Showing 39001 words to 42000 words out of 75226 words

Chapter 14 - Exiled Princess Book 1 Hausa Novel Complete

Meerah   

13 Dec 2024

298

na kallon su cike da mamaki ya ce " Amir wanene wannan kuma "

Bai bashi amsar tambayar shi ya wuce zai bar falon

Da sauri Moussa ya kauce ya bashi hanya ya na sakin trolley din hannun shi ya bi bayan su da sauri


Shi kuma Zayd ya na fitowa ya nufi parking space ,

Wani corridor ya bi ya koma bayan gidan wajen wata katuwar kofa ta mota ,
Sai da ya ka bakin kofar sannan ya janye hannun shi da ke saman bakin Moctar ya juyo da shi su na fuskantar juna

Ido cikin ido ya kaleshi kafin ya ce " ka yi sa'a ba ka taba ta ba , zan kyale ka a haka amma duk ranar da na sake kanin ka ko da cikin inuwar ta ne sai na kashe ka "
Ya na gama fadar haka ya kai hannun shi ya bude kofar ya tila shi waje , ya fadi kassa kan shi ya bugu da wani dutse nan wajen ya fashe

Zayd kuma ya na tila shi ya rufe kofar ya juya zai bar wajen nan ya ga Moussa ya na tsaye ya zuba mishi ido

" wai Amir wanene wannan, mi ya ke a cikin gidan nan " Moussa ya tambaye shi

Takawa ya fara yi zai bar wajen , sa sauri Moussa ya bi bayan shi su ka bar wajen a tare

Sai da su ka shiga cikin falon gidan sannan ya zauna saman sofa ya jingina a bayan sofar ya daga kai ya lumshe idanun shi ya na sauke ajiyar zuciya


Geffen shi Moussa ya zo ya zauna ya na son ya ji abun da ke faruwa dan shi an bar shi cikin dufu


❤⚘ EXILED PRINCE ⚘❤
(LOVE MEETS POWER ) 👑🔥


( A heart touching love story , Romance , injustice & destiny )



STORY & WRITTEN BY : ANISH


Marubuciyar littafin
TAURIN ZUCIYA 💖💍🌺

https://whatsapp.com/channel/0029VaGhJCqKmCPUvpvIJ80i

♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡

PAGE 17 ❤🔥


Sai da su ka dauki lokaci a haka ba wanda ya ce ma wani ko uppan sannan Zayd ya sauko da kanshi ya bude idanun shi

Kallon Moussa ya yi kafin ya ce " ban san ko wanene yaron nan ba , amma ya kai sau uku ina ganin shi ya tare wannan yarinyar , a na karshen ta mare shi dan ya ruko hannun ta , zai ramawa na iso wajen na yi mishi kashedin kar na sake ganin shi kusa da ita, nassan ya ji haushi maganar dalilin da ya sa ya fara bibiyar ta ya ga a ina ta ke in kuma ita kadai ce , tun ranar da muka tafi ta koma gidan uncle sai yau ta dawo gidan nan , dan ya san ita kadai ce a nan shi ya sa ya yi anfani da hakan ya zo ya yi raping din ta "


Da sauri Moussa ya katse shi da cewa " what ? Rape fa ? "


Jinjina mishi kai Zayd ya yi kafin ya ce " tun safiya na ke jin gaba na na faduwa na rasa dalili , sai da na ce maka mu tafi tun lokacin da na yi maka magana amma ka shiga ce min sai ka Kamala aikin da ya kawo mu , in ba dan Allah ya sa mun iso da sauri kai ka san irin abun da zai mata "

Ya na gama fadar haka ya mike ya nufi corridor

Jim kadan ya fito rike da torch din Moctar da rigar shi da belt , ya ajiye su saman table sannan ya ce wa Moussa in ya tashi ya jefar da kayan da ga haka ya koma bedroom din shi ya bar Moussa nan zaune a falon


Ya na shiga bedroom din shi ya koma bakin gado geffen ta ya konta , ya daura hannun shi daya saman goshi dayan kuma saman cikin shi , ya lumshe idanun shi ya na tunanin da yanzu bai zo da wuri ba a wane irin hali zai tardo ta , sa yanzu Moctar ya cutar da ita da wane ido zai kali malam
Da irin wannan tunanin barci ya yi gaba da shi


