Showing 93001 words to 96000 words out of 104589 words

Chapter 32 - Tubali Book 2 Hausa Novel Complete

Unknown   

21 Dec 2024

179

ya sake jiyo, ringtone din wayarsa akaro na biyar, wanda yake tashi daga can cikin falon.

Ahankali ya zuro da k’afafunsa k’asa, saboda baisan wanene mai kiran nasa da wannan lokacin ba, bud’e kofar dakin yayi tare da kutsa kansa cikin falon, Ganin wutan falon akunne ne kuma, yasa da mamaki ya karaso cikin falon.

Dai-dai yazo tsakiyar falonne kuma, kunnuwansa suka jiye masa yanda sautin, numfashin Jannart din ke fita, tamkar Wacce zata shid’e, domin da dukkan alama numfashinne ya k’wace mata.

Da sauri ya juyo ya kalleta, tare kuma da maida dubansa ga way’ansa Wacce take ta k’ara.

Screen din wayar ya kalla, ganin kuma sunan Barrister Kabir ne, ke yawo akan wayar yasa shi sake dawo da kallonsa ga Jannart din, cikin wani irin yanayi yake kallonta.

Saidai kuma ganin kiran wayan na shirin katsewa ne, yasa shi daukar wayar tare da karawa akan kunnensa.
Daga can b’angaren kuwa Barrister Kabir din, jin Rayyern ya d’aga wayarne yasa cikin tashin hankali yace.

“Rayyern wani ya ganku yau?”
Yanayin yanda Barrister Kabir din yayi, maganar kamar adan tsorace ne kuma yasa Rayyern din gyara tsayuwarsa.

“Eh wani ya ganmu wani wanda bansan ko waye ba, ita kuma harda rungumeshi tayi, bansan dalilin ta nayin hakan ba.”

Rayyern din ya fad’a yana me kura mata idanu, fuskarsa kuwa ahad’e take, daga jin yanayin muryarsa kuma kasan cewa, ransa amatukar bace yake har yanzu.

Abba Kabir kuwa jin abunda Rayyern din ya fad’a ne, yasa shi dan yin shiru, kana kuma asanyaye yace.

“Azeez ne Tabbas Azeez da gaske yake yaga Jannart, nasan Kai baka sanshi ba amma ita ta sanshi, saboda yayanta ne d’an Alhaji Idi Sale Dakata ne.”

Fuska Rayyern din ya dan ya mutsa, still cikin rashin sakewa yace.

“Oh haka ta fad’a but I don’t trust her, cause naga tayi hugging nasa.”
Haka nan yaji yana ta maimaita gayawa Barrister Kabir yaga ta ruggumeshi like yana kai kararta ne garesa.

Ajiyar zuciya Barrister Kabir ya sauke, fahimtar wani abu dake sukar zuciyar Rayyern din da yayi ne kuma yasa shi, Dan tausasa murya kana asanyaye gane azabebben kishine ke cinsa yace.
“I’m sorry Rayyern yayanta ne da gaske kamar yanda ta fada ma, yanzu Ina Jannart din take.”

Kalonsa ya maida ga Jannart din, cikin kuma haushin ta da yakeji yace.

“Gatanan wai fushi takeyi dani dan na hanata ruggumeshi sai wani numfashi takeyi sama-sama.”

Ya fad’i maganan in don’t care manner.

Abba Kabir kuwa jin hakanne yasa, cikin tashin hankali yace.

“What Rayyern numfashi sama-sama kuma? Please check her tana da problem fa.”

Abba Kabir din ya fadi haka cikin gaggawa.

Wanda jin hakanne kuma yasa Rayyern kashe wayan, da sauri ya k’arasa kanta, saboda ganin yanda take ta mimmik’ewa.

“Ke.”
Ya fad’a yana me d’an zungurinta da k’afansa.

Ko kallonsa baiga tayi ba balle yasaka ran zata amsa masa, saidai har yanzu numfashin nata bai daina k’wacewa ba.

Ganin hakanne kuma yasa shi d’an rank’wafowa kanta, idanunsa ya d’an kura mata Ganin abun nata like serious ne ya sashi cewa.

