Showing 21001 words to 24000 words out of 104589 words

Chapter 8 - Tubali Book 2 Hausa Novel Complete

Unknown   

21 Dec 2024

156

sauri-sauri, lokacin da ta daura ƙafarta kan step din forko.
Tunda tazo gidan yanzu kusan kimanin watanni biyu cur harda kwanaki, ƙafarta bai taɓa taka wurinba.
Bare ta haura saman, da sauri ta juyo jin muryar Mamy na cewa.

“A'a Jannart me kike jira, kiyi maza ki kaimashi.”
Da sauri tace.
“Toh”.
Kana ta fara tattakawan a hankali.

Shi kuwa Rayyern fitowar shi daga wonka kenan.
Dan Abba ya hada masa ruwan wonka kenan ya fita.

A hankali ya matso gaban gadon shi.
Kayan da yasa Ramadan ya ciro mishi ya kalla.
Wani singlet ne mai faɗin hannu fara ƙal mai masifar taushi.
Daga gefen damanta kan kirjin da al'jihun.
Sai kuma wondonshi wanda bazai wuce masa iya guiwa ba.
A hankali ya ɗan sunkuyo ya zauna sabida yar tafiyar da yayin yaji ya gaji.

A hankali ya ware wondon tare dasa kafafunsa yana daga zaunen.

Cikin tattaro sauran ƙarfinshi ya yunƙura ya taso.
Tare dasa hannunsa daya ya ware towel din dake daure, a kugunsa ya fadi ƙasa, hakan yasa yatsaya ba komai a jikinsa.
Sai gajeren wondon da yake dai-dai kan guiwarsa, bai jawoshi zuwa sama ya suturce shi ba.
Dai-dai lokacin kuma Jannart ta turo ƙ...!



*GARKUWAR taku ce dai MA'AURATA, da masu shirin aure, da masu jego, da yan gayu masu son k’amshi kece raini, da gyaran da zaike maimaita muku dararen forkon kuruciya*

Ko kunsan Jikinmu na da sinadaran hormones da suke taimakawa dan’adam akan komai musamman lokacin da mace take mu’amalar aure da mijinta. Mafi akasari wannan hormones din ne ke samun matsala ko su yi sanyi koma su daina aiki kwata-kwata shi ne dalilin da zai sa mace tace bata jin sha’awa ko bata san dadin aure ba. Albishirinku ina da kayan da ke taimakawa wannan sinadaran du dawo aiki tukuru don karkato miki da kimarki wajan mai gida sannan su taimakawa wannan sinadaran hormones dinki su dinka secreting din ni’ima wadatacciya da zata taimaka miki ki gamsu mijinki ya gamsu fiye da tunaninki. Note: Kayana ba sa tsinka ruwan ni’ima suna dai taimakawa hormones dinki ne su tsattsafo da ni’imar musamman wacca cutar sanyi ko dattin mahaifa ya dankarar da su ya hana su yin aikinsu yanda ya kamata. Haka zalika idan kina da kyau ki kara da wanka. Zaki iya amfani da magani na na gargajiya wanda zai gyara miki sex hormones din kullum ki kasance cikin humidify wato cikin damshi mai albarka kamar yanda ake son mace. Yana gyara miki mara.

Sai kamshi. Hajiyata daure ki fara amfani da turarena ki ji irin salon kamshin sa salo ne da zai daidaita ki da mijinki ya kankaro miki da kimarki a wajansa. Siyan na gari mayar da kudi gida.

