Showing 114001 words to 117000 words out of 143458 words
nasara in sha Allah” murmushin karfin hali Ni’ima tayi tana danne abinda takeji azuciyanta tace “shikenan hakan ma I’m grateful after kalan abinda namiki not everyone will even help me that much, kinada zuciya mai kyau Hawwa, thank you” gyadamata kai Hawwa tayi, daidai nan wayan Hawwa yahau ringing Ni’ima ta saci kallon screen din ganin number data kwashe ne kaman Hawwa bazata dauka ba, but ganin Ni’ima and tanaso tanunama Ni’ima she’s cool with Khaleel kodan tacire tunanin Baban Yaseer da ita aranta yasa gently tadauka takai kunnenta, murya chan kasa Khaleel yace “I sent a delivery guy what’s your office number”? Shiru tayi chan tace “baza’abarshi ya shigoba” dan murmushi yayi yace “no one can stop my delivery, office number Kulu” murya chan kasa tace “0040” katse wayan yayi almost 1min saiga knocking anatse Hawwa tace “come in” bude kofan akayi wani delivery guy ne rike da flowers na red roses da akai wrapping katon gaske, saikuma platter na yan gayu na different intercontinental dishes da note ajikin both of them delivery guy din yace “I’m looking for Mrs Hawwa Alhassan Ibrahim Khaleel” Ni’ima jitayi yawun bakinta yayi daci da kyar tahadiye, ahankali Hawwa ta mike ta nunamai table din zuwa yayi yafara mika mata flowers din dake kamshi sosai like Khaleel plus kamshin roses again, office din yacika da kamshi, karba tayi ta ijiye sannan yabata platter na abincin shima ta ijiye yabata note nashi tai signing sannan ya tafi, kafin Hawwa ta zauna har Ni’ima tasa hannu tadauki card dayayi note ajiki tace “love bird bari muga meya rubuta miki” dasauri kafin Hawwa tace wani abu, tace “_I know you haven’t had breakfast banson matana looking skinny you are too light for my liking, eat and get chubby, cheers to starting your leave today! Sowie about yesterday with love Mijin Kulu❤️_”
Murmushin dole Ni’ima tayi ta ijiye card din, taja platter box na abincin tana budewa tace “eat mana” wow tafadi ahankali lafiyayen abinci ne aciki dat are very hot, mash potatoes da chicken wings, samosas, Pasta sai Mandi rice, ga salad ga fruits juice very cold ga sweet da cingum na mentos, kallon abincin itama Hawwa take, deep down she feels happy but then she don’t wanna feel d happiness ahankali tace “ke kici idan zakici” dasauri Niima ta girgiza kai tace “a’a inacin abinci nafito” gyadamata kai Hawwa tayi saita rufe platter ta matsar gefe idanunta suka sake saika akan rose din kawai ta tsaresu da idanu Niima duk na kallonta, aranta tace “munafukar mugun son mijinta take amman tana bobboyewa, hala ma sun riga sun sadu” wayan Hawwa ya shiga ringing dasauri ta waigo ganin Khaleel ne yasa ahankali tadauki wayan takai kunne murya chan kasa Khaleel yace “have you eaten? Is the food good? Kona chanza mana Chef? Shizai dinga mana girki bayan auren mu, abincin yayi”? Shiru Hawwa tayi murya ciki ciki tace “mesa baka dafa da kanka ba”? Dan zaro idanu Khaleel yayi yace “Momy bata barina in kitchen I don’t know me akayi a kitchen” murya chan kasa Hawwa tace “uhnn Moms boy” murmushi kadan Khaleel yayi yace “do you like the rose?” Kin magana Hawwa tayi, ahankali Khaleel yace “but I said sowie about yesterday” murya chan kasa Hawwa tace “sowie is not sorry” dan dariya kadan Khaleel yayi ahankali yace “wa akace tana tareda ke a office?”
