Showing 99001 words to 102000 words out of 143458 words
take zaune yanuna mata yace “check your phone?” Dasauri Hawwa ta dauki wayan tabude, tana dubawa taga yatura mata hoto ta iMessage guda daya inda take saman kanshi bakinta akan nashi tarikemai gaban riga duka jikinsu ajike hannunta yahau rawa takalli Khaleel da sauri cus she’s confuse, kanshi yadan sosa irin na iskancin nan yace “I have the video inhar u finally took off the shirt kina shamin this” yanuna mata nipples dinshi cikeda iskanci, yadan kalli saman motan kaman mai tunani yadaura yatsa abaki saikuma yacire yakalleta yace “I will just start crying to Baba ince yarshi beat me up ta turani cikin ruwa tafito dani kawai tahau kissing baki na and kikayi threatening dina kan cewa dole saina aureki, nazo nagayama Baba, Baba will easily believe me daman that crazy woman tace zaki iyama maza fyade so I’m your first victim” yakashe mata ido daya a iskance Hawwa na kallonshi hawaye na cika idanunta, Comfortably Khaleel yace “idan bakija bakin nan that talks like parrots kinyi shiru anyi bikinmu an kawomin ke gidana ba I will expose this” yanuna mata wayanta yace “family naki will lose all respect for you and zama dani dole, anyhow u look at it I’m still the winner, ko kinaso ko bakiso saikin zauna dani, don’t forget you started this war with me Kulu!” Glass nashi ya warware ya sanya a idanu sannan ya kalleta yace “see you Kululuwa Yar Sanda bye” yabude kofa yafice abinshi yawuce nashi motar aka budemai brabus dinshi yazauna aka ja motan harsaida Hawwa ta daina ganinshi tafashe da kuka sosai tana kallon hoton tana mamaki what happens to her? How come is this picture photo shop ko sun bata wani abu ranan ne tunda yan kwaya ne how did she kiss this man cus batasan sanda akaiba, takai 20min tana kuka amota sannan ta tada motan tabar wajen.
**
Ijiyan zuciya Momy tasauke cikeda damuwa tana kallon Salman daya gama koramata bayani acikin office dinta hannu tasa ta zare glasses dake kan idanunta tashafa goshinta cikeda damuwa tace “why that police girl in all matan dake duniyan nan dan Allah? Ko yar india Khaleely yake bukata zan iya auromai why that girl? Akanme yake chasing nata up and down tell me the truth Salman sonta yakeyine?” Cikeda girmamawa yace “I can’t say Hajiya gaskiya, but one thing is bantaba ganin Yallabai na bin mutum up and down kaman yanda yakebin yarinyar ba shi kanshi ba lallai yasani ba but he’s giving her all of his attention his time and komi Ma’am” table Mom tabuga tace “that’s wat I don’t want, yarinyar will take my son for granted wlh, zata wahalar min dashi Khaleely baitaba bibiyan any girl aduniyan nan ba saidai su suyita bibiyansa what is so special about tsohuwan yarinyar nan da he’s all over her eh? Hmm, u can go Salman just keep me posted whenever he sees her and wat they discuss about” gyadamata kai yayi yace yes Ma yawuce yafita.
