Showing 33001 words to 36000 words out of 104589 words
kafin kiyi min mgn.
đ€đ»đ„°đ Daga taku AYSHA ALIYU GARKUWA
*(GARKUWAR MA'AURATA)*
By *GARKUWAR FULANI*Tare da fuskantarsu dukansu, cikin dan nisawa yace.
âGaba dâaya matsalarmu a kullum akan Dr Rayyern Bashir Muhammad Mai-nasara ne, wanda kuma ni kaina bani da iko, ko wani matsayi da zan iya dakatar dashi akan abunda ya saka agaba, saboda duk wani kâaâida da dokokin da akebi ya bisu, Idan kuma har nace zan wargaza masa tsari.
To tabbas zai iya Kai kâarata wajen na sama dani, hakan kuma zai iya sawa na rasa aikina, yaron ya wuce duk yanda muke tunani, kowacce hanya da zamu bâullo masa ya sani, kansa yana ja sosai, babban abunda na lura dashi kuma shine, kwata kwata baya tsoron magautansa yaron yana nan Tamkar a haifeshi ne domin daukan fansa!!!.â
Numfashi mai nauyi duk suka ja, musamman Alhaji Idi Sale Dakata wanda gaba daya abubuwa suka hadâe masa.
Ga zafin bâatan Jannart ga kuma, na wannan shegen yaron Dr. Rayyern.
Barrister Kabir kuwa, kalaman Alhaji Bala Tambari na karshe yaketa nanatawa a zuciyarshi don son fahimtar wani abin.
Haka dai taron nasu ya watse gaba dâaya zuciyar Alhaji Idi, da kuma na Dr. Lukman Alhaji Abdu Tababa babu dadi, kowannensu kuma saboda Rayyern.
Dr. Lukman din, da kuma Alhaji Abdu Tababa ne suka hadâa hanya wajen tafiya, haka ma Alhaji Bala Tambari shima tafiya yayi.
Hakan yasa falon ya rage daga, Daddy sai Barrister Kabir.
Juyowa Alhaji Idi Sale Dakataân yayi? Ya fuskanci Barrister Kabir, cikin kuma nuna halin damuwa yace.
âKabir ayanzu babu abunda yake damuna, kamar bâacewar Jannart, har yanzu babu wani labari, kwata kwata ayanzu ma ba batun companyn Rayyern Mai-nasara bane ke damuna, matsalar bâacewar Jannart itace ke damuna hukuma suna iya yinsu abin yaci tura.â
Afakaice kuma ta kâasan idanu, Barrister Kabir ya kalli Yayan nasa, tare da dâan ya mutsa fuskarsa.
Wanda kuma daga wajen Alhaji Idi Sale Dakataân ma hakan yake, domin kuwa bayan yayi maganar shima, ta kâasan idanu, ya kalli Kâanin nasa, tare da sakin wani Shuâumin murmushin, da shi kadâai yasan maâanar yinsa.
Barrister Kabir kuwa, mur yasha tare da saka fuskar tsare gida, irin tasu ta lawyoyi, saboda shima akwai wani abu daya gano amatsayinsa na lawyer.
Shi yanayiwa Barrister Kabir kallon biri, shi kuwa Barrister Kabir yanayiwa yayan nasa kallon Ayaba.
Koda suka fito daga dâakin taron Alhaji Idi Sale Dakataân, main falon gidan suka dawo, inda suka samu Momy ta gama hadâa abinci.
Sama sama haka Barrister Kabir yaci abincin, bayan sun kammala ne kuma yayiwa Yayan nasa sallama, kaitsaye kuma daga gidan Alhaji Idi Sale Dakataân, gidansa ya nufa.
Koda ya isa gidan afalo ya samu Dijat.
Hira kadan suka tabâa kana kaitsaye ya wuce bedroom dâinsa.
Key ya sawa kofar bedroom din, tare da komawa ya zauna, bayan ya dâauko wasu takardu.
Anutse yake wargaza takardun, tare da Ware wasu daga ciki yana duddubawa.
