Showing 96001 words to 99000 words out of 143458 words
sharing da Ni’ima gwara tayi da ita, tabata labaran hakan zaisa ta manta da Ni’ima, Ammi ta karba tana budewa tarike baki tace “au dan gidansu yartawa yake cewa Yar Sanda Kulu lallai Ibrahim yacika sarkin tsokana” Ammi tabude kwalin agogon taciro tana kama hannun Hawwa ta dauramata tace “masha Allah cip cip idan gobe yazo saikisa yaganki dashi yaji dadi haka akeyi ma miji” Hawwa tadan turo baki tana tauna baki batadai magana ba gudun karta batawa Ammi rai Ammi tasamata bracelet din shima yamata kyau sannan ta bude turarukan ta feffesa mata itama Ammi ta fesa anata jikin tace “uhm ni Maman Amarya nima nayi kamshi” dan murmushi kadan tayi Ammi tace “kai gaskiya mijinki ya san kan turare Hawwa kinji kamshi” dasauri tace “Ammi nabaki ki daukesu ni dama inada turare na” dakuwa Ammi tamata tace “kwal ubaki Hawwa mijin naki yamiki kyauta zakimin, kaji yarinya inga kin bama wani saikin sani” turo baki tayi ta tashi kawai tana rage kayan jikinta Aminu yayi sallama yashigo wani waya daban yakawoma Hawwa yace “Ya Ibrahim yace nakawo miki” wayan takalla Iphone ne bamatasan wanne ba ganin Ammi na kallonta ta wutsiyan ido yasa tasa hannu ta karba tace “to” ta ijiye tawuce bayi.
Around 10 duk sun kwanta ita Hawwa sabida zatai azumi gobe Ammi kuma sabida zatai tafiya gobe, sabon wayan dataki bi takanshi tuntuni ne yahau ringing ita batamasan sim dinta ne ciki ko wani dabanba hakanan dai taji bazata dauka ba, wayan na karewa yashiga ringing again Ammi tace “wai ba ke ake kira ba Hawwa nafasan ba bacci kikeba” tashi tayi ta sauka daga gadon tasa hannu tadauki wayan akan mirror tadawo gadon ta kwanta sannan ta danna wayan takai kunnenta sabida Ammi yasa ta kwantar da murya sosai hakan yasa muryanta yayi wani irin dadi ahankali tace “hello” lumshe idanu Khaleel yayi yana gyara kwanci afalo ashagwabe yace “I’m hungry Kulu” wani iri Hawwa taji yanda yayi magana hakan yasa tayi shiru, Khaleel ahankali tace “I don’t feel like eating abinda chef namu suka dafa, nazo kimin girki Kulu?” Runtse idanu Hawwa tayi tace “nace banson sunan nan” ahankali yace “but Hawwah is Hawwa Kulu” Shiru Hawwa tayi the way yake kiran Hawwa dadi, sabida Ammi tadaure tace “bacci zanyi zan tashi nayi azumi anjima good night” zata cire wayan daga kunnenta yace “but it’s not Ramadan, azumin me kikeyi ramuwa?” Shiru tayi ta lumshe idanu kaman bazata amsashi ba tace “nafila ina azumi Monday and Thursdays” cikin yar karaman murya yace “nima zanyi” yayi shiru jin batace komiba Khaleel yace “sainai addu’a Allah karya baki ikon bata auren mu, I want to live my life with you” yafadi ahankali baimasan mesa yake fadin hakaba but kawai yanaji ajikinshi bazai iya rabuwa da ita ba dan juyawa Hawwa tayi ganin Ammi tayi bacci ga ijiyan zuciyanta tanaji hakama Ramla yasa ahankali tace “you’re a liar! Kaida ke wulakanta mata bakasan darajansu ba, imagine locking your Baby Mama in jail, Allah bantabaji I hate someone kaman the way na tsaneka ba” shiru Khaleel yayi sai kuma chan yace “do you love my gift?” Cikeda tsana tace “I will never love anything that comes from you” shiru yayi baice komiba Hawwa kawai tazare wayan daga kunnenta daidai yasake kira kaman bazata daukaba tadauka kafin yayi magana tace “how could you send that video to Nursing Council don’t even deny it nasan aikinka ne, why would you do that to my friend?” Hamma taji yayi yace “zan fita I know you don’t have friends so bansan wat you are saying ba bye” Hawwa tace “aikin kenan party giya da mata” murmushi yayi yace “gashi na aureki” zatai magana ya katse wayan jitayi ranta yana kuna yana susa tasan yanzu club zaije maybe Allah kadai yasan time dazai dawo shiru tayi sai chan ta tuna yanda yamata kiss a kumatu a mota dasuri takai hannu tashiga share kumatunta kaman yasamata dafi ahaka tai bacci.
