Showing 66001 words to 69000 words out of 104589 words

Chapter 23 - Tubali Book 2 Hausa Novel Complete

Unknown   

21 Dec 2024

170

garin da kike, in baki shirya saya yanzuba Please kada mu wahal da juna ki bari sai kin shirya kafin kiyi min mgn.

đŸ€đŸ»đŸ„°đŸ˜˜ Daga taku AYSHA ALIYU GARKUWA
*(GARKUWAR MA'AURATA)*
By
*GARKUWAR FULANI* “Naan please ka bud’e idanunka, Dan Allah kayi numfashi!!”

Ta kare maganan cikin matsanancin kukan, dake bayyana karyewar zuciyarta da rauninta.

Hakan da Dr. Sulaiman ya ganine kuma ya sashi, k’arasowa cikin falon da sauri, hankalinsa amatukar tashe yace.

“Innalillahi Wa’inna Ilaihirraju’un, please Jannart stop crying, kiyi min bayanin abunda yake damunshi.”

Jin muryar Dr. Sulaiman acikin kunnuwanta ne kuma, ya sata d’ago Kanta da sauri cikin shasshshek’an kuka, kana murya asark’e tace.

“Ka taimakamin Doctor, Dan Allah ina tsoron ya rasa rayuwarsa, numfashinsa tafiya yakeyi, tun d’azu cikinsa keyi masa ciwo, kuma bansamu maganin da zan basa ba.”

K’arasowa wajen nasu Dr Sulaiman yayi, cikin kuma tsananin yanayin damuwa yace.

“Calm down Jannart, Insha Allah Rayyern zai samu lafiya, ki daina kuka kinji.”

Ya k’are maganar yana me lalub’o waya daga aljihunsa.

Rayyern dake rungume acikin k’irjinta kuwa, har yanzu da sauran numfashinsa, sannan kuma ahankali zuciyarsa ke bugawa, wanda kuma hakan na tafiya ne, da taimakon bugun zuciyar Jannart din da yake iya jiyowa acikin kirjinsa, kasancewar k’irjinsa da nata suna manne awaje d’aya.

K’warai yana so ya bud’e idanunsa da suke lumshe, amma kuma bashi da k’warin guiwar yin hakan, saboda zuwa yanzu komai na jikinsa yayi sanyi.

Jannart kuwa ahankali tasa hannayenta, ta sake matsetshi acikin jikinta, still kuma hawayen dake kwance akan fuskarta na d’iga ajikinsa.
Duk ta rud’e Yayinda Idanunta sukayi ja sosai.

Dr. Sulaiman kuwa Ganin yanda take arud’en ne yasa shi d’an rank’wafowa, kana cikin kulawa yace.

“Ya kamata mu kaisa asibiti mafi kusa, domin bashi taimakon gaggawa, amma firstly yanzu sakeshi bari na fara sakashi a mota.”
Ya ƙare mgnar yana matsowa kusa dasu,
Sunkuyowa yayi da niyar janye Rayyern dake jikinta.

Dai-dai lokacin kuma Rayyern ɗin ya fara wani irin numfarfashin masu nauyi.

Saurin girgiza kanta tasoma yi, cikin tsoro da kuma fargaban abunda ka iya zuwa tace.

“A’a Doctor Idan na sakeshi suma zaiyi fa.
Kalli yadda numfashinsa keyifa zai d’auke gaba d’aya, Ina jin tsoro ni dai bazan iya sakeshi awannan yanayin ba, Dan Allah kakira mana Dr yazo ya duba shi.”

Ta kai k’arshen maganan nata tana me, sake rungume Rayyern din acikin jikinta, Yayinda hawayen dake kwance akan fuskarta kuwa ke ci gaba da tsiyaya, tamkar ankunna famfo.

Baki Dr. Sulaiman din ya bud’e da niyar cewa wani abu, saidai kiran daya shigo cikin wayar tasa ne, yasa shi yin shiru tare da d’aukan wayan ya kara akan kunnensa.

Daga can b’angaren Ramadan jin Dr Sulaiman din ya d’aga wayan, cikin tsananin tashin hankali yace.

