Showing 63001 words to 66000 words out of 143458 words

Chapter 22 - Gargada So Hausa Novel Complete

M SHAKUR   

19 Nov 2024

598

ya zauna ganin yanda suke zazzaro idanu yasa yace “ku kwantar da hankalinku bawai wani abu bane dalili yasa nakiraku, na farko dai banda ciwukan data samu daga accident din nan yarku batada lafiya, mun gano tanada Hypertension wato hawan jini” daga Baba har Ammi atare sukace “hawan jini!”? Gyadamusu kai Dr yayi yace “yes BP yayi high sosai shinema dalilin dayasa na kiraku tunda nasan kune iyayenta in tambayeku ko akwai wani tunani da yarku keyi ko akwai takamaiman abinda ke damunta?” Shiru daga Baba har Ammi sukayi cus they know amsan tambayan Dr, abinda ke damun Hawwa is rashin aure da yawan tunanin dalilin, Ammi kuma tasan harda fadanta da Ni’ima yahadun mata but bata taba sanin Hawwa nada hawan jini ba, and she’s sure Hawwa ma batasan tanada shi ba danda zata gayamata, ganin sunki magana yasa Dr yace “I guess kunsan abinda kesa yarku damuwa dakuma tunanin datakeyi, banson na shiga family issue dinku dan haka bazan tambaya ba, amman dai kusani hakkin iyaye ne su kauda duk wata matsala da damuwa daga jikin yaran su especially idan damuwan yasoma haifar musu da cuta ajikinsu, arayuwan nan there’s nothing like yarona yayi girma he can take care of kanshi, naga kasa shekaranta 29 da 10months haka karubuta mana, Baba yaro ko shekaransa dari yana bukatan iyayensa su kula dashi, ku kula da ita dan Allah, ku taimakama yarku cus BP ta yayi high sosai, ku bata farin ciki, ku kauda mata damuwan and support her, BP yatashi yasa tai loosing control kanta tana tuki harta hada hatsari, hawan jini muguwan cuta ce da tashi daya takan dauki ran mutum, dan Allah akiyaye, babu maganin dayafi aiki kaman maganin iyaye a rayuwan yaransu, menene maganin nan danake magana akai? Shine support na iyaye da love da mantar da yaransu damuwa da bama yaran farin ciki da natsuwa……” Dr yaciga da advising Ammi da Baba sosai……

