Showing 21001 words to 24000 words out of 143458 words

Chapter 8 - Gargada So Hausa Novel Complete

M SHAKUR   

19 Nov 2024

587

wayan tareda mata murmushi yace “tashi kije kiyi wanka kiyi salla, anjima sai muje mu gaidata ko tareda su Yaseer”? Gyadamai kai tayi asanyayye tasa hannu ta karba wayan, hannunshi yakai yashafa kumatunta ahankali yace “Ni’ima”kallonshi tayi asanyaye daukanta yayi yay gaban bayi da ita ya sauketa yace “go and shower” shikuma yajuya ya shirya yasa jallabiya yafice.


Hawwa na fitowa daga bayi taci karo dawata wata mata da tadan manyanta rike da buta a hannu ga asuwaki a bakinta tsaye dab da bayin tana mata wani kalan kallo dasauri Hawwa ta dauke kanta cikeda dan kunya dajin nauyi danta daura towel akanta tace “ina kwana Umma” mugun kallo Umma ta watsamata ta juya ta tofar da ruwan asuwakin bakinta a wajen tace “anje anyi abinda aka sabayi tohh Allah kyauta tir da wannan hali” dudda Hawwa tajita bata bata amsaba tawuce dakinta ta shiga da basket din sabulunta da soso dakin ta ijiye taje gaban mirror taja dan stool ta zauna tana kallon kanta dake daure da dankwali da duk ya jike zare dankwalin tayi ta ijiye gashin kanta ya zubo sannan tadauki abubuwan face nata tafara shafawa kafin ta shafa cream ajikinta ta feffesa turare sannan tawuce tabude sip tadauki wani simple gown tasaka lokacin an fara kiraye kirayen salla, shanya zanin da towel data cire tayi a kofa sannan tasa hijabi tahau kan dadduma.

