Showing 96001 words to 99000 words out of 104589 words

Chapter 33 - Tubali Book 2 Hausa Novel Complete

Unknown   

21 Dec 2024

184

inajin nauyin wannan abun azuciyata kullum.”
Ajiyar zuciya Aunty Dijat din ta sauke, cikin kuma so da tausayin mijinta tace.

“Kayi hakuri Barrister Tabbas kowacce rayuwa da irin k’addararta, amma Insha Allah babu wanda zaka sake rasawa.”

“Dole zan rasa Dijat nina sani lallai dole zan rasa, rashin da nayi shekaru 22 da suka wuce, shi zaisa na sakeyin wani rashin ayanzu. Maraicin Jannart nake dubawa Dijat, Maraicin Jannart maraicine da yake cike da abubuwa masu tarin yawa, haka kuma maraicine da yake buk’atar tausayawa da jin k’ai, Ina matuk’ar tausayin Jannart....”

Ya kare maganan still cikin kuka, wanda hakan yasa Aunty Dijat soma shafa bayansa ahankali, kuma cikin lallashi take tausasa sa.

Rayyern kuwa dake Jin duk wani abu dake faruwa acikin wayar, idanunsa ya rumtse da k’arfi, saboda wani irin masifaffen raunin da yaji ya lullub’esa haka nan yaji wani irin tausayin Jannart da Barrister Kabir keta nanata maraicinta.

Tabbas bazai iya jurewa jin abubuwan da suke fad’ad’in ba, wanda hakanne kuma ya sashi zare wayar daga kunnensa, tare da katse k’iran gaba d’aya.

Ahankali kuma cikin dogon tunanin daya fad’a, ya juyawa tare da zubawa Jannart din dake kwance idanu hannunta ya manna kan bakinsa tare da liƙa mata wani sassayan kiss.

Filla filla kuma haka yakejin maganganun Barrister Kabir na dawowa kunnuwansa.
Babu kuma abunda yafi tsaya masa arai, kamar Maraicin Jannart din, da yaji Barrister Kabir din nata ambata.

Asanyaye cikin kuma tsananin tausayinta da yaji ya dirar masa azuciya, ya ronk’ofo jikin.
Lallausan tafin hannunsa ya d’aura akan goshinta, wanda yaga yana ta tsatstsafo da gumi, ahankali ya share mata gumin, tare kuma dasa Y’ar yatsarsa ya gyara mata, dogon gashinta wanda ya d’an rufe mata gefen fuskar ta.

Still kuma duk abunda yakeyi din idanunsa, nakan kyakkyawar fuskarta wacce tayi fayau, ga kuma zara zaran gashin Idanunta wanda suka baje, suka kuma k’arawa fuskarta ta kyau.

Akaron farko yakejin wani irin matsanancin tausayi, da rauninta na ratsa cikin zuciyarsa.

“Maraicin Jannart nake dubawa, Maraicin Jannart yana matuk’ar buk’atar kulawa, da kuma tausayawa.”

Way’an nan kalaman sukeyi masa yawo acikin k’wak’walwa, wanda har saida hakan yasa shi jin wani nauyi azuciyarsa.

Wannan dalilin yasa asanyaye ya d’an sukuyo da kansa gareta, wanda hakan yasa numfashinsa soma sauk’a akan kyakkyawar fuskarta.

Ahankali kuma cikin tausasa murya yace.

“Allah ya baki lafiya My Janna.”
ya kare maganan nasa da tausayawa.

Ahankali kuma ya jawo kujera ya zauna akusa da ita, cikin dan yanayin sanyi ya kamo hannunta na dama ya rik’e acikin nasa.
Wanda hakan yasa tafukan hannayensu had’ewa awaje d’aya.

Wani irin d’umin dad’in da yaji ne kuma yasa shi, kwantar da kansa agefenta, tare kuma da d’aukan hannun nata, ya d’aura ak’asan hab’arsa.
Idanunsa ya lumshe anutse kuma yake shak’an, daddad’an k’amshin turaren dake tashi ajikinta.

Almost 5mn suna nan ahaka, Yayinda Jannart din keta baccinta cikin nutsuwa.

