Showing 117001 words to 120000 words out of 143458 words

Chapter 40 - Gargada So Hausa Novel Complete

M SHAKUR   

19 Nov 2024

946

batai aure ba bata taba kallon zina as solution na matsalolinta ba, duk ina maka bayanin nan sabida ni uwa ce bazanga ana so akashe auren y’ata naja baki nai shiru ba, duka sakon nin nan karya ne Khaleel koda bakai trusting Hawwa ba trust me ni mahaifiyarta, I will never lie to you kaji”.


Sosai Khaleel yake kallon Ammi natsuwan da tun jiya yakasa samu bayan yaga sakonnin nan sai Ammi tabashi natsuwan in just few minutes ya yarda and he believed her, gyadama Ammi kai yayi ahankali yace “I know! Deep down I know my wife is not like this, kawai bansan mesa zuciyana keta zafi yana radadi ba bayan na karance messages din” yasan inda Hawwa yar iska ce da bazata taba tsanan halinshi ba, sabida batayi saisa she despise his way of life, dan murmushi kadan Ammi tayi tace “sabida kana sonta ne saisa kakejin haka!” Tsare Ammi Khaleel yayi da ido jin tace yanason Hawwa bayan shi yasan baya sonta he just wants to show her he can have her idan yanaso, ahankali Ammi tace “Khaleel aure dole agina foundation da trust, you have to trust matarka, itama matarka have to trust you, ta hakan ne zaku iya strengthening bond naku ta yanda babu any makiyi dazai iya zuwa ya jijjigaku kaji” gyadama Ammi kai yayi ahankali Ammi tace “tashi kaje gida kai wanka Ni’ima zanje har gidansu naga mahaifiyarta” gyadama Ammi kai yayi baiso yagayama Ammi what he’s planning dan zata iya hanashi but Ni’ima zatasan she messed with the wrong person this time, tashi yayi yawuce haryakai kofa saikuma yajuyo hada ido sukayi da Ammi kai yadan sosa yana sauke idanunshi kasa ahankali yace “thank you Mom for guiding me” yana maganan yawuce yafita Ammi tai shiru tana kallon inda yabari saiga hawaye ya sauko daga idanunta daidai Malam na zuwa zauren ahankali Ammi tace “Malam ina alfahari da wannan miji dakama Hawwa hakika Hawwa tai sa’a! Hawwa tai dace” ahankali Baba cikeda damuwa yace “nagode Zainabu da babu ke da bansan yanda zanyi handling issue din nan ba, me Ni’ima ta turo a sakon”? Karantama Baba sakon tayi tass sannan suka tashi suka wuce dakin Hawwa tana zaune ganinsu yasa ta tashi ta taho wajen Ammi tace “Ammi wlh ita tazo wajena an off…….” Tassss! Ammi ta yanka mata mari mai kyau da lafiya Baba yace “nagode Zainabu!” Hawwa ta dafe kuncinta dasauri, wani irin feeling Ammi keji aranta, irin after much struggles da wahala da kata katan rayuwa da gori, habaici maganganun banza, gulman makota da mutanen gari, kasamu ka aurar da diyarka wata yar iskan kawa na kokarin kashema yarka aure, cikin murya mai rauni Ammi tace “Hawwa magani Ni’ima tabaki a abinci kikaci da bazaki iya rabuwa da ita ba ko me? What did I tell you about that girl ranan nan? Ni da mahaifinki nan mun gayamiki Ni’ima bata kaunarki kona miskala zarratin, ta tsaneki, kukanta kukan mazuru ne, kukan karyane da yaudara, so tabiyoki jiya office kika bari tazo, kinsan cewa Ni’ima ta dauki wayanki a sace ta kwashi number mijinki?” Hawwa dake dafe da kuncinta tana kallon Ammi da mamaki tabude baki in disbelief, tace “Ammi karya yamiki kawai ya tsani Ni’ima ne” “kinci mai garinku Hawwa kaniyanki” Baba yamata dakuwa yatsunshi kaman zasu shiga kwayan idanun Hawwa yace “mijinki kike kirada makaryaci”? Sauka kanta tayi kasa ahankali, Ammi tace “ta aikama Ibrahim sako cewa DIG oganki, Abraham da duk duka samarinki dasuka gudu jikinki kike basu suna amfani dake” dawani irin sauri Hawwa takalli Ammi, Ammi tace “tayi amfani da wayan masu bara jiya at exactly 2:15 ta tura” shiru Hawwa tayi basu wani dade da rabuwa ba aka tura sakon, Ammi tace “he tracked the number masu bara sukai kwatancen ta da motarta you are lucky bai sakeki ba Allah yaga zuciyanki yabaki miji mai sonki da tsaya miki haka” Ammi ta nuna kanta tace “idan har ni Ammin ki Zainabu na kai mahaifiyarki na isa dake, dagayau namiki iyaka da Ni’ima baki ba ita! Ko wayanta kika kara dauka ban yafemiki ba Hawwa!” Sosai Hawwa ke kallon Ammi, Baba yace “nima idan na isa nakuma kai matsayin mahaifi agareki namiki iyaka da Ni’ima har abada! Ni’ima bata kaunarki! Ta tsaneki, bakin ciki take dake, idan Ni’ima tasami hanyar kasheki zata kasheki Hawwa, dan haka bassss! Bassss! Enough! Bake ba ita, da raina bazan bude idanu inga kawa na neman kashema y’ata auren da ba’a riga an kai daki ba, tundadai an baki hutu awajen aiki dagayau na ijiye dokan kada ki kara fita daga gidan nan unless shi mijin naki ne yazo yanaso yafita dake, sa hijabi muje gidansu Ni’ima Zainabu”.
[10/6, 10:39 AM] +234 706 565 5343: EPISODE 5️⃣7️⃣


