Showing 87001 words to 90000 words out of 104589 words

Chapter 30 - Tubali Book 2 Hausa Novel Complete

Unknown   

21 Dec 2024

182

karasawa gaban dressing mirrorn ta, inda yaga wani cup ajiye agefe.
Lek’a Cikin kofin yayi wanda yake dauke da zuma.

Juyowa yayi ya kalleta, hakan ne kuwa yasa da sauri tayi kasa da kanta tana murza yatsun hannunta.

“Meye kike wani sunkuyar dakai, sai kace kinga Dodo.”

Kanta ta girgiza masa alaman “A’a.”
Still batare kuma da ta dago Kanta ta kalleshi ba.

Shikuwa Rayyern idanunsa ya cigaba da tsura mata, Ahankali kuma ya matso kusa da ita, tare dasa hannunsa acikin aljihun wandon sa, cikin tsareta da idanu yace.

“Meyasa bakya cin abinci, tell me mekike ci Janna?”

Kanta ta girgiza masa alaman “Babu.”
Still kuma bata dago ta kalleshi ba, haka kuma bata motsa labb’an bakinta ba.

Shikuwa Rayyern Ganin hakan ne yasa shi, bata fuska cikin tsare gida yace.

“Almost 2days baki ci abinci ba, meyasa ahaka kikeson kina rayuwa, bakisan cewar rashin cin abinci, yana haifar da Ulcer ba?”.

Saurin dan satan kallonsa tayi, saboda Jin abunda ya fada din, kasancewar tasan halinsa shine ma gwani wajen Kin cin abinci.
Amma wai yanzu da bakinsa yake fadin hakan.

Fuska tadan kwabe ashagwab’e kuma cikin narkar da murya tace.

“Nifa banason abincin ne, bayamin dadi kuma nace maka ka saya mana kayan provision amma kaki..”

Ta kare maganan tana me tura bakinta gaba.

Wanda hakan yasa shi dan lumshe idanunsa, ahankali yace.

“To kenan idan bake kika dafa abincin ba, bazaki ci ba?”

Sake kwabe fuska tayi, still a raunace tace.

“Ni fa yanzu ma yunwa nakeji sosai, kuma ni banason wancan abincin.”

Idanunsa yadan zuba mata, Cikin yanayin nazartar ta yace.

“Okay wani kalan abinci kikeso?”

“Nigerian Dishes nakeso, ba irin way’anda kake kawowa ba.”

Ta fada tana me karyar da wuyanta gefe.

“Nigerian dishes? a Mascow dinne zaki samu Nigerian dishes? like bakisan awacce k’asa kike ba ko?”

Yayi maganan yana me kallonta, Domin har yanzu idanunsa na gane masa saman breast dinta dake waje da nimples ɗin ta da suke tsaye cas.

Jannart kuwa Jin abunda ya fad’a dinne, yasa ta kwab’e fuska tare da yin rau rau da Idanunta.

“Alright Oya taso mu tafi.”

Rayyern din ya fad’a, yana me duba agogon dake daure atsintsiyar hannunta.

Itakuwa jin abunda yace dinne yasa ta tashi ta tsaya.

Kallonta ya somayi daga sama har kasa, inda take sanya da dogon wandon pencil jeans, sai kuma t-shirt mai fadin wuya, akanta kuwa hulan sanyi ne, sai kuma kafarta da ta sawa safa.

D’an soma Kallon dakin yayi, inda ya sauke idanunsa, akan wani shararan riga mai kaman abaya dake gefen gadonta.

Daukan rigan yayi tare da mika mata.

“Idan kinsa ki sameni a falo.”

Ya fadi haka yana me juyawa ya fice daga dakin.

Jannart kuwa jin hakanne yasa ta saka riga mai kaman abayan, tare da daukan wani karamin vail ta yane kanta dashi.

Cikin dan sauri ta saka wasu takalma sau ciki akafanta, wayarta ta dauka batare kuma da b’ata lokaci ba, ta rufa masa baya.


Koda ta fito falon hanyan waje taga ya nufa, wanda hakan yasa ta d’an tsayawa cikin sanyi tace.

