Showing 27001 words to 30000 words out of 104589 words
zare wayar akan kunnensa, cikin sanyi da kuma wani irin tunani dake dukan, kwakwalwarsa ya mikawa Riyyam nsra wayan.
Karb’an wayan Riyyam-nsra yayi tare da Karawa akan kunnensa.
Jin muryar Riyyam dinne kuma yasa, Mammy sauke wani irin nannauyar Ajiyar zuciya.
Cikin sanyi tace.
“Riyyam ka had’ani video call da Rayyern, inason naga ya yanayin jikin nasa.”
“To Mammy zan hadaku amma maybe sai gobe, saboda nasan yanzu haka yana sama, kuma Idan magriba ta kusa bayason yawan magana.”
Riyyam din ya fada atausashe.
Daga can b’angaren kuwa Kai Mammy ta jinjina, tare da cewa.
“Shikenan to badamuwa Allah ya kaimu goben.”
“Ameen”
Riyyam din ya amsa kana sukayi sallama da Mamyn.
Duk abunnan da sukeyi kuwa Jannart na kallonsu, saboda gaba daya hankalinta ya tafi garesu ne ma, yasa har yanzun take nan bata tafi ba.
Shikuwa Rayyern tuni ya shanye kunun da ta zuba masa din tas.
Ganin bata da niyan kara masa ne kuma yasa shi, dagowa ya kalleta.
Akaron farko kenan daya tsaya ya k’are mata kallo, idanunsa ya dan tsayar akan fuskarta, saboda yanda yaga hankalinta ya tafi izuwa wani waje na daban.
Ajiye cup din dake hannun nasa yayi, Karan ajiye cup dinnasa ne kuma yasa hankalinta dawowa garesa.
Ahankali ta juyo da kanta zuwa garesa, karab kuwa idanunsu suka sarke acikin na juna.
Sunkuyar da kanta k’asa tayi, tare da sauke numfashi, cikin silent voice dinta tace.
“Nak’ara maka ne?”
Kansa ya d’an girgiza mata, tare da lumshe idanunsa, cikin wani irin yanayin daya saka zuciyarta harbawa yace.
“Um um nakoshi.” yayi mgnar yana jin dadi bakinsa yayi masa wasai yawunsa ya sinke alamar dandanon bakinsa zai dawo.
Kallonsa tayi, haka kuma shid’inma.
Kasa tayi da Idanunta tare da matsowa ta durk’usa, tray din ta ke kokarin dauka.
Dan kusancin da sukayi ne kuma yasa, daddad’an kamshin turarenta ratsa cikin hancinsa.
Idanunsa ya dan lumshe, Yayinda itakuwa tray din ta dauka Anutse ta juya ta tafi.
Kaitsaye kasa ta sauka, bayan takai kayan kitchine ne kuma ta wuce dakinta.
Shikuwa Rayyern kiran Sallan magriba ne ya tadashi awajen.
Washegari.
Yau dinma kunun da Jannart din tayi masa jiya ya kuma sha, sai kuma abu mai romo da Mamy tasa ta dafa masa, babu laifi kuma yaci sosai.
After 3days.
Mamy ce tsaye agefensa, Yayinda shikuwa ke zaune akan daya daga cikin kujerun falon.
Murmushi Mamyn tayi tare da dubansa cikin danjin dadi.
Tace.
“Masha Allah Babana Lallai jiki yayi sauki, tunda har ka iya fitowa falo.”
Murmushi ya d’anyi tare da Kallon Mamyn nasa, cikin sanyi yace.
“Mamy yunwa nakeji sosai, kuma nafison abu mai dan tsami, please Mamy roasted fish da ruwan lemon tsami nakeso, ko kuma miyan da akayi ranan nan pls Mamy.”
Murmushi Mamyn tayi tare da cewa.
“To Rayyern amma ni bansan yanda akeyin miyan ba, rannan ma bani nayi ba Jannart ce tayi, amma bari na turo maka ita saikayi mata bayani.”
Fuskarsa yadan kwabe cikin shagwaba yace.
“Eyyah Mamy kifada mata mana, dole sai ni?”
“Eh mana bakaine kakeso ba.”
Mamyn ta fad’a tana me nufar dakin Jannart.
