Showing 69001 words to 72000 words out of 75226 words
ni , sai yanzu da na bude ido "
Rungume ta tsam malam ya yi ya na fadin " ki kontar da hankalin ki , va abun da zai faru kin ji ko "
Kassa amsa mishi ta yi saboda kukan da ta ke , haka ya shiga rarrashin ta har ya samu ta yi shiru su ka yi zugum waje guda kowa da irin abun da ya ke sakawa a cikin zuciyar shi
After two days
Kwana uku yanzu kennan da kontawar Zayd doguwar suma , a kullum bugun zuciyar shi kara rayuwa ya ke tun likoci na san ran zai tashi har ya kai sun daina , Moussa kuma kamar ya yi hauka don ya san idan Zayd bai tashi ba tabass shi ma sai ya bi shi
Adu'a babu dare babu rana ya ke samu da ga wajen mama dan ba abun da ke tada ta da ga saman sallayar ta , kullum ta na cikin yi wa ahalin na ta adu'a
Ga shi kuma har yanzu malam da Inaya shiru , sun je police station din amma abun mamaki sai dai a ce musu su je gobe su dawo , sau uku Abdoul ya na zuwa police station kai kara amma kullum su ce mishi ya dawo gobe har ya gaji ya bar zuwa ya mika al'amarin wajen ubangiji , ko da ma su satar mutane ne za su kira su
Nesrine ma ba a bar ta a baya ba wajen yi ma yan uwan ta adu'a , dan yanzu ta samu dauki amma ba sosai ba , a yanzu kuma ita ke debe ma Moussa kewa ta na taya shi hira duk lokacin da su ka je kai mishi abinci likita dan har yanzu su na cen shi da Zayd
In mu ka leko malam da Inaya kuma , tun ranar a ka sa su cikin wannan dakin , ba a sake waiwayar su ba , abinci ma sau biyu a rana a ke basu, shi ma bai fi ka yi spoon biyu ko uku ba
Amma a haka har su na samun damar su mika kukan su ga ubangiji, kullum cikin adu'a su ke ita da malam babu fashi
Misalin karfe 10 na safe
Yau dai kwana hudu da faruwar wannan abun
Inaya
Konce ta ke ta tada kai da cinyar malam, ya sa hannu ya na shafa mata kai ya na karatun kur'ani
Su na a haka su ka ga an bude kofar dakin
Da sauri malam da Inaya su ka datse idanun su dan sun saba da duhun dakin
Ba su kai ga bude idanun su ba su ka ji an dauke su an mikar da su tsaye a na fadin " mazza ku fita "
Riko hannun Inaya malam ya yi su ka fito wannan dakin
A hankali su ka fara ware idanun su , su na bin wajen da kallo
Wani katon falo ne , dauke da duk wasu kayan more rayuwa , da ga sofa har zuwa su Tv , amma komai black colour ne dakin duk zagaye ya ke da irin wadanan gardin da ya dauke Inaya sun kai su goma , kowa sanye da bakaken kaya fuskar a daure tamau kamar hadari , sai shan tsami suke
Cen su ka hango wani bokan zaune tsakiyar falon ga wata kwariya cike da wasu ruwa jajaye a gaban shi, sai wani karatu ya ke mara dadin ji
Su na tsaye su na kallon shi wani ya turo malam ya yi gaba zai fadi
Da sauri Inaya ta taro shi ta na fadin Abba
Riko hannun ta ya yi ya na fadin ba komai , sannan ya mike su ka karaso cikin falon
Cak malam ya tsaya ya na zaro idanu , zuciyar shi na duka uku uku
Ba komai ba ne ya gani face Youssef , ya yi wani zaman kasaita saman sofa geffen bokan ya na kallon malam ya na sakin wani makirin murmushi
Ya na ganin malam ya tsaya ya bushe da wata shegiyar dariya kafin ya mike tsaye ya karaso gaban malam ya tsaya ya na fadin " ohhhh Ibrahim , yaushe rabo " ya kai karshen ya na rungume malam
Shi dai malam ya kassa motsi sai kallon waje guda ya ke ya na faman muzurai da ido
Ganin bai motsa ba ya sa Youssef sakin shi ya yi baya kadan ya kali Inaya,
Wani cool murmushi ya saki kafin ya ce " my daughter gaskia kin girma ba ki dai manta da uncle din ki ba " ya kai karshen ya na kai hannu zai taba fuskar ta
Cak ya ji malam ya damko hannun shi
Da sauri ya dago kai ya na kallon malam
Cikin dakiya malam ya ce " kar ka kuskura ka taba min yarinya ta "
Murmushi Youssef ya yi kafin ya kauce hannun shi ya juya ya koma sofar da ya taso ya zauna ya kali bokan ya ce " Barbushi ga yarinyar da na ke baka labarin ta "
