Showing 51001 words to 54000 words out of 104589 words
shige bedroom ne, yasa Itama ta tashi ta wuce nata dakin, yau ko abincin daren ma bata ci ba.
Shikuwa Rayyern Bayan yayi wankane ya dawo falon, abinci yaci tare da komawa dakinsa ya kwanta.
Washegari kuwa kamar yanda ya saba haka ya fita bayan ya ajiye mata breakfast.
After 2weeks.
Ahaka sukeyin rayuwarsu ita dashi, daga wannan ranan kuwa babu wanda ya sake Ganin d’an uwansa, saidai kullum yana ajiye mata breakfast da kuma dinner, da rana kuwa saidai ta ci ragowar breakfast.
Gaba d’aya duk kad’aici ya dame ta, duk da ta saba da hakan amma yanzu batajin dadin hakan.
Shikuwa Rayyern gaba daya yanzu ya zama busy, domin course din da sukeyi din ya fara nisawa, shi yasa always he’s busy.
Daya dawo kuma ya gaji sosai, daga ya d’an tab’a system d’insa sai bacci.
Yau din kuma tunda ya fita da safe baidawo ba, domin Koda suka tashi ataron nasu, still meeting ya shiga da wasu manyan Doctors na k’asar.
Koda lokacin sallan magriba yayi, bayan yayi sallan meeting din ya sake komawa haka ma sallan Isha.
Basune suka tashi a meeting dinba kuwa sai 1:00 pm.
Agajiye yake sosai yau din, dan ko dak’yar ya iya biyawa ta restaurant ya saya abinci, da wasu chocolates d’insa, tun acikin mota kuwa yake cin chocolates din ahaka harya iso gida.
Koda ya dawo gidan kusan 11 ake nema.
Haka ya shigo cikin falon, yana mejin yanayinsa na d’an sanjawa, saboda yanzu Kwata-kwata baya ma shan maganinsa, especially now daya zama busy.
Direct d’akinsa ya wuce, tare da sakarwa kansa ruwa.
Itakuwa Jannart tana can cikin d’aki, duk yunwa ya isheta saboda duk yau bataci abinci ragowar breakfast din nata ba.
Tafito falon nasu kuma bata ga komai ba, wannan dalilin yasa ta koma ta kwanta, saidai duk yanda taso bacci yaki daukanta.
Ganin hakanne kuma yasa ta sha ruwa, tare da komawa ta kwanta, ahaka wani baccin wahala ya dauketa.
Ab’angaren Rayyern kuwa yana fitowa daga wanka, kaya ya sakawa jikinsa, batare daya sake bin takan abincin daya kawo ba, ya haura saman gadonsa, bacci ne sosai a idanunsa, shiyasa yana kwanciya bacci ya d’aukesa.
Washegari.
Saturday.
Bakamar sauran ranakun ba, kasancewar yau din weekend ne yasa, bai fito da wuri ba har sai 9:00pm.
Ahankali ya bud’e k’ofar bedroom din ya fito, maida k’ofar yayi ahankali ya rufe.
Ya juyo ya fuskanci cikin falon, idanunsa ya dan waro lokacin da suka suka sauk’a Akan...!
*Albishirinku! Ma'aurata, GA GARKUWAR KU nan tafe muku da tsarabobi na musamman gareku ma'aurata daga cibiyar mgnin mata mai taken GARKUWAR MA'AURATA*
NI DAI AYSHA ALIYU GARKUWA.
Ina matukar mamakin wani irin lokaci da ya riske mu mai wahalallan fassara. Kullum dai magana daya ce, akan ma’aurata, fada, rashin jituwa, mutuwar aure, akan kuskure kalilan, rashin kula, rashin yi wa juna uziri. Toh wai duk me ya janyo hakan? Na zurfafa a tsananin tunani hakan ya tilasta min bincike mai tarin yawa wanda ya kai ni ga gano inda matsalar take? Shin yar’uwa ke macece amma kin san wacece mace ku? Kin san me ake kira mace kuwa? Mace ita ce matar da take zama iyali a wajan namiji ta zame masa bango, sanyin idaniyarsa, ta zame masa gata da farin cikin rayuwarsa ta zame masa ruwa abar kore ƙishinsa ta zame masa mayafi mai karesa daga gigitar kadaice, ta kuma dorar da mijinta kan turbar gaskiya, ta kashe masa jiki da salonta ta rikita shi da baiwa da ni’imar da Allah ya bata idan har ta san hanyar mayar da kanta sabuwa dal awajanta, wato kullun takasance masa tamkar amarya har ya kasa tantance daren amarcinsu da sauran dararen rakun rayuwar su.
