Showing 42001 words to 45000 words out of 75226 words

Chapter 15 - Exiled Princess Book 1 Hausa Novel Complete

Meerah   

13 Dec 2024

302

ta, ta na debe min kewar ta "


Murmushi Moussa ya yi shi ma kafin ya ce " Amir yaushe za mu koma ne wai , ina kewar ahalin mu gaskia "

" very soon in sha Allah , amma kafin nan , na yanke wata shawara "

" wece shawara kuma ? "

Jinkirtawa ya yi kafin ya ce " za mu koma gidan mu na Abuja da zama , da ga yau ta daina zuwa college , zan fara nema mata admition a wani private college daban a cen Abuja , zaman ta a nan ya na da hatsari zai iya dawowa yace ya rama abun da mu ka yi mishi a kan ta , ni kuma ba zan so hakan ba "


Mikewa tsaye Moussa ya yi , ya yi takura guda gaba sannan ya ce " hakan ma shawara ce mai kyau amma ka na gani malam zai yarda ? "


Mikewa tsaye shi ma Zayd ya yi , ya tako ya tsaya geffen Moussa ya ce " zai yarda , ba ni shakkun hakan "
Ya na gama fadar haka ya taka ya bar dakin


Ya na fitowa ya koma bedroom din shi kai tsaye , amma abun mamaki ba ta ciki

A tunanin shi har yanzu ta na cikin toilet sai ya koma bakin gado ya zauna ya ciro wayar shi da ga cikin aljihun shi ya fara latsawa ,

Sannu sannu har ya share wajen good 30 minutes babu ita babu mai kama da ita

A hankali ya mike tsaye ya meda wayar shi cikin aljihu sannan ya nufi toilet

Bakin kofar ya tsaya ya kai hannu ya bubuga ya na fadin " wai har yanzu ba ki gama wankan ba ne "


Shiru ba a amsa mishi ba , ko karar ruwa ba ya ji
Hakan ya sa ya kai hannu ya tura kofar a hankali amma sai ya ga toilet din babu kowa a ciki

Da sauri ya juya ya fice dakin ya nufi dakin Moussa dai'dai lokacin da shi ma ya ke shirin fitowa har su ka bidi yin karo


Da sauri Moussa ya ce mishi " lafya ka ke irin wannan sauri haka ? "

" ba ka ga inda yarinyar nan ta shiga ba , na diba bedroom di na ba ta nan "

" kontar da hankalin ka ta na cikin gidan nan mana ya wuce ta na kitchen "

Tun kafin ya gama rufe bakin shi Zayd ya juya da sauri ya bar wajen
Kai tsaye kitchen ya nufa

Tun kafin ya shiga kitchen din ya gan ta ta fito rike da tray , ta na sanye da wando palazzo sky blue da t-shirt fara ta saka hijab zuwa kirji shi ma sky blue

Ya na ganin ta ya sauke ajiyar zuciya ya lumshe idanun shi

Ita kuma ta na ganin shi ta saki murmushi ta ce " yanzu da na ke shirin na je na yi muku magana da yaya Moussa ku zo muyi breakfast "

Ta kai karshen ta na shiga dining room ta ajiye tray din hannun ta saman dining table ta janyo chair ta zauna


Ya na kallon ta har ta zauna sannan ya tako cikin dining room din ya janyo kujerar da ke fuskantar ta ta ya zauna dai'dai lokacin da Moussa ya fito corridor

Ya na ganin su hakan ba karamin burge shi ba ya yi , sai da ya ciro wayar shi da ga cikin aljihu ya yi musu hoto a haka sannan ya karaso cikin dining room din ya na sallama


A tare su ka amsa mishi amma ta Inaya a ka ji Zayd cen kassan makoshi ya amsa mishi

Chair din geffen Zayd ya janyo ya zauna
Serving din su ta fara yi sannan ta gyara musu coffee su ka fara yin breakfast


Ko wane ya dukar da kai sai cin abincin shi ya ke cikin konciyar hankali

Cen su ka tsinci Muryar Inaya ta na fadin " yaya Zayd ka san ina ne Daular Saudiya ? "


Dum ya ji gaban shi ya fadi , a dubu dari su ka dago kai shi da Moussa su na kallon ta