Around 1:30 yashigo asibitin parking yayi yasauko yawuce ciki, ganin baiga Baba ko Ammi wajen ba yasa yayi wajen dakin da Hawwa keciki ya leka ta glass na kofan idanunta biyu amman idanun sun kankance sosai irin na mara lafiya tana kallon waje guda tai shiru tana tunani, daga ita sai dogon ringan jikinta ga gyalenta an rataya wajen bag hanger dake gefen wardrobe na dakin gashin gaban goshinta dukya kwanta luplup ansa bandage a goshinta hakama hannuwanta duk bandage wani kalan sonta da bala’in tausayinta ne ya mamayeshi kaman ya shiga ya karbe ciwon daga jikinta, hannunshi yakai yabude kofan gently yana shiga ciki, ahankali Hawwa ke juyo da kanta kadan da kadan dan har yanzu kanta na banging saidai ba kaman dazu ba so da kyar take juya kan kallo kofan dataji an bude tayi tahada idanu da Baban Yaseer daya shigo yana mata kallon tsantsan so kaman zai hadiyeta, faduwa gaban Hawwa yayi kaman taga dodo tashiga mikewa tana tashi daga kwance dasauri ya yunkuro zai taho yace “don’t move Hawwa ina zaki”? Da muryanta da baya fita sosai cikin rashin lafiya tace “karkazo nan!” Chak ya tsaya daidai tana tashi zaune da kyar idanunta har layi suke kanta yafara kwankwatsa sabida yanda ta tashi, dafe kanta tayi da hannunta da drip ke makale tana damtse idanunta cus her head is pounding kaman ana daka a turmi da kyar tace “kafita Baban Yaseer!” Cus bamata kaunan ganinshi arayuwanta, kallonta Baban Yaseer yake kaman yau yafara ganinta ahankali yace “Hawwa nafita kuma why? Nine fa? It’s Aliyu, Kinsan yanda nake cikin damuwa kuwa?” Ganin yanda yake wani irin kallonta zuwa kirjinta dan andan zage zip na bayan dogon rigan, tashin datayi yasa gaban rigan ya zazzago sama saman kirjinta na showing, da sauri tarike gaban rigan da hannu daya dayan hannun takai bayanta taja zip da mugu karfin hali Hawwa ta sauko da kafafunta daga gadon adan tsorace Baban Hawwa yakara yunkuro wa zai taho yace “ina zaki Hawwa sit please you’re not well, me kikeso ki dauka? I can give it to you”hannunta daya akai dayan ta daga ta nunashi tana haki tace “kafita I don’t want to see you! Stay away from me Baban Yaseer” yana kallonta gently and softly yace “har abada bazan taba ita staying away from you ba Hawwa” ganin yacigaba da kallonta yasa Hawwa ta diro daga gadon danta dauki gyalenta datagani a hanger kawai ta zube akasa babu karfi ajikinta ko digi kaman kafafunta basa aiki tai wani kara tana kama kanta da duka hannun biyu tace. “Kainaaa uhnnnnnn”
Dagudu Baban Yaseer yayi wajenta without having a second thought sabida tsabagen yanda yarude kawai yakai hannunshi yadauki Hawwa dake kasa idanunta a kulle takama kanta da duka hannuwa biyun jin an dauketa yasa Hawwa tabude idanunta da kyar dan kadan suka hada ido da Baban Yaseer hawaye masu zafi ne suka fito daga idanunta cikin muryan da baya fita bamata da karfi sosai tace “Baban Yaseer kaji tausayina kafita daga rayuwana! Ka ijiyeni! Stop touching me, ka ijiyeni nace” tai maganan tana lumshe idanu ta rirrike kanta, yanda hawaye ke fita daga idanunta tana magana kasa kasa kaman yar baby ya kashema Baban Yaseer zuciyan he just wants to kiss her and hug her so damn tight, kofa yakalla ganin babu kowa dake tahowa yasa ahankali yashiga sauke fuskanshi zuwa daidai fuskan Hawwa he just love Hawwa and feels like kissing her baimasan meyake ba, fuskanshi na dab da sauka anata akai mahaukacin bugokofan dakin dayasa yadago kanshi da gudu Hawwa tabude jajayen idanunta da kyar suka kalli kofan suna hada idanu da Ni’ima data bugo kofan tana sanye da abaya idanunta sunyi matsiyacin ja tana kallon Baban Yaseer daya dauki Hawwa ajikinshi kaman yanda yake daukan su Yaseer da Yasmeen, adaidai lokacin kuma Baba da Ammi na zuwa wajen duk sukaci tura suka tsaya abayan Ni’ima duk suna kallon Baban Yaseer, yanda gaban Hawwa yahau bugawa ganin Ni’ima ta dauka kirjinta zai fashene da sauri ta shiga kokarin kwace kanta batama da karfin motsi abin gwanin ban tausayi tana kallon Ni’ima Baban Yaseer kuma yariketa gam ajikinshi yana kallon Ni’ima, wani kalan mosti fuskan Ni’ima yafara tana huci tace “ba kiss zakuyi ba”? Tayi mahaukacin ihu tana daukan kujeran datagani adakin tayi kansu tace “ka sumbace ta mana Aliyu…….”

THIS BABAN YASEER IS HE TRYING TO TAKE ADVANTAGE OF HAWWA? CUS WAT WAS THAT DAYAKE KOKARIN YI PLEASE???

I GET YANA SONTA SOMA MAI ZAFI BUT COMMON SOYAYYA BA HAUKA BANE??