Ga masu buƙata ga number' wayata wanda nake whatsApp dashi 09097853276 kimin mgn ta whatsApp in har kin tabbatar kin shirya saya mu dai-dai ta, kayana ba ƙanana bane, shiyasa bana harkan karanta, muddin kinsan baki shirya sayaba Please kada kiyi min mgn ki bari sai kin shirya kuɗinki a hannu, ba ina nufin kayana bana talaka bane, no akwai ƙananan set na masu karamin karfi, banson aimin mgn a ɓatamin lokacin aiyukana a shirme baki shiryaba. Shine karantan da bana so.
0005388578 Jaiz bank AISHA GARKUWA ALIYU. In kin shirya ga number ta ga kuma account number ta wanda in mun gama mgn zaki turo kudin ki, kana insa miki kaya a mota, duk ƙasar da kike kayana zaije gareki, amman fa in kinada dalilin zuwan nasune🤝🏻sayan na gari meda kudi gida.

GARKUWAR MA'AURATA
By
*GARKUWAR FULANI* FULANI* *GARKUWAR FULANI* *GARKUWAR FULANI**GARKUWAR taku ce dai MA'AURATA, da masu shirin aure, da masu jego, da yan gayu masu son k’amshi kece raini, da gyaran da zaike maimaita muku dararen forkon kuruciya*

Ko kunsan Jikinmu na da sinadaran hormones da suke taimakawa dan’adam akan komai musamman lokacin da mace take mu’amalar aure da mijinta. Mafi akasari wannan hormones din ne ke samun matsala ko su yi sanyi koma su daina aiki kwata-kwata shi ne dalilin da zai sa mace tace bata jin sha’awa ko bata san dadin aure ba. Albishirinku ina da kayan da ke taimakawa wannan sinadaran du dawo aiki tukuru don karkato miki da kimarki wajan mai gida sannan su taimakawa wannan sinadaran hormones dinki su dinka secreting din ni’ima wadatacciya da zata taimaka miki ki gamsu mijinki ya gamsu fiye da tunaninki. Note: Kayana ba sa tsinka ruwan ni’ima suna dai taimakawa hormones dinki ne su tsattsafo da ni’imar musamman wacca cutar sanyi ko dattin mahaifa ya dankarar da su ya hana su yin aikinsu yanda ya kamata. Haka zalika idan kina da kyau ki kara da wanka. Zaki iya amfani da magani na na gargajiya wanda zai gyara miki sex hormones din kullum ki kasance cikin humidify wato cikin damshi mai albarka kamar yanda ake son mace. Yana gyara miki mara.

Sai kamshi. Hajiyata daure ki fara amfani da turarena ki ji irin salon kamshin sa salo ne da zai daidaita ki da mijinki ya kankaro miki da kimarki a wajansa. Siyan na gari mayar da kudi gida.

Ga masu buƙata ga number' wayata wanda nake whatsApp dashi 09097853276 kimin mgn ta whatsApp in har kin tabbatar kin shirya saya mu dai-dai ta, kayana ba ƙanana bane, shiyasa bana harkan karanta, muddin kinsan baki shirya sayaba Please kada kiyi min mgn ki bari sai kin shirya kuɗinki a hannu, ba ina nufin kayana bana talaka bane, no akwai ƙananan set na masu karamin karfi, banson aimin mgn a ɓatamin lokacin aiyukana a shirme baki shiryaba. Shine karantan da bana so.
0005388578 Jaiz bank AISHA GARKUWA ALIYU. In kin shirya ga number ta ga kuma account number ta wanda in mun gama mgn zaki turo kudin ki, kana insa miki kaya a mota, duk ƙasar da kike kayana zaije gareki, amman fa in kinada dalilin zuwan nasune🤝🏻sayan na gari meda kudi gida.
GARKUWAR MA'AURATA

K’ofar falon ta tura ahankali tare dasa k’afarta na dama ta d’an shigo cikin falon, bakinta d’auke da siririyar sallama, wanda ba kowane zai iya jin amo da kuma sautin muryar natan ba.

Ahankali tad’an sake kofar, tare da k’arasa shigowa, wanda hakan ya bawa kofar daman rufewa.

Shiru ta d’anyi na y’an wasu sakanni, kafun daga bisani ta soma yawo da Idanunta acikin, had’add’en falon wanda kaitsaye za’a iya k’iransa da suna Aljannar duniya, badon komai ba kuwa face saboda tsananin had’uwarsa, duk da cewar babu wani tarkace aciki, amma falone daya amsa sunansa falo.