Ramadan dake zaune agefe kuwa, Kallon Hamman nasa yayi, tare da mik’o masa magungunan daya b’are.
Cikin kulawa yace.
“Please Hamma Rayyern karb’a maganinka kasha.”
Fuskarsa yadan yamutsa, kamar zaice a’a sai kuma ya karba yasha.
Bayan yasha maganin ne kuma Ramadan ya Mike ya tafi, domin dama hospital zai tafi, ya tsaya bawa Hamman nasa maganine.
Already Abba kuma dama ya tafi company, Riyyam-nsra kuwa yana waje .
Jannart kuwa dake falon ta zaune take, inda tayi kyau cikin wani fitted gown na maroon lace dake jikinta, sosai rigar tabi jikinta ta zauna, saboda yanda dinkin ya fita sosai.
Bak’aramin kyau yau Jannart din tayi ba, musamman da ta watsa jelan gashinta haka bata kitseshiba, tare dasa dan siririn mayafi daga kanta zuwa kirjinta.
Shigowar Mamy ne kuma yasa ta d’agowa, fuskarta dauke da murmushi.
Itama Mamyn murmushi tayi, tare kuma da Kallon Jannart din Cikin kulawa tace.
“Jannart kije mijinki yana kiranki.”
Kai Jannart din ta d’an sunkuyar kasa, cikin sanyi kuma tace.
“To.”
Juyawa Mamyn tayi ta tafi, Ganin hakanne kuma yasa Jannart din mikewa, Cikin yanayin nutsuwarta ta nufi part din nasa.
Ahankali ta murd’a handle din kofar ta shiga, bakinta dauke da sallama.
Saidai kuma dan ja baya tayi, ganinsa da tayi yana waya, hakan yasa ta matsawa jikin kujera ta d’an zauna, wanda hakan yasa suka zama suna fuskantar juna.
Ahankali ta dan saci kallonsa, musamman yanda taga yayi kyau cikin shigar riga da wandon DG dake jikinsa.
Ahankali ya ajiye wayar tare da d’ago kansa ya kalleta.
K’asa tayi da Idanunta, cikin sanyi tace.
“Ina kwana.”
Idanunsa ya sauke akan labbanta zuwa kan kirjinta, wanda dinkin jikin nata ya masifar fitar da shape din samansu.
Kauda kansa yayi batare da ya iya amsa mata ba
Itakuwa Jannart jin bai amsa mata dinbane yasa ta cewa.
“Ya jiki.”
“Da sauki.”
Ya amsa mata da wani irin murya, wanda yasa ta dago ta kalleshi.
Ahankali kuma tace.
“Gani Mamy tace kana kira na.”
Idanunsa ya dan marairaice cikin sanyin murya mai hade da zallan shagwab’a yace.
“Yunwa nakeji sosai, kibani abinci, but mai dan tsami kawai kinji....”
Yaja maganar tasa cikin wani irin yanayi, tare dasa hannunsa ya shafa cikinsa.
Hakan kuwa shiya sanya Jannart ta d’ago Kai ta kalleshi, lokaci daya kuma taji wani irin tausayinsa ya cika mata zuciya.
Ahankali Cikin yanayin ta itama dake kama da shagwab’a tace.
“To meye kakeso? Miya ko kuma abinci?.”
Idanunsa dake lumshewa ya rufe, tare da bud’e labb’an sa ahankali yace.
“I don’t know kimin komai kawai, ko miyan da kika tab’ayi ranan mai ɗan sami.”
“To.” Tace asanyaye tare da juyawa ta nufi hanyar fita.
Koda ta fito daga dakin nasa, Anutse ta soma sauka daga kan steps din.
Dai-dai lokacin kuma Riyyam-nsra yake haurowa saman, hannunsa rike da waya.
Ganin Jannart dinne kuma yasa shi sakin murmushi, Cikin kulawa yace.
“Good morning My Aunty ya jikin Hamma Rayyern.”
Murmushi tayi tare da dubansa, cikin sakin fuska tace.
“Jikinsa da sauki Riyyam, yanzu ma na sameshi afalo.”
Murmushi Riyyam din yayi tare da cewa.
“Masha Allah, bari naje na sameshi.”
Riyyam din ya fada, Yayinda ita kuwa Jannart kaitsaye kasa ta wuce, inda ta nufi kitchine Dan fara had’a masa abunda zaici.
