Showing 42001 words to 45000 words out of 104589 words

Chapter 15 - Tubali Book 2 Hausa Novel Complete

Unknown   

21 Dec 2024

167

a barni”.
Amin
Mamy tace tana fita Kitchen din.
direct sashin Abba ta wuce, Koda taje ta sameshi yana shiryawa.

Zama tayi abakin gadonsa, cikin tausasa murya da kuma bashi girma amatsayinsa na Mijinta tace.

“Dama magana nazo muyi.”

Aje hular hannunsa yayi tare da cewa.
“Ina jinki”.
Cikin zuba mishi ido tace.
“Jannart ce ta sameni wai tanason zuwa bikin bud’e companyn, shine nace bari nazo naji ta bakin ka.”

Kai Abban ya dan jinjina cikin gamsuwa yace.

“To ai ba abundamuwa bane, zata iya binmu saimu tafi tare ko, kice mata ta shirya.”

Dan Murmushi Mamyn tayi, saidai kuma cikin jimami tace.

“Amma Alhaji kamanta cewar zamanta awajenmu sirrine.”

D’an Jim Abban yayi na wasu mintuna kana yace.

“Babu damuwa, zata iyayin shigar da babu wanda zai ganeta, misali ko irin shigar larabawa haka da suke rufe fuska, kinga Idan tayi haka babu wanda zai shaida ta ko!?.”

“Hakane To bari naje na sanar mata.”
Mamyn ta fad’a tana me mik’ewa tsaye.

A kitchen din ta samu Jannart, Cikin kulawa kuma tace mata taje ta shirya, saidai amma tayi shigar da bakowane zai ganeta ba.

Cikin jindadi Jannart din tace.
“To.”
Kasancewar ta kammala aikin da takeyi dinne kuma, yasa kaitsaye ta wuce d’akinta Dan shiryawa.

Acan b’angaren su Ramadan kuwa tsab suka shirya, cikin shigar manyan kaya, shida Riyyam-nsra kayansu iri d’aya Getzner ce orange color mai masifar maiƙo da kyau kalar kayan ya ƙara haska fatarsu saida sukayi wani yellow-yellow.

Bayan sun gama shiryawanne kuma duk suka fito falo.

Dai-dai lokacin kuma Rayyern ya fito daga cikin dakinsa, yayi kyau sosai cikin shigar suit din dake jikinsa Pink guava mai dan ɗigon maroon.
Wanirin sheƙi yakeyi suit din rigar cikin itama maroon hakama net din sa.
Kana ga takalmam toms maroon suma masu masifar kyau da sheki.
Ga kuma wani had’add’en agogon daya saka.
Sosai yayi kyau masifar kyau sajen shin nan ya kwanta lib-lib sai sheƙi sukeyi yan siraran lips ɗinsa jajaye suma suna sheki,
Tattausan sumar kanshi tana kwance lib sai ƙamshi da sheƙi sukeyi.
Wayarsa ce riƙe a hannunsa.
Yana takowa da dan sassarfa,
cikar haiba da kuma kwarjininsa duk sun bayyana.
“Wow Masha Hamma Rayyern kayi masifar kyau”.
Cewar Ramadan yayinda tuni Riyyam-nsra kuma yaketa daukansu hoto.

Haka suka rankayo zuwa falo, yana gaba Suna biye dashi abaya.

Koda suka sauk’o k’asa afalo suka samu Mamy.
Sai kuma Abba, Dr. Sulaiman, da kuma Usman P.A, duk sun shirya sauk’owan su Rayyern din kawai suke jira.

“Abba mutafi time yana kurewa.”
Rayyern din ya fad’a yana me duba agogon hannunsa.

Kai Abba Ya jinjina, tare da Kallon Mamy Cikin kulawa yace.

“Kira Jannart.”

“To” Mamyn tace, saidai batakai ga mikewa ba, Jannart din ta bud’e kofar falon ta ta fito.

Sanye take da doguwar riga maroon colour, Wacce aka k’awata jikinta da adon fararen duwatsu shuwariski.