“Please Dr ya ake ciki, ya jikin Hamma Rayyern din? Kun kaishi asibitin Ina fatan babu abunda ya sameshi?”

Ramadan yayi tambayan duk agigice.

Kai Dr Sulaiman din ya girgiza, kana cikin yanayin damuwa yace.
“Ramadan ya zanyi Jannart ta rik’e sa gam, ta yanda babu yanda zan iya d’aukarsa, saboda tace wai Idan ta sakeshi suma zaiyi, na rasa makama Ramadan Domin ciwon nasa ya tashi sosai awannan karon.”

“Innalillahi wa’inna Ilaihirraju’un, Dr Sulaiman kayi wani abu mana, kayi wani abu kada Hamma na ya rasa ransa, Dan Allah ko Doctor ne kaje ka kira a waje.”

Ramadan ya fadi haka cikin tashin hankali.

Kai Dr Sulaiman ya jinjina, tare kuma da kad’a kansa cikin gamsuwa yace.

“Okay Ramadan amma inajin tsoron tafiya nabarsu awannan yanayin, Rayyern yana gab da suma, gashi Jannart kuma sai kuka take kamar zata shid’e, gaba d’aya na kasa iya control dinsu dukansu biyu.”

“Yah Allah help us.”

Ramadan ya fad’a cikin muryarsa da tayi rauni sosai, cike kuma da tausayin d’an uwan nasa, ga kuma Jannart dake ta kuka, domin daga cikin wayar yana iya jiyo sautin kukan da takeyi.

Jannart dake rungume da Rayyern din kuwa, kwata kwata bama tasu Dr Sulaiman din takeyi ba, damuwarta shine taga Rayyern din ya bud’e idanunsa.

Ahankali ta dawo da kallonta garesa, tare dasa hannunta d’aya ta tallafo hab’arsa cikin kuka tace.

“Dan Allah Naan ka bud’e idanunka, kada ka daina numfashi, kada kuma ka cire rai da rayuwa in sha Allah, ai zaka samu sauki ko, nasan zaka warke zaka samu lafiya mu koma Nigeria lfy en Mamynka da Abbanka su ganka lfy, za kayi rayuwa kamar kowa muna bukatar ka a tsakiyar mu, dan Allah ka bud’e idanunka yanzu, ka dawo cikin hayyacinka Dan Allah...”

Ta k’are maganan cikin tsananin kuka da kuma raunin zuciya, ahankali kuma tasa hannunta akan kumatunsa tana d’an bubbugawa, cike dason taga ya bud’e idanunsa.

Idanu Dr Sulaiman ya zuba musu, lokaci daya kuma duk jikinsa yayi sanyi, musamman da yaga yanda Jannart din ke kuka sosai da sosai.

Maida wayar tasa cikin aljihu yayi, cikin sauri kuma ya d’auki key din motar Rayyern din, da ya gani akan table, tamkar wanda zai tashi sama saboda sauri, haka ya sa Kai ya fice daga cikin falon.

Kaitsaye wajen da motar Rayyern din yake ya nufa, yana shiga kuwa ya cilla motar kan titi, tare da nufar babban hospital din garin, wanda kuma shine mafi kusa dasu.

Jannart dake zaune kuwa duk da taji fitansa, amma bata d’ago Kanta ta kalleshi ba, Idanunta har yanzu suna kan fuskar Rayyern, still kuma ko wani d’igon hawayenta d’aya, da zai fita akan fuskarsa yake sauk’a.

Ahankali take yawo da hannunta dake kan hab’arsa, har ta k’araso zuwa kan kirjinsa.
Lallausan tafin hannunta ta kife akan kirjin nasa, dai-dai saitin zuciyarsa, Jin zuciyar tasa na d’an bugawa ahankali ne kuma ya sata, lumshe Idanunta tare da motsa labb’anta cikin sanyi tace.

“Ya Allah ka taimaki Naanu na Yah Allah ka bashi lafiya, kasanya juriya acikin rayuwarsa, Allah kagani bamu da kowa anan saikai, Kai ke kulawa damu akoda yaushe, Ya Allah yauma ka kula damu, ka saukaka mana tsanani izuwa sauki ya Allah ka rufa min asiri ka bawa Naanu na lfy.”