Riyyam kuwa direct falon ya wuce, yana zuwa zuwa kuwa ya zauna akusa da Hamman nasa.
Tare da dan rankwafar dakai cikin sanyi, yace.
“Hamma Rayyern Mammy tanason yin magana dakai, tace kuyi video call saboda taga ya jikin naka, na kirata please?”
Idanunsa ya dan lumshe, akasalance kuma ya d’an gyad’awa Riyyam din Kai alaman “Eh.”
Murmushi Riyyam din yayi cikin, Jin dadi kuma ya zaro wayartasa tare da dannawa numbern Mammy kira video call.
Ring kadan kuwa wayar tayi Mammy ta d’aga.
Tana d’agawa kuwa Riyyam yayi murmushi, tare da Kallon Mammyn nasa Cikin kulawa yace.
“Mammyna Barka da safiya, ga Hamma Rayyern dinnan ku gaisa.”
Ya k’are maganan yana me mik’awa Rayyern din wayar.
Kasancewar kuma kan Rayyern din yana dan jingine ne yasa, Riyyam cewa.
“Hamma Rayyern ga wayan.”
Ahankali ya d’an juyo tare da kai dubansa ga fuskar wayar, wani irin bugawa yaji zuciyarsa tayi da karfi, wanda hakan ya sashi zabura tare da yunkurawa ya gyara zamansa, inda ya sauke ganinsa akan fuskar.........!
Littafin TUBALI dai na kuɗine ko kin gansa a wasu group ɗin na sata By
*GARKUWAR FULANI*Matar da hoton fuskarta ya cika fuskar wayar.
Wani irin harbawa yaji zuciyarsa tayi da karfi, wanda har saida hakan yasa shi zaro idanunsa waje.
Da matukar mamaki yake Kallon fuskar matar, Wacce bata da wata maraba da fuskar Ramadan, domin kuwa tsananin kaman Ramadan daya hango akan fuskarta ne ma, ya sanyashi jin wani irin bugun zuciya.
Lokaci daya kuma yaji wani irin nauyi, da kuma dattakun matar ya cika idanunsa, Yayinda daga cikin zuciyarsa kuwa, wani irin girma, kima, karamci, martaba da kuma haibar matar ne ke hauhawa cikin duk harbawar da zuciyarsa keyi.
Ganin fuskar matar ne kuma yasa, kowanne kofar gashi dake jikinsa budewa, take yaji wani irin sanyi na ratsa shi tako Ina, Yayinda kuma nutsuwa ke kara saukar masa.
“Mammy Ina kwana!!”
Ya fad’a cikin tausasa murya daga can cikin maƙoshinsa har zuwa kan labbansa.
Daga b’angaren Mammy kuwa da ta tsura masa ido bata ko k’yaftawa, wani irin abu itama takeji acikin zuciya da gangar jikinta, lokaci daya kuma taji zuciyarta tayi rauni sosai, tabbas Kallon fuskar Rayyern din da tayi ayanzu, yana tattare da wasu abubuwa da dama, ciki kuwa harda abunda ke kwance acikin zuciyarta, a mafi rinjayen tsawon shekarun rayuwarta.
“Lafiya Maud’ona ya jikin ka?”
Mammyn ta tambaya cikin boye rauni, da kuma damuwar dake kwance akan fuskarta yace.
“Alhamdulillah jiki na yayi sauki Mammy.”
Rayyern din ya bata amsa, cikin sanyi da kuma sigar tausasawa.
Riyyam-nsra kuwa dake zaune agefe idanu ya zubawa, Hamma Rayyern din nasa.
Mammy kuwa Daga can b’angaren ta, murmushi ne ya dan bayyana akan fuskarta, cikin tsananin kulawa da kuma muryar tausayawa tace.
“Allah Ubangiji ya karamaka lafiya, ya kareka aduk inda kake, ya tsare gabanka da bayanka, ya kuma nisanta ku da duk wani sharrin mutum da aljan, Allah ya baku zaman lafiya kaida iyalinka, ya albarkaci rayuwarku ya cika haske a rayuwarku Allah yayi maka al'barka!!!.”
“Ameen thumma Ameen Mammy nagode sosai.”