Dâago wata takarda da yayi ne kuma, ya sashi tsurawa rubutu, da kuma hoton passport din dake jiki idanu.
*** ***
Almost 4weeks kenan yanzu da, dawowar Rayyern daga China, Alhamdulillah kuma jikinsa ya warware.
Bisa taimakon Ramadan da kuma Jannart, wayâanda suke kula da shan maganinsa.
Hakan yasa ciwon cikin nasa yayi sauki, ya kuma gama samun karfin jikinsa, duk da cewar time to time ya kanji, ciwon cikin na tashi masa, amma da yasha magani yake jin sauki.
Ahankali yake saukâowa daga kan matattakalan falon, inda yayi kyau cikin shigar Ash colour suit dake jikinsa.
Yayinda hannunsa ke rikâe da briefcase, da alama kuma aiki zaije.
Ya dawo asalin Rayyern dâinsa, big man wanda bai wani cika son wasa ba, wani Rama da yawan kasalan da yakeji ada, duk sun kama gabansu.
Mamy dake tsaye akan dining table, jin alaman takun takalmansa ne yasa, ta dâago kanta ta kalleshi.
Ganin yanda yayi kyau ne kuma, yasa Mamyn sakin murmushi, Cikin kulawa tace.
âBabana yadai, yau na ganka cikin shiri haka fita zakayi ne?â
Kansa ya jinjina, adaidai lokacin da yake gama saukâowa daga kan steps din yace.
âEh Mamy yau zanje company.â
Murmushin dake kan fuskar Mamy ne ya fadâadâa, cikin jin dadi tace.
âAh Lallai Masha Allah Babana ya samu saukâi, amma Ina fatan kanajin karfin jikinka sosai.â
Idanunsa ya dâan lumshe tare da jinjina mata kai alaman. âEh.â
âTo kayi breakfast tukun kafun ka tafi.â
Mamyn ta fadâa tana me nuna masa kujera, tare dayi masa alama akan ya zauna.
Fuskarsa ya dâan shagwabâe, kamar zaice aâa kuma saiya zauna.
Dai-dai lokacin kuwa Jannart ta shigo cikin falon, sanye take da riga da wando ajikinta, saidai wandon irin mai fadâin nan ne, haka ma rigar Wacce take da igiyan dâaurewa, hakan ne kuma yasa lafaffen cikinta bayyana, saboda yanda ta dâaureshi da igiyan, haka ma shape din cikin nata ya bayyana sosai.
Kasancewar kuma kayan nada kalan baki, shiyasa ta yafa siririn mayafi daga kanta zuwa wuyanta.
Sassanyan kamshi take bazawa, shigowarta cikin falonne kuma yasa shi saukâe idanunsa akanta.
Mamy kuwa Ganin Jannart dinne yasa Cikin kulawa tace.
âYauwa Jannart yi saving din mijinki mana, yana sauri zai tafi wajen aiki ne.â
Kai Jannart din ta dâan sunkuyar kâasa, cikin yanayin nutsuwa tace.
âTo Mamy.â
Kaitsaye dining table din da yake zaune ta nufa, saidai koda wasa bata bari sun hadâa idanu ba.
Koda ta kâarasa inda yake, plate ta dâauka tare da budâe food flask, cikin sanyin muryar dake bayyana nutsuwarta tace.
âIna kwana.â
âLafiya.â
Ya amsa mata atakâaice, tare da zubawa kyawawan fararen yatsunta idanu.
Abincin ta zuba masa, bayan ta kammala ne kuma ta turo masa plate din gabansa.
Tare da saka masa apple juice din da ta hadâa, acikin wani dâan glass cup.
Ahankali ya soma cin abincin, tare kuma da dan lullumshe idanunsa, saboda yanda yake jin kamshinta na shiga hancinsa.
Jannart kuwa Ganin ya fara cin Abincin ne, yasa ta wucewa kaitsaye ta nufi sama, Dan dâauko maganinsa.
Ahankali ta tura kofar dâakin ta shiga.
Lumshe Idanunta tayi saboda, wani irin kamshi daya bugeta.
Ga kuma sanyin ac dake busa ko ina.
