Showing 90001 words to 93000 words out of 104589 words
finciko hannunta ya fito da ita daga cikin motar.
Ransa ab’ace yake sosai shiyasa bai damu, dako dusan k’ank’aran dake saukowa yana sauka akansu ba.
Musamman ita Jannart da bawani kayan kirki bane ajikinta, wanda tun acikin motan dusan k’ank’aran ya bata mata jiki.
Kaitsaye wani park dake cikin hotel din suka nufa, suna isa wajen kuwa Rayyern din ya rike hannunta gam, tare da sunkuyawa ya durk’usar da, ita ak’asan wasu shuken shuken flowers suka zauna bisa kujera.
Batare kuma daya damu da irin yanda dusan k’ank’aran ke dukansu,
Still har yanzu kuma yana rike da hannunta.
Saidai yanzun tafin hannayensu ne ke had’e.
Dai-dai lokacin kuwa Yah Azeez ya shigo cikin hotel din, ganin motar mutumin dake tare da Jannart din da yayi a fake ne, kuma yasa shi saurin yin parking nasa motar shima, cikin hanxari kuma ya fito tare da nufan cikin hotel din Kaitsaye, saboda shi atunaninsa sun shiga cikin hotel dinne.
Rayyern kuwa da yake Kallon Azeez din, ganin ya shiga cikin hotel dinne, yasa shi yin kwafa tare da sake jawo Jannart din, kaitsaye ya nufi wajen motarsa.
Bayan sun shiga ne kuma yaja motar suka kara gaba.
Idanunta ta rumtse da karfi, tare kuma da matse jikinta waje daya, sosai jikinta yake karkarawa wanda hakan yasa numfashinta wani irin fusga sabida abubuwan sun had’e mata ga sanyin da tasha, ga na garin ga tsoro hakan yasa numfashin ya fara sauya salon fira.
Har yakai ga sautin fitan numfashin nata, na ratsa cikin kunnuwansa.
Juyowa yayi ya dan kalleta, tare kuma da watsa mata Harara, cikin zafin zuciya ya cigaba da tuk’a motar, yana shara gudu tamkar mai tashi sama.
Acan hotel kuwa Yah Azeez Kaitsaye receiption na hotel din ya nufa, saidai koda ya tambaya ko akwai mutanen da suka shigo yanzu, ce masa akayi babu.
Wannan dalilin yasa asanyaye ya fito daga cikin hotel din, yana fitowa kuwa idanunsa suka sauka, akan wajen daya bar motar Rayyern din.
Ganin babu motar awajenne kuma yasa shi dafe kansa, cikin takaici yace.
“Oh My God I lost them, who be this guy? Waye shi meye hadinsa da Jannart, nasani Jannart ba mutumiyar banza bace, saboda haka babu yanda za’ayi ace, tana da alak’a da mutumin da baisan koshi waye ba.”
Tsuka yaja tare dasa hannu ya buga sterring motarsa, cike da takaicin rasa su da yayi yace.
“Ina fatan sake ganinki Jannart, wancan guy din kuwa ko waye shi, saina koya masa hankali, koma meye ne ya faru asanadiyarka ne Junaid, saboda Kai da kuma banzan halinka ne, Jannart take cikin duk wannan yanayin, huuhhhhhhh.”
Ya fesar da wani irin numfashi mai zafi.
Asanyaye kuma cikin takaici ya koma cikin motarsa ya zauna.
Acan b’angaren Jannart kuwa zuwa yanzu, karfin hali kawai takeyi wajen kwato numfashinta, saboda wani irin sanyin da takeji, yana ratsa har cikin k’ashi da b’argonta.
Wannan dalilin yasa ta kankame jikinta waje daya.
Dai-dai lokacin kuma Rayyern din yayi parking motar, acikin wasu jerin motoci dake gaban wani had’add’en garden d’in Hermitage garden Mascow, wanda aka wadatasa da yalwan haske tako ta ina.
