Showing 60001 words to 63000 words out of 75226 words
sa yaran unguwa da kuma nawa yaran , bayan Inaya ta cika shekara 10 Youssef ya tado zancen ya na son ya nemawa yaron shi auren ta a lokacin ta na karama sosai a waje na sai na ki yarda hakan ko ba karamin bata mishi rai ya yi ba , har ya dauki gaba ya bani , wata daya bayan faruwar hakan na je na bashi hakuri dan Allah ya sani da zuciya daya na ke tare da shi tun farko , ba musu ya yarda shi ma ya bani hakuri da cewar shi ne mai laifi ba ni ba , mu na zaune a wajen Inaya ta tardo mu da gudu su na wassa ita da Nesrine , ta na ganin Youssef nunfashin ta ya dauke lokaci guda , ta shiga yin kara kamar dai yanzun nan ta na fadin " Abba shi ne , shi ne ya kone maka shagon ka " cike da rudu na shiga rarrashin ta dan ni ban san abun da ta ke fada ba , ashe dalilin da ya sa Youssef ke son ya aurawa yaron shi Inaya , sun je wajen bokan su ne sai ya ke fada mishi abun da ingozomar nan ta taba fada mana , nan bokan ya ke ce mishi wai matata ita ce silar arziki na tsawan shekaru , kuma duk wanda ya auri Inaya duk kofofin arziki za su bude mishi, sannan ya gani cewa ta na da wasu aljanu na gado da ga wajen mahaifin mamar ta , wadanan aljanu ko shi bai san irin su , dole sai ya kawo mishi Inaya in har ya na son ya tantance wane irin aljinu ne gare ta , duk yadda Youssef zai yi don ya ga ya kai Inaya wajen bokan sai da ya yi amma da Inaya ta sauke idanu saman shi ta ke tserewa ta buya , har ya kai abun ya fara bawa Youssef haushi , ya fara yi mana barazana a kan dole sai na aurawa yaron shi Inaya in ba haka ba ya kashe mu ba ki daya , a lokacin na yi matukar girgiza don na san halin shi ba karamin mugu ba ne in har ya yi niya , cike da tsoro na tatara iyali na cikin tsohon dare mu ka bar gidan , mu ka bar kaduna baki daya mu ka taho kano inda ba mu san kowa ba , a ranar da na roke ka, ka auri Inaya , ranar ina zaune na ga issa ya wuce , cike da mamaki na tsayar da shi na ke tambayar shi ya mutanan gida me ya kawo shi kano kuma , nan take kuka ya kubce mishi lokacin da ya ke sanar da ni cewa bayan tafiyar mu Youssef ya tarda shi ya yi mishi barazana a kan ya fada mishi inda muke sai dai shi kuma bai sani ba , har ya sace mishi yarinyar shi babba ya bawa bokan su ita , dalilin haka ya tsere shi ma ya tafi kwayan su , ya ce min a yanzu haka Youssef ya zama vice-president na Nigeria kuma har yanzu ya na neman mu , jin hakan ba karamar girgiza na yi ba har na baro issa nan tsaye na tafi gida dan na ce musu su shirya yanzu ma mu bar Garin , kawai sai na gan ka , lokaci guda wani tunani ya fado min , idan na aura maka Inaya , ba sai na bar garin ba tun da yanzu aure tsakanin ta da yaron Youssef ba zai yi yu ba , ni a lokacin ban duba nakassar ka ba kamai ina neman ceton ran yarinya ta ne "
Shiru Zayd ya yi kamar mai tunanin wani abu
Yayin da Moussa ya zuba mishi ido ya na kallon shi , ya na son ya karanta yanayin sa
Cen kuma sai ya dago kai ya kali malam ya ce " uncle zan iya sannin sunnan yaron da ku ke magana a kan shi "
" e sunan shi Sudais " malam ya fada
❤⚘ EXILED PRINCE ⚘❤
(LOVE MEETS POWER ) 👑🔥
( A heart touching love story , Romance , injustice & destiny )
STORY & WRITTEN BY : ANISH
Marubuciyar littafin