Rayyern din ya fada cikin nuna tsananin jin da d’insa, domin kowacce kalma da Mammyn zata fad’a, jinsa yake yana tasiri acikin zuciyarsa, Yayinda kuma yakejin wani irin farinciki na musamman yana lullub’eshi.
Mammyn ma Ganin farinciki kwance akan fuskarsa ne yasa ta jin dadi aranta, cikin kuma sakin fuska tace.
“Ya Ramadan da Mamyn ku?”
“Lafiyansu kalau Mammy, saidai Ramadan ya tafi wajen aiki, Mamy kuma tana k’asa.”
Ya bawa Mammyn amsa asake, yana mejin Karin nutsuwa na saukar masa sabida mgnar da yakeyi da itan.
“Masha Allah Allah ya taimaka, Ina Surukata Jannart, fatan itama tana lafiya.”
Mammyn ta tambaya da kulawa.
Idanunsa ya d’an lumshe tare kuma da bud’e su alokaci guda, cikin kwarin jikin daya samu yace.
“Lafiya yanzu ta sauk’a k’asa.”
Murmushi Mammy tayi, tare da jinjina kai, cikin farincikin dake da d’a mamaye zuciyarta duk bayan minti guda tace.
“To bari na bawa Zaytoon ku gaisa, gatanan duk ta tsareni da ido.”
Murmushi Rayyern din yayi dai-dai lokacin kuma, Mammyn ta mikawa Zaytoon dake gefen ta wayar.
Karb’an wayar Zayton tayi, tare da fadada fari’ar dake kan fuskarta, cikin muryarta mai dan sanyi tace.
“Hamma Rayyern.”
Saurin d’ago idanunsa yayi, ya kalli kyakkyawar yarinyar da ke magana acikin wayar, wanda muryarta tayi masa sak da wata muryar da yaji kwanannan , idanunsa ya Dan bud’e da kyau, tare kuma da zaro su waje, badon komai ba kuwa saidan Ganin still kamanin yarinyar sak na Ramadan ga kuma kamannin muryarta da waccar tsohuwar kamar dai yadda kamannin Muryar Ramadan Riyyam-nsra da ita Zayton ɗin a can wani sashin na zuciyarshi kuwa kamarsa da Riyyam-nsra ne ya fado masa “Yah salam”.
Yace a ransa a zahiri kuwa,
Idanu ya dan zubawa yarinyar, har na tsawon minti daya, kafun daga bisani ya fadada fara’ar dake kan fuskarsa, cikin sakewa yace.
“Na’am Zayton.”
Murmushi Zayton din tayi, kana cikin jin dadi tace.
“Sannu Hamma Rayyern ya jikinka, Ina fatan dai kayi sauki sosai, kuma kana cin abinci sosai ko?.”
Wani irin Murmushi Rayyern din yayi, wanda har saida kyawawan hakoransa suka bayyana, tashin farko yaji matashiyar budurwar tashiga ransa sosai.
“Jikina da sauki sosai Zaytoon, amma banason Ina yawan cin abinci saboda kada na zama ɗan lukuti kamarki.”
Dariya sosai Zaytoon ta kwashe dashi, saboda daga jin yanda yayi maganar ma kasan akwai tsokana aciki.
“Haba Hamma Rayyern ni har wani jiki ne dani, kanaga saboda banida jiki ne ma ai, Riyyam ya rainani, Hamma Rayyern Ina Auntyna Jannart take?”
Zaytoon din ta tambaya, cike da kulawa.
Murmushi yayi tare da d’an shafa lallausan sumar kansa, cikin muryar tausasawa yace.
“Tana k’asa.”
Kai Zaytoon din ta jinjina, tare kuma da dan rausayar dakai, cikin nuna kulawarta agaresa tace.
“To ka gaishemin da ita kaji, sannan please Hamma Rayyern kana kulawa da kanka kaji, Allah Ya baka lafiya mai amfani.”
Idanunsa ya d’an lumshe tare kuma da sauke Ajiyar zuciya, saboda sosai yaji dadin addu’ar da yarinyar ta masa kana har cikin ransa yake jin sonta a ransa.
Wanda har hakan yasa shi cewa.
“Ameen nagode Zaytoon.”