[10/6, 10:39 AM] +234 706 565 5343: EPISODE 5️⃣5️⃣
Faduwa gabanta yayi jin tambayan daya mata, hakanan sai takasa magana, “answer me” yafadi da kakkausan murya still kin magana tayi sai kawai ta zare wayan daga kunnenta takatse ta ijiye takalli Ni’ima ahankali tace “zan tafi gida natashi” tashi Ni’ima tayi tace “toh nima bari natafi, bari natayaki daukan rose din saike ki dauki platter” wani iri Hawwa taji amman saita daure ta mike tashiga hada abubuwanta tadauki car key suka fito tare ita tana rikeda platter Ni’ima na rike da rose din har zuwa inda motar Hawwa yake, Ni’ima sai kallon motar take tanaji kaman tahadiye zuciya ta mutu idanunta harsun kada sun chanza, abayan motan sukasa komi Ni’ima na kallon motan irin wannan fa ba tokunbo car Hawwa ke dashi ba no, asalin sabuwa gal ce, komi na motan ba ariga an daye mata ledaba, maida kofan bayan Hawwa tayi tarufe tace “bye” tawuce ta shiga gaba Ni’ima na tsaye tana kallonta, Hawwa taja mota tabar wajen abinta, da kyar Ni’ima ta iya wucewa zuwa wajen tata motar zuciyanta kaman an barbada busheshen barkono da danye tsabagen azaban radadi dayake mata, sai kawai ta tsaya tana kallon motan ta, motar Hawwa tada Toyota Camry ce 2006/2007 ita lokacin da Baban Yaseer yabata Camry nan na 2014 kaman zata haukace dan tafi na Hawwa kyau da tsada gata latest, but yanzu dataga motan da Hawwa keja benz datakai irin 150M sai taji ta tsani tata motar, saitaji ta rainata, wai tayaya ma rana daya Allah zai dauki miji mai bala’in kudi yabama Hawwa ne? Eh? Within a blink of an eye rayuwan Hawwa ya chanza kakap, big phone iPhone 15 pro max, ita tana fama da Samsung S21 dinta da ada takejin dadi yafi na Hawwa S10, Hawwa ce big car, ga sadaki mai tsoka, ga gwalagwalai, Hawwa ko sisi taki bata, da dane da hala yanzu Hawwa tabata like 20M from that sadaki wlh dan Hawwa bata kyashin bata abu, Hawwa is going to big house now and yaron seems to love her alot, jibi yanda yake bata gifts, ranan su diamond agogo dasu turare yau abinci da flowers masu tsinannen kamshin dadi, he’s so romantic, she thought babu miji that will be as sweet and romantic as Baban Yaseer yanzu taga wanda yafisa.
Hawwa ta hadu da irin gayen kan taki fadamata har sai bayan tayi hauka? The way suke soyayya hakan nan she can swear Hawwa tadan jima da sannin gayen? Wannan dayaketa bata gifts sunyi sex ne? Hawwa is so happy she wants her to be sad, tafison taga hawaye da bakin ciki da bacin rai da damuwa akan fuskanta, wannan gayen ya shigo rayuwanta yasa Hawwa ta chanza bata damu da itaba yanzu, imagine wai ita Hawwa ke shama kamshi, what will she do yanzu? Da kyar ta lallaba tashiga motan ta tada tabar wajen tana tana tafiya akan titi tazo ta wajajen banex ta kalli masu bara dake wajen, sai kawai tayi parking motan tafito taje wajensu tace “zan baku kyautan kudi sosai amman saikun bani wayanku na tura wani sako” har rige rigen bata wayan ake, kakkarba tayi marasa kati har tana samusu ta bank dinta, sako tashiga turama number Khaleel da kusan duka number su sannan ta basu 5k suraba tawuce takoma mota tana murmushi taja abinta zuwa gida.
**
Khaleel na cikin mota tareda Sam wayanshi yayi kara daukan wayan yayi yaga messages guda 5 from different numbers hardly unknown ke kiranshi ma talk more of sako, kaman bazai budeba saikuma yabude daya.
