Showing 9001 words to 12000 words out of 143458 words

Chapter 4 - Gargada So Hausa Novel Complete

M SHAKUR   

19 Nov 2024

589

zagaye premises din tana patrol chan tace “Halt!” Da sauri Khaleel ya kalleta, hankalinta nakan screen din gabaki daya tace “I just saw another haske I’m going there right now to check” daidai takai wajen tace “is not just 4 of them akwai 3 more a wajen they’re holding rifles” Dasauri Hayatu yace “wat do we do Miss Hawwa?” Dan lumshe idanu tayi kadan chan ta budesu tana sauke ijiyan zuciya tace “can you take four men at a go Hayatu?” Dasauri yace “Yes Ma’am” gyadamai kai tayi tace “proceed to inda target namu take extract her and bring her to extraction point, Abraham lay low awajen and stay alert incase they move take them down, makesure Hayatu yadauko the little gurl, I repeat karkai komi lay low until I give you signal to” dasauri Abraham da Hayatu sukace “yes Ma’am” ahankali Khaleel ya matso dab da ita dago kanta tayi da sauri ta kalleshi kamshin dayake na ratsa hancnta dan kallonta shima yayi kafin ya dauke kai ya maida kanshi kan screen din hakan yasa itama ta maida idanunta kan screen din, tafiya suka farayi tana kallon screen din Abraham yashige cikin ciyayi yana watching those 3men shikuma Hayatu ya wuce wajen maza hudu, dukawa yayi yadauki dutse ya wurga dayayi kara hakan yasa suka zabura suka tashi suka fara tafiya suna dube dube, ganin daya na tahowa inda yake yasa Hawwa tace “stay on alert a guy is approaching wajen bishiyan dakake ta bangaren dama” da dan sauri Khaleel yasake matsowa dab da ita cus so yake yaga screen din da kyau, ta gefen idanu Hawwa ta kalleshi batare datai motsi ba ko magana dan batason tama kulashi daidai guy din na zuwa Hayatu ya kwasheshi ya bugamai kan bindiga a keya ya sume warwas yafadi, karan dasukaji yasa sauran suka jujuyo daya yadauke katuwar security torchlight ya hasko wajen ganin dayansu a kwance yasa da sauri suka taho wajen suna kokarin daga bindiga Hayatu ya kwashesu ya barar dasu ya sumar dasu duka within a blink of an eye yasa tape ya kulle musu hannu sannan yawuce ciki dasauri sauri gudu gudu shiga cikin container yayi zuwa inda yarinyar take kwance baiyi wata wata ba ya duka zai dauketa yaji an bugamai kai ashe dawani adakin but drone baiyi capturing ba sabida daga window suka leka dakin, dasauri gayen yafito yana kalle kalle ganin they’re under attack, ganin wani yafito daga container ba Hayatu ba yasa Hawwa tace “oh no, Hayatu, Hayatu, talk to me” tashiga kiranshi but shiru arude Abraham yace “what happened Miss Hawwa? Meya sami Hayatu”? Kafin Hawwa tai magana taji mutumin yayi blowing whistle sannan yadaga kanshi yana kalle kelle kaman ance ya kalli sama, ganin drone yasa yaciro bindigar shi Hawwa na gudu da drone din but yayi shooting drone din yayi crashing suka daina ganin komi a screen na controller Hawwa tace “shit!” Dasauri Abraham yace “what happened? Miss Hawwa gasunan they’re leavin……..” shiru Hawwa