Kan ta na sunkuye sai cin abincin ta ta ke kamar ba ita ta yi magana ba

Zayd na shirin magana Moussa ya riga shi cewa " ina ki ka jiyo wannan sunnan "

Daga kafadun ta ta yi allamun ban sani ba kafin ta ce " kawai ya shigo min a kai ne "

Kallon Zayd Moussa ya yi, shi ma Zayd Moussan ya ke kallo ya na son ya yi magana amma ya kassa kawai sun kurawa juna ido babu mai bakin magana


Sai da su ka Kamala breakfast din su , ta tatare dishes din ta kai kitchen

Ta na barin wajen Moussa ya ce ma Zayd " ya a ka yi ta san Daular Saudiya ko dai kai ka fada mata ? "

Girgiza mishi kai Zayd ya yi kafin ya ce " no ban fada mata ba "

" to ya akayi ta san hakan dan ni ma fa ban taba fada mata ba "

Shiru Zayd ya yi ya na tunanin wani abu , sai da ya jima bai ce komai ba sannan ya mike ya nufi falo ya zauna saman doguwar sofa

Ya na zama Moussa shi ma ya tasso ya zauna geffen shi ya na kallon shi
Su na a haka Inaya ta fito da ga kitchen ta karaso cikin falon ta zauna saman sofa two seaters ta fara kallon Tv


Da ga haka ba wanda ya sake cewa wani abu kowa ne ya fada duniyar tunanin shi

Ba su tashi da ga wajen nan ba sai da su ka ga lokacin sallat ya yi , sannan Zayd da Moussa su ka tashi a tare su ka tafi bedroom din su dan su yi Alwalla


Jim kadan su ka fito Moussa ya na sanye da jallabiya fara amma shi kuma Zayd ya saka trouser black da shirt red


Nan su ka ce da ita sun tafi mosque , da to ta amsa musu kafin ta tashi ta shiga bedroom din Zayd dan ita ma ta yi sallat



Misalin karfe 7 na dare ( bayan sallar isha )

Inaya

Zaune su ke cikin falon gidan su na kallon film a Tv , Moussa da Inaya su na hirar su Zayd kuma ya na zaune kamar gunki ya zubawa Tv ido


Su na a haka su ka jiyo a na sallama

Kallon Moussa Zayd ya shi ma kallon shi ya yi irin kallon nan ka na jiran wani

Su na a haka su ka ga Inaya na shirin tashi ta je ta dubo ko waye
Da sauri Zayd ya mike ya ce " zaune zan je na duba " ya na fadar haka ya nufi door ya fice


Ya sha ruwan mamaki ganin malam cikin gidan shi cikin wannan gidan ga kuma duk yanayin shi a birkice da allamun wani abu ya faru


Da sauri Zayd ya yi kan shi ya na fadin " uncle ya na gan ou cikin wannan halin, lafya dai ko ? " sai jero mishi tambayoyi Zayd ya ke ya ki tsaya ya ji abun da ke faruwa


Wasu yawu malam ya hadiye kafin ya ce " Zayd ina cikin tashin hankali " ya fada kamar zai yi kuka


Dafa kafadar shi Zayd ya yi ya ce mishi " mu shiga da ga ciki uncle sai ka fada min " ya kai karshen ya na yi mishi bismillah da hannu


Da sauri malam ya girgiza mishi kai kafin ya ce " Zayd ba zan iya shiga ciki ba , Idan auta ta ji abun da ke faruwa matsalar za ta zame min biyu dalilin da ya sa na kassa shiga ciki dan kar ta gan ni "


Katse shi Zayd ya yi da cewa " uncle kontar da hankalin ka , ka yi min bayani yadda zan gane wane ya faru ne ? "


Ajiyar zuciya malam ya sauke kafin ya ce " Zayd , Nesrine ce tun safe da a ka aike ta cepane har yanzu ba ta dawo ba , yanzu haka da ga police station mu ke ni da Abdoul na kassa hakura ya sa na zo na fada maka ka taimaka mu tafi neman ta " ya kai karshen kamar zai yi kuka

