Showing 39001 words to 42000 words out of 104589 words
kasa ya mishi mgn, sai yakeji tamkar Abba yaga abinda ya faru.
Da kallon mamaki Abba yabi bayan Rayyern din, musamman da yaga yanda bayan rigar Rayyern din, ke jik'e da ruwa, wanda kuma shi a iya saninsa, ko digon yayyafi ba'ayiba balle ko yace shiya jik'a Rayyern din.
Ajiyar zuciya kawai Abban ya sauk'e, tare da mik'ewa shima yayi b'angaren sa.
Rayyern kuwa yana haurawa sama, rigar dake jikin nasa ya cire.
Tare da sanjata izuwa wata, Ahankali ya d'an zauna abakin gadonsa tare da jawo Laptop d'insa ya soma hidimar tafiyarsu Mascow.
Saidai gaba daya ya kasa daina jin k'amshin Jannart din acikin hancinsa.
D'an rumtse idanunsa yayi, tare kuma da bud'esu alokaci guda, cikin d'an yanayin k'osawa yace.
"Fitinanniya."
Acan b'angaren Jannart kuwa Koda ta shiga d'akinta, kwanciya tayi lub akan gado, tare da d'aukan wayarta ta soma buga game.
Duk yanda taso maida hankalinta akan game din kuwa abun yaki, domin hakanan takejin k'amshin jikin Rayyern din, ya kasa barinta tayi sukuni, duk da cewar baya wajen amma mayen kamshinsa yana wajen.
Fuskarta ta d'an ya mutse, tare da shagwab'e murya, cikin kasa da murya tace.
"Ai duk shiya jawo muka fad'i, da wani k'amshinsa awajen."
Yanayin yanda tak'are maganan tana murgud'a baki, Idan ka gani zakayi tunanin agabansa take.
Almost 40minute kuwa ana tsula iska kana hadarin gaba d'aya ya washe, dai-dai lokacin kuma aka soma kiraye kirayen sallan magriba.
Atare duk mazan gidan suka wuce masallaci, Abba, Rayyern Ramadan da kuma Riyyam-nsra.
Acan suka iske Baba Maud'o ma, wanda shi yakan riga ma kowa dake gidan tafiya masallaci.
Koda sukayi sallan magriban kuwa, basu fito daga masallacin ba har saida suka sallame sallan Isha.
Koda suka dawo gida, anan kan dining table suka zauna, Yayinda Abba kuwa ya wuce sashinsa kaitsaye.
Mamy ne takai masa abincinsa, Ramadan da Riyyam-nsra kuwa Jannart ce tayi saving d'insu.
Ubangayyan kuwa bai hawo kan dining table d'in ba, anan cikin falon ya zauna, batare kuma daya ce akawo masa nasa abincin ba.
Itakuwa Jannart tana sane dashi, amma saita share batare da ta tambayesa ko yana buk'atar abinci ba, ta nemi waje ta zauna, tare da soma tsakalan abincin da ta zubawa kanta.
Rayyern dake zaune kuwa Ganin Mamy ta fito daga b'angaren Abba ne, yasa shi mik'ewa tsaye.
"Babana kai bazakaci abincin bane?"
Mamy ta tambaya da kulawa.
Fuskarsa ya d'an yamutsa, cikin kuma halinsa na rashin son yawan mgn daya tashi masa yau din yace.
“Ba'a bani ba”.
Yanayin yadda yayi mgnar yana kuma kallon Jannart ƙasa-ƙasa ne yasa, Mamy yin murmushi tare da cewa.
“To bari a kawo maka”.
Cikin kauda kai yace.
"No Mamy ni nakoshi."
"Amma Babana kafasan baka jima da tashi daga ciwo ba, Meyasa bazaka maida hankalinka wajen cin abinci akan lokaci ba?"
Mamyn ta fad'i haka cike da nuna masa, tsananin soyayyar da takeyi masa.
D'an marairaice fuskarsa yayi, hakan yasa yayi tamkar k'aramin yaro.
"Seriously Mamy nak'oshi ne, kuma anjima zansha tea, yanzu bari naje wajen Abba."
