Showing 33001 words to 36000 words out of 75226 words
Allah kyale ni sauri na ke na koma gida "
Da sauri Nesrine ta bi bayan ta , ta dafa kafadar ta
Cak Inaya ta tsaya ta juyo ta na kallon ta
" Inaya ki na son ki ce min ba........." kut maganar ta yanke sakamakon wata mota da ta tunkaro su da gudu
Sarai Nesrine ta gane waye ke cikin motar , har sai da gaban ta ya fadi ta na zaro idanu
Kallon ta Inaya ta yi sannan ta juya ta kali motar da ta nufo su da mugun gudu
Dan rumtse idanun ta tayi sannan ta bude a kan motar dai'dai lokacin da ta ke jan wani wawan burki har sai da kura ta tashi
Motar na tsayawa Hafiz da Moctar su ka fito da ga cikin motar
Inaya na ganin Moctar ta saki tsaki ta kauda kai gefe , ta juya za ta bar wajen
Da sauri ya sha gaban ta ya na fadin " ina kuma za ki je ki gaisawa ba mu yi ba"
Hararrar shi ta yi da ga sama har kassa ta ce " ka ga malam ka bani lafya na fada maka ni matar aure ce "
Dariya ya yi kafin ya ce " yo ai ni ma mijin aure ne "
Tsaki ta ja ta raba ta geffen shi za ta wuce
Da sauri ya riko hannun ta ya na fadin " ki tsaya ki ji mana ! "
Cikin zafin nama Inaya ta juyo ta wanka mishi wani gigitacen mari ji ka ke tassss
Sai da Nesrine da Hafiz su ka zaro idanu su na kallon
Moctar kuma a dubu dari ya dago kai ya na kallon ta , idanun shi duk sun sauya sun koma ja sai rawar jiki ya ke murya na kerma ya ce " ni ki ka mara ? "
Cikin ko in kula ta hararre shi ta ce " eh na mare ka me kuma za ka yi sakare kawai "
Ta na gama rufe bakin ta, ta ga ya daga hannu shi saman zai mare ta
Da sauri ta rumtse idanun ta ta sa hannayan ta biyu ta toshe bakin ta na jiran saukar marin
Amma dai ba ta ji saukar marin ba , a hankali ta janye hannayan ta , ta bude idanun ta slowly sannan ta dago kai
Dum ta ji gaban ta ya fadi ganin Zayd tsaye ya na rike da hannun Moctar sai kallon juna su ke cikin ido
Murya na kerma ta bude baki ta ce " yaya Zayd "
Ba tare da ya juyo ya kaleta ba ya ce " wuce ku tafi gida "
Da sauri ta juya har ta yi taku daya ta tsaya cak ta na zaro idanu ta bude baki ta na tantamar abun da ta ji yanzu
Shi kuma Zayd ya na fada mata hakan ya saki hannun Moctar ya ce mishi " kar na sake ganin ka kusa da ita if not "
Kallon shi sama da kassa Moctar ya yi kafin ya juya ya ce ma Hafiz su ta fi cikin zuciyar shi kuma ya dauki alwashin sai ya rama abun da Inaya ta yi mishi ba za ta mare shi ta ci bilis ba
Da wannan tunanin su ka shiga cikin motar su su ka bar wajen
Su na barin wajen Zayd ya fara takawa ya yi gaba ya kali Nesrine ya ce me ku ke jira wuce ku tafi
Jinjina mishi kai tayi kafin ta karaso wajen da Inaya ke tsaye ta riko hannun ta ta ce su tafi
Ta na rufe bakin ta ta na ga Inaya ta sulale ta Zube a kassa
Da karfi ta saki kara ta na kiran sunan ta
Da sauri Zayd ya juyo ya kale ta, ta na konce a kassa sumamiya
Da sauri ya dawo inda ta ke ya tsuguna sannan ya sa hannayan shi duka biyu ya dauke ta cak kamar baby sannan ya tashi ya juya ya fara takawa Nesrine na biye da bayan shi su ka bar wajen
A haka su ka ci gaba da tafiya har su ka karaso bakin kofar gidan su Inaya sannan ya ce ma Nesrine " wu ce ki shiga gida sannan kar ki fadawa kowa abun da ya faru , idan yamma ta yi za ki iya zuwa ki gan ta "
Ya na gama fadar haka ko amsar ta bai jira ba ya wucewar shi
