Showing 60001 words to 63000 words out of 104589 words

Chapter 21 - Tubali Book 2 Hausa Novel Complete

Unknown   

21 Dec 2024

173

Jannart, Dan kawai su cutar da ita.”

Idanu Momyn ta tsura masa, saboda itama kullum irin tunanin da takeyi kenan, saidai kuma abubuwa da yawa ayanzu kan kulle mata Kai, Lallai akwai Sark’ak’iya mai nauyi, da kuma k’ulli mai wuyar kuncewa, wanda yake cikin gidan da basu sani ba, sau dayawa zuciyarta kan gaya mata, cewa Lallai akwai wani b’oyayyen abu, da ake b’oyewa.
Wanda kuma ita kanta batasan sai yaushe ne, sirrin b’oyen zai fito fili ba.

Ajiyar zuciya ta d’an sauk’e tare da gyara zamanta, cikin sanyin murya mai d’auke da damuwa tace.

“Abubuwa da yawa suna damuna Abdull, bayan b’atan Jannart da kuma rashin lafiyar Dadynku, har da son sanin wani abu da aka bunne, ay’an kwanakin nan bana iya bacci Abdull, bansan mai yasa ba kwata-kwata bani da nutsuwa, saidai koma meye Ina rok’on Allah da ya kawoshi da sauki.”

“Ameen.”
Abdull din ya amsa, tare da mik’ewa kaitsaye ya wuce d’akinsa, saboda agajiye yake sosai.

Itama Momyn mik’ewa tayi ta koma d’akinta, saboda tun daren shekaran jiya da kunnuwanta suka jiye, mata wani abu gaba d’aya ta kasa sukuni, duk da ta kasa fahimtar inda kalaman da taji Mijin nata na fad’a awaya suka dosa, saidai Tabbas tasan abune mai d’auke da Sark’ak’iya, wanda acikinsa babu komai sai zallan tashin hankali, rud’ani da kuma bayyanar b’oyayyar gaskiya.

Barrister Kabir.
Ahankali yake har had’a wasu takardu dake gabansa, zuciyarsa cike take da kwarin guiwa, na samun duka shaidun da yake buk’ata.

Har had’a takardun yayi awaje d’aya, har dai yazo kan wani file na k’arshe, wanda asaman file din, aka rubuta suna kamar haka, *Barrister ABDULKARIM SALEH DAKATA.*

Ajiyar zuciya Barrister Kabir din ya sauke, tare kuma da d’an jujjuya file din, lokaci d’aya kuma yaji idanunsa, sun cika da k’walla.
Cikin jajircewa da kuma tabbatarwa da kansa yace.

“Insha Allah Koda baka raye gaskiya zatayi halinta, abunda aka b’oye zai fito fili, Ranka bazai tafi a banza ba, Lallai dole kowa zai sani, nan babu jimawa zan tone duk wani abunda suka bunne da izinin ubangiji.”

Ya k’are maganan with full confidence, tare da tashi ya taka kan wata kujera, takardun dake hannun nasa ya maida, can sama wajen ajiyarsa ta sirri, da duk duniya babu wanda ya sani daga shi sai Allah.
Bayan ya b’oye takardun ne kuma, ya bud’e k’ofar d’akin nasa, ya fita zuwa wajen iyalansa dake falo.

*Mascow*

Sai 11:30 pm Dai-dai na k’asar yake shigowa cikin gidan.

Bayan ya gama dai-dai-ta parking ne kuma, Ahankali ya bud’e murfin motar ya fito.
Kallo d’aya zakayi masa kafahimci cewa agajiye yake sosai, saboda tunda suka zo kasar, wannan ne karo na farko daya fara lattin dawowa gida, haka zalika kuma yaune karo na farko da sukayi aiki sosai.

Agajiye yake takunsa, Yayinda yasa hannayensa duka biyu, ya zare suit din dake jikinsa.

Ahankali ya tura k’ofar falon ya shiga.