“Naan Ina zamuje?”

“Restaurant.”
Ya fada atakaice batare kuma daya juyo ya kalleta ba.

Itakuwa jin hakanne yasa ta gyara mayafin jikinta, cike dajin dadin fitar da zatayi a karo na forko tunda suka zo, ta rufa masa baya, Dan hakanan sai taji wani farinciki, saboda tun da suka zo Mascow din bata fita ba ko sau daya.

Koda suka karaso wajen motar tasa, cikin zumudi ta bud’e murfin motar ta shiga.

Shi kansa Rayyern ya lura da irin farincikin da take ciki, wanda hakan yasa shi jin wani irin abu a Cikin zuciyarsa.

Yana shiga cikin motar ya tada ita kaitsaye suka fice daga Cikin gidan.

Suna hawa kan titi ne kuma karamar wayar tasa dake hannunta ta soma kara, Ganin sunan Riyyam-nsra na yawo akan screen din wayar ne kuma, yasa ta d’agawa tare da kara wayar akan kunnenta.

Daga can b’angaren Riyyam-nsra din yace.

“My Aunty dazu muna waya dake kika katse lafiya kuwa?”.

Murmushi tayi cikin kuma kasa boye farin cikinta tace.

“Sorry Riyyam Hamma ne yake kirana zamu fita shiyasa na katse.”

Murmushi Riyyam-nsra din yayi, cikin jin dadi yace.

“Ahh Lallai To sai kun dawo.”

Yana gama fadin haka ya kashe wayan.

Ita kuwa Jannart juyowa tayi ta ɗan kalleshi a hankali tace.
“Naan”.
Shima ɗin juyowan yayi ya ɗan kalleta, tare da cewa.
“Na'am Janna”.
Cikin yanayin sanyi tace.
“Uhum dama akwai sakon da aka iko min ne daga Nigeria”.
Da sauri yace.
“Saƙon me kuma A wurin waye?”.
Gyara zama tayi tare da cewa.
“Magungunan sanyine da turaruka Aunty na ta aiko min, sabida ciwona kuma da yanayin sanyin garin”.
A nitse yace.
“Toh zamu amsoshi”.
Wayarta ɗago tare da cewa.
“Sai dai in kira Aunty Rabi'atu sai kuyi mgn ta gaya maka inda take, muje ko”.
Kai gyaɗa mata, yana mai kallon titin,
ita kuwa da sauri ta kira Hajia Rabi'ah kana ta bashi waya,
a mutunce suka gaisa kana tayi mishi kwatancen masauƙin.
Miƙa mata wayar yayi tare da cewa.
“Mu fara zuwa can dan muna kusa da inda suken.”.
Haka kuwa akayi tafiyar 13mnt sukayi suka riski gidan.
Mutunce aka tarbesu.
ganin kamar sauri sukeyine yasa ta ɗauko kayan ta bata, kana ta rakosu har wurin mota.
A sit ɗin baya ta ajiye katon ɗin tare da shiga gaba, kana yaja mota suka tafi.
Tafi kaɗan suka iso wani babban wajen shak’atawa Victory park wuri mai masifar kyau da kayan k’awa.

Parking motar yayi ya fita, jim kadan kuma sai gashi ya dawo hannayensa rike da robobin ice cream.

Gyara zamansa yayi, tare da ɗan juyowa ya kalli fuskarta mai kewaye da yanayin ta na sanyin rauni,
Mik’a mata yayi tare da cewa.
“Kina sha?!”.
Da sauri ta gyaɗa mishi kanta,
Tare da miƙo hannunta ta kama rubar, a hankali ya d’an kauda idanunsa tare da sa yatsunshi kan nata ya manna a jikin robar mai masifar sanyi.
“Sheyyyhhhhh”.
Taja wani irin dogon sauti sabida masifar sanyin da taji yana ratsa yatsunta.
Shi kuwa Rayyern wani irin yar-yar haka yaji tsikar jikinsa na zubawa sabida sautin da taja ya gigita masa kwanya,

“Ahshhhhy Naan sanyi”.
Ta faɗa cikin wata iriyar sassayar murya”.

