Showing 30001 words to 33000 words out of 104589 words

Chapter 11 - Tubali Book 2 Hausa Novel Complete

Unknown   

21 Dec 2024

159

bashi amsa, tare kuma da d’auke Idanunta daga kallonsa.

Idanunsa dake alumshe ya d’an bud’e, tare da k’ara d’aura hannunsa akan cikinsa.
Wanda yayi Dan ƙugin yunwa, har saida Jannart din ta jiyo sautin.

D’an kallonsa tayi, gaba daya duk ya marairaice, ya wani zama abun tausayi, da dukkan alama Yunwa ce ke wahalar dashi.

“Meye kike wani kallona haka kamar zaki cinyeni, ni yunwa nakeji.”
Rayyern din ya fad’a yana me sauke mayun idanunsa akanta.

Wanda kuma hakanne yasa tayi saurin dauke Idanunta daga kallonsa.

Batare kuma da tace masa komai ba ta juya, Cikin nutsuwa ta wuce kitchine.

Da idanu yabi bayanta, har saida yaga wucewarta cikin kitchine din kafun ya tashi ya dawo cikin falon.

Jannart kuwa tray da plates ta d’auko, tare da dawowa falon.

Ahankali ta sunkuya dai-dai zata ajiye tray din agabansa ne kuma, mayafin dake jikinta ya zame ya fad’i.

Saurin ajiye tray din tayi tare da juyawa da sauri dan daukar gyalen nata.

Juyawan da zatayi dinne kuma yasa, Rayyern din sauke Idanunsa akanta.

Ganin inda idanun nasa suka sauk’ane kuma, ya sashi saurin rumtse su, tare kuma da kawar da kansa gefe sabida gani yayi tamkar nimples ɗin ta zasu tsole mishi ido, kasan cewar batasa bra ba yasa breast ɗinta ke tsaye kam nimples ɗin sunyi tsaye cur motsin da take yasa duk ƙirjinta rausayawa kara rumtse idanunshi yayi sabida ganin abin da yakeyi duk da ya rufe idon.

Itakuwa Jannart cikin sauri ta d’auki mayafin nata ta yafa.
Saboda kunyan da taji ya lullub’eta ne kuma yasa ta kasa d’ago kanta ta kalleshi.

Ahankali ta bud’e food flasks din, roasted fish din ta zuba masa, sai kuma miyar kasen shima da ta zuba masa shi, awani plate na daban dasa mishi tuwo kwaya ɗaya.

“Gashi.”
Ta fad’a cikin wata irin sassanyar murya, still batare kuma da ta d’ago ta kalleshi ba.

Akasalance ya d’ago kansa, tare da mik’a hannayensa alaman ta basa plate din.

Sai Alokacinne kuma ta d’ago Kai ta kalleshi, kasancewar kuma tana d’an nesa dashi ne, yasa dole saida ta matsa gab dashi.

Ahankali ta d’an ajiye guiwowinta akan tattausan carpet din dake malale atsakiyar falon.

Hannayenta duka biyu ta sanya wajen Ganin ta mik’a masa plate din.

Ak’ok’arinta nayin hakanne kuma, batare da duk sun Ankara ba, Rayyern din yasanya hannunsa ta k’asa zai karb’i plate din, hakanne kuwa yasa shi sauk’e tafukan hannayensa, akan lallausan fatar hannayenta, masu tsananin taushi tamkar auduga.

Wani irin abu Jannart taji acikin jikinta, wanda har hakan yasa tsikar jikinta mimmik’ewa, lokaci daya kuma gyalen ta ya zame zuwa kan kafad’unta, hakan yasa lallausar sumar kanta ya bayyana.

Idanunsa ya d’an zubawa gashin kan nata, Yayinda ita kuwa ahankali ta zame hannunta daga cikin nasa tare da sanya hannu ta jawo gyalen zuwa kanta.

Dai-dai lokacin ne kuma Mamy ta fito daga d’akinta.

Ganin Rayyern da Jannart din atare ne kuma, ya sakata sakin murmushi Cikin kulawa tace.


“Babana lafiya kuwa Ina sallah naji kana ta rabka min kira.”