Ahankali ya zare sit belt din dake jikinsa, tare kuma da juyawa ya kalli bayansa, Ganin kuma babu wata mota dake bin bayansu ne, yasa shi bude murfin motar ya fito.
Still zagayawa gefenta yayi ya fito da ita, duk da cewar yanajin irin karkarwar da hannunta daya rike keyi, amma haka ya share tare da hade fuskar sa domin shi kansa bai san iya azabar fushin da ke ransaba wanda bai san na menene ba, ko kallonta kuwa baiyi ba sabida wani irin zafi da tafasa da zuciyarshi keyi ko gyabta idonsa yayi ganinta yake ruggume jikin Azeez, kaitsaye ya nufi cikin Garden din.
Suna shiga cikin kuwa ya sake hannunta, tare da nufan wani privet sit ya zauna.
Ahankali kuma ya juya yana me watsa mata Harara, saboda wani takaicin da yakeji, abanza ta jawo masa b’uya tamkar wani marar gaskiya ko b’arawo.
Jannart kuwa da duk jikinta ke karkarwa, Ganin irin Kallon da Rayyern din ke watsa mata ne, yasa ta kame jikinta waje d’aya, tare da rumtse Idanunta, saboda wani irin sanyi da takeji.
A kujeran dake facing nasa ta zauna, tare da sake kankame jikinta waje daya, hakanan ta samu kanta da wani irin tsoronsa, wanda ita kanta batasan kona meye ba.
D’aya daga cikin waiter na wajenne ya k’araso, tare da Dan rusunawa ya tambayesu me za’a kawo musu.
“Coffee.”
Rayyern ya bashi amsa atak’aice, Yayinda kasa kasa kuma yake hararan Jannart din, wanda daga inda yake din yana iya jiyo yanda, numfashinta ke fusga tamkar Wacce zata wacce tayi tsare.
Bakinsa ya d’an tab’e tare da kawar da kansa gefe, domin acan cikin zuciyarsa har yanzu, wani irin b’acin rai yakeji.
Cikin abunda bai wuce 5mn ba, waiter din ya kawo musu coffee two cup, wanda yake ta faman tururi saboda zafin da yake dashi.
D’an d’ago Kanta tayi ahankali ta saci kallonshi, Ganin kuma ba ita yake kallo bane yasa ta, d’aukan coffee din da sauri ta Kai bakinta.
Idanunta ta d’an lumshe tare da sauke ajiyar zuciya, domin duk da cewar coffee din akwai zafi sosai, amma hakan bai hanata kaiwa cikin bakinta ba.
Saidai kuma saboda tsananin sanyin da akeyi, yasa zafin Coffee din bai kona mata baki ba, madadin haka saima wani irin nutsuwa da taji yana saukar mata, Yayinda dumin Coffee din ke dumama mata hanjin cikinta.
Jin dadin hakanne kuma yasa ta shanye coffee din lokaci guda, domin dama bawai wani yawa ne dashi ba.
Ajiye cup din nata tayi ahankali tare kuma da turo dan karamin bakinta gaba, cikin rauni da kuma yanayin tsoronsa dake damunta, ta turo d’an k’aramin bakinta gaba.
Still Ahankali kuma ta soma motsa labb’an bakinta, wanda da’alama wani abu takeson fad’a, amma kuma ta kasa saidai Kallon Rayyern din da takeyi kasa kasa.
Rayyern kuwa duk abunda takeyi yana lura da ita sarai, bawai kuma Dan idanunsa basa kanta bane, shi yake nufin baya kallonta, a’a kawai dai da idanun zuciyarsa yake kallonta, kuma duk hankalinsa yana kanta ne.
Jannart ko Ganin da gaske idanunsa ba’a kanta suke bane, yasa ta jawo d’ayan kofin Coffee din, wanda aka ajiye dominsa, batare da wani tunani ba ta kafa kofin abakinta, bata ciresa ba kuwa saida ta shanye coffee din tas.