Juyo da kanshi yayi ya fuskanceta tare da jingina kan nasa jikin kujera.
A hankali ya turo harshensa waje kad’an ya d'am laso lips ɗinshi, still bai sake mata hannunba,
Cikin wata iriyar fitinenneyar murya yace.
“Kin cika raki sanyi nefa ba zafiba”.
Yayi mgnar yana tsareta da narkakkun idanunsa.
Rau-rau tayi tare da kwaɓe fuska.
Ƙara matse hannunta yayi.
“Ahsssshyyy Naan zafeeeeeh!”.
Ta kuma sakin ƙara da ɗan ƙarfi.
Bakinshi ya ɗan tura tare da cewa.
“Raki ki koyi juriya da kame bakin nan da iface-iface kada wata rana kiyi abin kunya,”.ya ƙare mgnar tare da
Sake hannun nata kana ya sa hannun kan siterin motar, sannan ya kifa kansa bisa tafukan hannunsa yayi shiru yana maijin wani irin masifeffen abu akanta ji yake tamkar ya ruggume ta ko zaiji sanyin abin.

Itama shiru tayi tana hurawa yatsunta dumin bakinta,
Shi kuwa Rayyern wasu tagwayen numfarfashin yake sauƙewa a hankali,
Kusan 56 second suka d’auka a haka
Kana ya gyara zamanshi Tare kuma da tada motar suka kara gaba.

Itakuwa Jannart duk da tasan bata wani shan sanyi sosai, amma tana matukar son ice cream sosai.
Ga kuma yunwan da takeji, shiyasa batare da wani tsawaita tunani ba akan illar da zai iya mata ta soma shan ice cream din tanasha tana lumshe ido, shi kuwa Rayyern a fakaice yake kallonta.

Ahaka har suka isa wani babban wurin cin abinci Russian pub restaurant wurine da akeji dashi a ƙasar wanda mutanen k'asashe ma banbanta ke zuwa shiyasa mafi akasari akwai abincin kasashe daban-daban ɗan wuri yafi kowanne girma acikin garin na Mascow.

Suna isa kuwa ya bud’e murfin motar ya fito, Ganin hakanne kuma yasa Jannart din fitowa itama.

Kaitsaye suka nufi cikin restaurant din.

Koda suka je Ab’angaren daya kasance na musamman suka zauna.

Daya daga cikin Waiters na restaurant din ne ya kawo musu menu.

Rayyern kuwa Kasancewar baya bukatar abincin ne, yasa shi mikawa Jannart din menu.

Duk da cewar bata ga Nigerian dishes acikin jadawalin abincin ba, amma ta zab’i abunda take Ganin zata iya ci.

Take kuwa aka kawo mata abunda ta buk’a din.
Nan aka jera mata abubuwan da ta zaɓa,

Shi kuwa Rayyern gyara zamanshi yayi tare da d’an fesar da numfashin cikin zuba mata narkakkun idanunsa yace.
“Kici”.
Jin abinda yacene, da kuma yunwar dake zaƙularta yasa ta sa hannu ta dauki spoon tare da gyara zama kana ta fara ci.
Yanayi tana kallon can woje kasan cewar akwai glasss mai ruwan garai-garai.
Kana iya ganin waje.

Rayyern kuwa Ganin ta soma cin abincin ne, yasa shi mikewa.
“Naan!”.
Tace ganin ya juya zai tafi,
Juyowa yayi ya dan kalleta,
Kanshi ya jinjina ganin kallon tambayar ina zakaje takeyi masane yasashi cewa.
“Kici ina zuwa zan d’an shiga cikin Mall d'in nanne”.
Kai ta gyaɗa mishi cikin gamsuwa.
Shi kuwa kaitsaye ya nufi mall din dake cikin restaurant din.


Jannart kuwa da idanu ta bisa, kana kuma taci gaba da cin abincinta yanayi tana d’an lallatsa wayarta.