taji hakan yasa tace “Abraham, Abraham” adan rude Khaleel yace “wat wat…..wat happened”? Cikeda damuwa Hawwa tace “my team are down” tayi maganan tana tashi tamika hannunta tadauko katuwar jakan Abraham dake front sit tashiga neme neme a jakan luckily taga grenade, da sauri tasaka a pocket na vest nata, ta zaro bindigarta tana kokarin fita, asanyaye Khaleel yace “where are you going?” Dan juyowa tayi takalleshi ba yabo ba fallasa tace “going to rescue your daughter”? Dasauri Khaleel yace “maza ne u can’t go alone sun miki yawa, call for backup mana” tana kallonshi ganin damuwa kan fuskansa sosai tace “I can’t wait for backup kafin suzo an tafi da yarka sun gudu cus they know we are here, before we track them again it will take time, maybe muma sun kashemu before back up yazo, if I leave now I might be able to save your daughter so I have to go” takai hannu zata bude motan karaf taji yarike mata bakin gyale hakan yasa gently Hawwa tajuyo tazubamai mayun idanunta, shi kansa Khaleel baimasan mesa ya riketa ba, cikeda damuwa sosai yace “I can’t let you go alone it’s too risky, you’re just a gurl, zan biki and protect you” duk yanda Hawwa kejin haushinsa saida tai smirking tace “I’m not just a girl, I’m police officer!” Ganin yaki sakinta sai kallonta yake cikeda damuwa yasa ahankali tace “kataba rike bindiga”? Girgiza mata kai yayi alamun no, juya idanu Hawwa tayi irin na raini din nan tace “how can you protect me kenan u can’t shoot? Just stay here I don’t want to be looking after an adult when my mission is your daughter, stay here ina zuwa don’t jeopardize my work” wannan karan bata jira amsanshi ba ta karbe gyalenta tafito da sauri Khaleel ya sauko shima Hawwa ta kalleshi zatai magana saita fasa kawai ta wuce tana tafiya ahankali without making a sound, Khaleel na binta abaya sukai wajen, har zuwa bayan bishiyan da Hayatu ya tsaya dazu ta duka ta leka tana kirgasu tajuyo ta kalli Khaleel dake kallonta looking damn scared cikin whispering tace “if you stay here u might be alive, I’m going to rescue yarka now” cikin yar karaman murya Khaleel yace “kefa?” Sounding like a bad ass bitch tace “uhmm, I don’t think yau zan mutu” sosai Khaleel ke kallonta yanajin wani adrenaline na bin jikinshi ganin suna filin daga and she seems to be having fun, shiko zuciyansa kaman zai fito ta baki, Hawwa tasa hannu taciro grenade daga aljihun vest din dake jikinta, takalli Khaleel dake kallonta tace “wanna see magic Pops Boy”? Sosai Khaleel yamata wani irin kallo jin sunan data kirashi dashi, Hawwa tasake smirking tadauke kai ta cire pin din grenade din sannan ta leka ahankali ta wurga musu grenade din awajen tajuyo takalli Khaleel tace “booom!!” Mahaukacin tashi bomb yayi da Khaleel baisan yayi hugging Hawwa ta gefe ba ya manna fuskanshi a kafadanta jikinshi na rawa ba cus baitaba experiencing something like this ba, ko harbin bindiga baitaba ji ba saidai a movie, he has never experienced crime world so he panicked.

