duk da cewar tana jin gajiya sosai ajikinta, tana kuma buk’atar son tayi wanka da ruwan dumi, amma babu yanda zatayi.
Sam batasan haka sanyin Mascow’n yake ba, domin taso ace wani yanki na daban dake, cikin Russia din suka zo, bawai Mascow nan ba.
Da wannan tunanin azuciyarta bacci ya d’auketa.
Still kuma ko acikin baccin nata batayi sake, abun rufawar nata ya fad’i ba.
Rayyern dake kwance akan lallausan gadonsa kuwa, sake gyara kwanciyarsa yayi, tare da lullub’e jikinsa da tattausan bargo.
Idanunsa ya d’an lumshe tare da sauke nunfashi cike da nutsuwa, kwata Kwata zuciyarsa ta kasa tuna masa Jannart daya bari a falo, yana nan ahaka har bacci ya d’aukesa.
5:00 am
Dai-dai alarm din dake gefen gadon nasa, ya soma fitar da sautin kara.
Wanda hakan yasa ahankali ya bud’e idanunsa tare dayin mik’a, sunan Allah ya fara ambata, kafun daga bisani ya tashi ya zauna.
Agogo ya kalla, tare da zuro
k’afafunsa k’asa.
Cikin d’an yanayin dake nuna har yanzu yana tare da, gajiya ya d’an lumshe idanunsa, acikin zuciyarsa kuwa tunanin yanda zai fara zuwa masallaci yake.
Saboda yasan tsakaninsu da masallacin akwai nisa, domin ko amota zaije saiyayi 15mn zai isa, Idan da k’afane kuma mutum sai ya share 30mn ma bai isa ba.
D’an ya mutse fuskarsa yayi, saboda gajiyan da yakeji ajikinsa.
Anutse ya tashi daga kan gadon, direct toilet ya nufa, da ruwan d’umi yayi wanka had’e da d’auro alwala, bayan ya fito Daga toilet dinne kuma, ya sanja kayansa zuwa riga da wandon SP, lallausan darduma ya shumfud’a tare da tada sallah.
Adai-dai lokacin ta soma bud’e Idanunta Ahankali, harta gama waresu.
D’an yunkurawa tayi ta tashi, ahankali ta mik’a hannu ta d’auki wayarta dake gefe, Ganin lokacin sallan asuba yayi ne kuma yasa ta, tashi ta zauna.
Ahankali ta soma k’arewa falon kallo, saidai kuma sam bata ga alaman akwai toilet acikin falon ba, gashi duk jikinta wani iri yakeyi mata, ga masifaffen sanyin dake busawa gashi kuma dole zatayi wonkan taci gaba da salla domin tasan zuwa yanzu ta samu tsarki zataci gaba da ibadunta daga sallan asuban.
Ahankali ta ajiye k’afafunta ak’asa tare da mik’ewa tsaye, kallonsa ta mayar ga kofofin d’akuna guda biyun dake cikin falon.
Idanunta ta d’an tsayar akan k’ofar da taga Rayyern din ya shiga jiya.
Ahankali ta sake gyara zaman babban abayan dake jikinta, Cikin yanayin takunta mai d’auke da nutsuwa ta soma takawa, kaitsaye ta nufi d’ayar k’ofar dake hannun hagu.
Koda ta k’arasa bakin k’ofar ahankali, ta d’aura hannunta akan handle din k’ofar, tare da d’an murd’awa, cikin sa’a kuwa taji k’ofar ta bud’e.
Ajiyar zuciya mai k’arfi ta sauk’e, tare da d’an tura kanta cikin d’akin.
Extra room ne mai kyau, wanda gaba d’aya aka malale k’asansa da wani lallausan carpet, Daga can gefe guda kuwa gado ne d’an madaidaici, sai kuma wani long mirror dake can gefe da gadon.
Bayan bedside carbinet kuwa, babu komai acikin d’akin.
Ajiyar zuciya ta kuma sauk’ewa, Ganin kuma akwai na urar dumama daki acikin dakinne, yasa ta juyawa ta koma falo, akwatinta ta d’auko tare da dawowa cikin d’akin.
Bayan ta ajiye akwatin nata ne kuma, tanu fi wani k’ofa dake cikin d’akin hannunta riƙe da miskil dahar ta nufi kofar, wanda take da yakinin cewa toilet ne.
Kamar yanda tayi zato kuwa hakanne, toilet ne me kyau sannan kuma akwai komai na amfani aciki.
Ganin da tayi kuma akwai shower mai bada ruwan dumi ne, yasa ta kwab’e kayan jikinta, Anutse ta sakarwa kanta ruwan d’umin bayan ta tabbatar da tsarkinta.
Wani irin dadi da nutsuwa taji alokacin da ruwan ya sauk’a akan fatar jikinta.
Sosai sanyin da takeji din ya ragu, bayan tayi wankan ne kuma tayi amfani da turaren miskin kamar yadda ta saba kana ta had’a da alwala.