Ahankali ta d’an lumshe Idanunta, tare da shak’an daddad’an k’amshin dake tashi acikin falon, wanda ya had’u da sanyin A/C da kuma, fitinannen turaren air conditioner mai k’amshin strawberry.

Daddad’an k’amshin da d’adinsa kan iya saka mutum jin bacci ta zuk’a, tare kuma da d’an bud’e lumsassun Idanunta, b’angaren dama da kuma hagunta ta kalla, inda taga d’akuna guda biyu, sai kuma kitchine dake can gefe guda, gefe dashi kuwa wani had’adden dining table ne, mai kyaun gaske.

Gefen damanta ta kuma kallo, kasancewar ance mata bedroom din nasa, ab’angaren dama yake.

Ahankali kuma Cikin nutsuwa ta nufi, kekkyawan kofar da take da tabbacin cewa, nanne d’akinsa, hannunta rike da tray.
Kowani taku zatayi kuwa sai tafukan k’afafunta sun amsa, da wani irin sanyi da kuma taushin dake tashi ak’asan tiles din dake malale acikin falon.

Acan b’angaren Rayyern kuwa, akasalance yaja wandon nasa sama, cikin yanayin gajiya da kuma kosawa da tsayuwan da yayi.

Idanunsa yadan lumshe Ahankali adai-dai sanda ya kawo wandon saman kugunsa, duk da cewar bai gama jan wandon ya haura masa can sama ba, hakan kuwa shiyasa duk shatin saman mararsa ya bayyana.

Akasalance ya jawo short sleeve ya saka ajikinsa, saboda yanayin da yake ciki ne kuma, yasa ko gama had’e bottum din rigar baiyi ba, hakan kuwa shiya saka kwantattun gargasan dake kwance akan kirjinsa suka Dan bayyana.
Haka ma gargasan k’afarsa saboda wandon daya saka din, ya tsaya iyaka guiwarsa ne, wannan shi yasa duk wani lallausan bakin gashin dake kwance a jikinsa suka bayyana.

Duk da cewar akwai rama ajikinsa, kuwa amma hakan baihana kyawunsa bayyana ba, musamman ayanzu daya saka kayan da suka k’ara fito masa da kyaun surarsa.

Ahankali ya sauke wani irin numfashi mai dauke da ‘alamar gajiya, cikin kosawa da tsayuwar da yakeyi din kuma, ya d’an juya tare da jawo wata had’add’iyar kujera dake gefen gadonsa.

Zama yayi akan kujera tare da fesar da numfashi mai dumi, Jin kansa yake ya gaji sosai, wanda kuma yasan hakan bai rasa na saba, da rashin karfin jiki da bashi dashi sosai.

Idanunsa ya lumshe tare da maida kansa ya daura ajikin kujeran, akai akai haka yake fitar da numfashi.

A dai-dai lokacin kuwa Jannart ta k’ara masowa jikin k’ofar d’akinnasa, tsayawa tayi ajikin k’ofar tare dayin shiru, zuciyarta cike da tunanin yanda zatayi ta shiga cikin dakin.

Sake gyara rikon tray din dake hannunta tayi, kana Ahankali ta d’an matso, hannunta na dama tasa ajikin kofar tare da soma knocking, cikin kuma tattausan muryarta tace.

“Assalamu Alaikum!”

Shiru taji babu alaman za’a amsa mata, gashi kuma ta kasa ci gaba da knocking din.

Daga can b’angaren kuwa sam Rayyern baima jita ba, saboda tunaninsa daya tafi izuwa wani waje na daban.

Itakuwa Jannart sanin da tayi cewar tana da raunin ji, ba lallaine ma taji koda ya amsa mata ba, hakan yasa Ahankali ta d’an murd’a handle din kofar.