Rigar irin abaya masu fad’innan ne, da tayiwa jikinta matukar kyau, sai kuma babban mayafin da ta saka akanta, wanda kuma ta nad’ashi har akan fuskarta, kamar dai yanda larabawa keyi, hakan kuwa shiyasa idanunta kawai ake iya gani.

Bak’aramin kyau tayi ba, domin tafito ne a balarabiya sak, tayi kyau ainun.

Wanda har hakan yasa akaron farko, Rayyern ya kasa d’auke idanunsa daga kanta.
Duk da yaji bakincikin cewar da ita zasu tafi, amma ya yaba da shigar jikin nata ainun.

“Masha Allah Jannart kinyi kyau.”

Mamy ta fad’a cikin yabawa shigar dake jikin Jannart din, saboda shigane na musulunci, da kuma shigane daya boye asalin kamanninta.

Atare duk suka rankaya suka fita, zuwa compound din gidan, inda tsala tsalan motoci suke jiransu.

Wata black Range Rover Rayyern ya shiga, haka ma Abba da Baba Maud’o.

Su Ramadan da Riyyam-nsra kuwa motocinsu daban, Yayinda Mamy da Jannart ma suka shiga nasu motar.
Haka Usman P.A da Dr Sulaiman.
Convoy motocin nasu sukayi, ahaka har suka isa cikin babban kamfanin. Daya amsa sunansa kamfani.

Jama’a da kuma yan jaridune cike awajen, bayan su Rayyern din sun isone kuma, wajen ya dinke da sowa.

Haka dai suka karasa wajen zama na musamman suka zauna, sosai Jannart ta yaba da tsarin kamfanin. Domin tayi imani ko kamfanin Dadynta bai kai wannan ba.

Taro akayi mai tsabta bayan kowa yaci yasha ne kuma, aka bude companyn.

Yan Jarida kam sun samu abunda sukeso, musamman da suka ga yanda Rayyern yasa, wasu daga cikin ma’aikatan kamfanin, suka cika motoci da kayan provision, inda ya bada umarnin, akai kowacce mota ta abinci, gidan yari, da gidan Marayu, sauran motocin kuma yace rabawa gajiyayyu.
Ai kuwa hakan da yayi ya daki zuciyar mutane da yawa, hakan yasa yan jarida suka kara kaimi wajen shooting.

Alhamdulillah anyi taro lafiya, inda taron ya samu halartar manyan baki, yan kasuwa shareholders mata da maza suke ta zuwa, kowa yanaso ya zuba hannun jarinsa a kamfanin.
Bayan duk Jama’an dake wajen sun watse ne kuma, suka tattara duk suka koma gida.
Zuwa lokacin kuwa har dare ya soma yi, wannan yasa agajiye dukansu suka koma gida.

Washegari Saturday still a busy suka tashi, musamman Rayyern.

Yayinda Riyyam-nsra kuwa keta shirye shiryen, komawarsa Ethiopia.
Saboda ranan Monday Insha Allah zai tafi.

Acikin yan kwanakin kuma duk cikin hidima suke, saboda mutane daban daban da suke zuwa gidan su Rayyern din Taya murna yayinda shi kuwa Rayyern yanzu bai samun zuwa asibiti ma, a Company yake wuni kullum sabida yana son dai-dai ta komai ta yadda in ya tafi ta online zaci gaba da aiyukansa wasu kuwa ya mikasu ga MD.

Kasancewar yau Lahadi ne kuma yasa, Riyyam-nsra shiryawa yaje gidansu Naseer.

Hira sukayi sosai da Naseer din kafun daga bisani yayiwa, Umman Naseer din sallama, daga nan kuma gidan Malam Mai-nasara suka wuce.

Bayan sunyi masa sallama ne kuma, suka dawo nan gidan su Rayyern din.

Hira suka sha sosai, duk da cewar zuciyarsu babu dadi, saboda sunsan zasu yi kewar Riyyam din sosai.

Washegari Monday kuwa, k’arfe 8 dai-dai jirgin su Riyyam din zai tashi.

Duk yau din haka suka tashi babu dadi, saboda shakuwar dake tsakaninsu more Especially Ramadan da yayi zugum,
dan har wani ciwon kai yakeji, saboda tafiyar Riyyam-nsra din.

