Showing 132001 words to 135000 words out of 143458 words

Chapter 45 - Gargada So Hausa Novel Complete

M SHAKUR   

19 Nov 2024

605




Gidansu tayi, tana kaiwa unguwansu babu kowa a kofar gidan amman kunya yahanata fita, ga idanunta sunyi jazir, takai almost 10min a motan sannan ta kalli fuskanta a mirror lips nata sunyi pink yirr, idanunta sunyi ja, tadai daure kafin su Baba suzo waje tabude motan tafito tashiga gida tana tafiya awaware tanadan dingishi, tana shiga compound nasu mutane, su Miemie suka fara rungumeta ga jama’a agidan ana bude akwaitinta da bamata san an kawoba, ga yan anguwa ana ganinta aka fara ayiriri Ammi data ganta fitowanta daga dakin Aminu kenan ta taho wajenta da sauri tace “amarya ba lafiya sannu an sallamoki muje kihuta” Ammi ta kamata suka wuce daki, Ammi tabita da kallo ahankali tace “ya jikin? Shiya kawoki”? Gyadama Ammi kai tayi tana sauke kai ba bakin magana tai zuru zuru, Ammi da hartaga shedan ruwan gashinta ta saman hijabi tace “kinsha asibiti bari nakai miki ruwa bayi kiyi wanka ko sannu zakici abinci akawo miki?” Girgizama Ammi kai tayi da kyar tace “wanka zanyi nai bacci” gyadamata kai Ammi tayi tace “akwai ruwan zafi bari nahada na kai miki” Ammi tafice ruwa mai zafin gaske takai mata abayi da botiki daya daban na sirki sannan tadawo ganin Hawwa tayi harta cire kaya tadaura zani tasa another hijabi daban, Ammi tabi dakin da kallo tace “ina kayan da kika cire na bada awanke”? Dasauri tace “uhmm ahh suna cikin akwati na ki barshi zan wanke” Ammi tace “toh muje” kamata tayi daurewa tayi tabi Ammi har bayi ta kaita Ammi tai murmushi kadan kawai ta dawo tadan gyaramata gadon ta kakkabe taje tadawo da ita daki kuma tafita, Hawwa tacire hijabinta ahankali tadauki ribbon ta kulle gashinta dayake sharkap tadauki dankwali na atampa ta kulle kan kar agane da ruwa, dogon riga har kasa na abaya tasa ta kwanta sai bacci.


Khaleel yadinga kiranta rannan taki dauka tama maida wayan silent mode, rannan bacci tayi da daddare mai kyau har gari yawaye ko farkawa batayiba batasan me Khaleel yayi ba but dai kaman ta zubar da abinda ke damunta da daddare.