D’agowa yayi ya d’an kalli Mamyn, cikin yanayin sigar shagwab’a yace.

“Mamy To ba yunwa nakeji ba.”

Murmushi Mamyn tayi, tare kuma da neman waje ta zauna.
Cikin sakin fuska tace.

“To Rayyern Idan kanajin yunwa, baga matarka ba, komai ita zaka tambaya ba niba, kuma ga abincin ma, Ina naga ankawo ma, Jannart sannu da aiki.”

Mamyn ta fad’a tana Kallon Jannart, da ta janye jikinta daga kusa da Rayyern din.

D’an murmushi tayi, batare kuma da tace komai ba, ta dawo kusa da Mamyn nan k’asan sofa ta zauna.

Shikuwa Rayyern d’an k’aramin bakinsa ya taɓe, kana ashagwab’e cikin kuma yanayinsa na marar lafiya, ya soma cin abincin da Jannart din ta kawo masa.

Tun aloman farko da yayi kuwa, ya lumshe idanunsa, saboda dadi da kuma gardin kifin daya ratsa shi, bugu da kari ga kuma ruwan lemon tsamin da taste d’insa, ya hadu dana kifin sai ya bada wani dandano na daban.

Ci gaba dacin abincin nasa yayi, duk da cewar bata wani sa masa da yawa ba, saboda sanin halinsa da tayi na rashin son cin abinci.

Mamy da Jannart kuwa hira suke d’an tab’awa kad’an kad’an.

Wanda hakan yasa sam basu ma lura da cewar Rayyern din ya cinye abincin ba.


“Bank’oshi ba fa.”

Maganar Rayyern din ya katse su daga hirar da sukeyi.

D’agowa Jannart tayi, karab kuwa idanunsu suka sark’e acikin na juna.

Saurin janye Idanunta daga kallonsa tayi, tare kuma da mikewa ahankali, ta k’arasa inda yake zaune.

Mamy kuwa Murmushin jin dadi tayi, tare kuma dajin wani sanyi aranta, saboda dama burinsu ne Ganin Rayyern din yaci abinci ya kuma fara sakewa da matarsa.

Jannart kuwa durk’usawa tayi agabansa, tare da daukan plate din, ta soma kokarin kara masa gasashshen kifin.

“Idan ba rowa bama tayaya za’a bawa mutum abunda ansan bazai ishesa ba.”

Rayyern din ya fad’a k’asa k’asa ta yanda, yasan Jannart dince kawai zata iya jiyosa.

Aikuwa karab maganganun nasa, suka sauk’a acikin kunnuwanta kasan cewar tana kusa dashi ainun kuma hankalinta na kanshi.

Hakan yasa Ahankali ta d’ago Idanunta ta kalleshi.

“Malama meye?”

Ya tambaya yana me tsareta da idanu da tsuke fuska.

Fararen hakwaranta ta sanya, Ahankali ta ciji labb’anta, Cikin yanayin sanyi da kuma, yanayinta mai kama da shagwab’a, ta d’an maida bakinta gefe, alaman murgud’a baki.

Idanunsa ya d’an zaro, saboda ganin abunda tayi masa din, duk da cewar kuwa hakan da tayi din, ba k’aramin k’ara mata kyau yayi ba, musamman saboda yanda lips dinnata suka sha, oil lipgloss.

“Me bakin rashin kunya.”

Yayi maganan k’asa k’asa, tare da motsa k’afarsa Ahankali, wanda kuma niyarsa shine ya take mata yan yatsun k’afarta.

Dai-dai nan kuma Abba da Baba Maud’o suka shigo cikin falon.

Hakanne kuwa yasa shi maida k’afartasa.

Jannart kuwa plate din ta tura masa gabansa, tare da komawa baya ta zauna.

“Sannu da shigowa Abba, Baba Maud’o sannu.”

Jannart din ta fad’a cikin girmamawa.

Murmushi dukansu sukayi, kana cikin jin dadin girmamasu da Jannart din keyi, Baba Maud’o yace.

“Yauwa Jannart sannu, ya gidan?”