Wani babban bathrobe ta saka, tare da bud’e kofar bathroom din ta fito.
Cikin d’an hanzari gudun kada sanyi ya dake shiga jikinta, ta jawo akwatinta tare da bud’ewa, ta zaro wata had’add’iyar riga mai kaman na sanyi, duk da kasancewar rigar english wears ce amma tana da kauri sosai, saidai bata da yawan tsawo domin da kad’an ta wuce mata guiwa, domin rigane irin fashion dinnan.
Koda tasaka rigar cas tayi mata, musamman da rigar ta kasance irin mai kwala dinnan ne.
Tubke dogon gashinta tayi, tare kuma da d’aukan safa mai kauri da tsawo ta sanya ak’afafunta.
D’aya daga cikin sallayun da tazo dashi ta shumfud’a, tare da zura wani dogon hijabin daya rufe mata duk jikinta, bayan ta kunna na’urar dake d’uma d’aki ne kuma, ta koma kan sallaya tare datada sallah.
Bayan ta idar da sallan tayi azkhar ne kuma ta koma ta kwanta akan lallausan gadon, tare da jan blanket ta rufe jikinta.
Wani irin ajiyar zuciya mai karfi ta sauk’e, badon komai ba kuwa, saidan nutsuwar da taji ta samu.
Acan b’angaren Rayyern kuwa Koda ya idar da sallah, karatun Alqur’ani yayi, bayan ya idar da karatunne kuma ya soma shirya kansa.
Saboda zuwa lokacin har k’arfe 7 tayi, hasken sararin samaniya ya bayyana ko ina.
Tsab ya shirya cikin wani had’add’en suit da yayi matuk’ar amsar jikinsa, takalmin Gucci da kuma Gucci parfume ya fesa ajikinsa.
Sosai yayi kyau yau din, Yayinda suit din ta k’ara fito dashi, amatsayin babban likita, yayi kyau ainun, briefcase da kuma wayoyinsa ya dauka.
Ahankali ya murd’a handle din kofar d’akin ya fito, yana me gyara agogon dake daure atsintsiyar hannunsa.
Wayarsa dake rik’e ahannunsa ne ta soma k’ara, alaman shigowar kira, picking call din yayi tare da kara wayar akan kunnensa, batare kuma da ya gama sauraran, abunda ake fad’a masa acikin wayan ba, cikin d’an yanayin gaggawa yace.
“I’m on my way.”
Yana gama fadin hakan ya zare, wayar daga kan kunnensa, cikin sauri kuma ya fice daga cikin falon.
Kaitsaye babban titin dake k’ofar gidan ya nufa, tsayawa yayi abakin titin tare da d’an soma lallatsa wayarsa, da alama sak’o yake turawa.
Bayan ya gama tura sak’onne kuma, ya maida wayar tasa cikin aljihun sa.
Almost 10mn kacal wata had’add’iyar mota ta k’araso inda yake, parking motar akayi, cikin sauri kuma baturen dake cikin motar ya fito, aladabce ya mik’awa Rayyern din key din motar.
Cikin muryar turanci baturen yace.
“We’ll come back Sir.”
“Thank you Jonas.”
Rayyern din ya fad’a atak’aice tare kuma da bud’e murfin motar ya shiga, wanda da dukkan alama dama, yana da motar Wacce Idan yazo k’asar yake amfani da ita, kasancewar ak’asar yayi karatun Degree d’insa na biyu, wannan dalilin yasa yake zaune a gidan da yake mmkin yadda akayi Abbansu ya mallakeshi anan k’asar ta Russia.
Jonas shine Wanda yake kula da komai na gidan dama duk wani abu nasu, duk da ya manyata.
Koda zuwa ya kamashi, shi yake gayawa ya gyara musu komai.
Jonas din ne ya rufe masa murfin motar, shi kuwa Rayyern cikin k’warewa yaja motar yayi gaba.
Ganin Dr. Rayyern din ya tafi ne kuma yasa, Jonas tare taxi ya koma inda ya fito.
Rayyern kuwa kaitsaye babban hospital din, dake cikin garin Mascow ya nufa, kasancewar tuntuni ya bawa sauran Doctors din, umarni akan su had’u acan hospital din, so already ma sunje shi kawai suke jira.
A hankali ya kusa hancin motarsa cikin farfajiyar.
*HSCT centre Mascow*
Cikin parking space na hospital din yayi parking, Cikin nutsuwa ya fito, tare da nufan cikin hospital din da tafiyarsa ta k’asaita...!
By
*GARKUWAR FULANI*Yana isa farfajiyar asibitin su Dr. Sulaiman dake jiransa, suka k’araso garesa da sauri, hannu ya basu suka gaisa, bisa jagorancinsa kuma kaitsaye suka wuce, wani babban sashi na musamman dake Cikin hospital din.
HSCT centre Hospital ne me kyaun gaske wanda aka yi masa tsari mai kyau, komai dake cikinsa na musamman ne sabida shine babban asibitin