Da sassafe yau Wednesday aka fara shirye shirye henna day, still tayi using hot water zafin yaragu sosai tasoma dainaji, an aiko da bridal dresses nata jiya da daddare, tayi wanka kenan tana cikin saka HKG atampan dasu Hafsa suka fito mata dashi daga akwatinta na henna party Aminu ya shigo yace “Ya Hawwa Khaleel na waje yakawo miki Noor” faduwa gabanta yayi sosai dan kallonshi tayi sai kuma tace “okay” kanninta ko wanne yashiga makale dariya shikuma Aminu da gulma yace “suna miki dariya Ya Hawwa” kallonsu tayi aiko suka bushe da dariya Hafsa tace “ayiriri amarya” hararansu tayi tadauki gyale maroon tayafa kan atampan wlh tayi kyau tana tafiya ahankali sai kanshi take tayi waje, a zaure taga Khaleel da Noor da katon box na kayanta, tana ganin Hawwa tai wani ihu tai tsalle Hawwa ta dauketa tana murmushi Noor tace “My FAA” haderai Khaleel yayi yace “careful Noor stop rough handling my wife kaman yanda kikemin batada karfi kaman ni, besides she’s sick” dan hararanshi Hawwa tayi batare data kalleshi ba tana kallon Noor tace “don’t mind him your FAA have power” kankameta Noor tayi saikuma ta mata kiss a kumata tace “I love you soo much FAA, you look super duper beautiful right Dad”? Khaleel na kallon Hawwa kaman zai hadiyeta yana tuna abinda yafaru jiya tsakaninsu yace “right princess, she’s beautiful external and internal” sauketa Hawwa tayi da sauri tazo wajen takai hannu zata karbi akwatin Noor sabida su koma ciki kafin yafara iskanci wannan daya fara maganan banza gaban yarinya kawai Khaleel yajawota zuwa jikinshi and just give her a tight hug daidai Baba da Aminu na shigowa zauren hakama kanninta su Hafsa kawai suka fasa ihu. “Wuyuuuuuuhuuuu” Baba yawani kume murmushi akunyace Hawwa ta fizge kanta kaman zata nutse akasa ganin Baba da kanninta sunga yanda yake rungumeta, Baba yama su Hafsa dakuwa yace “kunci gidanku me kuke haka”? Noor sai washe baki take tana kallon Dadynta da Hawwa, Hawwa tai sauri zataja jakan wlh Khaleel yakasa daurewa dudda gasu Baba kaman wanda Hawwa tama magana yakama hannunta yace “karki tafiiiiiii” awani shagwabe sai kawai su Hafsa sukahau “ayiriririiiii” Baba yadan kwashe da dariyan manya kadan yadaga sanda zai rapka musu suka kwasa aguje sukai cikin gida Baba yace “Noor muje na kaiki dakin Mamanki tunda Babanki na magana da ita” dasauri Noor tabi Baba hakan yasa Hawwa tajuyo cikeda masifa still taki kallon idanunshi tace “mehaka kakemin gaban mutane”? Kaman zaiyi kuka yace “I’ve missed you, baki daukan wayana, baki magana dani why? Mena miki wai”? Akufule Hawwa tace “I don’t accept you, I don’t accept wannan auren, ban sonka nagaya maka” shiru yayi yana kallonta yakasa magana, kawai Hawwa ta fizge hannunta da jakan tawuce cikin gida abinta, nan fa aka fara henne party ga komi Juzzyfabevent event takawo, hatta su zubo da bottle water, kunun aya, popcorn amsaka sticker sunan Hawwa da Khaleel so lovely, matan ta iya decoration da kowa yashigo mamaki yake compound din gidan Baba Juzzyfabevent ta komar haka, she sabi the job. Ana playing waka compound na Baba da girma so set up yayi kyau professional masu henna da aka kawo suka fara mata ana rawa, Noor na rawa dasu Miemie, Hawwa sai kallon Noor take tana kama da Khaleel tanada kyau kaman shi, dasauri ta girgiza kai tana gayama kanta me ruwanta da kyawunsa, duk wnada keson lalle zama kawai yake amai, Hawwa kawai bin kowa da kallo take especially yan uwanta barinma Ammi da Baba, Ammi stood as her Mom, komi ita keyi, ita ake tambaya, yan unguwan na Maman Amarya kawo gishiri, kawo omo, abada this and that duk haka suke kiran Ammi, Baba na farin ciki bini bini yashigo yaduba zanen da akema Hawwa yatafi yakara dawowa yace amata mai kyau, yasake dawowa yace azana sunan Ibrahima atafin hannunta, har aka faramai dariya, Hawwa kawai taji kuka na taso mata, she wish aure ne da mutumin arziki wanda yasan darajan mace, all this prep, farin cikin da Baba keyi, dasu Ammi da yan uwanta Allah yasa tamayi 1month bai saketa ba.
[10/6, 7:32 AM] +234 903 908 6385: EPISODE 7️⃣1️⃣