Dan budâe Idanunta tayi, tare da soma bin ko ina dake cikin dakin da kallo, komai nasa need babu alaman datti, duk da cewar ya kwana acikin dakin, amma saida ya gyara komai kafun ya fita.
Hakanan kawai ta samu kanta da sakin murmushi, kaitsaye kuma cikin nutsuwa, ta wuce ta dauko magungunan nasa.
Koda ta saukâo kâasa harya kammala cin abincin nasa, saidai juice dinne da bai gama shaba, wanda kuma yake sipping dâinsa ahankali.
Kâarasowa kan dining table din tayi, Anutse ta bâare magungunan tare kuma da zuba su acikin tafin hannunta.
Kallonsa ta dâanyi, tare da mikâa masa magungunan, alaman ya karbâa.
Dâago idanunsa yayi ya kalleta, cikin yanayinsa daya saba yi mata magana yace.
âNi yaro ne, da har sai kin bâaremin magani, ni bazan iya dakai na bane akace miki? Sai kiyi ta wani ÉuÉÉuramin magunguna babu ko tausayiâ
Idanunta ta dâan janye daga kallonsa, saboda ayanzu babu wani abu nasa da bata sani ba, saikayi masa abu sau goma, amma baya tabâa gani yanzu zai gwatsaleta ta fahimci zarginta yakeyi ma shi.
Kâwayoyin idanunta tadâan juya ahankali, sau dâaya kuma cikin sigar lallashi tace.
âOkay Iâm sorry take it.â
Hararanta ya dâanyi ta kâasan idanunsa, sanin Mamy na cikin falonne kuma yasa shi, budâe tafukan hannunsa, Anutse ta zuba masa maganin ahannunsa, gudun kada hannunta da nasa su hadâe, tayi hakanne kuma saboda, ita kadai tasan me takeji, aduk sanda ta tuna lokacin da fatar hannunsa ya tabâa nata.
Rayyern kuwa bayan yasha Maganin ne ya mikâe tsaye, tare da dâaukan briefcase dâinsa, cikin sauri yace.
âMamy na tafi saina dawo.â
âA dawo lafiya Allah ya bada saâa.â
Mamyn ta bashi amsa, Cikin kulawa.
Da âAmeen.â
Ya amsa kana ya sakai ya fice daga cikin falon.
Ganin hakanne kuma yasa Jannart dawowa, kusa da Mamyn ta zauna.
Shikuwa Rayyern yana fita kaitsaye company ya wuce,
Koda yaje kuwa ya samu maâaikatan nata aiki, kowa na aikinsa kamar yanda ya dace.
Gaba dâaya maâaikatan sun bada himmansu wajen yin aikin tsakani da Allah.
Domin har anfara har hadâa cattoon's din abubuwa, wanda kowanne kwali dâauke yake da sunan tambarin.
MAI-NASARA.
Komai Yayi masa sosai, hakanne ma yasa shi jinjina kansa, kaitsaye kuma ya wuce office dâinsa dake nan cikin companyn.
Wasu dâan aikace aikace yayi, bayan ya kammala ne kuma ya fito, kaitsaye hospital dâinsa ya wuce.
Bashi ne ya dawo gidan ba kuwa sai kâarfe 10:00 pm dai dai.
Hakan ya faru ne kuma saboda tsayawa da yayi, yiwa wata operation, baya ga haka kuma, ya tarawa kansa aiki sosai, wannan dalilin yasa shi tsayawa, ya dâan rage ayyukan.
Kâasa kâasa ya danna Horn din motar tasa, cikin abunda bai wuce mintuna 2 ba kuwa, aka wangale masa gate din gidan.
Anutse ya tura hancin motar ciki, bayan yayi parking motar ne kuma ya fito.
Tare da Kallon Baba Maudâo wanda shine ya budâe masa gate din.
âBaba Maudâo da kanka, ai daka bari na fito na budâe, sam banaso naga kana wahalar da kanka, saudayawa Idan naga kana wannan aikin sai naji duk babu dadi, please Baba Maudâo ka bari.â
Rayyern din ya fadâi haka ga Baba Maudâo cikin tausasa harshe.