Sai alokacinne kuma ya juyo ya kalleta, da sauri ta ajiye kofin dake hannunta, gudun kada yayi mata masifa ne kuma, yasa tayu rau-rau da ido tare da narke fuska.
Sai kuwa ta rumtse Idanunta, like masifan Idan yayi mata akan idanunta zai sauk’a.
Rayyern kuwa Ganin hakanne yasa shi, had’e fuska cikin muryar dakiya yace.
“Da kika shanye naki Coffee din, kika dawo kan nawa baki nayi? Kin iya shan abuna kice kina so in ruggumeki ne bazaki iya bako”.
Kanta tad’an girgiza Ahankali kuma Cikin yanayin tsoron kada, ya sake daka mata tsawa irin yanda yayi mata d’azu ta girgiza masa Kai alaman “A’a.”
Shikuwa harara ya watsa mata tare, da d’agawa waiter hannu kana yayi masa alama, akan ak’aro musu wani Coffee din.
Ita dai Jannart jin baiyi mata tsawan bane, yasa asanyaye ta bud’e Idanunta, tare da hade yan yatsunta waje daya, ta soma murzasu dan saboda sanyi, har ji take tamkar ba ahannunta suke ba.
Kamar yanda Rayyern din ya buk’ata kuwa, wani Coffee din aka sake kawo musu.
Tura mata kofi daya yayi gabanta, Yayinda shi kuma ya d’auki nasa ya soma sipping ahankali.
Jannart dake masifar jin sanyi kuwa, batajin zata iya sipping coffee din da kad’an kad’an, hakan yasa ta sake Kai cup din bakinta, bata ciresa ba kuma saida ta shanye duka Coffe din.
Wanda daga zamanta zuwa yanzu tasha 3cup kenan.
Har yanzu kuwa jarababben sanyin da takeji, yaki barinta saima kara shiga jikinta da yakeyi, kasancewar Cafe din da suke ciki, duk akewaye yake da shuke shuke, da yake cikin garden yake haka wajen yake da shuke-shuke, wannan dalilin yasa wajen yake da sanyi sosai.
Shiyasa har yanzu jikin Jannart din yaki daina b’ari, haka take ta karkarwa tamkar Wacce aka jonawa Shocking.
Rayyern ahankali ya ajiye cup din dake hannunsa, tare kuma da d’ago kansa ya kalleta.
Rawar sanyi takeyi sosai, domin hatta hakwaranta suma karkarwan sanyi sukeyi, kayan dake jikinta ya dan soma karewa kallo, wanda gaba daya duk dusan kankara ya b’atasu, musamman Y’ar abayan dake saman kayan nata, hatta gashin kanta ma dusan k’ank’arane.
Kawar da kansa gefe yayi, tare da mikewa tsaye ya sake had’e fuskarsa sosai, rigar sweater’n dake jikinsa ya zare.
Tare da takowa ahankali ya dawo bayanta, cikin tsare gida da hade fuska, ya yafa mata sweater din nasa ajikinta.
Wanda yasan hakan zai taimaka mata wajen rage sanyin.
Dai-dai ya juyo ne kuma idanunsa suka sauk’a, akan motar Azeez wanda tazo ta gilma ta wajen, ya hango motar ne kuma saboda duka wajen glass ne, wanda yake ciki zai iya hango komai dake waje.
“Oh my God wannan wanni irin mayene? Meyasa yake ta bibiyarmu? Why why???”
Ya k’are maganan cikin wani sabon b’acin rai, da kuma haushin ta da yakeji saboda itace ta jawo komai, domin da tun farko taci abincin daya kawo mata din, da yanzu basu fito har Suna wasan tsere da wani daban ba.