Wannan ita ce mace. Ina da wata saukakkar hanyar da zaki zama abar so da kulawa da soyayya a wajan mijinki ta hanya mafi sauki, 09097853276 hanyar ita ce ki gwada amfani da kayana na gyara ki gani, ina mai tabbatar miki da in sha Allahu sai kin dara da murna sai kuma kin gode min. Kayana kaya ne da aka yi shi da zallan itacanmu na gado marasa illa a cikin jikin dan adam musamman mace, kaya ne da suke taimakawa (sex hormones 😍) dinki.
Misali kina kallon India😘, hollywood, Asian film🥰 kina ganin yanda mazansu ke nunawa matansu tsananin soyayya kamar su ba su kyautar ransu!?
Saboda me hakan? Saboda suna sadaukar da lokacinsu wajan gyara jikinsu da kayan da ke tsattsafo da ni’ima cike da tsukewa, kayan nan kuma ana yinsu ne zallar magungunan gargajiya wanda ba su da illa domin haɗine na ingantattun itatuwa da yayansu.
Ina baiwar Allahn da miji ke daure mata fuska babu hirar arziki?
Zo ki ji yar’uwa zan baki gumbata da zallar gari wanda aka yi su da nagartattun itacen da ke da matukar amfani a jikin mace. Gubar ciko, gumbar tsalle dole, gubar da ba'a baiwa mai kishiya, garin maɗi, garin mallaka, tsumin goron tula, tsumin tsartai, tsumin maratsi, pala-pala butar sirri, kwanon k’asaitacciyar mace, furar mata madararta gareki Hajia takenta sha yanzu mgni yanzu,
Ina mata masu fama da sanyi? Sanyin mara ki zo na hadaki da magani na na sanyi wanda yake wanke mara ya fitar da duk wata cuta da ke samun mazauni a wajan.
Ina da ciccibi mai kyau. Ina da hadin amare mai kyau wanda zai gyara yarinya ya kankaro mata kimarta akwai hadin mai jego wanda muke yinsa na asali inada kekkyawan Hadi maida tsohuwa yarinya.
Akwai daya bangaren wato *KAMSHI*
Kimarki gyaranki da kamshinki. Matan da suka gane suka san yanda za su kankaro da mutunci su ne masu amfani da kayan gyara da kuma sanyaya jikinsu da kamshi, ina da turaren wanka da na bandaki na daki na jiki da na kaya dana tsuguno kamshin turarena na dabam ne mai sanyaya zuciyar wanda ya shaka ina da kayan kamshi na amarya da na maijego da na uwargida da dukkan macen da take kokarin mayar da kanta mai daraja a idon kowa ta zamo sarauni a idon mijinta, akwai shu'umar humra, sayan na gari maida kuɗi gida, banda karanta yayin gyara Hajia.
Zaku iya samun kayyakina a duk garin da kike, zakiyi min mgn ta whatsApp number na 09097853276 domin yin zaɓinki, ko karin bayani, zaki tura kuɗin ta account na 0005388578 Jaiz bank AISHA GARKUWA ALIYU in mun gama mgna zan sa miki kaya a mota yazo duk garin da kike, in baki shirya saya yanzuba Please kada mu wahal da juna ki bari sai kin shirya kafin kiyi min mgn.
🤝🏻🥰😘 Daga taku AYSHA ALIYU GARKUWA
*(GARKUWAR MA'AURATA) By
*GARKUWAR FULANI*Abincin daya kawo jiya da daddaren, idanunsa ya d’an zubawa ledodin, wanda da dukkan alamu babu wanda ya tab’a su, Dan suna nan kamar yanda ya ajiye su.
numfashi ya d’an fesar tare da soma takowa, ya k’araso tsakiyar falon, inda abincin ke ajiye.
Isowarsa wajenne kuma ya sake tabbatar masa da cewar, tabbas babu alamun an tab’a ledodin.
Bakinsa ya d’an tab’e tare kuma da komawa ya zauna, akan d’aya daga Cikin kujerun falon, idanunsa ya d’an lumshe Ahankali, dai-dai lokacin kuma daga can waje aka soma knocking kofar falon.
Ahankali ya d’an bud’e idanunsa, tare da mik’ewa tsaye, saboda already dama yayi musu order’n breakfast, to yanzun ma yasan breakfast din nasu ne ya iso.
K’arasawa yayi ya bud’e k’ofar tare, da karb’an ledodin breakfast din.
