Showing 24001 words to 27000 words out of 104589 words

Chapter 9 - Tubali Book 2 Hausa Novel Complete

Unknown   

21 Dec 2024

161

Dr. Sulaiman kuwa ya zauna akan bedside drawer, cikin nuna kulawa ga abokin nasa yace.

“Sannu Dr Rayyern ya jikin naka? da Fatan ka d’anji k’arfin jiki.”

Idanunsa ya d’an lumshe kana Ahankali yace.

“Alhamdulillah, nasan komai zai dawo dai-dai soon.”

“Insha Allah, amma fa kasan dole saika dage, musamman wajen cin abinci, domin yanzu ma haka akwai magungunan dana kawo ma, amma dole sai kaci abinci kafun kasha su.”

Cewar Dr. Sulaiman yana me fito da wasu magunguna daga aljihunsa.

Rayyern kuwa Ganin magungunan ne yasa shi d’an yamutse fuska, tare da komar da kansa ya kwanta.

Sanin da sukayi cewa Koda lafiyarsa, bayason yawan surutu, bare kuma yanzu da bashi da cikakken lafiya ne, yasa su mik’ewa tare dayi masa Allah ya sauwake, kana duk suka fice daga cikin dakin, Dan ayanayin da suka gansa kamar ma bacci yakeson yi.

Atare suka sauk’o k’asa dukansu.

Anan cikin falon suka zauna, inda Dr Sulaiman ya d’ago kansa ya kalli Mamy.

Cikin girmamawa yace.

“Mamy akwai wasu magunguna dana kawowa Rayyern, To amma kuma dole akwai buk’atar sai yaci abinci kafun yasha su, saidai kuma na lura kwata kwata Rayyern bayason cin abinci.”

Ajiyar zuciya Mamy ta sauk’e, cikin kuma yanayin sanyi tace.

“To ya zamuyi Sulaiman, kafasan halin Rayyern komai nasa dabanne dana kowa, amma Insha Allah Zamuna kokari akan cin abincinsa.”

Kai Dr Sulaiman din ya jinjina, domin kuwa yasan halin Rayyern din Sarai.

Jannart kuwa dake zaune anan dining table din, ahankali ta ajiye spoon din dake hannunta, tare kuma da d’aukan tissue ta goge bakinta.

Ganin alaman ta kammala cin abincin ne kuma yasa Mamy, kallonta cikin kulawa tace.

“Yauwa Jannart tunda kin kammala cin abincin naki, ga food flask nan d’auka ki kaiwa Rayyern nasa abincin, ki kula dan Allah ki sashi ya d’anci ko kad’anne, sai ki bashi magungunan kinji.”

Mamyn ta k’are maganan cikin sigar kulawan, da tasaka Jannart yin kasa da Kanta.

Ahankali kuma Cikin nutsuwa tace.

“To Mamy.”

Mik’ewa tsaye tayi, tare da gyara mayafin dake jikinta, kana ta d’auki d’an tray ta saka food flask da kuma cups, din da aka gama had’a masa duk breakfast din nasa aciki.

Cikin nutsuwa da kuma d’abi’arta na hankali kaitsaye ta nufi saman.

Ganin tafiyan Jannart dinne kuma, yasa Ramadan d’an gyara zamansa, tare da fuskantar su Abban nasa, cikin tausasawa da kuma yanda yasan zasu fahimcesa yace.

“Alhamdulillah wannan karon ba ayiwa Hamma Rayyern allura ba, saboda likitotin China sun sanja masa magani, wanda iya maganin ya wadatar basai an had’a masa da wannan, alluran mai matukar kashe jikin ba, sun kuma ce typhoid ne ke causing stomach pain din nasa, wanda kuma dama tuntuni munsan cewa akwai cronic typhoid ajikinsa, wanda ayanzu harya fara tab’a masa hanjinsa, shiyasa ma yake yawan sa masa ciwon ciki, amma yanzu likitotin can din sun bamu magunguna wanda, zasu na taimakawa wajen wanke masa hanjin nasa, dama kashe duk wata cuta dake cikinsa,
shiyasa ma suka sallamemu, amma hakan fa bawai yana nufin shikenan bane, sunce akwai yiwuwar dole za’ayi masa aiki, amma Idan anyi dace, magungunan zasu iya wanke duk wani cuta dake damunsa, Insha Allah zai samu sauki, akwai watarana na zuwa da Hamma Rayyern zaiyi bankwana, da wannan ciwon bazai sakeyi ba da Yardar Allah.”