Ya k'are maganar yana me nufan sashin, Abban kaitsaye.
Mamy kuwa da Idanu ta bishi har saida ya shige part din Abban, kafun ta janye idanunta tare da dawowa kan dining table din ta zauna.
Ahankali Rayyern ya tura k'ofar d'akin Abban ya shiga bakinsa d'auke da sallama.
Abba dake zaune akan carpet, yana cin abinci ne ya d'ago kansa, tare da amsawa Rayyern din sallaman, fuska asake yace.
"Rayyern shigo mana."
Abban ya fad'a cikin kulawa.
K'arasowa cikin falon Rayyern din yayi, tare da matsowa ya rusuna agaban Abban nasa, cikin girmamawa had'i da ladabi yace.
"Abba barka da warhaka."
Kai Abban ya jinjina, tare da d'aukan d'aya daga cikin spoons d'in dake, kan tray din abincinsa ya mik'awa Rayyern din.
"Muci abinci."
Abban ya fad'a cike da kulawa.
Kansa ya d'an rausayar gefe, tare dasa hannu ya shafa cikinsa, cikin sanyi yace.
"Abba nak'oshi."
Kallonsa Abban yayi kamar zaice wani abu kuma saiya fasa, saboda dama yasan halin Rayyern cin abinci akai-akai bawai ya wani damesa bane sai daifa idan ya ritsa abinda yakeso ba sauki.
Rayyern kuwa d'an gyara zamansa yayi, tare da fuskantar Abban nasa, cikin muryar dake nuna girmamawa yace.
"Abba dama akan maganan tafiyarmu Mascow ne”.
D’an zuba mishi ido Abba yayi kana ya dauki cup ruwa ya dan sha kana ya aje tare da cewa.
“Uhum ina jinka".
Gyara zamansa ya danyi tare da ci gaba da cewa.
“Yanzu mun kammala komai ranar tafiyan nata matsowa, kuma Ina d'aya daga cikin way'anda zasu tafi, saboda ni nema zanyiwa sauran Doctor's din jagora, da nayi tunanin bazanje ba, amma kuma sai naga zuwan yana da muhimmanci, saboda akwai babban likita daya daga cikin malamaina nacan, daya nunamin dacewar zuwan nawa, tunda duk way'anda zasuje din ak'ark'ashin kulawana suke, To ya kamata na kasance tare dasu."
D'an dakatawa da cin abincin Abba yayi, tare kuma da d'ago kansa ya kalli Rayyern din, cikin gamsuwa yace.
"Masha Allah, ashe har tafiyar tayi kusa, zuwa nanda yaushe ne zaku tafi?"
"Nan da sati biyu Insha Allah."
Kai Abba ya jinjina tare da cewa.
"Allah ya kaimu, amma naji ku biyar zaku tafi, saidai ka manta masauk'inmu da yake can, wajen zaman mutum biyu ne kawai sai inga kamar zaku takuru a ɗan gidan tunda ba wani babba bane."
Kai Rayyern din ya jinjina tare kuma da gyara zamansa, cikin kwantar da murya yace.
"Eh Abba, su sauran staffs din namu, hotel zamu kama musu, nida Usman P.A ne kawai zamu zauna, anan gidan."
Kallonsa Abba yayi cikin dan yanayin mamaki yace.
"Kaida Usman P.A kuma?"
"Eh Abba, dashi zamu tafi saboda nasan zai d'an ragemin wasu ayyukan."
Rayyern din ya fad'a atausashe, daga cikin zuciyarsa kuwa yana tsoron kada Abban, nasa ya shigo da wata buk'atar.
Abba kuwa kansa ya girgiza, tare da cewa.
"A'a kam bada Usman P.A zaka tafi ba, da matarka zaka tafi."
Azabure Rayyern din ya d'ago kai, tare da zaro idanunsa ya kalli Abban, cikin yanayin kad'uwa yace.
"What Abba...."
D'aga masa hannu Abban yayi alaman dakatarwa, cikin nuna masa gaskiya da kuma hakikanin tabbacin maganansa yace.