Shikuwa Rayyern ahankali yake d’an yawo da bayan hannun nata akan fuskarsa, har dai ya gangaro zuwa kan lallausan sajensa.

Idanunsa ya kuma lumshewa adai-dai lokacin, da ya kawo hannun nata saitin bakinsa, ba tare da zato ko tsammani ba kuma, saiji yayi ya d’aura mata sassayan kiss akan bayan hannun nata a karo na biyu.

Jin abunda yayi dinne kuma yasa shi sake lumshe idanunsa, ahankali ya janye hannun nata zuwa kan hab’arsa.

Itakam Jannart duk batasan ma meya keyi ba, saboda baccinta kawai takeyi.

To shima Rayyern din dai ahaka bacci ya d’aukesa, yana rungume da hannunta, yayinda kansa kuwa ke manne ajikin gadon nata.

Bacci sukeyi sosai saboda dama tuni dare ya raba, musamman ita Jannart wanda akayiwa allurar bacci, saboda ta sanadiyar baccinne numfashi da kuma bugun zuciyarta zasu dai-dai-ta.

*5:00am.*

Ahankali take d’an motsa jikinta, wanda takejin yayi mata nauyi sosai, cikin sanyi da kuma kalasar dake damunta, ta bud’e Idanunta wanda sukafi kama dana y’an maye.

Da sauri tasa hannu ta dafe saman marar ta, da takejin ya cika saboda tsananin fitsarin da takeji,wanda kuma shine ya tasheta daga baccin da takeyi.

Ahankali ta d’an juya Idanunta gefe, inda ta sauke ganinta akansa.
Bacci yakeyi atsanake still kuma hannunta na cikin nasa, wanda ya rik’e gam tare da d’aura kansa akai.

Idanu ta d’an zuba mishi hade dajan dogon numfashi, saboda har yanzu akwai oxygen akan hancin ta, saidai tuni numfashinta ya dai-dai-ta.

Ahankali tasa d’ayan hannunta ta tab’a oxygen din, cikin kuma wani irin yanayin dake nuna bata wani hayyacinta sosai, saboda alluran baccin da bai gama saketa ba.

“Naaaaaannnnn!!!”

Ta kira sunansa cikin sassayan murya, tare dajan dogon numfashi.
Still kuma Idanunta na ci gaba da rufewa, kamar wata y’ar maye.

“Naaaannn!!!”
Ta sake kiran sunansa asanyaye.

Rayyern kuwa acan cikin baccin nasa, ya d’anji sautin muryarta sama sama, hakan kuwa shi yasa ya bud’e idanunsa.

Ganin idanunsa abud’e ne kuma, cikin yanayin mayen baccin da baigama sake shiba yace.

“Janna, kin tashi ya jikin naki?”

Idanunta dake bud’ewa da rufewa ta d’an juya, kana asakalce cikin kuma yanayin marassa lafiya tace.

“Da sauki, please Naan kacire min wannan abun numfashina ya dai-dai-ta.”

Tayi maganan tana me nuna oxygen din.

Shikuwa Rayyern jin hakanne yasa shi, d’an rank’wafowa kanta tare dasa hannusa ya dafa saman kirjinta atsanake yaji numfashin nata na tafiya.

Wanda hakanne kuma yasa shi gangaro da hannun nasa, saman mak’oshinta saboda yanason yaji bugun zuciyarta.

Akokarinsa nayin hakanne kuma, lalausan tafin hannunsa ya sauk’a asaman breast dinta, batare daya sani ba.
Wani irin masifeffen abu yaji yana bin dukkan jijiyoyin jikinsa, wanda haka yasa ya
D’an d’ago da sauri ya kalleta, kana cikin tausasa murya dason shagwab’ata yace da narkewa da shima yayi yace.

“Bugun zuciyarki bai gama dai-dai-ta ba Janna, ki d’anyi hakuri kinji.”

Kai ta d’an jinjina masa kana cikin kasala ta zare oxygen din akan hancinta, ashagwab’e kuma tace.

“Naan zanyi fitsari.”

“To.”
Ya fad’a tare da k’arasa zare mata oxygen din, dai dai ta yunk’ura zata tashi ne kuma, Rayyern din ya saka hannayensa duka ya tallafota,tare da zaunar da ita akan
Saidai kuma yana zaunar da ita, yaga ta tafi luuuuu zata kwanta, alamun tana cikin magagin bacci.