Ajiyar zuciya duk su Abba da Baba Maud’on suka sauk’e, saboda bayanin da Ramadan din yayi musu, yasa sun samu gamsuwa sosai.

Cikin samun nutsuwar zuciya Abba yace.

“Allah yasa Ramadan, Allah Ubangiji ya yayewa Rayyern wannan ciwon, Insha Allah ma basai anyi masa aikin ba nasan zai warke, ai waraka ta Allah ce.”

“Sosai kuwa, da yardar mai duka watarana komai zai wuce, Allah dai ya yaye masa.”
Cewar Baba Maud’o.

Da “Ameen.” Duk suka amsa.

Inda Ramadan kuwa ya gyara zamansa, tare da sake Kallon su Abban nasa murya araunace yace.

“Amma Abba fa Doctors din sun tabbatar mana cewar, harda yawan shan zak’in da yake ma, domin shi zaki kana shansa yana taruwa maka aciki ne, bazai tashi yi maka illa ba kuwa, sai ya samu wani ciwon dazai tashi maka, zai iya had’ewa da wannan ciwon ya cutar dakai, batare da kasan da hakan ba, kuma shi kansa Hamma Rayyern ya sani, amma bansan yaushe ne Hamma Rayyern zai sanja ba, bansan yaushe ne zai daina maida abun zaki abun sonsa ba.”

Shiru duk su Abban sukayi saboda acikinsu babu wanda baisan halin Rayyern dason zaki ba sai dai sun sani laifinsune sune suka rainesa da zaƙin dan yawan soyyaya.

Saidai Abba ya kud’urtawa ransa cewar.

“Insha Allah zai dage tukuru wajen ganin ya raba Rayyern din, da yawan shan zakin da yakeyi.”

Haka dai suka d’an tattauna, kafun daga bisani Abba da Baba Maud’o suka fice, haka shima Dr Sulaiman.


Acan b’angaren Jannart kuwa ahankali, ta murd’a handle din kofar ta shiga bakinta d’auke da sallama.

Kwance yake akan lallausan gadonsa, Yayinda yayi kwanciyarnan irin ta rub da ciki.

Jin sautin muryarta ne kuma yasa shi, lumshe idanunsa dake bud’e.

Ita kuwa Jannart k’arasa shigowa cikin d’akin tayi, tare da ajiye tray din dake hannunta.

D’an Kallon yanda ya bawa kofar shigowa dakin baya tayi, cikin sanyi da kuma tausasa murya tace.

“Ga abincinka nan.”

“Nak’oshi.”
Ya fad’a atakaice saboda ayanzun Sam bayason takura.

“Katashi kaci abinci inji likita.”

Jannart din ta fad’a tana me bud’e food flask din, tare da d’aukan spoon ta zuba Coastarian breakfast dish din, gyara zaman plate din akan table tayi, tare da d’ago da Kanta ta kalleshi.

“Please ka tashi, Mamy ne tace kaci abinci sai kasha magani kaji ko.”

Tayi maganan cikin sanyin murya, da kuma zallan yanayin shagwab’an da ita kanta batasan tayi sa ba.

Idanunsa ya d’an rumtse ahankali, tare kuma da sa hannayensa duka biyu, ya sake matse pillow’n dake kirjinsa.

Kwata-kwata bayason yawan damuwa, bawai kuma dan bayajin yunwa ba, no kawai dai bayason yaga Jannart din akusa dashi har haka ne, musamman ayanzu daya fahimci wani abu, adangane da ita, shine tana da wani special Mood wanda yafahimci ita kanta batasan tana dashi ba tana kuwa yiwa zuciyarsa raraka.

Sake gyara kwanciyarsa yayi, cikin kuma nuna halin ko inkula yace.

“Kije zanci.”