Ahasale ya sake kamo hannunta, batare kuma da ya bari ta gama mikewa tsaye ba, ya soma janta bayan ya ajiye kudin Coffee din da suka sha, akan table din kaitsaye suka fice daga wajen.
Ita dai Jannart binsa kawai takeyi tamkar rak’umi da akala.
Suna shiga cikin mota kuwa yayi reverse, tare dayin yanke yabi wata hanyar na daban, wanda kuma yayi hakanne saboda, gudun kada su sake had’uwa da Azeez, wanda shi kwata kwata baisan waye shiba.
Tafiya kad’an sukayi ba wani mai tsawo ba, suka iso gaban wani makeken hotel.
Mascow Marriott Grand hotel, wanda kuma da dukkan alama hotel ne na musamman, da ko acikin garin ba kowane ke zuwa ba dan hotel ne daya amsa sunansa.
Bud’e murfin motar yayi tare da fitowa, Ganin hakanne kuma yasa Jannart dake, duk’unk’une cikin sweaternsa, bud’e murfin motar itama ta fito.
Ganin da yayi tana d’an waige waige ne kuma, yasa shi kama hannunta da karfi.
Haka suka nufi cikin hotel din yana gaba tana biye dashi abaya.
Koda suka k’arasa receiption d’aki ya kama musu, parlor and 1bedroom.
Bayan an basu key dinne kuma suka wuce sama.
Suna shiga cikin y... By
*GARKUWAR FULANI*Kamar jira yakeyi kuwa suna shiga cikin dakin, ya sake hannunta tare da turata gefe, Cikin yanayin b’acin rai da murtuk’e fuska yace.
“Waye shi? Waye wancan gardin da kika rungume, tell me wayeshi wanni d’an iska ne, da har kike had’a jikinki da nashi? Akanme zaki manna masa ƙirjinki mallakina a ƙirjinsa?”.
Ya k’are maganan cikin masifar tsawa Cikin fushi kuma da b’acin rai.
Jin ya kira Yah Azeez din da d’an iskane kuma, ya sata soma girgiza kanta, lokaci daya kuma cikin muryata da ta raunana sosai tace.
“Shifa ba d’an iska bane.”
“Ohhhh.”
Ya fada yana me kura mata idanu, tare kuma dasa hannayensa ya kama waist d’insa, cikin fushi yace.
“Da kikaje kika rungumesa, ya kwantar dake acikin jikinsa sadakin nawa ya biya aka d’aura muku aure? Waye shaidun ku!?”.
Da sauri ta fara jujjuya mishi kai hawaye na kwaranyo mata sam ta gaza cewa komai.
Shi kuwa Rayyern cikin takaici murya a sark’afe yace.
“Janna da aurena fa ya ruggumeki hakan shine ba iskanci ba kenan da aurena fa a kanki kefa matatace kika manna masa ƙirjinki a nasa Janna hakan dai-dai neeh.”
Ya kare mgnar tamkar zaiyi kuka.
Saurin girgiza masa kai tayi, kana Cikin yanayin tsoro tsoro tace.
“Allah ba d’an iska bane Yayanah ne.”
“Karya kikeyi taya ya ya zama yayanki, a ina kuma yaushe har kike kiransa yayanki, kina da aure amma saboda rainin na barki kina abinda kikaga dama kinje kina runguman wani k’aton banza! Sabida na barki ko?”.
Ya kare maganan atsawace wanda har saida taji yay’an hanjin ta sun kad’a.
Hakanne kuma yasa cikin raunin da yafi kama da shogob'owa a wurin mai kallonta da sakalci tace.
“K’aton banza kuma?
shifa ba k’aton banza bane, Allah Yaya nane Yah Azeez ne Babanmu d’aya dashi, shine yayanmu na biyu fa dama yayi karatunsa anan kuma anan yake aiki, Allah ba karya bane kuma ma ka tambayesa kaji...”
Ta kare maganan da sigar dake bayyana tsananin yarintarta.