TAURIN ZUCIYA 💖💍🌺
https://whatsapp.com/channel/0029VaGhJCqKmCPUvpvIJ80i
♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡
PAGE 24 ❤🔥
Mikewa tsaye Zayd ya yi ya shiga cikin bedroom din shi ya rufe kofar
Ya na shiga Moussa ya mike tsaye shi ma ya ce wa malam " uncle ni zan tafi "
Shi ma malam mikewa ya yi ya na fadin " mu je to , ni ma wajen Nesrine din na ke son zuwa "
Dan murmushi Moussa ya yi ya na sunkuyar da kai dan malam ya gano shi
A tare su ka jera su ka fito part din sannan su ka sauko falon kassa
Zayd
Tsaye ya ke bakin gadon shi ya zubawa Inaya da ke konce saman bed din shi ido , kamar mai barci
Dogon nunfashi ya ja kafin ya karaso bakin gadon ya zauna ya na ci gaba da kallon ta ya rasa dalilin shi na yin haka
Ya dauki wajen good 30 minutes a haka kafin ya ga ta fara motsi ta na son tashi
Bai motsa ba ya ci gaba da kallon ta , har ta bude idanun ta , ta na kallon ceiling ta kassa motsi
A hankali ya matso kussa da ita ya kai hannu saman kumatun ta ya ce " are you okay ? "
Kallon shi ta yi cikin ido ta ce " yaya Zayd me ya faru ne ? "
" nothing Mimi , ya jikin na ki ? " ya fada ya na taimaka mata ta zauna ta jingina a bayan gadon
Dan murmushi tayi kafin ta ce " yaya Zayd ni fa lafya lau na ke "
" kin tabbata ? " ya fada ya na daga mata gera guda
Murmushi mai dan sauti ta yi har sai da dimple din ta ya lotsa , sannan ta jinjina mishi kai allamun e
Geffen ta ya dawo shi ma ya zauna ya jingina a bayan gadon sannan ya kai hannu ya dauki remote ya kunna Tv din gaban su
Sannan ya kale ta ya ce " za ki kali cartoon ? "
Girgiza mishi kai ta yi kafin ta ce " yaya Zayd ni film na ke son kallo " ta fada cikin shagwaba
Jinjina mata kai ya yi , ya kali Tv din ya na neman chanel din da su ka saka film a yanzu
Cikin sa'a ko first chanel da ya saka , su na haska wani film na Avengers mai dadi
A tare su ka kali film din har sai da ya kamala dai'dai an fara kiran sallat
Ta na jin kiran sallat ta diro da ga saman gadon ta na shirin fita dakin
Da sauri ya riko hannun ta ya na fadin " where are you going ? "
Juyo wa ta yi ta kaleshi cikin shagwaba ta ce " yaya Zayd ba ka jin kiran sallat ne, zan je bedroom di na na yi sallat "
Ba tare da ya saki hannun ta ba ya ce " ba za ki yi ta ba a nan "
Noke mishi kafada ta yi ta na shagwabe fuska ta ce " yaya Zayd ai nan dakin ka ne "
Da sauri ya katse ta da cewa " bedroom din mu ne , ni da ke , in bai miki ba na sauya ? "
" to yaya Zayd dakin da na ke ciki kuma fa ? "
" zan sa a medo kayan ki nan , in kuma wannan part bai miki ba sai a sauya shi "
" yaya Zayd na ga duka dakunan gidan akwai mutane a ciki "
Mikewa tsaye ya yi ya tsaya gaban ba tare da ya saki hannun ta ba ya ce " akwai wasu part bayan wadanan , amma na sirri ne , yanzu shiga toilet ki yi Alwalla ki yi sallat ina zuwa " ya kai karshen ya na sakin hannun ta
Da to ta amsa mishi kafin ta fara takawa a hankali ta shiga toilet
Da kallo ya rakata har sai da ta shiga sannan ya juya ya ficewar shi
After some minutes ta fito da ga cikin toilet din
Abun mamaki ta na fitowa ta ga duk trolley din ta jere bakin gadon
Murmushi ta saki kafin ta tako ta karaso gaban trolley din ta bude guda , ta cire karamin hijabin ta ta saka a cikin ta dauki wani dogo har kassa ta saka , sannan ta nufi dan carpet din gaban gadon ta gabatar da sallar ta dan ba ta ga dadduma ba