Kana ya dawo ya zauna akan sofa.
Duk da cewar baya wani jin yunwa sosai, amma hakan baisa shi kincin abincin ba, bud’e ledan yayi ya somaci, saidai bai wani ci sosai ba ya ture abincin gefe.
Yanda yaji duk baya wani jin dadin cikinsa ne kuma, yasa shi mik’ewa ya koma d’aki, sachet din maganinsa ya d’auko, tare kuma da dawowa falon ya zauna.
K’wayoyin maganin da sukayi saura ya zubawa ido, wanda kwata kwata basu wuce guda 16 ba, kasancewar akowacce rana mutum zaisha guda d’add’aya ne.
To Yanzu dai way’anda suka rage masan, basu wuce na 2weeks ba, banda ma yayi wasa da shan maganin yasan da yanzu basu Kai haka yawa ba.
B’alle maganin yayi ya saka abakinsa, tare da Korawa da ruwa marar sanyi.
Bayan yasha maganin ne kuma ya mik’e tsaye, babban agogon Bangon dake sak’ale acikin d’akin ya kalla, wanda yake nuna masa 12:pm dai-dai kenan na rana.
Ajiyar zuciya ya d’an sauk’e tare da d’aukar wayarsa, hadi da car key d’insa, domin duk da cewar yau din weekend ne, amma suna da test da zasuyi akan, yanda ake dashen k’oda, wanda kuma yau dinne firstly da zasu fara, gwaji akan abunda aka koya musu.
Kaitsaye ya fice daga cikin falon, direct wajen da ya ajiye motarsa ya nufa, Ahankali ya d’aga kansa yana me Kallon yanayin garin, duk da kasancewar yanzun rana ne, amma sudai awajensu tamkar safiya ne, saboda gaba d’aya yanayin garin babu rana, sai wani irin sanyi mai ratsa cikin k’ashi da bargo, ga kuma dusan k’ank’ara da yake sauk’owa daga sama.
Snow kawai tako ta ina.
Yana shiga cikin motar kuwa yayi mata key, tare da cillata kan titi, kaitsaye ya nufi wani babban asibiti.
*JSC MEDICINA CLINIC MASCOW,* domin acanne zasu yi karatun nasu na yau.
Jin k’aran tashin motar ne, yasa ta bud’e Idanunta dake lumshe.
Ahankali takai dubanta ga jikin window’n dakin nata, wani irin sassanyar numfashi ta fesar, tare kuma da d’an yunk’urawa ta tashi ta zauna, Allah ya sani tana matukar shiga takura, azaman da takeyi ita d’aya acikin gidan, tana buk’atar waya sosai, amma bata da yanda zatayi, saboda tasani layinta ba kudi, shi kuwa gaba d’aga ya shareta, akullum yanayin abu tamkar baisan da zamanta acikin gidan ba.
Gashi tun da suka zo ko fita bata tab’a yi ba ko dan harabar gidan.
D’an k’aramin tsuka taja, saboda gaba daya ta gaji da kwanciyar da takeyi.
Ahankali ta sauk’o daga kan gadon, tare da zubo da k’afafunta k’asa.
Kallon kanta tayi, saboda sanye take da wani dogon wando mai kauri, wanda ya kama jikinta sosai, sai kuma wani top long sleeve, shid’inma dai mai kauri ne sosai, still kuma sai wata riga jacket da ta d’aura akan shigar nata, kanta kuwa sanye yake da hulan sanyi.
D’an kwab’e fuska tayi, domin duk da irin shigar da tayi din, bai hanata jin sanyin da akeyi ba, Sam har yanzu bata saba da sanyin garin ba.
Wayarta dake kan bedside ta d’auka, sanin da tayi cewar Rayyern din ya fita ne, yasa kaitsaye ta nufo falon.
Koda ta fito kuwa tv ta kunna, saidai gaba d’aya babu wasu channels, sai zallan na turawa, ba haka ta soba amma dole ta hakura, zama tayi tare da bud’e ledodin breakfast din da taga ya ajiye.
Chinese dishes ne, da kuma African dishes, kamar dai yanda ya saba yi musu order akoda yaushe.
Fuskarta ta d’an kwab’e tare kuma da turo d’an k’aramin bakinta gaba.
Cikin shagwab’a tace.
“Ni gaskiya I’m tired da way’annan foodies din, always abu d’aya ni nagaji, Nigerian dishes nakeson ci, me zanyi da Chinese dishes niba
mai kananan idanu ba.”
Ta k’are maganar cikin tura baki tamkar Rayyern din yana gabanta.
