Showing 12001 words to 15000 words out of 104589 words
buƙata ta ajesu a plate.
Kana ta ɗauki tukunyar tuwo number biyar tasa ruwa, kana ta hura wutan ɗaya gefen gas din ta daura tukunyar tuwon.
Yankekken albasan nan ta dauko ta watsa a ciki.
Kana ta ɗauki kifi bandan nan ta saka,
Tare da debo wani tafasheshen nama da ruwan tafashen kadan ta saka
Kana ta rufe su.
Shinkafar tuwon ta debo,
tazo ta ajiye a gefe.
Kana ta buɗe tukunyar miyar ta juye soyayyan kayan miyan nan nata duka aciki.
Sannan tasa duk kayan dandano dana ƙamshi, kana ta meda marfin ta rufe sannan ta ɗan rage wutan.
Ahaha gaba ɗaya gidan ya ɗauki kamshi, yayinda miyar kuwa taketa
Bul-bul mai yana ta tsastsafowa komai yayi dai-dai miyar tayi masifar kyau.
(Tsokaci ba dole sai da nama ko kifi ba, ana iya yinta haka nanma ita ɗaya kuma tana daɗi matuka gaya.
Tana son wuta sosai a wurarenmu fulani masuyinta a tukunyar ƙasa mukan ɗaurata tun safe ko azahar in zamuci tuwon dare da ita.)
Kai ta jinjina jin yadda miyar ke zuba ƙamshi, sai yanzu ta samu kuma hawayenta ya tsaya.
Shinkafar ta wonke wacce take mudu ɗaya kwanon sha, dan suna da ɗan yawa, gidan duk da ma dai tasan masu cikashi sosai.
So tana son ɗumamen miyar kase tasan kuma ba mamaki su Mamy ma su so.
Duk da shi miyar kase in kana cin tuwo malmala biyu to in itace malmala ɗaya ma zata isheki.
Buɗe tukunyar ta kumayi tare da motsa miyar ganin komai yayi yadda take sone yasa ta meda ta rufe, tare da kashe wannan wutan.
Dai-dai lokacin Mamy ta shigo Kitchen din tana mai cewa.
“Kai-kai Jannart yau me kike dafa mana haka gidan yaketa baza ƙamshi”.
Ta ida mgnar tana buɗe tukunyar miyar da sauri ta shaƙi daddaɗan kamshi tare da cewa.
“Masha Allah, tab lallai yau Ramadan akwai kwasar gara, irin wannan dege-dege haka, gashi dama gwanin son nama”.
Tayi mgnar a zatonta duk namane,
fahimtar hakanne kuma yasa Jannart ɗan yin murmushi tare da cewa.
“Ato in ya gani kam zaiyi zaton duk nama ne ba kasenba”.
Da sauri Mamy tasa ludeyi tana ɗan juya miyar kana ta juyo ta kalleta tare da cewa.
“Yoh ai nima nayi zaton duk namane".
Tana mai rage wutan tuwon ganin tsanewane ya rage mishi tace.
“Akwai naman ma kam, miyar tana son nama sosai”.
Murmushi Mamy tayi cikin jin daɗi tace.
"kai masha ALLAH.Yanzu bari in ƙarasa tuwon tunda kinyi mai wuyar, je kiyi wonka ga magriba ta gabato”.
Cikin yanayin gajiya tace
“Toh Mamy.”
Kana ta fita ta tafi.
Ita kuwa Mamy matso da foodflask guda uku tayi, biyu yan madai-daita daya karami.
Miyar ta zuba da zafinta cikin na miyansu Baba Mauɗo saida ta cika musu kular, kana tasa a ƙaramar na Abba kenan.
Sannan tasa a dayar tasu kenan, kowanne ta zuba namomin da tsokokin kifi bandan kana da kasen da kyau, rufe tukunyar tayi kana ta buɗe ƙasan gas din ta ajiye sauran miyar.
Muciya ta ɗauko ta tuka tuwon da kyau tana tarfa garin fulawa kaɗan, hakan yasa tuwon ya tuku yayi dank’o mai kyau, y’ar kwaryar da suke malmala ta ɗauko ta rinka malmalawa tana sawa a kulolin.
Kwaya biyu ta sawa Abba dan tasan cikin mijinta.