Rayyern kuwa Harara ya watsa mata, cikin kuma tsareta da idanu yace.
“Da Allah rufemin baki ke kina da Yayane.”
Idanunta ta d’an zazzaro tare da kwato numfashinta, murya na rawa tace.
“Mekake nufi ni bani da Yaya kenan? ka tambaya mana kaji Babanmu d’aya dashi.”
Ta fad’a tana me turo bakinta gaba.
Shikuwa Rayyern cikin halin ko in kula yace.
“Shutup dama ke kina da Babane? Waye baban naki?”
Saurin d’agowa tayi ta kalleshi, lokaci d’aya kuma taji numfashinta na kokarin k’wacewa, saboda abunda ya fad’a d’in yasa, taji numfashinta na slowdown.
Cikin yanayin rauni da kuma shagwab’ar dake damunta, kana cikin muryar kukan da yazo mata tace.
“Kamar ya zaka ce bani da Baba, wallahi ni dai inada Babana...”
Ta kare maganan tana me sakar masa kuka.
Ganin hakanne kuma yasa Rayyern din had’e fuska, tare da gyara tsayuwarsa cikin murtuk’e fuska, da kuma razanannen tsawa yace.
“Kirufemin baki duk uba baya juran ganin ana cutar da d’iyarsa naki da kike zaton mahaifinkine akwai ayar tambaya a kansa na raunin jink’ai na iyaye.”
Da sauri ta rufe bakinta tare da had’iye kukan nata, wanda hakan yasa numfashinta wani irin fusga, har saida taji kanta na juyawa luuuu Kamar zata fad’i.
Wani irin fusga ta soma yi da kirjinta, dan jawo numfashin nata dake kokarin kwacewa.
Shikuwa Rayyern saboda tsananin b’acin rai ko lura da hakan ma baiyi ba, juyawa yayi afusace ya nufi bedroom din dake cikin falon.
Shikansa ayau din baisan meya b’ata masa rai har haka ba, bai kuma san Meyasa zuciyarsa ke tafarfasa ba ya dai san tun ranar da yaga yadda Junaid na mata dukan mutuwa a gaban wanda take cewa mahaifinta bai kulaba yake da yak’in bai zama uban bad’ini ba kana in ya tuno yadda akayi aurensa da kalaman Barrister Kabir a lokuta ma-ban-ban-ta yakanji kansa na juyawa tabbas yasan akwai wani abu a k’asan tubalin wancan ahlin da take jin iyayenta ne.
Jannart kuwa Ganin ya wuce bedroom ne yasa ta, zama akan d’aya daga cikin kujerun falon, da sauri take maida numfashi, tare da rumtse idanunta.
Rayyern kuwa yana shiga bedroom din kayan dake jikinsa ya rage, tare da wucewa bathroom yayi wanka.
Bayan ya fito awankanne kuma ya sake maida kayan daya cire din, batare kuma daya sake bi takan al’amuranta ba, ya hau saman bed ya kwanta.
Har yanzu kuwa jin zuciyarsa yakeyi babu dadi, b’acin rai tsantsane kawai ke tafiya masa ya zama dole su kwana a hotel sabida gudun kar har yanzu wancan na bibiyarsu.....
Jannart.
Ahankali take sake matse jikinta waje daya, saboda wani irin masifaffen sanyin da takeji, wanda yake kara sawa numfashinta na seizing.
D’agowa tayi ta kalli agogon dake sak’ale ajikin bangon d’akin, wanda yake nuna mata k’arfe d’aya na dare.
Sake matse jikinta tayi tare da karyar da wuyanta gefe, tana me tunanin yanda zatayi ta kwana acikin falon.
Musamman ga yanda numfashinta keyi yanzun, tamkar wanda zai d’auke gaba d’aya, da alama kuma asthma dinta ne Keson tashi.
Tana nan ahakane kuma taji ringtone na tashi, acikin aljihun rigarsa dake jikinta, da alama dai wayarsa ya bari acikin aljihun rigar.