💫GARGADAN SO💫

✍🏻M SHAKUR


EPISODE 8️⃣

JOIN GARGADAN SO GROUP

https://chat.whatsapp.com/FKkyTo2kN1E3LrBfnyykbE
Mahaukacin faduwa gaban Hawwa yayi jin yanda Khaleel yariketa fuskanshi manne a kafadanta jikinshi na rawa kana gani kasan this is the first time yataba jin karan ko ganin bomb ma, da dan sauri ta tureshi yakoma baya yana kalle kalle kunnenshi sunmai dummm baiji ko kadan, yana kokarin kunnenshi yadawo daidai yaga Hawwa tai wani irin super tai wajen aguje tana shooting nasu, wow! Dabadan he knows this is real ba and he’s present a live location dinba dayace action movie yake kallo, she’s so fast in harbi, and wayanci he notice ba shoot to kill take ba, cus baiga wanda ta harba akai ko zuciya ko ciki ba, she mostly target legs and hands, da gudu ta shige cikin container yarinyar Hawwa tagani tana kuka sosai tana ihu ta kankame kunnenta sabida karan bomb ga wuta data gani, ahankali Hawwa ta duka gabanta tasa yatsanta akan lips nata tace “shiiiiiiu I’m fairy Angel Anty I come to rescue you from bad guys,, dena kuka” juya mata baya tayi tace “hop on my back, hau baya” takai yatsunta biyu tana taba wuyan Hayatu ganin yana numfashi yasa tashiga kiransa “Hayatu Hayatu, wake up” ahankali Noor tahau bayanta ta kankameta, dasauri Hawwa ta tashi she will come back for Hayatu, Noor first fitowa tayi ahankali goye da Noor ganinsu yasa Khaleel yatashi yataho wajen su da sauri yazo ta bayanta yana murmushi sosai looking and sounding so emotional ganin little baby shi that looks so scared and terrified a bayan Hawwa yace “Noory” dasauri yarinyar tace “Dadyyyyy” karban ta yake shirin yi daya daga cikin criminals din data harba a kafa dake wajen yadauki sandan dake wajen yadaga zai bugama Khaleel dake kokarin karbe Noor daga bayanta, karaf Hawwa tagani dawani irin sauri tai pushing Khaleel yafadi a side nata sandan ya sameta a hannu da karfi ya yagi skin nata sai jini, kafa tasa ta daki kan thug din ya sume dasauri Khaleel yatashi yana kallon hannunta da jini yabata hannun rigan already yace “you are bleeding” ahankali tace “it’s fine, leave Noor help me pick Hayatu” gyadamata kai yayi tawuce dajin goye da Noor neman Abraham taganshi a sume akasa, dagashi tayi sukai mota tasashi abaya tasauke Noor ta sata a baya itama daidai Khaleel na zuwa da Hayatu a sheme ya ijiyesa abaya yasa hannu ya dauki Noor ya kankame ajikinshi yarufe kofan baya yadawo gaba yashiga ya zauna Hawwa taja motan da mugun gudu tana calling DIG office waya for backup. “I repeat my team are down, goons are also down seriously injured calling for backup, code 22028IV” Khaleel ya kankame Noor data kankameshi dukansu suna kallon Hawwa dake tuki around 11 nadare tana magana har saida DIG yadaga wayan dan da farko voicemail ne, ahankali Khaleel yakalli hannunta dudda baya ganin ciwon but hannun riganta was bloody.
Kusan around 1:13AM na tsakar dare sukakai gidan sharp sharp aka bude musu gate cus DIG yarıga ya sanar da zuwansu, tun kafin su karasa tsakar compound din Excellency da Momy da mutanensu ke tsaitsaye suna jiransu, tun kafin tai parking Excellency da Momy suka shiga gudu suna tahowa wajen motan, tana parking mota Excellency yabude gaba Mommy tafashe da kuka tana kallon Noor datai bacci yarinyar ta rame tace “look at my Noor oh no no” takai hannunta tana karban Noor daga hannun Khaleel, shikuma Excellency yasa hannu yana fito dashi Khaleel yasauko yace “Dad did you call her Dr”? Dasauri yace “yes yes everything is set, yana clinic” Mommy tashiga shafa Khaleel da hannu daya tace “hope babu abinda yasameka Khaleely na welcome Alhamdulillah, babu abinda yasame ka”? girgiza mata kai yayi ahankali, Hawwa tadan matso taja kofan motan duk suka juyo suka kalleta takoma driving sit, Excellency yace “you guys did a great job Miss Hawwa welldone, dare yayi kuzauna anan zuwa safiya” calmly and politely tace “my team are down zan kaisu clinic dinmu” dasauri Excellency yace “ai da kin bari Dr ya gansu anan we have clinic anan” anatse tace “DIG yariga yace na kaisu clinic dinmu” dan ijiyan zuciya Excellency yace “okay but drive safe, bari nakara muku mopol su biku for extra security is night” dan gyadamai kai tayi cus batason ta kara gardama tai reverse da motan sannan tai kwana hakanan Khaleel samin kanshi da kallonta yayi daidai tana figar motan da gudu Excellency yace “ayi gudu a sannu” Khaleel yajuya ahankali yayi ciki.
[9/12, 10:23 AM] M Shakur: 💫GARGADAN SO💫



✍🏻M SHAKUR


EPISODE 🔟

JOIN INTIMACY CLASS WITH 5k ONLY
CHAT ME UP KISHIGA +2347012181461


Tabuga tagumi, a girl is a girl and will always be a girl, while a Man is a man kawai, daga gani kasan tagaji bacci kawai take.