Su Baba Mauɗo kuwa kwaya tara ta saka musu, sannan auran kuma da zasu kai goma sha ta juye a kularsu, kana ta tattare wurin ta wonke duk abinda suka ɓata.
Sannan ta dauki tray'n na Abba ta kai falonsa, sannan ta dawo ta shirya nasu kan Dinning table, Bayan tasa plate biyar da dan na miyarsu da spoons.
Sai kuma nasu Baba Mauɗo ta aje kular akan Fridge sannan ta hada musu plate da sauran abin buƙata.
Komawa tayi ɗakinta dan yin alwala.
Jannart kuwa tsaye take agaban dreesing mirror'nta.
Da alamun tayi wonkanta da al'wala, wani zazzafan lace ne ta saka mai orange, pink, and yellow color ɗinnan,
dinkin ayi masifar yi mata kyau.
Gashin kanta take tajewa, tana gamawa kuwa ta tubkeshi a keyarta, Kana ta ninke ɗan kwalin tayi ɗaurin da shi kaɗai tafi iyawa, sabida ita dama tafi ta'ammali da kananan kaya.
Banda hoda ba abinda ta sawa fuskarta, ko man baki bata saba tabar natural pink lips ɗinta.
Turare ta fesa kana ta gyara ɗaurin.
Yayinda ta tubke gashin a ƙeya hakan ya taimakawa ɗaurin yayi ras.
Hijabi tasa jin an kabbarta sallah a masallatai.
Bayan ta idar da sallan ma bata tashi ba.
Sai da akayi isha'i, tana idarwa ta yafa ɗan siririn mayafi pink color kasan cewar akwai ratsin pink a lace din.
A falon ta samu Mamy ita ɗaya.
Gefenta ta zauna tare da cewa.
“Mamy ke ɗaya?”.
Juyowa tayi ta kalleta cikin kulawa tace.
“Wlh kuwa kinga yau har yanzu Abbanku da Rayyern basu dawo ba.
Gashi su Ramadan ma shiru...”
Ta ƙare mgnar tana kallon himilin gashin Jannart ɗin.
Ita kuwa Jannart cewa tayi.
“Mamy ki kirasu mana to”.
Miƙewa zaune tayi tare da cewa.
“Toh".
Sai kuma ta ɗora da cewa.
“Jannart ko dai inyi miki kitso ne? Naga tunda kikazo kan a tsefe”.
Da sauri tace.
“Ai kuwa ina son kitso Mamy”.
Murmushi tayi tare da cewa.
“Toh ba matsala bari muci abinci sai inyi miki koda cukune, tunda naga bakya son barinshi a sake, kinga sai ki tubke abinki”.
Kai ta gyaɗa kana ita kuma Mamy wayarta ta ɗauka tare da cewa.
“Bari dai in kira s..”
Bata ida rufe bakinta ba Rayyern ya turo ƙofar ya shigo da sallama, kana PA na biye dashi abaya.
“Masha Allah kinga ɗan halal yaki ambato.”
Mamy ta fada.
Shikuwa Rayyern din cikin yanayin tarin gajiya da yunwa, ya zauna gefen Mamy tare da fesar da numfashi kana a hankali yace.
“Wash Allah na Mamy na gaji, kishi da yunwa kamar zasu karni.”
Da sauri Mamy ta miƙe tare da cewa.
“Toh Jannart kinji shi, ni nayi can nasan Abbanshi ma a gajiye ya dawo."
Ta ida mgnar tare da kallon PA kana tace.
“PA kada ma ka zauna a nan ku iso kan Dinning table kawai”.
Ai kuwa murmushi PA yayi tare da biyo bayanta yana cewa.
“Hajia azo a bamu abinci.”
Yayi mgnar yana kallon Jannart.
Ita kuwa Jannart miƙewa tayi a hankali ta ɗan saci kallonsa cikin sanyi tace.
“In kawo maka nanne?”.
Da alamun tarin gajiya da kuma fitinenneyar yunwar, daya kashe masa jiki ya kad’a kai kawai.
Ganin hakanne kuma ya sata juyawa ta nufi dining area.
“PA ya dai kana tsaye zauna mana”.
Ta fadi haka, saboda ganin Usman PA da tayi a tsaye.
Da alamun sauri yace.
“Kai inaga ni bani abincin zan wuce gida dashi naci ko a mota.”