TIR KASHI , YANZU KUMA INA NESRINE TA SHIGA
HMMMM NI DAI NA DASSA AYA A NAN SAI MUN HADE GOBE 🤘



❤⚘ EXILED PRINCE ⚘❤
(LOVE MEETS POWER ) 👑🔥


( A heart touching love story , Romance , injustice & destiny )



STORY & WRITTEN BY : ANISH


Marubuciyar littafin
TAURIN ZUCIYA 💖💍🌺

https://whatsapp.com/channel/0029VaGhJCqKmCPUvpvIJ80i

♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡

PAGE 19 ❤🔥


Dan lumshe idanun shi Zayd ya yi ya kara bude su a hankali kafin ya ce " uncle calm down , yanzu ka fadawa mamar ta abun da a ke ciki ? "

" to ya zan yi Zayd dole ta san abun da a ke ciki, yanzu haka da na baro ta ta na kuka sai da Abdoul ya samu ya rarrashe ta "


Jinjina kan shi Zayd ya yi kafin ya ce " okay ! Yanzu uncle ka koma gida ku kontar da hankalin ku, duk inda ta shiga zan nemo ta amma ku bari har da safe "


Da sauri malam ya katse shi da cewa " Zayd har da safe fa ka ce , gaskia bazan iya ba mu tafi yanzu don Allah kar aje wani abu ya same ta "

Girgiza mishi kai Zayd ya yi ya na fadin " no uncle ba abun da zai same ta, yanzu ko mun fita ina za mu je neman ta , mu jira mu gani ko da ma su garguwa da mutane ne za su kira mu , idan ba haka ba gobe sai mu je police station, amma cikin wannan daren ba abun da za mu iya yi "

Haka dai ya yi ta lalaba shi har ya hakura ya koma gida nan ma sai Zayd ya raka shi har gida su na tafe ya na kara kontar mishi da hankali


Bayan ya raka malam gida ya dawo gidan shi

Yadda ya bar Moussa da Inaya haka ya dawo ya same su su na hirar su

Inda ya tashi nan ya koma ya zauna

Ya na zama Moussa ya kaleshi ya ce " mi ya tseda ka haka ? "

Cikin harshen larabci ya ce mishi " gobe za mu je police station "

Cikin harshen larabci shi ma Moussa ya amsa mishi da cewa " me kuma za mu je yi police station , wanene ma ya zo ? Na ji kamar murya malam "

" e shi ne , yayar wannan yarinyar ce ta bata har yanzu ba ta dawo gida ba tun safe "

" whatt ? Ina kuma ta shiga ? "

" i don't know ! Kawai kai dai ka shirya tun safe mu tafi police station , sannan ka ce da yarinyar nan kar ta fita gobe ko da school ne "

Duk maganar nan da su ke cikin harshen larabci ne su ke yin ta dan kar Inaya ta ji abun da su ke fada

Sai da su ka Kamala maganar su sannan mourir ya kali Inaya ya ce " babyn Zayd ina ga gobe ba sai kin je school ba "

Da sauri ta kaleshi ta marairaice fuska ta ce " why yaya Moussa gobe fa monday "

Moussa na shirin magana Zayd ya riga shi cewa " na san gobe monday , ina neman muku admition cikin sabuwar makaranta ke da yayar ki , so ba sai kin je ba "

Jinjina mishi kai tayi ba dan ta so ba ta ce " shikenan yaya Zayd "

Ta na fadar haka ta tashi ta nufi corridor ta shiga bedroom din Zayd

Ta na barin wajen Moussa ya kali Zayd ya ce " ka tashi ka je ka rarrashi babyn ka , ba ka ga ran ta ya baci "

Ko kallon shi Zayd bai yi ba ya ci gaba da kallon Tv

Girgiza kan shi Moussa ya yi cikin ranshi ya ce " duk ranar da soyayyar ta ta kama ka wlh ba za ka yi da sauki ba , ba kai ba izza da miskilanci za ka gane kuran ka "


Da ga haka ba wanda ya sake cewa wani abu har wajen karfe 11 na dare su ka tashi daya bayan daya kowane ya koma bedroom din shi


Zayd

Bayan ya shiga bedroom din shi ya isko ta na konce saman bed din shi ta yi rub da ciki ta na sanye da kayan barci fara har ta yi barcin ta