“Hey what’s wrong with you Janna?”
Kanta ta d’an soma girgizawa, Ahankali kuma Cikin sheshshekan numfashi ta kamo hannunsa wanda ya dafe saman kujera dashi.

D’aura hannun nasa tayi akan chest dinta, cikin wani irin yanayin dake nuna galabaitar ta, murya na rawa tace.

“Pl...Please Na... Naan zan mutu numfashina, ka taimakeni Naan mutuwa zanyi, numfashina zaibar jikina, help....... help......me”.

Ta karasa maganan cikin shakewar murya, lokaci daya kuma Idanunta suka soma juyewa.

Idanunsa ya zuba mata cike da mamaki, hadi da kuma tashin hankali yake kallonta.

Murya na dan rawa yace.

“Janna open your eyes and tell me what’s wrong? Tell me Janna meyeke damunki fad’amin kinji faɗa wa Naan ɗinki?.”

Yayi maganan yana me daura hannunsa akan wuyanta.

Jannart kuwa duk ta fara ficewa a hayyacinta, Yayinda hawaye ke bin gefen fuskarta yana kwarara, tanason gaya masa cewar Asthma dinta ne ya tashi, amma ta kasa saboda numfashinta dake seizing.

“Naaaaaannnnnnnnn Numfashinaaaaaaaaaa.....”

Da k’yar ta fadi hakan afusge, lokaci daya kuma numfashin nata yayi low, take kuma Idanunta suka lumshe.
Cikin hanzari mamaki, tsoro, rawan jiki, da kuma tashin hankali Rayyern din yasanya duka hannayensa ya kama kafad’unta, hankalinsa amatukar tashe yace.

“Janna! Jaannaa!! please open your eyes, Janna are you okay? Janna weckup please..”

Ya kare maganan yana me jijjigata, hankalinsa atashe Ganin bata ko motsa bane, kuma yasa shi d’aukarta tare da rungumota jikinsa.

Tamkar wata Y’ar tsana haka ya d’auketa, Cikin hanzari kasancewar kuma key din motarsa yana cikin falonne, yasa yana dauka baijirayi komai ba, kaitsaye ya nufi hanyar fita daga falon.

Koda ya fito gudu ya fara Yayinda Jannart din ke cikin jikinsa, kasancewar kuma Acan sama d’akin nasu yake ne, shiyasa dole saiyayi tafiya mai nisa kafun ya sauko.

Hakan kuwa shiyasa duk inda yazo wucewa sai ankalleshi, Yayinda ma’akaitan hotel din ke tambayansa ko lafiya.

“She’s patient.”
Shine kawai abunda yake fad’a musu.

Ahaka har ya sauko kasa, inda yayi parking motarsa.

Ak’agauce yayi bud’e murfin motar ya shiga, agefensa ya kwantar da ita.
Tare da yiwa motar key a 360 ya ja motar yayi gaba.

Gudu yake sosai akan titin kasancewar kuma, dare yayi sosai shiasa babu yawan ababen hawa akan titin.
Wannan dalilin yasa cikin mintuna kad’an ya iso harabar babban asibitin, wanda ya kasance shine mafi kusa dasu.

Yana zuwa kuwa ko gama dai-dai-ta parking din motar baiyi ba, ya fito tare da ita ajikinsa.
Kaitsaye ya nufi cikin asibitin.

Ganinsa da Doctors sukayi ne kuma, yasa kaitsaye suka kawo gadon marassa lafiya, aka d’aura Jannart din akai.

Kaitsaye aka wuce da ita emergency, dan bata taimakon gaggawa, kasancewar tuni numfashinta yayi nasa gun.
Dole kuma sai an saka mata oxygen.

Kasancewar kuma Hospital din na d’aya daga cikin, inviglators din da suke koyar dasu abubuwa ne kuma musulmine, yasa aka yiwa Jannart din tarba mai kyau.

Domin Koda aka tashi shigar da ita Emergency din, tare da Rayyern aka shiga.

Gaba d’aya ya kasa ta b’uka komai, saidai idanu daya zubawa kan fuskarta, wanda aka sakawa Oxygen.