Kai Zaytoon din ta jinjina, Yayinda shikuwa Rayyern ya mikawa Riyyam nsra dake zaune agefe wayan.
Da sauri Riyyam da zuciyarsa ke cike da farinciki ya karb’i wayan tare da fuskantar screen din wayar, cikin kula dajin dadi yace.
“Mammyna yau kam kinga Hamma Rayyern dinmu ko.”
Kai Mammyn ta jinjina, cike da jin dadi tace.
“Kwarai kuwa Riyyam yau kam naga Rayyern.”
Tayi maganan cikin kasa da murya, ta yanda Riyyam dinne kadai zai iya Jiyota.
Jin abunda ta fada dinne kuma yasa Riyyam nsra tashi, rike da wayan a hannunsa kaitsaye ya nufi dakin Ramadan.
Shikuwa Rayyern maida kansa jikin kujera yayi, tare da lumshe idanunsa, ahankali yake lumshe idanunsa, yana mejin wani irin nutsuwa na saukar masa.
Mammy da Riyyam kuwa basu wani jima suna magana ba, Mammy ta katse kiran.
Acan Ethiopia kuwa bayan Mammy ta ajiye wayanne, Ta zame daga zaunen da take tare da durk’usawa k’asa tayi sujjada.
Na nunawa Allah tsananin jin dadinta, da kuma godiya agaresa, domin komai da yake faruwa shine ya tsarashi, shine kuma yake bawa ahalinta dama ita kanta kariya akoda yaushe.
Acan b’angaren Jannart kuwa Anutse ta kammala gasa masa roasted fish, tare da matsa masa ruwan lemon tsami aciki, kamar yanda ya gaya mata yana buk’atar abu mai d’an tsami tsami, bayan ta kammala had’a masa roasted fish dinne kuma, ta soma kokarin yi masa miyan kase kamar yanda ya buk’ata, saidai kuma kasancewar miyar tana daukan lokaci sosai, shiyasa gama ta ba yanzu yanzu ba.
Rayyern dake zaune afalo kuwa, Ganin almost 1hour ya kare ba akowa masa abincin nasa bane, yasa shi haurawa saman sofa ya kwanta.
Ahankali yake lullumshe idanuwansa, wanda da’alama kuma bacci yakeji, duk da cewar kuma yana jin yunwa, amma hakan baisa baccin yaki daukarsa ba.
Domin yana nan akwance cikin abunda bai wuce 20mn ba, bacci ya d’aukesa, kasancewar acikin magungunan da yake sha akwai mai dan saka yawan bacci.
2hours later.
Ahankali yake bude idanunsa, wanda suka shafe sama da awa biyu a kulle.
Mik’a ya d’anyi ahankali tare da ambaton sunan Allah acikin zuciyarsa.
Ahankali ya dan tashi zaune, tare dasa hannu ya shafa kan lafaffen cikinsa, da keyi masa kukan yunwa.
Numfashi ya d’an fesar akasalance kuma, yakai dubansa izuwa babban agogon dake cikin falon.
1:25 pm dai-dai agogon ya nuna masa, wanda hakan ya sashi d’an yunk’urawa ya mike.
Musamman saboda ganin da yayi lokacin sallah yayi.
Hannayensa ya zura acikin aljihun wandon dake jikinsa, kaitsaye kuma cikin tafiyar, dake nuna ya Dan samu karfin jikinsa ya nufi bedroom d’insa.
Koda ya shiga cikin bedroom din Anutse, ya soma kokarin rage kayan dake jikinsa.
Bayan ya cire trouser’n dake jikinsa ne kuma, ya d’auko wani towel ya d’aura akan waist d’insa.
Direct toilet ya wuce, inda ya had’ewa kansa ruwan wanka mai d’an d’umi.
Anutse yayi wankan nasa tare da d’auro alwala ya fito.
Koda ya fito daga toilet din kuwa wani irin kamshin shower jel ne ke tashi ajikinsa, Yayinda kuma tausassun gashin jikinsa suka kwanta lub.
K’awataccen sajen dake kwance akan fuskarsa kuwa, shek’i take tayi saboda danshin ruwa dake jikinta.
K’arasawa gaban mirror yayi, tare da d’aukan mini towel ya shiga goge ruwan dake jikinsa.
Komai nasa da nutsuwa yakeyinsa.