Cikin mamaki tace.
“Saurin me kakeyi haka?”
Tayi mgnar tana shigewa kitchine.
Wani dan kyakkyawan kula ta dauko mai haɗe da na miya.
Kana ta dawo shi kuwa PA fridge dake gefensa ya buɗe tare da cewa.
“Wlh banyi shiri bane kuma gobe da sassafe zamu wuce Abuja, saboda bayan azahar zamu wuce china.”
Kai Jannart din ta jinjina mishi, tare dasa mishi miyar bayan ta sa mishi tuwo malmala uku.
Amsar kular yayi kana ya sauka da sauri, ya sallami uban gidan nasa ya tafi.
Ita kuwa Jannart tray'n ma dai-dai-ci ta ɗauka, plate ta ajiye akai, kana tasa tuwo malmala biyu, tare dasa wani plate din ta rufeshi, sannan tasa miyar acikin wani dan bowl na glass k’arami mai kyaun gaske, Koda tazo diba masa miyar kuwa, sosai ta sa mishi nama da kifin, bayan ta kammala ne kuma, ta saka murfin bowl din ta rufe,
kana ta ɗauko goran faro mai sanyi da cup.
A hankali ta ɗauki tray'n tare da sauƙowa akan steps din.
System ɗinshi ne ke bisa cinyarsa, wanda hakan yasa bai kalleta ba, santer table ɗin baƙin Glass din,ta jawo gabanshi bayan ta aje tray'n a kai.
Batare kuma da tace masa komai ba, ta juya ta koma cikin Kitchine din.
Wani ɗan roba mai kyau ta ɗauka tasa ruwa a ciki kana ta koma ta ajiye a gefen tray'n.
Dai-dai lokacin ne kuma Mamy ta futo, hannunta riƙe da kum da kifiya.
Kan kujerar dake fuskantar wacce yake kai Mamyn ta zauna tare dace wa.
“Yauwa Jannart kin gama masa ko, to zo mu fara kitson kawai.”
Da sauri Jannart din tace
“To.”
kana ta matso gabanta ta zauna a ƙasa bisa carpet din.
Tare da ture ɗan kwalin kanta.
Ita kuwa Mamy dan matsowa tayi gaba kaɗan tasa hannunta.
Ta fara warware gashin Jannart din dake tubke.
“Wai-wai Masha Allah, Jannart gashin naki ya cika santsi anya zan iya kitsashi kuwa ga yawa ga tsawo”.
Mamy ta faɗa lokacin da ta gama warware jelar gashin.
A hankali tace.
“Yana da wuyan kitso kam Mamy, ko zamu bari saida safe.”
A hankali ya ɗago kansa ya kallesu,
Idonshi ya tsaida kan tarin gashinta dake kwance bisa kafadunta.
Fuskarshi ya ɗan ya mutsa kana a hankali yace.
“Mamy kitso kuma anan ga abinci na”.
Ba tare da ta kalleshi ba ta fara tattare gashin dan taga a taje yake.
“Ga can wurin cin abinci kaje can”.
Ta faɗa tana nuna mishi Dinning area.
Cikin gajiya yace.
“Wlh na gaji ne Mamy”.
“Toh zauna kana can muna nan, kuma ba taje kan zamuyi ba, me hadinmu da kai”.
Fuskarshi ya kwaɓe tare da aje system ɗin nashi.
Kana ya gyara zamanshi tare dasa hannunshi cikin roban wonke hannun yana mai cewa.
“Kiyi hakuri bari inci da sauri-sauri sai kuyi”.
Buɗe plate din yayi kana ya buɗe miyar.
Ido ya ɗan zubawa miyar tare da cewa.
“Mamy wannan fa miyar menene”.
Tana mai tsaga tsakiyar suman tace.
“Ka dan-da na mana ita kaji yadda take”.
Shiru yayi kamar ya maida ya rufe.
Toh kuma yunwar dake zakularshi kara kaimi tayi ganin abincin.
Hannunshi yasa bisa tuwon ya ɗan gutsuro ƙarami.
“Gaba ɗaya ni ba son cin tuwo da dare nakeyi ba, sabida sa katon ciki yakeyi”.
Ya faɗa yana mai ɗan yago miyar ya haɗa da gayan tare da yin bismillah.