“_Hawwa is a whore! Tsohuwan karuwa ce she sleeps with everyman dayake zuwa yace yana sonta saisa suke guduwa basa aurenta sabida tabasu abinda suke nema_”
Chak Khaleel ya tsaya yana kallon messege din to be very very honest he doesn’t care idan Hawwa sleeps around or not cus yasan tun zamanin da wato old days aka daina samin virgins, konji is real babu yanda za’ayi yataso maka baka nemi wanda you will sleep with ba so what ai d’ane tayi, baida right to judge her life is not easy takai this years 29 without a man, shi tun yana 24 yafara ai, but dudda haka saiyaji still zuciyanshi namai wani iri sai kawai ya ijiye wayan da sauri without opening sauran messages din ahankali yace “park the car” Dasauri Sam yace “lafiya? We are not there yet” dan murmushi Khaleel yamai yace “just give me a moment” fita yayi daga motan yafara tafiya zuwa chan gefen titi baitaba sani akwai randa za’a gayamai wata yar iska ce harma yaji abun yadameshi ba, ko yadingajin ciwo aransa ba, duk sai yaji wani iri, who even send the message? What if is Hawwa? He don’t think she will ever defame kanta dudda yasan batason auren su but Hawwa is someone that value self respect and image nata, ko kadan batason compromising self respect and imagine nata saisa he even use that picture and threaten her with it, cus yasan she will not want him to expose that koda ba gaskiya bane dan she values her self respect, juyowa yayi yakalli Salman daya fito daga motan yana kallonsa da hannu yama Salman alamu daya daukomai wayansa amota daukowa yayi yazo wajen yakawomai dasauri ya karba yabude second message din.
“_Hawwa babe din boss dinta ne DIG she slept with him in order ya dauketa yasata a task force din nan dan she was an ordinary police girl before without any star_”
Sai another message. “_Officer Hawwa sleep with yaran office example Abraham data girmeshi da shekaru slept with Hawwa countless times_”,
Yanda zuciyan Khaleel ke bugawa kasa cigaba da bude sauran messages din yayi ya manna ma Salman wayan a kirjinshi yace “track those numbers all of them for me, track them! I need information uuughhhhh!” Ya dunkule hannu yayi punching air yawuce fiuuuu yatafi mota ya shiga da kanshi yarufo da mahaukacin karfi akaja motan Sam yace “lafiya are you okay”? Lumshe idanu yayi yaki magana har sukakai party saukowa yana shiga yadauki about 5 shots na tequila yana sha Sam yace “Lee are you okay? Why are you drinking like that” ko kallonshi baiyiba shaye shayen dayahau yi saida yabama duka abokanshi tsoro saida yayı total out sannan Sam da Moh suka kaishi sama aka kwantar dashi agado Moh yace “kasan what’s wrong with him”? Girgixamai kai yayi suka wuce suka fita daga dakin aka barshi warwas agado.
[10/6, 10:39 AM] +234 706 565 5343: EPISODE 5️⃣6️⃣
Washegari Khaleel yafarka adakinsa da kyar ya lallaba yaje yayi salla wuraren 9, ko wanka baiyiba yafito yasauko kasa Mommy na falo tace “good morning Son” ko kallonta baiyiba Noor ta taho wajenshi da gudu tace “Daddy” kanta yashafa kadan yace “go to grandma I’m coming Noor” yafice idanunshi sunyi ja duk sun nuna alamun bacci, yayi waje yana kallon Salman daya taho da sauri Khaleel yace “ya?” Salman yace “we tracked the numbers duka numbers din beggars ne dake hanyar banex, da kyar bayan nabasu kudi suka iya sanar dani wata mace ce tazo tabasu 5k tayi amfani da wayansu” dasauri Khaleel yace “did you ask them description nata?” Salman yace “yeah wai batada tsawo sosai she’s very fair and da Toyota tazo” shiru Khaleel yayi kaman mai tunani, kawai yawuce wajen motar sa Salman yabiyosa ya shiga driver ma yashiga sukabar gidan, ahankali cikin muryan gajiya da bacin rai yace “my wife’s house” jan motan sukayi har zuwa unguwan su Hawwa.