IDAN KENE BABA KO AMMI WHAT WILL YOU DO???
[9/22, 4:58 PM] M Shakur: 💫GARGADAN SO💫


✍🏻M SHAKUR


EPISODE 3️⃣5️⃣


JOIN MY FACEBOOK GROUP

https://www.facebook.com/share/g/MhrpcozubuW3sxg8/?mibextid=K35XfP



Kyakkyawan baccin gagaran Khaleel yayi danko 30 minutes baikaiba ahankali yabude idanunshi yana juyowa daga rub da cikin dayayi yana kallon saman dakin baimasan meke damunshi ba, normally yakamata yayi bacci har zuwa 4 na yamma but yakasa baccin tunanin yarinyar chan kawai yake, kaman her sick spirit na kiransa, hannunshi yadaga yakalla da Hawwa ta ciza lumshe idanu kawai yayi yabude sannan yatashi zaune yasauka daga gadon, boxer yacire ya yar awajen yawuce abinsa naked yafada bathroom yayi wanka yafito yawuce walk in closet dinshi dake kama dawani exquisite boutique, shiryawa yayi yazaro Balmain monogram print flowing shirt dakeda kalan black print din kuma white yasaka, yadauko dogon denim wando na Diesel yasaka daya zauna ajikinshi da kyau dasdas, agogonshi yaciro from drawer na designers watch dinshi, yacire Furlan Marri yasaka dayama hannunshi kyau, yadan juya yakalli showglass na takalmansa kaman shago yasa hannu yaciro wani suede flat takalmi na Birkenstock Boston, sannan yadau turarukanshi yashiga fesawa yadauki brush yana taje kansa ya shimfada dadduma yayi sallan azahar sannan yamike yabude kofa yafito yasauka kasa, chan falo yayi yana kallon agogon hannunshi is 1:30 ba kowa afalo probably Mommy ta kwanta ko tana spa nasu ana mata massage, kofa yawuce aka budemai yafita wajen black Mercedes Maybach S class dinshi yayi dake kyalli tsabagen kyau da kudi, da sauri security nashi suka taho wajen yakalli Salman dake budemai motan yace “when did you come back?” Dasauri yace “not quite long Sir everything is sorted babu wani matsala motanta I called auto shop sunzo sun dauka har an fara gyaransa” yatsine fuska yayi kadan baice kome ba ya shiga bayan motan ya zauna, Salman ya maida kofan yarufe yakoma gaba yashiga ya zauna driver shima na shiga mopol dinshi ma haka, anatse yace “hospital” Dasauri driver yace “yes sir” yatada motan suka fita yana kallon hanya chan yace “music” waka aka samai yafarabi yanadan shaking kai yadaga wayanshi yayi selfie yasa a instagram story nashi hankalinshi kwance.

*
Kansu Ni’ima tayi da plastic chair data dauka dasauri Baban Yaseer yajuya yana sauke Hawwa agadon yajuyo yasa hannu da zafi zai karbe kujeran ta zame tai gefenshi zata rafkama Hawwa dake kallon Ni’ima completely heart broken Baban Yaseer yabude hannuwanshi ya tsaya agaban Hawwa, Ni’ima tace “kama rungumeta idan zakayi amman saina halakata, saina halakata wlh, Allah ya kasheki ya dauki ranki sai inga wazakaso Aliyu? Inaso naga ko zaka bita kabari kuyi soyayya, ba sumbatar juna kukeso kuyi ba kuka ganni kuka wayance? Ka tashi agabana” hannu daya Baban Yaseer yasa ya fizge kujeran daga hannunta yana kokarin ijiye chair a gefe tabi gefenshi zatayi kan Hawwa taji an riketa gam juyowa tayi daidai Ammi na dauketa da mari jikake tasss! Hawwa ta zabura tana kokarin mikewa ganin yanda Ammi ta zubamata mari but takasa tashi, Ni’ima ta dafe kuncinta tana kallon Ammi da jan idanu, Ammi tace “kika kara maganan banza anan saina sake daukeki da wani marin shashasha” Ammi takalli Baban Yaseer dake tsaye yana kare Hawwa cikeda fushi tace “tashi agaban yarinya na bar wajen nan, tashi nace!” ba musu yatashi ahankali yakoma wajen kofa ya tsaya ranshi in yayi dubu yabaci sabida abinda Ni’ima keyi, Ni’ima takalli Ammi idanunta jajir har lokacin kallon Ammi take tace “kika mareni Ammi? Ko uwata bata taba bari naba saike”?Ammi na kallonta jin maganganun datake rai abace tace “saisa ni nake tayata bawa diyarta tarbiya, kika karamin gara gara anan saina sake daukeki dawani marin, you’re very, very and very stupid Ni’ima hauka kikeso kiyi sabida namiji? Eh?” Shigowa Baba yayi zuwa wajen ya tsaya kusada Ammi babu alamun wasa akan fuskanshi yace “meke faruwa Zainab”? Ni’ima Ammi ta nuna tace “Malam Ni’ima tana daya daga cikin dalilan dayasa Hawwa kenan wajen” azuciye Ni’ima tace “menayi? Nakira yarku na yanke alaka da ita, naja mata layi, bansonta arayuwana dayake mayya ce, bakar mayya mara zuciya ce ita wacce tai kwantai haka ta dinga bina tanajan gwuiwowinta akasa tana rirrikeni tana kuka tana karna rabuda ita, nikuma na tattake hannuwan banzan nawuce nayi tafitata” sosai Baban Yaseer ke kallonta hakama Baba da Ammi yanda take magana kaman ba Ni’ima ba, can a sweet person turn monster over night? Sabida namiji? Ni’ima tace “mijina nawane kadai wlh, ba best friend ba ko kanwata ce saina jamata layi wlh, kugayama yarku tafita daga harkan mijina” nuna Baban Yaseer Ammi tayi tace “ga mijin naki nan ai shiya kawo kanshi nan, dau abinki kubar nan” cikeda rashin kunya tace “eh zan dauki abuna amman saina gama, yar iskan yarku kokarin sumbatan mijina take, mara kamun kai da natsuwa, Hawwa zata iyama maza fyade sabida tsabar bukat……” tsawa Ammi daka mata tace “Ni’ima!” Rai abace sosai tace “nasan waye Y’ata! Jedai ki bincike mijin naki, munsan kalan tarbiyan da muka bata” ganin Ni’ima zatai magana tabi Ammi da chachan baki yasa Baba yakalli Baban Yaseer strictly yace “Aliyu dauki matarka kutafi, mungode Allah saka da alkhairi” cikeda tsantsan rashin kunya Ni’ima tace “ba dole kace ka gode ba anci kudin mijina an koshi, yazo yabiya kudin asibiti da kudin magani, mayu kawai kwadayayyu masu neman kai da yars……” fizgota Baban Yaseer yayi yajuyo da ita tai facing nashi ganin abin nata yazama hauka yadaga hannu zai kwasa mata mari Baba yace “kul!”