Jin ringtone din yaki dai nawa Ne kuma, yasa ta sa hannu ta zaro wayartasa tare da ajiyesu akan table.
Kwata kwata ta kasa Koda kwanciya saboda, da zaran ta kwanta sai taji kamar numfashin nata zai bar jikinta.
After 10mn
Zuwa yanzu gaba d’aya ta fara shidewa saboda, yanda numfashin nata ke fita, yana yin sama da kasa, kirjinta kuwa sai duka yakeyi tamkar zai rabe biyu.
Acan b’angaren Azeez kuwa yawo yasha sosai, Ganin babu alamar zai sake ganinsu ne kuma, yasa shi hakura da neman nasu ya koma gida.
Saidai duk hankalinsa atashe yake.
Hakan yasa shi soma kiran Daddynsu amma kwata kwata, wayan Dadyn baya shiga.
Duk da cewar yasan yanzun dare ne, amma kwata kwata bazai iya hakura da abunda ya gani yau din ba, Lallai ya zama dole yakira gida ya sanar musu.
Samun wayar Daddyn nasu da yayi akashe ne kuma, yasa shi kiran wayan Abba Kabir, cikin sa’a kuwa wayar ya shiga.
Bugu biyu kuwa Barrister Kabir din ya d’auki wayar, tare da karawa akan kunnensa.
Azeez kuwa jin Abba Kabir ya d’aga wayarne, yasa batare daya jira wani abu ba, cikin tsananin rudani hadi da damuwar dake damunsa yace.
“Abba Naga JANNART.”
Wani irin bugawa Barrister Kabir yaji zuciyarsa tayi, cikin tsananin tashin hankalin daya shiga yace.
“Innalillahi wa’ Ilaihirraju’un Azeez wani irin magana kakeyi ne haka?”
“Magana nakeyi akan Jannart Abba, wallahi yau da idanuna naga Jannart a Mascow, Abba Jannart ba bata tayi ba, na ganta da idanuna kuma itama ta ganni, har na rungumeta kuma munyi magana da ita.”
Yah Azeez din ya fada Cikin confidence.
Abba Kabir din kuwa gumin da suka keto masa ya share, cikin sabon tashin hankalin da yakejin kansa aciki yace.
“Azeez ba Jannart bace, ba Jannart ka gani ba Azeez watakila idanunka gizo sukayi maka, amma ba ita bace.”
Cike da tsananin mamaki Azeez ya murtsuka idanunsa, saboda Jin abunda Abban nasu ya fad’a, lokaci daya kuma ya girgiza kansa, with full confidence yace.
“Abba ba karya nakeyi maka ba, ba kuma gizo idanuna sukeyi minba, Wallahi wallahi Jannart nagani ba wata ba, Abba taya kake tunanin zan kasa gane Jannart aduk inda na ganta, Jannart ce Abba wallahi ita nagani tare da wani saurayi, wani wanda bansan shiba, bana son zuciyata ta zargi Jannart, nasan ba halinta bane bare nayi tunanin ko wani saurayi ta biyo, kuma amma a yanayin dana ganta, batayi kama da irin wanda za’ace an saceta ba, naganta cikin kwanciyar hankali da jin dadi, Abba Ina cikin matuk’ar rud’ani, akan meya kawo Jannart Mascow..”
Shiru Barrister Kabir yayi, still kuma gumi ne ke sake keto masa, ya shiga tashin hankali kwarai.
Wacce amsa zai bawa Azeez? Shine abunda ke dukan kwakwalwarsa...
Acan b’angaren su Jannart din kuwa, duk yanda Rayyern yaso bacci ya daukesa abun yaci tura, domin da zaran ya rufe idanunsa, To hoton Jannart da wannan gayenne keyi masa yawo acikin idanunsa.
Doguwar tsuka ya kuma ja alokacin da