Koo kadan jikin Hawwa ba karfi jin abubuwan da su Baba suka fadi, dafe katifa tayi tazauna ahankali tai shiruuu tana tunani, duka abubuwan da Ni’ima tamata abaya she kind of give her excuse sabida Aliyu duk shi yaja da sauransu, so tasan ba kowa ya iya handling kishi ba, kuma tasan yanda Ni’ima ke mugun son Aliyu, so tamata excuse dudda she goes as far as tana zagin iyayenta tana tonamata asiri, but this! Yaushe ta dauki wayanta harta dauki number Khaleel dabatai saving ba? Takasa yarda still, kodai Khaleel sheri yayi mata da karya sabida ya tsaneta? Sai kawai ta tashi da sauri ta dauki wayanta takira Abraham ringing daya ya dauka tace “Abraham I remember kataba cewa kasa wani invincible CCTV camera an office dina right?” Dasauri yace “yes Miss Hawwa” ahankali tace “can you send me footage na jiya at about 1Pm zuwa 2pm” Dasauri yace “sure give me 3mins” ta katse wayan ta zauna tana kada kafa she really don’t wanna believe Ni’ima did all this dasu Baba suka fadi noo! Ni’ima tai nadaman everything datayi abaya, she’s a changed person, kishin Aliyu yasa tayi all those things ada.

3min basu cikaba Abraham yaturo mata video ta watsapp dasuri tashiga downloading yana gamawa tabude dasauri tashiga kallo gabanta na mugun faduwa tana cewa kanta No No Ni’ima can’t do this to her, aiko saiga Ni’ima na daukan wayanta tana daukan number tana kallon kofa atsorace, wani irin runtse idanu Hawwa tayi murya araunane dake cikeda mamaki tace “Ni’ima!” Ijiyan zuciya ta sauke ta fuzar da iska mai dumu ta ijiye wayan a gefe, she’s really hurt dudda bataga text dinba but for Ammi to slap her this hard that means she said alot tabata mata suna, dole Khaleel yaji ba dadi zaiga tana crucifying nashi on something da itama tanayi, fuzar da iska tayi bataso tayi kuka akan Ni’ima yau but zuciyanta namata wani iri kaman ma idan tai kuka zaifi rage mata zafin dayake mata yanzu.