Takai karshen maganan hawaye yana me shatata akan fuskar nata.

Rayyern dake kwance ajikinta kuwa, duk wani abu da take fadi yana jinsu acikin kunnuwansa, saidai kuma yakanji kalaman nata da sautin amon muryar nata tamkar acikin mafarki, saboda gangar jikinsa ne kawai take wannan duniyar, hankalinsa kuwa ya tafi izuwa wata duniyar ta daban.

Suna ahakanne kuma k’iran Ramadan ya shigo cikin wayar Rayyern din dake gefe, Ganin sunan Ramadan ne kuma, yasa ta d’aga wayar da sauri tana k’arawa akan kunnenta, ta sake fashewa da kuka, still cikin muryar sheshshek’a tace.

“Ramadan har yanzu baidawo cikin hayyacinsa ba, na shiga uku Ramadan banason wani abu ya sameshi, duk jikinsa rawa yakeyi, gaba daya ya fita ahayyacinsa, Ramadan ya zanyi....”

Sautin kukan nata ne yasa Ramadan d’an rumtse idanunsa, zuciyarsa cike da damuwa, da kuma tashin hankali yace.

“Zai dawo Hayyacinsa Aunty Jannart, Insha Allah nan bada jimawa ba Hamma Rayyern zai dawo hayyacinsa, ki daina kuka dan Allah, ki kula dashi kafun Dr. Sulaiman ya dawo.”

Cikin kukan ta jinjina kai, saidai ta kasa cewa komai sai sheshshekanta da yake tashi.

Acan Nigeria din kuwa Mamy dake gefen Ramadan, itama hawaye takeyi gaba daya ta shiga cikin damuwa.

Haka ma Abba wanda ya zauna yayi ta gumi, abubuwa da yawa yake sak’awa acikin zuciyarsa, kallo daya kuma zakayi masa kafahimci cewa yana cikin matsananciyar damuwa.

Kasancewar kuma Ramadan din a hands free ya saka wayar ne, yasa dukansu suke iya jiyo kukan Jannart din, harma da nishin Rayyern dake tashi k’asa k’asa.

Ahankali Abban ya d’ago ya kalli Ramadan, da hannu Yayi masa alama akan ya bashi wayar.

Ganin hakanne kuma yasa Ramadan mik’a masa, kara wayar Abban yayi akan kunnensa, cikin son b’oye damuwa da kuma tausasa murya yace.

“Jannart.”

Jannart dake zaune kuwa jin muryar Abban acikin wayanne yasa ta d’an zabura, cikin rawar murya tace.

“Abba Hamma! Hamma!! Abba jikinsa yana ta b’ari, ga numfashinsa ya kusa d’aukewa, ciwo yakeji sosai, Dan Allah Abba ka taimakeshi.”

Idanu Abban ya d’an lumshe saboda tsananin tausayin yarinyar da yaji, domin ayanzu kukan ta yafi komai d’aga musu hankali sabida yanaga tashin hankali da take ciki zai hanata yin abinda ya dace.

“Jannart, Jannart!!”

Abban ya kira sunanta ahankali.

Yanda taji sautin muryar Abban ne kuma yasa ta, d’an tsagaita kukan nata tare da amsawa.

“Kiyi shiru kinji ki kwantar da hankalinki, ki daina wannan kukan In sha Allah Rayyern zai samu lafiya, ki daina kuka ki zama mai juriya akan ciwon sa kinji ko Jannart, yanzu addu’a ya kamata ki masa, ki daina kuka domin yawan kuka zai iya jawo miki wata matsalar kema, saboda haka ki share hawayenki Allah nanan kuma zai Iyar muku.”

Abban ya fad’i haka cikin son bata k’arfin guiwa.

Jin hakanne kuma yasa ta sanya hannu ta share hawayenta, cikin nuna biyayyarta agaresa tace.

“To Abba.”

