Showing 84001 words to 87000 words out of 104589 words
jiya muke mgn da Hajia Rabi'ah, kin san itama maigidanta yana Mascow to jiya da muka haɗu wurin aiki take cemin, next week zata taho wurinsa”.
Cikin jin dadi tace.
“Kai Alhamdulillah my Aunty in tazo zatazo wurina ko?”.
Murmushi Fa'iziyya tayi tare da ci gaba da cewa.
“Akwai wasu kayyakine na gani a wurin AYSHA ALIYU GARKUWA, kayane irin namu na mata da kuma kayyakin ƙamshi toh nama saya miki, na bata 80k tayi miki haɗin mai kyau nasa tasa miki komai ɗan dai-dai, in sha Allah zan bawa Hajia Rabi'ah, zata kawo miki”.
Cikin tsananin jin daɗi tace.
“Allah sarki my Aunty ngd Matuƙa Allah ya biyaki da mafi kyawun sakamako”.
Amin Ya Allah ta amsa cikin son yarinyar.
Daga nan sai sukayi sallama murmushi Jannart tayi
tare da zare wayar akunnenta.
D’an Jim tayi nay’an wasu mintuna, kana atsanake kuma ta cigaba da aikin da takeyi.
Bayan ta kammala wanke wanken ne kuma, ta dawo falo tare da kunna tv.
K’aramar wayar dake rike a hannun nata ta kunna, tare da yin dialing numbern Mamy.
Cikin sa’a bugu biyu kuwa Mamyn ta d’aga.
“Assalamu Alaikum Mamy barka da yamma ci.”
Jannart din ta fada cikin girmamawa.
Mamy kuwa jin muryar Jannart dinne, yasa ta fadada fara’arta, tare da amsa mata sallaman, cike kuma dajin dadin kiranta da Jannart din tayi tace.
“Yauwa Jannart barkadai, ya kuke ya mai jiki ya kuma fama da sanyi?”
Murmushi mai sauti Jannart din tayi, kana anutse tace.
“Alhamdulillah Mamy, jikin kam yayi sauki sosai, saidai amma fa muna shan sanyi, Allah Mamy duk nayi kewarku sosai.”
“Muma haka Jannart munyi kewarki sosai, ko d’azu ma saida Ramadan yayi korafin wai ya gaji, zai biyoku Mascown zaizo kiyi mishi miyan kase, nace masa Lallai kuwa bazai tab’a cin miyan kase ba ashe, indai acikin Mascow ne.”
Dariya sosai Jannart din tayi, tare da gyara zamanta, cike da kewarsu tace.
“Allah sarki Ramadan Idan muka dawo Insha Allah, zanyi mishi miyan kase, Mamy Ina Abba da Baba Maud’o.”
“Sunanan lafiya Jannart, shekaran jiya ma Baba Maud’o ke tambayanki, saboda yace Rayyern kam suna waya dashi sosai.”
“Allah sarki Baba Maud’o tunda muka tafi bamuyi magana ba, amma Insha Allah yau zan kira Ramadan sai ya had’amu mu gaisa.”
“Aikuwa da kin kyauta saboda yana ta tambayanki.”
Mamyn ta fad’a cikin kulawa.
Hira suka Dan tab’a da Mamyn kafun daga bisani sukayi sallama.
Mamyn na kashe wayar kuwa, Jannart tayi dialing numbern, Ramadan saidai jin wayar tasa bata shiga ne, yasa ta ajiye nata wayan tare da kwanciya akan kujera, kana ahankali ta maida idanunta ga tv.
Tananan cikin falon azaune kuwa, har saida aka soma kiraye kirayen sallan magriba, kafun ta tashi ta wuce daki.
Koda ta shiga dakin kayan dake jikinta ta cire, tare da wucewa toilet kaitsaye tayi wanka.
Koda ta fito daga wankan, mai da powder kawai ta shafa akan fuskarta, sai kuma oily lips stick.