Babu kowa acikin falon, wanda dama kuma bai tsammaci hakan ba, shiyasa ma kaitsaye ya wuce d’akinsa.

Briefcase da kuma car key d’insa ya ajiye akan bed, Ahankali kuma Cikin nutsuwa ya soma, rage kayan dake jikinsa, takalmi da kuma safar k’afarsa ya cire, kana ya zare duk wani kaya dake jikinsa.

D’aya daga cikin sabin towel d’insa ya d’aura akan kugunsa, duk sanyin da akeyi kuwa hakan bai damesa ba, kaitsaye ya wuce toilet yayi wanka.

Koda ya fito daga wankan kuwa, mai kawai ya shafawa jikinsa, sai wani 3quater daya saka.

Tabbas ya gaji sosai domin har wani rufewa idanunsa keyi, bud’e d’an madaidaicin fridge’n dake cikin d’akin yayi, wani babban packet na chocolate d’insa ya d’auko, tare da dawowa ya kwanta akan gado.

Idanunsa ya lumshe ahankali tare dasa, hannunsa ya d’an shafa saman mararsa, saboda kasala yakeji sosai ajikinsa.

Ahankali kuma yana daga kwancen, ya saka hannunsa ya d’auko chocolate d’aya yakai cikin bakinsa.

Jin zakin chocolate din abakinsa ra d’aune kuma, yasa shi sake lumshe idanunsa, tare kuma da gyara kwanciyarsa, bayan ya sake zuba wasu chocolates din abakinsa.

Yana taunawa ahaka har bacci ya d’aukesa, da ledan chocolate din ahannunsa tamkar wani k’aramin yaro.

Jannart kuwa tuntuni dama ta riga da tayi bacci, Dan koda tayi sallan isha, da tazo falon bata samu abinci ba, komawa tayi ta kwanta, kasancewar dama bawai wani yunwa takeji sosai ba.


Washegari kuwa kamar yanda ya saba, tun kafun ya fita yasa aka kawo masa breakfast, bayan yaci nasa yabar mata nata, kaitsaye ya sake wucewa wajen aiki.

*** ***

After 9days.

Tabbas Rayuwa tafiya take, haka ma kwanaki k’arewa suke, akullum kuma lokaci baya jira.

Koda yaushe haka sukeyin rayuwarsu shida ita, zasu kwana agida d’aya amma sai su share, sama da sati babu wanda yaga d’an uwansa, musamman Rayyern da ayanzu, yake cikin tsananin busy, Dan Koda ishashshen lokacin kansa ma bashi dashi.

Domin tun awancan ranan da takai masa wayarsa, bata sake sakashi a Idanunta ba, takan fito ta zauna afalo Idan bayanan.

Sannan aduk sanda ya ajiye mata abinci, takanci kad’an tabar sauran.

Kasancewar kuma ranar yau ta kama Wednesday ne, ya sata fitowa falon dan akwai wani series film din da takeson kallo.

Ahankali take tafiya harta k’araso tsakiyar falon, inda ta sauk’e idanunta akan ledodin halal restaurant dake ajiye akan table.

Sam bata wani jin yunwa sosai shiyasa, ko kula abincin ma batayi ba.

Zama tayi akan kujera tare da kunna tv, saidai taga ba’a fara series dinba, hannunta ta mik’a saman kujeran, dan d’aukan remote, karab kuwa idanunta suka sauk’a akan, sachet din maganin Rayyern din, wanda babu komai aciki, da alama ya shanye ragowan.

D’aukan empty sachet din tayi, tare da d’an jujjuyawa aranta tana me mamakin, Kodai ya k’arar da wannan din, har ya fara shan wani ne?

Sanin halinsa nak’in magani da tayi ne, kuma yasa ta watsar da tunanin gefe, ledan abincin daya ajiye tun na safe ta d’auka takai kitchine.