Kai Abban ya jinjina cike da yabawa halin yarinyar, kana Ahankali ya zare wayar akunnensa ya kashe, saboda shi d’inma dazai samu dama, kukan zaiyi Domin har abada bazai tab’a son ace wani abu ya samu Rayyern din ba, haka kuma bazai so ace Rayyern yabar duniya batare da ya sauk’e wani k’aton nauyin dake wuyansa ba, Lallai zaiso ace Rayyern ya rayu, har zuwa lokacin da gaskiya zatayi halinta.
Baya ga haka kuma Rayyern din shine komai nasu, shine AHALI’nsu kuma k’ashin bayansu.


Ahankali ta zare wayar daga kan kunnenta, tare da lumshe Idanunta tana mejin yanda Rayyern din ke sake shigewa cikin jikinta, Yayinda ya saka duka hannayensa biyu ya rungume cikinta gam.

Wanda hakan da yayi din kuma alamace dake, nuna cewar yanajin ciwo sosai.

Acan b’angaren Dr Sulaiman kuwa.
Koda yaje EUROUPEAN Medical senter mascow (E.M.S) din emergency Doctor ya nema, bayan ya shaidawa Doctorn matsalan Rayyern din ne kuma, suka nufo gidan kaitsaye.

Suna isowa kuwa ko gama dai-dai-ta parking ba suyi ba, direct suka nufi cikin gidan Dan bawa, Rayyern din agajin gaggawa.

Jin motsin shigowar su Dr Rayyern dinne, kuma ya sata d’ago da kanta ahankali ta kallesu.

Dr James ne wanda Sulaiman din ya d’auko, ya k’araso cikin falon tare da matsowa inda suke, Cikin kulawa da kuma harshensa na turanci yace.

“Madam ko zaki iya matsawa na dubashi, saboda akwai buk’atar sai nayi checking nasa sosai.”

Idanunta da sukayi jajur ta zubawa farin baturen likitan dake gabanta, kaman mai nazartar wani abu, Cikin sheshshek’an kuka kuma ta girgiza masa kai, murya araunace tace.

“Ka dubashi ahaka saboda bazan iya barinsa ba, inaji ajikina Idan na barshi mutuwa zaiyi, Dr ka kalla fa numfashinsa seizing yakeyi, Dan Allah kayi sauri ka dubashi ahaka kada wani abu ya sameshi.”

Kai Doctorn ya girgiza saboda yasan duba, patient din ahaka ba abu bane da zai yiwu, saboda akwai buk’atar dole sai anyi checking d’insa, saidai kuma da gaske yaga Jannart ba zata tab’a bari a dubasa, ba tare da yana jikinta ba.

Sanin cewar Idan aka k’ara wasu mintuna ahaka komai zai iya faruwa ne, yasa doctor din matsowa, ya d’aura hannunsa akan wuyar Rayyern, tare dasa wani abu mai kaman na’ura adai-dai kan cikin Rayyern din.

Bayan ya gama saka abunne kuma, ya d’ago ya kalli Jannart dake hawaye, shikam har acikin ransa yana me mamakin k’arfin halinta.

Wani k’wayan magani ya b’allo daga cikin wani sachet, mik’a mata maganin yayi kana Cikin harshen turanci yace.

“Kisa masa wannan ak’asan harshensa, saboda zaifi saurin yi masa aiki, zai kuma yi tasiri acikin jijiyoyin jikinsa.”

Da sauri ta jinjina kai tare da karb’an k’wayar maganin, kasancewar har yanzu Rayyern din na kwance ajikinta ne kuma, yasa ahankali ta juyo da fuskarsa, ya zamana suna fuskantar juna, fuskar tasa da tayi ja sosai ta d’an kalla, cikin sanyi da kuma tsananin tausayawa, tasa hannunta na dama ta saka mishi cikin bakinsa, d’aya daga cikin yatsunta tasa ta d’an d’aga harshensa, tare da tura k’wayan maganin ak’asan harshen nasa, kamar yanda doctor d’in ya buk’ata.

Ganin nan take maganin har ya soma narkewa, acikin bakin nasa ne yasa ta, zare yatsarta ahankali tare da zubawa kyakkyawar fuskarsa idanu.

Lokaci d’aya har rama ta bayyana akan fuskar tasa, Yayinda saman fatar idanunsa sukayi wani irin ja, haka ma labb’an bakinsa, da tsabar ja tamkar zaka latsa jini ya fito.