Washe gari


Misalin karfe 6 na safe ta ware idanun ta a hankali ta na karanto adu'ar tashi da ga barci


Juyo kan da za ta yi ta gan shi konce a geffen ta sai da gaban ta ya fadi , cike da mamaki ta bude baki a hankali ta ce " yaya Zayd "


Ya na jin ta kiri sunnan shi ya bude idanun shi slowly ya na kallon ceiling kafin ya dawo da kallon shi kan ta


Dan murmushi tayi kafin ta ce " yaya Zayd ba sai gobe za ku dawo ba , shi ne za ka yi min irin wannan bazatar, ni na dauka aljani ne ma "


Kallon ta ya ke cikin ido babu ko kiftawa ya ki ba ta amsa

Ganin kallon nashi ya fara takura mata ya sa ta yi sauri ta yi kokarin mikewa za ta bar wajen


Da sauri ya riko hannun ta ya janyo ta da karfi ta koma ta konta ya na fadin " ina za ki je ne yau fa week-end , konta ki huta "

Kallon shi ta yi ta na murmushi kafin ta ce " amma yaya Zayd zan je ne f......"

Da sauri ya dora yatsar shi saman lips din ta ya katse ta da cewa " shiiiiiiiiii ki konta na ce , ko kema yanzu Nesrine ta koya miki kin jin magana ? "


Da sauri ta girgiza mishi kai ta na son ta ce mishi sallat ta ke son ta je ta yi dan yau ba ta samu ta tashi da asuba ba amma ya hana ta magana


Daga mata gera guda ya yi ganin yadda ta kura mishi ido ya ce " why ki na kallo na haka , ko za ki dake ni "


Da sauri ta girgiza mishi kai ta na murmushi

Slowly ya janye yatsar shi da ga saman lips din ta

Kamar jira ta ke dama, ya na janye yatsar shi ta bude baki za ta yi magana
Da sauri ya meda yatsar shi ya na fadin " no shiru za ki yi yau baza ki cika ni da surutu ba , bakin dan guntu amma sai bala'i surutu kamar parrot "


Matse girar ta ta yi ta turo dan bakin nan nata ta fara gunguni kassa kassa wai ita ta ji haushin ya ce ta na da surutu


" oh babyn malam duka na za ki yi , shikenan zan janye yatsa ta amma kar ki yi magana kin ji ko ? "


Da sauri ta girgiza mishi kai allamun to

A hankali ya janye yatsar shi ya zuba mata idanu

Sai da ta dauki lokaci dan ta shan'mace shi sannan ta ce " ni ba di surutu kamar parrot " ta kai karshen ta na murguna mishi baki

Dan zaro idanu yayi ya na kallon kafin ya ce " ke wa ki ke ma wannan abun "

Hararrar shi ta yi kafin ta ce " kai na ke ma , ni yaya Zayd ka kyale ni mun ma bata "

" da wani shiri mu ke bare ki ce mun bata , amma shikenan tun da haka ne bara na tashi na koma inda na fito " ya kai karshen ya na kokarin mike wa zaune

Ya na shirin sauko da kafafun shi kassa ya ji an buga mishi pillow a baya
Da sauri ya juya ya na kallon ta

Ta na zaune saman guyiwowin ta na rike da pillow sai hura kumatu da iska ta ke


Ta na ganin ya juyo ta kara kai mishi wani bugun da pillow a fuska ta ce " wlh yaya Zayd ba bu inda za ka koma , sai dai mu tafi tare "


Ta na rufe baki ya ce " ke lafiyar ki za ki buge ni ? "

Bai gama rufe baki ba ta kai mishi wani bugun a fuska ta ce " e na buga , kuma na kara " ta kai karshen ta na kara kai mishi wani bugun

Ta na shirin yi mishi na biyar ya damko pillow ya ce " kin yi na ki saura nawa "

Dan zaro idanu ta yi ta na jan pillow din da karfi amma ina da hannu daya ya damko shi amma ta kassa kwace shi