Yayinda sauran Doctors din kuwa, suka shiga checking dinta, saboda akwai hanyoyin da zasubi wajen Ganin hakikanin abunda ke damunta.

Shikuwa Rayyern Ganin hakanne yasa shi zaro wayarsa, tare da fita daga Emergency din.

Numbern Dr. Sulaiman ya kira saidai kwata kwata baya shiga.
Hakanne kuma yasa shi kiran layin Ramadan.

Cikin sa’a bugu biyu kuwa Ramadan din ya d’auki wayar.

“Ramadan.”
Rayyern ya kira sunansa cikin yanayin damuwa, batare daya bari Ramadan din yace wani abu ba kuma yace.

“Please Ramadan Jannart bata da lafiya, kwanaki da aka kawota Hospital namu meyake damunta?”
Yayi mgnar cikin ruɗu sabida bai san tanada matsalar numfashi ba.

“Subahanallah Hamma Rayyern meyake damunta yanzun? Ina take yanzu?”

Ramadan din ya fada cikin tashin hankali.

“Stop Ramadan ka amsamin tambayata.”

Rayyern din ya fada cikin zakuwa.

“I’m sorry Hamma Rayyern bani na kula da issues din nata ba, Dr. Sulaiman ne, kuma bansan meye problem din nata ba, but ka tambayi Dr. Sulaiman?”

“Way’ansa akashe Ramadan are you in Hospital?”

“Yeah.”Ramadan din ya bada amsa, saboda dama yana Cikin Hospital din, kasancewar yau din night duty ne dashi.

Ajiyar zuciya Rayyern ya sauke, tare kuma da gyara tsayuwarsa cikin gaggawa yace.

“Okay kayi checking folder dinta, date folder 24/2/2020 please Ramadan hurry up.”

“Okay I will.”
Ramadan din ya fada tare da kashe wayan.
Kaitsaye kuma ya tashi ya nufi inda suke ajiyan folders dinsu.

Rayyern kuma tsayuwa yayi tare da zubaw fuskar Jannart din idanu, kasancewar daga inda yake tsaye din yana iya hango fuskarta ta jikin wani glass.

Jin wayarsa na kara ne kuma yasa shi, saurin dagawa tare da kara wayar akan kunnensa.

Ramadan kuwa jin Rayyern din ya d’aga ne, yasa shi cewa.

“Hamma Rayyern banga foldern Jannart ba fa, babu nata kwata kwata saidai ga wani nan, da nagani amma sunan da aka rubutu, shine Jannart Abdulkarim Sale Dakata.”


“What Abdulkarim Sale Dakata!!”

Rayyern din ya fad’a cikin mamaki, da kuma wani irin tunani da yaji ya tsaya masa Acikin zuciyarsa.

Saidai kuma ganin babu lokaci ne yasa, shi cewa.
“Meye problem din mai folder din? Sannan shekarunta nawa?”.

“22. Asthma.”
Ramadan ya fad’a yana me jujjuya folder din, dake hannunsa.

Rayyern kuwa jin hakanne yasa shi, kashe wayan tare da juyawa ya nufi cikin emergency room din.

Koda ya shiga kuwa ya samu har sun Gano matsalarta, Cikin ikon Allah kuma har sun shawo kan matsalar nata.

Domin numfashinta ya dai-dai-ta sun kuma yi mata duk wani abu daya dace.

Saidai har yanzu basu cire mata oxygen dinba.

Ahaka aka kaita har zuwa dakin hutu.

Agefenta ya zauna tare da zuba mata ido,
A hankali ya lumshe idanunsa tare dasa hannunsa bisa hannunta dake gefensa,
Wani irin sassayan numfashi ya fesar lokacin daya haɗe tafin hannunnsu wuri ɗaya.
dai-dai lokacin ne kuma wayarsa ta soma kara, alaman shigowar kira.

Kallon screen din wayar yayi, Ganin kuma sunan Barrister Kabir ne ke yawo akan wayar, yasa shi d’aga kiran.

Yana karawa akan kunnensa Daga can b’angaren Barrister Kabir yace.
“Rayyern ya Jannart din, fatan tana lafiya?”