Cikin sa’a kuwa kofar ta bud’e, wanda hakan ya bata daman d’an tura kanta ciki ta shigo ciki bakinta dauke da sallama.


Rayyern kuwa Jin alamun bude kofar ne yasa shi dan bud’e idanunsa Ahankali, inda ya sauke ganinsa akanta, ganin ita dinne kuma yasa shi maida idanun nasa ya lumshe, ba tare da ya bari sunyi ido hudu ba.

Jannart kuwa sauk’e idanunta da tayi akansa ne yasa ta d’an tsaya, tare da sauk’e ganinta akan kyakkyawar fuskarsa, Ahankali ta dan soma yawo da idanun nata akansa, har dai ta sauke ganinta akan lallausan sajen dake kwance agefen fuskar tasa, sajen nasa da kuma wuyansa ta d’an k’urawa ido, saboda yanda taga tsaruwa da kuma k’awatuwarsa, ga kuma wani irin haske da taga cikin jikin nasa ke dashi.

Sak ayanayin nasa da mai bacci yayi mata kama, domin hakanne ma yasa ta d’an tsaya kallonsa na d’an wasu sakanni.

Ahankali kuwa ta kauda kanta tare da janye Idanunta daga garesa.

Cikin sanyi da nutsuwa ta k’arasa shigowa cikin d’akin, tare kuma da nufo inda yake.

Anutse ta d’an rusuna adai-dai gabansa, inda wani glass stull ke aje anan gefensa, sunkuyawa tayi tare da soma kokarin ajiye tray din dake hannunta.

Batare kuma da takai ga ajiye tray dinba, ta d’an d’ago da kanta ta kuma Kallon fuskarsa.

“Ina kwana.”
Ta fad’a asanyaye, duk da kuwa bata da yakinin cewar zai amsa mata.

Hakan kuwa akayi domin shiru yayi bai amsa mata ba, saidai taga kwayan idanunsa sun d’an motsa, wanda kuma hakan shiya tabbatar mata da cewar ba bacci yake yi ba.

D’agowa tayi daga ajiye tray din, still kuma cikin muryarta dake bayyana sautin nutsuwa tace.

“Sannu Ya jiki?”

Akaro na biyu kenan daya d’an motsa, tare kuma da jan wani dogon numfashi, kana ya bud’e maraitattun idanunsa, masu cike da kasala, gajiya, had’i kuma da bayyana yanayi irin na marassa lafiya.
Inda ya saukesu acikin nata idanun.

Da sauri tayi kasa da kanta, saboda har abada bazata tab’a iya jurewa Kallon cikin idanunsa, a irin wannan yanayin ba.

Shikuwa Rayyern Jajayen labbansa masu sheki ya motsa.

“Da sauki.”
Ya amsa mata cikin muryarsa da bata fita sosai.
Kasan cewar ta kasa kunne kuma hankalinta na gareshi yasa taji,
Jin yanda sautin muryar tasa ke fita ne kuma yasa, Jannart d’ago Kanta ta kalleshi.

Gaba d’aya ya rame sosai, labbansa sun sakeyin ja, Yayinda idanunsa duk suka bayyana ramar fuskarsa, tabbas kallo daya zakayi masa kafahimci cewa ya matukar jin jiki sosai, saboda yanda komai nasa ya sanja, amai makon yayi muni kuma sai ramar ta k’ara masa kyau.

Wato atakaice dai Dr Rayyern Bashir Muhammad Mai-nasara irin mutanen nanne, da a kowani irin yanayi suka samu kansu suna kyau, badon komai ba kuwa, sai dan kyau din a jininsu yake.

Idanunta ta d’an kawar daga kallonsa.

Akaron farko kuma kenan da ta tausasa muryarta sosai, cikin nuna kulawa tace.

“Allah Ya baka lafiya.”

“Ameen Idan da gaske kike.”
Ya fad’a akasalance, cikin kuma kauda Kai daga Kallon ta.