Ta na tsaka da sallar ta ya shigo dakin ya na sallama kassa kassa kamar ba ya son bude baki
Ya na shigowa idanun shi su ka sauka saman trolley din ta
Bai tsaya bata lokaci ba ya dauke su ya shiga dressing room ya shiga gyara mata kayan ta cikin closet
Sai da ya Kamala sannan ya fito dressing room din , har yanzu ta na nan zaune ta daga hannayan ta sama ta na karanto aduo'i
Bakin gadon ya zauna ya zuba mata idanu ya na kallon , gwanin burgewa
( na so Moussa na wajen ya yi musu pic ko da biyu ne 😭😭😭 )
Sai da su ka dauki wajen good ten minutes a haka kafin ta shafa adu'ar ta , sannan ta tasso ta tsaya gaban shi , ta shiga karanto mishi aduo'i cikin ranta sannan ta tofa mishi
Dan lumshe idanun shi kadan ya yi , abun da ta yi ba karamin dadi ya yi mishi ba , har cikin zuciyar shi ya ji dadin adu'ar ta duk da bai san adu'ar micece ta karanto mishi ba , amma ya na da tambacin al'heri ne
Ya na a haka ya tsinci wannan zazzakar Muryar ta, ta na fadin " yaya Zayd yunwa na ke ji "
Slowly ya bude idanun shi ya na kallon ta , ta na tsaye gaban shi ta shagwabe fuska , ta rike hannayan ta a baya , sai hura kumatu ta ke
Mikewa tsaye ya yi ya mika mata hannu , dan murmushi mai sauti ta yi kafin ta daura hannun ta saman nashi
Ta na daurawa ya fara takawa ta yi gaba ya na rike da hannun ta , su ka bar part din baki daya
Bari dai mu dan leko Nesrine nassan kafin nan sun Kamala cin abincin su
Nesrine
Zaune ta ke tsakiyar gado na cikin bedroom din Inaya ta ke da farko
Ta daga kai sama , ta lumshe idanu sai ruwan hawaye ta ke yi , amma kukan ya ki fitowa
Ta na zaune a haka ta jiyo a na sallama , sa sauri ta dube idanun ta , ta saka hannayan ta biyu ta na goge hawayen ta
Ta shiga amsa sallamar ba tare da ta kali kofar ba
A hankali ya tako ya iso cikin dakin ya na kallon face din ta
Sai da ya kawo bakin gadon sannan ya tsaya ya ce " Nesi lafya ki ke kuka haka ? "
Da sauri ta juyo da kan ta , ta na kallon shi jin ya kira ta da Nesi ,
Dan karamin murmushi ya yi mata ya na daga mata gera guda allamun lafya
Da sauri ta kauda kai gefe ta rumtse idanun ta , nan take wasu hawayen su ka sake zubo mata
Da sauri ya ce " don Allah ki yi hakuri ki daina kukan nan Nesi "
Ba tare da ta bude idanun ta ba ta ce " don Allah yaya Moussa ka daina kira na da wannan sunnan " ta fada da dan karfi dan wannan sunnan da shi ne Hafiz ke kiran ta
Bakin gadon ya hau ya na fadin " please sister ki daina kukan nan to , wlh ba na jin dadin ganin ki haka "
Ajiyar zuciya ta sauke a hankali sannan ta bude idanun ta sai cikin nashi su ka yi ido hudu
Da sauri ta sunkuyar da kai ta ce " ina wuni yaya Moussa "
Murmushi yayi kafin ya ce " da ga baya kenan , yanzu dai fada min ya jikin ki , ki na da bukatar wani abu ? "
Dan murmushi kafin hali ta yi ta na girgiza mishi kai allamun ba komai
Gyara zaman shi ya yi saman gadon sannan ya ce " shikenan to , tun da ba ki bukatar wani abu na zo muyi hira "
Yanzu ma murmushi ta yi dan har ga Allah ta ji dadin hakan dama ta fara gajiya da zama ita kadai
" hira kuma yaya Moussa ? " ta fada kassa kassa
Gyada mata kai ya yi allamun e