Hawwa na zaune a wajen idanunta sunyi ja almost 1hr dafitan su Baba da Ammi taji ana bude kofanta dasauri tadago kai, ganin Khaleel again saida gabanta yafadi da sauri taboye wayan dake hannunta na video akasan bedsheet sabida karya ga video, yana shigowa babu wata wata kawai yazo inda take zaune tana kallonshi, hannunshi yasa yakamata yadagata yajata turjewa tayi tace “stop touching me ina zaka kaini kuma”? Cikin bacin rai Khaleel yace “i want to show you wacece wacce kikai considering as true friend” kawai yajata takalmi tasaka sukai waje takasa kwace hannunta Salman yabude musu bayan mota ita tafara shiga sannan shima ya shiga aka rufe motan aka ja, to her biggest suprise hanyar office nata taga sunyi, dasauri takalleshi tace “ina zaka kaini?” Banza yamata yaki amsata har office nasu, parking yayi yana rikeda hannunta suka wuce ciki har zuwa office na DIG kai tsaye Khaleel yabude office din batare dayama yi knocking ba, DIG Hawwa tagani tareda Abraham duk zaune, DIG na ganinshi da sauri DIG yatashi yace “Mr Ibrahim I……” hannu Khaleel yadagamai strictly yace “did you bring her here yes or no?” Rai abace DIG yace “not just she duk ma wani wanda ke gidansu cus I will never take this defamatory statement likely” yakalli Abraham yace “bring everyone in” wucewa yayi yafita chan saiga wasu manyan yan sanda guda biyu sun shigo da Mama da Ammi sai Baba da Ni’ima dake sanye da doguwan rigan atampa dukansu sunyi zuru zuru dan duk suna zaune suna magana agida wasu yan sanda sukazo sukace ana inviting nasu to police station dukansu haka suka taho, Baba na ganin Khaleel da Hawwa yace “Ibrahima me kukeyi anan? Munje gidansu yarinyar nan ana cikin magana saiga yan sanda akace muzo chaji opis” ahankali Khaleel yace “nina turasu Baba” hannun Hawwa yasaki gently yasa hannu ya karbi karafunan Baba ya zaunar dashi a kujeran wajen yakalli Ammi yace “Mom sit” zuwa Ammi tayi ta zauna, gaban Mama dana Ni’ima suka shiga bugawa especially gaban Ni’ima dabatasan meke faruwa ba gabanta sai fadi yake cus su Baba dasukazo cewa sukayiwa Mama basuson yarta tareda Hawwa basuce komiba, kawai faduwa gabanta yake dudda bata kawo text messages na jiyaba dan batajin za’a iya gano ita bane, Hawwa takalla cikin makirci tace “Best is everything okay? Why did you call us here”? Wani daci Khaleel yaji aranshi yanda take kiran matarsa wani best azafafe yace “wlh kika amsa that beast sai ranki yabaci” yafadama Hawwa dake kallon Ni’ima jikinta yagama sanyi da Ni’ima sosai, faduwa gaban Niima yayi itama Hawwa tadauke kai kawai Ammi saitaji wani son Khaleel ya lullubeta.
Anatse DIG yakalli daya daga cikin yar sandan mata dake taredasu Mama, ba zato ba tsammani Ni’ima taji saukan bulalaaa akafanta dayasa kawai ta zube akasa tace “wayyooo Allah na” dasauri Hawwa ta juyo jin karan bulala da dukan Ni’ima, Yar sandan tace “mai laifi kneeling yakeyi ba tsayuwa ko zama ba a police station” rawa jikin Mama yafara dasauri ta duke itama kusa da yarta, DIG yakalli Ni’ima da kafafunta ke bari sabida zafin wayan inji yace “kece Ni’ima?” Gyadamai kai Ni’ima tayi tace “eh yallabai nice” gyadamata kai yayi yace “an shigo da karanki office dina daga Mr Ibrahim akan kinyi defaming matarsa, dakuma ni, da yaron aiki na” yanuna Abraham dake tsaye ransa abace yana kallon Ni’ima, DIG yace “No body ya isa yabata min suna, idan kowa na dakin nan yabarki ni bazan barki ba!” Faduwa sosai gaban Ni’ima yake tace “yallabai bantaba ganin ka bama, saidai wanchan na sansa ta dalilin Hawwa amman me dalilina dazaisa nabata maka suna wani sherin aka kulla min ne? Best something yafaru ne”? “stop calling matana da Best!” Khaleel yafada aharzuke kowa ya kalleshi har Hawwa dasauri dan kaman zai rufe Ni’ima da duka, DIG yace “calm down Mr Ibrahim” rike kansa Khaleel yayi kirjinshi na tafarfasa yayi punching air, DIG yace “jiya wuraren 2:16 kin tura sakonni marasa dadi zuwa wayan Mr Ibrahim”? Faduwa sosai gaban Ni’ima yayi ta zaro idanu tareda dafa kirjinta Mama na kallonta hankalinta atashe Ni’ima tace “Yallabai an ina zan sami number sa har na turamai sako? Ni kuma? Sheri akamin” Dan murmushi DIG yayi yakalli Abraham yace “play the first evidence” saramai yayi yace “yes sir”.
[10/6, 10:39 AM] +234 706 565 5343: EPISODE 5️⃣8️⃣