Da sauri ya tallafota ta fad’a jikinsa, idanu ya d’an zuba mata ganin yanda jikinta ke rawa ne kuma, yasa shi rungumeta tsam ajikinta.

Pat-pat haka zuciyarshi take harbawa.
“Yah salam”.
Ya faɗi a cikin zuciyarsa domin yaune karo na forko da yayi mata irin wannan ruggumar murya a narke can ƙasan maƙoshinsa.
“Janna.”
Ya kira sunanta cikin dan tausasa murya.

Jannart kuwa jinta ajikinsa ne yasa ta sake narkewa, tare da lumshe Idanunta.

Cike da sabon shagwab’a tace.

“Naan zanyi fitsari.”

“To muje na kaiki toilet tunda naga kaman baccin bai gama sakeki ba.”

D’an k’aramin bakinta ta turo gaba, tare da cewa.

“A'a zan iya zuwa da kaina.”

“Bazaki iya zuwaba Janna muje na kaiki.”Ya fad’a cikin serious, tare da kamo hannunta ta sauko daga kan gadon.

Bisa jagorancinsa kuma suka nufi toilet din dake cikin dakin.

Shiya bud’e mata k’ofar toilet din ta shiga, har ta saka k’afarta acikin toilet din kuma saita dakata, tare da juyowa ta kalleshi da maraitattun idanunta.

Gane abunda take nufi ne kuma yasa shi, d’auke kansa gefe tare da cewa.

“To kiyi fitsarin mana.”

Bakinta ta d’an turo gaba, cike da salon shagwab’a tace.

“a’a nidai ka fita.”

Idanunsa ya d’an jujjuya saboda Jin abunda ta fad’a, Ahankali kuma yace.

“Ok ashe abun babu dadi kenan.”

Da sauri tayi k’asa da kanta, saboda gane abunda yake nufi.

Shikuwa Rayyern kansa kawai ya girgiza, batare kuma daya sake cewa komai ba, ya juya tare da sakar mata kofar ya fice daga cikin toilet din.

Ganin hakan da tayi ne kuma yasa ta, tsugunnawa tayi fitsarin, Koda ta gama alwala tayi, saboda tasan zuwa yanzu lokacin sallan asuba yayi.
Bayan ta idar da alwalanne kuma, ta Mike asanyaye ta murda handle din kofar ta fito.

Tana fitowa dinne kuma sukayi karo dashi, saboda dama bai bar jikin kofar ba.

Da sauri tayi baya baya kaman zata fad’i, Ganin hakanne kuma yasa Rayyern din rik’ota, tare da jawota ya zaunar da ita akan gadon.

Idanunsa ya dan zuba mata, Ganin hakanne kuma yasa ta lumshe nata idanun, tare da bud’e bakinta ahankali tace.

“Naan Zanyi sallah.”

Dan karamin bakin nata dake matsowa ahankali ya kalla, Cikin kulawa yace.

“Janna anan babu sallaya, kuma kinga ko hijab babu, amma kijira bari na duba Dr. Imran tunda shi Musulmi ne, nasan baza’a rasa sallaya ba, amma samun hijab kam zaiyi wuya.”

Kai ta d’an langwab’ar kana ahankali tace.
“To ai mayafina ma zaiyi sallah idan na nad’ashi ya rufe duk gashina, kuma kayana baya nuna jiki.”

Yanayin yanda ta k’are maganan tana lumshe Idanunta ne, kuma yasa shi jinjina kai.

Saidai batare daya sake cewa komai ba, ya shige cikin toilet din dake cikin dakin.

Al'wala ya dauro, bayan ya fito daga toilet dinne kuma, ya dan kalleta tare da cewa.

“Bari naje nayi sallah, Idan na dawo sai kiyi naki sallan.”
Kai ta jinjina masa tare da maida jikinta ta kwanta, akan gado shikuwa Rayyern ficewa daga cikin dakin yayi.

Kaitsaye kuma Dan madaidaicin masallacin dake cikin Hospital din ya nufa.

Koda yaje ya samu har an idar da sallah, hakan yasa shi kad’ai yayi nasa sallan.