Ita kuma ta shige gidan ta na sallama
Yayi tafiya kadan sannan ya iso gidan shi
Da sallama bakin shi ya shigo cikin falon gidan
A hankali Moussa ya dago kai ya na amsa mishi sallamar
Da sauri ya mike tsaye ya nufe shi ya na fadin " Amir me kuma ya same ta "
Bai amsa mishi ba ya wuce ya kontar da ita saman doguwar sofa sannan ya ajiye bag din ta saman table
Ya kali Moussa ya ce " ba komai ina ga yar firgita ne ta yi " ya kai karshen ya na zama saman sofa
Komawa Moussa ya yi ya zauna geffen shi ya na fadin " firgita kuma garin yaya "
Kallon shi Zayd ya yi kafin ya ce " na ga kai kace min na yi mata magana to shi ne nayi "
Bushewa da dariya Moussa ya yi kafin ya kai hannu ya bugi damtsen Zayd ya na fadin " kai amma Allah Amir ka cika dan duniya , dan na ce ka yi mata magana ai da sai ka bari ta dawo gida mana "
Hararrar shi Zayd ya yi ya na shirin magana ya ga Inaya ta fara murkuso ta na neman tashi
Kallon Moussa ya yi kafin ya ce " toh ai gashi nan ka tayar da ita " ya kai karshen ya na dan siririn tsaki ya tashi ya nufi corridor ya koma bedroom din shi
Ya na barin wajen Inaya ta bude idanun ta a hankali ta na karanto kalmar shahada
Sai da Moussa ya ji ta ida karanto kalmar shahada sannan ya ce " babyn Zayd , ya har kin tashi na dauka doguwar suma ki ka yi " ya kai karshen ya na yar karamar dariya
A dubu dari ta mike zaune ta na zaro idanu ta kaleshi ta ce " yaya Moussa , amma abun da na ji ba gaskia ne ba ko ? "
Daga mata gera ya yi kafin ya ce " wane abu kuma baby ? "
Cike da tantama ta ce " yaya Zayd na ji wai ya yi min magana "
Dan karamin murmushi Moussa ya yi kafin ya ce " to minene a ciki dan ya yi miki magana ko ba ki son ya na yi miki magana ne ? "
" yaya Moussa ce maka fa na yi yaya Zayd ya yi min magana "
" eh na ji abun da ki ka fada "
" kuma shi ne ba za ka damu a kai ba yaya Zayd fa kurma ne ba ya magana ace lokaci guda ya yi magana babu shiri "
Yar dariya Moussa ya yi kafin ya mike tsaye ya kale ta ya ce " shi ya kamata ki yi ma wannan maganar ba ni ba "
Ya na gama fadar haka ya fara takawa ya nufi corridor ya shiga bedroom din shi
Nan ya bar Inaya sai faman muzurai da ido
Ta na zaune a haka Zayd ya fito da ga cikin corridor din ya na sanye da jallabiya dark blue mai dogayen hannu ya na sanye da bakin glass din shi
Tun da ya fito corridor din ta zuba mishi ido har sai da ya kai bakin kofar fita falon sannan ta ce " yaya Zayd "
Cak ya tsaya shi bai juyo ba shi bai yi tafiyar shi ba
Shiru ta yi ta zuba mishi ido ta na son mishi magana amma harshen ta ya yi mata nauyi ta kassa
Shi kuma jin yadda ta yi shiru ta tsaida shi ba tare da ya juyo ba ya ce " zan je massalaci idan na dawo ma yi magana " ya kai karshen ya na ficewar shi dan ya san maganar da ta ke son yi mishi kennan
Ta na kallon shi baki sake har ya fita sannan ta koma ta zauna saman sofar ta na zaro idanu ta rassa me za ta yi dan ta na neman ta zauce
A haka Moussa ya fito ya same ta shi ma sanye de jallabiya fara , bai bi ta kanta ba ya wucewar shi ya bar gidan
Da kallo ta raka shi har ya fita sannan ta sauke ajiyar zuciya ta mike ta shiga corridor ta nufi bedroom din Zayd
Kai tsaye toilet ta nufa ta yi wanka ta daura Alwalla sannan ta fito ta shirya cikin doguwar riga mara nauyi sannan ta gabatar da sallar ta