Wucewa Abraham yayi yana connecting laptop nashi to office television sai kawai ga video Ni’ima sanda take kwashe numbers daga wayan Hawwa, Hawwa na kokarin shigowa ta ijiye wayan da gudu, Mama tace “na shiga uku na lalace Ni’imaaaa” yanda kirjin Ni’ima ke rawa zaka dauka an sokashi da electricity ne, Hawwa ta tsareta da idanu just looking at reaction dinta, Ni’ima da sauri ta kalleta tace “Bes…..Hawwa I can always take anything daga wayanki, baki tabamin shamaki da wayanki ba, kaman yanda ban miki da nawa ba, ba lallai number Khaleel na dauka ba ai, abinda na kwafe daban fa number Ammi na dauka inaso namata sako na bada hakuri naga bata hakura ba” Baba yace “shegen karya kaman bokanya! Yau za’ayi maganin ki” DIG yadagama Baba hannu Ammi tace “kai shiru Malam” Baba yace “raina sosuwa yake ne Zainabu Amman nayi” DIG yace “bring in the second evidence” fita yan sandan sukayi chan sai gasu sun shigo da beggars din nan su biyar duk jikin su na rawa, Ni’ima jikinta yafara bari sosai data gansu, Hawwa kawai saitaji Hawaye yazo idanunta zuciyanta ya tsinke ganin reaction na Ni’ima so ita ta tura text din, DIG yace “zaku iya nunamin acikin dakin nan matar datazo tayi amfani da wayanku jiya bayan karfe biyu” dawani irin sauri dukansu sukai wajen Ni’ima dake susunnar dakai suna cewa “gata nan gatanan itace tabamu dubu biyar bayan tagama” DIG yace “fita dasu a sallamesu” sutafi ficewa dasu akayi.
Ni’ima jikinta yahau rawa, in her wildest dream bata taba tunani abinda tayi jiya will backfire like this ba before 24hrs like this is just 11 na safe, tadauka ma dazu dasu Ammi sukazo sunzo suce an fasa auren, Khaleel ya saki Hawwa ne fa, sai kuma taji suna magana kan arabata da Hawwa. Dasauri Ni’ima tashiga jan guiwa tafashe da kuka tana zuwa wajejen da Hawwa take tace “Hawwa wait I can explain, wlh wlh sherin shedan ne kuma harda naji haushi dakika ki kiramin Baban Yaseer…………” Tasssss! Aka dauketa da mari da saida ta kwanta flat akasan wajen tanaji kaman kunnenta yafita, Hawwa takalli Khaleel daya sauke mata mari yana huci da mugayen idanu tama kasamai magana, Mama ta dago Ni’ima dasauri dataki dawowa daidai tana jijjigata, DIG yataba kansa yana kallon su Baba da Khaleel yace “Baba, Mr Khaleel ni mahaifine, dudda ban haifi kaman Hawwa ba but I have a daughter of 24yrs, ni father figure ne all mata na office din nan I consider them y’ay’ana, bazan taba having wani abu dawata ba, an sanni my record is clean, mata basa gabana, matana daya aduniya rak 25yrs of marriage, as for Abraham data kira sunansa zan iya tsayawa Hawwa in tsayama Abraham, Hawwa y’ace da kowa a office din nan fara tundaga yan gate sunsan tanada kamun kai, infact Hawwa itace one officer namu da baka ganin murmushinta anyhow! This is police station fa kace zaka bama wani kanka ai saika dawo abincin kowa, the only relationship between Hawwa da Abraham is strictly work and will always be work!” Yakalli Ni’ima dake kuka sosai tadawo daidai yace “zanyi maganinki dagayau zakisan akwai freedom of speech but shin akwai freedom after the speech? Zan barki da question din dazaki amsa kanki da kanki daga baya” wasu takardu yashiga signing gaban Hawwa yashiga faduwa sosai ganin stamp din daya daga dasauri