Dai-dai lokacinne kuma Azeez ya shigo cikin restaurant din, yana shigowa Cikin wajen daya kasance VIP ya
Zauma kujerar dage can gefenta wanda shima da glasss a tsakaninsu,
Bayan an kawo mishi abinda yake buƙata ne kuma ya ɗan fara ci,
Loma biyu ana uku ya ɗan ɗago kansa dan jin alamun akwai mutun gefensa, ai kuwa idanunsa sauka akan ta.

Cikin wani irin tsananin mamaki, kaɗuwa, al'ajabi ya zaro Idanunsa waje cike da tsananin mamaki hadi da firgici ya mik’e tsaye, jiki na rawa ya ya soma nufo inda take zaune.
Saboda yana son ya tabbatar da cewa, idanunsa bawai gizo sukeyi masa ba.

Aikuwa isowar sa wajen ya tabbatar masa da cewar, bawai gizo idanunsa keyi masa ba.

Wannan dalilin yasa cikin tashin hankali da kuma firgici da tarin mamaki yace.

“JANNART.”

Da sauri Jannart din ta juyo saboda Jin muryar ɗan uwanta Yah Azeez d'in tayi acikin kunnuwanta.

Aikuwa tamkar ba zata haka taga Yayan nata tsaye akanta.
Da wani irin sauri ta Mike tsaye baki na rawa tace.
“Laah Yah Azeez”.
batare da ta jirayi komai ba kuma ta fad’a jikinsa.

Tare da rungume sa kam kam cike da tsananin Jin dadi kuma tace.

“Yah Azeez.”

Rungume ta sosai Yah Azeez din yayi sabida ganin abin yake tamkar a mafarki shiyasa ya ruggumeta gam dan ya tabbar ido biyune.

Dai-dai lokacin kuma Rayyern ya fito daga mall din, fitowar tasa kuwa tayi dai-dai da rungumetada Azeez din yayi.
Atake kuwa idanunsa ya sauka akansu cikin wani irin....!
By
*GARKUWAR FULANI*Idanun nasa ya zazzaro waje cikin kuma yanayin tsantsar mamaki, yake Kallon Jannart din wanda take rungume akirjin wani Namiji wanda baimasan dashi ba.

Lokaci daya kuma cikin few second yaji wasu irin abubuwa na yawo acikin brain d’insa, zuciyarsa kuwa wani irin zafi takeyi tamkar Wacce aka hurawa wuta.
Ransa yakai kololuwar b’aci musamman tunawa da yayi, cewar akwai igiyar aurensa akanta wani irin abu mai masifar ɗaci yaji ya tokari ƙahon zuciyarsa.

Jannart kuwa da tsananin farinciki ya cika zuciyarta, sake rungume Yayan nata tayi, Yayinda takejin wani irin nutsuwa da dadi acikin zuciyarta.

Yah Azeez din kuwa ahankali ya tallab’o kanta, muryarsa adan raunace, da kuma tsananin mamakin ganinta ak’asar da yayi yace.

“Jannart kece? I can believe inajin har yanzu kaman mafarki nakeyi.”

Sake rungumeshi sosai Jannart din tayi, cike da matsanancin farincikin da take ciki kuma tace.

“Nice Yah Azeez bawai mafarki kakeyi ba, nayi kewarku sosai, Nayi kewarka Yah Azeez.”
Ta kare maganan cikin rawan murya, tare da jin wasu irin hawaye na kokarin, cika Idanunta.

Yah Azeez kuwa Ganin hakanne yasa shi, tallafo hab’arta tare da Kallon fuskarta, bakinsa dauke da tarin tambayoyi yace.

“Jannart Meya kawoki Mascow? Jannart ke dawaye kukazo? Meyasa kikabar gida Jannart Meyasa? Kowa yana cewa kin b’ata hankalin su Daddy duk atashe yake akanki? Jannart wa ya kawoki k’asarnan???”

Yah Azeez din yayi mata duka tambayoyin, cikin tsananin damuwa da kuma wani tarin fargaba, saboda bayason ya yarda da abunda zuciyarsa ke fada masa, cewar Jannart din guduwa tayi ko ta biyo saurayine.