Tashi tayi ta tsaya jikin window ta hango Khaleel din na buga ball da Noor he looks so happy haka Noor ma Mom ta sauke ijiyan zuciya, bude kofan office din nata Mom tayi tashiga another elevator dake wajen tasauka kasa tana tafiya zuwa garden da Khaleel ke buga kwallo Noor dake sanye da jersey na Liverpool looking so cute tace “Granny join us” murmushi Mommy tamata tace “continue playing Princess dina” takalli Khaleel dake wasa da kwallo abinsa kaman bai ganta ba tace “why do you keep chasing that Police girl Khaleely?” Batare daya dagokai ya kalli Mom ba yana bugama Noor kwallo yace “what is your business with my affairs Momy”? Dan shiru Mom tayi taji zafin amsan daya bata inda sabo sun saba haka yake musu magana agantale, ahankali tace “common My Leely I didn’t train you to be going after kowace kalan mace aduniya! You have everything na rayuwa babu wacce kakeso dabazaka iya samuba” daidai lokacin yabuga kwallo araga shida Noor sukahau suna jumping suna ihu yadagata yana ihu suna dariya sannan yasauke ta yace “go to your Nanny tamiki wanka” dasauri Noor tawuce tana gudu shikuma yadauki kwallon cikeda iskanci ya wurgama Mom tai baya baya kaman zata fadi sannan tarike ball din da kyar tana haki tace “Khaleely banson iskanci fa, karyewa kakeso nayi?” Khaleel ya kwashe da dariya sannan yataho inda take yabata sidehug yana daura hannunshi akafadanta cikin sangarci yace “Mom tsoro kike zan auro miki yar sanda?” Hade fuska tayi hakan yasa ya kwashe da dariya again Mom ta tsaya tana kallonshi he’s so happy this days, Khaleel yace “Mom do you think she will stop me from living my life? And enjoying myself?” Cikeda damuwa Mom tace “eh mana Khaleely girls like her sunfi karfinka” dariya yayi yace “Mommy I’m man enough to control kowace kalan mace na aura your Son is not a boy” yasaketa yawuce saikuma yadawo ashagwabe yace “Moma we will be having wedding on 23rd get ready invite all your friends, I want my side furnitures change, sannan agayara my main flat” yanuna wani arnen flat dake dayan barayin gidan dasauri Mommy tace “no Khaleel you will never leave my sight gaskiya side dinka dake cikin flat dina zaka dinga zama not bangaren chan kaji ba” wucewa yayi abinsa batare daya kulata ba yatafi sama gym dinshi yashiga yashiga yin exercise kafin daga bisani yafada shower yayi wanka yafito Sam haryazo suka tafi party abinsu.
[10/6, 10:39 AM] +234 706 565 5343: EPISODE 5️⃣4️⃣
Ranan gabaki daya Hawwa jitayi batajin dadin komi, har Ramla saida taga Hawwa was not in good mood sabida yanda tai shiru batama iya magana da kyau, sai lissafi take how zata fita daga this mess? Idan yanuna video ko pictures yacema Baba tayi kokarin mai fyade duk zasu yarda ta ina kunya zai barta ta kallesu dagashi har Ammi that means everything Ni’ima said is true about her.
Washe gari tsaf ta shirya ta tafi aiki around 12 DIG yakirata tashigo office nashi murmushi yamata yace “okay Ogana gabaki daya yakirani yace nabaki leave sabida kiyi planning wedding naki da kyau an baki 60 days” zaro idanu Hawwa tayi tace “Innalillahi 60 days that’s 2month, mezanyi da all this time Sir”? Dan murmushi DIG yamata yace “Hawwa have you seen abinda nafada miki jiya? Imagine danaje wajen Babanki to, wannan da Ogana ne yakira yace abaki 2months wedding leave abinda 3weeks ake bayarwa but naki is different, so zaki iya tafiya, we will see you on the