Jin abunda ya fad’a d’inne kuma yasa Jannart din, girgiza kanta batare da tace masa k’alaba ta maida hankalinta wajen had’a masa tea.
Acikin zuciyarta kuwa cewa tayi.

“Mai Hali dai baya sanja halinsa, ko bashi da lafiya sai yayi.”

Ta k’are zancen zucin nata, tana me sauke Idanunta akan fararen legs d’insa, wanda gargasa suka yi musu k’awanya, ba kuma irin normal gargasa da kowa ya sani ba, gargasane dogaye kuma masu taushin gaske, wanda suka kwanta lub-lub ajikin fatar nasa.

Kauda kanta daga Kallon k’afan nasa tayi, adai-dai lokacin kuma ta kammala juya masa tea d’in.

Tea spoon ta sanya acikin cup din tare kuma da d’ago kanta ta kalleshi.

“Ga Tea din.” Ta fad’a tana me mik’a masa cup din.

Ahankali ya d’an jujjuya mata kai, tare da karyar da wuyansa gefe.
Alamun bazai shaba.

Idanunta tad’an zuba masa, saboda wani irin tausayinsa da taji, sanin kuma halin marassa lafiya da kin son cin abinci ne yasa, cikin tausasawa da kuma kwantar da murya tace.

“Bazaka sha ba?”

Kansa ya kuma jinjina mata, alaman “Eh.”

“To Meyasa?” Ta tambayeshi da wata irin murya, kana kuma cikin yanayin da ita kanta batasan tayi ba.

Fararen hakwaransa yasa ya dan danne lipsl d’insa, cikin wata iriyar fitinenneyar murya yace.

“Banaso!! Bsnaso! banassso!!!”.
Idanu ta zuba mishi tana mai jin yadda tsikar jikinta ke zubawa sabida yadda yayi mata mgnar like ɗan yaye mai shogoba.

Kai ta ɗan kwantar kana cikin murya da bata san ta yaya ya ziyarci harcentaba tace.
“Bakason me?”.
Kwaɓe fuskarsa tayi tamkar zaiyi kuka yace.
“Banason tea me madara empty zaki baneeee.”
Yayi maganar cikin sake yin kasa da murya, saboda gaba daya baya wani jin dadin jikinsa, ga kuma rashin karfi dake damunsa, wanda hakan yasa maganan ma wahala yake basa.

Jannart kuwa jin abunda ya fad’ane yasa, ta d’an kwantar da kanta gefe, tare kuma da Kallon kayan tea din da ta shigo dashi.

Ajiyar zuciya ta d’an sauk’e, kana cikin sanyi tace.

“To bari naje na d’auko wani cup, saina had’a maka empty din.”

Ta k’are maganan tana me mik’ewa tsaye,batare kuma da ta jira wani abuba kaitsaye ta fice daga Cikin d’akin.


Direct falon nasa ta dawo, harta kawo bakin kofar fita daga falonne kuma sai ta hango, kofar dake gefe da dining area d’insa, da dukkan alama kuma nanne kofar kitchine din dake Cikin falon nasa.

Ahankali ta k’arasa jikin kofar tare da turawa ta kutsa kanta ciki.

Idanunta tad’an ware saboda ganin yanda kitchine din nasan ya tsaru, da komai na zamani, domin wani irin kitchine carbinet akayi na musamman acikinsa, ga kuma plates da cups hadi da sauran kayan aiki masu kyau kana Kitchen din nada girma ga kuma kofar store ta ciki.

Jinjina kanta tayi saboda yanda ta yaba da kyawun kitchine din.

Wani cup ta d’auka tare da k’arasawa gaban sink ta wankesa.

Juyowa tayi Anutse ta dawo cikin d’akin.

Yana nan zaune a inda ta barsa dan ko motsawa baiyi ba, saidai idanunsa daya sake lumshewa.

A ranta tace.
“Ga kafiya faɗa ga kuma raki da sakalci”.