Bayan ta gama shafan ne kuma, atsanake ta nufi wajen trolley dinta, bud’e trolleyn tayi tare da ciro wani riga da sket.
Mai kalan baki, Koda ta sanya kayan cib cib sukayi mata ajiki, Yayinda lafaffen cikinta ya bayyana.
Bayan ta saka d’aya daga cikin hijab dinta ne kuma, ta tada sallah, saboda zuwa lokacin tasan anshiga sallan magriba.
Koda ta idar da sallan kuwa bata tashi akan sallayan ba, har saida ta idar da sallan Isha.
Ahankali ta murd’a handle din kofar dakinta ta fito, zuwa falon.
Zama tayi akan kujera tare da lumshe Idanunta, cikin sanyi take sauraran karan tv’n dake tashi acikin falon.
Dai-dai lokacin Ya bud’o kofar falon ya shigo, hannunsa rike da ledodin Halal Restaurant.
Jin alamun shigowarsa ne kuma, yasa Jannart din bud’e Idanunta, Ahankali ta sauke ganinta akansa.
Kasancewar kuma shi dinma kallonta yakeyi ne, yasa idanunsu sarkewa acikin na juna.
D’anyin kasa da kanta tayi, Ahankali kuma ta mik’e tsaye, cikin sanyi,
ta nufi inda yake.
Ganin hakanne kuma yasa kashi zuba mata narkakkun idanunsa.
Jannart kuwa ahankali ta k’araso inda Rayyern din ke tsaye, cikin kuma yanayinta na sanyi, ta mika hannu ta karb’i ledan dake hannunsa.
Batare kuma da ta dago Kai ta kallesa ba, cikin sanyin murya tace.
“Sannu da dawowa.”
Kansa ya d’an jinjina mata ahankali, Cikin yanayin kasalan da ganinta ya haifar masa kuma, ya karasa shigowa cikin falon.
Ganin hakan kuwa shiya saka Jannart din rufa masa baya.
Akan daya daga cikin kujerun falon ya zauna, tare da lumshe gajiyayyun idanunsa, kana akasalance kuma yake shak’an daddad’an k’amshin turaren dake tashi acikin falon.
Jannart kuwa atsanake ta ajiye ledan daya kawo din akan table, Kaitsaye kuma ta wuce kitchine.
Ta k’asan idanunsa yabi bayanta da kallo, Yayinda acikin zuciyarsa yakejin wani irin abu nayi masa yawo, ga kuma kasalan daya saukar masa lokaci guda hannunsa yasa ya dafe kanshi yana mai sauke numfashi.
Jannart kuwa Koda ta shiga kitchine din, plate, cup and spoon ta d’auko, sai kuma fridge da ta bud’e ta d’auko drinks.
Atsanake ta nufo cikin falon, saidai kuma bata yarda ta saka Idanunta acikin nasa ba.
K’arasowa gabansa tayi, tare da jawo table ta ajiye plate da kuma cup din awajen.
Ledodin restaurant din daya kawo ta bud’e, tare da zuba masa abincin acikin plate din.
D’agowa tayi ahankali ta kalleshi, musamman kyakkyawar fuskarsa da ta sakeyin haske, ga kuma yalwataccen sajensa da yake kwance lub lub.
Zara zaran eye lashes d’insa da suke alumshe ta kalla, ahankali kuma cikin tausasa murya tace.
“Naan ga abincin .”
Kansa ya d’an jinjina mata, hade kuma da bud’e idanunsa, Cikin nutsuwa ya jawo plate din abincin gabansa ya soma ci.
Ganin hakanne kuma yasa ta zama ad’an nesa dashi, tare da sadda kanta k’asa, Ahankali take wasa da y’an yatsun hannunta, wanda ayanzu yin hakan ya zame mata jiki, saidai kuma azahirin gaskiya gaba, daya tunaninta ya tafi ne, izuwa wani waje na daban, saboda hakanan takejin maganganun Aunty Fauziya nayi mata yawo a kwakwalwarta.