Idanunta ta d’an zubawa faffadan bayansa, tare da kama waist dinta ta rik’e, dama tasan halinsa, ta kuma san cewar bazai tab’a daina wa ba.

“Nifa bawai na wani damu dakai bane, Dan kawai kaga Ina baka attention dina, saboda baka da lafiya ne kawai Malam, baya ga haka me mazaisa nazo wajenka.”

Ta fad’i hakan acikin zuciyarta, tare kuma da murgud’a bakinta gefe.


“Da kika tsuramin ido haka wani abu ne zaki bani? Ko cinyeni danye zakiyi!?”

Rayyern din ya fad’a, batare daya juyo ba.

Saurin kawar da kanta gefe tayi, tare da turo dan karamin bakinta gaba, cikin yanayin Mood din shagwab’a tace.

“Ni ai ba kallonka nake ba kuma ba kai nake kalloba”.

A hankali yace.
“Toh wa kike kallo”.

Baki ta ɗan turo.
“Ni babu”.

Dan gajeren tsaki yaja tare da cewa.
“Mayya”.
Yayi mgnar a hankali so batajiba.
Sai ta d’an kwab’e fuska tare da cewa.
“Kuma ni Mamy ce ta aikoni, Dan Allah katashi mana katashi ka tashhhhhi....”

Ta kare maganar tana slowdown da muryarta.

Hakan kuwa shiya sanya, Rayyern din d’an juyowa akaron farko ya kalleta.

Karab kuwa kyawawan idanunsu suka had’e acikin na juna, da sauri Jannart din ta kawar da kanta gefe.

Shidinma kuma janye kallonsa daga gareta yayi, inda ya sauke ganinsa akan Coastarian breakfast dish din.

Idanunsa ya d’an lumshe akasalance, kuma cikin muryarsa da tayi sanyi yace.

“Give me the water.”

Kallon d’an madaidacin bakinsa dake motsawa tayi, sai kuma Ta kau da kanta, tare da rusunawa ta zuba masa ruwan swan acikin cup.

Mik’a masa ruwan tayi.

Ganin hakanne kuma yasa shi d’an yunk’urowa ya zauna.

Karb’an cup din ruwan yayi, tare dayi masa kurb’i d’aya ya ajiye.

Kyawawan yatsun k’afarta ya zubawa ido, cikin sauk’e numfashi yace.

“Naji zanci amma ki tafi, nima zan iyaci da kaina, banason abunda za’amin wanda baikai zuci ba, dan ni bana son abun zuciya biyu da manufa.”

Ya k’are maganar still yana me Kallon yatsun k’afar nata.

Idanu Jannart din ta d’an tsura masa, saboda har yanzu tana mamakin wasu kalamai da yake yawan jifanta dasu, wanda batasan me hakan suke nufi ba ta dai fahimci tabbas bai yarda da ita bane zarginta yakeyi.

Pink lips dinta ta d’an turo, tare da soma motsasu tana mamul mamul dasu, tamkar dai Wacce takeson fad’an wani abu.

Lips din nata ya kalla, ganin yanda suke motsawa ne kuma yasa shi kauda kansa gefe.

“Da wani k’aramin bakinta kamar na tsuntsu.”

Ya fad’i hakan acikin zuciyarsa, Yayinda afili kuwa idanunsa ya lumshe tare da cewa.
“Zagina kikeyi ko?”.
Da sauri ta zaro ido tare da cewa.
“Ni dai a'a”.
Kana ta juya, tana me wasa da y’an yatsun hannunta ta nufi hanyar fita daga cikin dakin.

Har takai bakin k’ofar d’akin nasa kuma saita tsaya tare da juyowa, cikin sanyi da kuma muryar dake nuna lallashi tace.

“Kaci abincin dan Allah sai kasha magani.”

Batare kuma da ta jira abunda zaice dinba ta fice daga cikin dakin tana mgnar zuci.
“Sherri kayan kolba, wannan ai yafi Yah Junaid neman sababi da hujja wai na zageshi”.

Bayanta yabi da kallo harta fice din.
Idonsa ya lumshe tare da sauke wani irin sassayan numfashi,
Kana a hankali ya buɗe su,
Anutse ya jawo plate din abincin, cikin sanyi da kuma yanayi irin na marassa lafiya, ya soma dan tsakalan abincin.