Dago kai barbushi ya yi kafin ya ce " tabass ita ce , dan ina jiyo kamshin arzikin ta , amma auren ka da ita ba zai yi yu ba "
Mikewa tsaye Youssef ya yi ya na fadin " what kamar ya bazan iya auren ta ba "
Barbushi na shirin magana malam ya riga shi cewa " Youssef kenan dama ba Sudais ka yi niyar aura ma ita ba , kai ne za ka auri yarinyar da ka yi jika da ita, saboda me Youssef , kawai saboda abun duniya , wlh ka ji tsoron Allah "
Cikin tsawa Youssef ya katse shi da cewa " kai don Allah ya isa haka , lokacin da ka ke ci moriyar kudin ka , ka ji tsoron Allah ne , a tare mu ka fito neman aiki amma duk ka fi mu kama kudi duk da waje guda mu ke aiki , don Allah ya ba ka shi ne za ka yi wa wasu bakin ciki, wlh wlh duk yadda za ayi ko da in kashe ka ne sai na auri Inaya , wannan arzikin da ka ke ci ni ma sai na ci shi "
Wasu hawaye ne ma su zafi su ka zubo ma malam ya na fadin " haba Youssef wane arziki kuma , dubi inda Allah ya kai ka duk da ba ta hanyar halal ba , amma wane arziki za ka nema bayan wannan da har za ka cutar da rayuwar yarinya ta , na roke ka ka kyale mu mu tafi "
" Ibrahim bazan kyale ku ba , a yau din nan a wajen nan sai na auri Inaya , ai na ga ba kudi ne ba kadai arzikin ta ba ko ? " ya kai karshen ya na sakin wani makirin murmushi
" ina lillahi wa'ina illaihi raji'un , haba Youssef da girman ka , yanzu ko kunyar fada min wannan maganar ba ka ji ba , kai con ka wlh , ka yi girman banza , Allah waddaran hali irin na ka Youssef na yi nadamar abotar mu , ta Allah ba ta ka ba wlh ba ka isa ka taba mamana ba , aure kuma ya haram ta tsakanin ku " ya kai karshen cikin kunar rai
Duk abun da su ke fada Inaya na geffen malam rike da hannun shi sai in wannan ya yi magana ta kale shi , in wannan ya yi ta dawo da kallon ta gare shi
Youssef na shirin magana barbushi ya riga shi cewa " gaskia ya fada ba za ka iya auren ta ba , saboda mijin ta na a raye har yanzu bai mutu ba "
Kallon barbushi Youssef ya yi cike da rudu ya ce " kai barbushi ya isa haka, kar ka manta ko ni wanene , a yau din nan sai na aure ta "
Dariya malam ya yi ya na fadin " ai auren ku ba zai yi yu ba , domin Inaya dai da ke gani matar wani ce , shekara biyu yanzu da na mata aure " ya kai karshen ya na sake bushewa da dariya
Wannan maganar ba karamin konawa Youssef rai ta yi musaman dariyar da ya ga malam na yi abun ya kona mishi rai
Cikin fushi ya kai hannu bayan shi ya fido gun ya harbe malam a zuciya
Kara Inaya ta saki ta na toshe kunnuwan ta ta rumtse idanun ta da karfi , zuciyar ta na bugu da karfi
A hankali ta bude idanun ta ta na kallon kassa , sai ganin malam ta yi konce a kassa ya dafe saitin zuciyar shi , babu rai a jikin shi
Wata irin razananiyar kara ta saki ta na zubewa saman guyiwowin ta ta talabo kan malam ta na fadin " Abba , Abba ka tashi don Allah kar ka tafi ka barni na roke ka , wayoooo ni Allah na Abba " ta kai karshen ta na sakin sabuwar kara da ga nan ta sunkuyar da kan ta , ta gama goshin ta da na malam ta na kuka kassa kassa
Ta na a haka ta ji Youssef ya riko hannun ta ya na fadin " ke tashi mu tafi "
Shiru Inaya ta yi , ta lumshe idanun ta ko motsi ba ta yi
Daka mata tsawa Youssef ya yi ya na fadin " ba za ki tashi ba ko dai ke ma na kashe ki "
A dubu dari Inaya ta dago kai
A razane Youssef ya saki hannun ta ya ja da baya ya na zaro idanu
Ba karamar razana ya yi ba ganin yadda idanun Inaya su ka koma bakake kirin ko digon fari babu
Bai ida shan mamaki ba sai da ya ga ta mike tsaye, cikin wata irin murya mai sauti ta ce " kai ne ka kashe min Abba na " ta kai karshen ta na takowa gaban shi
Da sauri Youssef ya yi baya ya na fadin " barbushi me ya samu idanun ta haka "
Mikewa tsaye barbushi ya yi ya na kallon Inaya ya ce " ba ita ba ce , aljanun ta , su ne s....."