Tana kan dadduman nan har gari yawaye sannan ta tashi tazauna tana duba hannunta da har yasoma warkewa tai shiru she’s just happy yau bazata aiki ba DIG yabasu off taga message din a group dinsu na watsapp, kwanciya tayi agadon tadauki wayanta ta danna tana kallon hoton dake jikin screen dinta da wata yarinya ce dake kama da ita ahankali tace “I miss you Mims” tashi tayi tafara gyara dakinta da babu datti tafito da sharan waje sannan tafara share tsakar gidan lekowa daga kitchen Umma tayi ganin itane yasa taja tsaki takoma cikin kitchen din abinta.
Tana cikin sharan Baba yashigo gidan da sallama using crutches dinshi dukawa tayi gabanshi tace “ina kwana Baba” binta yayi da kallo kaman mai nazarin wani abu sai chan yace “kin tashi lafiya, yau babu aikin naki ne”? Kanta na kasa tace “ance muhuta yau sabida operation damukayi” shiru yasakeyi kawai kallonta yake chan yace “muga hannun” ahankali ta dago kanta for the first time ta kalleshi da dan masifa Baba yace “kina kallona Baban Yaseer ya sanar dani kinji ciwo a hannu wajen aiki, tashi ki nunamin in gani” ahankali ta mike tsaye daidai lokacin Umma na lekowa daga cikin kitchen tahaderai, dan jan hannun dogon riganta tayi tanunamai ciwon wanda yake small cut, matse crutches nasa Baba yayi a hammata yakai hannunshi ahankali yakamata hannunta dan boyayyen ijiyan zuciya Hawwa ta sauke rabon da Baba yarike hannunta tun tana secondary school, kallon fuskanshi take, cikeda so dan damuwa Baba yace “bakince ke a office ko a mota kike aiki ba meyakai har kikaji ciwo haka iyye? Idan wani abu yasameki fa iyye Hawwa”? Baba yayi maganan yana dago kanshi yana kallon fuskanta, maida kanta kasa tayi batai magana ba, ahankali yasa hannunshi yadawo da hannun riganta yarufe yace “ai shikenan, Allah baki lafiya, zansaka Auwallu ya karbo mini maganan hausa saiki shafa awajen kinji ko”? Ahankali tace “to Baba nagode” sakin hannunta yayi yace “gama sharan kizo falo muyi kari tare” ahankali tace “toh” yawuce ciki itakuma Umma takoma kitchen rai abace ahankali ta duka ta cigaba da sharan shikuma Baba yashiga katon falonsu ya daga labule ya daura a kofa ya zauna yana kallo Hawwan dake shara yanason diyarsa wani zubin haushi da bakincikinta ke mamayemai zuciya yayita zuba masifa, hango Umma tafito daga kitchen rikeda flask, Hawwa tace “ina kwana” ko kallon inda take batayiba tawuce ta tazo ta shiga daki ta ijiye abubuwan data dauko tasake ficewa takwaso sauran abubuwa tadawo ta ijiye komi ta shiga budewa zata zubamai ya juyo ya kalleta yace “zuba dana Hawwa” dagokai tayi ta kalleshi rai abace tace “kadaisan bana abincina da yarka ko? Bakuma yau yarka tasaba ciyar da kanta ba” hade giran sama da kasa Baba yayi yace “yo da bata kawo kayan abincin ba da a ina zaki sami wanda zakici eh mara kunya” kallon Baba tayi baki sake saichan tace “wannan kuma tsakaninku har gobe ni kaine ke ciyar dani ba wata ba dan kai nake aure kuma kaike bani kayan bacci, banda haka naga ai nima nawa yaran na kawomin kayan abinci” dan dariya kadan yayi yace “Zainabu kenan yau banso nafara rigima dake dan nasan ba cikakken mutunci gareki ba, to meya hanaki cin abincin yaran naki? Bari kiji idan ni nayi fushi da diyata wannan ni mahaifinta ne, bakida ikon fushi da ita, ke har kinada bakin magana dabadan Hawwa ba da tayaya zamu aurar da yammatanki hudu mu musu kayan daki ni da bani aikin komi, wayasa Aminu a university? Wayakai Maryama boarding yake biyan kudin makarantan ta?” Magana Umma zatayi ya nunata da hannu yace “kul, karki batamin rai da safen nan zubamata kari nace” hadiye abu Umma tayi daya tsayamata a wuya tashiga zubawa Baba yajuya ganin tagama shara tana wanke hannu yasa yace “zo kiyi karin kumallo Hawwa” Gyadama Baba kai tayi ta wanke hannu ta taho ta shigo dakin Umma ta tashi ta shige ciki ko ajikin Baba yace “yi kari maza” dumamen tuwo ne da shayi dayaji kayan kamshi hannu tasa tafara ci Baba yace “yaushe ne ziyaran Maryama a school”? Ahankali tace “nan da kwana bakwai ne Baba next week” ahankali yace “Toh Allah kaimu” saikuma yayi shiru yakai kofi baki ya kurbi shayi chan ya kalleta yace “Hawwa inaso nai magana dake!”