"Na maimaita da matarka zaka tafi Rayyern, ba kuma zan sanja magana ba, saboda banason irin abunda ya faru dakai a China ya sake faruwa, Ina da tabbacin cewa matarka zatafi kula dakai, fiye da Usman P.A, domin shi ba ad'aki d'aya zaku dinga kwana ba, kaga bai zama lallai yasan awani hali kake ciki ba a cikin dararen zamanku a can, amma matarka fa tana tare dakai akoda yaushe, Dan haka za tafi kowa, sanin wanne hali kake ciki."
D'an numfasawa Abban yayi, kana cikin kulawa yaci gaba da cewa.
"Lafiyarka tafi mana komai Rayyern, akoda yaushe bama son duk wani abu na cutarwa dazai sameka, saboda haka bazamu tab'a barinka ka kasance awata duniya, Kai kad'ai babu wani mai baka kulawa ba."
Fuska Rayyern din ya kwab'e, lokaci d'aya kuma yaji komai duk ya daina yi masa dad'i, bakinsa ya bud'e ahankali da niyar yin magana.
Saurin dakatar dashi Abban yayi, cikin tsare gida yace.
"Kada kace komai Rayyern domin wannan Umarni nane, bawai shawara ba."
Abban ya fad’i haka cikin tsare gida, tare kuma da jajjadada umarninsa.
K’asa Rayyern din yayi da kansa, tare kuma da d’an marairaice fuska cikin sanyi yace.
“Kayi hakuri Abba bawai Ina ja da umarninka bane, amma Barrister Kabir yace baya son kowa yasan cewar tana nan gidan, Koda kuwa zuwa nan da compound d’in gidan ne.”
“Nasan da hakan, shiyasa ma tafiyar da zakuyin babu wanda zaisan kun tafi tare, tunda bawai da kowa da kowa muke mu’amala ba sannan kuma tafiyarku tare kamar wani matakin tsaretane.”
Abban ya fad’a yana me gyara zama danci gaba dacin abincinsa.
Rayyern kuwa badon yaso ba, haka ya mik’e tare da yiwa Abban sallama, kaitsaye ya fice daga cikin falon.
Direct main falo d’insu ya nufo.
Dai-dai lokacin kuwa Mamy da Jannart d’in ke zaune, inda Mamyn ke kan sofa, sai Jannart dake zaune ak’asa tana latsa wayarta.
K’arasowarsa cikin falonne kuma, ya sanyashi kama k’ugu, tare da Kallon gefen da Jannart d’in take, k’asa k’asa ya watsa mata wani kalon da bai san manufarsa ba.
Cikin kuma yanayin shagwab’a ya kalli Mamynsa, tare da karyar da wuya, asanyaye yace.
“Mamy inason muyi magana.”
Jin abunda ya fad’a d’inne kuma yasa, Mamy d’agowa ta kalleshi.
“Magana kuma Rayyern, to inajinka.”
Mamyn ta fad’a tana me maida hankalinta garesa.
“No Mamy dake kawai nakeson magana.”
Ya fad’i hakan cikin gatse da kuma gayya, tare kuma da sake hararan Jannart k’asa k’asa, wanda ita batama san yanayi ba.
Mamy kuwa jin abunda ya fad’a d’inne yasa ta, Kallon Jannart dake zaune, ganin kuma gaba d’aya hankalin Jannart din ba akansu yake bane, yasa Mamyn mik’ewa, cikin nutsuwa tace.
“To mu haura sama.”
Ai kuwa kaman jira dama yake tuni ya shige gaba, Mamyn na biye dashi a baya.
Suna shiga cikin falon nasu kuwa ya juyo, tare da Kallon Mamyn nasa, cikin son isar mata da k’orafi yace.
“Eyyah Mamy kiji Abba fa, wai da wancan yarinyar yakeson naje Mascow, Mamy takurani zatayi Allah, ni kuma Mamy banason takura, yanzu meye laifi Idan na tafi da Usman P.A?.”
Murmushi Mamy tayi, tare da kallonsa Cikin kulawa tace.