Ganin yanda kitchine din ya d’an hargitse ne, kuma yasa ta tsaya gyarawa.

Tana cikin gyaran ne kuma Idanunta, suka sauk’a akan wani babban roba mai murfi, k’arasawa tayi ta bud’e robar, ga mamakinta kuma sai taga pure honey ne, mai kyau aciki.

Wani irin dadi taji saboda dama tanason honey, kasancewar ta kammala duk wani abu da zatayi ne kuma, yasa ta d’auki wani d’an plate na glass ta zuba honey din aciki.


Anutse ta dawo cikin falon, hannunta rik’e da plate din tana lasar zuman da yatsanta na dama.

Zama tayi akan kujera tare da nannad’e k’afafunta, ta ci gaba da lasan zuman, rabin hankalinta kuwa naga tv saboda ansoma haska series film din.

Acan b’angaren Rayyern kuwa, yau din tun 1:00pm
suka shiga heart surgery, basu suka fito ba kuma sai 3:00 pm.

Tunda suka fito yakejin kansa duk wani iri, kasancewar tun safe yakejin cikinsa na d’anyi masa ciwo, dan ko abinci bai iya samu ya sakawa cikin nasa ba, drinks kawai yasha.

Ahankali ya saka tissue ya goge fuskarsa, saboda wani irin gumi dayaji na fesowa akan goshinsa, duk da sanyin da garin ke dashi.

Still jin cikin nasa nad’an ci gaba da ciwo ne, yasa shi tuna rabonsa da magani yau kwana 3 kenan wunin na hud‘u, gashi kuma magungunan nasa sun k’are bai samu ya sayo wani ba.


Sulaiman dake gefensa ne ya d’an kalleshi, cikin kuma d’anyi k’asa da murya yace.

“Rayyern are you okay?”

D’agowa Rayyern d’in yayi, batare daya kalli Sulaiman dinba yace.

“Yea I’m okay.”

D’an Jim Sulaiman din yayi, saboda tun daga cikin hospital din ya fahimci, kamar Rayyern din baya jin dadi.

Saboda ya sake tabbatar da abunda yake zargi ne kuma, ya sashi cewa.

“Rayyern ka tabbata you’re okay.”

Idanu Rayyern din ya d’an lumshe, kana cikin kosawa yace.

“I’m okay mana Sulaiman, if I’m feeling bad mood, I will tell you, so please leave me alone, cause I’m tired..”

Ya k’are maganan cikin cije l’abbansa, saboda baya son yawan tambayoyi.

Sulaiman kuwa Ganin yanda Rayyern din keyi ne, ya sake yardarwa kansa cewar he’s not okay.

D’an gyara zamansa yayi tare da fuskantar Rayyern din, cikin tausasawa yace.

“No Rayyern k’arya ba d’abi’arka bace, wallahi zan iya rantsewa baka da lafiya, gashi kana zufa a inda ban tab’ayin zufa ba, Rayyern a Mascow fa muke, garin da ko ina dinsa sanyi ne, kayi tunani Idan mutum yana lafiya zaiyi zufa awannan garin ne a irin wannan lokacin? Rayyern baka da lafiya, saboda haka tell me what’s wrong with you?”

Idanu Rayyern din ya lumshe, saboda yasan halin Sulaiman da takura, Idan bai fad’a masa gaskiya ba bazai k’yaleshi ba.

“My stomach has paining.”

Ya fad’a atak’aice.

Idanu Sulaiman din ya zaro, cike da fargaba hadi da tsoro yace.

“Subahanallah Rayyern, kana shan maganinka kuwa?”

“Eh but two days ban Shaba, saboda sun kare ban samu time na saya ba.”

Rayyern din ya basa amsa kaitsaye.

Sulaiman kuwa ido ya tsura masa, kana cikin dan yanayin tausayawa yace.