Baiwani ci sosai ba kuma ya ture plate din gefe, tare da d’aukan tea yasha, bayan yasha tea dinne kuma ya b’alli magungunansa yasha.

Yanasha kuwa ya koma ya kwanta.

Jannart kuwa Koda ta sauk’a k’asa, Bata samu Mamy ba, Riyyam nsra kawai ta samu, da shidinne kuma suka sha hira, kafun daga bisani kowannensu ya tashi ya tafi.


Alhamdulillah yau kwanan su Rayyern, uku da dawowa daga China, Masha Allah kuma ciwon cikin nasa yayi sauki sosai, saidai jikin nasa ne baigama samun karfi ba, har yanzu.

Kulawa kuwa yana samunshi sosai daga wajen ahalin nasa, Abba, Baba Maud’o, Mamy, Ramadan Riyyam, da kuma Dr. Sulaeman harma da Usman P.A duk suna iyaka kokarinsu wajen bashi kulawa, saidai kuma har yanzu bai iyacin abinci sosai.
Wanda kuma hakan al’adarsa ce ta tuntuni.


Yau ne kuma Barrister Kabir da kuma Dr Sajo suka shirya musamman dan zuwa duba Rayyern din.

Koda suka Iso gidan tarba na musamman, Abba da Mamy sukayi musu, bayan sun gaisa dasu Mamy da Jannart ne, Abba yayi musu jagora zuwa part din Rayyern din.

Koda sukaje akwance suka iske shi, duk da cewar bayajin karfin jikinsa, amma daya gansu ya d’an sake sunyi hira.

Yanzun kuma saukowarsu k’asa kenan.

Dr Sajo ne ya kalli Abba, cikin kulawa yace.

“Amma Alhaji Bashir me zai hana baza’a sake maida Rayyern din, hospital ba tunda naga har yanzu jikin nasa bawani karfi sosai.”


Mamy dake zaune acikin falonne, ta d’an gyara zamanta, tare da fuskantar Dr Sajon, cikin bayyana damuwarta tace.

“Ai bawai wani abune matsalar ba, bayason cin abinci ne kwata kwata, komai aka basa sai yace a’a, Koda an matsa masa kuwa, bai wuce yayi loma biyu ko uku ba, sai yace ya koshi, bashi da wani abinci sai tea, nan ma yanzu ne yake d’an shan tea din da madara, da bayason ko madaran saidai empty, shiyasa bayi da karfin jiki.”

Kai Dr Sajo ya jinjina, cikin gamsuwa yace.

“Eh to kin san dama duk inda dan adam yayi ciwo abinci yake fara tsana.
Tabbas kuwa bazai samu wadataccen karfin jiki ba, harsai in ya dage da cin abinci, amma ana tambayansa ko yana da buk’atar wani abu, sai anayi masa.”

“To.”
Mamyn tace.

Yayinda Abba kuwa cewa yayi.

“Idan naga abun nasa yaki karewa ai, dolensa na daukesa na maidashi hospital, yasan duk wani illar rashin cin abinci, amatsayinsa na Dr amma baya kiyayewa.”

“Hakane kam sai hakuri da majinyaci, Allah dai ya bashi lafiya.”

Cewar Barrister Kabir.

Da “Ameen.” Duk suka amsa.

Basu wani jima ba kuma, Abba yayi musu rakiya suka tafi.

Bayan suntafi dinne kuma Mamy ta haura saman.

Azaune tasa meshi yasaka Laptop d’insa agaba, yana Dan lallatsata.

“Rayyern.”
Mamy takira sunansa da kulawa.

Jin sautin muryar Mamyn nasa ne kuma yasashi d’ago kansa Ahankali ya kalleta.

“Na’am Mamy.”
Ya amsa adan kasalance.

Karasa shigowa cikin dakin Mamyn tayi, tare da matsowa kusa dashi, cikin kulawa da kuma nuna tausayawa agareshi tace.

“Meyasa ne haka Babana? Meyasa kwata kwata bakason cin abinci? kasani fa bazaka samu isashshen karfi ba, har sai inkana cin abinci, yanzu fad’amin mekakeson ci, ko meye saina dafa maka.”