Ya nufi bakinsa da loman yana mai kallon miyar.
A hankali yasa loman a baki.
Da sauri ya murza harshensa yayi gefe dashi tare ɗaukan gayan da miyar.
Garɗin miyar ne ya sashi jan nannauyan numfashin kana ya lumshe idonshi.
Zamanshi ya gyara tare da kai hannunshi ya gutsuro loma ta biyu.
Yana mai jin wani irin tsinkewa da yawun bakinshi sukayi.
Ga ɗan-danon Nama, kifi, kasen.
Kana ga wani ɗan tsami-tsami mai shegen daɗi more Especially ga bakin mara lfy.
Miyar ya diba da ɗan yawa ya haɗa da gayan kana yasa a baki.
Yan kananan tsokokin naman da kifin, ne da diddigin naman ya tauna cikin jin marmarin cin abincin.
Mamy kuwa ido ta zuba mishi.
Sabida taji yadda Abba yayi ta santin miyar har ya cinyeta tsab.
Har yana cewa gobe ɗumamen zaici, ya shiga wonkane ta fiton.
Sunkuyar da kanta tayi ta fara yiwa Jannart ɗin kitson.
Shi kuwa Rayyern matsowa yayi bakin kujerar da kyau.
Yaci gaba da cin abinci.
“Bari kawai inyi miki manyan ibra zasuyi miki kyau”.
Mamy ta faɗa tana fara kitson.
Dago kanshi yayi ya kallesu.
Yatsun Mamy ya ɗan kalla ganin yadda take sasu cikin tattausar sumar mai ɗan karen sulbi.
Haka nan sai ya gaza ɗauke idonshi kan gashin.
Wuyanta ya ɗan kalla fatar fara ƙal kana wuyan yayi wani rin zane kamar guru-guru haka.
Ta goshinta kuma gashin ne ya kwanta lib-lib Mamy na janshi yana suɓalewa.
A hankali ya rumtse idanunshi sabida sun gaza daina kallon.
A fizge ya sunkuyar da kanshi yaci gaba da cin abincin.
Yayinda idanunshi kuma suka sauka akan.
Tattausan tafin kafafunta da suke a naɗe.
Sosai yaci abincin yana mai kallon himilin gashin.
A hankali yayi wani sassanyan gyatsa, tare da aje goran ruwan daya sha.
Kana ya ɗan ture tray'n gefe tare da ɗaura sawunshi kan table ɗin ya samu yayi balance domin cikinsa yayi masa nauyi.
Dan kab tuwon ya cinye.
A hankali yace.
“Alhamdulillah".
Sai kuma yayi wani sassanyan gyatsa
Kana ya ɗan kallesu.
“Kai tray'n Kitchen kizo muci gaba”.
Mamy ta faɗa tare da sake kan Jannart.
Ita kuwa miƙewa tayi tare da isowa gareshi ba tare da tasa dankwali ba.
Sunkuyowan da tayi ne kuma yasa gashin tahowa.
Har yana taɓa yatsun ƙafarsa.
Wani irin masifeffen taushi da tsulbin gashin ne yasashi jin tsikar jikin sa mimmiƙewa,
Kauda kanshi yayi tare da miƙewa.
Ya nufi sama.
Ita kuma ta kai tray'n kana ta dawo sukaci gaba.
Suna gamawa su Ramadan na shigowa.
Haka yasa suka wuce Dinning area.
Sosai sukaci abinci fiye da zatonsu sunaci suna zuba santi.
“Kai gsky nima gobe d‘umame zanci Mamy”.
Ramadan ya faɗa yana taunar tattausan sokan nama.
Riyyam-nsra kuwa cewa yayi.
“Ni gsky bazanci dumameba amman a ajiye mana miyar gobe da rana amana tuwo.”
Dariya Mamy tayi tare da cewa.
“Gsky dai miyar tayi daɗi, kamar za'a iya cinta da shinkafa fara ko?”.
Dariya sosai Ramadan yayi tare da cewa.
“Jama'a waiji yaseen Mamy kema yau kin shiga motar santi”.
Cikin danne dariya Jannart tace.
“Ba wani santi Mamy ana iya cinta da farar shinkafa madadin miyar stew ko mai da yaji".
Haka dai sukayi ta hira sai kusan karfe goma da rabi suka watse.