Baba Maudâo kuwa Murmushi yayi tare da dâan gyara tsayuwarsa, kana Cikin kulawa yace.
âHaba Rayyern meye na damuwa kuma, bayan kasan hakan aikina ne, kuma gashi Ari yayi bacci shiyasa.â
Fuska Rayyern din ya dâan kwabâe, hade da karyar da wuyansa yace.
âNi dai Baba Maudâo da gaske banason hakan, banajin dadi Idan naga kana budâe gate inajin wani nauyi a zuciyata.â
Murmushi Baba Maudâo yayi, tare da komawa wajen zamansa ya zauna.
Ganin hakanne kuma yasa Rayyern dâin ma, matsawa ya zauna akusa da Baba Maudâon.
âDâazu Barrister Kabir yazo dubaka da jiki, amma baisame ka ba, saidai yace agaisheka.â
Baba Maudâo ya fadâa yana me Kallon Rayyern din.
Shikuwa Rayyern Ajiyar zuciya ya saukâe, tare da dâan mammatsa hannunsa.
Cikin kuma taushin murya yace.
âIna amsawa, bari na shiga ciki Baba Maudâo, yau duk na gaji aikin office ya gajiyar dani.â
âTo Rayyern Mukwana lafiya.â
Da âAmeen.â
Rayyern din ya amsa, tare da wucewa ciki kaitsaye.
Koda ya shiga main falon nasu babu kowa, hatta su Ramadan da Riyyam nsra duk suna daki.
Kaitsaye kuma shima dâakin nasa ya nufa.
Yana shiga kuwa ya soma rage kayan jikinsa.
Bayan ya shiga toilet yayi wanka ne kuma, ya shirya kansa cikin lallausun kayan bacci.
Bayan yasha Nutri milk ne kuma ya koma kan gado ya kwanta.
Kasancewar agajiye yake ne kuma, yasa yana kwanciya bacci ya dâaukesa.
Washegari.
Arewa24 tv station.
Aunty Fauziya ce ke tafe cikin dâan sauri, saidai kallo dâaya zaka yiwa Fuskarta, ka fahimci cewa tana cikin yanayin damuwa.
Fitowarta kenan kuma daga dakin yadâa labaransu, sukayi Karo da Salman.
Kallonta Salman din yayi, Ganin damuwa afuskarta ne kuma yasa shi dâan tsayawa, Cikin kulawa yace.
âAunty yadai naganki haka, wani abu ya faru ne?â
Kai ta dâan girgiza, cike da damuwa tace.
âSalman bâacewar Jannart ke damuna, tayaya za âace mace kamar Jannart ta bâace bâat kamar kudâi? hankalina yana tashi sosai Salman, ka duba dai irin jamiâan tsoron da Babanta ya bawa cikiyar nemo ta, ga kuma mu da kullum sai munsa cikiyarta, amma har yau babu wani wanda yace ya ganta, abun yana min ciwo Salman, ga mahaifinta asanadin haka ko lafiyar kirki bashi dashi, kwanan nan naji har India aka fita dashi, duk kuma akan lamarin bâacewar Jannart, Ina cikin damuwa akan hakan.â
Ajiyar zuciya Salman ya saukâe.
Dai-dai lokacin kuwa Asiya tazo ta wucesu, saiwani karairaya takeyi tamkar zata bâalle.
Ganin hakanne kuma yasa Aunty Fauziyan wucewa office dinta, take kuwa Salman ya rufa mata baya.
Koda suka isa cikin office din zama, duk sukayi, ananne kuma Salman ya dâago ya kalli Aunty Fauziyar.
Cikin sanyi ya dâan gyara zamansa tare da cewa.
âGaskiya da banyi niyan fadâawa kowa ba saboda sirrine, saidai ke naga gaba dâaya hankanlin atashe yake, akan bâatan Jannart, amma Dan Allah duk wata magana da zan fadâa miki inason ta zama sirri.â
Nisawa Aunty Fauziyaân ta dâanyi, tare kuma da fuskantar sa tace.