Har dare party akeyi bamatasan yaushe aka sai generator agidan ba, itafa komi yi akeyi batasan ya aka samu ba dan su Ammi sun daina sata a lissafi maybe Khaleel yakawo, wanka tayi Munawwarah ta turareta ganin su kadaine adakin tace “Ibrahima yadan rage miki jaraban ko”? Kunya kama Hawwa tayi ta sauke kai kasa da gangan taba Hawwa wani magani a cup dudda Ammi tace adakata a daina bata haka Hawwa tasha tana tane baki suka gama komi tawuce taje gado, yau su Ramla ma sun sauka kasa daga ita sai Noor, Noor is so happy kaman ba yar gidan masu kudi ba, Ramla sun mata wanka tasa kayan bacci suna wasa kowa na son yarinyar she’s so sweet, abubuwan da aka samata a box ma bataci ba, tuwo da miyan kuka da aka dafa agidan taci cikinta kaman zai fashe saida Hawwa tama hanata ci ta hakura.

Kiranta Khaleel yahauyi awaya taki dauka, tai lamo tana sauraron su Hafsa dake planning dan gobe bridal shower kanninta sai planning suke tana kallonsu ita yar kallo ce kawai.

Washe gari Alhamis aka fara baki yan uwa da abokan arziki, yan uwan su Baba daga kauye sunzo wayanda ko bikin su Hafsa ma basu zo ba amman anzo na Hawwa, yan uwan su Ammi ma haka sunzo yan Bauchi kuma sun nunama Hawwa tanada dangi, sun kawo waina tundaga Bauchi, ga yan uwan Baffa ma mijin Ammi duk ya gayyacesu duk anzoma Ammi biki, gida ya kachame abubuwa kawai ake kawowa drinks, menene, menene, banda girkin dasu sukayi Juzzyfabevent suma sunyo abinci cus they also handle catering services, babu kalan abincin da babu, kowa dazaizo yanada gifts, ko yaushe akai wannan planning din oho yan uwanta suma kowa ya gayyaci mutanensa da friends nasa, Aminu ma ya gayyaci abokansa na school dudda babu daurin aure akwai event.
Wuraren 4 aka shiryata makeup artist tazo Hawwa sai kallon ikon Allah take dan batasan daga ina takeba kowa yaturota akama Hawwa makeup aka shiryata cikin gold gown kunga Hawwa aka fara rawa kawayen kannenta ne kawayenta dan batada kowa ga DJ, ga masu hoto ga MC, ga jama’a ga abinci akai wasa akai quiz akan amarya aka gama games na balloons, it was fun, Hawwa tagaji still taki waya da Khaleel.