Rayyern dake cin abinci kuwa, duk wani yanayinta yana lure dashi, time to time kuma yake yawan kallonta, saboda ba kad’anba bak’in kayan da ta sanya yayi mata kyau.
Suna nan ahaka dai harya kammala cin abincin.
Ahankali ta d’ago Idanunta ta kalleshi, ganin yana goge bakinsa da tissue ne kuma, yasa ta fahimtar cewa ya koshi.
Kasancewar kuma ita ba wani yunwa takeji sosai ba, shiyasa ta soma tartare wajen.
Ganin Rayyern din na kokarin mikewa tsaye ne kuma, yasa cikin sauri ta d’ago da Idanunta ta kalleshi.
“Naan.”
Takira sunansa asanyaye cikin kuma Dan yanayin shagwab’ar, da ta sashi tsayawa da abunda yakeyi.
Atsanake ya juyo ya kalleta, Ganin ta sunkuyar da kanta kasa ne, kuma ya sashi komawa ya zauna akan kujera.
Again idanu ya zuba mata, tare da soma karantar yanayinta.
Jannart kuwa hakanan taji ta kasa fad’an abunda takeson fadad’in, saima zuciyarta da taji tana bugawa da k’arfi.
“Kinyi shiru tell me what happened?”
Ya fad’a cikin wata irin murya mai sanyi, da kuma tausasawa wanda hakan ne ya bata wani confidence.
D’ago da kanta tayi ta kalleshi araunace, cikin cool da kuma son fahimtar dashi tace.
“Please Naan ka kawo mana abubuwan buk’ata saboda inason na fara girki.”
Ta kare maganan tana me tsaresa da idanu, tare da fargaba akan zai amince ko a’a...! By *GARKUWAR FULANI*Idanu shima Rayyern din ya zuba mata, Ahankali kuma ya d’an nisa tare da gyara zamansa, atsanake yace.
“You’ll cooking why? Ko bakyason abincin restaurant din da nake kawo miki ne?”
Yayi tambayar Cikin kulawa, still kuma yana me kallonta.
Itakuwa Jannart Ganin irin Kallon da yakeyi mata ne, yasa tayi k’asa da kanta, asanyaye tace.
“A'a kawai dai inason na fara girki ne.”
“Okay shima girkin yana cikin aikin da yasa Abba ce mu taho tarene?.”
Kai ta ɗan ɗago ta kalleshi ganin yadda ya tsareta da idone yasata yin ƙasa da kai.
“Abba yace mu taho tarene dan ki kula sani, so in Kuma na liƙa miki aikin girgi ai baki da lokacin kula dani, in dai da gaske kike kula da nidin zakiyi”.
Yayi mgnar cikin kauda kai dan shi kanshi mmkin kansa yake a kwanakin nan.
Ita kuwa Jannart a hankali tace.
“Toh ai shima kula da kaine”.
Da sauri yace.
“Toh shi na yafe ki bari sai mun koma gida, a nan dai cewa akayi ki kuladani da gadina ko”.
Ya ida mgnar murmushi ya tsubce mishi.
Ita kuwa shiru, tai
“Kin ganeko?”.
Ya fada atakaice tare kuma da tashi, kaitsaye ya nufi bedroom d’insa, saboda dama bai shigo cikin gidan ba, saida yayi sallan Isha.
Da idanu ta bishi har saida taga shigewarsa, cikin dakin kafun ta tashi tare dakai plate and takeaways din kitchine, itakam yoghurt kawai tasha, tare da wuce wa dakinta ta soma buga game.
Yana shiga bedroom nasa,
ya rage kayan jikinsa kana nufi saman gadonsa ya kwanta.
Idanunsa ya dan lumshe saboda wani irin daddad’an kamshi, daya bugi hancinsa, wanda yake tashi ajikin bedsheet din.
Sake gyara kwanciyarsa yayi, tare da jawo laptop d’insa ya soma duba, sakonnin da suka shigo email dinsa.
Yana kwance ahaka kuwa bacci ya daukesa.