Shiru Rayyern din ya d’anyi, kamar bazai amsa ba can kuma, cikin dakiya yace.

“Barrister Waye Abdulkarim Sale Dakata?....!
*GARKUWAR taku ce dai MA'AURATA, da masu shirin aure, da masu jego, da yan gayu masu son k’amshi kece raini, da gyaran da zaike maimaita muku dararen forkon kuruciya*

Ko kunsan Jikinmu na da sinadaran hormones da suke taimakawa dan’adam akan komai musamman lokacin da mace take mu’amalar aure da mijinta. Mafi akasari wannan hormones din ne ke samun matsala ko su yi sanyi koma su daina aiki kwata-kwata shi ne dalilin da zai sa mace tace bata jin sha’awa ko bata san dadin aure ba. Albishirinku ina da kayan da ke taimakawa wannan sinadaran du dawo aiki tukuru don karkato miki da kimarki wajan mai gida sannan su taimakawa wannan sinadaran hormones dinki su dinka secreting din ni’ima wadatacciya da zata taimaka miki ki gamsu mijinki ya gamsu fiye da tunaninki. Note: Kayana ba sa tsinka ruwan ni’ima suna dai taimakawa hormones dinki ne su tsattsafo da ni’imar musamman wacca cutar sanyi ko dattin mahaifa ya dankarar da su ya hana su yin aikinsu yanda ya kamata. Haka zalika idan kina da kyau ki kara da wanka. Zaki iya amfani da magani na na gargajiya wanda zai gyara miki sex hormones din kullum ki kasance cikin humidify wato cikin damshi mai albarka kamar yanda ake son mace. Yana gyara miki mara.

Sai kamshi. Hajiyata daure ki fara amfani da turarena ki ji irin salon kamshin sa salo ne da zai daidaita ki da mijinki ya kankaro miki da kimarki a wajansa. Siyan na gari mayar da kudi gida.

Ga masu buƙata ga number' wayata wanda nake whatsApp dashi 09097853276 kimin mgn ta whatsApp in har kin tabbatar kin shirya saya mu dai-dai ta, kayana ba ƙanana bane, shiyasa bana harkan karanta, muddin kinsan baki shirya sayaba Please kada kiyi min mgn ki bari sai kin shirya kuɗinki a hannu, ba ina nufin kayana bana talaka bane, no akwai ƙananan set na masu karamin karfi, banson aimin mgn a ɓatamin lokacin aiyukana a shirme baki shiryaba. Skarantan da bana so.
0005388578 Jaiz bank AISHA GARKUWA ALIYU. In kin shirya ga number ta ga kuma account number ta wanda in mun gama mgn zaki turo kudin ki, kana insa miki kaya a mota, duk ƙasar da kike kayana zaije gareki, amman fa in kinada dalilin zuwan nasune🤝🏻sayan na gari meda kudi gida.

GARKUWAR MA'AURATA
By
*GARKUWAR FULANI*Wata iriyar bugawa zuciyar Barrister Kabir tayi, wanda har saida Rayyern din yaji sautin kakkarfar Ajiyar zuciyan daya sauk’e.

Ahankali kuma Cikin sanyi dason b’oye babbar damuwarsa yace.

“Barrister Abdulkarim Saleh Dakata yayana ne, sannan kuma k’anin Alhaji Idi Saleh Dakata ne, mu ukun duka acikin mahaifiya d’aya muka fito, haka ma kuma babanmu d’aya, amma Dr. Rayyern me yasa kayi min wannan tambayar?”

Barrister Kabir din ya tambaya, cike kuma dason jin amsar abunda ya tambayan.

Rayyern kuwa jin abunda Barrister Kabir din ya fad’a ne, yasa shi juyawa ahankali ya sauk’e idanunsa akan Jannart dake kwance, Wacce take shak’an numfashi ta Oxygen.
Yanayin yanda take kwance flat ne kuma yasa, Idan ba mutum ya kula da cewar tana shak’an numfashi ta oxygen ba, to direct zakayi tunanin matacciya ce, Dan babu wani abu na jikinta dake motsawa sai zuciyarta.
Murza tafin hannunta dake cikin nasa yayi tare, da ɗan ɗago hannun nata sama ya manna shi kan tattausan sajensa.Ahankali kuma ya janye kallonsa daga gareta, tare da rumtse idanunsa, cikin dakiya ya gyara tsayuwarsa kana yace.