Baba na kofar gida azaune da aswaki a bakinsa ya hango mota yasan Khaleel ne kawai sai yafara murmushi kafin ma abudemai Khaleel yabude da kanshi yafito Baba ya tsareshi da idanu ganin idanunshi adan kumbure hakama fuskanshi dasauri Baba yataso shima Khaleel yawuce wajen Baba kafin yayi magana har Baba yakai hannunsa kan fuskanshi cikeda so yace “bakada lafiya ne Ibrahima”?Baba Khaleel ya kalla dan ranshi abace yake yayi shiru yakasa magana sai dan huci da yasauke Baba sai kawai hankalinsa yatashi yace “meya sameka? Tell me”? Dan ijiyan zuciya yasauke yajuyo yakalli Salman da hannu yamai alamu yakawomai wayanshi wayan aka kawomai muryan Khaleel ba dadi yanunama Baba wayanshi yace “Baba wasu sakonni aka turamin marasa dadi bazan iya karanta maka ba kaima, nasa ammin tracking number” yadanyi shiru Baba da gabanshi ke faduwa yace “ina jinka gayamin menene ke faruwa”? Cikeda jin zafi Khaleel yace “Baba matana ta batamin rai sosai, ina kyautata zaton har yanzu tana tareda mahaukaciyan nan, so nazo na ganta ne”
Dudda Baba baiga sakon ba but ayanda yaga Khaleel yasan Ni’ima tayi wani abu ranshi inyayi dubu yabaci tsabagen bacin rai yace “muje ka shiga gidan kacimata mutunci ba anan waje zan kiramaka itaba, ai gidana nakane ban maka iyaka da ko’ina acikin gidannan ba, muje” Baba yayi gaba Khaleel yabishi abaya suka shiga cikin gidan ko’ina a gyare ta buga sallama gaban dakin Hawwa, Ammi ta amsa yace “da mijin Hawwa nazo Zainabu” Hawwa dake zaune daga ita sai dan rigan bacci tana danna wayanta dasauri tadauki hijabi tasaka dark blue har kasa, ita dama Ammi da hijabi ajikinta Ramla kuma na kitchen tana aiki dasauri Ammi ta tashi da fara’a tace “bismillah bismillah kushigo” shigowa Baba yayi Khaleel biyeda shi abaya, kan Khaleel na kasa yace “ina kwana Mom” “muntashi lpy Khaleel” ahankali Baba yace “biyoni Ammi” binshi Ammi tayi suka fice daga dakin tareda maido musu da kofan suka rufe, Khaleel yazuba hannu a pocket nashi yana kallon Hawwa dako dagokai batayi ta kalli inda yakeba, kaman ma batasan da mutum awajen ba, Babu wasa kan fuskanshi rai abace yace “wacece ke tareda ke jiya a office?” Batare da Hawwa ta kalleshi ba tace “da wanda nake tare, ko wanda nai magana, ko wanda nagani a office is none of your damn business” ran Khaleel abace ya daka mata tsawa da saida dakin ya amsa. “Nace dawa kike tare jiya an office!”? Dagokai Hawwa tayi adan tsorace sabida yanda yayi mata tsawa ta tabbata anji a tsakar gidan, tashi tayi daga gadon ta taho inda yake dasauri dan bataso su Ammi suji tanamai ihu suhau mata fada akanshi, hakan yasa tace “who do you think you are kanamin ihu aka?” Ran Khaleel abace yanunata da hannu yace “dawa kike tare an office jiya?” “My friend!” Hawwa ta amsa kai tsaye ganin yadameta da tambayan, cikeda jin haushi tace “I was with Ni’ima me akayi? Sabida an auramin kai saina tambayeka kafin naga kawata konai magana da kawata”? Wani irin fizgota Khaleel yayi yakai hannunshi zuwa wuyanta ranshi abace yace “what is so special about that witch of a woman da kin kasa hakura da ita? Are you a lesbian!? Are you really into girls?”