Washe gari da Asuba, bayan sun dawo masallacin.
Zaune suke a falon baki ɗayansu.
Yayinda PA ma shigowarsa kenan
A hankali yake takowa yana saukowa.
PA ne ya nufi inda yake yana kallon agogon hannunsa.
Shida da rabi kuma bakwai dai-dai jirginsu zai tashi.
Yana gama saukowa yazo ya zauna kusa da Abba tare da cewa.
“Toh Abba zamu tafi.”
Cikin tsananin kulawa Abba yace.
“Toh Rayyern Allah ya bada sa'a ya kaiku lfy ya dawo daku lfy ya tsareka da sharrin abin ƙi”.
Da “Amin.” suka amsa baki ɗayansu.
Kana ya kalli Mamy.
Mamy ko gane me yake nufi ne yasa tace.
“Allah ya kaiku lfy babana ya dawo daku lfy, PA ka kular min dashi da kyau musamman kan cin abinci.”
Kai Usman PA ya gyaɗa bayan sunce Amin.
Shi kuwa juyowa yayi ya kalli Riyyam-nsra tare da cewa.
“Zan dawo in sameka ko?"
Da sauri ya gyaɗa mishi kai yana mai yin rau-rau da ido yace.
“Yesss Hamma Rayyern zan jiraka sai ka dawo, duk da Mammy tana matsawa in koma".
Kanshi ya jinjina tare da cewa.
“Toh banda yawon banza, da shashanci, kai kuma Ramadan ka kula da aikinka, kasan ganinka zaisa sauran Doctor's din karsashi.”
Cikin gamsuwa Ramadan yace.
“Toh Hamma Rayyern Allah ya kiyaye hanya, Insha Allah kuma zan kula.”
“Amin.” Yace yana mai miƙewa tsaye.
PA kuwa tuni ya fita, yayinda Ramadan da Riyyam-nsra suka mara mishi baya.
Kana shima Rayyern ya bisu a baya.
“Rayyern!!”.
Yaji muryar Abbanshi da sauri ya ɗan juyo.
Ƙofar ɗakin Jannart ya nuna mishi tare da cewa.
“Dan Allah ka shiga ka sallameta, na roƙeka da girman Allah.”
Wani irin abu mai nauyi yaji ya danne masa zuciya.
“Ya salam".
Ya fadi a ransa jin Abban yace ya hadasa da girman Allah wato badon shiba.
Wani rauni, da damuwa ne suka rufesa, sabida ganin da yayi suna gab da sashi a sahun ya'ya marassa biyayya.
A hankali ya juya nufi ƙofar dakin.
Ita kuwa Jannart kasan cewar bakonta (al'ada) ya dawo daren jiya ne, yasa yanzu ta fito daga wonka daga ita sai towel ajikinta, take zaune agaban dreesing mirror'nta.
Rayyern kuwa ahankali ya tura ƙofar falon ya shigo, tare kuma da maida kofar ya rufe.
Ahankali kuma ya tako zuwa tsakiyar falon.
Murya a dakile yace.
“Salamu alaikum.”
Jannart dake zaune kuwa shiru tayi, tare da aje goran man da take shafawa, dan jin kamar mgnar mutum, Jin shiru babu alaman wani motsinne kuma yasa ta cigaba da shafa mai dinta.
Still tana cikin shafa maidin ne kuma tasake jiyo kamar sautin muryar mutum.
Da sauri ta mik’e tsaye tare da nufar kofar fita, ahankali ta bud’e k’ofar tare da d’an lek’o kanta tace.
“Waye?”
Shiru yayi ba tare daya bata amsaba.
Jannart kuwa hakanne yasa ta sake leƙo da kanta, sai dai bata ganshiba.
Jin kaman da gaske ba kowa acikin falonne kuma yasa ta fito gaba ɗayanta.
Inda tayi taku ɗaya ana biyu ta ganshi tsaye.
Cikin wasu irin fitinannun Suit bakake masu masifar kyau da sheƙi.
Da wani irin sauri ta juya ta koma cikin labule.
Shi kuwa Rayyern dauke kansa yayi gefe, kamar bai ganta ba murya a dakile yace.
“Na tafi.”
Da sauri, kuma cikin muryarta dake rawan fargaban ganinsa da tayi, da kuma ganinta da yayi ahaka tace.