Ahankali Hawwa ke bude idanu ta saukesu kan agogon dakin ganin 7 yasa da sauri ta tashi zaune babu kowa a office din, ahankali ta sauka daga gado tawuce bayi bata wani dade ba tafito daidai Ni’ima na shigowa tace “kin tashi”? Ahankali Hawwa tace “maisa baki tadani ba nasa kin dade” murmushi Ni’ima tamata tace “muje kiyi breakfast a canteen” dasauri Hawwa tace “not now banyi brush ba sainaje gida” hararanta Ni’ima tayi tace “brush idan kin koma gida kindaisan that woman ba baki abincin zatayi ba ko, don’t tell me zaki girki idan kin koma gida you can’t cook, kin gaji and kinada ciwo a hannu let’s just go na saya miki” tana maganan tazo gaban gadon tadauki gyalen Hawwa ta yafa mata saman kai batare data mata rolling ba takama hannunta suka fito suka shiga canteen abinci tamusu order sukaci still tamata takeaway wanda zataci da rana sannan suka fito tace “wai kinsan tun dazu Baban Yaseer na nan”? Dasauri Hawwa ta kalleta tana haderai, Ni’ima tace “ai daman nasan dana gayamiki bazaki tsaya kici ba, wlh tun kina bacci yazo ya daukeni, kuma shima yace makesure na tsaya kinci abincin, muje ku gaisa” taja hannun Hawwa batare data jira tai magana ba, yadade zaune cikin mota cus tun around 6:30 yazo daukanta, kallonsu yake kyar bayako kyafta idanu, yanda Ni’ima ke jan Hawwa itakuma tadan haderai kana gani kasan bataso tazo har zuwa wajen motan dayake nan Lexus na 2022 hadaddiya baka, ahankali yabude motan yafito


Bakin dogon gaye ne kyakkyawa gashi da tabon salla a goshinsa, duka duka bazai wuce 36yrs ba yana sanye da farin jallabiya mai kyau yasa faran hula akai sai zuba kamshi yake, a kunyace Hawwa tasauke kanta kasa dan tanajin kunya da nauyin Baban su Yaseer aduniyan nan, she always regard him as Yayanta, sabida shida Ni’ima su dauketa yar uwarsu tajini sun tsayamata, adan kunyace tace “ai dakai zamanka aciki Baban Yaseer Ina kwana, dan Allah kayakuri munbata maka lokaci” kafin yayi magana Ni’ima tarikemai hannu tace “Baby kaga kamata fada, niko na mata fada batajin tawa amman kai nasan zataji naka tunda tana kunyarka, field taje yau harda injury a hannu kalli hannun” tanunama Baban Yaseer hannun dayake tai folding hannun riganta sama, anatse yana kallon hannun sounding serious and caring yace “Hawwa why did you go to the field eh”? Adan kunyace tace “kidnapping jikan senate president akayi shine Oganmu ya aikamu I have no option saisa” dan ijiyan zuciya yasauke yana kallonta yace “but yaya hannun yanzu? Are you sure you’re fine? Babu wani abu dake miki ciwo kuma? Tayaya kikaji ciwo haka eh Hawwa”? Ahankali tace “wlh I’m fine is just a minor injury I can’t even remember ta yanda na samu” anatse yace “Hawwa!” Ahankali tadago kanta ta kalleshi kasa jure kallon dayake mata tayi da sauri ta sauke kanta Baban Yaseer kwarjini yake mata sosai ahankali tace “karki kara wani aiki dazaisa kiji ciwo haka, ni da Mom Yasmeen will support akoma mekikeso but we will never support something dazaiyi harming lafiyanki ba, you’re a criminologist not a fighter am I clear” cikeda jin dadi Ni’ima tace “yauwa bada amsa muji” Baban Yaseer cikin dan kakkausan murya yace “kada ki kara bari something yayi tampering da lafiyarki kinji” gyadamai kai Hawwa tayi tace “naji” dan murmushi kadan tayi tace “thank you” tafi Ni’ima tafara tace “Baby kome kakeyi da wannan mai taurin kan kejin maganan ka nima zan koya sabida tadingajin maganata” dan hararanta Hawwa tayi, kallon Ni’ima yayi yace “tana tareda motarta ne komu kaita gida wife?” Dasauri Hawwa tace “zan iya tuki” strictly Baban Yaseer yamika mata hannu yace “bani your keys zansa akawo miki motan gida muje mu kaiki” wlh kawai dan tanajin nauyin Baban su Yaseer ne saisa, jakanta tadauke daga kafada tasa hannu taciro key motar ahankali tabashi ya karba Ni’ima tabude mata bayan motansu tace “zoki zauna” zuwa tayi tana ballamata harara Ni’ima tai mata gwalo tai kwafa ta zauna tarufe mata kofan takoma gaba ta zauna sannan shima ya shiga gaba yaja motan.