“Alhamdulillah.”
Ta amsa tana me dukar da kanta k’asa.

Abba ma fuska asake, yana me zama akusa da Rayyern din kuma yace.

“Yauwa Jannart, sannunki .”

Baba Maud’o ne ya kalli Rayyern din cikin kulawa yace.

“Maud’ona ya jikin naka.”

Murmushi Rayyern din ya d’anyi, kana cikin sakin fuska da nuna Jin dadin kulawar Baba Maud’on yace.

“Alhamdulillah Baba Maud’o yanzu kam jikin da sauki.”

“Masha Allah Allah ya kara sauki, dama nace bari nazo na duba ka.”

Baba Maud’on ya fad’a yana me mik’ewa tsaye.

“Ameen Nagode Baba Maud’o.”
Rayyern din ya amsa.

Shikuwa Baba Maud’o juyawa yayi ya fice daga cikin falon.

Hakanne kuma yasa Abba ma tashi yabi bayan Baba Maud’on.

Dai-dai lokacin kuma Riyyam nsra ya fito falon, hannunsa rike da wayarsa.

Anan kusa da Rayyern ya zauna, Ganin kuma irin delicious din da Rayyern din keci ne, yasa shi dan tand’e baki.

Cikin dan yanayin zak’uwa yace.

“Gaskiya Hamma Rayyern kana cin dadi, tun Ina sama nake jiyo kamshin abincin kan nan gsky My Aunty kina mana ƴan ubanci.”

Hararan wasa Rayyern din ya d’an watsa masa, shikuwa Riyyam din wayarsa ya ciro, tare da dannawa numbern Ramadan kira.

Mamy da Jannart kuwa murmushi sukayi.

Bugu biyu kuwa Ramadan din ya dauka.

Cikin zak’uwa Riyyam din yace.

“Albishirinka Hamma Ramadan, yau kada Kaci komai awaje, ka dawo gida Aunty Jannart irin miyar ranan tayi.”

Daga can b’angaren Ramadan yace.

“Ai ganinan ma Ina dawowa, kace Aunty Jannart ta ajiyemin nawa.”

“To.”
Riyyam nsra din yace, daga haka ya katse kiran.

Rayyern kuwa d’ago kansa yayi ahankali, tare da Kallon Mamynsa cikin sanyi yace.

“Mamy d’azu munyi waya da Mammyn Riyyam tace tana gaidaki.”

Murmushi ne ya bayyana akan fuskar Mamy, cikin jin dadi tace.

“Masha Allah Ina amsawa.”

Juyo da kallonta ta kumayi inda ta sauke idanunta akan Riyyam nsra.
Cikin nuna kulawa tace.

“Ni kam Riyyam baka tab’a had’ani da Mammynka ba ko awaya, bani hotonta na gani mana Idan kana dashi.”

Murmushi Riyyam nsra din yayi, cikin tausasawa da jin daɗin satan amsar da Mamy ta bashi mgnar ta yace.

“Ayyah Mamy yi hakuri, amma babu hoton Mammy awayana sabida randa zanzo na sai sabuwar waya kuma na bar waccar a gida.”

Ya kare maganar yana dan karyar da wuyansa gefe.

“To had’ani da ita mana muyi video call.”

Mamyn ta fad’a tana me kallonsa.

Wani irin bugawa yaji kirjinsa nayi, wanda hakan yasa shi sadda kansa k’asa.

“Tayaya zai had’a Mamy da Mammynsa video call?”

Yayiwa kansa tambayar.

Mamy kuwa Ganin yayi shiru ne yasa ta cewa.

“Lafiya kuwa Riyyam inayi maka magana kayi shiru, had’ani da ita muyi magana.”

Kansa ya d’an langwab’ar gefe, cikin kuma yarda da k’aryar da zuciyarsa ta tsara masa yace.

“Ayya Mamy d’azu muna waya dasu, naga kiran ya katse, ashe wai Zaytoon ce ta raɗa mata wayar a ƙasa, dana sake kira kuma baya shiga, saida ga baya Mammy kecemin wai, cameran wayan nasu ya samu matsala, saidai ko voice call.”