tace “Sir!” Atare daga DIG har Khaleel suka mata ihu. “Wat!” Dan kowa ransa abace yake, Ni’ima Hawwa takalla dake kuka sosai sannan takalli DIG ahankali tace “Sir tun dazu nasa Abraham yaturomin CCTV footage na office dina nagani, I knew ita tamin, I already have it a heart dina is over between us na bar Ni’ima har abada, amman dan Allah Sir karka turata prison, she’s a mother, banda haka ita ke kula da mahaifiyar ta, karka turata prison kaji Sir” wani kallo Khaleel kema Hawwa kaman ya dauketa da mari yakeji hakama Baba da Ammi tahanashi magana amman kana ganinsa kasan ashar yakeso ya durama Hawwa, DIG ransa abace yace “idan ke kadai tama laifi saiki yafe mata, this lady tayi making so much accusation ciki harda process na promotion namu tai mocking, she played with my name! I! Ni DIG! Da ma’aikatana You and Abraham my asset, government asset! Hawwah zan wurgata gidan yari tai kaman 1month kafin law yayi taking cause nashi, ashiga kotu abata proper punishment na defamation of character na mutane uku datayi, gidan yarin nan dazata zauna na wata daya punishment ne na ambato sunayenmu wanda nine nake mata shi kafin punishment na asalin law” daga Mama har Ni’ima fashewa da kuka sukayi jin abinda DIG yace, Mama tace “yallabai amata rai, amata rai, kumin rai nima, namuku alkawari ko hanyan da Hawwa zatabi Ni’ima bazata karabi ba Billahil Azeemu, dan girman Allah kuyakuri sherin shedan ne” mtsww DIG yayi tsaki yawani buga stamp a paper dayasa Hawwa tace “noooooo” DIG yamikama yar sandan takardun yace “akaita prison now now ku jefar da ita” Ni’ima tarungume Mama da karfi tana ihu sosai. “Mama Mama karki bari su tafi dani, Mama na shiga uku na lalace, Mama karki bari su tafi dani, Hawwa, Hawwa kiyafemin Hawwa is me fa, kiji tausayina Hawwa, kimin rai, kituna su Yaseer da Yasmeen, Hawwa tare muka girma, muka taso and did everything together, Hawwa tundaga Abuja nataso nazo kano graduation ceremony dinki na yar sanda ko Baba baizo wajen ba sai ni sai Ammi” Afusace Baba yace “sabida kafana ne banje ba badan banso najeba kinji makira mai bakin hali, annamimiya algumguma, shi ramin mugunta dama kurarre ne idan baka hakashi ahankali ba kaine ke fadawa cikinsa, gashinan ai abinda kikama kanki, kinso kashe ma y’ata aure amman kalli kece kika kwana ciki, wannan saiya zama darasi da ishara agareki, adinga sara ana duban bakin gatari, kikaje gidan yari kiyita tofama kanki da Alhamdu ko Allah zai yaye miki bakin cikin nan, da kishi, da hassada azuciyanki kinji makir……” muryan Hawwa na rawa sosai tace “Babaa!” Shiru Baba yayi Hawwa ta share fuskanta Ni’ima tabata tausayi, bawai sabida tana sonta or anything ba as a human being kawai tana tuna yaranta, ahankali muryanta na rawa tace “Sir Ni’ima made a mistake okay, wlh nabarta har abada No more friendship amman please don’t send her to prison” DIG ya dauke kai kaman baijitaba, saikawai tajuyo takalli Khaleel idanunta sunyi jaa sosai cikin raunin murya tace “dan Allah Khaleel kayakuri please” dauke kai yayi tareda juya mata baya, zagayowa Hawwa tayi ta gabanshi takasa daurewa tafashe da kuka tana kai hannunta ahankali ta kama hannunsa tace “if you loook at

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login