Bai kai karshen maganar shi sakamakon juyowar sa Inaya ta yi ta wurga mishi wani mugun kallo sai da ya sha jinin jikin shi
Nuna shi ta yi da dan yatsar ta , a hankali ta fara yin sama da yatsar
Nan take shi ma barbushi ya fara yin sama cikin iska ya na rike da wuyan shi da hanayan shi biyu , ya na reto da kafafun shi kamar wanda a ka shake
Sai da ya daina motsi ya koma ga m'halluciné shi , sannan Inaya ta sauko da yatsar ta kassa , barbushi ya Zube a wajen
Barbushi na faduwa a wajen waddaran katin gardin da ke zagaye da dakin su ka fara bacewa bat bat daya bayan daya
Kenan dama ba mutane ba ne
Youssef na ganin abun da ke faruwa ya saki wata irin kara kamar mace ya juya da gudu zai bar wajen
Amma ina ya na juyawa ya ga Inaya tsaye a gaban shi , duk ta sauya kamar ba ita ba
Zubawa ya yi saman guyiwowin shi ya rike hannayan shi ya na fadin " don Allah ku bar ni na tafi , ina da iyali , don Allah ku kyale ni "
Shiru Inaya ta yi ta na kallon shi
Sai da ta dan jima kafin ta dago da yatsar ta slowly ta nuna shi , ta fara yin sama da yatsar
Kamar yadda ta yi da barbushi, haka shi ma Youssef ya yi tsaye cikin iska ya na reto , hannayan shi duka biyu a wuya an shakke qui
Sai da ya bar motsi sam , sannan ta tila shi gefe da karfi ya bugi bango
Bayan ta tila shi ta dawo da kallon ta kan malam
Nuna shi , shi ma da dan yatsa ta yi , nan take ya fara reto cikin iska a konce
Kamar ta san hanyar fita ta juya ta nufe ta, ta na taku kamar namiji , gawar malam na biye da bayan ta cikin iska
❤⚘ EXILED PRINCE ⚘❤
(LOVE MEETS POWER ) 👑🔥
( A heart touching love story , Romance , injustice & destiny )
STORY & WRITTEN BY : ANISH
Marubuciyar littafin
TAURIN ZUCIYA 💖💍🌺
https://whatsapp.com/channel/0029VaGhJCqKmCPUvpvIJ80i
♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡
PAGE 29 ❤🔥
Fitowa tayi ta ga harabar gidan cike da sojoji , da motoci wajen goma
Sojoji na ganin ta su ka shiga tayi tayin su musaman da su ka ga idanun ta baki kirin
Da sauri su ka saita ta da gun sa fadin ta tsaya nan
Amma ina sai ci gaba da takowa ta ke ta na shirin barin wajen
Har za ta bar gidan gonar ta tsaya ta juyo ta nufi wata motar ta bude gidan baya gawar malam ta shiga ciki
Ita kuma ta juyo ta kali sojojin da su ka saita ta da gun , hanayan su sai kerma su ke dan tsoro , sun ma rasa ya za su yi da ita , idan su ka ce su harbe ta , in ba ta mutu ba to tabas su za su mutu
Nuna guda cikin su ta yi kafin ta ce " zo ka meda ni gida "
Da sauri ya saki gun din hannun shi ya nufi motar da gudu ya shiga gidan driver, Inaya kuma ta shiga wajen mai zaman banza
Ta na shiga ya tada motar ya bar wajen da gudu
Ita kuma ta jingina a bayan kujerar ta lumshe idanun ta ba ta sake cewa wani abu ba