“I’m sorry to say Barrister ba dangartakar ku dashi nakeson sani ba, inason sanin matsayinsa da kuma alak’arsa da Matata Jannart ne?.”

Wani irin dogon numfashi hadi da ajiyar zuciya, Barrister Kabir ya sauke, lokaci daya kuma duk idanunsa suka ciko da hawaye dan abubuwa biyu da suka zo masa lokacin daya kalmar matata da Rayyern ya kira Jannart da ita shine karsashinsa, son jin alak’anta da Barrister Abdulkareem Saleh Dakata kuwa shine mafi rinjayen rauninsa a rayuwar duniya, haka kuma damuwa mai tarin yawa ta bayyana akan fuskarsa, domin tambayar da Rayyern din yayi masa, ya tono masa wani rauni da kuma mikin dake kwance a zuciyarsa.

Asanyaye kuma cikin son kawar da maganan yace.

“Rayyern mubar wannan maganan, yanzu ka fad’amin wanni hali Jannart take ciki?”
Ya k’are maganan cikin raunin muryar da tasa, zuciyar Rayyern karaya, saboda ayanda yaji ak’asan muryar Barrister Kabir din, tsananin damuwa ne da kuma wani abu mai kama da fargaba.

Idanunsa dake alumshe ya d’an bud’e, kana cikin yin k’asa da murya yace.

“Zataji sauki da yardar Allah, saboda na kawota hospital dan yanzu haka ma oxygen ne ahancinta.”

Still ajiyar zuciya mai karfi Barrister Kabir din ya sauke, cikin tarin yanayin damuwa kuma yace.

“Allah Ya bata lafiya, kayi hakuri Rayyern Dan Allah ka kulamin da amanata, Jannart tana da buk’atar kulawarka ako da yaushe, Jannart marainiyace kada ka manta kuma duk wanda ya kula da maraya , Allah zai kula dashi sannan zaiyi masa Garkuwa aranar tashin Alk’iyama, Dan Allah Rayyern ka kula sosai, saboda tana da cronic asthma, nasan baka san da hakan ba, amma dole saika kiyaye wajen rabata ta'ammali da abu mai sanyi.”
Idanu Rayyern din ya kuma alumshewa kana ahankali, kuma cikin sanyi yace.

“Insha Allah zan kula da hakan, soon kuma zata samu sauki.”

“Allah yasa haka Rayyern, sannan kayi hakuri da ganinku da Azeez yayi, ya kuma tashi hankalinsa akanku ne, saboda yana d’aya daga cikin mutanen da suke kamar kashin bayan farin cikin Jannart, yana nuna tsananin kulawarsa agareta, shiyasa itama Jannart din da ta gansa, ta kasa hakuri har saida taje garesa.”

Kai Rayyern din ya dan jinjina, batare kuma daya sake cewa komai ba, ya maida idanunsa ya lumshe.

Barrister Kabir kuwa ci gaba da cewa yayi.

“Tabbas plan dinmu yaso lalacewa saboda ganinku da Azeez din yayi, amma Allah ya rufa mana asiri, saboda Koda Azeez ya kira wayan Alhaji Idi Sale Dakata, dan sanar dashi cewar yaga Jannart, wayar bata shigaba Wannan dalilin ne kuma, yasa Azeez din ya kirani, sanin bani da wata hujja ta karya da zan iya fad’a masa, Wacce zai gamsu da ita ne kuma, yasa na sanardashi gaskiya da kuma hakikanin abunda ke faruwa, saidai na fad’a masa cewar akan matsalar dake tsakaninta da Junaid ne yasa aka b’oyeta.”

Ajiyar zuciya Rayyern din yayi, tare da fesar da wani iska daga bakinsa.
Cikin kuma d’an yanayin rashin gamsuwa yace.