D’an Jim Mamyn tayi, kamar me nazartar wani abu kuma saitace.

“To Wayar Zaytoon fa?”

“Ai Zaytoon bata da waya, Mamy ta hana ta rik’e waya, tace wai bayanzu ba.”

Ya k’are maganan yana me waskewa, gudun kada kowannensu ya fahimci cewar bashi da gaskiya.

Kai Mamyn ta jinjina, kana cikin gamsuwa da bayanan nasa tace.

“Ai hakan da Mammyn naka tayi shine daidai, barin waya ahannun y’a Mace budurwa adai-dai wannan lokacin hatsari ne, kodan wannan babbar masifa ta Tiktok dinma, saidai Wacce Allah Ya kare kawai.”

Murmushi Riyyam din yayi, cike dajin dadin yanda karyar tasa ta samu karb’uwa kuma ya samu sun kauda mgnar ma.

Rayyern kuwa mik’ewa yayi, saboda dama ya kammala cin Abincin.
Anutse ya nufi sama, saboda surutun nasu na damunsa.
Har ya fara haurawa yace.
“Uhum Mamy ai su kansu yara masa basu waya da barinsu yin shuhura a social media babbar masiface, yanzu kigafa yadda Riyyam-nsra yake kamar mazari, wanda a baɗini kuma Allah ne kaɗai yasan me yake shukawa”.
Ya ida mgnar ya juyowa ya tsurawa Riyyam-nsra ido.
Wanda shi kuwa yayi wani irin firgita dan sai yake ga Hmma nasu ya gane komai da yakeyi ne.

Mamy kuwa cikin yarda da yaron tace.
“A babu ma abinda yakeyi”.
Uhum kawai yace yaci gaba da tafiyarsa.

Tashinsa awajenne kuma yasa ita kuwa Jannart sakewa, bayan ta gyara wajen da yaci abincin ne kuma ta dawo, suka zauna ita da Riyyam hira suka sha sosai, suna nan zaune dai har Ramadan ya dawo.

Bayan sunyi sallan magriba ne kuma, Jannar din ta zuba musu sauran ragowar abincin Rayyern din sukaci.

After 3day.

Alhamdulillah acikin kwanaki ukun nan, jikin Rayyern ya k’ara sauki sosai, domin babu laifi yanzu ya samu karfin jikinsa.
Domin yana iya fitowa har can compound din gidan, wajensu Baba Maud’o, sannan har motsa jikinsa yana iyayi yanzun.

Ab’angaren Jannart kuwa tun ranan bata sake sakashi a Idanunta ba.
Sosai kuma takejin dadin zaman gidan, musamman ayanzu da duk sanda Ramadan ya dawo, sukan zauna suyi hira sosai, harma game sukeyi.

Ga kuma wayarta dake d’ebe mata kewa, kasancewar ta bud’e Twitter, Instagram, da kuma Tiktok, da wani suna na daban, bawai original account dinta da kowa ya sani ba, sunan da ta bud’e dashi kuwa, ba wai normal sunane da kowa zai gane ba.
Akomai nata da Unique kawai take using.


Acan b’angaren gidan su kuwa.

Har dai zuwa yanzu babu wani mai gamsashshiyar nutsuwa acikinsu, more especially Alhaji Idi Sale dakata.
Momy da kuma Abdull, wanda abun ya had’e musu biyu, rashin lafiyar Dadyn da kuma b’acewar Jannart.


Yanzu ma zaune su Alhaji Idi Sale Dakata, Alhaji Abdu Tababa, Dr. Lukaman, da kuma Barrister Kabir, Alhaji Bala Tamnari suke acikin katafaren dakin ganawa'n Alhaji Idi Saleh Dakata.

D’ago da kansa yayi ya kalli Alhaji Bala Tambarin, cikin dan yanayin damuwa yace.