Washegari around 8 suka fito dudda tanajin bakin cikin shiga motan nan haka ta shiga Ammi tafara kaiwa park sannan tawuce office.
Tundaga gate ake mata yajiki ana mata Allah kyauta tana zuwa direct office na DIG tayi tai knocking yabata izinin shigowa yana ganinta yadakatar da rubutun dayake yace “Hawwa are you sure you’re strong enough kidawo aiki?” Murmushi tamai tace “yes Sir thank you” anatse yace “welcome back” gyadamai kai tayi ganin ta tsaya bata wuce ba yasa yace “akwai wani abu ne?”
Gyadamai kai Hawwa tayi cikeda damuwa, seat dake gabanshi ya nuna mata hakan yasa ta zauna akan kujeran ya ijiye pen na hannunshi yace “I’m listening Miss Hawwa” gyadamai kai tayi anatse tace “Sir I have a very serious problem I need your help” gyara zama DIG yayi dan yana bama Hawwa respect da girma dan ijiyan zuciya ta sauke tace “Sir I’ve never been to Senate President house banda time din nan damukaje aiki, I know nothing about them or household nasu” with so much anticipation DIG yace “what’s with Excellency Hawwa?” Ijiyan zuciya ta sauke cikin raunin murya sosai tace “Sir ranan danai accident ina hospital Babana yabasu aurena, sai bayan mun dawo gida anyi discharging dina ake sanardani wai wannan yaron nasa Khaleel aka auramin” tayi maganan hawaye mai zafi na sauko mata DIG kanshi was in shock yazaro idanu yana kallon Hawwa yace “you mean Khaleel Baban Noor”? Gyadama DIG kai tayi bakinta na rawa tace “I have no idea me suka gayama Babana, banso Khaleel yake yakarani acikin sahun matansa sabida yayi using dina and dump me bayan 1 or two weeks” Ko kadan DIG baiji dadin news dinba but still cikeda damuwa yace “Hawwa akanme mahaifinki zai bada auren ki batare dayayi bincike ba? I’m not saying that because maybe zasu miki mugunta or something no su basa wannan, kawai dansu baisan menene aure ba, baisan darajan auren ba, mata are like papers zai iya bude this page ya yaga and open another page, so why will your father get your married to such kind of man”? Bayan hannu Hawwa tasa tagoge idanunta tace “sabida he’s tired of me, yagaji da yanda nake zaman mai agida ba miji” DIG ko kadan baiji dadi ba yasakeyin shiru sai chan yace “to wani help kike magana zan miki”? Share fuskanta tayi tass kaman batai kuka ba takalleshi tace “I want you to come with me Sir muje ka gayama Babana the type of Man Khaleel is cus wai on 23RD this month za’ayi biki zan tare, I don’t want this marriage I don’t want to be victim of circumstance na gayama Babana all I know yaki yarda I’m sure ka tayani gayamai zai yarda”.
[10/6, 10:39 AM] +234 706 565 5343: EPISODE 5️⃣2️⃣
Kallonta DIG ya tsaya yana yi kaman mai lissafi na kusan 2min sai chan ya sauke ijiyan zuciya yace “Hawwa listen ki fahimceni keba yarinya bace I will be very raw in whatever I will tell you now” yadan sauke ijiyan zuciya yace “I’m a father inada yara mata babu wanda ya isa yazo yace zai aure yarana nabashi batare danayi bincike ba, for mutanen nan suzo mahaifinki yadauke ki sharp sharp batare daya damu dako kinaso ko bakiso, ko kinsan guy din ko baki sansa ba yabada ke only mean one thing” yadanyi shiru yana kallon Hawwa yace “just like rest of the victims parents kema maybe mahaifinki just did it for money ne so kina gani koda zanzo nace gashi gashi mahaifinki zai yarda akashe auren?” Hawwa tai shiru yace “saikuma second abu, Hawwa you’ve been in this job kinsan yanda aikin gwamnati yake, Baban yaron nan sune Nigeria gabaki daya do you want me to be on the bad side of such kind of people?? Naje nace kaza kaza ko baban ki baice ni ba ne las las zasu gano nine kinsan abubuwan da hakan can cost me?”