Sai da su ka yi tafiyar wajen good one hour kafin su iso cikin gari , nan ta ke ce mishi ya kai ta babban private Hospital
Ba musu ya kama hanyar babbar private Hospital , inda a ka kontar da Zayd
Cikin abun da bai fi 15 minutes ba su ka iso Hospital din
Ta na jin motar ta tsaya, ta bude idanun ta slowly
Wannan karan dai idanun ta sun dawo dai'dai
A hankali ta bude kofar ta , ta sauko da ga cikin motar ta na ce ma sojan nan ya sauko da gawar mahaifin ta
Ita kuma ta nufi hall din Hospital din ta shiga
Ta na shiga ta ci karo da Abdoul , ya na sauri zai je gida ya dauko su mama
Ya na ganin ta sai da zuciyar shi ta buga , ya na zaro idanu ya ke kallon ta ya ce " Inaya , ke ce ? " ya fada cikin rudu
Ita kuma ko tsaya wa sauraron shi ba ta yi ba ta yi gaba abun ta
Ya na shirin bin bayan ta ya ga sojan nan dauke da malam a saman kafada
Da sauri Abdoul ya nufe shi ya na tambayar lafia , ya na gama fadar haka ya dinga kwala wa nurse kira
Da sauri su ka nufo shi ture da gadon jinya
Su na isowa sojan nan ya kontar da shi sama sannan ya juya da gudu ya bar wajen dama a kage ya ke ya tsere
Ya na kontar da malam , Abdoul ya ga uban jinin da ke zuba da ga kirjin shi , dan zaro idanu ya yi ya na fadin " Abba ! Abba "
Bai gama rufe bakin shi ba nurse din nan su ka tura gadon su ka shiga A&E room doctor na biye da bayan su
Su na shiga room din Abdoul ya juya da gudu ya bi bayan Inaya da ta nufi dakin da a ka kontar da Zayd , kamar ta san inda ya ke
A hankali ta tura kofar ta shigo ta sallama
Moussa da ke zaune saman wata sofa cikin dakin , ya dago kai ya na amsa sallamar
Ya na ganin ta ya mike tsaye cike da rudu ya ke fadin " sister , ina kuma ki ka shiga "
Ita ko kallon shi ba ta yi , idanun ta na kan Zayd da ke konce saman gado , hannun shi sanye da catheter a na yi mishi Karin ruwa , jikin shi sanye da wasu kaya blue irin na ma su jinya
Nan take idanun ta su ka kawo ruwa , da gudu ta nufe shi ta fada saman kirjin shi ta na sakin kuka ta na fadin " yaya Zayd don Allah ka tashi kar ka bar ni kai ma , na rasa Abba na a yau , bazan so na rasa ka ba a rana guda, don Allah ka tashi " ta kai karshen ta na kai mishi bugu a kirji
Shi dai Moussa, da Abdoul sun tsaya su na kallon ta an rasa mai cewa wani abu
Su na a haka su ka ji Zayd ya ja wani dogon nunfashi har sai da kirjin shi ya yi sama sannan ya koma
Da sauri Moussa da Abdoul su ka yi kan shi su na ambatar sunan shi , Inaya na konce saman kirjin shi sai kuka ta ke
Da gudu Moussa ya fita da ga dakin , jim kadan ya dawo tare da doctor ya nuna mishi Zayd ya na fadin " don Allah doctor ka duba shi , wlh duk a tsorace na ke kar a je mutuwa ya yi "
Jinjina mishi kai doctor ya yi kafin ya nufi Zayd ,
Ya na isa ya ce da Inaya " madam tashi na duba shi "
Girgiza mishi kai tayi cikin fitar hayaci ta ke fadin "