Dai-dai lokacin kuma Rayyern dake tsaye, wanda zuwa yanzu ya gama cika fam, zuciyarsa tafasa take sosai, Yayinda ransa kuwa yayi masifar b’aci idanunsa har rufewa sukeyi, ahasale kuma cikin takaici ya soma takowa zuwa inda suke.

Jannart kuwa jin tambayoyin da Yah Azeez din keyi mata ne, yasa ta dago idanunsa da suka cika da k’walla ta kalleshi, bud’e bakinta da niyar yin magana da tayi, yayi dai-dai da isowar Rayyern wajen.

Ransa amatukar b’ace yasa hannunsa d’aya ya damko Jannart din, tare da janye ta ajikin Azeez, ahasale kuma cikin fad’a, da b’acin rai ya saka hannunsa d'aya akan kirjin Azeez ya turesa gefe.

Cikin bayyana tsananin b’acin ransa, ya watsawa Azeez din wani irin mugun kallon da yasa hantar cikin Azeez kad'awa.
Taune lip d'insa na k'asa yayi tare da nuna masa yatsa afad’ace yace.

“You’re very stupid man, waye kai da zaka zo ka rike min matata haka? I say Who are you?”
Ya k’are mgnar da karfi cike da hautsinewar tunani.
Idanu Yah Azeez ya zubawa Rayyern din, wanda yafi yi masa kama balarabe, saidai jin yayi Hausa ne yasa shi kankance idanunsa, shima ransa ad’an b’ace yace.

“Bakai zaka tambayeni ni waye ba, ni zan tambayeka ko kai waye, akan meye zaka zo ka tureni haka? Kasan ko ita din wacece awajena, waye kai meye kai sannan akan meya zaka janye ta daga gareni, meye alak’arka da ita da har kake cewa matarka wanne ubanne ya aura maka ita!?”.

Wani irin buguwa Jannart taji zuciyarta tayi, saboda ita sai ayanzu ne ma take tunawa, da cewar babu wanda yasan inda take.

A matuk’ar tsorace ta dawo da kallonta ga Yah Azeez, wanda yake jifahta da Kallon tuhuma, Yayinda shi kuwa Rayyern gaba daya ma yanayin fuskarsa ta sanja, idanunsan nan sunyi jajur, haka ma fuskarsa dake bayyana alamun bacin rai.

Wani irin tsorone taji ya kamata, wanda hakan yasa ta rumtse Idanunta.

Rayyern kuwa wani irin hautsinennen kallo ya watsawa Azeez, din Cikin yanayin bacin rai kuma yaja wani irin dogon tsuka, tare da bangaje Azeez din.

“Tamyata kakeyi akan matata mallakina dana biya sadaki aka ɗauka mana aure da cikakkun shaidu kamar yadda musulunci ya tsara, akan matata sirrina kake cemin haka Stupid kawai.”
Ya fad’a in don’t care manner.

Batare dako Kallon Azeez din ya sake ba, ya damke hannun Jannart, tare da janta cikin zafin Rai suka nufi hanyar fita daga restaurant din.

Ganin hakanne kuma yasa Azeez rufa musu baya, cikin tsananin mamaki da rudu yake cewa.

“Hey you stop, ina zaka kaita meye hadinka da ita, da har kakeson guduwa da ita?!!!!”

Yah Azeez din ya fad’a da d’an k’arfi, adai-dai lokacin suka fito daga restaurant din.

Jannart kuwa Ganin idanun Rayyern din sun rufe da b’acin rai ne, yasa ta soma dan jujjuya kanta, cikin muryarta dake fitar da sautin kuka take cewa.

“Naan please leave me, Dan Allah ka tsaya kaji please Naan ka tsaya nayi maka bayani pleaseeeeeee....”

Ta kare maganan cikin tsananin damuwa, tare kuma da dan waiwayawa tana Kallon Yah Azeez dake biyosu.

Sam Rayyern kam kamar ba dashi ma Jannart din take ba, kwata kwata yaki sauraranta, hasalima ji yake tamkar ya fara buga wasan, kwallo da ita awajen tsabar takaici.