“Wato Alhaji Bala, har yau ina mamaki kan al’amarin daya shafi yaron nan Rayyern, musamman akan company’s d’insa, akullum hab’aka abubuwan nasa sukeyi, na kuma rasa gano tushe da madafan arzikinsa, saboda ayanzu haka nasa ayimin bincike akan sabon companynsa, ankuma tabbatarmin da cewa, zuwa yanzu ankawo komai da komai na amfani acikin companyn, kama daga kan engines dama dai sauran abubuwa, saboda har anfara sarrafa kayayyakin abinci, amma naji ance bazasu fara fitar da kayayyakin nasu ba, sai farkon shekara mai kamawa ina mamakin dukiyar yaron dan a iya wannan Company nasa zaikai biliyoyin kuɗi da sunfi shekarunsa yaushe aka haifesa har ya yarasu.”

Kai Alhaji Bala Tambari’n ya jinjina, cikin gamsuwa kuma yace.

“K’warai kuwa nima nasan da haka Alhaji Idi Saleh Dakata.”

Gyara zama Alhaji Abdu Tababa yayi, kana cikin takaici yace.

“Wannan abu ni Ina mamakinsa, amma Meyasa ba zaka dakatar dasu ba Alhaji Bala? Naga Kaike kula da duk wasu harkan filayen da ake gine gine masana'antu, ni har yauma ina mamakin tun farko ma meyasa ka basu takardar izinin fara ginin companyn?”

Murmushi Alhaji Bala Tambarin yayi, saboda shi yasan meya sani, kamar yanda suka kasa gane waye, Dr. Rayyern Bashir Muhammad Mai-nasara din, to shima hakane.

Dr. Lukman ne ya cab’i zancen da cewa.

“Gaskiya dai kam, amma ni yanzu sauki na daya, abubuwanshi na harkar asibiti gaba daya sun dakata, yafi maida hankalinsa, akan abubuwan da suka shafi companyn.”

Barrister Kabir dake zaune agefe ne ya saki wani murmushin jin daɗi.

Tare da gyara zamansa, Cikin nutsuwa yace.

“Anaka tunanin kenan Dr. Lukman, domin da alama baka da labarin cewa, acikin kwanan nan akwai likitotinsa da ya ware kusan guda biyar dashi na shida, way’anda zasu tafi Russia Mascow yin wani course, baya ga haka kuma Idan sunyi wannan course din sun dawo, akwai ci gaba na musamman wanda za’a samu, a hospital din nasa, domin zasuje suyi course dinne, akan abunda ya shafi dashan k’oda, dana zuciya aikin ƙwaƙwalwa da juyen jini ga masu cutar sikila uwa uba da safarar tunanin kwakwalwar ɗan Adam, dama dai sauransu, kuma Insha Allah zasu kawowa K’asa cigaba.”

Idanu Dr. Lukman ya d’an zazzaro, cikin bakinciki takaici da kuma kunci yace.

“Wallahi kwata-kwata Barrister bani da wannan labarin, kuma ai wannan plant din nima, najima da tsarashi azuciyata, wanda kuma nakeso na aiwatar acikin hospital dina, amma kuma sai next year nakeson haka, why? Why? Wannan yaron ya shigemin hanci, komai zanyi saiya rigani kafin ma in tuna abu shi yayi, na shiga uku Anya zai barni na ci gaba arayuwata kuwa?”

Dr. Lukman din ya fad’i haka cikin tashin hankali, saboda ya fahimci cewa, duk saurinsa Dr. Rayyern din yana gaba dashi akan komai.

Boyayyen Murmushi Barrister Kabir yayi, tare da maida kansa ya ajiye ajikin kujera, yayi hakanne kuma saboda yanda yaga, hankalin Dr. Lukman din ya tashi sosai.

Alhaji Bala Tambari kuwa, gyara zamansa yayi...!