Washegari Sunday around 11 tafito su Hamza na samata komi a booth, Baffa yace “Hawwa ayi tuki ahankali kinjini” murmushi tayi tace “toh Baffa na” Ammi tace “Allah kiyaye hanya, dan Allah banda gudu” Gyadamata kai Hawwa tayi su Ramla suka rungumeta tamusu sallama tafito, text tama Ni’ima tace “gani nashiga hanya zan dawo office gobe”.

Karfe biyu dawani abu anadai neman karfe uku Hawwa ta shigo Abuja hanyan hospital din su Ni’ima tawuce direct ta shiga tai parking ta kashe motan, wayanta tadauka tafito abayane ajikinta baki tawuce ciki office din Ni’ima tawuce tareda knocking tana budewa wata nurse ce aciki tana ganin Hawwa tai murmushi tace “wajen Ni’ima kikezo? Bakuyi wayaba ai batanan yau is her off” amutunce Hawwa tace “okay okay nagode” tajuyo tafito motanta tashiga tafita daga hospital din wlh she’s so worried rabon datai magana da Ni’ima tun Friday wani irin fushi Ni’ima keyi da ita haka, hanyar gidansu Ni’ima tayi har zuwa layinsu mai kyau, gaban gidansu ta tsaya tai horn maidaidaicin gidane mai kyau ga babban bakin gate nasu, lekowa mai gadin yayi Hawwa tadanmai murmushi tana jiran taga yabude gate saitaga yabude karamin gate da fara’a kan fuskanshi yace “Hajiya barka da yamma” gyadamai kai tayi tace “ya kuke” yace “Alhamdulillah” saikuma ya tsaya sakaka yana kallonta Hawwa tace “budemin gate ko basanan ne”? Bazai taba iya maimaita abinda Ni’ima tacemai ma hakan yasa dasauri yace “eh basanan tun safe suka fita” danjimm Hawwa tayi kaman daga sama sukaji muryan Yasmeen ta tsandala ihu tana kuka wayyo kafanta dasauri maigadin yakalli gate saikuma yajuyo yasauke kanshi kasa, Hawwa dake juyo muryan yaran tace “kace basanan ba muryan Mims naji na kuka ba” dan sosa kai yayi da hannu kanshi na kasa yakasa kallonta yace “ahhhmm Madam tacemini duk randa nakara barinki kika shiga gidan abakin aikina kiyakuri Hajiya” dasauri da kunya yajuya ya shiga gidan tareda maida gate din yarufe Hawwa tai shiru tana wajen she don’t even know wat to think, her mind just went blank wlh takai minti ashirin awajen kafin tadan fuzar da iska taja motan tabar wajen.
[9/23, 8:52 PM] M Shakur: 💫GARGADAN SO💫