Haka dai ta d’an tsakali abincin taci, domin kwata kwata bata iyacin chinese dishes din.
Bayan ta kammala cin abincinne kuma, ta haye saman kujera ta kwanta.
*Kano Nigeria*
Abba da Mamy ne ke zaune, acikin katafaren falon nasu, inda Abban ke zaune akan sofa, Mamy kuwa na durk’ushe agabansa tana had’a masa coffee.
Abban ne ya d’ago kansa ya kalli Mamyn, kana cikin kulawa yace.
“Ni kuwa Ruƙayyah ya labarin y’arki Jannart, tunda suka tafi kun gaisa da ita kuwa?.”
D’agowa Mamyn tayi ta kalli Abban, domin dama kamar ya Sosa mata inda yakeyi mata k’aik’ayine.
Numfashi ta d’an fesar, cikin kuma rashin jin dadin abunda zata fadad’in tace.
“A’a ba muyi waya da ita ba har yau, kwata-kwata bansan me yake damun Rayyern ba, domin duk sanda zamuyi waya dashi, Idan nace ya bawa Jannart din wayan, sai yace min baya gida, To amma kuma nasan bazaimin k’arya ba, saboda dama ba zamanne ya kaishi ba, kasan Rayyern da sabgogi.”
Kai Abban ya jinjina, tare da gyara zamansa, cikin sanin halin Rayyern din yace.
“Ni ai banma tambayesa itaba, saboda nasan dole wani uzurin zai kawo, amma yanzu ke kinyarda da uzurin da yake baki, na cewar ko yaushe baya gida? ai tunda yana da lokacin da zai iya dawowa gida yayi bacci yayi wonka ya sauya kaya, To yana da lokacin zama ya bata wayar ku gaisa, bansan Meyasa Rayyern yake haka ba, da gasken gaske na fahimci cewar, zama da Mace ne bazai iya ba, saboda baisa abun acikin zuciyarsa ba shiyasa, amma babu komai na zuba masa ido, awannan karon zanga iya gudun ruwansa a gari irin Mascow mai yanayi na musamman da kuma mace kamar Jannart da kuma keɓantaccen wuri zan bishi da ido inga iyakar yaudar da zuciyarsa ke masa na cewa zai iya rayuwa ba mace.”
Ajiyar zuciya Mamy dake gefe ta sauk’e, cikin nazartar maganganun mijin nata kuma murmushi tayi tare da cewa.
“Tabbas nima dai sau dayawa ina mamakin yanda yake cewa baya gida, amma da fari na yarda da maganganunsa, saboda kasan Rayyern bai cikayin k’arya ba, Dan banace baya k’arya ba kwata kwata arayuwarsa, saboda babu wani d’an Adam d’in da baya k’arya a dai wannan ƙarni namu, saidai na wani yafi na wani amman dan nasan karya ba dabiarsa bace, amma gaskiya nidai kam jikina yayi sanyi, kada fa Rayyern yaje ya ajiye y’ar mutane ne, kawai ya fita harkarta.”
K’wafa Abban yayi tare da d’aukan kofin coffee din nasa, cikin yarda da hukuncin da zuciyarsa ke yanke masa yace.
“Hmmmm zanyi magananinsa kuwa Idan har hakan ta kasance, saboda matarsa ce ko da ace bayasonta kuwa akwai, hakkinta da ya rataya awuyansa, amma ki barni dashi kawai.”
Abban ya k’are maganan yana me Kai kofin bakinsa.
Mamy kuwa shiru tayi, saboda tasan idan abun da tayi yakini gaskiya ne, to kuwa Rayyern bai kyauta ba.
Ganin da tayi kuma Abban ya ci gaba da shan coffee dinne, yasa ta tashi ta wuce kitchine Dan k’arasa had’a abincin dare, domin bata son Ramadan ya dawo ya samu bata gama had’a abincin ba, kasancewar yanzu duk hankalinsa, ya koma kan hospital dinsu, tun safe Idan ya fita sai bayan magrib yake dawowa, hatta yau Weekend ma bai zauna ba.
*Moscow.*
Gaba d’aya cikin d’akin da suke gwaji din, ya d’auki shiru babu abunda kakeji kuwa, sai k’aran na’urori da kuma sanyin, AC dake tashi duk da sanyin dake garin kuwa, amma yanayin aikin da sukeyi din yana tsananin buk’atar sanyi.