*Albishirinku! Ma'aurata, GA GARKUWAR KU nan tafe muku da tsarabobi na musamman gareku ma'aurata daga cibiyar mgnin mata mai taken GARKUWAR MA'AURATA*

NI DAI AYSHA ALIYU GARKUWA.
Ina matukar mamakin wani irin lokaci da ya riske mu mai wahalallan fassara. Kullum dai magana daya ce, akan ma’aurata, fada, rashin jituwa, mutuwar aure, akan kuskure kalilan, rashin kula, rashin yi wa juna uziri. Toh wai duk me ya janyo hakan? Na zurfafa a tsananin tunani hakan ya tilasta min bincike mai tarin yawa wanda ya kai ni ga gano inda matsalar take? Shin yar’uwa ke macece amma kin san wacece mace ku? Kin san me ake kira mace kuwa? Mace ita ce matar da take zama iyali a wajan namiji ta zame masa bango, sanyin idaniyarsa, ta zame masa gata da farin cikin rayuwarsa ta zame masa ruwa abar kore ƙishinsa ta zame masa mayafi mai karesa daga gigitar kadaice, ta kuma dorar da mijinta kan turbar gaskiya, ta kashe masa jiki da salonta ta rikita shi da baiwa da ni’imar da Allah ya bata idan har ta san hanyar mayar da kanta sabuwa dal awajanta, wato kullun takasance masa tamkar amarya har ya kasa tantance daren amarcinsu da sauran dararen rakun rayuwar su.

Wannan ita ce mace. Ina da wata saukakkar hanyar da zaki zama abar so da kulawa da soyayya a wajan mijinki ta hanya mafi sauki, 09097853276 hanyar ita ce ki gwada amfani da kayana na gyara ki gani, ina mai tabbatar miki da in sha Allahu sai kin dara da murna sai kuma kin gode min. Kayana kaya ne da aka yi shi da zallan itacanmu na gado marasa illa a cikin jikin dan adam musamman mace, kaya ne da suke taimakawa (sex hormones 😍) dinki.
Misali kina kallon India😘, hollywood, Asian film🥰 kina ganin yanda mazansu ke nunawa matansu tsananin soyayya kamar su ba su kyautar ransu!?
Saboda me hakan? Saboda suna sadaukar da lokacinsu wajan gyara jikinsu da kayan da ke tsattsafo da ni’ima cike da tsukewa, kayan nan kuma ana yinsu ne zallar magungunan gargajiya wanda ba su da illa domin haɗine na ingantattun itatuwa da yayansu.
Ina baiwar Allahn da miji ke daure mata fuska babu hirar arziki?
Zo ki ji yar’uwa zan baki gumbata da zallar gari wanda aka yi su da nagartattun itacen da ke da matukar amfani a jikin mace. Gubar ciko, gumbar tsalle dole, gubar da ba'a baiwa mai kishiya, garin maɗi, garin mallaka, tsumin goron tula, tsumin tsartai, tsumin maratsi, pala-pala butar sirri, kwanon k’asaitacciyar mace, furar mata madararta gareki Hajia takenta sha yanzu mgni yanzu,
Ina mata masu fama da sanyi? Sanyin mara ki zo na hadaki da magani na na sanyi wanda yake wanke mara ya fitar da duk wata cuta da ke samun mazauni a wajan.
Ina da ciccibi mai kyau. Ina da hadin amare mai kyau wanda zai gyara yarinya ya kankaro mata kimarta akwai hadin mai jego wanda muke yinsa na asali inada kekkyawan Hadi maida tsohuwa yarinya.


Akwai daya bangaren wato *KAMSHI*
Kimarki gyaranki da kamshinki. Matan da suka gane suka san yanda za su kankaro da mutunci su ne masu amfani da kayan gyara da kuma sanyaya jikinsu da kamshi, ina da turaren wanka da na bandaki na daki na jiki da na kaya dana tsuguno kamshin turarena na dabam ne mai sanyaya zuciyar wanda ya shaka ina da kayan kamshi na amarya da na maijego da na uwargida da dukkan macen da take kokarin mayar da kanta mai daraja a idon kowa ta zamo sarauni a idon mijinta, akwai shu'umar humra, sayan na gari maida kuɗi gida, banda karanta yayin gyara Hajia.

Zaku iya samun kayyakina a duk garin da kike, zakiyi min mgn ta whatsApp number na 09097853276 domin yin zaɓinki, ko karin bayani, zaki tura kuɗin ta account na 0005388578 Jaiz bank AISHA GARKUWA ALIYU in mun gama mgna zan sa miki kaya a mota yazo duk garin da kike, in baki shirya saya yanzuba Please kada mu wahal da juna ki bari sai kin shirya

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login