✍🏻M SHAKUR


EPISODE 3️⃣7️⃣



Kusan 5min Khaleel da Baba sukai ahaka sannan yadaga kanshi daga kafadan Baba yakalli Baba yace “kahuta? Kadena damuwa”? Gyadamai kai Baba yayi yace “nahuta Ibrahima” sauka Khaleel yayi yadauki crutches din yabashi Baba ya karba suka fito tare, Ammi bata wajen hanyar dakin sukayi Khaleel yaci tura dagadan nesa Baba yajuyo yakalleshi yace “bazaka shiga ba” dan sosakai yayi saikuma ya dauke kai ahankali yace “uhmmm kunyan nakeji” dariya Baba yayi irin na manya dinnan jin maganan dayayi yace “kunya? Wai kunyan Ammi”? Dasauri Khaleel yajuya yana gyadamai kai yace “bye Baba sai munzo anjima” kafin Baba yayi magana har yayi kofa su Salman dake wajen suka budemai kofa yafice suka bishi Baba yace “jama’a wannan yaro akwai shiga rai, Ya Allah inama Hawwa na kwadayinsa sosai, Allah inhar alkhairi ne auren nan kasa ya tabbata yau” yayi maganan a yana shiga cikin dakin da murmushi kan fuskanshi yayi inda Hawwa take dake bacci anmata allurai da dama, Ammi na zaune ta buga tagumi ganninshi yasa Ammi takalleshi da damuwa akan fuskanta, Baba yajuyo yaja kujeran plastic chair ya zauna cikeda farin ciki yace “kidena damuwa Zainabu kiyi addu’a inhar Ibrahima rabon Hawwa ne kuma mijinta ne yau za’a daura mata aure” dasauri Ammi ta kalleshi tace “waye kuma Ibrahima Malam”? Labarin Khaleel yashiga bata all abubuwan daya sani, tai shiru Allah yasani yanda taga Khaleel yayi da Baba taji ya burgeta, banda haka Ni’ima said some disturbing about Hawwa, ita mace ce, sannan ita uwace, ko yara irin su Ramla sunsan sha’awa yanzu, Hawwa ba yarinya bace, babu bawa da baida sha’awa, tanaso Hawwa tai aure ta sami natsuwa da kwanciyan hankali, ba maza Hawwa kebi ba, bata iskanci so dole ne a irin shekarunta taji yana bukatan namiji, tabbas Hawwa na bukatan natsuwa, abun yamata, 50/50 Ammi keji azuciyanta, one side na zuciyanta ya goyi bayan auren sabida abubuwan da Ni’ima tafada especially bukatun Hawwa kafin yarsu tafada halaka, kota kauce hanya amata auren, zuciya ba kashi bane tsokace duk yanda takai da karfin imani shedan zai iyacin galaba akanta wata rana idan takasa hadiye sha’awar, another bangaren zuciyanta kuma zaiso ayi bincike akan koma waye Ibrahiman but idan aka tsaya bincike kafin agama yaron yagudu ko yace yafasa fa? Cus abinda ke faruwa kenan dazaran sunzo su gudu, yagudu yaushe Hawwa zata kara samin wani yafito ga Ni’ima ta tasata agaba? Sotake tai aure tai nisa da anguwan ta huta da bakin cikin Niima, she kind of reason with Baba sabida yanda samari ke guduwa gwara su kama Khaleel dinnan as earlier as possible, zata taya Hawwa addu’a Allah ya albarkaci auren ya kauda fitina su sami fahimtan juna, amman dai tai auren Hawwa na bukutan natsuwa kafin tafada wani hali, ganin tai shiru tana tunani yasa Baba yace “kin yarda Zainab? Dan banso mukara fada yanzu komi yawuce, ni da kene iyayen Hawwa, banda mu batada kowa, ada nai kuskure dana dinga bala’i dake, gayamin abinda ke ranki

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login