“To meye abun damuwa acikin wannan Rayyern, ka tafi da ita mana, kuma kasan baka isa tsallake umarnin mahaifinku ba, Lallai dole abunda yace shi za’ayi, kuma nima bani da wani ja akan hakan.”
Fuskarsa ya shagwab’e tare da karyar da wuyansa gefe, cikin sanyi da rashin samun k’arfin guiwa yace.
“To yanzu Mamy Dan Allah kiyi wani abu mana.”
“Ni babu abunda zan iya Rayyern, kasan waye Abban ku Idan yayi magana baya tab’a sanjawa, nima kuma Ina goyan bayan hakan, saboda hujjar daya kawo hujja ce mai kyau.”
Mamyn ta fad’i hakan cike da son jaddada masa yiwuwar hakan.
Shikuwa Rayyern gane akan maganar tasu babu wani sauyi ne, ya sashi juyawa tare da neman waje ya zauna.
Mamy kuwa kanta kawai ta girgiza, tare da juyawa ta fice daga falon.
Kaitsaye falon k’asa ta nufa, anan. Ta iske Ramadan da kuma Riyyam-nsra wanda yanzu shigowansu, kasancewar bayan sunci abincin daren sunfita wajen su Baba Maud’o.
Ganin sunata hira ne kuma yasa Mamyn wucesu, kaitsaye ta nufi b’angaren Abba.
Su kuwa su Ramadan sun jima suna hira, kafun daga bisani Jannart ta wuce d’akinta, Ganin hakanne kuma yasa suma duk suka watse.
D’aki suka koma inda kowannensu ya rungumi wayarsa, Musamman Riyyam-nsra da ya sakeyin wata sabuwar budurwa, y’ar k’asar Nigeria kuma y’ar nan cikin garin kano, wanda ta nace masa akan cewar tana son su had’u.
Shikuwa Ganin yanda take tura masa wasu part, daga cikin body dinta ne yasa shi, bata duk wani attension d’insa.
Saidai kuma gaba d’aya ya kasa, sanin wani karya zaiyi, Dan samu ya fita ko zuwa hotel ne su had’u da yarinyar dan sam Rayyern ya saka masa takunkumi.
Acan b’angaren Jannart kuwa, tana shiga d’akinta kwanciya tayi, kasancewar ta gaji ne kuma yasa cikin mintuna kad’an bacci ya d’auketa.
Washegari
kamar kullum ita ta taya Mamy duk wasu aikace akace, bayan sun kammala breakfast bayan taci nata ne, kuma ta koma daki ta kwanta.
Ab’angaren Rayyern kuwa tun 6 ya wuce hospital, saboda akwai wasu patient da yake son dubawa.
Bayan kuma Rayyern din ya tafi ne kuma, Ramadan shima ya mara masa baya, saidai yau harda Riyyam-nsra suka tafi hospital din, saboda shi yace bayason zaman gida.
Ganin duk gidan yayi shiru ne kuma, yasa Mamy da Jannart watsewa afalon suma.
Rayyern kuwa bashi ya dawo gidan ba, sai bayan oppsallan magriba.
Bayan sunyi sallan Isha ne kuma duk suka shigo gida.
Bayan sun kammala Diner ne kuma, suka dawo cikin falon suka zauna.
Jannart ce ta fito daga cikin d’akinta, inda take cikin wani had’add’en doguwar riga navy blue, wanda yayi mata matukar kyau.
Musamman da ta yafa d’an siririn farin mayafi akanta.
Fitowan nata kuwa, yayi daidai da shigowar Rayyern cikin falon, karab kuwa ya sauk’e idanunsa akanta.
Duk da cewar ba akusa suke ba, amma hakan bai hanasa.
Ganin k’yallin da fuskarta keyi ba, still ga kuma bakinta, da yake fitar da shining na pink lipstick din da ta saka.
Janye idanunsa yayi daga kallonta, tare da k’arasowa cikin falon ya zauna.
Ita kuwa Jannart batare ma da ta lura dashi ba, kaitsaye kitchine ta wuce.
Koda taje ta samu sandwich d’in da take gasawa ya gasu.
Kashe oven din tayi, tare da d’aukan wani bowl, bayan ta saka poil paper aciki ne kuma, ta juye duka sandwich din.