Yanayin test din nasu kuwa ya kasu kashi biyu ne, domin kanana daga cikin Doctors din suna gwada aikinne, akan robot ma’ana wasu halittun da aka kirkira ma tsakaita kuwa, akan halintun kananan dabbobi sukeyi nasu gwajin.
Yayinda manya manyan Doctors din, da suka amsa sunansu masu experience ke gwada, aikin akan mutane majinyata way’anda, suke fama da lalurar kidney.
Acikinsu kuwa harda Dr. Rayyern Bashir Muhammad Mai-nasara, wanda ya bada gaba d’aya attension d’insa, akan wanda yakeyiwa aikin, agefensa kuwa Dr. Sulaiman ne da kuma Dr. Nick Michel, wanda shima Babban Dr. ne ak’asar France.
Saidai duk da k’warewansa idanu ya zubawa, Rayyern alokacin da yake aikin dashen k‘odan.
Saboda su iya nasu mik’o masa kayan aiki ne.
Adai-dai lokacin da Rayyern ya kammala, dasa k’odan bayan ya d’inke cikin mutumin dake kwance, ne ya sauk’e wani irin nannauyar Ajiyar zuciya, tare kuma dasa hannu ya dafe saitin zuciyarsa.
“Yah Rabbi”
Ya k’ira sunan Allah abayyane,
Cike da gamsuwa hadi da samun k’arfin guiwa, da yarda akan cewar Allah’n ne maiyi, shine kuma mai bada sa’a akoda yaushe shike rayawa ya kuma kashe.
Kashe wutan theater room din da yake ciki yayi, da kansa kuma ya turo gadon da mutumin ke kwance har zuwa wani extra room, wanda acikinsa ne za’a jere way’anda akayiwa surgeryn, saboda a tabbatar da lafiyarsu.
Kusan Atare Doctors din suka kammala aikin nasu.
Yayinda zuciyoyinsu ke cike da alhinin, yanda way’anda sukayiwa aikin zasu tashi.
Dukansu kuwa Fatansu shine, patients din su tashi lafiya batare da wata sabuwar matsala ba.
Almost 1hour suna zaune cikin zullumi, saboda har yanzu babu d’aya daga cikin majinyatan da ya farka.
Ak’a’idan aikin nasu kuwa, wanda patient d’insa ya fara farkawa batare kuma da wata matsala ba shine yazo first.
Cikin sa’a kuwa Patient din Dr. Rayyern Muhammad Mainasara ne ya fara bud’e idanunsa.
Inda kuma ya tashi garau batare da juyewan, brain ko haddasuwan wata matsalan ba, Dan Koda ya bud’e idanunsa acikin hayyacinsa yake sai yan kananun surutan da suke dole, bayan ƙaƙkanin lokaci kuma ya zama dai-dai.
Wani irin farinciki na ya cika zuciyar Rayyern, lokaci d’aya kuma ya shiga godewa Allah, saboda yasan bayin kansa bane, kowacce Nasararsa daga Allah ne.
Gaba daya Doctors din sun Taya Rayyern farinciki, tare kuma da mamakin k’warewarsa, musamman Envigelators da suka kasance consultant's ne, saboda basu tab’a tunanin wani
Daga cikin Doctors din zai k’ware da sauri akan abun har haka ba, musamman ma shi da yake d’an Nigeria, basu tab’a tunanin shi zaiyyi wining ba.
Domin faruwar hakan alamace dake, nuna musu babban nasararsa, shine kuma zai karb’i award na ban girma, tare kuma da certificate din da zai nunawa duniya, cewar shi babban likita ne, amintacce kuma yardajje akowacce k’asa.
Tabbas Rayyern yaji dadin hakan azuciyarsa, domin ko babu komai zai kankaro mutumcin k’asar sa.
Alhamdulillah Sauran
Patients dinma, da akayiwa operations din sun bud’e idanunsu, cikin sa’a kuwa kowanne da hayyacinsa ya dawo hakama nasu Dr Sadiq da sukayi gwajin su kan ƙananun dabbobi suma na Dr Sadiq ya tashi lfy bisa alamu gaba zai taka matakin da Rayyern ya taka a yau.
Sosai Doctors din sukayi kokari, harma way’anda suka gwada nasu akan mutum mutumi.
3:00 pm Dai-dai suka kammala, duk wani abunda zasuyi, Ganin garin nata k’ara gumewa da snow ne kuma, yasa duk suka watse, kaitsaye Rayyern ya nufo gida.
Saidai kuma kafun ya k’araso saida ya tsaya, amasallaci yayi Sallan La’asar, kana ya biya Halal restaurant yayi musu takeaway, na Arab dishes kafun ya