Sosai Ni’ima keta musu hira a motan Baban Yaseer na amsata jefi jefi, bini bini yana kallon Hawwa ta mirror datai shiru tana hamma once in a while cus harda gajiya ke damunta, har unguwansu, unguwa ce dake cikeda mutane da dama yara anata wasa, ga manya haka yan anguwa da samari, mahaifinta ta hango kofar gidansu zaune, kana ganinshi kaga mahaifinta don tayi kama da Babanta ya manyanta sosai, yana zaune akan wata yar tsohuwar kujera 2sitter dake wajen ga crutches dinsa guda biyu a gefe a jinginasu dan kafansa ta haggu an guntule daidai wajen guiwan sabida wani hatsari daya tabayi da dadewa, tunda molar ta shigo anguwan yake kallonta, dan layin nan kakap idan kana neman wanda yasan yaro da babba da jika da duk wani labari na anguwan da dangin kowa to aka sami Baba an gama danshi kofar gidane wajen zamansa, to baya aiki the only abu dake shigar dashi gida shine idan lokacin bacci yayi ko zai zaga bayan gida. Parking Baban Yaseer yayi yabude motan yafito hakama Ni’ima itama Hawwa tafito, Baba naganin Baban Yaseer da Ni’ima fuskansa ya yalwatu da murmushi shiga rumfar sukayi yana nuna musu tabarma yace “maraba maraba yau Baban Yan biyu da Maman yan biyu ne agidan namu ga waje bismillanku, ku zazzauna yan albarka” hannu Baban Yaseer yabasa suka gaisa yace “ina yaran mesa baku kawominsu ba” daidai lokacin Hawwa takaraso wajen ahankali tace “Baba ina kwana” kallonta yayi saikuma ya dauke kai yakalli Ni’ima yana nunata da hannu yace “kalli kawarki ke bakijin kunya kinama binsu zindimemiya dake ba aure ba miji sai kwana awajen aiki, kap layin nan yaran dakuka taso tare sunyi aure, kannensu sunyi aure, kannin kannensu ma sunyi aure banda ke” sosai Ni’ima kirjinta yahau zafi cus Baba irin mutanen nan ne masu katon murya sai kallonsu ake sabida duk anajin maganan sa, juyawa Baba yayi ya kalli Baban Yaseer da kansa ke kasa yace “Aliyu” ahankali Baban Yaseer yadago kanshi yace “na’am Baba” nuna Hawwa da kanta ke kasa Baba yayi yace “cikin Abokanenka babu me neman mata? Koda yake karnaje da nisa ni wlh ko bakaniken ka ne ma idan zai aureta zan bashi, kannin Hawwa biyar hudu sunyi aure, Miemie ma datake sha hudu

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login