âKafadâi duk abunda kakeson fadâa Salman, Insha Allah bazan gayawa kowa ba, kasanni kasan koni wacece zan rikâe duk wani sirri.â
Kai Salman din ya jinjina, tare da dan gyara zamansa kana yace.
âKâwarai nasan hakan Aunty Fauziya, nasan ke ta musamman ce shiyasa ma na yanke shawarar sanar dake, danki cire wannan damuwar dake zuciyarki, agaskiya Jannart ba bâata tayi ba.â
Idanu Aunty Fauziyan ta tsura masa cike da mamakin, Jin abunda ke fitowa daga bakinsa tace.
âKamar yaya Salman ka warwaremin maganar ta yanda zan fahimta.â
âJannart ba wai bâacewa tayi ba, Kâanin Babanta Barrister Kabir shi yayi mata aure, batare da sanin kowa ba, yace kuma yayi hakanne saboda wani dalili nasa maikâarfi, wanda kuma acewarsa hakanne kadâai zai tseratar da rayuwarta, daga fadâawa koman magauta masu farautar rayuwarta.â
Wani irin gauron Ajiyar zuciya Aunty Fauziyan ta sauke, duk da cewar taji mamakin maganan kâwarai, amma kuma taji sanyi acikin zuciyarta.
Numfashi ta dâanja tare da Kallon Salman din, cikin sanyin yanayi tace.
âTo wannan alâamarin da dâaure kai yake gaskiya, amma kuma shi yaron da aka aura mata dâin tana sonshi ne, ko kuma shi yana sonta?â
Kai Salman din ya girgiza, kana asanyaye yace.
âAgaskiya kuma wannan ne bansani ba Aunty.â
Dâanjim Aunty Fauziyan tayi, na yâan wasu dakâikâu kuma tace.
âKayi hakuri Salman, agaskiya ada nayi tunanin duk abunda zaka fadamin zan rufeshi, amma kuma sai gashi yanzu, naji ajikina tamkar akwai wata rawa da zan iya takawa, akan wannan alâamarin, lalle dole zan san yadda zanyi naga Jannart, muje wajen MD.â
Ta kâare maganan tana me mikâewa tsaye.
Hakan yasa Salman rufa mata baya, kaitsaye suka nufi ofishin MD.
Koda sukaje Aunty Fauziyan ce ta kawo masa maganan Jannart, tare da nuna bâukâatar ta nason Ganin Jannart din.
Jin bukâatar tasu ce kuma yasa MD jinjina kansa, cikin kokonton hakan yace.
âAgaskiya inajin kamar hakan bazaiyiwu ba Fauziya, saboda maganan nan sirrice da baâaso kowa ya sani, nima kaina baâa gayamin Dan matsayina ko wani abuba, a'a kawai dai angaya minne saboda, kada Jannart din ta rasa aikinta anan gaba, haka ma Kai Salman kasan dalilin da yasa aka gaya maka, saidai ba damuwa bari mu jarraba, zan kâira Barrister Kabir din muji.â
Ya kâare maganan yana dâaukan wayarsa.
Aunty Fauziya kuwa murmushi tayi, tare dayi masa godiya.
Shikuwa MDân kiran numbern Barrister Kabir yayi, cikin saâa kuwa ya samu Barrister Kabir din ya dâaga wayan.
Bayan sun gaisa ne kuma yake shigar da bukâatar Aunty Fauziyan awajen Barristerân.
Dâan Jim Barrister Kabir yayi, cikin dâan nazari kuma yace.
âTo shikenan MD, amma kana ga kayarda da matar kuwa, kana ga sirrinmu bazai fita awajenta ba.â
Yayi mgnar murya a sake dan yanzu ko mgnar ta fita yana da Éan yaÆini fito na fito da magautanta sai dai baida cikekkun hujja.
âSosai kuwa Barrister, saboda Fauziya D Sulaiman macece mai amana, karanci, tausayi, da saukin kai, kuma akwai rawar da zata iya takawa, musamman Kodan wajen bawa, Jannart din shawarwari ma.â
MD din ya fadâa.