Yayinda a b’angaren Jannart ma hakanne ya kasance, domin tana tsaka da latsa waya, bacci mai nauyi ya dauketa.
Batare dako kofar d’akinta ta rufe ba.
Washegari.
Kamar yanda suka saba haka yau dinma, da sassafe kafun gari ya gama yin haske yayi musu ordern abincin.
Koda ya gama shiryawa kuma, abincin ya d’anci kadan, batare kuma daya jira fitowar Jannart d’in ba, ya wuce Azimut hotel Olympic Mascow inda zasuyi meeting.
Yayinda Jannart kuwa sai bayan ya tafin ta iya fitowa taci nata abincin.
*After 3days*
Ahaka suka ci gaba da rayuwa, Yayinda take iya kokarin ta wajen kulawa dashi, domin aduk sanda ya dawo takan fito ta bashi abinci yaci, sannan kuma akan Idanunta yake shan magungunan sa kana ta gyara masa ɗaki, a hankali wata iriyar sassayar shaƙuwa ta ɗan fara ratsa zuƙatansu.
Tun daga wancan ranan da sukayi maganan kayan abinci kuwa, bai sake dago mata maganar ba, har zuwa yau din kuma bai kawo kayan provision dinba.
Itama kuma ganin yayi shiru shiyasa bata sake ce masa komai agame da hakan ba, duk abunda ya kamata kuwa tana yi mishi.
Domin kullum bayan ya fita takan shiga ta gyara masa d’akinsa, tare da wanke masa toilet.
Saidai kuma dare nayi kowannensu yake kama gabansa.
Bata shiga d’akin nasa da dare ne kuma, gudun kada ya sake koranta kamar yanda yayi mata a wancan ranan duk da tana ganin sauye-sauye sa yawa daga garesa.
Ranar yau ta kasance Tuesday, kuma yaune zasu fara gwaji akan heart surgery, wannan dalilin yasa gaba d’aya, Doctors din a ankare suke.
Kowa ya shirya tsab tare da fatan samun nasara.
Kamar yanda ya saba kuma ordern abinci yayi musu, bayan ankawo yaci nasa ne kuma, ya d’auki briefcase d’insa ya wuce Hospital.
Koda ya karasa Hospital din already ya samu duka Doctors din, kasancewar shi kawai dama ake jira, shiyasa yana zuwa suka shiga theater room dan fara aikin.
Acan gida kuwa Jannart kwata kwata, ko fitowa yau din batayi ba, bacci tasha ta koshi, Koda ta tashi daga baccin kuwa game ta d’anyi awayanta, kana daga bisani bacci b’arawo ya sake d’aukarta.
Atak’aice dai haka ta k’are wunin ranan, batare da ta fito taci abincin da Rayyern din ya ajiye mata ba.
Asashin su Rayyern kuwa komai ya tafi musu yanda suke so, domin kuwa har sunyi surgery din, kuma komai yayi kyau, inda kowannensu ya fito da kyakkyawan result.
Bayan sun kammala duk wani abun da zasuyi ne kuma, kaitsaye ya nufo hanyar dawowa gida, saboda yau din duk agajiye yake jin kansa.
Kafun ya karaso gidanne kuma ya tsaya, a wani restaurant ya saya musu abinci.
Koda ya karaso gidan bayan ya gama dai-dai-ta parking din motarsa, anutse yake tafiya har ya k’araso cikin falon, yana shigowa kuwa ya soma kokarin zare, suit din dake jikinsa, yana acikin hakanne kuma idanunsa suka sauka akan takeaway din daya ajiye mata tun safe, Wanda kwata kwata babu alaman an tab’ashi.
Idanunsa ya d’an kankance cike kuma da mamaki yake Kallon takeaway din.
Ahaka har ya karasa shigowa cikin falon.
Saboda ya tabbatar da abunda yake zargi ne kuma, ya sashi bud’e takeaway din, Aikuwa abincin yana nan babu alaman ko cokali daya anyi.