wedding day in sha Allah idan kinyi inviting namu, Hawwa May Allah bless your home, Allah miki albarka, nasanki da ibada da yawan azumi Allah shine maganin komi so call on to him shine yasan wats best for you” kuka taji yana zuwan mata amman tahadiye ta gyadamai kai ta tashi ahankali tafito tana tafiya zuwa office nata wani officer yace “Miss Hawwa kinada bakuwa bamu barta tashigo nan ba tana chan” yamata pointing waiting room nasu, da mamaki tadinga tunanin waye ko wacece zatazo wajenta, dudda Ammi na hanya dan yau zata dawo amman ai baici ta iso ba tace mata by 11 zatabar gida, why is she even thinking of Ammi? Ammi bazata taba zuwa wajen aikinta ba, hanyar waiting tayi ganin Ni’ima taci gayu cikin atampa mai kyau ta yafa dan gyale ta rike handbag a hannunta yasa ta tsaya turus Ni’ima tamata murmushi kawai ta taso da gudu tazo batai wata wata ba ta rungumeta tace “Best suprise” chak Hawwa ta tsaya without hugging her back harsaida Ni’ima tadago ta kalleta tace “are you not happy to see me?” Dan girgizamata kai Hawwa tayi tace “no is not like that” dasauri Niima tace “muje office naki anata kallonmu anan” kawai takama hannun Hawwa, ahankali Hawwa tabita har zuwa office nata suka shiga idanunta ne suka sauka akan iPhone 15 pro max na Hawwa dake kan table last she check Hawwa was using Samsung S10 harya chanza mata wayane? Lallai gayen nan, abu taji ya tsaya mata arai dasauri tasaki hannun Hawwa tai wajen wayan tadauka tace “wow kin chanza waya Hawwa? Kin koma iPhone? Ni fa banson iPhone ance basu rike charge duk application saika saya? Baka iya downloading movies anyhow, komi kudi, Ke kika siya ko mijinki ya saya miki”? Karasowa Hawwa tayi ciki tazauna ahankali tace “shi ne” wani irin murmushi Ni’ima tana danne bakin ciki da zafi datakeji aranta tayi tace “awwwn lovebirds, ohh my my, Hawwa I’m happy for you Allah yaga how patient you are yabaki mai sonki, wai yaushe kuka hadu ne baki taba bani labarinsa ba, eh yaushe kuka hadu?” Baki Hawwa tabude zatai magana akai knocking kofan da sauri dukansu suka kalli kofan Abraham ne ganin Ni’ima yasa ya tsaya yace “can I see you Miss Hawwa”? Gyadamai kai tayi tace “sure” ta mike suka fice tarufe kofan dawani irin sauri Ni’ima ta danna screen din wayan ganin babu password yasa tashiga cikin wayan dasauri tace “calls” call log tashiga d only number datai magana dashi for long batai saving ba saina Ammi datai saving da Ammi hakan yasa tashiga kwashe number da she’s sure Khaleel ne dan ya kikkirata bata dagawa daidai tana gama kwasa tanaji ana taba kofan da sauri tafita tarufe wayan ta ijiye kan table Hawwa ta shigo rike da Maltina ta ijiye gaban Niima, Ni’ima tace “thank you Best” Hawwa ta zauna Ni’ima tace “gist me Best ya shirye shirye? Kayan daki kayan kitchen? Na kaiki wajen wanda yamin na dakina?” Ahankali Hawwa tace “Baba da Ammi are in charge of everything bansan mesuke ba” gyadamata kai Ni’ima tayi saikuma tace “wai har yanzu kin rikeni azuciye ne? Best I’m really sorry wlh ina sonki you mean the world word to me kinji” dan lumshe idanu Hawwa tayi saita gyadamata kai tareda bude idon, Ni’ima tace “anko fa? Nafitar miki da anko?” Shiru Hawwa tayi saikuma ta gyada mata kai, murmushi Ni’ima tayi tace “thank you, can you call Baban Yaseer for me yanzu da wayan naki”? Shiru Hawwa tayi all maganganun Ammi nadawo mata ahankali tace “Ni’ima banso nakara