Bayan ya idar da sallan ne kuma, direct ya wuce office din Dr. Imran.

Yana isa bakin office din kuwa, suka hadu da Dr. Imran din.
Cikin mutum tawa sukayi musabaha, kana fuska asake Dr. Imran din yace.

“Ya jikin Madam din, yanzu nake rayawa araina cewar zanje na duba ta.”

Murmushi Rayyern din yayi, tare da cewa.

“Alhamdulillah jikinta yayi sauki sosai, yanzu ma ta tashi wai tanason tayi sallah ne.”

Murmushin Jin dadi Dr. Imran din yayi, kana cikin farinciki yace.

“Masha Allah ai indai ma numfashinta ya dai-dai-ta, to zaku iya tafiya gida babu wani matsala, yanzu muje na duba jikin nata mugani.”

“To.”
Dr. Rayyern din yace tare da juyawa, suka nufi dakin da Jannart din take.
Suna shiga kuwa suka sameta akwance, saidai kuma ganinsu da tayi ne yasa ta tashi zaune.

“Mrs Rayyern sannu ya jikin naki?”
Dr. Imran ya fad’a yana me kokarin, d’auke oxygen din dake kan gadon.

Jannart kuwa jin sunan da ya kira ta dashi ne, yasa tayi kasa da kanta Ahankali kuma cikin sanyi tace.

“Da sauki sosai.”

“Masha Allah haka akeso ai, Allah ya kara afuwa, yanzu babu wani abu dake yi miki ciwo kenan?”

Kanta ta gyad’a alaman “Eh”

Hakanne kuwa yasa Dr. Imran juyowa ya kalli Rayyern.

“Doctor zaka iya daukanta ku tafi gida babu matsala, saidai kaman yanda kasanine mai asthma dole sai anayi ana kiyayewa, sannan ka tafi da way’annan alluran guda 5 kullum, guda d’add’aya zaka na yi mata.”

Kai Dr Rayyern din ya jinjina tare da karb’an alluran, ya rik’e.

Jannart kuwa jin ance allurai za’ana yi mata ne, yasa ta juyo ta kalleshi, araunace da kuma yanayin tsoro tace.

“Naan allurai za’ana min kuma”.
Ido ya d’an zuba mata tare da gyaɗa mata kai.

Cikin yanayin sanyi tace.

“Abba na ya hana amin allura kawai abani magani.”

Idanunsa ya d’an zuba mata Ganin kuma da gaske batason alluranne, yasa shi gyara tsayuwarsa tare da cewa.

“Janna dole ai miki alluran sune zasu taimaka miki ai wajen samun sauki, ko bakyason ki rabu da asthma dinne?”

Still rau-rau tayi da idanu, tare da soma kunkuni acikin zuciyarta, saboda harga Allah ita batason allura dama a dole Dr Lukman keyi mata data samu Abbanta ya hana kuma ta huta.

Dr. Imran kuwa ganin suna magana da wani, yaren da baisani bane yasa shi, sakin murmushi tare da mikawa Rayyern din takardar sallama.

Rayyern kuwa bayan ya karb’i takardar, hannun Jannart din ya kamo.

Cikin yin k’asa da murya yace.

“Muje ko.”

Babu musu kuwa ta kama hannun nasa, saboda har yanzu jikinta babu kwari, sannan kuma idanunta basu daina rufewa ba saboda bacci.

Ahaka dai suka fito daga cikin Hospital din.
Inda Dr. Imran ya rakosu har bakin mota.
Saida yaga tashin motarsu kuma, kafun ya koma cikin asibitin nasa.

Su kuwa su Rayyern Koda suka dau hanya, shagwab’a sosai Jannart din take tayi, tare kuma da wasu irin sambatu wanda shi baisan ma na meye ba.

Saidai duk abunda takeyi yana kallonta, ta gefen idanunsa, yanayin yanda take abubuwan nata ne kuma, yasa shi fahimtar cewa har yanzu alluran da akayi mata dinne bai gama sake ta ba, shine kuma ke sawa tana sambatu, kasancewar bata samu isashshen bacci ba.