“Allah ya tsare ya kiyaye hanya”.
A takaice yace.
“Amin, idan da zuciya ɗaya kika fada”.
Yana faɗin haka ya juya ya fita.
Jin alamun fitansa ne kuma yasa ta fitowa, daga inda ta boye cikin sauri ta koma cikin bedroom din, tana nanata mgnar sa ta karshe, da taji ya fada.
Shi kuwa yana fita, kai tsaye Airport suka wuce.
Su Ramadan kuwa basu dawo ba, saida sukaga jirginsu ya tashi suka dawo tare dasu Hadi.
Su Rayyern din kuwa a Abuja sukayi breakfast.
Kana sai ƙarfe huɗu dai-dai na yamma jirgin da zai kaisu China ya tashi.
Acan gidan kuwa Ramadan na dawowa ya tafi aiki, Yayinda Riyyam-nsra kuma kofar gida ya fita wurin Baba Mauɗo.
Su kuwa su Dr.Rayyern Mai-nasara dare ya fara nisa sosai jirginsu ya sauka a.
Beijing Capital International Airport China.
Suna fitowa a jirgi.
PA yace.
“Yah Subahanallahi, tsarki ya tabbata ga Ubangijin talikai mai duniya da ƙiyama.”
Rayyern kuwa limshe idanun sa yayi.
Duk da yazo wurin nan a ƙalla sau biyar.
Amman idanunsa kullum a sabo suke ganin Airport ɗin, sabida masifar kyau da tsananin haɗuwa.
Duk da tsakar dare ne kai kace tsakar ranace, sabida yadda wurin yake da masifar kyau da ƙawatuwa.
Ina in an haɗa Airport's dinmu na Nigeria da nasu tofa ai namu jujine.
Da dan sassarfa suka fito inda zasu samu taxi.
Bayan sun shigane PA yace ya kaisu hotel mafi kusa da Airport ɗin.
Dan campany'n injinun da suke da akalar kasuwancin yana kusa.
Kai PA ya jinjina cikin takaicin Yaren masu idanun kwadin nan wato China sam basu cika gane turanci ba.
Saida Rayyern yayi masa karin bayani da kyau kana ya gane.
Tafiya mai ɗan nisa kaɗan sukayi sai gasu a wani tamfatsetsen hotel.
China world hotel beijing.
Bayan sun sallameshi ne, suka shiga.
Bayan sun kama daki sun, haura wonka sukayi kana sukayi ramuwar sallan magriba da isha'i, kasancewar sunci abinci a jirgi ba yunwa ba kishi ne, yasa kawai suka kwanta dan yin baccin gajiya, saboda tafiya dai ko ya take tafiya ce.
A nan gida kuwa Riyyam-nsra ne zaune gefen Baba Mauɗo yana masa gugan kayanshi.
Yayinda shi kuma yake can gefe,
wayarsa dake kusa da Riyyam-nsra ne ta fara ringing.
Juyowa yayi ya kalli Riyyam-nsra tare da cewa.
“Wake kirana?”
Ido Riyyam-nsra ɗin ya zubawa fuskar wayar cike da mamaki, ya juyo ya kalli Baba Mauɗo kana ya Kuma juyowa ya kalli fuskar wayar.
Hakan yasa Baba Mauɗo yun ƙurowa da sauri, cikin rawan jiki ya jawo wayar tasa.
Da sauri kuma ya juyo ya kalli Riyyam-nsra.
Shi kuwa Riyyam-nsra cikin wani irin kallo mai cike da mamaki yace.
“in...!
*Albishirinku! Ma'aurata, GA GARKUWAR KU nan tafe muku da tsarabobi na musamman gareku ma'aurata daga cibiyar mgnin mata mai taken GARKUWAR MA'AURATA*
NI DAI AYSHA ALIYU GARKUWA.
Ina matukar mamakin wani irin lokaci da ya riske mu mai wahalallan fassara. Kullum dai magana daya ce, akan ma’aurata, fada, rashin jituwa, mutuwar aure, akan kuskure kalilan, rashin kula, rashin yi wa juna uziri. Toh wai duk me ya janyo hakan? Na zurfafa a tsananin tunani hakan ya tilasta min bincike mai tarin yawa wanda