shiga lamarinki da Baban Yaseer I promise kaina that, for licence naki nayi magana za’a samu nasara in sha Allah” murmushin karfin hali Ni’ima tayi tana danne abinda takeji azuciyanta tace “shikenan hakan ma I’m grateful after kalan abinda namiki not everyone will even help me that much, kinada zuciya mai kyau Hawwa, thank you” gyadamata kai Hawwa tayi, daidai nan wayan Hawwa yahau ringing Ni’ima ta saci kallon screen din ganin number data kwashe ne kaman Hawwa bazata dauka ba, but ganin Ni’ima and tanaso tanunama Ni’ima she’s cool with Khaleel kodan tacire tunanin Baban Yaseer da ita aranta yasa gently tadauka takai kunnenta, murya chan kasa Khaleel yace “I sent a delivery guy what’s your office number”? Shiru tayi chan tace “baza’abarshi ya shigoba” dan murmushi yayi yace “no one can stop my delivery, office number Kulu” murya chan kasa tace “0040” katse wayan yayi almost 1min saiga knocking anatse Hawwa tace “come in” bude kofan akayi wani delivery guy ne rike da flowers na red roses da akai wrapping katon gaske, saikuma platter na yan gayu na different intercontinental dishes da note ajikin both of them delivery guy din yace “I’m looking for Mrs Hawwa Alhassan Ibrahim Khaleel” Ni’ima jitayi yawun bakinta yayi daci da kyar tahadiye, ahankali Hawwa ta mike ta nunamai table din zuwa yayi yafara mika mata flowers din dake kamshi sosai like Khaleel plus kamshin roses again, office din yacika da kamshi, karba tayi ta ijiye sannan yabata platter na abincin shima ta ijiye yabata note nashi tai signing sannan ya tafi, kafin Hawwa ta zauna har Ni’ima tasa hannu tadauki card dayayi note ajiki tace “love bird bari muga meya rubuta miki” dasauri kafin Hawwa tace wani abu, tace “_I know you haven’t had breakfast banson matana looking skinny you are too light for my liking, eat and get chubby, cheers to starting your leave today! Sowie about yesterday with love Mijin Kulu❤️_”
Murmushin dole Ni’ima tayi ta ijiye card din, taja platter box na abincin tana budewa tace “eat mana” wow tafadi ahankali lafiyayen abinci ne aciki dat are very hot, mash potatoes da chicken wings, samosas, Pasta sai Mandi rice, ga salad ga fruits juice very cold ga sweet da cingum na mentos, kallon abincin itama Hawwa take, deep down she feels happy but then she don’t wanna feel d happiness ahankali tace “ke kici idan zakici” dasauri Niima ta girgiza kai tace “a’a inacin abinci nafito” gyadamata kai Hawwa tayi saita rufe platter ta matsar gefe idanunta suka sake saika akan rose din kawai ta tsaresu da idanu Niima duk na kallonta, aranta tace “munafukar mugun son mijinta take amman tana bobboyewa, hala ma sun riga sun sadu” wayan Hawwa ya shiga ringing dasauri ta waigo ganin Khaleel ne yasa ahankali tadauki wayan takai kunne murya chan kasa Khaleel yace “have you eaten? Is the food good? Kona chanza mana Chef? Shizai dinga mana girki bayan auren mu, abincin yayi”? Shiru Hawwa tayi murya ciki ciki tace “mesa baka dafa da kanka ba”? Dan zaro idanu Khaleel yayi yace “Momy bata barina in kitchen I don’t know me akayi a kitchen” murya chan kasa Hawwa tace “uhnn Moms boy” murmushi kadan Khaleel yayi yace “do you like the rose?” Kin magana Hawwa tayi, ahankali Khaleel yace “but I said sowie about yesterday” murya chan kasa Hawwa tace “sowie is not sorry” dan dariya kadan Khaleel yayi ahankali yace “wa akace tana tareda ke a office?”