D’aukan bowl d’in tayi ahannunta, tare da nufowa falon cikin takun ta na nutsuwa.
D’an tsayawa tayi ta d’auki tissue paper, kana ta k’arasa isowa cikin falon.
Da Murmushi Mamy ta kalleta, kana fuska asake tace.
“Jannart sarkin aiki, sannu duk kin cika mana gidan namu da k’amshin sandwich din naki.”
Murmushi Jannart din tayi, tare kuma da matsowa ta ajiye bowl d’in sandwich din agaban Mamy.
Cikin kuma d’an yanayin alk’unya tace.
“Bismillah Mamy kici sandwich din.”
“Haba My Aunty Mamy kawai, tun d’azu fa muke zaman jiran sandwich din, da k’amshinsa ya cika ko ina dake cikin falon nan, Allah tun kafun ki kammala yawuna yake ta tsinkewa.”
Ramadan ya fad’a yana me matsowa, kusa da bowl din, tare da yagan tissue ya d’auko sandwich din guda d’aya.
Janart kuwa Murmushi tayi, tare da neman waje ta zauna akan sofa.
Ramadan kuwa Koda yakai sandwich din bakinsa idanu, ya lumshe, tare da jinjina kai, bakinsa cike da sandwich din wanda yaji rid’i yace.
“Gaskiya Aunty Jannart you’re the best, komai kin iya domin ban tab’a cin sandwich mai dadin wannan ba da Allah waya koya miki girki haka?.”
Murmushi Jannart tayi tare da cewa.
“Malamai na nada yawa, Mom Aunty Dijat da kuma AYSHA ALIYU GARKUWA marubuciyar littafin GARKUWA dan na koyi abubuwa da yawa a ciki littafin sai kuma shirin Akoshi da rufi na tasharmu”.
Yana mai haɗiye na bakinsa yace.
“Kai Allah yayi musu al'barka ya jikansu suda iyayensu al'farma Annabi da al'ƙur'ani, ai mu sun mana gata Allah kawo Raihana ki koya mata komai”.
Dariya sosai Riyyam-nsra, Jannart, Mamy sukayi suna masu cewa Amin.
Riyyam nsra dake zaune ne ya taso cikin dariya da sauri, tare da cewa.
“Nima ai baza’ayi banda niba wanga santi.”
Ya kare maganan yana me daukan sandwich din yakai bakinsa.
Idanu ya lumshe tare da jinjina kansa, saboda yanda yaji dadin sandwich dinma harya zarce yanda Ramadan ke fadi.
Rayyern kuwa tab’e bakinsa yayi, tare da kawar da kansa gefe.
Riyyam-nsra kuwa sake gyara zama yayi, tare da ninke k’afafunsa, d’ago da kansa yayi ya kalli Mamy da kuma Rayyern, lokaci d’aya kuma sai yaji duk jikinsa yayi sanyi, wanda hakan yasa asanyaye yace.
“Mamy, Hamma Rayyern this week dinnan fa zan koma Ethiopia”.
Cikin abinda ba gaza one second ba duk suka katse dariyarsu tare da zuba mishi ido cikin tsareshi da ido Rayyern yace.
“Meyasa? Yaushe ka tsara tafiyar?”.
Kanshi ya jingina jikin kujera cikin sanyi yace.
“Saboda Mammy ta matsa akan na dawo, tun last week take min maganan dawowa na to daga nan na fara shirin tafiyar, kuma nima nayi kewarsu sosai, sannan kuma na gama aikin da nazoyi ak’asar nan, yanzu babu wani abu daya ragemin sai komawa”.
Cike da tsananin mamaki Ramadan, ya d’ago da kansa ya kalli Riyyam-nsra din.
Murya araunace yace.
“Koma wa Ethiopia kuma Riyyam? sannan kuma this week why ka bari sai end of the month mana.”
Murmushi Riyyam-nsra din yayi, tare da kwantar da kanshi, cikin sanyi yace.
“Dole zan koma Hamma Ramadan ko shekarane ai zaizo dole in koma, saboda yanzu bani da wani reason na zaman k’asar nan, dama daliline ya kawoni.”