Bayan ta Kamala ta shiga gyaren gidan har da bedroom din Moussa ta gyara sannan ta nufi kitchen ta shirya musu abinci
Misalin karfe 5 na yamma
Ta na zaune cikin falon gidan ta kurawa Tv ido amma a zahirin gaskia hankalin ta ba a kan Tv ba ya ke ta fada duniyar tunanin ta
Ta na a haka Zayd da Moussa su ka shigo falon su na sallama amma ta Zayd cen kassan makoshi ya ke yin ta, ta Moussa kadai ta fito fili
A tare su ka karaso cikin falon su ka zauna saman sofar da ta ke fuskantar ta ta
Kare mata kallo Zayd ya yi ya na son ya karanci wani abu saman face din ta
Duk sun yi nisa cikin tunanin su , su ka tsinci Muryar Moussa ya na fadin " baby me kuma ki ke kallo haka ko sallama ba ki amsa mana ba ? "
Ko motsi ba ta yi ba, ta kura wa Tv ido
A hankali Zayd ya mike tsaye ya karaso sofar da ta ke zaune , ya zauna geffen ta ya kai hannu a hankali ya kyasta mata yatsun shi biyu saitin face din ta
A razane ta dawo cikin hayacin ta , ta na sauke ajiyar da karfi
Slowly ta dawo da kallon ta gare shi
Daga mata gera guda ya yi allamun minene ?
Wasu yawu ta hadiye cike da tsoro ta ce " yaya Zayd ka na iya gani na ? "
Jinjina mata kai ya yi ba tare da ya ce komai ba
" kuma ka na iya magana ? " ta sake tambayar shi
Jinjina mata kai yanzu ma ya yi ya na tsare ta da idanu shi
Lumshe idanun ta tayi a hankali ta sake bude su a kan shi cikin zuciyar ta ta na fadin " kenan yaya Zayd mayaudari ne , duk abun da muka sani kan shi ba gaskia ba ne ? "
TIR KASHI AIKI SABO, YANZU YA INAYA ZA TA YI JIN ZAYD BA MAKAHO BA NE BA KUMA KURMA BA NE ZA TA CI GABA DA SON SHI ? HMM SAI DAI GOBE IN MUN HADE ZA KU JI AMSAR
❤⚘ EXILED PRINCE ⚘❤
(LOVE MEETS POWER ) 👑🔥
( A heart touching love story , Romance , injustice & destiny )
STORY & WRITTEN BY : ANISH
Marubuciyar littafin
TAURIN ZUCIYA 💖💍🌺
https://whatsapp.com/channel/0029VaGhJCqKmCPUvpvIJ80i
♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡
PAGE 15 ❤🔥
Ta yi nisa cikin tunanin ta ta tsinci wannan zazzakar Muryar ta shi ya na fadin " ni ba mayaudari ba ne kamar yadda ki ke tunani "
Da sauri ta kaleshi kennan ya san abun da ta ke tunani ? Ta tambayi kanta
Ta na tsaka da wannan tunanin ta ga ya sa hannu a hankali ya zare bakin glass din shi ya zuba mata wadanan Hazel eyes din shi
Da sauri ta dafe saitin zuciyar ta , ta datse idanun ta da karfi dan ba karamar tsorata ta yi ba
A hankali ya juyo ya kali Moussa da ya zuba musu ido tun dazu ya na murmushi
Ya na ganin kallon Zayd ke yi mishi ya sa ya mike tsaye ya koma bedroom din shi ya basu wuri dan ya san haka kallon Zayd ke nufi
Ya na barin wajen ya dawo da kallon shi kan Inaya , slowly ya ce da ita " kin tsora ta ne ? "
Jinjina mishi kai ta yi ba tare da ta bude idanu ba
Jinkirtawa ya yi kafin ya ce " open your eyes ba abun da zai faru "
Girgiza mishi kai tayi cikin murya kamar za ta yi kuka ta ce " yaya Zayd bazan iya ba "
" bude idanun ki ina son muyi wata magana " ya fada mata cikin sanyi murya
Yanayin da ya yi mata maganar ya sanya ta sauke ajiyar zuciya , a hankali ta fara kokarin bude idanun ta
Karafff ko sai cikin nashi dan shi ma ita ya ke kallo
Sai gani ta yi ba karamin kyau ya kara yi mata ba , wadanan eyebrow sun fito ainahin su a cike sun konta luff kamar shi ya zana su , da wasu zarazaren eyelashes din shi sun kara kayata fuskar ta shi , da ya cire glass din shi sai ta face din kamar ba tashi ba