Kai tsaye toilet ya wuce ya yi wanka
Jim kadan ya fito sanye da bathrobe, kai tsaye closet din kayan shi ya nufa ya dauki kayan barcin shi , shi ma farare ya koma toilet

Bayan minti biyar ya fito sanye da kayan barcin shi ya nufi bed din shi

Geffen ta dan nesa kadan ya konta ya na kallon ceiling ya daura hannun shi daya saman goshin shi daya dayan kuma saman cikin shi , ya lumshe idanun shi kamar mai barci


Ya dan jima a haka kafin ya bude idanun shi a hankali ya juyo da kan shi ya na kallon ta


Ya na tsaka da kallon ta ta juyo suna fuskantar juna , duk gashin kan ta ya zubo ya rufe mata fuska ta zama kamar wata aljana


Sai da ya dauki lokaci ya na kallon ta a haka kafin ya kai hannun shi slowly ya janye mata jelar gashin ta


Kamar jira ta ke ya na janye mata ta bude idanu ai ko sai cikin nashi sai da ta ji tsoro lokacin da ta ci karo da Hazel eyes din na shi

Da sauri ta yi baya za ta tashi da ga saman gadon

Hannun ta ya riko ya lumshe idanun shi dan ya san su ne su na bata tsoro cikin wata cool voice ya ce " dawo ina za ki je "


Cak ta tsaya ta lumshe idanun ta ta koma ta konta ta na sauke ajiyar zuciya

A hankali ta juyo da kan ta ta na kallon shi , ganin ya lumshe idanun shi ya sa ta cewa " yaya Zayd lafya ka rufe idanun ka "


Ba tare da ya bude su ba ya ce " no kar ki damu konta ki yi barchi ki "

" to Amma yaya Zayd ka bude su mana in gani "

" ba za ki ji tsoro ba , la ga kin tsorata da farko shi ya sa na rufe su "

Dan matsowa ta yi kusa da shi kadan , ta rage sautin Muryar ta ta ce " ka bude ba zan ji tsoro ba yaya Zayd "


Jinjina mata kai ya yi kafin ya fara bude idanun shi slowly , sai cikin nata dan ita ma shi ta ke kallo


Haka su ka tsaya su ka kurawa juna ido babu ko kiftawa duk sun kassa janye idanun su

" wai me ya ke shirin faruwa da ni ne haka, duk lokacin da na kalli yarinyar nan sai na ji zuciya ta ta yi min wani sanyi, why ? Na ke jin haka , na san a shekaru na ninka nata amma me ya sa ko wane lokaci na ke ganin kamar ta na dai'dai da ni ? " ya fada cikin ranshi ya na tsare ta da wadanan hazel eyes din na shi


Ita cikin ranta cewa ta ke " ban san dalilin da ya sa ni ke maka irin wannan son haka , why kai ma baza ka so ni ba ? " ta na fadar haka ta saki wani cool murmushi ta lumshe idanun ta slowly


A hankali shi ma ya lumshe idanun shi , ba jimawa barci ya yi gaba da su


Washe gari


Misalin karfe 8 na safe , Zayd da Moussa su ka bar gidan , su ka bar Inaya ita kadai ta na ta barci dan yau ba school ba za ta je


Gidan malam su ka nufa , dai'dai sun isa bakin kofar gidan , malam da Abdoul su ka fito da ga cikin gidan su na ta sauri har su ka wuce Zayd da Moussa ba su sani ba


Da sauri Moussa ya taro su ya na fadin " uncle ina zuwa haka "

Juyowa malam ya yi ya kaleshi ya ce " zan je police station na gaji da zaman jiran nan "

Jinjina kan shi Zayd ya yi kafin ya fara takawa ya na rike da hannayan shi a baya ya yi gaba ba tare da ya ce musu komai ba


Da sauri malam da Abdoul su ka bi bayan shi tare da Moussa
A haka su ka jera su ka nufi police station


Sun dauki wajen good 10 minutes su na tafiya kafin su iso police station

Zayd ne ya yi magana officer din bayan ya gaishe da shi ya ce mishi ya na son ganin DPO

Nan officer din ya ce mishi " sai dai ka yi hakuri in kara ce ku ka kawo ni za ku fada ma ba DPO ba "

Cikin sanyi Zayd ya ce mishi

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login