Dogon hancinsa da ya tafi straight ta kalla, hadi da Zara zaran gashin idanunsa wanda sukayi wasar wasar.

Wani irin hawayen tausayinsa ne ya cika Idanunta, wanda yasa ahankali tasa hannu ta shafa fuskar nasa.

Sauk’an d’umin hannunta akan fuskarsa ne kuma, ya sashi sauk’e wani irin ajiyar zuciya.

Ahankali kuma ya sake shigewa jikinta, batare da sanin abunda yakeyi ba kuwa, ya cusa fuskarsa acikin k’irjinta, domin ananne kad’ai Idan ya saka kansa, yakejin nutsuwa na saukar masa, duk da baisan cewa akan k’irjinta yake ba, amma aduk sanda ya d’aura kansa akan kirjin nata, yana iya jiyo sautin bugun zuciyarta, hakan kuwa na taimakawa zuciyarsa, wajen ci gaba da bugawa amaimakon tsayawa da take kokarin yi.

Jin yanda ya saka fuskarsa acikin k’irjinta ne kuma, ya sata lumshe Idanunta, tare da d’aura hannunta akansa, ahankali ta shiga tura y’an yatsun hannunta, acikin tarin sumar kansa.

Dr James kuwa fatar jikin Rayyern din ya tsurawa ido, ganin yanda kowacce gashin jikinsa ke mimmikewa ne, kuma ya sashi zare wannan abu mai kaman na’urar daya lik’a masa acikinsa.

Ahankali ya koma kan kujera ya zauna, saboda yasan zuwa yanzu maganin daya bawa Rayyern din ya soma aiki, kasancewar yasan maganin yana da k’arfi sosai.

Ganin Dr James din ya zauna ne, yasa Dr. Sulaiman shima ya zauna.

Kallon Dr. Sulaiman James din yayi, cikin son bashi k’warin guiwa yace.

“Zaiyi sauki domin maganin dana bashi yana da karfi sosai, just 20mn zai samu relief don’t worry.”

Ajiyar zuciya Dr Sulaiman ya sauk’e, Dan bashi da wani burin da ya wuce haka.

Duk idanu suka tsurawa su Rayyern din, wanda har yanzu jikinsa ya kasa daina b’ari.


Jannart kuwa hab’arta ta d’an d’aura akan Rayyern din, tare da zubawa hannunsa dake kan marar tasa idanu.

Ganin yanda yake ta danna marartasa ne, yasa ahankali ta d’aura hannunta akan nasa hannun.

Aikuwa kamar jira yake hakan ya kasance, cikin sauri ya kamo hannun nata ya d’aura ak’asan nasa.
Ak’agauce ya shiga danna hannun nata asaman cikinsa, wanda da dukkan alama anan yafi jin ciwon.

Ahankali hankali kuma ya shiga tura hannun nata zuwa kan mararsa, har dai ya zamana yatsunta na d’an tabo boxer d’insa, ma’ana asalin kan mararsa, wanda hakan yasa take iya tab’o, kwantaccen gashin dake saman marar tasa.

Ahankali ta lumshe Idanunta, da suke fitar da wasu irin hawaye masu zafi, duk da tasan cewar agaban su Dr Sulaeman suke, amma ta kasa janye hannunta daga inda ya kai mata, kuma Koda ace zatayi hakan ma, to ba zata samu dama ba, saboda wani irin riko da yayiwa hannun nata.

Sake damk’e hannun nata yayi, cikin kuma zafin ciwon da yakeji ya danna tafin hannunta akan mararsa da k’arfi.

Atake ya saki wani irin nishi da kuma Ajiyar zuciya mai karfi, still cikin gigita ya sake danna hannun nata akan mararsa, wanda ayanzu har tana iya jiyo tudun marar tasa.

Idanunta ta sake lumshewa, fahimtar abunda yake so dinne kuma yasa, Ahankali ta soma yawo da hannunta akan marar tasa, tare da d’an daddanawa tana yi masa massaging jin yanajin sassaucin ciwon yasa cusa hannunta cikin boxer ɗinsa kad’an yana mai danna hannunta.