" yaya Zayd ka sake min pillow na " ta fada kamar za ta yi kuka

Da karfi ya janyo pillow tare da ita ta fado saman fafadar kirjin shi , ya na kallon ta cikin ido ya ce " sai bala'in jan fada amma ba karfi "

Kallon shi ta ke ita ma cikin ido sai ta ji ba za ta iya janye idanun ta daga cikin nashi ba


Sun dauki lokaci su na kallon juna cikin ido ba wanda ya iya cewa wani abu
Cen kuma Inaya ta ce dashi " yaya Zayd , ka taba kamuwa da soyayyar wata a cikin zuciyar ka "


Ya na kallon ta cikin ido sai da ya dauki lokaci kafin ya koma slowly ya konta da ita a saman kirjin shi , a hankali ya kai hannu ya janye jelar gashin da ta zuba mata a geffen fuska ya ci gaba da kallon ta cikin ido


Sai ya da ya jima a haka kafin ya ce " never ! Ko so guda ban taba jin ina son wata mace a cikin zuciya ta bayan Ammie na da kuma sister di ta sai kaka ta, su kade matan da na ji ina son su har cikin zuciya ta , bayan haka ban taba jin ina son wata mace ba , assali ma ni ko kallon mace ba na yi , ko magana idan mace ta yi min kyale ta na ke , idan har ba da maganar aiki ta zo min ba ko kuma an aiko ta ta kamin sako "

Cikin zuciyar shi kuma ya ce " amma ban dalilin da ya sa ko wane lokaci na ke da bukatar ganin ki ba , ban san dalilin da ya sa kullum ni ke son na yi miki magana , ban san dalilin da ya sa ko wane lokaci na ke jin zuciya ta na bukatar ki kusa da ita "

NI KUMA NA CE HUMMM TUKUNNA MA BA KA GA KOMAI BA 😝😂😂


Ya yi nisa cikin tunanin shi ya tsinci Muryar ta ta na fadin " yanzu yaya Zayd ka na da sister amma ba ta taba zuwa nan ba, ko dai kai ka ke tafiya ka gan ta "

Girgiza mata kai ya yi kafin ya ce " no ba ta zuwa ni ma ba na zuwa assali ma a tunanin su na mutu , shi ya sa na kyale su amma kullum su na cikin raina duk lokacin da na yi sallat sai na saka su a cikin adu'a , ko ina son in je wajen su bazan iya ba , ba dan rashin kudi ba, sai dan abun da zan je na tayar , ba na bukatar shi a rayuwa ta amma ya zaman min dole, shi ya sa na ci gaba da zama na a nan gashi kuma Allah ya bani wata familyn daban "

" yaya Zayd minene wannan abun da ba ka son ka tayar da shi da zai sa ka rabu da duk familyn ka , har su ringa tunanin ka mutu , kennan guduwa ka yi ? " ta kai karshen ta na zaro idanu


Dan karamin murmushi geffen fuska ya yi kafin ya kai hannu shi saman face din ta ya ce " e guduwa na yi dan an nemi a kashe ni , amma ba su yi nassara ba , na san duk lokacin da na koma sai sun ida cika aikin su , shi ya sa na bar musu kayan su har lokacin da kaddara za ta meda ni amma ba ni fatan komawa na fi jin dadin zama a nan "


A hankali ta kontar da kan saman kirjin shi kamar ta yi kuka ta ce " ban san abun da ya sa dan Adam ke yawwan son abun duniya , har ya kai ga kashe yan uwan shi saboda wani abun da a nan duniya zai bar shi , abun ba zai anfane shi da komai ba a ranar gobe kiyama sai ma ya jefa shi a halaka , ban san dalilin abun da ya sa su ke neman kashe ka ba yaya Zayd amma na san ko sun mallaki wannan abu ba za su rike shi tsakani da Allah , in har za su iya kashe mutun saboda shi "


Hannun shi ya kai a saman bayan ta ya na shafawa a hankali sannan ya ce " ikon Allah ne kawai ya cece ni a ranar nan , kuma na gode mishi da ya kawo ni a cikin wannan garin , ko so guda ban taba yin nadamar guduwar da na yi , amma har ga Allah ina kewar family na amma ba zan iya komawa ba "