Yasake shiru yace “banda haka this is personal matter not work related, maganan aure ake ni as Oganki ko Boss dinki baikamata na shiga ba sai inzo naji kunya nan gaba cus of What If dayawa dana hararo in the case, what if ke bai sakeki like the rest of the matan ba? What if ya zauna dake har abada? Hawwa you have power what if you somehow influence him ya gyara all those hali and changed? Idan ya chanza is a good thing since he’s not a murderer ko wani kidnapper” Ahankali DIG yace “just think it through but I don’t think is proper for me to interfere Hawwa, kiyakuri but I don’t think hurumina ne tunda har Babanki ne yabada ke da kanshi just pray and seek Allah guidance Allah sadaki da alkhairinsa” hawaye Hawwa taji ya zubomata sharrrr tai shiru a office din anatse DIG yace “so sorry Hawwa” tadade ahaka sannan ta share fuskanta tamike tace “is it okay nai resuming gobe Sir I have to be somewhere”? Gyadamata kai yayi yace “sure take your time” wucewa tayi tafita yabita da kallo tawuce tashiga motanta ta tada Maman Noor kawai tafado mata arai, she’s her only second hope.
Sanin tana prison hakan yasa tawuce prison na mata, parking tayi tana zuwa ta nuna ID card nata tawuce office na prison warden din ta zauna bayan sun gaisa da Matar Mrs Adebayo tace “wakikeson gani yau Miss Hawwa”? Anatse Hawwa tace “Hadiza Muntari wacce was convicted sabida kidnapping yarta datayi that senate president case ish” dasauri Mrs Adebayo tace “ohh Hady we call her Hady anan, ai jiya an fitar da ita, wasu yan sanda sukazo da clearance from court they withdrew the case against her wlh she’s so lucky” sosai Hawwa ke kallon Mrs Adebayo Khaleel ne ya yafemata sabida jiya ta gayamai she will find evidence against him? Mrs Adebayo tace “why are you looking for her”? Murmushi kadan Hawwa tayi mai ciwo tace “kinsan nine nai investigating case din but well that aside nace ko kunada home address nata yar wani gari ce kinsani”? Girgiza mata kai tayi tace “no gaskiya yar Bidda ce but bamu da address nata” Shiru Hawwa tayi saikuma chan tamike tabata hannu suka gaisa tace “thank you very much” tawuce tafita.
Tunda tafito tana tafiya zuwa parking space ta hango Khaleel tsaye jikin motarta tsaye yana sanye da dogon wando da shirt dabai saka boturan sama ba, faduwa gabanta yayi akwai tracker a motarshi ne datake ja yanzu? How did he know tana nan? Daurewa tayi ta karasa ko kallo bai isheta ba tazo zata wuceshi tabude motan ya fizgota tadawo baya kaman paper azuciye Hawwa ta buge hannunshi tace “don’t touch me again! Stop touching me!” dan zaro manyan fararen idanunsa Khaleel yayi yace “someone is in a bad mood today wow!” Yadanyi dariya yana kallon yanda tahade fuska tana kallonshi yace “smile it’s Sunna!” Hararanshi tayi jin abinda yace tace “so kasan sunna” tashiga fizge hannunta yaki saki sai kawai yabude bayan motanta dan tariga tai unlocking car din da key hannunta tun dazu datazo wajen, yaturata cikin motan yashigo shima da sauri ta matsa baya tamai ihu. “Wai mehaka? Leave me alone!” Dan cute smile yamata yace “sabida kinga matar nan an saketa is that why you’re in this bad mood?” Ja idanun Hawwa sukayi takalleshi azuciye tace “even if it means me bringing down the whole world searching duk lungu da sako I will do it! I will get Evidence and I will show Baba and my entire family the kind of person you’re! Khaleel just know this and keep it at the back of your mind bazan taba zaman aure dakai ba, you’re a worthless boy da baisan darajan mata ba! You don’t value mata! You treat us like trash! And I refuse to be one of your victim”Khaleel na kallonta yadan rage murya yace “konama wasu kenamawa? Why do you hate me?” Ihu Hawwa tamai tanaji kaman ta shakesa tace “I hate you sabida you’re a piece of thrash! I hate you sabida you’re a f*ck boy! I hate you sabida you’re a playboy! I hate you sabida you think life is just about women, money and parties! Kace nikamawa dazan tsaneka?” Tadanyi shiru kadan takalleshi da masifa eyes nata tace “kasan abinda ake cema ciwon y’a mace na y’a mace ce? I hate you sabida abinda kama all those women daka wulakantar” dan tabe baki yayi yace “I don’t want them why should I keep them?” Hawwa afusace tace “you don’t want them why did you marry them and ruined their life eh Pop boy”?.