D’an durk’usawa tayi, agaban stull din tare da d’aukan lipton ta saka acikin cup din, sai kuma k’wayan shugar guda hud’u da ta d’auka acikin k’wali, bayan ta saka shugar’n ne kuma ta saka ganyen lemongrass leaves wanda already dama tazo dashi akan tray din, murfin flask ta bud’e tare da zuba ruwan zafi acikin cup din, kana tasa cokali tadan jujjuya.

Ganin sugar din ya narke ne kuma yasa ta, d’ago cup din tare da mik’a masa cikin kulawa tace.

“Gashi.”


“Ki ajiye.”
Yafad’a agajarce tare kuma da gyara zamansa, wanda kuma daga yanayin maganarsa kad’ai zaka fahimci cewar bayajin dadin komai.

Ajiye cup din tayi agefensa kamar yanda ya fad’a. Cikin nutsuwa kuma ta mik’e tsaye, tare da d’aukan tray din.

Ahankali batare kuma da ta sake ce masa komai ba, ta juya ta fice daga cikin dakin, tare da mayar masa da kofar ta rufe.

Kaitsaye k’asa ta nufa.

Shikuwa Rayyern jin alamun fitanta ne yasa shi sake lumshe idanunsa.

Ahankali ta gama sauk’owa daga kan steps din.
Ganin babu kowa acikin main falon ne kuma yasa kaitsaye ta wuce kitchine.
Dan aciki ne takejin motsin Mamy.

Tana shiga kuwa ta samu Mamyn nata aikace aikace.

“Sannu da aiki Mamy.”
Ta fad’a tana me ajiye tray din dake hannunta.

Mamy kuwa jin muryar Jannart abayanta ne yasakata sakin murmushi, cike kuma dajin dadin d’an jimawan da taga Jannart din tayi a sashin Rayyern din tace.

“Yauwa sannu dai Jannart.”

K’asa Jannart din ta d’anyi da kanta, kana anutse tazo kusa da Mamyn tare da k’arb’an aikin da Mamyn keyi ta soma Taya ta.

Hakan yasa cikin yan mintuna suka kammala had’a komai na breakfast.
Bayan sun zuba komai acikin food flask ne kuma, Jannart takai kulolin kan dining Table.

Mamy kuwa na Abba ta d’auka takai masa zuwa part d’insa.

Dai-dai lokacinne kuma Ramadan da Riyyam nsra suka shigo.

Jannart dince ta bawa Riyyam nsra food flask din su Baba Maud’o ya Kai musu.

Koda ya dawo kuwa anan falon suka zauna su dukansu, atare sukayi breakfast, inda suna cin abincin Riyyam-nsra nata zuba musu surutu, wanda kuma bashi da wani labari saina y’an tiktok.

Suna ahaka ne kuma Dr. Sulaiman da kuma Baba Maud’o suka shigo cikin falon.

Fuska d’auke da fara’a suka gaisa, dasu Mamy dai-dai lokacin kuwa Abba ma ya fito daga nan part d’insa.

Bayan Abban sun gaisa da Dr. Sulaiman ne kuma yayi musu jagora zuwa sama.

Ahankali Abba ya tura kofar dakin Rayyern din ya shiga bakinsa dauke da sallama, Yayinda su Baba Maud’o ke biye dashi abaya.

Rayyern dake dan kishingid’e kuwa jin muryar Abban nasa ne, yasa shi dan yunkurawa ya tashi zaune.

Akusa dashi Abba da Baba Maud’o suka zauna, cikin kulawa Baba Maud’o yace.

“Rayyern ya jikin naka?”

Murmushin karfin hali ya d’anyi, tare da gyara zamansa, kana cikin tausasawa yace.

“Alhamdulillah jiki da sauki Baba Maud’o.”

Kai Abba da Baba Maud’o suka jinjina, cikin kuma danjin dadi suka had’a baki wajen cewa.
“Allah ya baka lafiya.”

Da “Ameen.” ya amsa.

Inda

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login