Dago kan ta tayi ta na kallon face din shi ta ce " yaya Zayd don Allah ina son in san wanene kai , da ga ina ka ke , minene wannan abun da ya sa a le neman kashe ka har ka gudu ka bar familyn ka, don Allah yaya Zayd fada min "


Girgiza mata kai ya yi kafin ya ce " ba zan iya ba gaskia , labari na me tsawo ne , ban shirya ba ki shi yanzu ba amma wata rana zan fada miki , wata rana za ki san wanene ainahin ....."
kut maganar ta yanke sakamakon wani abu da ya tuno


Kallon ta ya yi cikin ido kafin ya ce " kafin ku dawo kano da zama za ki iya tuna wane gari ku ka baro ? "


Daga kan ta sama ta yi kamar mai tunanin wani abu kafin ta medo shi ta na kallon shi ta girgiza mishi kai tace " gaskia bazan iya tunawa ba , ni dai a sani na a nan kano na tasso "

" ni fa za ki iya sannin da ga ina na gudo na zo Nigeria ? " ya tambayeta zuciyar cike da tsoro kar abun da ya ke tunani ya zama gaskia


Dariya ta yi kafin ta ce " yaya Zayd ta ya zan iya sani bayan ka ki fada min "

Hannu ya kai ya ja kumatun ta ya ce " na ji yanzu tashi ki je ki yi wanka ki shirya , sau je mu yi breakfast "

Da to ta amsa mishi kafin ta yi kokarin tashi da ga jikin shi , ta sauko da ga saman gadon da gudu ta shiga toilet


Ya na kallon ta har sai da ya ga ta shiga toilet ta rufo kofar , sannan ya mike ya nufi closet ya dauki kayan shi , wandon jeans brown da t-shirt fara , sannan ya fice dakin ya nufi bedroom din Moussa


❤⚘ EXILED PRINCE ⚘❤
(LOVE MEETS POWER ) 👑🔥


( A heart touching love story , Romance , injustice & destiny )



STORY & WRITTEN BY : ANISH


Marubuciyar littafin
TAURIN ZUCIYA 💖💍🌺

https://whatsapp.com/channel/0029VaGhJCqKmCPUvpvIJ80i

♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡

PAGE 18 ❤🔥


Tsaye gaban dressing mirror ya isko Moussa ya na fessa turare
Bai tsaya bin ta kan shi ba ya wuce toilet kai tsaye

Jim kadan ya fito sanye da kayan shi , ya karaso bakin gadon Moussa ya zauna a lokacin shi ma Moussa ya na zaune bakin gadon


Kare mishi kallon da kyau Moussa ya yi kafin ya ce " me ya ke damun ka , na ga ka sauya lokaci guda "


Shiru ya yi bai amsa mishi ba ko kallon shi ba baya yi ya fada duniyar tunanin shi

Hannun shi Moussa ya kai ya dafa kafadar Zayd kafin ya ce " Amir me ya ke faruwa ne ? "


Ajiyar zuciya ya sauke ba tare da ya dago kai ba ya ce " Diya wlh har yanzu zuciya ta zafi ta ke yi min , har yanzu ina jin zafin yadda ya so ya bata mata rayuwa , dama kashe shi na yi na huta da wannan zafin da na ke ji "


Wani iska mai zafi Moussa ya furza da ga bakin shi kafin ya ce " ni kai na ina jin zafin abun nan , dama da ita muka tafi ko ba komi ta debe mana kewa , yanzu da wani abu ya same ta wlh ba zan iya kallon malam ba cikin ido , amanar ta ya ba mu ka ga dole mu kula da ita , ba kowa ne cikin duniyar nan zai dauki d'iyar shi guda ya bawa mutuman da bai san assalin shi ba , ko ainahin sunan shi bai sani ba, amma a haka ya yarda da kai ya baka ita ya kamata mu kula da ita tamkar rayuwar mu "


Dan karamin hijab geffen fuska Zayd ya yi sannan ya ce " ta na yawwan tino min Amira Tesnim , wani bangaran cikin zuciya

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login