Kaitsaye gida suka nufa, suna zuwa kuwa ya yi parking motar, tare da fitowa ya zagayo b’angaren Jannart din ya fito da ita.

Yana rike da hannunta haka suka nufi cikin gidan.

Koda suka kawo bakin kofar falon, hannunsa ya d’aura akan security door din, tare da danna wasu numbers, almost 4 minute glass din ya nuna masa reguest.
Ganin yadda take layine, yasashi gyara tsayuwar sa tare da manna bayanta da k’irjinsa kana ya d’an zuro kanshi ta kan habarta na dama.
Hannunta ya kamo ahankali ya daura akan glass din, take kuwa duk na’urorin wajen suka amsa, inda sunanta ya bayyana b’aro b’aro ajikin d’an na’urar.

Idanunta ta d’an zaro tana Kallon abun.

Dai-dai lokacin kuma na’urar ta rubuta, Accepted.

Zare hannunta daga kan na’urar yayi, Ahankali kuma yace.
“Sake d’aura hannunki.”

“To.”
Tace tare da d’aura hannun nata, take kuwa saiga kofar ta bud’e.

Kallonsa tayi da mamaki, shikuwa Rayyern gefenta ya rab’a tare da wucewa Cikin falon.

Ganin hakanne kuma yasa itama ta rufa masa baya.

Koda suka shiga falon zama tayi akan kujera, Yayinda shi kuwa ya wuce bedroom dinta, ya d’auko mata hijab da sallaya.

Koda ya dawo anan cikin falon ya shumfud’a mata sallayan, tare kuma da mika mata Hijab din.

Kana ya koma gefe ya zauna, itakuwa Jannart ganin hakanne yasa, Ahankali ta tashi tsaye, tare dasa hijab din ta tada sallah.

Shikuwa Rayyern wayarsa ya d’auka, yayi musu ordern abinci.
Bayan ya gama order ne kuma ya ajiye wayar, tare da maida kansa ya jingina da jikin kujera, Ahankali yake Kallon fararen tafin k’afarta, kasancewar tana zaman tahiya ne.

Jannart kuwa tana gama tahiyan ta sallame sallan, tare da jingina ta kwanta akan sallayan.
Ahankali kuma ta lullub’e duk jikinta, da hijab din nata, tare da maida Idanunta ta lumshe.

“Ya jikin naki?”

Ya tambaya yana me Kallon kyakkyawar fuskarta.
“Da sauki.”
Ta amsa masa batare da ta bud’e Idanunta ba.
Saboda wani irin bacci takeji yana fusgarta.

Dai-dai lokacin kuma aka soma knocking kofar falon, Ahankali ya mike tare da k’arasawa ya bud’e kofar falon.

Kamar yanda ya tsammata kuwa abincin da yayi order ne ya iso, bayan ya k’arbi abincinne kuma ya dawo falon.

Akasalance ta Dan bude Idanunta ta kalleshi, cikin sanyi da kuma kasala tace.

“Naan zanyi bacci.”

D’an rank’wafowa Kanta yayi ahankali, kuma cikin tausasa murya yace.

“Okay amma tashi kici abinci, Idan nayi miki allura saiki kwanta kinji...”

Bakinta ta turo gaba, tare da Dan yi masa kallon wannan mugunta zaimin mai kama da shagwab’a tace.

“Allura da sanyin safiyan nan, Naan kayi haƙuri dan Allah sai anjima bayana ma ciwo yake.”

Ta kare maganan tana me daura hannunta, akan hips dinta.

Rayyern kuwa Ganin hakanne yasa wani, irin sihirtaccen Murmushi kwace masa, ahankali kuma ya zauna akusa da ita.
“Don’t worry alluran ai ba abaya akeyinta ba, a hannune malama.”

Ya fad’i hakan yana me danne dariyar dake ransa, tare kuma da soma bud’e ledodin restaurant din dake hannunsa.

Jannart kuwa jin hakanne yasa ta tashi ta zauna, cikin sigar shagwab’a tace.

“Ayyah Naan ni hannun nawa ma ai ciwo yake, duk karkarwa ma yake bazai iya tsayuwa waje daya ba, kuma ni banason allura ya karyemin ajiki.”

Takare maganan tana me d’an yin mui-mui da k’aramin bakinta.