Idanu Rayyern dake zaune ya zubawa Riyyam din, Cikin yanayin nazarta yace.
“Wani aiki ne ya kawo ka, then wani reason?”
Murmushi mai kama dana waskewa Riyyam-nsra din yayi, kana cikin samun madafa yace.
“No Hamma Rayyern ba wani babban aiki bane fa, d’an k’aramin aiki ne kuma ma harna gamashi, dama kawai inada passion nazu wa Nigeria ne kan TIKTOK nema fa.”
Idanu Rayyern ya zuba masa batare daya sake cewa komai ba.
Mamy kuwa cikin dan yanayin damuwa tace.
“Haba Riyyam tafiya hakanan lokaci d’aya, ba zato ba tsammani ka bari mana kad’an k’ara kwanaki.”
Murmushi Riyyam din yayi, tare kuma dasa hannu ya shafa sumar kansa, cikin dan sakewa yace.
“Mamy Mammy ta matsa akan saina dawo, baya ga haka ma najima a k’asarnan almost 4to5 month fa.”
Shiru duk sukayi cike da jimamin tafiyar Riyyam din.
Musamman Ramadan da yakejin zaiyi kewar Riyyam din sosai, haka ma Jannart Domin ba kad’anba Riyyam-nsra din ke d’ebe mata kewa, domin akullum tana ganinsa kaman Abdull d’insu ne, baya ga haka kuma Riyyam din yana da shiga zuciya.
Rayyern kuwa mik’ewa yayi tsam ya nufi sama, saboda yagaji sosai a hospital baya ga haka, kuma yau dinma yaje company saidai ba new company dinsu yaje ba, yaje company dinsu wanda ake sarrafa auduga ne.
Koda ya haura saman kwanciyarsa yayi.
Acan falo kuwa basu yi wani hira sosai ba, duk suka watse kowa ya koma d’akinsa.
Almost 3days.
Kenan yau wanda acikin kwanaki ukun kuma, komai yana tafiya dai-dai musamman ab’angaren new Company, din da su Rayyern din suke son budewa.
Dan zuwa yanzu ankammala komai da komai, har an fara sarrafa kayan provision.
Kowanne store dake cikin company din kuwa, an cika sa da sarafeffen kayan provisions kala daban daban.
Komai na dafawa sun sarrafa shi.
Alhamdulillahi kuma ranar Friday aka tsaida amatsayin, ranar da za’a bud’e companyn.
Kasancewar kuma yau alhamis, shiyasa ake ta shirin bude companyn gobe, wannan yasa gaba d’aya Rayyern bai samu ya zauna ba.
Hasalima Koda ya fita bashi ya dawo gida ba, sai k’arfe 10 dai-dai.
Wannan yasa agajiye yayi bacci.
Washegari ranar jumma’a.
Kusan gaba d’ayansu Atare suka tafi masallacin jumma’a, bayan sun Idar da sallah ne kuma, Abba ke sake shaidawa Baba Maud’o cewar yaune, zasu bud’e sabon kamfanin nasu.
Sosai Baba Maud’o yayi farinciki, tare kuma da fatan Allah ya sanya al'khairi, ya kad’e duk wata fitina, ya kuma sanya musu riba mai albarka.
Da. “Ameen Ameen.”
Abba ya amsa.
Bayan sun dawo daga masallacin ne kuma, suka soma shiri dan zuwa bud’e companyn.
Ganin yanda suke ta hada
hada ne kuma yasa, Jannart dake gefen Mamy matsowa kusa da Mamy cikin sigar rok’o tace.
“Ayyah Mamy dan Allah nima zanje in ba matsala.”
Murmushi Mamy tayi tare da juyowa ta kalleta cikin sakin fuska tace.
“To Jannart ai zaki iya zuwa, amma bari na tambayi Abbanku naji me zaice tunda kin san a tsare kike.”
Kai Jannart din ta jinjina, cike kuma dajin dadi ta cigaba, da juya pepper chicken din da takeyi tare da cewa.
“Toh Mamy a gaya mishi Allah yasa