Dan karamin murmushi ta yi , ta lumshe idanun ta wasu hawaye su ka sake zubo mata
Da sauri Moussa ya kai hannun shi zai goge mata hawayen , sai dai bai kai ga taba ta ba ya janye hannun shi da sauri dan ya San idan ya taba ta yanzu za ta iya birkice mishi
Cikin sanyi murya ya ce " to shikenan in ba ki so sai in tafiya ta "
Slowly ta bude idanun ta , ta na kallon shi ta ce " why lokaci guda ka sauya bayan lokacin da mu ke gida ko magana ba ta shiga tsakanin mu , akasi ma ko ka yi min magana sai dai na yi maka kallon wulakanci "
❤⚘ EXILED PRINCE ⚘❤
(LOVE MEETS POWER ) 👑🔥
( A heart touching love story , Romance , injustice & destiny )
STORY & WRITTEN BY : ANISH
Marubuciyar littafin
TAURIN ZUCIYA 💖💍🌺
https://whatsapp.com/channel/0029VaGhJCqKmCPUvpvIJ80i
♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡
PAGE 25 ❤🔥
Dan karamin murmushi ya yi kafin ya gyara zaman shi ya koma geffen ta , ya jingina a bayan gadon shi ma
Sannan ya ce " kin ga ko ni fa ba mutun ne ba mai rike abu a zuciya , kin san fa ni tsiwar ta ki burge ni ta ke , shi ya sa na zo nan dan ki yi min dan tsiwar nan ta ki , kwana biyu na yi kewar ta " ya kai karshen ya na kashe mata ido guda
Dan murmushi mai sauti ta yi kafin ta ce " i'm sorry , duk wani abu da na yi maka ka yi hakuri ka yahe min "
Da sauri ya katse ta da cewa " kin ga sister, ki daina ba ni hakuri ni fa ba ki yi min komai ba , don Allah ki bar tuno min baya , ni fa hira na zo muyi "
Sunkuyar da kai ta yi ta na fadin " hirar mi kuma za ka yi ni , da dai ka tafi ka kira budurwar ka , ku yi hirar ku ba de da ni ba "
" why ? Ko hira da ni ne ba ki so.? "
Dago kai ta yi ta kaleshi ta na girgiza kai kafin ta ce " ba haka ba ne yaya Moussa k....."
Da sauri ya katse ta da cewa " to minene ? "
Sunkuyar da kai ta yi kassa kassa ta ce " ga ni kawai na yi ban dace da hakan ba "
Dan matsowa ya yi kusa da ita , ya kali gaban shi ya ce " ni a waje na kin ma wuce hakan , na san saboda abun wacen saurayin ne ya yi miki ki ke fadin hakan , amma ina so ki san ba laifin ki ba ne , please kar ki rike wannan abun a ranki everything will be okay in sha Allah "
Ya na gama fadar hakan ya ji kuka ya kubce mata , cikin kukan ta ce " a'a yaya Moussa , yanzu ya ka ke so na yi , yanzu wane namiji ne zai yarda ya aure ni bayan na rasa abun da ya fi komai daraja a rayuwa ta "
Kallon ta ya ke yi babu ko kiftawa , sai kuka ta ke yi har da hadiyar zuciya
Da sauri ya rungume ta ya na dan bubuga bayan ta ya ce " ya isa haka don Allah ki daina kukan nan , na fada miki ki daina ganin laifin ki , na yi miki alkawari wanda zai aure ki , tsakanin shi da Allah zai aure ki babu ruwan shi da abun da ya faru da ke , ki yarda da ni tsakanin shi da Allah zai so ki "
Ajiyar zuciya ta sauke ta na rage sautin kukan ta
Ba tare da ta dago kai ba ta ce " babu shi yaya Moussa , na san ka na fada min haka ne kawai dan na yi shiru , amma ni na san ba zan taba samun wanda zai so ni tsakanin shi da Allah ba "
Hannayan shi ya kai saman kafadun ta , ya dago ta ya na kallon face din ta ya ce " ki daina cewa haka mana , ba ga ni ba "
Tsit ta tsaya da kukan nata ta dago kai ta na kallon shi cikin ido , duk sai ta nemi kukan ta ta rasa kawai sai kallon shi ta ke yi cikin ido
Ganin ta yi shiru ya sa shi