Haka ma Jannart.

K’arfe 7:50 am dai-dai kuwa Abba, Baba Maud’o, Rayyern da kuma Ramadan suka rakashi airport, cike da kewarsa, kyautttuka kuwa babu irin wanda basu bashi ba, domin Rayyern ma ba k’aramin kud’i yayiwa Riyyam-nsra din transfer ba.

Jannart kuwa har snacks tayi masa, tare da basa kyautan wani Apple Watch dinta mai kyau.

Sosai yayi musu godiya da irin karamcin da suka nuna masa, Koda yazo shiga jirgi,
Ruggume Ramadan yayi sai ga hawaye shar-shar a idanunsa
Cikin rawar murya yace.
“Hamma Ramadan azanzo aurenka”.
Cikin rawan murya Ramadan yace.
“Zanyi kewarka Riyyam-nsra inaji ba dadi tamkar zan rabu da rabin jikina nakeji”.
Da sauri Baba Mauɗo ya juya musu baya yana maijin wasu irin zafafan hawaye na tsastsafo mishi.
A hakan yaji Riyyam-nsra ya ruggumeshi ta baya kawai sai yaji hawayen sun silalo mishi.
“Allah sarki Baba Mauɗona zanyi kewarka”.
Ina ya kasa mgn domin in yayi mgn zasu gane yana kuka.
Cikin rauni Rayyern ya ɗan kamo hannunsa tare da cewa.
“Toh Riyyam-nsra mu zauna kawai mana”.
Da sauri ya sharce hawayen sa tare da juyawa gaban Abba ya ruggumeshi yana cewa.
“Mammay na nake son gani da kai mata sakonta amman in sha Allah nan kusa zan dawo”.
Daga nan ya juya ya nufi wurin shiga jirgin
Yana zubda k’walla tare da daga musu hannu, aransa yakejin zaiyi kewarsu sosai.
Saidai kuma yasani cewa.
Lallai watarana zai dawo, zai dawo ya zauna acikinsu, zama kuma na musamman bawai irin wanda sukayi ayanzun ba.

K’’arfe 8 dai-dai jirgin su Riyyam-nsra din ya d’aga, zuwa k’asar Ethiopia.

Haka su Rayyern din suka dawo gida, jikinsu asanyaye.

Ramadan ne ya zauna akusa da Jannart, cikin sanyi yace.

“Wallahi duk gidannan babu dadi, Riyyam shi ke samu duk wani farinciki, gashi yanzu ya tafi, again kuma Hamma Rayyern ma nanda one week zai tafi, gaskiya nima tafiya zanyi.”

Cikin.sanyi Jannar tace.

“Gsky dole muji gidan ba daɗi,
To ba gani ba ga Mamy, ka daina fushi.”

Longoɓar da kai Ramadan din yayi, tare da mikewa tsaye, Cikin yanayin jin yuwa yace.

“Muje ki bani abinci My Aunty.”

Mamy dake kallonsu ne tayi murmushi, cike da k’aunar y’ay’annata tace.

“To Ramadan kamanta da cewar, Rayyern da Jannart zai tafi? ai zama mu kad’ai kam ya kama mu.”

Jin abunda Mamyn ta fad’ane kuma, yasa Jannart saurin juyowa ta kalli Mamyn, domin kwata kwata ita bata masan da zancen ba.

Ramadan kuwa fuska ya sake kwab’ewa Cikin yanayin damuwa yace.

“Gaskiya Mamy nima zan tafi London shak’atawa, ko ki gayawa Abba Dan Allah yaje, gidansu Rayhanna mana, atambayamin aure, gidan ya rame da yawa, please Mamy.”

Ya k’are maganan yana me had’e hannayensa, alaman rok’o.

Murmushi Mamy tayi, kana cikin kulawa tace.

“To me kakeci na baka na zuba Ramadan, ai komai ya kusa, tunda har ankai kudin, nagani inaso, kuma iyayen Rayhannan sunce zasu tuntub’i Abbanku.”

Idanu Ramadan din ya dan zazzaro cikin, mamaki hadi da tsananin jin dadi yace.

“Wow Mamy yaushe akayi haka bansani ba, Dan Allah su Abba sunje.”