Jin hakanne kuma yasa Barrister Kabir cewa.
âBadamuwa bari na turo muku numbern, amma ko Salman ban yarda a bashi numbern ba, ita matar kawai zaâa bawa.â
âTo Insha Allah.â
MD din ya fadâa.
Nan ya katse wayar, da kaman minti dâaya kuwa sai ga, text na numbern Jannart din ya shigo cikin wayar MD.
Take kuwa MD ya tura mata numbern.
Godiya Aunty Fauziyan tayi masa, cikin jin dadi kuma ta juya ta tafi.
Haka dai Rayuwa ta ci gaba, inda yau ansamu kâarin kwanaki, akan wata dâayan daya shudâe.
Alhamdulillah kuma abubuwa duk, suna tafiya yanda ya kamata, musamman a bâangaren Rayyern, wanda ayanzu kusan kullum Idan ya fita, baya dawowa sai dare, saboda yakanje asibiti da company, shiyasa gaba dâaya ma ko isashshen zama baya samu.
Abâangaren Jannart kuwa rayuwarta take normal, saboda ayanzu ta gama sabo da duk yâan gidan, Masha Allah komai yana tafiya mata daidai sai dai time to time tana tuno gidansu har tayi kwalla.
Acan tashar tasu kuwa, yau din Aunty Fauziyan ce zaune, acikin office dinta, wayarta ce kuma ke rike ahannunta.
Gaba daya ta shiga cikin nazarin kiran wayan Jannart, saboda yanda take kokonto akan ta kira ne ko aâa.
Ayau dai kam ta yanke shawarar kiran wayan Jannart din.
Acan gidansu Rayyern kuwa, yau Nasir yazo, hakan yasa suka hadâu shida Riyyam nsra da kuma Ramadan.
Gaba dâayansu afalon saman suka zauna, haka duk suka cika musu gidan da sowa, saboda Kallon wasan kâwallo da sukeyi.
Wanda kuma sun samu freedom din nasu ne, saboda ganin Rayyern baya nan.
Ciye ciye kuwa ba kalan wanda ba suyi ba, bayan pizza da shawarman da sukaci, hatta sweet saida suka sha, anan kuma cikin falon suka zubar da ledodin musamman Nasir shima dan masifan son zaÆine, haka kuma duk wasu pillows dake jikin kujerun falon, saida suka watsar dasu sukayi musu dâaddâaya.
Bayan sun gama abunda za suyi ne kuma suka fice, batare da sun gyara falon ba.
Rayyern kuwa yaudin adâan gajiye ya dawo gidan.
Wanda hakanne ma yasa bainemi su Mamy ba, kaitsaye ya wuce saman.
Saidai yana shiga, abunda ya gani ya sashi dâan zaro idanunsa.
âWhat is this?â
Ya fadâa yana me Kallon yanda falon nasu ya haukace.
Saurin Ajiye briefcase dâinsa yayi, tare da juyawa cikin sauri ya koma, domin yasan hakan ba aikin kowa bane, saina su Ramadan da Riyyam-nsra.
âMamy Mamy!!â
Da kâarfi yake dâan kâwala kâiran sunan Mamyn, yana me saukowa daga kan steps din.
Mamy kuwa jin kiran da Rayyern din keyi mata ne, yasa ta dâan lekâowa daga kitchine tare da cewa.
âLafiya kuwa Rayyern?â
Fuskarsa ya dâan kwabâe tare dasa hannu, ya kama waist dâinsa, cike kuma da takaici yace.
âMamy Ina su Ramadan, kinga yanda suka yi min kaca kaca da falo kuwa? sunbâata min komai, sunyi ciye ciye sunbar duk wani datti awajen, Mamy wallahi ki kirasu suzo su share.â
Ajiyar zuciya Mamyn ta saukâe, tare kuma da komawa ta zauna, tana me cewa.
âNifa banmasan da yaushe suka fita ba, nasan dai dâazun sunanan harma da Nasir, amma yanzu kam da âalama basa ma cikin gidannan.â
Fuskarsa ya sake kwabâewa, still cikin kame