Fuskarsa yad’an kwabe tare da marairaicewa.

Cikin yanayin sakalci yace.

“Nifa Mamy bana sha’awan komai, kawai dai abincin yanzunne baya min, nafison abu me d’an melting da kuma tsami, like Chinese dishes dai, ko Mamy amin irin kunun ranan.”

Ya k’are maganan yana langwabar da kansa gefe.

Murmushi Mamy tayi tare da cewa.

“To za’ayi maka kunun kaji kada ka damu.”

Mamyn ta fad’a tare da juyawa ta fice daga cikin dakin.

Direct kasa Mamyn ta sauk’o, inda ta samu Jannart ta gaya mata, cewar Rayyern yana son ayi masa irin kunun ranar.

“To.” Jannart din tace, babu musu kuwa ta wuce kitchine, Anutse ta soma had’a kunun kamar yanda ya buk’ata.

Tsab ta gama had’a kunun, da yayi kyau sai tashin kamshi yake, juye kunun acikin flask tayi, tare da daura flask din akan tray ta daura cups agefe, sai kuma madara da zuma wanda suke cikin wani abu mai kaman glass.

Fitowa falo tayi rike da tray din ahannunta.

Mamy dake zaune afalon kuwa Ganin Jannart din harta kammala ne yasa, cikin jin dadi tace.

“Masha Allah Jannart har kin kammala, Allah Dai yayi miki albarka, ki kai masa nasan yana nan yana jira.”

Murmushi Jannart din tayi, tare kuma da dan sunkuyar da kanta, cikin nutsuwa ta nufi saman.

Tafiya take Ahankali, Yayinda tayi kyau cikin riga da wandon pallazon dake jikinta, wanda ta yafa mayafi. Dan babba akan shigar nata, saidai duk da hakan ga wanda yayi mata Kallon k’urulla, tsab zai iya hango tsararren cikakken hips dinta.

Ga kuma rigar shirt din da yayi mata cibcib ajikinta, cikin tan nan alafe yake, tamkar babu hanji acikinsa.

Karasowa bakin kofar falon nasa da tayi ne kuma yasa ta, tura kofar ahankali, bakinta dauke da sallama ta kutsa kanta ciki.

Babu kowa acikin falon hakane yasa ta nufi, Bedroom nashi,
a hankali ta tura ƙofar tare da sallama a bakinta.
Still nan ɗin ma babu shi,
Cikin mamaki ta ɗan ware idanunta tare da jujjuya kanta, tana mai kasa kunne wai ko zata jiyo mostinsa a Bathroom,
jin shirune ba motsin komai, harta nufi kofar dakin dan fitowa falon nasa ne kuma, saita hangosa zaune acikin wani balcony wanda labulayensa keta kaduwa saboda iska.

Kaitsaye wajen ta nufa tana isa wajen kuwa, idanunta suka sauka akansa.
Da sauri tayi kasa da kanta, saboda ganinsa ahaka da tayi, domin yau dinma ba wani kayan kirki bane ajikinsa, singlet ne da kuma gajeren wando.

Shikuwa Rayyern jin sallamanta ne yasashi dago kansa, ya sauke idanunsa akanta.

Tashin farko kuwa idanunsa suka sauka, akan lafaffen cikinta, wanda ta daure kasansa da adon igiyan wandon dake jikinta.

Janye idanunsa yayi daga Kallon nata, tare da maida kallonsa gefe.

Anutse ta karasa isowa inda yake, tare da Dan dukawa ta ajiye tray din dake hannunta.

Cup ta d’auka tare da zuba masa kunun, kana ta saka masa madara da zuma aciki.

D’an d’agowa da kanta tayi, hade da mik’a masa cup din.

Cikin sanyi tace.

“Gashi.”

Tayi maganan tana me sauke idanunta, akan lallausan beard d’insa. Wanda yake matukar yi mata kyau.

Ahankali ya juyo da kallonsa zuwa gareta, lokaci daya kuma ya sauke idanunsa akan kyakkyawar fuskarta, da kuma dan karamin lips dinta, dake shining din lipgloss.