“Haba Rayyern Meyasa kakeson yin wasa da lafiyarka? kasan yanda ciwon nan keyi maka idan ya tashi, please dan Allah kana kiyayewa, kasani bawai kai kad’ai kake da buk’atar lafiyarka ba, su Abba da Mamy suna da buk’atar ka, can you imagine yau ace bakanan, mekake tunanin zai faru? bana fatan haka Rayyern Dan Allah kana kulawa da kanka, yanzu tunda yau mun fito da wuri kaje pharmacy ka saya maganin.”

Kai Rayyern din ya jinjina kawai, tare da mikewa tsaye, batare daya sake cewa komai ba kaitsaye ya nufi wajen motarsa.

Ganin hakanne kuma yasa Dr. Sulaiman had’a sauran Doctors dinsu, suka tare taxi dan komawa masaukinsu.

Rayyern kuwa yana shiga cikin motar yayi mata key, kaitsaye wani babban pharmacy dake gefen Hospital din ya nufa, Koda yaje bai samu maganin nasa ba, saidai sunyi masa kwatancen wani pharmacy, wanda suke da tabbacin cewa zai iya samun maganin idan yaje can.

Agajiye sosai yakejin kansa shiyasa bai iya jurewa, tafiyanba kaitsaye restaurant ya biya ya saya abinci, saboda yunwa yakeji sosai.

Isowarsa gidan kenan yana gama dai-dai-ta parking din, motar ya fito hannunsa rike da ledan abincin da kuma suit d’insa, ya nufi cikin gidan.
Ahaka ya shigo falon da cikinsa ya riga ya d’an d’auki dumi, saboda na’urar d’umama d’aki da Jannart din ta kunna.

Ahankali ya zauna akan kujera, tare da bud’e ledan abincin, take away d’aya ya ciro tare da bud’ewa, Ahankali ya d’auki spoon tare da Kai loman abincin bakinsa.

Idanunsa ya d’an rumtse tare da ajiye spoon din, kana ya maida jikinsa ya kwantar, Hannunsa na dama ya d’aura akan cikin nasa dake ciwo, domin zuwa yanzu ciwon nata k’ara tsumuwa...!
By
*GARKUWAR FULANI*Da k’yar ya iya had’iye abincin dake bakin nasa, batare kuma dajin zai iya ci gaba da cin abincin ba, ya mik’e tsaye tare da wucewa bedroom d’insa.

Bayan ya rage kayan jikinsa ne kuma ya shiga wanka.

Abu fa kamar wasa duk bayan wasu yan mintuna, yakanji ciwon cikin nasa na k’aruwa, saidai kasancewar sa mai dauriya shiyasa yake iya jurewa.

Ahankali ya murd’a handle din kofar ya fito, sanye yake da rigar wanka fara k’al, Hannunsa na dama kuwa rik’e yake da towel yana goge ruwan jikinsa.

Ganin da yayi lokacin sallah ya kusa ne kuma, yasa shi sanya wani riga da wando agurguje, saidai rigar irin short sleeve dinnan ne, slippers ya saka ak’afafunsa saboda sauri kuwa, ko wayarsa bai d’auka ba, yana mejin ciwon na tasar masa kadan kadan, haka ya d’auki key din motarsa ya wuce masallaci.

Jannart kuwa yau din Koda ta idar da sallan Isha ba ta fito cin abincin ba saida tayi wanka, inda ta shirya kanta cikin wani riga da wando, like sleeping dress, saidai suna da kauri sosai, sannan jikinsu nada laushi da kuma gashi tamkar jikin kuliya-mage, sosai kayan ya bi jikinta musamman wandon, daya bayyana shape din hips dinta, sai kuma rigar da ta kasance tana da d’an fad’i, saidai hakan bai hana tudun breast dinta bayyana ba.

Kamar yanda ta saba kuwa hulan sanyi ta saka akanta, tare da watsa dogon gashinta baya.
Turaren oud ta shafa ajikinta, cikin d’an hanzari ta fito falon saboda cikinta ya fara yi mata kukan yunwa.