Ajiyar zuciya ya d’an sauk’e tare kuma da juyawa, ya kalli kofar dakinta dake kulle.
Ahankali kuma ya janye idanunsa daga Kallon dakin, ledan dake hannunsa ya ajiye, Kaitsaye kuma ya wuce bedroom d’insa.
Yana shiga ya soma rage kayan jikinsa, tare da wucewa toilet yayi wanka hadi da dauro alwala, kasancewar ankusa kiran sallan magriba.
Yana fitowa awankan kuwa mai kawai ya shafa, sai turare wanda shafasa ya zame masa d’abi’a.
Anutse ya zura wata army green jallabiya ajikinsa, wayarsa da kuma key din motarsa ya dauka, kaitsaye kuma ya fice daga falon, bayan ya saka wasu slippers a kafafunsa.
Koda ya fito falon zama yayi Ganin akwai dan sauran lokaci ne kuma, yasa shi zama ya d’anci abincin kad’an.
Bayan ya kammala ne kuma ya shiga, kitchine ya kuskure bakinsa, batare da wani jinkiri ba kuma, ya juya kaitsaye ya fice daga cikin falon.
Cikin sa’a kuwa yana zuwa masallacin ana shiga sallan, hakan yasa da hanzari ya shiga jam’i.
Bayan sun idar da sallan kamar yanda ya saba, zama yayi a masallacin har saida suka sallame sallan Isha, Kafun ya kama hanyar dawowa gida.
Again Yana shigowa falon takeaway din abincin daya ajiye ya kalla, saidai ganin bataci abincin ba kamar yanda ya ajiye haka yazo ya samu, ya sashi d’ago kansa fuskarsa d’auke da yanayin mamaki yake Kallon kofar dakinta.
Inda yake jiyo sautin muryarta na tashi, wanda da’alama kuma waya takeyi.
Ahankali ya dan matsa kusa da kofar nata, dai-dai lokacin kuwa yaji sautin muryarta na fadin.
“Okay My Aunty Insha Allah zan kiyaye, eh zan bashi number Hajia Rabi'ah wata ƙil zai yarda ya amso min su.”
Ajiyar zuciya ya dan sauke, saboda Jin muryar nata ya tabbatar masa da cewar tana lafiya.
Kasancewar babu abunda zaiyi acikin falonne kuma, yasa shi juyawa ya wuce bedroom d’insa.
Yana shiga kuwa ya zare jallabiyan dake jikinsa, tare da komawa ya kwanta akan gadonsa, had’e da lullub’awa jikinsa blanket, kana ya jawo system d’insa ya soma latsawa.
Yana nan ahaka har bacci ya daukesa.
Jannart kuwa har dare ya raba bata fito taci abincin ba, tun tana buga game awayarta kuwa, har bacci b’arawo ya dauketa.
Washegari.
Yau dinma tun kafun ya fita yayi musu order.
Kamar yanda ta saba ay’an kwanakin kuma, ita da kanta ta zuba masa abincin a plate yaci.
Saidai ita bai ga alaman zata ci ba, Dan komawa can gefe tayi ta zauna.
Ahaka harya kammala cin abincinsa ya tafi.
Ita kuwa Jannart Ganin ya tafi ne, yasa ta tattare wajen daya ci abincin.
Batare kuma da ita taci ba ta koma d’aki tayi kwanciyarta dan fruits take dan ci in taji yunwa kasancewar akwaisu a Fridge.
*some hours ago*
Ahankali ya daura hannayensa akan waist d’insa, tare kuma da fesar da wani irin numfashi.
Abincin safe da kuma na daren daya ajiye mata, wanda duk bata ci ba ya kuma kallo, Cikin yanayin tsananin mamakin kwana biyu da ta dauka, bata saka abinci acikinta ba, ya dago ya kalli kofar dakinta.
Yayinda acikin ransa yake tambayar kansa, abunda zai hanata cin abinci har na tsawon 2days.