Ja idanun Hawwa suka soma yi tafara dukan hannunshi hakan yasa yasaki wuyanta tadanyi tari kadan sannan ta kalleshi tace “da aurenka gwara zama da Ni’ima! At least ita bata living wayward life irin naka!”Radadi zuciyan Khaleel yafara sai kawai yakara fizgo Hawwa yakama kafadunta ya matse yana kallon cikin idanunta zuciya yakaimai wuya da kishi kai da komi ma ganin yanda Hawwa ke son Ni’ima yace “idan nakara ganin ki da yarinyar nan i will killl her! I will ruin her life! I will make her life a living hell you know me so well to know duk abinda nakeso nayi sainayi, stay away from that witch evil vile woman inba hakaba saina kasheta!”
[10/6, 10:39 AM] +234 706 565 5343: EPISODE 5️⃣7️⃣
Ayanda yau taga idanun Khaleel saida Hawwa ta tsorata wlh, bata taba ganinshi haka ba, yanda ranshi yakai ga baci yasa kawai ya turata yajuya yabude kofa yafito Baba da Ammi na tsakar gidan sunyi charko charko a tsaye, yama kasa kallonsu sabida baison suga kwayan idanunshi yawuce zaure da sauri Ammi tabiyoshi daidai ya shiga zaure tace “Ibrahim!” Chak Khaleel ya tsaya batare daya juyoba, dasauri Ammi ta taho tazagayo ta gabanshi sai kawai Ammi tasa hannu takamashi ta zaunar dashi kan bench dake zauren ahankali yazauna sai kawai yakai hannayensa biyu yarufe fuskansa yafuzar da iska masu zafi kaman zai kama da wuta sakonnin nan nacimai rai, ahankali Ammi tace “it’s okay ya isa Khaleel ya isa” sauke hannunshi yayi ya gyadamata kai ahankali yace “thank you Mom” anatse Ammi cikin hikima tace “can you show me sakonnin da aka turamaka game da Hawwa”? Araunane ya girgiza kai yace “Mom banso kowa yagani, sirrin matana ne I can’t show you banso kumata wani kallo” kirji Ammi tanuna tace “nine mahaifiyar Hawwa, show me Ibrahim idan akwai abinda yakamata namaka bayani zan maka, banso ku fara aure da zargi ko kokonto aranka, ayanda abin ke tafiya nan gaba hala za’a iya maka sakonnin dayafi wayan nan daci ma da tada hankali ma, so show me” Allah yasani sabida nauyin Ammi dayakeji ne yasa gently yamikama Ammi wayanshi daya bude mata message yace “5 numbers suka turo sakkonni, nasa anmin tracking akace lambobin wasu beggars ne, jiya danai magana da ita suna tare a office dinta, I believe somehow she took my number from wayan Matana batare datasan anyi ba” duka sakon nin Ammi tabi takaranta ran Ammi yama Ammi badadi sai kuma takaraji ta natsu da Khaleel tama aminta dashi gabaki daya, dawani ne da yasaketa yace yafasa aure but shi yazo kawai yayi warning nata kan zama da Ni’ima ne, ahankali tace “Khaleel wlh karyane kazafi akeso ama Hawwa! Babu wani abu na Hawwa daban sani ba, Ni’ima so take takashe auren ku, wlh Hawwa bata taba soyayya da Oganta ba, Hawwa maza tsofaffi ma basa burgeta, sheri ne diyata ba haka takeba, sai kuma abokin aikinta Abraham tabbas ta sanar dani yaron na bibiyanta shima bawai ya iya yafurta da bakinsa yana sonta ba, ai bata bashi fuska, yana mugun shakkanta, Hawwa bazata taba iya soyayya da wanda ta girma ba Khaleel kuma wanda yake ba addininta ba, saikuma na karshe sauran samarinta“ anatse Ammi tace “Ibrahim Hawwa na can be everything, stubborn, mafadaciya da sauransu amman Hawwa na ba mazinaciya bace! Dudda ta dade