K’arasowa cikin falon tayi ta zauna, tare da jawo ledan takeaway din gabanta.

Abincin ta tsurawa ido saboda taga kamar ba, alaman anci abincin sosai, da alamar Koda ancisa ma to bai wuce loma d’aya akayi ba.

D’an Jim tayi kamar meyin nazarin wani abu, sanin bai wani damu da cin abinci sosai bane yafi ta'ammali da kayan zaƙi, yasa ta share tunanin, abincin ta d’anci kad’an kafun ta tashi ta wuce d’aki, saboda yau din ana d’an tab’a sanyi sosai, gashi kuma bacci sosai takeji.

Rayyern shi kuwa Dr Rayyern.
Tun da ya shiga cikin masallacin bai fito ba, saida aka idar da sallan Isha, bayan ya d’an tab’a karatun Al’Qur’ani ne kuma ya d’auko hanyar dawowa gidan.

Ahankali yake taka k’afafunsa, tare kuma da kutso kansa cikin falon, gaba d’aya bayajin yana yanayi mai dad’i saboda ciwon cikin dake damunsa, duk da cewa ciwon nasa bai tsananta ba, amma dai yanayi masa kad’an kad’an, kaitsaye d’akinsa ya wuce batare da ya lura da ko Jannart din taci abincin ba, yana shiga kuwa ya fad’a kan gadonsa, tare dayin rigingine kana yaja blanket ya rufe jikinsa.

Cikin nutsuwa yake ambaton sunan Allah abakinsa, hade da lumshe kyawawan idanunsa da suka d’anyi ja, yana ahaka cikin ikon Allah bacci ya d’aukesa.

Washegari.

Kamar yanda ya saba tashi akowacce rana haka ma yau din ya tashi, saidai kuma tun tashinsa yaji cikin nasa na ci gaba da yi masa ciwo.

Duk da yana jin ciwon kuwa haka ya shirya kansa, cikin riga da wandon suit, sai kuma wani babban jacket daya d’aura akai.

Yana fitowa kuwa aka kawo breakfast, saidai ko ci baiyi ba haka ya tafi, saboda duk yana jin bakinsa babu dadi.

Jannart kuwa yau din bacci tasha sosai, Dan bata tashi ba sai k’arfe 10, bayan tayi wanka ne kuma ta fita zuwa falon.

Abincin ta d’auka taci, saidai bata wani ci sosai ba ta ture shi gefe, anan cikin falon ta kwanta, tare da d’aukan wayanta ta soma buga game.

Rayyern kuwa Koda ya shiga wajen meeting dinsu, gaba daya ya kasa nutsuwa, domin tun yana maida attension d’insa garesu, har dai abun ya soma fin karfinsa.

Fahimtar hakan da Dr. Sulaiman yayi ne kuma yasa shi, d’anyin k’asa da murya cikin kulawa yace.

“Gaskiya Dr. Rayyern ya kamata mufita mu nemo maganinka, domin naga har yanzu kamar you’re not okay.”

Idanu Rayyern din ya d’an rumtse, batare kuma da yace komai ba, ya jawo system d’insa ya soma latsawa.

shi dai kam Dr. Sulaiman yasan halin kafiyar Rayyern din Sarai, shiyasa ma baisake bi ta kansa ba, d’aya daga cikin manyan Doctors din da sukeyi musu, invigilators Dr. Sulaiman din ya samu, tare da gaya musu matsalan Rayyern din.

Wani magani d’aya daga cikin manyan Doctors din, ya rubuta tare da bawa Dr. Sulaiman yace ya nemo ya bawa Rayyern din yasha.

Sanin halin ciwon Rayyern din Idan ya tashi ne kuma, yasa babu wani b’ata lokaci Dr. Sulaiman ya fita zuwa sayo maganin.
Sosai kuwa maganin ya basa wahalan samu, Dan saida ya zagaye pharmacy har biyu amma babu, cikin sa’a kuwa a pharmacy na uku ya samu maganin.