Yau Friday budan kai a hall za’ayi tun around 1 motoci luxurious bus na yan gayu sukai layi a unguwan kai mutane zuwa venue ga kaya an kawoma duka kanninta ashobe harda su Noor ga kayan Ammi na yan gayu, kasa daurewa Hawwa tayi tace “waya muku kayan nan”? Doddo tace “mijinki duka harda kayan ranan asabar yama kowa da takalma da jaka, wasu ma’aikata sukazo suka aunamu muma mu zama yan gayu” shiru Hawwa tayi aka shiryata cikin wani traditional clothes na atampa blue light and dark daya mata bala’in kyau ga katon lullubin atampa da aka dauramata akai, da Ammi tashigo taga Hawwa sai hawaye yataru a idanunta duk yanda taso ta daure saita fashe da kuka Hawwa tafashe da kuka itama Ammi tace “inama Mamanki na raye taganki Hawwa kinyi kyau Allah miki albarka, Allah sanya albarka a aurenki” kankame Ammi tayi da kyar aka hanata kuka aka gyara makeup din kafin finally aje asata awani arnen sabon jeep gal aka tattafi Umma kawai aka bari agida da Baba, Event aka fara harda yan uwan su Khaleel but banda Mom but Maman Sam da Hajiya Daraja na wajen, duk wanda yazo daga side na Khaleel dadan korafinshi Khaleel na auren yar gidan talakawa ya auro da akaga Hawwa sai ayi shiru cus Hawwa ta hadu ba karya, Khaleel carry better eye go market, chan akai annoucing zuwan ango yaye lullubi, waka aka saka na burina by Hamisu breaker saiga Khaleel yashigo yana sanye da dark blue yard da babban riga dayamai kyau na bala’i yasa hula ga manyan abokanshi Moh da Sam da sauran abokanan all in white da black huluna kana ganinsu ka ga big boys, mic yarike yana murmushi yana kallon Hawwa yafara mata wakan yana nunata da hannu filled with love ba kunyan iyaye yace.
Babban burina ki kasanche dab da ni
In za ki kirga masoya ne ki sanyo dani
Ki duba kan ki ana kallo na majanuni
Ni kuma nace indai kai naki ne ban fadi ba
Sako ya bayyana ni tun daga zuciya
Sannan kaunar ki tana kaman zuciya
Kin kama mini kurwa ta tun jiya
Har ya kai matsayin bana samun lafiya….. yawani nuna kirjinshi yace
Kin shiga raina
Kin zauna dan kin sami guri
Naji kiranki
Na amsa kuma nazo da wuri
Kece farko kuma kece karshe
Bishiyar nan tai girma wadda kikayi mini dashe daidai ya iso gabanta yawani duka yana kallon fuskanta yanuna kanshi yace
Bana ji bani gani bana son mai kushe
Buri na rayu dake har numfashin karshe
Kin rikita duka tunani na
Taimaka ki bani gurin kwana
Son ki ya hana mini bacci na
Ina ganin ki har a mafarki na
Son ki yanai mini dadi ban son mu rabu
Ki jaddada jarumta ta ki nadan kambu
Bani da komai sai ke
Ina tafe ya wa wani falke
Ina duhu ki kunnan haske
Ina na je dake?
Ihu akahau yi na bala’i awajen na Khaleel is super romantic, he’s just madly in love da Hawwa, yamika hannu Moh yabude jakan LV dasuke rikeda shi yafara zubama Hawwa dollars Mom Sam tarike baki da sauran kawayen Mom like dama Khaleel ya iya soyayya haka? Ya iya wakan hausa haka wat? Rufe Hawwa sukayi da manni shida abokanshi, MC tace “abudemai fuskan amarya” Babban Aminiyan Ammi Anty Lami ta zo tabudemai fuskan Hawwa fuskan Hawwa da Khaleel yagani kawai saiya rungumeta baimasan meyake ba zokaji ihu DJ yasaka musu kida MC tace “Ango fito da amarya ku taka” dayake kamu ne wakokin hausa ake sawa komawa baya su Moh sukayi Hawwa bataso ta tashi amman haka Khaleel yadagata yana rungume da ita kunya ya gama kasheta, yafito da ita dance floor kanta akasa daidai DJ na sakin beat yasaka wakan Mai kishina na Sadiq Saleh kaman Khaleel aka samawa kawai kama hannun Hawwa yayi yawani jawota jikinshi yakama waist nata ko kadan baida kunyan iyaye, Hawwa namai wani irin kallo da jama’a ke gani na soyayya ne but shi yasan na haushi ne dana mehaka, yawani lumshe mata idanu yana daga mata gira daidai anfara wakan yace”
uhm Uhmmmmmmmmmmmmmm
Uhmmmmmmmmmmmmmm
Uhmmmmmmmmmmmmmm
kunga inajin dadi
inajin dadi na samu muradin raina tana kishi na nidai
kunga inajin dadi inajin dadi na samu muradin raina ya na kishi na nima
Uhmmmmmmmmmmmmmm
Uhmmmmmmmmmmmmmm
sonki ya fattatakenii harna durkusa shiya addabeni haryasa na fallasa Ni Dake mu raini so takai mu kyankyansa nayi binciken kamarki babu na rasa”
woooo haukacewa akayi a hall din kawayen Mom su Hajiya Daraja da Mom Sam suka taso ana ciro bundle na kudi dan Khaleel da Hawwa sunyi kyau, abokannan shi suka taso su Ammi da Jama’anta suka taso dan Khaleel yabama Ammi sababbin kudi dayawa bana wasaba tai manni cus itace Maman Amarya, Khaleel ganin an tattaso za’azo kawai yawani bude babban riganshi yajawo Hawwa cikin jikinsa yarufe babban rigan da ita yana rawa.