[10/6, 10:39 AM] +234 706 565 5343: EPISODE 5️⃣5️⃣
Faduwa gabanta yayi jin tambayan daya mata, hakanan sai takasa magana, “answer me” yafadi da kakkausan murya still kin magana tayi sai kawai ta zare wayan daga kunnenta takatse ta ijiye takalli Ni’ima ahankali tace “zan tafi gida natashi” tashi Ni’ima tayi tace “toh nima bari natafi, bari natayaki daukan rose din saike ki dauki platter” wani iri Hawwa taji amman saita daure ta mike tashiga hada abubuwanta tadauki car key suka fito tare ita tana rikeda platter Ni’ima na rike da rose din har zuwa inda motar Hawwa yake, Ni’ima sai kallon motar take tanaji kaman tahadiye zuciya ta mutu idanunta harsun kada sun chanza, abayan motan sukasa komi Ni’ima na kallon motan irin wannan fa ba tokunbo car Hawwa ke dashi ba no, asalin sabuwa gal ce, komi na motan ba ariga an daye mata ledaba, maida kofan bayan Hawwa tayi tarufe tace “bye” tawuce ta shiga gaba Ni’ima na tsaye tana kallonta, Hawwa taja mota tabar wajen abinta, da kyar Ni’ima ta iya wucewa zuwa wajen tata motar zuciyanta kaman an barbada busheshen barkono da danye tsabagen azaban radadi dayake mata, sai kawai ta tsaya tana kallon motan ta, motar Hawwa tada Toyota Camry ce 2006/2007 ita lokacin da Baban Yaseer yabata Camry nan na 2014 kaman zata haukace dan tafi na Hawwa kyau da tsada gata latest, but yanzu dataga motan da Hawwa keja benz datakai irin 150M sai taji ta tsani tata motar, saitaji ta rainata, wai tayaya ma rana daya Allah zai dauki miji mai bala’in kudi yabama Hawwa ne? Eh? Within a blink of an eye rayuwan Hawwa ya chanza kakap, big phone iPhone 15 pro max, ita tana fama da Samsung S21 dinta da ada takejin dadi yafi na Hawwa S10, Hawwa ce big car, ga sadaki mai tsoka, ga gwalagwalai, Hawwa ko sisi taki bata, da dane da hala yanzu Hawwa tabata like 20M from that sadaki wlh dan Hawwa bata kyashin bata abu, Hawwa is going to big house now and yaron seems to love her alot, jibi yanda yake bata gifts, ranan su diamond agogo dasu turare yau abinci da flowers masu tsinannen kamshin dadi, he’s so romantic, she thought babu miji that will be as sweet and romantic as Baban Yaseer yanzu taga wanda yafisa.
Hawwa ta hadu da irin gayen kan taki fadamata har sai bayan tayi hauka? The way suke soyayya hakan nan she can swear Hawwa tadan jima da sannin gayen? Wannan dayaketa bata gifts sunyi sex ne? Hawwa is so happy she wants her to be sad, tafison taga hawaye da bakin ciki da bacin rai da damuwa akan fuskanta, wannan gayen ya shigo rayuwanta yasa Hawwa ta chanza bata damu da itaba yanzu, imagine wai ita Hawwa ke shama kamshi, what will she do yanzu? Da kyar ta lallaba tashiga motan ta tada tabar wajen tana tana tafiya akan titi tazo ta wajajen banex ta kalli masu bara dake wajen, sai kawai tayi parking motan tafito taje wajensu tace “zan baku kyautan kudi sosai amman saikun bani wayanku na tura wani sako” har rige rigen bata wayan ake, kakkarba tayi marasa kati har tana samusu ta bank dinta, sako tashiga turama number Khaleel da kusan duka number su sannan ta basu 5k suraba tawuce takoma mota tana murmushi taja abinta zuwa gida.
**
Khaleel na cikin mota tareda Sam wayanshi yayi kara daukan wayan yayi yaga messages guda 5 from different numbers hardly unknown ke kiranshi ma talk more of sako, kaman bazai budeba saikuma yabude daya.
“_Hawwa is a whore! Tsohuwan karuwa ce she sleeps with everyman dayake zuwa yace yana sonta saisa suke guduwa basa aurenta sabida tabasu abinda suke nema_”
Chak Khaleel ya tsaya yana kallon messege din to be very very honest he doesn’t care idan Hawwa sleeps around or not cus yasan tun zamanin da wato old days aka daina samin virgins, konji is real babu yanda za’ayi yataso maka baka nemi wanda you