“Amma kana ga fad’a masa hakan bazai zamo matsala, ko sanadin rugujewar komai ba?”

“Bazai zama ba Rayyern, nasan Azeez nasan waye shi bazai tab’a fallasa abunda na fad’a masa ba, duk da na b’oye masa wasu abubuwan, amma nasan shikansa bayason irin cutarwar, da d’an uwansa Junaid ke nunawa ga k’anwar tasu, saboda haka karka damu Azeez zai iyayin komai dan bawa Jannart kariya, musamman ayanzu dana gargad’esa da kar ya fad’awa kowa, ya kumayi min alk’awarin cewa bazai tab’a fad’ad’in ba zuwa gaba kuma zan sanar dashi dukkan abinda bai saniba.”

Again numfashi Rayyern din ya fesar, cikin kuma maida kallonsa ga Jannart din dake kwance yace.

“Shikenan ba damuwa.”

Shima Barrister Kabir din Ajiyar zuciya ya sauke kana anutse, cikin maida hawayen dake kwance acikin idanunsa yace.

“Rayyern akwai lokacin da zaka san waye Abdulkarim Saleh Dakata da alak’arsa da matarka, saidai kuma ba yanzu ba, amma kamar yanda Kaga Azeez haka shima yake, domin duk wani suffa da kamanninsa Azez ne ya d’auka, domin sometimes Idan Jannart tana tambaya na, akan kamannin Baffan nata Abdulkarim Saleh Dakata, saboda bata sanshi ba nakan ce, ta kalli Azeez domin idan taga Azeez kamar photo copy d’insa ta gani, saboda tsananin kamar da sukeyi....”

Ya k’are maganan cikin wata irin muryar, dake bayyana alaman kuka, wanda hakanne kuma yasa shi, tsagaitawa da maganan.

Rayyern kuwa jin hakanne yasa shi, d’anyin shiru acikin zuciyarsa yana me mamakin abunda, zaisa Barrister Kabir din awannan yanayin, Lallai Tabbas yasan cewa akwai wani abu, da Barrister Kabir din yake b’oyewa, more especially yanzu da yayi masa tambaya, akan Abdulkarim Saleh Dakata, meyene To wannan abun?

Itace tambayar da bashi da amsarta.

Ganin shirun yayi yawa ne kuma yasa shi cewa.

“Allah ya jik’ansa da rahama, yasa can yafi masa nan.”
“Ameen summa Ameen nagode matuk’a Rayyern.”

Barrister Kabir din ya fad’a cikin wani sabon sheshshek’an daya zo masa, Jin da yayi kuka mai sauti na shirin k’wace masa ne kuma, yasa shi ajiye wayan batare kuma daya katse kiran ba.

Araunace ya kifa kansa akan pillown dake hannunsa, cikin tarin damuwa da kuma ciwon da yakeji aransa, ya saki kuka mai tsuma zuciya.

Dai-dai lokacin kuma Aunty Dijat dake tsaka da bacci ta farka, tare da bud’e Idanunta arazane, saboda sautin kukan mijin nata da taji.

Ganinsa da tayi azaune yana kukanne kuma, yasa ta matsowa inda yake tare dasa hannunta ta dafa shoulder d’insa.

Tabbas tasan abunda yakesa mijinta kuka, alokuta daban daban, musamman ma dai Idan tagansa a irin wannan yanayin.

Araunace kuma cikin sanyin da jikinta yayi tace.

“Abban Hafeez.”

Jin muryar matar tasa acikin kunnuwansa ne, yasa shi dagowa ya kalleta lokaci daya kuma, ya maida kansa ya d’ora acinyarta.

Cikin muryarsa dake fitar da Amon kuka yace.

“Dijat zanyi rashi biyu asanadin rashi d’aya, nayi rashi d’aya acikin shekaru 22 da suka wuce, sannan kuma sanadin wancan rashin, zan sakeyin wani rashin anan kusa, Dijat Ina kukane saboda inason y’an uwana, banason rasa su, amma ya zanyi Dijat nasani dole zamu rabu, k’addara da jarrabawar Ubangiji zata rabamu,

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login