Dai-dai lokacin suka iso bakin motarsa, gefen me zaman banza ya bud’e, batare da tunanin ko zataji ciwo ba, ransa amatukar bace ya cillata cikin motar, tare da maida murfin motar ya rufe gib.

Cikin fusata ya juyo ya shige cikin motar shima, tare da yi mata key ahasale ya cillata kan titi.

Ganin hakanne kuma yasa ran Aziz sake b’aci, afusace shima ya tafi da gudu ya shiga tasa motar Dan rufa musu baya, saidai kafun ma ya tada nasa motar har sun hau kan titi.

Tuni kuma wasu motoci sunsha gabansa, wanda hakan yasa motar su Rayyern din yi masa nisa, kasancewar kuma dare ne shiyasa cinkoson ta d’anyi yawa, saidai duk da haka bai dauke idanunsa daga kan, motar Rayyern dinba saboda bayaso su b’ace masa.

Rayyern kuwa wani irin gudu yake shararawa akan titin, tamkar wanda zai tashi sama, wanda kuma daga gani kasan zuciyarsa cike take da bacin rai.

Hakanne kuma yasa ko Kallon Jannart din baiyi ba, wanda taji ciwo a hannunta sanadiyar wurgata acikin motar da yayi.

Jannart kuwa gaba daya duk ta rud’e, Yayinda hawaye ke gangara akan fuskarta.
Cikin tsananin damuwa da kuma magiya take cewa.

“PLEASE Naan dan Allah ka tsaya, kaji D’an uwa.........”

“Shut up, ki rufemin baki ko na tattaki acikin motar nan zaki tsaya da aurena a kanki kina ruggume ko wani Tom and Jerry d'in!!! In ruggumar kikeso ki gaya min Mana in ruggumeki ko na hanaki ruggumeni ne!!!!”.

Ya katseta ta hanyar fadin haka atsawace.

Tsawar da ya haifar mata da kad’awan yayan hanji, da kuma wani irin fad’uwar gaba, saboda tunda take dashi yaune kawai, taji yayi irin wannan tsawan, ga kuma wata irin murya da yayi mata magana dashi, mai saka mutum firgicewa.

Numfashinta dake kokarin k’wacewa, saboda tsawan da yayi mata din ta fusgo, lokaci daya kuma taji wani irin matsanancin kuka, na taso mata.

Hakanne kuma yasa ta manna kanta da jikin glass din window’n motar, asanyaye ta saki wani marayan kuka, wanda ita kanta batasan kukan na meye bane, na tsoron Rayyern dinne ko kuma na jimamin ganin Yah Azeez dinta ne, itama bata sani ba.

Kasancewar kuma glass din windown b’angaren da take zaune, yana d’an sauk’e ne yasa duk wani snow da akeyi, yake busata Yayinda dusan kankara keta saukowa ajikinta.

Rayyern kuwa duk da yana iya jiyo sautin tashin kukanta, amma haka yayi banza da ita, saima gudu daya ci gaba dayi tamkar wanda zai tashi sama.

Suna ahaka dinne kuma taga ya kama wata hanya ta daban, ba hanyar da suka biyo ba, domin duk da bata tab’a fitowa ba tunda suka zo, amma tasan inda suke bi yanzun ba hanyar gidansu bane.

Yah Azeez da har yanzu ke biye dasu kuwa, gaba daya awahalce yake tukin, saboda yanda motoci sukayi yawa agabansa, kasancewar tuni su Rayyern din sunyi masa nisa.

Rayyern dake driving kuwa fahimtar Azeez din na biyosu ne, yasa shi shiga wata kwana mai yawan go slow, tafiya sukayi na tsawon 30mn kafun suka iso, gaban wani makeken hotel d’in izmailovo alfa hotel, wanda aka k’awatasa da furanni masu matuk’ar kyau.

Parking motar Rayyern yayi, batare daya jira wani abu ba kuma ya bud’e murfin motar ya fito.

Kaitsaye b’angaren da Jannart din ke zaune ya nufo, bud’e murfin motar yayi, tare da

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login