Dan rage murya Baba yayi dudda haka babu wanda zai shigo gidan bazaijisa ba yace “Hawwa baki tunanin aikin nan naki nasa maza na tsoron tunkaran ki? Kin taba zama kinyi tunanin ko dalilin haka yasa suke guduwa? Ta iya yuwa kuma iyayensu na nuna bazasu dansu ya auro musu yar sanda ba iyye? Hawwa!” Baba yadan rage murya yasake kiranta kaman zaiyi kuka yace “gashi baki murmushi kullum fuskan nan taki ahade kaman kinga yan ta’adda” Baba yadan sauke ijiyan zuciya yace “nasan aikin nan ke ciyar damu, sune kudin makarantan Aminu da Maryam, amman ni wlh banki naji yunwa inhar hakan zaisa kisami mijiba, nagaji da zuba miki ido” yayi shiru yace “maganan danakeso nayi dake itace nama Malam Sama’ila magana ya sanar a masallaci ina nemamiki miji tun satın daya gabata, ya sanar ina nema miki miji” ahankali Hawwa tadago kai takalli Baba zuciyanta yamata badadi sosai Baba yace “dazu da asuba yasanar dani zai kawo wani anjima, kowaye yafito yace yana sonki zan bada ke banson ki kara wata biyu agidan nan, banso ki cikashe talatin agidan nan Hawwa, naga alamu idan nacigaba da linke hannu ina kallonki Maryama dake shakara sha hudu zatazo tagama sakandire tasami miji tai aure ke baki auren ba, lamarinki naga alamu saina shiga ciki nai dumudumu sannan zakisan da gaske nake kinajina ko”? Kasa magana Hawwa tayi sabida ji datayi tuwon dake bakinta ya makale mata a wuya, Baba yacigaba. “Idan akai nasara Malam Sama’ila wanda ya samo yanada dan abinyi ko cikin dalibansane zan badake” dasauri Hawwa takalli Baba tace “amman kisani saikinbar aikin nan gaskiya zakibar aikin” dasauri Hawwa ta kalli Baba, Baba shima kallonta yake yace “kwarai, me ake da aiki? Aure shine rabin addinin diya mace, aure bautan Allah, aure ibada ne kuma sunna ne, dan Allah idan mijin kwarai yafito yanuna baison aiki zaki barsa duk shirme ne aiki da yawon banza, inada yan gonaye saina saida mu dinga cin abinci, Hawwa idan bakibar aikin nan ba bazaki auru ba kowa zaita guduwa kinajina ko”? Sauke kanta Hawwa tayi kasa batare datai magana ba, daidai nan wani yaro yabugo sallama yana shigowa tsakar gidan yace “wai Malam Sama’ila yace nayi sallama da mai gidan” annuri ne ya fadada a fuskan Baba yashiga kokarin tashi yana daukan crutches dinsa yace “Ya Allah, Ya Allah kasa Malam ya samawa Hawwa na miji zanyi azumi tasami miji” da sauri yafita Hawwa tabi Baba da kallo kafin ta sa hannu ta dauki cup da ruwa ke ciki zata sha ko abin wuyanta zai sauka takai baki Umma tafito ranta abace tasami waje tazauna tace “ai alhakina bazai taba bari kisami miji ba duk wahalan banza mahaifinki yake” ijiye cup din Hawwa tayi ta kalli Umma still abincin na wuyanta, Umma tai murmushi tace “ni da mahaifinku tun muna yara aka mana alkawarin aure, muntaso tiryan tiryan munason juna rana daya ya hadu da mahaifiyarki marigayiyi ta kwacemin shi yajuya yace sam bayasona mahaifiyarki tasa saida aka sami matsala adanginmu, kuka ne, roko ne babu wanda banmai ba amman yace baya sona haka ya auri uwarki nakasa wani auren, sai bayan shekaru goma da sukai hatsari ta mutu shi kafafunshi suka koma haka sannan yazo ya aureni yadauramin wahalanki akai lokacin kina yar shekara shidda, tamoreshi ni na sameshi a gurgu ai bazaki taba ganin daidai ba” dan murmushi kadan Hawwa tayi kaman bazatace komiba saikuma tasa hannu tadauki cup tasha ruwan tass ta ijiye ta kalli Umma tace “Umma kenan ai ko azaban dakika azabtar dani yabiya koma wani kalan laifi Mamana tamiki, kibar tunanin dakikeyi, lokaci kawai baiyi bane, duk sanda lokaci yayi zanyi aure Umma, bakece dalilin ba” tayi maganan tana mikewa Umma tace “sai ayi mugani, mara kunya kwantai kawai”.
[9/15, 10:26 AM] M Shakur: 💫GARGADAN SO💫