Dai-dai hannunta ya iso saman penis d’insa ne kuma, ta d’an danna kad’an, batare da ta bari kuma hannunta ya tab’a penis din nasa ba.
“Hyyyyhhhhhhhhhimm”.
Haka da tayi dinne kuma yasa shi, sauke wani irin nannauyan Ajiyar zuciya, tare da jan dogon numfashi, ya sake shigewa cikin jikinta.
Bayan ya d’aura hannunsa akan nata hannun.

Haka ya dinga danna hannunta akan marar nasa, yana me sauke Ajiyar zuciya akai akai, idanunsa dake arufe kuwa, ahankali suka soma matsawa, saidai yanajin yanayinsa tamkar wani d’an maye.

Ahankali ya gyara kwanciyarsa, tare da juyawa ya kifa kansa akan cikinta, saidai kuma still har yanzu hannunta na kan mararsa, tana d’an mammatsa mishi.

Dr James ne ya kuma Kallon Dr Sulaiman da yayi jigum.

duk alamomin damuwa sun bayyana akan fuskarsa.

“Calm down Dr, zai samu sauki na fad’a ma, saidai maganin dana bashi yana sa bacci, amma daya farka komai zai dawo normal, saidai amma kada yayi wasa da maganin, ya zamana yana sha kullum kuma akan lokaci.”

Dr James din ya fadi haka yana me mik’awa, Dr Sulaiman magungunan Rayyern din.

K’arb’an maganin Dr. Sulaiman yayi cikin kuma nuna godiyarsu yace.

“Insha Allah zamuna kulawa wajen shan maganinsa, mun gode sosai doctor.”

Kai Dr James ya jinjina tare da mik’ewa tsaye, hannunsa rike da y’ar jakar maganinsa, ya kalli Jannart da take rungume da Rayyern din.

“Don’t worry madam mijinki zai warke nan bada jimawa ba, amma kina kulawa dashi sosai akan shan magani.”

Kai Jannart din ta jinjina masa alaman to.

Shikuwa Dr Sulaiman d’an kallonta yayi, cikin tausasawa yace.

“Bari nayi dropping d’insa I’m back, ko akwai abunda kike buk’ata?”

Still kanta ta girgiza alaman babu, saboda duk kukan da tayi ya galabaitar da ita.

Dr Sulaiman kuwa bayan Dr James yabi, suka fice daga falon.


Fitar nasu ne kuma yasa ahankali ta dawo da kallonta ga Rayyern d’in.
Wanda yayi kwance lub ajikinta.

Idanu ta zuba masa saboda zuwa yanzu, duk wani karkarwa da jikinsa keyi ya bari, sannan numfashinsa ya d’an dai-dai-ta, Dan ahankali yake sakin ajiyar zuciya, saidai kuma har yanzu ya kasa sakin hannunta dake kan mararsa.

Kyawawan Idanunta masu d’auke da ruwan hawaye, ta tsayar akan kyakkyawar fuskarsa.

Idanunsa dake marairaicewa ta kalla, wanda sukayi yanayi dana d’an maye ko kuma maijin bacci.

“Naan!!”

Ta k’ira sunansa da wata irin cool voice, mai ratsa jiki da jijiya.

Muryar da amon sautinta ya ratsa cikin kunnuwansa, duk da cewar baya cikin yanayi mai dadi amman yajita kuma ya gane muryarta ne.

“Naan!!!”

Ta sake kiran sunan nasa akaro na biyu, saidai kuma ganin bai amsa ta bane, yasa ahankali ta sake tura d’ayan hannunta cikin sumar kansa.

Ajiyar zuciya mai nauyi ta ji ya sauk’e, ahankali kuma taji ya sake matsewa ajikinta, tare da gyara zaman hannunta dake cikin boxer d’insa.

Sassanyar Ajiyar zuciya Itama ta sauk’e akaron farko, tun bayan tashin ciwon nasa, da taji nutsuwa ya d’an sauk’ar mata.

Sak’e mik’e k’afafunta tayi, tare da d’an rank’wafowa kansa ahankali.

Idanunsa dake ta narkewa ta kalla.
Hakan kuwa shiya k’arawa zuciyarta wani irin

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login