Murmushi Mamyn tayi tare da jinjina masa Kai tace.

“Eh su Abbanku sunje shekaran jiya, shine kuma yace kada na fad’a maka, da alama surprising dinka yakeson yi yanzuma subutar bakine.”

“Masha Allah Alhamdulillah, thank you Mamayna, soon nima zanyi aure wow.”

Ramadan din ya fadi haka cikin tsananin jin dadin daya rage masa kewar Riyyam-nsra.

Mamy da Jannart kuwa murmushi sukayi.

Haka dai suka d’an tab’a hira, kafun daga bisani suka watse.

Jannart kam gaba daya jin cewa da ita, za’a tafi Mascow yasa jikinta yin sanyi.

Wanda hakanne ma yasa ta d’aukar waya, ta kira Abba Kabir.

Bugu biyu kuwa ya d’auka bayan sun gaisa ne, kuma ta gyara zama kaman Abban yana gabanta tace.

“Abba kaji wai dani zai tafi Mascow, d’azu Mamy take fad’a.”

Daga can b’angaren Abba Kabir yayi murmushi, Cikin kuma jin dadi yace.
“Waye ɗin”.
Cike da kunya tace.
“Shi Doctor din”.
Murmushi mai sauti Barrister Kabir yayi tare da cewa.
“Masha Allah Jannart, ai babu damuwa zaku iya zuwa, Allah Ubangiji ya tsare ya kuma kareku aduk inda kuke, yaushe ne zaku tafin?”

Fuskarta ta d’an shagwabe Cikin yanayin sanyi, tace.

“Abba basu fadamin ranar ba, amma nasan zasu fada ma Idan lokaci yayi.”

“To shikenan Jannart.”

Abba Kabir din ya fad’a, daga haka kuma hira kadan sukayi sannan sukayi sallama.

Washegari kuwa Abba da kasan ya kira Barrister Kabir ya sanar masa batun tafiyar.

Wanda kuma yau ya kama saura kwana biyu tafiyar tasu, sosai kuma suke ta shirye shirye tuni Rayyern ya tsara ayukan campany'nsa yadda ya dace.

Ana Gobe zasu tafi dinne kuma, Abba Kabir yazo sukayi sallama da Jannart din.

Washegari.

1:pm dai-dai jirginsu zai t
Yashi zuwa Mascow, hakan yasa tunda safe suka kammala shirinsu.

Cike da yakinin kewarsu, Mamy Abba da kuma Ramadan suka rakasu airport.

Karfe takwas jirginsu ya tashi zuwa, Abuja.

Bayan sun isa Abujan ne kuma, da kammanin awanni biyu jirginsu na zuwa Mascow ya d’aga zuwa sararin samaniya.

Ko acikin jirgin kuwa kujeransu na hade dana juna, tunda suka kama hanya kuwa, Jannart ta kwantar da kanta akan kujera tare da lumshe idonta dan bacci dake fuzgarta,
haka ma Rayyern shidinma lub yayi, Ahankali yake sauke ajiyar zuciya, tare kuma da ajiye idanunsa akan, yatsun hannunta wanda suke shinning.


Tafiya sukayi mai Nisan zango k’arfe.
8: 30 na daren garin, jirginsu ya sauk’e ababban airport din dake cikin garin na Mascow...!




*Albishirinku! Ma'aurata, GA GARKUWAR KU nan tafe muku da tsarabobi na musamman gareku ma'aurata daga cibiyar mgnin mata mai taken GARKUWAR MA'AURATA*