✍🏻M SHAKUR



EPISODE 1️⃣6️⃣


JOIN MY WATSAPP GROUP
https://chat.whatsapp.com/DvCYR6o87F40OMWr9J8HZL

Fitowa Hawwa tayi daidai zataje dakinta taji Baba na kwalamata kira yana shigowa gidan da saurinshi. “Hawwa, Hawwa, Hawwa, Jiddah” tsayawa tayi chak tace “na’am Baba” cikeda farin ciki Baba yataho yace “maza shiga ki sanyo hijabi kifito munyi baki, Zainabu ke fito da tabarma ki shimfida anan tsakar gida” yana maganan ya shiga juyawa Hawwa ta bishi da kallo kirjinta na mata zafi saikuma tawuce tafada dakinta itakuma Umma tafito da tabarma ta shimfida musu shigowa Baba yayi ga Malam Sama’ila gakuma wani dan tsoho haka da akalla zaiyi 50 plus yana sanye da kaya masu dan mutunci da hula akanshi ga gemu kaganshi siriri kaman iska zai kwashesa, ga yar gemunsa siririya da gashin duk yayi fari fari Baba yace “bismillah ku bismillah ku” zama sukayi Baba ya kwalama Umma kira da katon murya yace “Zainabu kawo musu ruwa”Malam Sama’ila yayi gyaran murya yace “to Malam Hamisu bayan maganan damukayi dakai kwanakin baya nabada sanarwan kaman yanda kace sabida shi d’a dakake gani nakowa ne” Baba yace “kwarai!” Malam yace “Hawwa yarinya ce mai hankali datai boko tana aiki a matsayin yar sanda, maza da dama sun fito but gaskiya yawancinsu gajiyayyu ne ko matayensu na gida basu rike ba balle su kara da Hawwa, shi Kabiru daya zomin da maganan shi kadai na aminta dashi”
Yanuna mutumin yace “dudda Kabiru ba a unguwan nan yake ba but anan aka haifesa anan yataso marigayi mahaifinsa aminina ne, Matan Kabiru biyu yanada yara goma sha daya, Alhaji ne yasauke farali, yanada gonaki sannan shi principal ne a makarantan gwamnati ta cikin Bwari” Baba jikinsa har rawa yake yace “uhmm Masha Allah da kyau” Malam yace “yanada rufin asiri daidai gwargwado sannan yanada gidan kansa, danamai magana ya nunamini ai ya dade da kaunar Hawwa azuciyansa shi tsoronsa aikinta, baison mace mai aiki ballema irin nata aikin na yan sanda zaiso tabar aikin, sharadinsa kenan saiya kawo kudin aure, sati biyu zuwa uku inhar kun yarda yakeso adauka ayi auren ayi komi koba hakaba Alhaji Kabiru”? Anatse ya gyadakai yace “kwarai Allah gafarta Malam hakane” dariya Baba yayi irin na manya yace “indai aiki ne matsalan bakada matsala Kabiru kaman tabar aikin nan tagama, hana karya dai kasan irin aikin nasu dole kaje ka kai takardan barin aiki dan idan baka kaiba ana iya zuwa a kamaka koba hakaba Malam to zanso kabarta taje tabasu takardan ayi signing komi tarabu dasu lafiya koba hakaba”? Kabiru yace “hakane, indai wannan ne ba matsala Abba zata iya zuwa” washe baki Baba yayi kaman an basa kujeran makka Baba yace “Malam tashi muje waje shi saiya gana da Hawwa” ba musu Malam Sama’ila yatashi yayi hanyar zaure Baba yawuce jikin kofan Hawwa ya bubbuga yace “maza kifito kinada bako Hawwa” sannan yawuce waje yana murmushi sosai. Kusan duka abinda suka tattauna a kunnen Hawwa, dan koda bataji maganan kowaba zataji na Baba cus Baba akwai katuwar murya, she’s feeling so sad and so angry with Baba, like akanme zatabar aikinta bayan bawaima auren ya tabbata bane wat is wrong with Baba? Why is he so blind and obsess with tayi aure da he’s not seeing clearly, she’s regretting abinda yasa bataje aiki bama yau dan dataje da bazama a sameta a gidan ba balle amata wannan maganan kusan 15mins tabata aciki kawai babu yanda zatayi mahaifi mahaifine hakan yasa tadauki wani nude color hijab tasaka dayamata bala’in kyau tazo wajen kofa tadan daga labule ta leko compound din, amai taji yazo mata wuya cus this is not the man datai imagining living life with, he’s too old for her! He’s not handsome at all, he’s too slim kaman ana dibanshi ayi miya, gawani dogon baki dayake dashi kaman na fish, yawani zauna akan tabarman kaman wanda yazo wa’azi, itafa tanada taste, she loves fine classy men dasuka iya gayu not this types, ijiyan zuciya tasauke tace “Hawwa calm down” lumshe ido tayi tabude sannan ta fuzar da iska daga baki kafin tasa hannunta tabude net, karan bude net din yaji dasauri Alhaji Kabiru yajuyo yazuba mata wasu mayun idanu azuciyansa yace “mace har mace wayyoo Allah, na sameta bakaramin hutawa zanyi da itaba, Allah ne ya taimakeni Babanta yabada sanarwan nan daban isa na tunkareta da zancen soyayya ba”


in reality yahade fuska cus bayason ta rainashi wannan da har sanarwa ake ana nema mata miji tayi kwantai dole yanuna mata shi mai tsada ne sabida tadinga binshi, dük yanda yaso yajaye idanunshi karya kalleta yakasa tundaga kan kafafunta yake kallo har ka,