Hannunsa yasa ya karb’i cup din, Ahankali kuma ya dan motsa lips d’insa, saidai kuma ita kanta bataji mai ya fad’a ba.

Kan Wani had’add’en rug dake gefensa ta zauna, tare kuma da rike flask din ahannunta.

Saurin kallonta yayi, saboda baiyi tunanin zama zatayi ba, kamar zaice wani abu kuma sai ya fasa,Ahankali kuma ya janye idanunsa da suka sauka akan waist dinta.

Cikin nutsuwa ya soma sipping kunun, yana me lumshe idanunsa saboda yanda yakejin dadin kunun.

Itakuwa Jannart gaba daya kallonta ta mayar k’asa, inda take hango Riyyam-nsra da Baba Maud’o wayanda suke zaune abakin gate.

Kallonsu takeyi sosai, musamman ayanzu da taga Riyyam din na waya, ba tare da taga ya jima yana wayan ba kuma ya mikawa Baba Maud’o.

Hannayenta duka biyu ta had’e tana kallonsu.

Yayinda acan kasan kuwa.

Mammy ce takira tana tambayan Riyyam din jikin Rayyern .

Nan Riyyam din yake shaida mata cewar jikin da sauki, Koda ta nemi ta gaisa da Rayyern dinne kuma, Riyyam yake sanar mata cewa, baya kusa da Hamma Rayyern din, ananne kuma Riyyam din yace.

“Mammy Ina tare da Baba Maud’o bari na bashi ku gaisa.”

“To.” Mammyn tace.

Yayinda Riyyam-nsra kuwa ya mikawa Baba Maud’o wayar.

Karb’an wayan Baba Maud’o yayi tare kuma da karata akan kunnensa, Cikin nutsuwa yace.

“Assalamu Alaikum.”


Acan Ethiopian kuwa Mammy dake zaune akan kujera, Jin amo da kuma sautin muryar daya daki dodon kunnenta ne, yasa taji zuciyarta tayi wani irin bugawa, take kuma tsikar jikinta suka shiga wani irin mimmikewa, cikin wani irin yanayi ta mik’e tsaye, tare da sake sauraran muryar dake kan wayar.


“Assalamu Alaikum.”

Baba Maud’o ya sake maimaita sallaman nasan, saboda Jin shiru da yayi.

Komawa Mamyn tayi ta zauna, tare kuma da sanya hannu ta dafe kirjinta, cikin rawar murya tace.

“Wa’alaikassama.”

Zumbur haka Baba Maud’o ya mik’e tsaye daga zaunen da yake, tare kuma da d’an zazzaro idanunsa waje, lokaci daya wani irin yanayi ya bayyana atattare da Baba Maud’on.

Wanda hakan yasa Riyyam dake zaune kallon Baba Maud’on, Cikin yanayin mamaki yace.

“Baba Maud’o lafiya?”

Kallonsa Baba Maud’on yayi, tare kuma da komawa Ahankali ya zauna, saidai kuma har yanzu jikinsa bai daina tsuma ba.

Daga can b’angaren kuwa cikin rawar murya Mammy tace.

“Ina wuni, ya maijiki?”


Hannu Baba Maud’on ya d’an dunkule cikin wani irin abu dake dukan zuciyarsa yace.

“Lafiya mai jiki kuma Alhamdulillah.”


“Masha Allah Allah ya kara sauki, mungode sosai Baba Maud’o nasan kuna nan kuna fama da rigiman Riyyam, Allah ya bada lada.”

Mammyn ta fad’a cikin sanyin murya.

Baba Maud’o kuwa murmushi ya aro ya sakawa muryarsa, kana shima cikin sanyi yace.

“Ameen summa Ameen, ai Riyyam kam babu wani rigiman da yake yi mana, harma mun saba dashi kwannan yana ta cewa kin matsa ya komo mu kuma bamu son rabuwa dashi.”

Murmushi Mammyn tayi, cikin kuma karfin hali da danne bugun zuciyar da takeji, tace.

“Shikenan to Baba Maud’o ahuta gajiya.”

“Yauwa.”
Baba Maud’on ya amsa, tare da

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login