Tundaga kan Abokan Khaleel da family shi babu wanda yataba ganin Khaleel this happy, su Moh at first sun dauka this marraige is just to teach the police girl a lesson but yau different abu suke gani a idanun Khaleel cus this is love! Khaleel has never been this happy, sosai Hawwa take kallon Khaleel ganin farin cikin dayakeyi and he looks damn handsome bata taba ganinshi da manyan kayaba sai yau.
[10/6, 7:32 AM] +234 903 908 6385: EPISODE 7️⃣2️⃣



Wajajen 7:30 aka gama kamun su hafsa kanninta da Khadija wanda sune suka dawo best ladyn Hawwa suka kaita jeep ganin Khaleel na cikin jeep din yasa tahade fuska ta shiga ta zauna suka rufe kofa suka wuce tasu motar, Driver yaja motan Khaleel yakai hannunshi zai kama hannunta dayasha lalle ta dauke hannun dasauri maida hannunshi yayi back sai kawai yaciro wayanshi yataho inda take yawani jawota zuwa jikinshi yamusu hoto tana turomai baki sannan yasaketa yace “lemme post it on insta all those girls Susan I’ve been taking ga yar sandan data kwance musu ni” hararanshi tayi shima bai kulata ba ganin kumbure kumbure takeyi kiris take jira so he’s going to be patient daga gobe ne on Saturday ware haka an kawomai ita gidanshi har gida sukaje da kanshi ya sauko yabude mata mota yamika mata hannu danta rikeshi ta sauko sabida gown nata ta kabar da hannunshi ta sauko ahankali abinta tawuce shi tai cikin gida yabita da kallo dakinta tawuce Ammi kadai ne tana kwasan some jakan gifts ganinta yasa tace “kun dawo Amaryana” adan kunyace ta sauke kanta kasa tace “Ammi zip” ijiye bags din tayi tazo tashiga jamata zip tana kwance mata head tace “Hawwa Khaleel na miki matsanancin so kinga hakan kuwa?” Shiru Hawwa tayi tashiga cire kayan tana mamaki inasu Noor dasu Ramla da Miemie, Ammi tace “suna gidan Malam Sama’ila wajen yammatan gidan wai harsunyi kawaye, bari na sallami baki na” Gyadamata kai Hawwa tayi tana mamakin duk inasu Hafsa wannan da dakinta is empty.

A uwardaka duka suka zagaye mahaifiyar tasu dake zaunw abinta tana duba wani azkar, daga Aminu har Hafsa, Kadija da Rahama Mimie ce kawai babu wajen suma sabida yarane. Anatse Aminu yace “Umma this is your last chance akanme zaki rike Hawwa aranki kan abinda ba itane tamiki ba? Bata duniya akayi? Ni aganina koma menene mahaifiyarta tamiki base on abinda yarinyar nan tamana yaci kin hakura kin yafemata, Umma school dina kap zuwa yau dana gama Hawwa ce babu kwandalan Baba, gasu Khadija, Hafsa da Rahama su basuyi university ba amman Hawwa ce ta aurar dasu Baba baida ko sisi kudaden Hawwa ne akayan dakinsu, banda haka akai akai take turamanakudi takirasu ta tambayesu yaransu, Mama kinga makarantan masu kudi da Miemie keyi Hawwa ce Umma menene wannan abun wannan wani irin tsana ne eh Umma” ahankali Hafsa tace “Umma dukanmu yaranki mun hadu yau muna miki fada muna nuna miki gaskiya bazaki dauka ba?” Khadija da duk tafisu zuciya tace “kai wlh Umma Allah karya bani bakar zuciya irin taki” dasauri Umma ta kalleta saikuma tafashe da kuka tace “ohh nice mai bakar zuciya ba Mahaufitae Hawwa data rabani da baban ku ba, nakasa auruwa sai bayan tarasu yadawo yawani aureni kuna cemin kaza kaza, ina mahaifiyarku baku sona kin fison Hawwa shikenan na barkı da Hawwa

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login