Duk sai ta ji ta tsargu sa kallon shi ta kassa janye idanun ta da ga cikin nashi
Su na a haka ta jiyo wannan zazzakar Muryar ta shi cikin nitsuwa ya ce mata " nassan za ki tambayi kan ki dalilin mi na meda kai na makaho da kurma , nassan cikin zuciyar ki ki na min kallon mayaudari , amma zan so ki san ba haka ba ne "
Dan lumshe idanu ta yi kafin ta bude su a hankali ta sunkuyar da kai ta riko hannun ta kafin ta ce " ban san dalilin ka na yi haka ba yaya Zayd , a ce duk wannan shekarun da muka dauka tare ko kalma daya ba ka taba fada ba a gaba na , ni ba ma wannan ba yaya Zayd ina son in san wanene kai " ,
Sunkuyar da kai kassa shi ma ya yi ya riko hannayan shi biyu kafin ya fara magana kamar haka " ba zan iya fada miki ko ni wanene a yanzu ba , kawai ki yi min kallon Zayd dan haka na ke , babu abun da zai sauya ko na fada miki , ni a sani na tun lokacin da na shigo garin nan ban taba ce ma wani ni kurma ne ko makaho akasi ma ni haka na ke magana nauyi ta ke yi min ko yanzu ji na ke kamar harshe na zai fado kassa , lokacin da mu ka zo garin nan ba na jin haoussa duk yadda zan yi magana mutane ba su ganewa haka ya sa na dinga yin shiru kawai , a dalilin mourir da shi ma da kyair ya koyi haoussar ya koya min , ni fa har yanzu ba wata cikakiyar haoussa na iya fa "
Bai karasa maganar shi ba sakamakon yar dariyar da Inaya ta yi ta na fadin " yadda ka ke wannan maganar kuma ka ce ba ka iya haoussa , wanda bai sanka va zai ce a bakin ka a ka yi haoussar "
Wani dan karamin murmushi geffen fuska ya yi ba tare da ya dago kai ba ya ce " nassan abu mai wuya ne ki yarda da hakan amma bazan ga laifin ki ba , har yanzu ke yarinya ce , ko na fada miki wasu abubuwa baza ki fahimta ba , amma zan so ki sani , ni ba mayaudari ba ne banzo nan da niyar cutar wa ba , ban aure ki ba da niyar cuta , akasi ma ba a son raina ba a ka yi wannan auren kuma ban san manufar wannan auren ba , bazan iya sakinki ba , kuma bazan iya daukar ki a matsayin matata ba , kin yi min kannanta gaskia , amma zan rike ki a matsayin sister di ta , kema zan so ki dauke ni a matsayin brother din ki , duk wani abu da za ki bukata ki fada min , kar ki ji kunyar yi min wata magana , idan har kuma Allah ya saka miki soyayyar wani a cikin zuciyar ki zan so ki fada min da kai na zan aura miki shi a matsayi na na brother din ki "
Ya kai karshen ya na dago kai ya kale ta
Ita ma dago kai ta yi ta na murmushi ta kaleshi ta ce " shikenan yaya Zayd ni ma zan dauke ka a matsayin brother di na duk da dama a hakan na dauke ka "
Jinjina mata kai ya yi kafin ya ce " shikenan sister yanzu kin ga lokacin sallat ya yi sai ki tashi ki tafi ko , nan da next week ina son mu sauya gida dan ina ga fa wannan ya fara yi mana kananta "
Yar karamar dariya ta yi har sai da fararen hakoran ta su ka bayana sannan ta ce " shikenan yaya Zayd , kai ma ka tashi ku tafi massalaci idan kun dawo mu ci abinci a tare yau "
" okay ba matsala " ya fada mata a takaice
Murmushi ta yi kafin ta mike ta nufi corridor ta shiga bedroom din shi
Ta na shiga Moussa ya fito ya ce ma Zayd su tafi
Ba musu ya tashi ya bi bayan shi su ka tafi mosque
After one week
A takaice haka rayuwa ta ci gaba da tafiya a cikin wannan gidan ,