Bayan ya dawo ne kuma ya bawa Rayyern din yasha.

Ahankali ya jingina bayansa da jikin kujera, tare da lumshe idanunsa, numfashi kawai yake sauk’ewa akai akai, Yayinda zuciyarsa kuwa ke bugawa da k’arfi.

Yana nan zaune ahaka har tsawon 30mn cikin, taimakon Allah kuwa ahankali yakejin ciwon nasa na lafawa.

3:30pm dai-dai yauma suka tashi daga meeting din nasu, inda suka tsaya wani d’an tattaunawa kuma wanda ya d’aukesu tsawon 30mn.

4 dai-dai amfanin maganin daya sha din ya k’are, Aikuwa ko mintuna biyu ba’a cika ba, yaji cikin nasa ya dawo da ciwo.

Ciwo kuma gadan gadan ba kaman yanda, ya tashi masa da safe ba.
Hakan yasa duk bayanan da sauran Doctors din keyi, baya fahimta.

Ahankali ya janye jikinsa baya, tare kuma da d’aukan car key d’insa.
Batare kuma daya tsaya sauraran wani abu ba, ya nufi inda ya ajiye motarsa.

Dr Nura dake ya dan zuba mishi ido ne.
Ya ɗan nunawa. Dr Sulaiman dake kula da duk wani motsinsa shi
Ganin ya juya ya fitane, ya biyosa saidai kafun ma ya iso, tuni Rayyern ya cilla motar tasa kan titi.

D’an Jim Dr. Sulaiman din yayi , acikin ransa yana me fatan Allah yasa kada ciwon Rayyern din ya tashi.

Rayyern kuwa tunda ya cilla motar tasa kan titi, ya daina fahimtar wasu abubuwan, murza steering motar kawai yakeyi, batare da yana tantance abunda yakeyi ba, saboda zuwa yanzu ciwon nasa ya tsananta sosai.

Wani irin gudun da yakeyi ne kuma, yasa cikin mintuna kad’an ya iso bakin k’ofar gidan nasa.
Yanayin yanda yakejin ciwon nasa ne kuma yasa, ko tsayawa saya musu abinci yau din baiyi ba.

Bayan ya dai-dai-ta parking ne kuma ya bud’e murfin motar ya fito, Cikin yanayin tafiyar dake nuna galabaitarsa, kaitsaye ya wuce cikin falon.

Yana shiga ya fad’a akan kujera, tare dasa hannayensa duka biyu ya rik’e cikinsa, idanunsa ya rumtse da k’arfi.
Domin har cikin jijiyoyin jikinsa yakejin rad’ad’in ciwon cikin.

Wani irin numfashi yake fitarwa, mai d’auke da tsananin wahalan da yakeji, saboda zafin ciwon da yakejin ne, yasa shi soma jujjuya kansa Ahankali, yake sakin nishi wanda yake fita daga bakinsa.

Jannart kuwa dake kwance a d’aki tana game, kwata-kwata bata ma ji koda motsinsa ba, saboda dama takan gane cewar ya dawo ne, ta hanyar k’aran motarsa.

Almost 1hour.

Ahankali ya bud’e idanunsa wanda yakejin sunyi masa nauyi, tare da soma sauk’e Ajiyar zuciya akai akai, lokaci d’aya kuma ya d’anji jikinsa na sakewa.
Anutse ya d’an d’ago kansa ya kalli agogon dake falon.

“6:19 pm Dai-dai da ya ganine, ya sashi yunk’urawa cikin k’arfin hali ya mik’e tsaye.

“Alhamdulillah.”
Ya fad’a k’asa k’asa saboda yanda yaji ciwon ya d‘an lafa masa.

Asanyaye ya nufi bedroom d’insa, Koda ya shiga kayan jikinsa ya cire, tare da shiga toilet yayi wanka had’i da d’auro alwala.

Duk way’annan

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login