NI DAI AYSHA ALIYU GARKUWA.
Ina matukar mamakin wani irin lokaci da ya riske mu mai wahalallan fassara. Kullum dai magana daya ce, akan ma’aurata, fada, rashin jituwa, mutuwar aure, akan kuskure kalilan, rashin kula, rashin yi wa juna uziri. Toh wai duk me ya janyo hakan? Na zurfafa a tsananin tunani hakan ya tilasta min bincike mai tarin yawa wanda ya kai ni ga gano inda matsalar take? Shin yar’uwa ke macece amma kin san wacece mace ku? Kin san me ake kira mace kuwa? Mace ita ce matar da take zama iyali a wajan namiji ta zame masa bango, sanyin idaniyarsa, ta zame masa gata da farin cikin rayuwarsa ta zame masa ruwa abar kore ƙishinsa ta zame masa mayafi mai karesa daga gigitar kadaice, ta kuma dorar da mijinta kan turbar gaskiya, ta kashe masa jiki da salonta ta rikita shi da baiwa da ni’imar da Allah ya bata idan har ta san hanyar mayar da kanta sabuwa dal awajanta, wato kullun takasance masa tamkar amarya har ya kasa tantance daren amarcinsu da sauran dararen rakun rayuwar su.

Wannan ita ce mace. Ina da wata saukakkar hanyar da zaki zama abar so da kulawa da soyayya a wajan mijinki ta hanya mafi sauki, 09097853276 hanyar ita ce ki gwada amfani da kayana na gyara ki gani, ina mai tabbatar miki da in sha Allahu sai kin dara da murna sai kuma kin gode min. Kayana kaya ne da aka yi shi da zallan itacanmu na gado marasa illa a cikin jikin dan adam musamman mace, kaya ne da suke taimakawa (sex hormones 😍) dinki.
Misali kina kallon India😘, hollywood, Asian film🥰 kina ganin yanda mazansu ke nunawa matansu tsananin soyayya kamar su ba su kyautar ransu!?
Saboda me hakan? Saboda suna sadaukar da lokacinsu wajan gyara jikinsu da kayan da ke tsattsafo da ni’ima cike da tsukewa, kayan nan kuma ana yinsu ne zallar magungunan gargajiya wanda ba su da illa domin haɗine na ingantattun itatuwa da yayansu.
Ina baiwar Allahn da miji ke daure mata fuska babu hirar arziki?
Zo ki ji yar’uwa zan baki gumbata da zallar gari wanda aka yi su da nagartattun itacen da ke da matukar amfani a jikin mace. Gubar ciko, gumbar tsalle dole, gubar da ba'a baiwa mai kishiya, garin maɗi, garin mallaka, tsumin goron tula, tsumin tsartai, tsumin maratsi, pala-pala butar sirri, kwanon k’asaitacciyar mace, furar mata madararta gareki Hajia takenta sha yanzu mgni yanzu,
Ina mata masu fama da sanyi? Sanyin mara ki zo na hadaki da magani na na sanyi wanda yake wanke mara ya fitar da duk wata cuta da ke samun mazauni a wajan.
Ina da ciccibi mai kyau. Ina da hadin amare mai kyau wanda zai gyara yarinya ya kankaro mata kimarta akwai hadin mai jego wanda muke yinsa na asali inada kekkyawan Hadi maida tsohuwa yarinya.


Akwai daya bangaren wato *KAMSHI*
Kimarki gyaranki da kamshinki. Matan da suka gane suka san yanda za su kankaro da mutunci su ne masu amfani da kayan gyara da kuma sanyaya jikinsu da kamshi, ina da turaren wanka da na bandaki na daki na jiki da na kaya dana tsuguno kamshin turarena na dabam ne mai sanyaya zuciyar wanda ya shaka ina da kayan kamshi na amarya da na maijego da na uwargida da dukkan macen da take kokarin mayar da kanta mai daraja a idon kowa ta zamo sarauni a idon mijinta, akwai shu'umar humra, sayan na gari maida kuɗi gida, banda karanta yayin gyara Hajia.

Zaku iya samun kayyakina a duk garin da kike, zakiyi min mgn ta whatsApp number na 09097853276 domin yin zaɓinki, ko karin bayani, zaki tura kuɗin ta account na 0005388578 Jaiz bank AISHA GARKUWA ALIYU in mun gama mgna zan sa miki kaya a mota yazo duk garin da kike, in baki shirya saya yanzuba Please kada mu wahal da juna ki bari sai kin shirya kafin kiyi min mgn.

🤝🏻🥰😘 Daga taku AYSHA ALIYU GARKUWA *(GARKUWAR MA'AURATA)*
*GARKUWAR FULANI**Mascow International Airport.*

Ahankali Jannart ta bud’e Idanunta dake lumshe, tare da d’an muskutawa ta gyara zamanta, wanda kuma tayi hakanne saboda ganin, an bud’e k’ofar jirgin, har ma wasu daga cikin mutanen dake cikin jirgin, sun fara fita.