Rayyern kam dariyarta gaba d’aya duk ta kamasa amma saiya danne, saboda tunda yake bai tab’a ganin mai tsoron allura irinta ba.

D’agowa yayi ya kalleta.

“Da wani idanunta kamar na y’an shaye shaye.”

Ya fad’i hakan acikin zuciyarsa.

Azahiri kuwa takeaway din abincin ya turo gabanta, tare da zuba mata narkakkun idanunsa.

Cikin kulawa yace.

“Oya eat idan kuma ba haka ba, To ya zama lallai dole sai anyi miki allurai guda biyu kuma in sossoka miki su da k’arfi.” Da sauri ta zazzaro Idanunta, lokaci daya kuma ta k’wabe fuska tamkar zatayi kuka, badan taso ba kuwa haka ta dauki spoon ta soma tsakalan abincin.

Rayyern kuwa Idanu ya zuba mata, tare da harde hannuwansa akirjinsa.

Ganin hakanne kuma yasa ta d’an tuttura abincin bisa dole badan taso ba.

Bayan ta danci kadan ne kuma ta ture abincin gefe, tare da kwaɓe fuska cikin murya kaman zatayi kuka tace.

“Ni nakoshi.”

“Yauwa to sai allura kuma ko?”

Rayyern din ya fad’a yana me gyara zamansa, tare da d’auko daya daga cikin alluran.

Da sauri ta matsa nesa dashi, cikin dan yanayin roko, hawaye har yana fita daga Idanunta tace.

“Please Naan, Dan Allah kar kamin alluran yanzu, ka bari sainayi bacci na tashi kaji, please kaji Naan...”

Ta kare maganan tana me yarfa yan yatsun hanunta, cike da tsananin tsoro.

Idanu Rayyern din ya zuba mata, aransa yana me matuk’ar mamakin irin yanda Jannart din, take matuk’ar tsoron allura.

Fahimtar yanda duk take atsorace ne kuma, yasa shi dan tausasa murya.Cikin kulawa yace.

“Kwantar da hankalinku Naji bazanyi miki allura ba, tashi kije ki kwanta.”

Ajiyar zuciya mai karfi ta sauke, saboda Jin abunda ya fad’a d’inne kuma yasa, ta Dan lumshe Idanunta tare kuma da matsowa kusa dashi, murya araunace tace.

“ai bazan iya tashi ba, anan zan kwanta, jikina duk babu karfi.”

“Kinason sanyi ya sake kamaki ne? Ko kinason na miki allura, maza tashi muje daki.”

Ya fad’a yana me mik’a mata hannunsa.

Da sauri ta kama hannun nasa ta Mike tsaye, saidai tana tashi din taji jiri na neman kada ita, wanda hakan yasa da sauri Rayyern din ya tallafota, tare da kwantar da ita ajikinsa.

Batare kuma daya jirayi wani abu ba, kaitsaye ya nufi bedroom d’insa da ita.

Ita kuwa ganin sun nufi bedroom din nasa ne, yasa ta karya fuska tare da d’agowa ta kallesa.
Ashagwab’e tace.

“Naan dakinka kuma? ka kaini bedroom dina mana....”


“Shiiii ni bazan iya kaiki bedroom dinki ba, kinji nauyinki kuwa saikace na buhun masara, taya yama mai nauyi kaman na doki, zai dauki mai nauyi kaman na buhun masara.”
Ya fad’i maganan yana me matse hannunta dake cikin nasa.

Da sauri ta kalleshi, saboda ta tabbatar abubuwan da tayi masa ne yake ramawa.

Bakinta ta turo gaba cike da shagwab’a kuma, ta d'an muntsineshi wai ko zaiji zafi ya sauk’eta.

Duk da yajita amma bai kulata ba, ahaka har suka k’araso cikin d’akin nasa.

Suna shiga ya direta abakin gado, tare da komawa ya zauna yana meda numfashi, kamar wanda yayi aikin karfi.

Wanda kuma yanayin hakanne kawai son rai, bawai Dan tana da nauyi ba, Dan hasalima Koda ya dauketa ji yayi kamar ya daga Y’ar shekara 13 ne.

Itakuwa Jannart ganin hakanne yasa ta, sake

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login