[10/6, 10:39 AM] +234 706 565 5343: EPISODE 5️⃣3️⃣
Dan shiru Khaleel yayi yana kallonta ganin yanda zuciyanta ke tafarfasa, she’s really angry today, and as far as he’s concern he didn’t ruin any girls life rather he makes their life even better and colorful, all of them and family nasu are living large yanzu, lumshe idanu yayi yabudesu kadan ya kalleta murya chan kasa yace “I can’t stay 2days without having s*x!” Wani irin yammm kunnen Hawwa yayi jin abinda yafadi tadan dauke kai daga kallonshi da sauri, murya chan kasa yace “I started getting married at 24yrs, call me anything ni ba mazinaci bane Mommy na auramin su ne nayi s*x” runtse idanu Hawwa tayi da kyar tabudesu zuciyanta na radadi yanda yake magana akan mata tace “sannu Moms boy! Mata sun dawo maka toys for your selfish satisfaction eh dan gata”? Kallonta Khaleel yayi asanyaye Hawwa taji kaman zata kama da wuta ganin yanda hankalinshi kwance tace “okay nima so kake na shiga cikinsu tell me I will be your 10th wife ko 20th?” Anatse kai tsaye kuma yace “14th wife actually!” Wani zuciyane ya debi Hawwa batasan sanda tayo kanshi takama gaban riganshi ba fearlessly ta jijjigashi ranta na kuna tace “how dare you marry me Khaleel? Sabida kaga nakai 29yrs banyi aure ba is that why you took advantage of desperate state na Baba na and use the perfect timing ka aure ne eh talk?” Tayi maganan Hawaye na cika idanunta sosai tana kallon fuskanshi ta rike gaban shirt nasa gam gam, Khaleel yayi shiru yaki magana ganin ranta abace yake yau sosai cikeda bakin ciki ganin yaki magana Hawwa tace “how dare you take away the only evidence danake sa ran zan samu na nunama Baba wayekai eh? Khaleel I don’t deserve you, after good 29yrs banyi aure ba clocking 30 I’ve been so patient cus nasan Allah will reward me for imanin danayi, why will I end up with the worst person dana sani aduniya you!? I’m too good to be your wife, you are a bad bad badddd person Khaleel I hate that kai Baba ya auramin!” Tai maganan hawaye na saukowa daga idanunta tana kallon cikin kwayan idanunsa kaman yanda yake kallonta shima, all this while batai kuka ba sabida tanasa ran she will have something to show Baba but yau da Khaleel yayi outsmarting nata sai taji duniya yamata zafi, duka takaimai a robust chest dinshi hawaye na dauka daga idanunta tace “I hate that kai Baba ya auramin! I hate you Khaleel I hate hate hate you na tsaneka! Na tsaneka” tafashe da kuka tana kaimai duka sosai akirjinshi duk yana kallonta asanyaye, cikin kuka tace “I remembered the day daka fadamin one day sainai kuka ina begging naka for mercy agaban that super market” cikin kuka har shesheka take hawaye har gemunta tace “you won! You won! You won Khaleel, I’m sorry for everything Ibrahim! I’m sorry for being rude, for insulting you calling you jobless, I’m sorry for everything dan Allah kasakeni! Please divorce me dan Allah” tashiga kuka sosai bana wasaba, bata taba sanin zata iyama Khaleel kuka hakaba, ahankali Khaleel ya lumshe idanunshi da hannu daya ya fizgota yasata ajikinshi “leave me leave me” Hawwa tai ihu amman saida yasata ya kankameta sosai tun tana hargowa hartai shiru ajikinshi tana kuka ahankali.
Lumshe idanu Khaleel yayi yana shakan cool kamshin datakeyi dayamai dadi sosai tana kuka yakai bakinshi saitin kunnenta yana matseta ajikinshi ta yanda bazata iya fitaba murya chan kasa yace “I’m glad kinyi admitting defeat Kulu Khaleel never loose a fight! Mace bazata taba winning dina ba!” Zatai motsi yariketa gam ahankali yace “I will never divorce you Kulu! This Khaleel you hate so much saikinyi rayuwa dashi har abada!” Yadanyi dariya kadan mai sound yace “maybe da baki tsaneni ba danai letting naki go” awani irin hankali yace “and I will sex you just like yanda nakeyi da all the rest of those girl creatures, I will add you to the collection of women I slept with!” Yanda Hawwa ke fizge fizge kaman zata tashi amman yahanata fita daga jikinshi, yakara kai bakinshi wajen kunnenta yace “kinata neman evidence akaina bayan nine keda evidence akanki” yayi wani makirin murmushi yace “imagine Baba yaga video or pictures of when you were trying to rape me kina shamin baki, grabbing my shirt just like yanda kikayi dazun nan, trying to reap off my shirt and strip me naked, how will Baba feel?” Fizgo kanta Hawwa tayi daga jikinshi ta sauka gefe takalleshi da jajayen idanunshi tace “wat are you talking about? Ko zanyi raping maza aduniya trust me i will never go for national cake irinka da karabama all matan garin nan jikinka!” Shiru Khaleel yayi yana kallonta babu macen data taba gwada kalan zagin da Hawwa kemai, she just called him national cake, dan ijiyan zuciya ya sauke, wayanta dake inda