Kasancewar a (VIP) very important people SECTION sukene shiyasa kuma ba suyi fitan farko ba.

Ahankali ta zare belt d’in dake d’aure agefen cikinta, tare kuma da mik’ewa tsaye, y’ar k’aramar hand bag d’inta ta d’auka, dai-dai lokacin kuma shima Rayyern d’in ya mik’e tsaye.

Hakan yasa ya zamana tana gaba shi yana biye da ita abaya.

Tafiya suke Cikin nutsuwa, wanda kuma hakanne ya bashi daman k’arewa shape din bayanta kallo, kasancewar doguwar rigan English wears ne ajikinta, mai d’an santsi da kuma sharara, bak’aramin kyau kuwa rigar tayi mata ba.

Ahankali ya janye idanunsa daga kallonta, tare da gyara zaman face mask din dake fuskarsa.

Dai-dai lokacin kuma suka kawo bakin, k’ofar fita daga cikin jirgin.

Ahankali Jannart ta sak’o jiki da kuma k’afarta ta dama waje.
Wani irin masifaffen sanyi ne taji ya shigeta, wanda har saida yasa ta manne hannayenta duka akan kirjinta, cikin kuma yanayin mamakin kyaun da garin ke dashi, ta soma jujjuya Idanunta tako ta ina.

“Yah Allah.”
Ta fad’a adai-dai lokacin da ta sauk’e idanunta, akan tsarin burgewa da akayiwa, babban filin airport din, wanda ayanzun yake tamkar rana, saboda tsananin hasken wuta, daya cika ko’ina nawajen, domin matuk’ar ba sama ka kalla ba, ba zama ka tab’a cewa dare yayi ba.

Idanunta ta d’an lumshe Ahankali, tare da k’ara sanya hannayenta ta matse jikinta.

Acikin yanayin nata na hakane kuma, ta k’arasa sauk’owa daga Kan steps din.

Rayyern dake bayanta kuwa, idanunsa ya zuba mata, lokaci d’aya kuma ganin yanda take ta matse jikinta, yasa shi fahimtar cewa sanyi takeji.

Wanda azahirin gaskiya shi sanyin ma, dad’i yayi masa domin haka yakejin kowani kofar gashin jikinsa na bud’ewa.

Ahankali ya k’arasa sauk’owa daga kan steps din jirgin, dai-dai lokacin kuma sauran Doctors d’insa, way’anda already sun riga da sun sauk’o bisa jagorancin Dr Sulaiman, suka k’araso inda yake.

Hannayensa ya zuba acikin aljihun wandon jeans din dake jikinsa.

Tare da d’an soma takawa ahankali ya matsa, kusa da inda Jannart d’in ke tsaye.

“Muje.”
Ya fad’a cikin yin k’asa da murya, batare kuma da ya jirata ba ya soma tafiya.

Ganin hakanne kuma yasa ta rufa masa baya, kaitsaye suka nufi Cikin airport din, inda ananne zasu d’auki akwatunansu, suna gaba sauran Doctors din na biye dasu abaya.

Sudai mamaki da kuma tarin tambayoyi ne, kwance acikin zuciyarsu, saboda wannan ne karo na farko da suka ga, Ogan nasu da wata Mace agaba d’aya tsawon rayuwarsu, macen ma kuma da basusan wacece ba, kasancewar akwai face mask akan fuskarta, shiyasa har yanzu babu wanda yaga fuskarta, hasali kuma duk acikinsu basu da labarin auren Rayyern din sai Dr Sulaiman kadai ne ya sani, sun kuma san cewar kwata-kwata Dr Rayyern ba ma'abocin ta'ammali da mata bane, baya neman mata, to wacece ita awajensa?

Tambayar dake cin zuciyarsu kenan, wanda kuma basu da amsarta.

Ab’angaren Jannart kuwa sake matse jikinta takeyi sosai, domin duk yanda tayi tunanin sanyin garin ya

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login