Hakan yasa duk wanda zai kallesa sai yaji ya burgesa.
Had’add’en body lotion d’insa ya shafa, sai kuma turaren companyn Gucci daya shafa ajikinsa.
K’arasawa gaban drawern d’insa yayi, inda ya ciro wani riga da wandon companyn Ouchpan masu kyau da taushi.
Rigar irin long sleeve d’innan ne, sai kuma wandon daya kasance tight, Wato mai dan kama jiki, amma kuma irin jeans dinnan ne, masu yanayi da crazy.
Anutse ya zura kayan ajikinsa, tare da d’aukan wasu simple shoe ya zura akafafunsa.
Masha Allah! Ba k’aramin kyau kayan sukayi masa ba, kasancewar su black colour kuma shiyasa suka k’ara bayyana, hasken da fatarsa ta k’ara.
Ahankali ya d’an ciji jajayen labb’ansa, tare kuma dasa hannunsa ya shafa cikinsa dake kukan yunwa.
Fuskarsa ya d’an kwab’e tare da karyar da wuyansa gefe, Allah ya sani yunwa yakeji sosai.
Domin har wani jiri jiri yakeji.
Wayarsa dake kan gado ya d’auka, tare kuma da nufan falon nashi kaitsaye.
Koda ya fito idanunsa ya sauk’e akan dining table din dake cikin falon, saidai kuma rashin ganin an ajiye masa abunda zaici ne yasa shi b’ata fuska, tare da d’an rausayar da idanunsa, cike da kasala da kuma yunwa ya nufo main falon nasu kaitsaye.
Acan b’angaren Jannart kuwa bata jima da kammala had’a abincin ba, kasancewar kuma garin ana d’an yanayin zafi shiyasa, Koda ta kammala had’a abincin a tray, kaitsaye part dinta ta koma.
Wanka tayi da sabulun beauty touch, wanda yasa gaba daya jikinta ya d’au sassanyan k’amshin sabulun.
Bayan ta fito daga wankanne kuma ta shirya kanta, cikin wani had’add’en English wear gown, wanda kwata kwata bashi da nauyi, kasancewar kuma rigar tight gown ne shiyasa ya bayyana duk wani shape din jikinta.
Harta kan nipples dinta kuwa saida ya bayyana, sosai rigar tayi mata kyau, tare da k’ara bayyana tsararren surar jikinta.
Turaren oud mai kamshin gaske ta shafa ajikinta, bayan ta tubke dogon gashin kanta, wanda yasha kitson da Mamy tayi mata ne kuma, ta yafa wani mayafi mai kauri ajikinta, daya rufe duk wani shape dinta, tayi hakanne kuma saboda sanin da tayi cewa, akwai maza agidan.
Juyawa tayi Ahankali kuma Cikin nutsuwa ta fice daga cikin dakin.
Kaitsaye kitchine ta nufa, dan daukan abincin da ta dafa din.
Rayyern kuwa Ahankali yake saukowa daga matattakalan steps din.
Cikin nutsuwa da kuma d’aukar hankali yakeyin kowanne takunsa.
Ahaka yake saukowa daga kan steps din.
Hannunsa daure akan cikinsa, yana shafawa tare da d’an lumshe idanunsa.
“Mamy Mamy!!”
Sunan Mamy yake kira ahankali, cikin kuma muryarsa da tayi sanyi sosai, saboda rashin k’arfi da kuma yunwan da yake fama dashi.
Adai-dai lokacin kuwa Jannart ta k’araso tsakiyan falon, Jin kamar muryar mutum ne kuma yasa ta d’aga kanta, karab kuwa Idanunta suka sauk’a akansa.
Kyawawan Idanunta ta d’an zuba masa, tare da soma Kallon shigar dake jikinsa, Wacce tayi masa kyau sosai.
Dai-dai lokacin kuma shima ya sauk’e idanunsa akanta.
Ahankali ya zame tare da zama akan steps din karshe dake kan matattakalan, idanunsa ya d’an lumshe tare dasa hannu ya dafe cikinsa, wani irin numfashi yake sauk’ewa mai d’auke da gajiya, cikin sanyin muryar dake nuna gajiyawarsa ya k’wala kiran sunan Mamy.
“Mamy tana d’akinta.”
Jannart din ta