Kallon dayake mata kaman zai tashi ya lasheta yasa Hawwa ta dauke kai har takai gaban tabarman taja ta dakata ta tsaya dan jitayi bazama ta iya zama kusada shi ba, agogon hannunshi yashiga kallo yace “da fitan Babanki zuwa yanzu kimanin minti sha biyar, haka kikaga babar ki na batama mahaifinki lokaci”? Dasauri Hawwa ta zubamata shegun idanunta da saida yaji gabanshi ya yanke ya fadi dahar hakan yasa bakinshi ya shiga rawa yabasar yamike tsaye da sauri yace “nan da kwana uku dan kawo kudin auranki dan haka ki tabbatar kinyi resigning daga aikin nan kafin nazo” yashiga saka takalmi zai wuce Hawwa ta mike hannunta taya ta tarasa da kakkausan murya tace “Kai!”

Dan rage murya Baba yayi dudda haka babu wanda zai shigo gidan bazaijisa ba yace “Hawwa baki tunanin aikin nan naki nasa maza na tsoron tunkaran ki? Kin taba zama kinyi tunanin ko dalilin haka yasa suke guduwa? Ta iya yuwa kuma iyayensu na nuna bazasu dansu ya auro musu yar sanda ba iyye? Hawwa!” Baba yadan rage murya yasake kiranta kaman zaiyi kuka yace “gashi baki murmushi kullum fuskan nan taki ahade kaman kinga yan ta’adda” Baba yadan sauke ijiyan zuciya yace “nasan aikin nan ke ciyar damu, sune kudin makarantan Aminu da Maryam, amman ni wlh banki naji yunwa inhar hakan zaisa kisami mijiba, nagaji da zuba miki ido” yayi shiru yace “maganan danakeso nayi dake itace nama Malam Sama’ila magana ya sanar a masallaci ina nemamiki miji tun satın daya gabata, ya sanar ina nema miki miji” ahankali Hawwa tadago kai takalli Baba zuciyanta yamata badadi sosai Baba yace “dazu da asuba yasanar dani zai kawo wani anjima, kowaye yafito yace yana sonki zan bada ke banson ki kara wata biyu agidan nan, banso ki cikashe talatin agidan nan Hawwa, naga alamu idan nacigaba da linke hannu ina kallonki Maryama dake shakara sha hudu zatazo tagama sakandire tasami miji tai aure ke baki auren ba, lamarinki naga alamu saina shiga ciki nai dumudumu sannan zakisan da gaske nake kinajina ko”? Kasa magana Hawwa tayi sabida ji datayi tuwon dake bakinta ya makale mata a wuya, Baba yacigaba. “Idan akai nasara Malam Sama’ila wanda ya samo yanada dan abinyi ko cikin dalibansane zan badake” dasauri Hawwa takalli Baba tace “amman kisani saikinbar aikin nan gaskiya zakibar aikin” dasauri Hawwa ta kalli Baba, Baba shima kallonta yake yace “kwarai, me ake da aiki? Aure shine rabin addinin diya mace, aure bautan Allah, aure ibada ne kuma sunna ne, dan Allah idan mijin kwarai yafito yanuna baison aiki zaki barsa duk shirme ne aiki da yawon banza, inada yan gonaye saina saida mu dinga cin abinci, Hawwa idan bakibar aikin nan ba bazaki auru ba kowa zaita guduwa kinajina ko”? Sauke kanta Hawwa tayi kasa batare datai magana ba, daidai nan wani yaro yabugo sallama yana shigowa tsakar gidan yace “wai Malam Sama’ila yace nayi sallama da mai gidan” annuri ne ya fadada a fuskan Baba yashiga kokarin tashi yana daukan crutches dinsa yace “Ya Allah, Ya Allah kasa Malam ya samawa Hawwa na miji zanyi azumi tasami miji” da sauri yafita Hawwa tabi Baba da kallo kafin ta sa hannu ta dauki cup da ruwa ke ciki zata sha ko abin wuyanta zai sauka takai baki Umma tafito ranta abace tasami waje tazauna tace “ai alhakina bazai taba

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login