Wani tunani da yazo cikin ransa ne kuma, yasa shi juyawa ya nufi bedroom d’insa.
Jannart dake dakinta kuwa, tana sane bawai kuma tana kin cin, abincin bane saboda wani abu na daban, kawai dai tana yin hakanne saboda tana son, ya tuna da maganan kayan provision dinsu, ba ya ga haka kuma, ta gaji da cin kalan abubuwan da yake kawo mata din, shiyasa yanzun kawai take shan fruit.
Rayyern kuwa Koda ya shiga dakinsa, kwanciya yayi tare da lumshe idanunsa.
Ahankali yake sauke ajiyar zuciya, Yayinda acikin ransa yakejin, rashin Jin dadin cin abincin da Jannart din batayi ba.
Wani abu daya sake tunawa ne kuma, yasa shi tab’e bakinsa tare da d’age kafad’unsa, cikin halin ko in kula yace.
“Wannan damuwarta ne, bataji yunwa bane.”
Daga can wani b’angare na zuciyarsa kuwa, sai yaji kaman abunda ya fada din ba dai-dai bane, domin har abada bazai tab’a manta irin yanda tayi kuka sosai akansa ba, ta tsaya dashi alokacin da yake halin buk’atar taimako, ta kula dashi sosai more especially akan lafiyarsa ya lura tunda yayi ciwo take bashi kula ta musamman mai cike da tausayawa ta kula dashi fiye da yadda Abbanshi, da Mamy da Ramadan kan kula dashi in ciwonsa ya tashi.
Yanaji ajikinsa bai kyautu yayi mata haka ba, kodan abubuwan da tayi masa.
Ahankali ya fesar da wani irin numfashi, tare da mikewa atsanake ya karasa gaban drawern sa.
Wani riga da wando ya ciro, tare da saka kayan ajikinsa, kaitsaye ya nufi hanyar fita daga dakin.
*Nigeria.*
Alhaji Idi Sale Dakata ne ke zaune, acikin tamfatsetsen falonsa, Yayinda Abba Kabir ke zaune acan gefensa.
Zugum haka suka zauna kowannensu da irin abunda, yake sak’awa acikin zuciyarsa.
Dai-dai lokacin kuma Momy ta shigo, ta iskesu acikin irin yanayin, Dan jim tayi tana me nazartarsu, domin da dukkan alamu ta fahimci cewar, wani magana suka tattauna atsakaninsu, wanda hakan yasa duk sukayi jigum.
Ganin mood din nasu ne kuma, yasa Momyn juyawa ta koma, batare da ta ce kala ba, saboda ma ta lura kwata kwata su Abba Kabir din basu ganta ba.
Acan Mascow kuwa Jannart ne ke kwance, Yayinda wayanta ke sakale akan kunnenta, tana waya da Riyyam nsra, wanda ya hadata da Mammy da kuma Zaytoon suka gaisa.
Rayyern kuwa Koda ya fito daga cikin dakin nasa, sosai yayi kyau cikin shigar dake jikinsa.
Inda ya daura babban jacket akan shigar tasa, saboda wani irin matsanancin sanyi da akeyi.
Dan jim yayi tare da Kallon ƙofar nata, acikin zuciyarsa yake tunanin me zai fada mata, sanin bashi da wani abun cewa ne kuma, yasa shi nufar dakin nata kai tsaye.
Ahankali ya tura kofar dakin ya shiga, bakinsa dauke da sallama.
Jin alamun bud’e kofar dakinne kuma, yasa Jannart dake zaune saurin juyowa suka had’a idanu dashi.
Wayar dake kunnenta ta zare, tare da tashi ta zauna tana me fuskantar shi.
Cikin kuma Dan yanayin mamakin ganinsa acikin dakin tace.
“Naan.”
Idanunsa ya zuba mata, saboda ganin yanda duk saman breast dinta ya bayyana, kasancewar wuyan rigar dake jikinta ya zame batare da tasan hakan ba.
Ahankali ya karasa shigowa cikin dakin, tare da